Babi na 174-175
***
Haka wannan maɗaukaka uku suka ci gaba da tafiya acikin gajimare tsahon lokaci wanda babu yasan iyakacinsa. Domin kuwa shekara a wajen waɗannan ma'abota izza kamar daƙiƙa take. Basa tsufa kuma basa zancen mutuwa a al'amuransu.
Bayan tsahon lokaci suka iso titin Bayajidda inda a lokacin Hidaya ta dubi Amaraikugyu ta ce, "kana raye a lokacinda Tarifil-fakta ya gina wannan titi?"
Amraikugyu y girgiza ya ce, "A'a, amma kakana Andil Bayajidda dashi aka gina. Na gani acikin rubuce-rubucensa yana cewa Tarifil-fakta yayi niyyar amfani da wannan titi ya afkawa doron ƙasa na farko to amma ɓoyayyun al'amura suka sha kansa. Tunda Tarifil-fakta ya kammala wannan titi ba'a ƙara ganinsa ba. Amma dai yana nan a raye kuma a lokacinda ya gama shiri zai bayyana."
Suna haura titin Bayajidda suka fuskanci cewa rana ta fara sakkowa ƙasa-ƙasa. Suna ƙara matsawa tana ƙara yiwowa ƙasa. Ana cikin haka sai wata ya bayyana ya fara sakkowa ƙasa. Kan kace meye wannan rana da wata sun sakko ƙasan duniya. Daga inda Hidaya take tana iya hangen rana da wata sun tokare hanya sama da ƙasa kai kace wata katafariyar katanga ce.
A dai-dai ƙasan rana da watan suka hangi wani ƙaton garin wanda yake kewaye da badala. Tsahon badalar ya tokare da sararin samaniya. A jikin katangar akwai koriyar gansa-kuka wadda ke nuni da tsabagen shekaru. Kana gani kasan wannan katanga ta shekara aru-aru ana damawa da ita.
Amraikugyu ya nuna garin ya ce, "Garin Ƙayyiduba kenan, garin da aka fara bautar rana da wata a ban ƙasa. Kina matsawa kusa dashi bada izini ba rana da watan dake saman garin zasu ƙone ki har lahira."
Hidaya ta dube shi ta ce, "Zan samar maka hanya amma ban yadda da maganarka ba. Kafin nayi wani abu ina buƙatar ALƘAWARIN IZZA?"
Hidaya ta fiddo da wata takarda daga jakarta ta miƙa masa. Amraikugyu ya fasa ɗan'yatsansa ya zuba jini akan takardar. Takardar tayi haske sannan ta zuƙe jinin. Ita ma Hidaya ta zuba jininta akan takardar.
Irin wannan alƙawari shi ake kira da Alƙawarin Izza. Duk wanda yayi shi dole ya cika ko kuma izzarsa ta tarwatse.
Bayan kammala komai Hidaya ta tunkari garin gadan-gadan. Babu kowa a ƙofar garin. Kuma ƙofar a ƙulle take. Idan bakai amfani da Yanayin-izza ba sai kace ba kowa aciki. Amma Hidaya tana jin motsin halittu jinsi daban-daban wanda aƙalla sunkai jinsi ɗari. Kowa yana harkokinsa.
Tana ƙarasawa bakin ƙofar wani mai gadi ya daka tsawa, "Koma wacece, koma daga ina kike ki juya bama buƙatarki. Baza mu buɗe ƙofar garinmu ga kowa ba. Idan kunne yaji jiki ya tsira."
Hidaya tayi kamar bata jiba taci gaba da tunkarar ƙofar garin. Nan take ragowar masu gadin suka taso a fusace. Kafin su ƙaraso rana da wata dake sama suka nufo Hidaya da mugun nufi. Dukkan dubunnan mutanan dake cikin garin suka hangi abinda ke faruwa saboda haka sukai azama wajen tara hankalinsu akai domin suga maike faruwa.
