Skip to main content

428-433

 Abu kamar wasa sai Han'ibal ya ƙara azama wajen jifansu. 


"Kuyi gaba kada ku tsaya," inji Armad. "Zan tare shi."


Armad ya fita daga tawagar yayi sama ya tari Han'ibal. 


"Hannun Aradu."


Hannun hagun Armad ya juye izuwa walkiya ya tunkari Han'ibal. Han'ibal ya samarda tasa ƙawanyar ya tunkari Armad da ita. Suna haɗuwa aka dare aka basu guri. Tartsatsin garwashi da zafin wuta da walkiya ya feshe wajen. Ƙananun mayaƙa dake ƙasa suka fara gudu. 


"Ku gudu, sarkin jinzidal ya fusata," inji wani sadauki. 


Armad ya danna da karfi amma Han'ibal ya tare shi. Idan walkiyar Armad ta fara yin ƙarfi tana ture wutar Han'ibal sai kaga wutar ta fara ruruwa tana zafi. A hankali sai kaga ta danno ta rufe wutar. 


Armad ya juyar ɗayan hannunsa izuwa walkiya ya kawowa Han'ibal duka. Han'ibal ya tare da wata ƙawanyar. Tururi da zafin wuta ya cika filin yaƙin. Maƙogoron mayaƙan dake kusa ya bushe. Dole aka fara neman ruwan sha amma babu. Kishi ya fara kai bayi ƙasa. 


Ana cikin haka ne Armad yaji su Nusi sun isa bakin inda aka ajiye Fatima. Ya kuma jiyo izzar Zaikid a wajen. 


"Faɗan mu dole ya jira," Armad ya gayawa Han'ibal. "Mu haɗu a nan gaba." 


"Kaban'Zhisu!"


Ɗalasimin yana barin bakinsa ya bayyana acikin tawagarsa. Ganin Armad yasa Ayubu da Iluru suka dakata daga afkawa Zaikid. Zaikid yayi tsalle ya dawo wajen su Armad. 


A dai-dai lokaci da tawagar Armad da Zaikid suka ƙaraso wajen Fatima, a lokacin Diwani ya isa gurin Maikiro'Abbas. Zaka iya cewa kawo yanzu babu kowa a tare da Maikiro'Abbas sai salsansa. 


"Maikiro'Abbas," inji Diwani yana juya al'amudinsa kamar wanda yayi kamu. "Wai yaushe kayi Salsa bamu sani ba? A iyakacin sanin mu baka da Salsa. Ance kai ne wanda baka buƙatar kariya daga kowa saboda haka Salsa a wajenka ɓata lokaci ne."


Yana cikin magana mayaƙan Maikiro'Abbas suka taho da gudu wajen suna harbinsa da kibiya. 


"Ku kashe shi," inji wani sadauki. "Kada ku bari yaje gurin sarki."


Diwani yaja numfashi tare da cilla musu al'amudinsa. Al'amudin yayi kansu. Yana zuwa ya share su kamar tsintsiya da shara sannan ya dawo hannun Diwani.


"Ƴan takura kawai," inji Diwani. Ya juya wajen Maikiro'Abbas yana yamutse fuska kamar wanda ya kore ƙudan daya dame shi. "Ni zan halaka ka na kammala wannan yaƙi."


Yana faɗar haka ya kaɗa al'amudinsa. Dai-dai saman kan salsan Maikiro'Abbas yayi nakiya. Wuta ta tashi sama ta rufe Maikiro'Abbas. 


"Sarki!"


"Sarki!!"


Mayaƙan Maikiro'Abbas suka fara kiran sunansa cikin tsoro. Shin Diwani ya halaka shi kenan? 


Rabi dake can nesa ta juyo ta kalli babanta. Fuskarta babu alamun tsoro ko firgici akai. 


Shima Najunanu kawai kallon wutar yake yana jira ta lafa, amma babu kokwanto a tare dashi. 


A hankali wutar ta lafa. Maikiro'Abbas ya fito fili. Babu rauni ko ɗaya a jikinsa. Kayansa ko ƙura basu yi ba. Amma abin mamaki salsansa sun ƙone ƙurmus sun narke sun bi iska.


Nan take mayaƙa suka fara salallami. 


"Wayyo mun shiga uku. Kwamanda Diwani ya hallaka salsan sarki."


"Wayyo ALLAH, wayyo ALLAH. Salsa sun faɗi ƙasa. Yanzu waye zai kare sarki?"


"Kai," Rabi ta daka musu tsawa. "Mahaukatan banza. Sarki bashi da Salsa. Sarki yafi ƙarfin yayi Salsa."


Mayaƙan suka juyo suka kalli Rabi cikin mamaki. Mai take nufi da sarki bashi da Salsa? 


"Haba, Rabi, kina gani ya kashe su fa? Tayaya zaki ce sarki bashi da Salsa?"


Rabi taja dogon numfashi. Hankalin mayaƙan bazai kwanta ba idan bata faɗa musu gaskiyar labarin ba. 


"Me mutumin daya gagari mutuwa zaiyi da Salsa? Tun Farkon Lokaci bashi da Salsa. A Dogon zango bashi da Salsa. Haka al'amarin ya kasance har sai da mutane suka fara raɗe-raɗin ƙarya akansa, suna yi masa ƙazafi akan girman kai. Ko kaɗan sarki bai damu ba. Sannan kuma hakan bai saka ya naɗa Salsa ba duk kuwa da ƙoƙarin yan'uwana su Anbalu daya naɗa su wannan muƙami. A haka ya rayu har zuwa zamanin Rawar Sani wanda a lokacin sarki ya yadda ya naɗa Salsa. Sai dai tunda akai nadin sarki bai ɗora wani akan wannan muƙami ba. Wanda kuka gani an kashe yanzu hazo ne kurum dan a yaudari idanun maƙiya. Sarki bashi da Salsa. Sarki baya buƙatar Salsa."


Tana magana tana ƙara imani. A lokacin bayi suka zube a ƙasa suka kwashi gaisuwa. 


