Can bayan wani lokaci Rabi ta ƙara ji ya kira sunanta. Ta buɗe baki zatai magana amma tayi shiru ganin cewa babu wanda yaji sai ita.
"Tar...ko... ne..." Inji Anbalu. Har yanzu Rabi ita kadai take jin mai yake cewa. Ya ƙara maimaitawa. "Tarko ne."
Rabi ta tsaya cak ta kalli Fulafunu. "Wai kana nufin duk baka jin abinda yake cewa?"
Fulafunu yayi jim yana kallonta cikin mamaki.
"Ni banji komai ba," ya ce.
Rabi ta ɓata rai. Tabbas akwai wani abu dake faruwa a wajen. Mai ya kamata tayi?
"Zarru? Kai ma baka ji ba?"
Hadimin ya girgiza kai.
"Banji ba."
To ko mafarki take yi? Amma kuma tabbas taji murya a kunnenta. Anbalu yace mata 'tarko ne', to amma wane irin tarko? Mai yake nufi? Wa aka sawa tarkon acikinsu?
"Mu koma," inji Rabi. "Mu koma wajen su Shema'u."
Fulafunu ya ɓata rai. Tabbas akwai abinda yake damun Rabi. A ɗazu ta dage sai an kai Anbalu gida amma kuma ace har ta canja shawara, mai yake faruwa?
"Ki gayamin mai yake faruwa?" Inji Fulafunu.
Rabi ta ɗanyi shiru tana lissafin abinda ya kamata ta gaya masa. Daga ƙarshe ta yanke shawara ta gaya masa gaskiya.
"Anbalu ya gayamin 'tarko ne'," inji Rabi, tana nazarin fuskar Fulafunu taga ko zai fashe da dariya.
Sai dai maimakon haka sai Fulafunu ya haɗe gira.
"Rabi? Mai kika sha yau da safe?"
Rabi ta ɓata rai. "Mai na sha kuma? Kana nufin ƙarya nake."
"To yaushe Anbalu ya gaya miki wannan soki-burutsun? Naga dai tare muke tafiya, ko? Kuma tabbas ba'a taɓa samu na da matsalar kunne ba."
Rabi tayi shiru kawai tana zulumi. A zahiri ita ma bata san mai yasa Fulafunu baya jin abinda Anbalu yake cewa ba, amma tabbas ita taji, kuma ba mafarki take ba. Sai dai meye hujjar ta?
"Wallahi naji," inji Rabi, fuskarta tayi kalar tausayi.
"Hmm.." Fulafunu yaja numfashi. "To, koma meye dai muje mu ajiye Anbalu a gida tukunna."
Rabi ta buɗe baki tana so tace su juya to amma ta kasa. Wacce hujja zata bawa ɗan uwanta idan ya tambaye ta mai yasa?"
Da haka suka juya suka nufi gida. Akan hanyarsu Anbalu yaci gaba da gayawa Rabi 'tarko ne'. Sai dai har yanzu Rabi ita kaɗai take jin maganar. Ta share suka ci gaba da tafiya.
"Mu koma," inji Anbalu. "Baba Abbasu suke so su kashe. Kama ni tarko ne kawai."
Rabi najin haka taci birki. Fulafunu da Maikiro Zarru suka tsaya suna kallonta suna jira suji mai zata ce.
"Ku tsaya," inji Rabi. "Baba Abbasu yana cikin hatsari."
"Eh? Wannan ma Anbalun ne ya gaya miki?" Fulafunu ya tambaye ta cikin al'ajabi.
Rabi ta gyaɗa kai.
"Kaga, Fulafunu," inji Rabi. "Ni fa ko kai baza ka koma ba ni zan koma."
"Mai ya faru da fara taimakon Anbalu," inji Fulafunu. "Naga kece kika ce Anbalu shi ne mafi a'ala kuma shi yafi kamata mu kubutar kafin Baba. Har kina cewa Baba zai iya kare kansa. Mai ya faru kika canja shawara?"
"A da babu Ashura a zancen," inji Rabi. "Idan Ashura sun sauka to tabbas so suke yi su halaka Baba. Tabbas ya kamata mu taimaka masa. Anbalu zai iya jira."
Fulafunu ya yamutse fuska. Ya rasa meye yake masa daɗi a rai. Tuni ya fara dana-sanin biyo Rabi.
Rabi bata bashi dama yayi dogon tunani ba. A lokacin ta juya ta nufi gari ta bar Fulafunu a tsaye a wajen. Maikiro Zarru ya bin bayanta.