Garin Ƙayyuduba gari ne wanda sukan shafe shekara ɗari ba tare da sunga baƙo ba, saboda haka da kansa sarkin garin ya taso ya nufo ƙofar garin.
Rana da wata da sarkin garin da masu kareshi da masu tsaron ƙofa. Kai harma da mutanen gari tsoffi da yara kowa hankalinsa ya yiwo kan ƙofar garin.
Ana cikin haka Hidaya ta buɗe idanunta masu izza. Wani haske ruwan ƙasa ya fara ɓulɓula daga ciki. Kan kace meye wannan hasken ya dusashe hasken rana da watan dake tunkaro ta. Nan take rana da watan dake ƙoƙarin halaka ta suka tsaya cak a sama kamar suna tsoron ƙarasowa.
A dai-dai wannan lokaci Sarkin garin da ragowar muƙarrabansa suka ƙaraso. Sarkin na ganin abinda ya faru ya zube a ƙasa yayi sujjada ba tare da cewa komai ba. Suma ragowar mabiya, duk da basu san dalili ba suka zube a ƙas.
Hidaya ko kallonsu batai ba ta tashi sama akan iska ta nufi inda rana da watan suka tsaya. Duk tsananin zafin dake tashi daga cikin ranar ko'a jikinta.
A ranta tana cewa, "ba lalle na ƙara samun wannan dama ba. Wannan shi ne kaɗai wajenda a duniya rana da wata suke sakkowa ƙasa-ƙasa. Lokaci ne na samarda sabuwar fasaha."
Bayan tsahon lokaci tana nazarin ranar sai ta zauna ta lanƙwashe ƙafa akan iska ta rufe ido ta fara nazari akan sabuwar fasaharta ta rana da wata.
A kwana a tashi mutane na ƙasa sunyi sujjada ita kuma Hidaya na ƙasan rana da wata tana nazari. Sarki Ammgraikugyu ya zauna shima yana kallo. Saida aka kwashe shekaru wanda tun ana lissafi saida aka daina. Sannan Hidaya ta buɗe ido. A idonta na dama hoton rana ya bayyana. Ana hagu kuma hoton wata ya bayyana.
Tun daga wannan rana Hidaya ta sami fasahar rana da wata wadda tayi shura har a doron ƙasa na farko an santa.
Amraikugyu da Hidaya suka wuce ta cikin wannan gari suka kai iyakar ƙasa bakwai. A lokacin Amraikugyu ya warkar da Armad kamar yadda aka alƙawarta. Hidaya ta dawo doron ƙasa na uku shi kuma Amraikugyu ya wuce iyakar duniyar ƙasa bakwai ya shige duniyar dake gaba.
***
A wannan lokaci, a wannan zamani bayan an kammala YAƘIN SARAKUNAN JINZIDAL, Nostaljiya da taimakon Hidaya ta tseratar da Armad zuwa cikin kurkukun Bango.
Tana shiga taji sanyi mai ratsa ƙashi kamar an saka mata tubalin ƙanƙara aciki. Abu na farko data fara yi shi ne rungume Armad ta ƙunshe shi ajikinta yadda sanyin bazai dame shi ba. Sannan ta fito da kwale-kwale daga zobenta ta nufi cikin kurkukun gadan-gadan. Duk bayan lokaci tana waiwayawa ta hangi Hidaya tana fafatawa har ta daina ganinta.
Bayan kwana bakwai ta iso gaɓa. Tunda wannan ne karo na farko data zo wannan waje bata san yadda abin yake ba. Kafin ta ankara ta faɗa ƙasa kamar irin yadda Armad da Babara suka faɗa a baya. Nan take ta fara kiran ɗalasimai a banza. Saida ta shafe awanni sannan ta dira. Taci sa'a ta faɗa cikin wani kudiddifi.