Daga can gaba kuma Diwani dariya ya fashe da ita. "Haha... Sarki bashi da Salsa? Sarki baya buƙatar Salsa? Ki saurara da zancen banza da hofi, Rabi. Yanzu zan nuna miki kuskuren mahaifinki na rashin Salsa."


Kwamandan yayi tsalle sama ya kawowa Maikiro'Abbas duka da al'amudinsa. Duk abinda ke faruwa idanun Maikiro'Abbas basa kan Diwani. Kai kace bai san yana wajen ba. Sai a yanzu da Diwani ya kawo masa hari kai tsaye sannan ya juya ya kalleshi. Suna haɗa ido Diwani ya shiga kokwanto. Asalin tsoro ya shiga zuciyarsa kamar matafiyin da yayi arba da kura. Ya fara tambayar kansa anya kuwa ya ƙarasa? Anya ba juyawa zaiyi ba? To amma kuma idan ya juya ya bawa Ururu baki ɗaya kunya. Sunansa har abada zai tafi a matsoraci duk kuwa da muƙaminsa na kwamanda. Sannan kuma wai waye Maikiro'Abbas ne da har zai sa ya juya? Dama abinda ya kawo shi kenan. Yazo ne ya kashe sarkin saboda a kammala faɗan. 


Diwani yayi ƙaraji ya afka kan Maikiro'Abbas. Yana zuwa Maikiro'Abbas ya dunkule hannu ya daki al'amudin dake hannunsa. Al'amudin ya buɗe baki zai haɗiye hannun sarkin amma sai kawai ya haɗiyi iska. Ƙarfin izza yayi fatali da al'amudin gefe guda sannan hannun Maikiro'Abbas ya wuce ya cafi wuyan Diwani. Kafin Diwani ya kauce sarkin ya damƙe shi. Yana ƙoƙarin ƙwacewa, sarkin ya dunkule hannu ya daki ƙirjinsa. Wajen daya daka ya ƙanƙare ta waje, ta ciki kuma ruwan zafi ne ya shiga ƙirjin kwamandan. Diwani yaji kamar ana ƙanƙare shi ana dafa shi duk a lokaci guda. Kamar hakan bai isa ba sai ƙarfin dukan ya ɗauki Diwani yayi cilli dashi gefe guda. 


Al'amudin ya tashi sama zai bi ubangidansa amma Maikiro'Abbas ya miƙa hannu ya riƙe shi. 


Abin mamaki sai al'amudin ya fara wutsil-wutsil yana ƙoƙarin ƙwacewa. Kamar yasan ba ubangidansa ne ya riƙe shi ba.


Sarkin ko a jikinsa. Da yaga al'amudin bazai tsaya ba sai ya buɗe baki ya hura masa dusar ƙanƙara. Nan take ya ƙanƙare ya daina motsi. Sarkin ya cillashi cikin jakar tsafinsa.


"A haka sarki ya tara kayan daya haɗa fasahar Non-toch-teka. Kai ma, Diwani, al'amudinka ya shiga ciki yau," inji Rabi.


Acan gefe Diwani ya farfaɗo daga ɗan gajeren suman da yayi. Mayaƙan Ururu sun zagaye shi. 


"Kwamanda," inji kyaftin Burugu. "Zaka iya tashi?"


Diwani ya harari kyaftin ɗin. 


"Uban me zai sa na kasa tashi?" 


Ya miƙe a fusace yana kallon Maikiro'Abbas daga nesa. A ransa yana tunanin al'amudinsa da Maikiro'Abbas ya kwace. Wai meye ya faru ne? Yasan ya kamata ace al'amudin ya kama hannun Maikiro'Abbas. Amma kuma sai ya kasa. Kamar wata izza ta musamman ta hana hakan faruwa. Sannan kuma dukan da sarkin yayi masa shima ya bashi mamaki tunda ya kula da sanda sarkin ya kawo hannu, kuma yaga inda sarkin zai yi ta hanyar fasahar Saɓani, amma duk da haka sai da dukan ya same shi. 


"Hmmm..." Diwani yaja dogon numfashi. "Ga dukkan alamu bazan iya kashe shi ni kaɗai ba."


Yana rufe baki ya juya wajen rundunar su. 


"Kwamanda," inji kyaftin Burugu. "Ina zaka? Mai ya kamata muyi?"


"Ku dawo gida ku tare hanya," inji Diwani. "Babban aikin mu shi ne hana su kwatar Fatima."


Jin haka mayaƙan suka fara kallon-kallo. Wasu daga cikinsu suna jin kamar kwamandan tsoro yaji. Sai dai babu wanda ya isa ya furta. Dole suka fara jada baya. Maimakon kai hari sai suka koma tare hanya. Sai dai duk da haka anfi mutanen Maikironomada yawa, kuma har yanzu a kewaye suke. 


Idan muka koma wajen da za'a sare kan Fatima zamu ga abin ya rincabe. Armad da Zaikid da tawagarsu duk sun iso. 


"Formation B," Inji Armad. 


Nan take tawagar ta rabe gida biyu. Armad, Shísu, Inyaya da Barilu suna dama. Nazára, Cokali, Giwa, Asifu da jan doki suna hagu. Nusi tana tsakiya. 


Zaikid yana ganin shirin yayi murmushi. Ba tare da cewa komai ba ya shiga gaban Nusi.


"A bani dama na tare gaban," inji farfesan.


Armad ya gyaɗa kai alamun amincewa. 


Kowa ya tsaya a wajensa. Ba tare da tsoron Ururu ba suka danna gaba. 


Suwainah ta motsa zata shiga gaba amma Ibraham Nil ya riƙe ta. 


"Tsaya tukun," ya ce. "Saurin mai kike yi?"


"Sake ni," inji Suwainah. Ta fizge hannu tayi kansu Armad. 


Armad yaga tahowar ta saboda haka ya bawa kowa inkiyar kada ya shiga ya bar masa ita. 


Sai da ta kusa zuwa gab da gab sannan Armad ya ɓace ya bayyana a saman kanta. 


"Linzami!" 


Ya ɗaura fasahar Linzami 

a hannunsa ya damƙi wuyanta da hannu. Kafin tayi wani abu ya saukar mata da hannun aradu da ɗayan hannunsa. Ya wujijjigata sannan yayi cilli da ita gefe, jikinta yana hayaki. Tawaga kuwa taci gaba da tafiya tana tunkarar Fatima. 