A can bakin gaɓa kuwa yaƙi yayi tsamari tsakanin masu bakaken idanu da Abbasu. Shi kaɗai gayya.
Ana tsaka da yaƙin Haruta da Maruta suka bayyana. Haruta yana riƙe da Kulu a sume. Maruta kuma yana rike da Shema'u tana ta wutsil-wutsil amma ta kasa kwacewa.
"Ko ka tsaya ko kuma mu kashe ƴaƴan ka," inji Maruta.
Abbasu da Dul'Ururu suka juyo suka kalli ma'abota Ururun biyu.
"Zaka yadda ka zama sarkin jinzidal ko kuwa zaka bijire mu kashe ƴaƴanka?" Inji Haruta, ya ɗaga Kulu sama Abbasu ya gani.
Abbasu ya haɗe rai. Babu abinda yaƙi jini irin barazana da rayuwar yara. Tabbas koma mai sarkin jinzidal ɗin nan take nufi bazai karba ba. Kuma sai yayi hukunci akan wannan fitinannu dake aikata fasadi aban ƙasa.
Ana cikin haka Rabi ta ƙaraso. Tana zuwa bata tambayi ba'asi ba ta haɗe hannu guri guda. Wani shingen haske ya bayyana ya kewaye Shema'u da Kulu a inda suke a hannun Haruta da Maruta.
Haruta da Maruta sukai jifa da Kulu da Shema'u hannunsu yana tururi. Hasken ya kona musu fata.
Ana haka sai Uznu Ururu da Yurba suka bayyana sun kamo Fulafunu da Anbalu. Suna zuwa sai suka tsaya daga nesa.
"Mun san yadda fasahar kafin ki take aiki," Yurba ya gayawa Rabi. "Kina yin taku ɗaya kusa damu zamu kashe ɗaya. Idan kika ƙara taku ɗaya mu kashe ɗayan."
Rabi ta dakata domin har ta ɗaga ƙafa. Tana iya samar da kafi ta hanyar yin taku da kuma motsa hannu. Babu wanda yasan wannan sirri sai Baba Abbasu, sai yan uwanta, sai kuma hadiminta Zarru. Ta yaya wannan mutane suka sani?
Maruta ya juyo ya fuskanci Maikiro'Abbas.
"Zaka karbi muƙamin sarkin jinzidal ko kuwa sai mun kashe wani?"
Maikiro'Abbas ya ƙurawa Anbalu da Fulafunu ido. Tabbas bashi da ƙarfin dazai tsallake Dul'Ururu yaje ya ceto su. To amma kuma bashi da niyyar karbar wannan muƙamin da bai san meye ba.
A nata ɓangaren Rabi lissafi ta shiga. Wato bayan ta taho Fulafunu bai tafi ba biyo yayi. Sannan kuma bayan sun rabu dasu Shema'u, Haruta da Maruta suka tare musu hanya suka kama su. Duk abin yayi tsari da yawa ace ba tsara shi akai ba. Da fasahar ta da ta Kulu suna taimakon juna. Idan suna tare ko Maruta bazai iya cin galaba cikin sauki akansu ba. Sannan da fasahar Shema'u data Fulafunu suna taimakon juna. Idan suka haɗa ƙarfi da ƙarfe zaiyi wuya Uznu da Yurba yaci galaba akansu. Wato kamar ana sane aka raba su. Sannan akayi amfani da wannan damar aka kama su. Dama anaso ayi amfani dasu a tursasawa babansu ya karɓi wannan banzan muƙamin wai shi sarkin jinzidal.
Rabi ta ɗanyi shiru tana tunani. Ta yaya har aka raba su basu kula ba? Waye ya raba su... A lokacin ta tuna da Maikiro Zarru da kuma yadda ya basu shawarar suyi kuri'a. Tabbas badan bayyanar hadimin nata ba da babu yadda za'ai su rabu. To amma kuma ta yadda da hadimin nata. Yau shekarar su biyar kenan suna tare. Ita ce ta ceto shi a yayin da ake ƙoƙarin kashe shi. Tun daga wannan rana yake yi mata aiki. Babu yadda za'ai ya cuceta.
A hankali ta juya inda ta bar hadiminta Zarru domin tayi masa tambaya. Cikin mamaki taga baya wajen. Ta juya baya, nan ma taga baya nan. Ta ƙara juyawa hagu da dama, nan ma duk baya nan.