Saboda tsabagen sanyi jikinta ya fara karkarwa haƙoranta na rawa kamar zasu cire. Ta duba ta tabbatar Armad ƙalau yake saboda haka ta fara laluben mafaka. Amma a lokacin ne ta gano cewa akwai wasu mutun biyu zaune daga ɗan nesa sun ɓoye yanayin izzarsu. Suna matsowa suka faɗi ƙasa sukai gaisuwa sannan ɗaya daga ciki ya ce, "Ni suna na Babara wannan kuma shi ne Lamarudu Wilbafos. Munzo nan muna jiranki saboda saƙo da Hidaya ta turo mana cewa zata aiko Armad."
Nostaljiya tayi matuƙar mamaki kuma a zahiri da baɗini bata yadda da wannan mutane ba domin bata taɓa ganinsu ba. Hasalima neman hanyar guduwa daga garesu take. A dai-dai wannan lokaci taji jikin Armad ya fara zafi kamar ana kunna masa wuta. Tana dubaws taga har yanzu a sume yake. Amma kuma hawaye na zuba daga idanunsa. Kafin ta farga taji wata irin iska mai ɗauke matsananciyar izza na tashi daga jikinsa. Ana haka gashin kan Armad ya fara juyewa daga baƙi yana komawa jajawur kai ka kace kwakwalwarsa ce ke ci da wuta. Wani sinadarin Negrinki jajawur ya fara ɓulɓula daga jikinsa yana yin sama kai kace jinin jikinsa ne yake ƙonewa. Take ƙanƙarar dake cikin kurkukun ta fara narkewa. Ran maza ya ɓaci.
Nostaljiya ta tsorata matuƙa da ganin wannan canje-canje ta rasa yadda zatai. Babara ya ɓace daga inda yake ya bayyana a kusa da ita ya fara yiwa Armad tofi yana kiran manyan ɗalasimai.
***
Wannan yaƙi wanda aka sakawa suna YAƘIN SARAKUNAN JINZIDAL ya jawo canje-canje da dama a doron ƙasashen ƙasa. Abu mafi ɗaukar hankali shi ne yadda hukumar ASHURA suka kwace alhakin kula da dokar Jinzidal daga hannun sarkunan Jinzidal suka dawo da ita hannunsu.
Dul'Ururu dashi da Salsa ɗinsa sun sakko daga doron ƙasa ta biyu sun kafa sansani a filin da akai yaƙin sarakunan Jinzidal. A wannan fili anyi katafaren gini wanda ya zama shalkwatar wannan runduna. Sannan kuma rundunar Mayaƙan Ururu tada ta koma hannun sabbin fuska. Wasu Kwamandu guda biyu wanda ake kira da MARUTA da HARUTA. Babu wanda yasan taƙamaiman tarihinsu amma wasu da dama suna ganin ƙannen sarki Kuyurussa'ayi ne uwa ɗaya uba ɗaya. Suna sauka dukkan zanga-zangar da akeyi ta lafa komai ya koma dai-dai tamkar wani abu bai taɓa faruwa ba. Hasalima mutane sun daina zancen sirrin dazai rikita duniya, bawai dan sun mantaba. Sai dan kawai wani sabon tsoro daya cika zuƙatansu wanda ya girmi duk wani tunanin tawaye dake ransu.
An cimma yarjejeniya tsakanin sarakunan Jinzidal da Ururu. Kowa anyi masa alƙawarin Dordor mai matsayi ɗaya da aljaninsa. Sannan kuma bayan an ƙwace fasaha daga hannun aljanu za'a barwa aljanun sarakunan suci gaba da bada kwangila. Abinda kawai ake buƙata daga garesu shi ne suci gaba da yin biyayya tare da mutanansu.