Binani yayi tsalle ya tare su. Kafin su haɗu ya zana hannu akan iska inda katangar ƙarfe ta bayyana. 


"Duniyar Negrinki," inji Armad, ya shiga gaba. Negrinki ta fara bulbula daga jikinsa. Kafin su ƙarasa Negrinkin Armad ta rufe katangar ruf. Suna zuwa suka shige cikin Negrinkin suna tunani zasu daki katangar. Sai dai kafin su shiga tuni Negrinkin ta cinye katangar zuwa wata duniyar kamar ma ba'a taɓa yinta ba. Hakan yasa rundunar basu samu wata matsala ba ko kaɗan. 


Suna wucewa, Armad 3 ya bayyana da Najunanu ɗauke a hannunsa. Kamar daman sun shirya sai Najunanu ya shige gaba ya hau kan kafin dake kewaye da Fatima. Su kuma tawagar suka juya baya suka rufe shi cikin bada kariya. 


"Kaga yaro da dabara," inji Maruta. "Wato ba Nusi ce alkalamin ba kenan. Kawai yasa mun yadda da hakan ne amma a zahiri Najunanu ne alkalamin."


"Har yanzu kana ganin kune da nasara?" Fatima ta tambaye shi.


"Bari muga kaifin alkalamin nasa tukun," inji Maruta.


A ɓangare guda kuma Dul'Ururu da Yurba da Binani da Ibraham Nil da Maruta su kaɗai suka rage. A wani salo mai ban al'ajabi sai suka zuba ido suna kallon su Armad ba tare da sun far musu ba. Acikin idanun Dul'Ururu akwai yadda dakai da kuma raini. Kai kace ya raina su Armad ko kuma yana ganin babu yadda zasu iya karya kafin. 


Ganin Armad da tawagarsa sun iso sai dukkan mayaƙan dake ƙasa suka zubo musu ido. Kallo ya koma sama. Saboda yawan idanun dake kansu sai da su Nusi suka ji tamkar ana caka musu wuƙa. 


"Yaya?" Armad ya tambayi Najunanu. "Ka gama?"


"Da saura," inji Najunanu. 


Suna cikin haka kwamanda Yurba ya tako a hankali yazo kusa dasu. Armad da Zaikid suka shiga gabansa. Amma maimakon ya kai musu hari sai kawai yayi murmushi. 


"Zan baku minti guda," inji Yurba. "Idan kun karya kafin shikenan ku ɗauki Fatima ku tafi da ita, idan kuma baku karya ba to zanyi muku hukunci."


Armad ya buɗe baki zai maida martani amma Zaikid ya riga shi. 


"Mun yadda," inji Zaikid. "Ka bamu minti guda. Idan bamu karya kafin ba kayi duk hukuncin da kake so?"


Armad ya kalli kakan nasa cikin mamaki. Da yayi magana ba haka zaice ba. 


"Hmm.. to, na amince," inji Yurba. "Lokacin ya fara daga yanzu."


Abin mamaki kawai sai wasu mayaƙan Ururu ƴan abi-yarima-asha-kiɗa suka fara lissafi. 


"Ɗaya, biyu, uku, huɗu, biyar..."


Armad ya rasa mai zaice. Abin ya zama kamar wani al-mara. Wai shin Ururu sun raina su haka suna ganin baza su iya ba? A gaban idon duniya hakan take faruwa saboda haka Armad ya lura cewa wannan yaƙi kawai wani salo ne da Ururu suka fito dashi domin nunawa duniya ƙarfinsu. 


Tun anan Armad yaso ya tarwatsa abin ya damƙi wuyan Yurba amma ganin kallon da Zaikid yake masa yasa ya fasa. 


"Talatin, talatin da ɗaya, talatin da biyu, talatin da uku..."


Mayaƙa suka ci gaba da lissafi. Shi kuwa Yurba yana tsaye a gabansu ya karya hannu yana jiran lokaci. Saboda haushi Armad ko tambayar Najunanu ko ya gama baiyi ba. Acikin ransa kawai so yake lokacin ya cika dan yaga mai Yurba yake taƙama dashi. 


"Hamsin da biyar, hamsin da shida, hamsin da bakwai," suna matsowa suna ƙara ɗaga murya. "Hamsin da takwas, hamsin da tara, sittin!" 


Suka kwalla ihun murna. Yau kwamandan su zaiyi hukunci.


"Yarima mai jiran gado?" inji Zaikid. "An samu nasara?"


Najunanu ya shagala wajen aikin sihiri baya ko sauraron abinda Zaikid yake faɗa. A gabansa kwabbai ne na fata ya ajiye. Kowanne kwabo sai kaga yana haske yana yin sama. Idan hasken yaje iyakacin tafiyarsa sai kaga ya lankwaso ya dawo ƙasa. Idan yayi kamar rabi sai yayi gaba ya daki kafin sai kaga ya tarwatse. Hasken da kwabon yake bayarwa ya baje. Shi kuwa Najunanu sai ya ƙara zaro wani daga jakar tsafinsa ya saka a wajen na da, ya kuma ƙara maimaita irin abinda ya faru a baya, amma a banza. Duk abinda ya taɓa kafin sai kaga ya tarwatse ya baje. 


"Nasan kwarewar ka a fannin kafi," inji Zaikid. "Zaka iya fasa kafi kowane iri ne. Na yadda dakai."


A yayinda Zaikid yake yabon Najunanu yana ƙara masa kwarin gwiwa, shi kuwa a nasa ɓangaren yarima kawai gumi yake haɗawa. Ƙarfin kafin ya kere tunaninsa. Yawanci duk kafin daya dannawa kwabbansa na tsafi guda uku ya gama dashi, amma kawo yanzu kafin yaci kwabbai sunfi talatin amma ko gezau baiyi ba. 


"Ya gagara," inji Najunanu. "Babu alamun wannan kafi zai faɗi."