Zuciyarta ta fara dukan uku-uku. Shin hakan yana nufin Zarru ya munafince ta ya haɗa kai da abokan gaba, ko kuma dai ya tsaya ne a baya? Ko kuma wani ya kashe shi ba tare da ta kula ba? Koma dai meye zata yi bincike a hankali bayan sun fita daga wannan tarko. A halin yanzu babban abinda ya kamata shi ne ta kubutar da Anbalu da Fulafunu daga hannun Uznu Ururu da Yurba.
"Kina matsawa zan murkushe ɗaya," inji Uznu, ya matsa wuyan Anbalu da safar dake hannunsa wadda akayi da jan hayaki.
Rabi ta cije baki. Tabbas baza ta bari ya kashe yan uwanta ba. Kuma baza ta bari Baba Abbasu ya durkusawa abokan gaba ba.
Sai dai shi Baba Abbasu Bai yadda da hakan ba. A nasa ɓangaren yana ganin rayuwar yaransa tafi muhimmanci akan sunansa da kuma buwayarsa.
"Duk da ban san mai sarkin jinzidal ɗin take nufi ba," inji Baba Abbasu. "Amma zan amince da..."
Rabi ta riga ta ƙuduri niyyar baza ta bari ba. A dai-dai wannan ɗan taƙin kafin Abbasu ya ƙarasa furucinsa tayi taku guda ta haɗe hannayenta. Farin haske ya bayyana ya rufe Shema'u da Fulafunu. Uznu da Yurba sukai jifa dasu daga hannunsu saboda zafi.
"Sai ni amanar Maikironomada," inji Rabi, tana cika baki. Sai dai a lokacin ta fuskanci kamar ita kaɗai ce take murna a ɓangarensu.
Acikin kafin data rufe Anbalu jini ne yake kwarara daga wuyansa. Uznu ya murde masa wuya kafin ta ƙarasa samar da kafin. Shema'u da Fulafunu da Kulu duk suna nan lafiya acikin kariyar kafin, amma Anbalu ya daina numfashi.
Rabi ta kwalla ƙara.
"Zaka amince ka zama sarkin jinzidal ko kuwa?" Maruta ya ƙara tambayar Abbasu. A lokaci guda hankalin Rabi ya fara gushewa saboda ganin jinin ɗan uwanta. Hakan yasa kafin data rufe su Shema'u dashi ya fara yin hatsa-hatsa zai ɓace. Maruta yayi amfani da damar ya ƙara cafko wuyan Shema'u. "Zaka amince?"
Maikiro'Abbas ya cika da tausayin Rabi. Yasan halin ƴarsa sarai. Akan abu ƙalilan sai ta daɗe tana jimami. Tabbas idan tayi sanadiyar mutuwar ɗan uwanta baza ta iya rayuwa da alhakin ba. Sai da har yanzu akwai sauran dama. Yana jiyo ragowar rai a jikin Anbalu. Watakila idan aka kai shi wajen Numbula mai sirace ta iya warkar dashi.
"Na amince," inji Maikiro'Abbas. Yana ganin babu buƙatar a ƙara ɓata lokaci.
Da wannan Maikiro'Abbas ya zama sarkin jinzidal na farko. Rabi ta ɗauki Anbalu suka garzaya wajen Numbula mai sirace aka fara yi masa magani. Amma daga ƙarshe Anbalu ya riga mu gidan gaskiya. Tun daga wannan rana Rabi tayi alƙawarin ta daina taɓa kafi. Ta dawo ta tara hankalinta akan fasahar warkarwa. Tana ganin da ace ta kware a wajen warkarwa da Anbalu bai mutu ba.
***
Idan muka dawo filin jiri kuwa yaƙi yaci gaba da wakana. Rabi tana kallon kafin tana tuno ɗan uwanta Anbalu. Watakila badan abinda ya faru ba da tuni Anbalu yana raye.
"Rabi," inji Fatima. Ta ɗago kai suka hada ido. "Har yanzu ban san hakikanin abinda ya faru da Anbalu ba. Amma daga ganin idanunki nasan kina jin ciwo a yanzu. To amma idan baki karya kafin nan ba zaki rasa wasu ƴan uwan yanzu."
Fatima ta kalli inda Najunanu yake fafatawa da Han'ibal. Sannan ta kalli inda akwatin ƙanƙarar yarima Umaru yake. Da kuma inda yarima Abba yake akan iska yana lilo.