Amma duk da haka a wani sihirtaccen waje dake fadar sarki Bihanzin wata tattaunawa ce ke afkuwa tsakanin sarki Maikiro'Abbas da Sarki Han'ibal da sarki Bihanzin. Sarki Bihanzin ya ce, "a hankali a hankali zasu ƙwace dukkan abinda muka mallaka. Sun kwace sarautar Jinzidal sannan kuma sun saukarda Haruta da Maruta. Mai kuke tunani zai afku nan da shekara ashirin? Ƙasashen ƙasa zasu zama nasu kamar yadda sukaiwa doron ƙasa na farko. Ina kiranku da kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe. Ga wannan Han'ibal. Dukkan abinda kake nema na fasahar dauwamammen sara yana cikin wannan littafi. Na baka shi ne saboda ka gane da kyakkyawar zuciya nazo. Kaima Maikiro'Abbas ga wannan idan ka duba ciki zaka ga sirrin Al'yaya wanda aka manta dashi."
Bihanzin ya basu wasu tsoffin littafai guda biyu. Sannan ya tsaya yana jiran amsarsu.
Dukkansu sun san cewa indai abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka Ururu sai sun kwace komai to amma basu da ƙarfin takara dasu shi yasa suka goya musu baya a yaƙin sarakunan Jinzidal.
Maikiro'Abbas ya dubi Bihanzin ya ce, "wacce fasaha ce dakai wadda idan muka bika zaka karemu daga Ururu? Hatta Hidaya ta kasa, kuma kai baza kace kafi ta ƙarfin izza ba."
Bihanzin ya kyalkyale da dariyar farin ciki kamar daman tambayar da yake jira kenan. "A ƙarni na farko an samarda fasahar jini-uku wadda aka sakawa suna izza. Nima a yanzu na samarda fasahar jini-uku wadda na sakawa suna... LÂIDÀN."
Bihanzin ya tafa hannayensa biyu wani baƙin haske mai kashe ido ya bayyana. Hasken na bayyana idanuwa Maikiro'Abbas da Han'ibal suka zaro cikin mamaki. Duk su biyun suka miƙe suka matso kusa suna kallon abinda ke hannun Bihanzin.
Bihanzin ya ci gaba da cewa, "bayan wannan kuma ina da matafiyan alwashi kuma inada dauwamammen sara. Lallai idan kuka biyo ni baza kuyi dana sani ba domin kune na farko dazan bawa wannan fasaha tawa mai suna Lâidàn."
Bayan Bihanzin ya ɗauke hasken sun dawo cikin hayyacinsu Han'ibal ya dube shi ya ce, "To amma meye matsalar Deniz Iluru? Naji ance yabi ta ƙarƙashin ƙasa ya koma sashin ikwatora."
Bihanzin ya bushe da dariya ya ce, "kada ku manta nine na basu ɗalasiman ƙasashen ƙasan da taswirar da sukai amfani da ita. Dama nasan zasu koma sashin ikwatora. Bama ɓuƙatarsu acikin shirin mu. Yanzu kunga da Armad, ƙanin Hidaya, da Ikenga sai su kashe juna a sashin ikwatora. Kunga kawai Ururu ne suka rage, su kawai zamu kashe mu koma doron ƙasa na farko."
Nan take Han'ibal da Maikiro suka fara tunanin karɓar tayin Bihanzin.
A dai-dai lokacin da suke wannan tattuanawa sauran canje-canje da dama suna afkuwa a sassa daban-daban na duniya.
Wani babban canji daya afku shi ne kame daular Rafiya da Bihanzin ya tura mayaƙan alwashi sukai kafin Ururu su farga. Kaɗan daga cikin Rafiyawa kamar su Rafiyan Nazara sun gudu an neme su an rasa amma da yawa an kame su an sasu a kurkuku. Bihanzin ya kammala fasaharsa ta jini-uku amma babu wanda yasan maiya cimma. Babban abinda ya tsoratar da mutane shi ne yadda Bihanzin ya bautarda Matafiyan Alwashi. Da dama suna yiwa Bihanzin kallon yakai matakin Ururu saboda yadda ake tsoron matafiyan alwashi da kuma yadda suka gagari kowa a baya. Sannan kuma ga tsoron fasahar jini-uku da ake. Idan ka haɗa wannan abubuwa da ƙarfin Bihanzin nada, da kuma yadda yake da tsananin lissafi da hangen nesa zaka fuskanci akwai abin tsoro mai girma a tattare da lammarin Bihanzin.