"Hahaha..." Maruta ya kyalkyale da dariya. Dama tun ɗazu ya nutsu yayi tagumi yana kallon Najunanu cikin nishadi. "Kana da kwazo akan kafi amma wannan tsarin kafin mutanen sama ne. Mai zai hana muyi cinikayya? Ni na gaya maka yanda zaka karya kafin, kai kuma ka gayamin inda ɗan uwana Haruta yake."


Koda jin maganar Maruta sai dukkan wanda ke wajen ya juya yana kallonsa harda Dul'Ururu. Tambayar da take ran kowa ita ce: wai daman Haruta ɓata yayi? Ko kuma kama shi akai? 


"Kada ku yadda dashi," inji Fatima cikin sauri. "Duk abinda zai faɗa ba gaskiya bane."


Maruta ya juya ya kalleta fuska a yamutse. Baiji daɗin maganar data faɗa ba. 


"Shin kina zargin mutanen Farkon Lokaci da yin ƙarya ne?" Inji Maruta fuska a murtuke.


"A'a," inji Fatima. "Ko kaɗan bana zargin zaka yi ƙarya. Amma abinda nake tunanin zaka yi shi ne zaka fadi abu mara amfani."


Maruta ya karkata kai cikin mamaki. 


"Haha..." Ya ƙara fashewa da dariya. "Wannan ƴar taka farfesa akwai hangen nesa. Sai dai ba haka abin yake ba. Ni ɗin kalamin dake kan harshe na shi ne a zuciya ta. Tabbas bazan yi ƙoƙarin yi muku dabara ba, ko kuma na gaya muku abinda bazai taimaka muku wajen karya kafin ba."


"Kuma kana tunanin zamu yadda dakai kawai saboda ka faɗa?" Inji Armad. 


"Ehem..." Zaikid yayi gyaran murya. "Ni na yadda. Idan Maruta yayi ƙarya mutanen Farkon Lokaci zasu barranta dashi saboda haka bazai iya yin ƙarya ba. Ya gaya mana yadda zamu karya kafin, ni kuma zan gaya masa inda Haruta yake."


Armad ya juya da sauri wajen Zaikid. "Meye haka, farfesa?"


"Ka nutsu," inji Zaikid. "Ka kuma lura da abinda zanyi."


"Haha... Kaga mutanen kwarai. Zaikid Wilbafos mijin...? Yaya sunan matar taka da Umuk-li ya kashe ma?" Maruta ya tambayeshi.


A lokaci guda nutsuwar dake fuskar Zaikid ta kauce. Fuska a murtuke ya dunkule hannu yayi kan Maruta. Nusi ta shiga gabansa.


"Dattijo, yanzu fa kake cewa jikanka ya nutsu, kada ka bari yaci riba akanka."


Zaikid ya tsaya a gaban Nusi yana huci. Bayan ƴan dakiku ya huce ya dawo baya ya tsaya.


"Faɗa mana yadda zamu karya kafin," inji Zaikid.


Maruta yayi murmushi wanda bai wuce leɓensa ba. Sannan ya nuna kafin ya fara bayani da cewa, "wannan kafin mai hawa uku ne..."


"Maruta?" Dul'Ururu ya kwala masa kira. "Mai kake yi ne? Wane irin hauka ne wannan?"


Maruta ya juya a hankali wajen Dul'Ururu. 


"Indai zasu gaya mana inda Haruta yake ai ciniki ne mai kyau," inji Maruta. "Nasan dai ɗan uwana Haruta yafi wannan kafin muhimmanci a wajen ka, ko kuwa ba haka bane?"


Dul'Ururu ya cije haƙora. Fuskarsa tana kumbura kamar zata fashe.


"Bazan yadda da wannan haukan ba," inji Dul'Ururu. "Yurba, Binani, bana son ganin wannan shirman."


Kamar wani umarni daga sama sai Yurba da Diwani suka jeru akan layi. Zaikid yayi tsalle zaiyi kan Yurba, a yayinda Armad yayi kan Binani, amma kafin suyi taku ɗaya anyi jifa dasu. Bawai su kaɗai ba, hatta su Nusi da Najunanu, dukkaninsu sun faɗo ƙasa daga kan gado. Armad yana dubawa yaga ainihin ƙasar dake ƙarƙashin ƙafafunsu ita ce tayi sama. 


"Aikin Yurba ne," inji Zaikid. "Kowa ya tashi sama mu tarwatse kafin ya juya mu ya kifar."


Armad ya yamutse fuska. Wane irin ya juya su ya kifar. Har akwai wanda ya isa ciccubi ƙasa baki ɗayanta ya ɗaga sama ya kifar da mutanen dake kai kamar wata tabarma? Yana cikin tunani ya hangi Yurba ya durkusa ya ɗora hannunsa akan ƙasa yana kiran ɗalasimai. Binani yana kusa dashi ya haɗa hannu yana kiran nasa ɗalasiman daban. Watakila su biyun suka haɗa ƙarfi guri guda domin dai har yanzu bai ga harin Binani ba....


Ai kafin ya rufe baki yaga saman kansu yayi duhu. Yana ɗaga ido ya hangi wani mahaukacin murfi na ƙarfe yana dirowa kansu da niyyar ya rufe su ruf. Armad bai san mai kwamandan yake so ya cimma ta haka ba amma dai tabbas bazai bari ya rufe su ba. 


"Kuyi maza ku gudu," inji Armad. "Zan riƙe murfin."


Zaikid ya shiga gabansa. 


"Meye amfani na kenan?" Inji Zaikid. "Ku gudu. Ni zan tare shi."


Babu lokacin yin musu ko shawara. Saboda haka Armad ya rabu da kakan nasa. A zuciyarsa yana ganin sinadarin Negrinkinsa shi ne mafi dacewa ya tare murfin ƙarfen. 


