"Bazan iya ba." Inji Armad a nutse. "Abu ne a fili: idan ina da wannan izzar mai zai hana a yanzu-yanzu na afka musu na gama dasu a rufe babin kowa ya koma harkokin sa kawai? Na tabbatar idan Ikenga ko Bihanzin nada yaƙinin iya yaƙar mutun uku a lokaci guda kuma suyi nasara da tuni sun afka mana. A taƙaice babu wanda acikin mu yake da wannan ikon. Tambayar daya kamata kuyi ita ce: acikin Ikenga da Bihanzin da Dul'Ururu wanne zamu fara aikawa lahira, sannan kuma yaya zamu yi da sauran a lokacin muna yaƙar sa."
Nan take Babara da Iliyasis suka rusuna, lallai sun yadda akwai kuskure a tambayar su. Hasalima bai kamace su suyi wa Armad wannan tambayar ba a matsayin sa na shugaban su.
"Tuba muke." Inji Babara.
Armad yai shiru yana kallon su kafin kwatsam fashe da dariya. "Tuba kuke? Hahaha... Kunji wai tuba suke? Nusi, kinji Iliyasis yana tuba, Nostee, Babara yana tuba."
Nan take ɗakin ya ɓarke da hayaniya kowa na tsokanar su Babara.
A dai-dai wannan lokacin aljanun dake gadi a waje suka dubi juna cikin mamaki. Wai daman K'Narbig 'babbar izza' tana dariya? Wannan aljanu an ɗebo sune kawai sabida su hana sauti da iska ɗaukan abinda ake tattaunawa acikin tantin su kai wajen da ba'a so. Tuni Armad ya ɗaure tantin tayadda ba komai ake ji ba, to amma duk da haka lokaci-lokaci sauti ɗaya ko biyu yakan wuce ya fita waje (kamar dariyar da Armad yayi yanzu) wanda anan aljanun zasu bada gudummawar su.
Daga ƙarshe Armad ya kaɗa kai ya ce, "Kufa abokai na ne, bani da wanda suka fiku. Duk abinda kuke so ku tambaya zan baku amsa iyakacin sani na."
Wato haka Armad yake, duk yanda sukai ƙoƙarin mai dashi shugaba su ringa girmama shi suna ɗaukaka shi kamar yanda akewa Ikenga da Bihanzin yaƙi. Shi dai kullum a matsayin abokai suke, wanda hakan ba ƙaramin ƙara danƙon zumunci yake a tsakanin su ba.
Bayan ɗan lokaci ana raha Nusi ta nuna taswirar yaƙin dake kan teburin, ta ce, "meye abinyi? Wanne zamu fara afkawa?" A zahiri tambayar ta Armad ce, to amma Armad yana sane yayi shiru yaƙi amsawa domin bawa abokan tafiya damar tofa albarkacin bakin su.
Iliyasis ne ya fara tofa albarkacin bakin sa. "Ikenga zamu fara afkawa. Badan komai ba sabida yana ƙunshe a sashin ikwatora, har ayi yaƙin a gama wani ma bai sani ba."
Nostaljiya ta girgiza kai. "A haba dai, Iliyasis, kana tunanin wani bango ko kurkukun bango zai hana Bihanzin shiga sashin ikwatora? Kuma idan babu Bihanzin ai akwai Ururu. Da kurkukun da bangon duk nasu ne, umarni kawai zasu bayar a buɗe musu hanya. Ko kaɗan bana ganin Ikenga zai fi sauƙi. Amma mai zai hana mu afkawa Bihanzin wanda ke cikin ƙarƙashin ƙasa a ɓoye? Na farko na yadda shiga ƙarƙashin ƙasa matsala ne, to amma muna da zaren izza, haka kuma idan an shiga shi kan sa nemo garin Shadeniz matsala ne, to amma muna da Nusi wadda ƴar asalin garin ce. Har ayi yaƙin a gama ba lallai wani ma ya sani ba. Muna da Armad wanda zai shigar damu, sannan kuma muna da Nusi wadda tasan hanya. Kafin wani ya ankare an gama."