A dai-dai lokacin da wannan abubuwa ke faruwa Salsan marigayi sarki Daljari suna riƙe da sumammen jikin Niyashi suna gudu akan iska inda mutanen Bihanzin ke ƙoƙarin cimmusu.
A dai-dai wannan lokaci Iliyasis da Cokali da mutane goman da suka karɓi kwangilar Armad suna tsaka da ratsawa cikin kurkukun Bango. Da kyar suma suka sha domin mayaƙan Ururu ne suka bayyana a wajen suka sa tafka. Ba daban akwai Bango ba da basu sha ba.
Cokali ya dubi Iliyasis jiki a mace ya ce, "akwai damuwa. Ya kake ganin Armad zaiyi? Naji labarin yadda suke da yayarsa gashi abinda ya faru."
Iliyasis ya numfasa ya ce, "wannan yaƙin ya tashi damu amma zamu fanshe a yaƙi na gaba. BIHANZIN, DUMAƘISU DA SAURAN SARSKUNAN JINZIDAL KOWA SAIYA BIYA BASHIN DAYA ƊAUKA."
Ba jimawa sanyin dake ratsa jikinsu ya fara raguwa inda suka iso gaɓar kurkukun. Saboda girman kurkukun da faɗinta da kuma kasancewar zaka iya faɗawa ko'ina saida suka shafe sama da sati biyu suna neman Armad da Nostaljiya amma basu gansu.
Daga ƙarshe suka haɗu da ɗaya daga cikin mutane Lamarudu Wilbafos wanda bayan ƴan tambayoyi ya gane mutanen Armad ne ya nuna musu hanya.
Abu na farko da suka gani shi ne Armad zaune kan wani dutse idanunsa a rufe. Gashin kansa ya koma jajawur kaikace wuta ce take balbala acikin kwakwalwarsa. Gashin ya ƙara tsayi ya mimmiƙe tsaye kamar wuta mai ci da balbali. Wani irin sinadarin Negrinki ja na ɓulɓula daga jikinsa.
RAN MAZA YA ƁACI. AN KWANTO KURA.
***
Babi na 176 : Nusi-ya
***
Fada takai fada. Dogarai dubu na tsaye a ɓangaren dama, dubu na ɓangaren hagu. Dukkansu kansu a sunkuye yake. A can ƙarshen fadar sarauniya Nusi ce zaune kan karaga ta kishingiɗa. A gabanta akwai waziri Saiza wanda ya fito daga jinsin jan Dordor da kuma galadima Naru, mutun mai yawan doguwar haɓa da farin gashi, sai kuma sarkin Bai Rayaya a kusa dashi wanda shima ya fito daga jinsin mutane.
Daga wajen fadar akwai dubban mutane na tsaye suna jiran hukuncin sarauniya.
Waziri ya umarci ɗaya daga cikin dogaran, "a shigo da mai ƙara na gaba."
Nan take wata mace mai gashi ruwan ɗorawa ta shigo ta zube a ƙasa tayi gaisuwa sannan ta fara bayani. "Suna na Ƙaulatu. Na kawo ƙarar Aburu mai saida nama a kasuwar Ɗandai. Ya siyi saniyata Ayird dubu takwas da ɗari uku da hamsin amma har yanzu wata uku bai bani cikon kuɗin ba."
Waziri ya kalli wani dogari ya ce, "akawo wanda ake ƙara. Yana rufe baki dogarin ya fice. Ba daɗewa ya shigo da ɗan gajeren mutun mai faɗi."