Koda Armad ya fara ƙoƙarin guduwa sai ya fuskanci akwai matsala. A halin yanzu ba'a ƙasa suke ba. Kafatalin ƙasar dake ƙasan ƙafarsu ta ɓubɓugo tayi sama kamar an yanko ta. Armad bai san yadda hakan ya faru ba, kuma bashi da masaniya akan yaya, amma abu guda ɗaya daya ɗauki hankalinsa shi ne gefe da gefen ƙasar da suke kai lankwasowa yake yi yana ƙoƙarin haɗe su a ƙasa ya rufe. Wato abubuwan sunyi musu yawa. Na farko ga murfin ƙarfe daga sama, na biyu ga ƙasa tayi sama dasu, sannan ma uku gashi ƙasar da suke kai tana ƙoƙarin binne su aciki. 


To amma duk da haka Armad ya lura zasu iya fita. Ɗalasimi ɗaya zai fitar dashi. Suma ragowar mutanensa duk wanda ya tashi sama zai iya fita...


Kafin ya gama lissafi fuskarsa ta ƙara canjawa. Duk mutanensa sun kasa tashi sama. Suna tsaye a inda suke sun kasa motsawa. 


"Nusi, ya akai? Mai yasa kuke tsaye?"


Maimakon ta bashi amsa sai ta nuna masa ƙafarta. Ƙasa ta kama ta iyakacin idon sahu bata iya ko motsi. Sannan kuma ƙasar sama take ƙara yi. Armad ya dubi ƙafarsa yaga lafiya. Amma hatta Nazára a riƙe yake.


Ana wata ga wata. Armad ya bayyana a wajen Nusi ya daki ƙasar data riƙe ta da ƙafa. Ƙarfin izza ya fita daga ƙafarsa ya shiga cikin ƙasar ya tarwatsa ta. Kafin ƙasar ta haɗe ta ƙara riƙe ta Armad ya zaro ta ya kira Kaban'shisu yayi waje da ita. Acan sama yana jiyo ƙarar takobin Zaikid yana arba da murfin ƙarfen. 


Cikin sauri Armad ya tashi sama da Nusi a hannunsa yana hangen inda zai ajiye ta domin ya koma ya ɗakko ragowar. Sai dai fitowarsa yaga abin mamaki. Wato ba kamar yadda yake tunanin ƙasar ce gaba ɗaya ta ɓubɓugo ba, a'a, iyakacin dai-dai inda suke kai ne ya fito daga ƙasa inda ya bar wani wawakeken rami baƙi-kirin. Idan ka leƙa ramin zaka rantse bashi da ƙarshe. Sannan kuma tsayin ƙasar data fito daga ƙasa, wadda a yanzu Zaikid da sauran mutanensa suke kai, takai ƙafa ɗari biyu zuwa ɗari uku. 


Armad yana neman inda zai ajiye Nusi sai kurum yaji murfin ƙarfen ya rufe su Zaikid ruf. A wani salo mai ban al'ajabi sai kurum ƙasar ta juye dasu a saman tayi walankeluwa dasu ta dawo ƙasa zata kifar dasu a ramin data fito. Armad da Nusi suka kalli juna. Idanunsu a wage: rabi firgici, rabi mamaki. 


Idan Armad ya bari ƙasar ta kife dasu to babu makawa sun halaka. Wani kabari ne kurum wanda babu wanda zai iya buɗe shi. To amma tayaya zai iya tare tsaunin ya hanashi kifewa duk da gudun da yake yi?


"Zan iya baka dakiku goma," inji Nusi. 


Armad da Nusi suka haɗa ido sannan ba tare da cewa komai ba suka tari tsaunin a sama. Bishiyar Nusi ta sauka ta rufe ramin da tsaunin yake niyyar faɗawa ciki. Murfin kwanon dake rufe dasu ya daki bishiyar inda wata ƙara mai firgitarwa tayi sama. 


Armad yana ganin tsaunin ya tsaya sai yayi kansa. Hannu biyu ya saka ya danna Negrinki cikin murfin ƙarfen. Nan da nan kwanon ya ɓace su Zaikid da Nazára suka bayyana a fili. Sai dai zuwa wannan lokaci tuni ƙasa ta kusa cinye su domin tazo wa Barilu da Inyaya cinya. Masu ɗan sauƙin sune Nazára. Sai kuma Zaikid wanda bata riƙe shi ba. 


Armad yayi kan tsaunin zai tarwatsa shi ya kwato ƴan uwansa amma kamar tsaunin yana gani sai yayi bindiga ya tarwatse. Wata iska mai haɗe da wuta da narkakkiyar ƙasa tayi watsi dasu sama. Kowanne acikinsu yayi nasa guri. Nazára yayi gabas, Asifu yamma, Barilu kudu, kai sauran babu wanda yaga inda sukai ma. 


A hankali ƙura ta lafa. Armad da Nusi da Zaikid da Najunanu suna tsaya a tsakiyar filin yaƙin. Su kuwa ragowar babu alamunsu. 


"Kamar yadda nayi tunani," inji Zaikid. "Karɓar Fatima bazai zamo abu mai sauki ba."


"Dattijo, sai yanzu ka gano haka?" Inji Najunanu yana goge jini daga wuyan rigarsa.


Armad yayi shiru yana kallon ƙasa. Sunje har kusa da Fatima amma sun dawo baya ba tare da sun karɓo taba. Abokan faɗansu sun kware matuƙa sama da yadda yake tunani. Wato kamar zaka iya cewa suna sane suka basu hanya saboda sun san idan sunje ma babu abinda zasu iya yi. 


"Ka ajiye kafin a gefe," inji Nusi. "Ai indai bamu gama da Dul'Ururu, Yurba, da Binani ba to babu tayadda zamu iya ceto Fatima."


"Koda na kama Dul'Ururu waye zai rike Yurba da Binani," inji Armad. "Kuma kada ku manta Diwani da Ki'jinu suna nan a filin nan bawai mutuwa sukai ba. Karaiƙisu a yanzu yana can yana wasa da Saif-Al-Barzak amma duk sanda na ɗauke ta zai dawo fili."


"Ga Ibraham Nil," Inji Zaikid. "Tabbas faɗan ɗai-ɗai zaiyi tsamari da yawa."


"Amma kuma shi ne kaɗai mafita ba," inji Armad. "Bawai sai mun kai su har ƙasa ba. Kawai mu riƙe su tsahon lokacin da zamu karya kafin. Ni zan riƙe Dul'Ururu. Farfesa, ka riƙe Yurba. Najunanu, ka riƙe Binani. Nusi, ki riƙe Ibraham Nil."