"A'a, kwata-kwata wannan ba dabara bace." Inji Nusi. "Idan dai har shiga ikwatora bai yiwa Ururu da Bihanzin wahala ba, to ai kuwa shiga ƙarƙashin ƙasa bazai yiwa Ikenga da Ururu matsala. Ina ganin ma sai sunfi jin daɗi su tarfa mu a ƙasa."
Nan take hayaniya ta ɓarke. Kamar kullum gida ya rabu ɓari biyu: akwai masu goyon bayan a fara tarar Ikenga (wanda yawanci ƴan gidan Nusi ne) da kuma masu goyon bayan a tari Bihanzin.
Bayan ɗan lokaci Armad ya ɗaga musu hannu. "Ku dakata, duk babu wanda za'ai aciki. Dul'Ururu zamu fara kawar wa kafin Bihanzin da Ikenga."
"EH...?"
Kowa ya juyo suka dubi Armad baki buɗe. Babu wanda ya taɓa tunanin Armad zai yanke wannan shawara duk kuwa da adawar su da Dul'Ururu.
"Ehmm.. Armad, ina ganin rundunar Dul'Ururu (musamman a lokacin nan na kamfen tafi ta kowa ƙarfi, anya kuwa farawa da ita dabara ce?" Inji Nazara.
Akai jim, kafin daga bisani kowa ya gyaɗa kai alamun amincewa.
Take Armad ya canja fuska ya fara bayani a fusace. "Dul'Ururu ya shirya, muma mun shirya. Akwai wanda acikin ku ya fito bai shirya ba? Domin idan akwai to ya koma ya sake shiri. Lallai ina da yaƙinin zamu iya turmuza hancin doron ƙasa ta biyu idan muka haɗa dukkan ƙarfin mu waje guda." Ya ɗakko dutse guda ya ɗora akan sashin ikwatora. "Aljanu sun bani labari akwai rigima a halin yanzu a tsakanin alƙalan sashin ikwatora da rundunar Ikenga. Da farko sun karɓi Ikenga, to amma daga baya yaƙi amincewa ya bautawa baƙar guguwa. A cewar Ikenga baƙar guguwa ce ya kamata ta bauta masa. Tun sanda yayi wannan iƙirari da dama daga cikin alƙalan sun riga sun juya masa baya wanda hakan ya bashi matsala matuƙa wajen haɗa rundunar sa waje guda. A lissafi na Ikenga zai ɗauki wata guda zuwa sama kafin ya daidaita komai. Banda kuma yaƙin da manyan kwamandun sa suke da sarkin-sarki."
Ya nuna garin Shadeniz, ya ce, "shima Bihanzin akwai tasa matsalar: yadda aljanu suka labarta min shi ne akwai rashin jituwa tsakanin Bihanzin da ɓangarori biyu dake mulkin garin Shadeniz. Ɓangare na farko sune ƴan asalin garin Shadeniz. Duk da rufe garin da akai har yanzu suna nan da ƙarfin su da sojojin su. Kuma sunƙi karɓar Bihanzin. A cewar su baƙo bazai mulke su ba. Ɓangare na biyu da suke bawa Bihanzin matsala sune matafiyan alwashi. Kamar yadda Hidaya ta faɗa Bihanzin bai da ikon samun fasahar jini uku, kuma tayi gaskiya. A wajen matafiyan alwashi ya karɓi ɗalasiman fasahar a bisa yarjejeniyar cewa zai basu nasu kason daga ciki. To Bihanzin ya basu fasahar to amma wani abun al'ajabi har yanzu fasahar taƙi karɓar jikin su - sun kasa sarrafa zaren na laidan.
"Wasu daga cikin su suna ganin Bihanzin ne yayi wa fasahar wani abu na mugunta dan kada su samu. Wanda hakan ya jawo kace-nace a tsakanin su. Har yanzu abin bai kai ga zub da jini ba, kuma Bihanzin yana ta ƙoƙarin shawo kan matsalar ta hanyar gyara samfurin laidan yadda zai ɗauki jikin matafiyan amma bai kai ga cimma nasara ba. Bana tunanin Bihanzin zai fito yaƙi kafin ya warware matsalar sa."