"Sannan kuma zaki rasa jarira," Fatima ta nuna kanta.
Rabi ta zare ido inda kwalla guda ta faɗo.
***
A shekarar da aka kawo Fatima gidan Maikiro'Abbas, akwai mai aiki wadda ake kira da Jummala.
A kullum Jummala zata ɗauki Fatima tana yi mata wasa a ƙofar ɗakin Rabi. Ga Fatima da shegen kuka. Kullum sai ta tashi Rabi daga bacci.
Ran nan dai Rabi ta gaji ta fito a fusace ta dakawa Jummala tsawa. Jummala ta firgita tayi jifa da Fatima ƙasa. Kan Fatima ya bugu da ƙasa ta ringa tsala kuka. Ita kuwa Jummala ta juma da suma tun sanda Rabi ta daka mata tsawa. Dolen Rabi ta ɗauki Fatima ta fara rarrashinta.
"Ke ishiru, jinjirata!"
"Mai kike so, jinjirata?"
"Ko ruwa ko madara, jinjirata?"
"Ko ƙanƙara ko buski, jinjirata?"
"ALLAH yasa naga auren jinjirata."
"Harma naga ƴaƴan jinjirata."
"Dama naga jikokin ta ma."
"Ke ishiru, jinjirata!"
A hankali Fatima tayi shiru. Daga baya sai ta fara dariya. Koda Rabi taga murmushin jaririyar sai taji farin-ciki a ranta. Daga nan ta fara son Fatima. An rawaito dai a ɗakin Rabi aka ƙarasa raunon Fatima.
***
Jin Fatima ta kira sunan 'jinjira' sai Rabi ta dawo hayyacinta. Duk da Anbalu ya tafi har yanzu tana da ƴan uwa. Tana da jinjirarta.
Rabi ta miƙe tsaye. Ta kalli Fatima ta gyaɗa mata kai gami da murmushi. Sannan da sauri tayi taku ɗaya gaba, ta juya gaba tayi biyu, ta dawo da baya tayi ɗaya da rabi. Daga nan ta juya sau uku sannan ta fuskanci kafin. Tana haɗe hannunta guri guda sai kafin ya ɗau haske. A hankali ya fara ƙonewa. Hatta wanda ke nesa suna hango hayakinsa.
Sannu a hankali kafin ya dunkule guri guda izuwa wani koren haske. Rabi ta zira hannu ciki taji ya wuce. Ta juyo ta kalli Burjan da Nusi tayi murmushi.
Ta karya kafin kamar yadda tazo yi. Abinda kurum ya rage shi ne a shiga a karbo Fatima daga hannun Maruta.
"Mama," inji Fatima. "Kinyi nasara. Kin karya kafin."
Armad yana daga nesa ya hango abinda ke faruwa. Duk da faɗansa da Dul'Ururu baya tafiya yadda ya kamata amma sai da yaji farin ciki.
Dul'Ururu ya kawowa Armad damƙa da hannunsa na hagu. Armad ya ɓace gab da sanda hannun zai taɓa shi ya bayyana a bayan Dul'Ururu yakai masa naushi da Hannun Aradu. Walkiyar ta sauka akan Dul'Ururu amma a banza. Ko gezau baiyi ba.
Ganin haka sai Dul'Ururu ya tsaya cak ya daina bin Armad.
"Armad," inji Dul'Ururu. "Baka da fasahar da zata iya cutar dani. Amma ka samar da wata fasaha mai ban mamaki. Kamar tana da hankali nata na kanta. A duk sanda nake gab da samun ka sai ka ɓace. Idan abubuwan suka ci gaba da tafiya a haka zaka ɓata min suna. Mai zaj hana baza ka gayamin sirrin wannan fasaha ba, ko nayi maka hukunci kowa ya huta?"
Armad yayi murmushi.
"Dul'Ururu sarki bisa doron ƙasa ta biyu," inji Armad. "Shin da daɗi ganin fasahar da baka da ilmi akanta?"
Jin haka Dul'Ururu ya ɓata rai.
"Amma kada ka damu," inji Armad. "Ina da kyakkyawar fahimta da abokan gaba ta. Musamman kasancewar nima ban fahimci fasahar da kake amfani da ita acikin sandar tsafin ka ba. Mai zai hana ka bani sirrin taka fasahar, nima na baka sirrin tawa?"
Dul'Ururu yayi shiru yana kallon Armad. Bayan ɗan lokaci ya buɗe baki ya ce, "a'a, kowa ya riƙe nasa sirrin."