Nan take kowa ya fara kallon abokin karawarsa yana lissafin yiwuwar hakan a ransa. 


"Amma idan akai hakan waye zai karya kafin?" Inji Nusi. "Ina ganin karya kafin shi ne abu mafi muhimmanci a yanzu. Domin koda mun isa ga Fatima baza mu iya yin komai ba zarar akwai kafi a tsare da ita."


"Tunda na kasa to babu wanda zai iya a maikironomada sai dai sarkin da kansa," inji Najunanu. "Amma zuwansa wajen kafin shi ne matsala. Maikiro'Abbas shi ne yake kula da rundunar mu a yanzu. Kuma shi ne yake riƙe da ikon Kuyurussa'ayi kuma shi kaɗai Ururu suke tsoro a filin nan. Kasancewarsa a tsaye a baya ita take basu tsoro suna ganin a kowane lokaci zai iya kawo musu hari saboda haka a tsorace suke. Kuma wannan tsoro shi ne zai saka Ururu baza su iya sakar jiki su yaƙe mu ba. Daga sanda muka cire wannan tsoro daga zuciyarsu to zasu yi amfani da yawansu su halaka mu."


Koda jin haka sai Armad ya fuskanci dalilin tsayawar Maikiro'Abbas a baya. Wato shi kamar wani makami ne wanda yake bada tsoro daga nesa. Kuma shi ne yasa har yanzu Ururu suke ɗari-ɗari dasu. Da ace zai shigo yaƙin to da sakar jiki zasu yi su fito gaba ɗaya. 


"Sannan idan Maikiro'Abbas bai shigo ba zaiyi wuya Dul'Ururu ko Maruta su shigo," inji Zaikid. "Zasu jira su ajiye ƙarfinsu domin su iya tare shi a sanda ya shigo. Kaga kenan kai Armad akwai yiwuwar ba sai ka tari Dul'Ururu ba."


"Har yanzu dai bamu samo maganin matsalar mu ba," inji Armad. "Waye zai karya kafin?"


"Akwai Rabi," inji Zaikid. 


Najunanu najin haka ya girgiza kai. 


"Kasan baza tayi ba," inji Najunanu. "Tunda Anbalu ya mutu ta rantse baza ta ƙara shiga harkar kafi ba."


"Waye Anbalu?" Inji Armad.


"Anbalu ɗan'uwana ne wanda..."


Wata ƙara ta katse shi. Ƙasar da suke kai ta fara girgiza ta watsar dasu gefe. Koda suka waiga sai suka fuskanci gaba ɗayan filin ne yake rawa. Kafin su ankara sai suka ji ƙasar ta fara motsi tana yin baya dasu. Ita kuma ƙasar bayansu tana tahowa gaba. 


"Mai ke faruwa?" Inji Nusi. 


"Yurba," inji Armad. Ya nuna kwamandan a inda suka baro shi a tsugunne ya ɗora hannu a ƙasa yana kiran ɗalasimai. "Har yanzu bai gama ba."


Zaikid ya runtse ido cikin tunani. "Kowa ya zamo cikin shiri. Ban san mai zaiyi ba, amma ance yana iya canja tsarin taswira ya zana ƙasa da garuruwa da hannunsa."


Kafin ya rufe baki ƙasar da suke kai ta ɗebe su tayi cilli dasu baya. Ba su kaɗai ba. Duk wanda ke cikin rundunar Maikiro'Abbas haka akai masa. Su kuwa mayaƙan Ururu sai ƙasar ta mayar dasu gida. A ɗan wannan lokaci filin yaƙin ya rabu gida biyu: Ururu suna ɓangaren inda aka ajiye Fatima, maikiro kuma suna ɓarin Maikiro'Abbas. 


Yurba ya miƙe ya ɗaga hannu sama yana kiran ɗalasimai. Take ƙasar da mutanen Maikiro'Abbas suke kai ta fara ɓubɓugowa tana fitowa daga ƙasa. 


Armad da Zaikid sun fuskanci abinda ke shirin faruwa. Da sauri suka haɗa hannu guri guda suka danne ƙasa.


"Zauna da ikon Wilbafos!" Suka faɗa a tare. 


Kasar tayi kiki-kaka kamar zata tsaya amma sai wani iko na musamman ya sakko daga sama ya danne nasu. Ƙasar taci gaba da motsi. Dai-dai inda suke kai ya shata kamar an yanka da wuƙa. 


"Kowa ya kama na kusa dashi," inji Najunanu. "Yurba yana ƙoƙarin ɗaga mu sama ya kifar."


Maikiro'Abbas ya ɗaga hannu ya daki iska. Nan take ƙatotuwar ƙawanyar ƙanƙara ta bayyana tayi kan Yurba. 


Kafin ta ƙaraso, Binani da Diwani sun shiga gaba. Diwani ya daki ƙanƙarar da al'amudin dake hannunsa ta fashe ruwan zafi ya fito. Shi kuma Binani ya saka ƙarfe ya rufe ruwan. Kamar an gama amma sai ikon dake cikin ƙanƙarar yayi jifa dasu gefe kamar an watsa yara sama. Ƙanƙarar ta dawo ta haɗe sannan taci gaba da tunkarar Yurba. Kaji babban iko.


Dul'Ururu yana ganin haka ya ɗaga sandarsa ya dake ta. Wata wuta tayi sama. Iko da iko suka haɗu. Taurari suka bayyana a bayan Dul'Ururu. A hankali, a hankali sai girman ƙanƙarar ya fara raguwa. Taurarin suna raguwa, ita ma ƙanƙarar tana raguwa. A haka har sai da ta ɓace. 


Dul'Ururu da Maikiro'Abbas suka kalli juna daga nesa. 


Ƙarfin harin Maikiro'Abbas yasa Yurba ya durkusa ƙasa kada ayi cilli dashi. Hakan yasa tsafin da yake amfani dashi akan su Armad ya ragu wanda yayi sanadiyar tsatstsagewar ƙasar da suke kai. Babu inda bai tsage ba sai inda Maikiro'Abbas yake kai. 