Mutumin ya zube a ƙasa ya risuna.
Waziri ya daka masa tsawa, "faɗi tsakaninka da wannan mata."
Cikin ƙinƙina ya fara bayani yana cewa, "saniyar data siyarmin sace ta akayi, wannan shi ne dalilin da yasa ban biya taba. Amma.."
Waziri ya ƙara daka masa tsawa, "ciniki ya shiga. A hannunka aka sace saniya saboda haka an baka kwana uku ka biya ta kuɗinta ko kuma ka fuskanci fushin Nusi-ya."
[Ana kiran sarautar Nusi da -ya, saboda haka maimakon ace sarauniya Nusi sai ace Nusi-ya]
Nan take dogarai suka ɗauke shi sukai waje dashi aka shigo da mai ƙara na gaba.
Haka wannan majalisi ya ci gaba da gudana. Amma kana ganin fuskar Nusi kasan hankalinta na wani wajen. Idanuwanta sun ƙara haske sannan kamannin mulki sun bayyana a fuskarta.
La'asar sakaliya aka kammala wannan majalisi. Karagar mulkin da Nusi-ya ke zaune akai tana da dogayen ƙafafu wanda suka miƙe gudu da gaba, yamma da arewa. Dogarai suka gabato suka kama wannan ƙafafu suka ɗauki Nusi zuwa cikin gidan sarautar.
Waziri, galadima da Sarki Bai suka bi baya kansu a durƙushe.
Bayan an ƙarasa an ajiye ta aciki ɗakin tattaunawa na sirri sai dogaran suka basu waje. Waziri ya fito da wasu takardu na sirri daga aljihunsa ya miƙa su ga Nusi-ya.
Bayan ta karanta ta dube su ta ce, "da gaske ne ranar zaɓar sarkin ikwatora na sashi na shida yazo. Dukkan alamu sun nuna cewa Baƙar-guguwa zata bayyana a sashin cikin wannan wata."
Waziri ya numfasa ya ce, "gaskiya ne, Nusi-ya. Kuma daga cikin wanda zasu taka rawa akwai sarkin sashin na yanzu Ƙaraiƙisu. Da sarkin sashi na huɗu Tambaɗisu da waziri Jilani na sashi na ɗaya. Wannan sune manyan gwaraza da zasu taka rawa amma akwai sauran sadaukai wanda suke ganin karansu yakai tsaiko daga dukkanin sashe shida na Ikwatora. Akwai ƙiyasin mutane maitan ga sunayen a wajen sarkin bai."
Waziri ya ƙara durƙusawa sannan cikin ladabi ya ce, "Mutane suna neman wannan kujerar saboda shugabanta kamar shugaban sashin ikwatora ne. A yau da Nusi-ya zata shiga wannan gasa tayi nasara ita ce zata zamo shugabar sashin ikwatora. Sannan kuma a matsayinki na sarauniya baƙar-guguwa ta riga ta zaɓeki, saboda haka koda bakiyi nasara ba guguwar baza ta ciki ba. Zaki dawo gida lafiya."
Nusi ta tari numfashinsa, "bani da ra'ayi. Babban abinda nake son ji shi ne labarin ƴan aikenmu wanda muka su nemo mana hanyar shiga kurkukun Bango."
Galadima shi aka ɗora akan wannan aiki saboda haka ya risuna ya ce, "sun kawo labari mai daɗi Nusi-ya. Sarki Ƙaraiƙisu yana da hanyar da yake bi kuma sunyi ƙoƙari sun gano wannan hanya. Amma har yanzu basu da tabbashi akan ina zata kaika idan ka shiga. A halin yanzu akwai tsaro da yawa a wajen saboda haka basu iya ƙarasawa kusa ba. Amma zarar aka fara yaƙin neman zaɓen, Baƙar-guguwa ta bayyana hankalin masu tsaron zai koma can saboda haka zasu samu damar ƙarasawa."