"To shikenan," inji Armad. Yana rufe baki ya ƙara kaiwa Dul'Ururu sara da takobinsa. Dul'Ururu ya kauce bawai dan yana tsoron takobin ba.
To a yayinda Armad da Dul'Ururu suka ci gaba da kai-komo acikin filin yaƙin. A lokacin Burjan ya ɗauki hankalin kowa. Ganin kafin ya faɗi ya zare takobinsa ya afka kan Maruta.
Nusi ta motsa zata take masa baya amma Diwani ya shiga gabanta ya tare ta. Duk wanda ke filin ya juyo domin yaga mai zai faru. Kada dai a manta wannan shi ne karo na farko da mayaƙan Maikiro'Abbas suka samu damar karya kafin. A halin yanzu babu abinda ya raba su da Fatima sai Maruta. Idan kwamanda Burjan ya sare kansa shi kenan sun kwato Fatima.
Ganin haka Dul'Ururu ya rabu da Armad ya juyo da gudu yayi kan Burjan. Armad ya juya zai tare shi amma ya zille. Kafin Armad ya ƙara kiran wata fasahar Dul'Ururu yayi masa nisa.
Har Burjan ya ƙarasa wajen Maruta bai motsa ba. Sai da Burjan ya miƙa hannu zai ɗauki Fatima sannan Maruta ya motsa. Hannu a dunkule ya bayyana a saman Burjan. Sannan a wani sauri mai kama da walkiya ya naushi fuskar kwamanda Burjan.
Yadda kasan anyi cilli dashi, Burjan ya tashi sama yayi kololuwa sannan ya faɗo can ƙasa akan ƙanƙarar da Maikiro'Abbas ya samar. Takobinsa ta faɗa ƙasa can nesa dashi.
A firgice kwamandan ya tashi yana dube-dube. Ga dukkan alamu bai gama fuskarta abinda ya faru ba. Can dai hankalinsa ya dawo jikinsa ya shafa kumatunsa. A lokacin yaji ya kumbura ya tsattsage kamar an yanka da lauje.
"Marutal Ururiy, mutumin da yasan ranar dazai mutu!" Inji kwamanda Burjan cikin jinjina da yabo.
To a yayinda Burjan yake jimami, suma mayaƙan Maikiro'Abbas suna masu jimamin.
"Kai... Maruta ne!"
"Maruta yayi cilli dashi!"
"Ku kauce masa, shaiɗani ne!"
Su kuwa a nasu ɓangaren, mayaƙan Ururu shewa suka fara suna murna.
"Ƙani a wajen babban sarki Kuyurussa'ayi. Indai muna da Maruta ai bamu da sauran fargaba."
To a ƙasa kenan wajen ƙananun mayaƙa, a sama kowa ya ɗan dakata ana kallon Maruta domin a ga mai zai aikata nan gaba.
Maruta ya zaro wani allo daga cikin jakar tsafinsa. Ya ɗaga ƙaramin ɗan yatsansa na hagu ya ciza jini ya fito. Sannan yayi amfani da jinin yayi rubutu akan allon.
Diwani na ganin haka yayi dariyar mugunta. A lokaci guda ya kawowa Nusi duka da al'amudinsa. Nusi ta saka rassan bishiya ta tare. Sai dai bata san mai ya faru ba sai kurum ji tayi al'amudin ya sauka a ƙirjin ta anyi jifa da ita. Tayi sama bata faɗo a ko'ina ba sai can baya kusa da Burjan. A lokacin ta fuskanci kamar ƙarawa al'amudin Diwani ƙarfi da gudu akai saboda yadda ya fasa ta cikin rassan bishiyar data samar ya kuma dake ta ba tare da ta kula ba.
Wani abin haushi tana dira, sai ga Najunanu da Cokali sun dira a gefenta jikinsu yana hayaki.
Kafin su tambayi mai yake faruwa sai suka hangi mutun a sama. Ba shiri suka dare suka bashi guri. Jan doki ya diro tim a ƙasa. Can sai ga Zaikid ya faɗo daga sama inda suke faɗa da Yurba. Nusi tayi ƙoƙarin tare shi amma ya faɗo a kanta suka zube. Yanzu wanda kaɗai suka rage sune Armad da Nazára da Rabi.