A haka a tsagen, ƙasar ta fara yin sama dasu, lamarinda yasa ƙasar ta ƙarasa rabewa gida-gida. Kowane ɓangare ya zama mai zaman kansa kamar tsibiri. Duk inda ka duba sai kaga tarin mutanen akan tsibiri yana yin sama. Murafen ƙarfe suka bayyana a saman kowanne tsibiri kamar ɗazu. Armad yasan mayaƙansu baza su iya ji da abinda zai faru ba saboda haka da sauri ya samar da tafkeken gidan gizo-gizo a samansu ya tare murafen kwanon. Sai dai hakan ya bawa ƙasar da suke kai damar yin sama. Gashi ya tare murfin amma kuma sama suke yi saboda haka ba daɗewa ƙasar zata haɗe da murfin ta rufe su. 


Da sauri ya samar da Negrinki ya danna cikin zaren. Hakan ya bashi damar zuƙe ƙarfen da akayi murfin dashi. Sai dai kamar Binani ya gano Armad domin kuwa hakan bai saka murfin ya ɓace ba. Kamar ma ƙara tsayi yake yi. A lokacin Armad ya fuskanci abu biyu: kodai bayan ƙarfen ya shiga duniyar Negrinkinsa Binani yake janyo shi ya fito dashi, ko kuma wani ƙarfen sabo Binani yake samarwa a wajen wanda Armad ya zuƙe wanda hakan zai nuna kamar babu abinda Armad yake yi kenan. Koma dai meye Armad ya kasa zuƙe ƙarfen Binani kamar yadda yayi a ɗazu. Saboda haka sai yayi ƙoƙarin dawo da gidan gizo-gizon ƙasa domin ya hana tsibiran tashi sama. Sai dai hakan bai yiwuwa ba saboda mutanen dake kan tsibirin. Idan yace zai ɗaure tsibiran ya hana su yin sama to kuwa zai zuƙe wasu mutanen dake kai cikin duniyar Negrinki. 


Yana cikin tunanin mafita murafun suka sauka suka fara rufe su. Duk inda mutane suka taru sai kaga murfin farin ƙarfe ya sauka ya rufe su. 


Ƙatoton murfi ya bayyana a saman su Armad zai rufe su. Najunanu ya tashi sama da takobinsa ya sari tsakiyar murfin. Koda takobinsa ta taɓa murfin sai murfin ya narke ya zama ruwa ya zubo musu. Ya yunkura zai kaiwa na kusa dasu ɗauki amma kafin ya bar kan tsibirinsu wani murfin ya ƙara bayyana zai rufe su. Ya sare shi ya mai dashi ruwa. Wani murfin ya ƙara bayyana. 


Yurba da Binani suka taso a sama suka taho kansu suna kiran ɗalasimai. 


Murfin kwano ya bayyana a saman Maikiro'Abbas zai rufe shi. Kada dai a manta ƙasar da sarkin yake kai ita kaɗai ce bata zama tsibiri ba. Wani zaiyi tunanin Ururu sun manta da sarkin ne, amma ko kaɗan ba haka abin yake ba. Murfin kwanon yana sakkowa ƙasa yana ƙara faɗi da kauri. Muddin ya ƙaraso to sai ya rufe Maikiro'Abbas da dukkan mutanen dake kewaye dashi.


Maikiro'Abbas ya jira har saida murfin ya ƙaraso. Sannan a wani salo mai ban mamaki, kamar uba yana yiwa ɗansa ladabi, sarkin yasa tafin hannunsa ya daki kwanon. Kwanon ya fita da gudu yayi sama ya fasa gidan gizo-gizon Armad sannan yayi kansu Binani da gudu zai buge su. Dole Diwani ya kawo musu ɗauki yasa al'amudinsa ya doke kwanon gefe. 


Maikiro'Abbas ya haɗe hannu guri guda zai kira babban tsafi amma a lokacin Dul'Ururu ya bayyana a kusa dashi. 


"Ba zan bari ka shiga faɗan yara ba," Inji Dul'Ururu. 


Maikiro'Abbas ya kawo masa duka da dunkulallen hannunsa na dama. Karfin izza ya shiga hannun yasa iska ta fara kaɗawa. Dul'Ururu ya maida sandar tsafinsa hagu sannan ya buɗa kawo naushi da hannunsa na dama. Hannayensu biyu suka haɗu da juna. Babu fasaha, babu sihiri, ƙarfin izza ne ziryan ya haɗu da juna. Wani tururi mai kama da sanyin babban sihiri ya fara fita yana sama. Ƙasar da suke kai ta fara rawa. Mutanen Maikiro'Abbas dake tare dashi suka fara ja da baya


A nasa ɓangaren, Armad ci gaba da ƙoƙarin cinye murfin kwanon yayi da Negrinkinsa. Shi kuma Binani ya hana. Yurba kuma yana ta ƙoƙarin ɗaga mutane sama ya kifar dasu. Wata dabara da Armad yayi shi ne samar da hannaye a jikin gidan gizo-gizon wanda yayi amfani dasu ya riƙe ƙasa. Hakan ya takawa Yurba birki sosai domin kuwa da tuni ya fara ɗaga mutane yana kifarwa. Duk haka a yanzu Binani ya rufe kowa da murfin kwano banda su Armad wanda Najunanu ya kare, da kuma Maikiro'Abbas. 


"Wai mai kake jira ne?" Diwani ya tambayi Yurba.


"Baka ganin ya riƙe ƙasar da zaren izza?" Inji Yurba cikin fushi. 


Diwani ya ɗanyi tunani kafin ya fusata ya afka kan gidan gizo-gizon da niyyar ya farfasa shi. A lokacin Armad ya ƙara sakar Negrinki ta rufe zaren. Diwani yaja tunga fuska a yamutse. Wannan ne al'amudinsa na ƙarshe tunda Maikiro'Abbas ya kwace ɗayan. Idan ya bari Armad zuƙe shi to sai dai yayi faɗa da hannu. 