Armad yaja dogon numfashi sannan yaci gaba da bayani. "Dul'Ururu shi kaɗai ne bashi da wata matsala ko ta wanne ɓangare. Kuma mu kaɗai muke adawa da jinzidal. Kada ku manta an fara wannan kamfen ɗinne domin a kaɗe irin mu masu adawa da jinzidal. Kuna tunanin baza su afka mana ba zarar muka juya baya? Nasan lamarin da sarƙaƙiya: idan muka zaɓi Ikenga, Bihanzin da Dul'Ururu su afka mana ta baya; idan muka tari Bihanzin, Ikenga da Dul'Ururu su afka mana; idan kuma muka tari Dul'Ururu, Ikenga da Bihanzin su afka mana ta baya. To amma kuna tunanin na fito babu shiri ne? Ku saurara kuji."
Armad ya gyara zama tare da gyaran murya. "Amsar ita ce Hidaya. Akwai wanda zai iya ja da Hidaya idan ta dawo? Babu. Tuni na gama tsara yadda zan dawo da Hidaya duniya. Ina kammala shiri na zamu afkawa Dul'Ururu. Hidaya zata kare mu daga Bihanzin da Ikenga har zuwa sanda zamu kammala rugurguje jinzidal mu juyo kan su muyi musu taron dangi mu ƙarasa su."
Koda jin wannan shiri sai kowa ya aminta. Babu ko shakka Hidaya zata iya kare su daga sharrin Bihanzin da Ikenga tsahon daɗewar da fafatawar zata yi. To amma matsalar ita ce...
"Idan zan iya tunawa har muka rabu dakai a duniyar aljanu baka samu jiki mai kwarin da zai ɗauki ruhin Hidaya ba. Shin an samu canji ne?" Inji Nusi.
Armad yayi murmushi tare da ɗakko dutse ɗaya daga cikin duwatsun dake gefe ya ɗora akan daular denizawa, ya ce, "Anan shirin yake, anan zamu yi musu illa. Akwai wanda acikin ku yasan labarin kamfen na farko?"
Kowa ya girgiza kai alamun bai sani ba. Amma banda Ayubu. "Eh.. to, Iluru yaso ya gayamin amma naƙi."
Armad kawai yamutse fuska yayi bai ce masa komai ba. A kullum ɗabi'un Ayubu sake bauɗewa suke, amma Armad bai damu ba, domin kuwa a zuciyar sa ya yanke shawara da jikin Ayubu zaiyi amfani ya haɗa na Hidaya. A taƙaice kwanakin Ayubu sun kusa zuwa ƙarshe. Dama shaihu Ailan Wilbafos ya faɗa cikin baitocin sa na waƙar maƙabarta cewa har kullum ɗabi'un mutun-mutumi canjawa suke, tun daga ranar da aka halicce su har zuwa lokacin da aka ɗiba musu. A wani babi ya bayyana cewa wasu mutun-mutumin gaba ɗaya juyewa suke zuwa wasu mutanen daban masu halaye daban. Kuma idan ba'ai maganin su ba sai su fara aikata ta'asa.
"Deniz Ururu (wanda ke tawagar Ikenga) basamude ne, Deniz Iluru sarkin denizawa na yanzu, kuma sarkin Jinizdal shima basamude ne, baku taɓa mamakin yadda hakan ta kasance ba? Komai da kuka gani akwai dalili." Inji Armad. "Tayaya Iluru zai zama basamude amma ɗansa Bizaya mutun? Tayaya Iluru zai samu jiki wanda baya lalacewa kuma baya jin ciwo, amma ɗansa bashi dashi? Labarin sai mun koma zuwa kamfen ɗin daya afku kafin wannan, kuma anan sirrin da zamu dawo da Hidaya yake. Ku saurara kuji..."
Anan Armad ya zayyane musu biri har wutsiyar sa.
Comments
Post a Comment