Nusi ta tambayeshi, "Mutanena nawa ne a wajen?"
Sarkin Bai ya amsa da cewa, "akwai sarkin yaƙi Barilu da Salsa ɗinsa. Da mai unguwa Shísu da Salsa ɗinsa. Da Inyaya [Takobin-Jini] da salsa ɗinsa."
Dukkan sashi na shida na ikwatora babu wanda yakai wannan mutun uku kwarewa a fannin izza domin kuwa babu wanda a cikinsu bai kan matsayin Sammai ba. Nusi da kanta ta umarci sarkin Bai ya zaɓi wanda suka kowa ƙarfin izza.
Nusi ta ce, "Ana fara bikin zaɓe zamu je wajen na gani da idona."
Sarkin bai ya zare ido cikin tsoro ya ce, "Nusi-ya da kanki. Idan arnan daji suka kawo farmaki da matsala."
Yana rufe baki shima waziri ya numfasa ya ce, "nima na yadda da sarkin Bai. Akwai hatsari babba a fitarki. Musamman duba ga cewa akwai Arnan-dajin Felis wanda suke tashe. Naji ance karon-battarsu da sarkin sashe na uku baiyi daɗi ba. Hasalima ance sune sukai masa rauni wanda badan haka ba da shima zai taka rawa a zaɓen sashi na shida. Wasu suna ganin wannan arnan-daji Ƙaraiƙisu suke wa aiki amma dai jita-jita ce."
Galadima ya gyaɗa kai alamun amincewa.
Nusi ta daki tebur ta ce, "wai me kuka ɗauke ni? A halin yanzu indai ba mahaluƙin daya shiga wadin Déba ba babu wani mahaluƙi da nake tsoro. Duk wanda yake ganin cinta ya tare mana hanya."
Yanayin dagiya na furucinta da alamun kafiya a fuskarta yasa sukai shiru.
Bayan an tattauna sauran al'amuran mulki galadima ya miƙa mata sunayen mutun maitan da za suka shiga gasar zaɓen gwani da za'a gudanar a sashi na shida. Wanda zasu shiga cikin baƙar guguwa kamar yadda Nusi ta shiga. Wanda ya sami nasara acikinsu ya zama sarki.
Nusi ta karɓi sunayen sannan ta miƙe ta nufi turakarta. Kuyangi ɗari biyu suka kewaye ta. Bayan ta ƙarasa ta zarce wani sihirtaccen tafki inda tayi wanka ta canja kaya. Sannan ta dawo ɗakinta na sarauniya. Girman ɗakin yakai taku ɗari uku a kowanne ɓangare. Ƙanshi da turare kala-kala na tashi. Wani ƙaton gado ya cika rabin ɗakin. Daga jikin bango akwai hotunan mutane uku an zana su. Armad, Cokali da Iliyasis.
Ta ƙurawa hotunan ido hawaye na zuba daga idanunta. A waje gimbiya ce amma acikin wannan ɗaki budurwa ce wadda ta rasa abin ƙaunarta da kuma ƴan'uwanta.
Bayan lokaci ta kwanta tana kallon sama. Gabda bacci zai ɗauketa taji motsin takarda acikin rigarta. Takardar da sarkin bai ya bata ta sunayen wanda zasu taka rawa a zaɓe mai zuwa.
Ta zaro takardar da niyyar tayi jifa da ita amma ƙaddara takai idonta kan suna na takwas. IKENGA O. BAYAJIDDA.
Take ta miƙe gumi na kwaranya a wuyanta. Ta kwalawa kuyangar dake bakin ƙofa kira.
Kuyangar ta shigo ta zube a ƙas.
"Kirawo sarkin bai. Sannan a shirya siddi, zanyi tafiya zuwa sashi na shida." Nusi ta bada umarni tare da miƙewa ta saka alkyabbarta.
Comments
Post a Comment