Zaka iya cewa yaƙin ya tsaya cak. Kuma tabbas Armad bazai bari Yurba ya ɗaga su sama ba, balle ma ya kifar. Diwani kuma bazai iya shigowa ta cikin zaren izza ba, shi kuma Binani amfaninsa kurum ya rufe mutane da murfin kwano wanda ya kasa rufe su Armad. 


Ganin halin da ake ciki, Nusi, Nazára da Zaikid wanda suke tare da Armad suka tashi sama suka nufi tsaunin dake kusa dasu. Najunanu ya tsaya tare da Armad domin ya taimaka masa. 


"Ni zan samar da ƙofa," inji Zaikid.


"Ni kuma kafin kofar ta rufe zan saka bishiya na buɗe ta," inji Nusi.


"Ni kuma idan zaku iya bani dakika uku to zan zuba yashin ƙarfe acikin kwanon na lalata shi," inji Nazára. "Binani bazai iya sarrafa shi ba zarar yashi na ya shiga ciki. Kuma kafin ya samar da wani mun ɗebe mutanen dake ciki."


Suna isowa bakin tsibiri na farko Zaikid ya zare takobi ya sari ƙarfen kwanon daya rufe mutanen. Ƙarfen ya dare gida biyu. Kafin Zaikid ya janye takobinsa tuni ya fara haɗewa. 


Nusi tayi maza ta saka bishiya ta buɗe tsagar wanda hakan ya rage saurin haɗewar da ƙarfen yake yi. Shi kuma Nazára ya danna yashin ƙarfe ciki. Nan da nan ƙarfen Binani ya fara canjawa daga farin karfe zuwa jaja-jaja. 


Jin ƙarfin Binani ya ragu sai Nusi ta ƙara jan ƙofar ta buɗa ta. Murfin ya tarwatse. Zaikid ya faɗa ciki da fasahar Kaban'shisu ya ɗebo mutane ya kai su wajen da Armad yake. Yana ajiye su ya dawo ya ƙara ɗiban wasu. Cikin dakika ashirin sun ceto mutun casa'in da uku dake cikin wajen sun mai dasu wajen da Armad da Najunanu suke tsaye. 


Hakan ya rage saura tsibiri takwas a rufe. ALLAH ne kaɗai yasan yawan mutanen dake ciki. 


Zaikid da Nusi da Nazára suka nufi tsibiri na gaba. Suna zuwa Zaikid ya buɗa hanya. Nusi ta faɗaɗa hanyar da rassan bishiyar ta. Shi kuma Nazára yayi amfani da ƙofar da suka samar ya lalata ƙarfen tayadda Binani bazai iya sarrafa shi ba. Kafin Binani ya samar da wani tuni sun ɗebe mutanen dake ciki sun mayar dasu wajen Armad.


A haka sai da suka ɗebe mutane ɗari tara da doriya. 


Yurba ya dubi Binani a fusace. "Wai meye amfanin wancan murfin kwanon naka?" 


Binani ya harareshi. "Kai meye amfanin tsibiran daka samar bayan ka kasa ɗaga su ka kifar? Da ace baka bari Armad ya tare ka ba da babu wanda zai iya fasa ƙarfe na. Saboda haka idan ma akwai matsala to taka ce."


"Mai kace?" Yurba ya cije haƙora. 


"Yadda kaji haka nace," inji Binani ba tare da ya kalleshi ba.


Yurba ya dunkule hannu yana hararar Binani.


Diwani yayi sauri ya shiga tsakani.


"Ku tsaya, ina da amsar wannan halin da muke ciki. Ku kalli can." Diwani ya nuna akwatin ƙanƙarar da Ki'jinu yake ciki. 


Suka kalli akwatin sannan a tare sukai murmushi. 


"Ku bani minti guda zan dawo da Ki'jinu," inji Diwani.


Armad yana jiyo abinda ya faru. Tabbas idan Ki'jinu yazo an gama dasu. Da irin fasahar kwamandan cikin sauki zaiyi amfani da gashin gemunsa ya karya alkadarin gidan gizo-gizon tayadda zai baiwa Yurba damar ɗaga tsibirin ya kifar dasu.


"Armad 1, Armad 2, Armad 3, Armad 4," inji Armad. "Ku tare shi."


Mutun-mutumi huɗu suka shiga gaban Diwani. Kwamandan yasa al'amudi yakai musu duka. Su huɗun suka haɗa hannu suka tare. Kafin al'amudin ya haɗu da hannunsu sai zaren izza ya fita ya kare. Akwai ƴar Negrinki a jiki amma duk da rashin yawanta sai da Diwani yaja da baya.


"Kunci sa'a ba al'amudina na asali bane," inji Diwani. 


Ba tare da sunce masa uffan ba, su huɗun suka zagaye shi. Armad 1 ya kai masa sara da takobin ɗorawa. Armad 2 yakai masa duka da hannun Negrinki. Armad 3 ya tsaya a gefe da fasahar Kaban'shisu koda zai gudu ya tare shi. Shi kuma Armad 4 ya kai masa duka da Hannun Aradu. 


Diwani ya tashi al'amudin dake hannunsa. Ƙarfin wutar tasa mutun-mutumin Armad suka matsa baya. Lamarinda ya bawa Diwani dama ya fice daga tsakiyarsu. 


Fuska a murtuke ya kallesu. Yasan ko kaɗan bazai iya tsere musu ba, sannan kuma kashe su zai ɗau lokaci. Faɗa dasu kuma ɓata lokaci ne. Shin wane ci gaba zai samu dan ya kashe mutun-mutumi? 


Yana cikin sake-sake sai Ayubu ya bayyana a gabansa. 


"Jeka," inji Ayubu. 


Diwani ya dube shi ya gyaɗa kai cikin godiya. Ya juya zai wuce amma Armad 1 ya shiga gabansa. Ayubu yasa ƙafa ya doke mutun-mutumin. 


"Ni ne na farkon ku," inji Ayubu. "Dole kuyi min biyayya."


Diwani ya wuce kai tsaye wajen akwatin ƙanƙarar da ɗan'uwansa Ki'jinu yake ciki. A yayinda aka fara yaƙin mutun-mutumi tsakanin Ayubu da mutun-mutumin Armad guda huɗu. 


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...