Wani abin mamaki har yanzu hasken kafin daya dunkule guri guda bai gama ƙonewa ba. Ana cikin haka sai kawai kafin ya juye ya koma gudan jini. Daga nan ya koma tsoka. Sannan ya juye izuwa siffar mutun. A hankali ya tashi ya zama mutum. Koda ya juyo sai jama'a suka fuskanci ba kowa bane illa Rabi da kanta.
Rabi ta kalli abin mai kama da ita ta ɓata rai. Shima ya kalleta ya haɗe gira kamar yana mamakin yadda take kama dashi.
Can dai abin ya gaji da kallon da take masa ya afka mata. Nan da nan aka ware sabon faɗa tsakanin Rabi da wannan abu mai kama da ita.
A ɗaya ɓangaren kuma Armad ya bayyana a bayan Dul'Ururu da fasahar Aiban'shisu. Dul'Ururu ya juyo ya kawo masa duka da sandarsa amma Armad yayi amfani da sabuwar fasaharsa ta Aiban'shisu ƙarni na biyu.
Armad yayi hatsa-hatsa zai ɓace amma kurum sai yaga Dul'Ururu ya ƙara mahaukacin sauri ya same shi. Kafin ya ankara ya daki ruwan cikinsa. Kayan cikin Armad suka yi sama. Armad yayi tarin jini da kayan hanjin sa ta baki.
Shima a gefe Nazára yana cikin tsaka mai wuya. Bai san meye dalili ba amma a lokaci guda Binani ya ƙara mahaukacin ƙarfi. A da idan Nazára ya samar da guduma yana iya karawa da gudumar da Binani ya samar. Amma a yanzu abin ya faskara. Karfen da Binani yake samarwa ya gagara yaƙi lalacewa. Fasa shi bazai yiwu ba.
Nazára ya samar da ɗan ƙaramin gidan ƙasa wanda ya haɗa da yashin ƙarfe ya shiga ciki a boya. Duk inda Binani ya daka sai kaga ya burma yana neman fashewa. Dole sai ya ƙara yashi a gurin.
Armad duk yaga abinda ya faru. Ba komai bane illa rubutun da Maruta yayi acikin allon daya ɗakko a jakar tsafinsa. Bayan ya gama rubutun sai kawai Armad yaji izzar abokan karawarsu tana canjawa. Bawai yawa take ƙarawa ba, a'a, kawai dai tsarinta da fasalinta ne yake sauyawa. Hakan shi ne ya ƙarawa abokan karawar tasu ƙarfi. Kuma hakan shi ne ya bawa Dul'Ururu damar cin nasara akan fasaharsa ta Aiban'shisu ƙarni na biyu.
To amma idan Aiban'shisu ƙarni na biyu baza tayi aiki ba, mai ya ragewa Armad kenan?
Suna gab da samun nasara. Idan suka koma to abu ya dawo baya. Armad bazai ƙara komawa ba. Tunda ya riga yazo nan to fa bazai koma ba sai ya ɗauki mahaifiyarsa.
***
Bari mu koma duniyar aljanu, kafin a buɗe kurkukun lokaci...
***
Armad yana zaune a gefen gado. A kusa dashi Nostaljiya ce take kwance tana kallonsa. Suna sanye da kayan bacci duk kuwa da safiya ce wanda hakan yake nuna basu daɗe da tashi ba.
"Asali," inji Nostaljiya. "Kaban'shisu ka fara samu. Daga baya sai ka gyara ta ya zamanto kana iya amfani da ita a kullum da koda yaushe ba tare daka gaji ba. Da hakan kayi amfani ka fita daga kurkukun bango.
"Daga nan sai ka samar da Kaban'Zhisu. Bambancin wannan fasahar da Kaban'shisu guda biyu ne: na farko tafi Kaban'shisu dogon zango, na biyu kuma zaka iya daukan wani ko kuma wani abin da ita. Da haka ka kai mu duniyar aljanu.
"A yanzu kuma ka samar da Aiban'shisu. Ko zaka gayamin bambamcin ta da Kaban'Zhisu?"
Armad ya juya ya kalleta yayi murmushi.
"Sauri shi ne bambancin kawai. Kaban'shisu da Kaban'Zhisu duk suna ɗaukan tsahon dakika guda kafin su samu. Ita kuma Aiban'shisu rabin dakika kawai take ɗauka. Ko kinsan cewa Kaban'shisu da Kaban'Zhisu duk canji suke yi?"
Nostaljiya ta haɗe gira cikin kokwanto. "Ban gane ba. Wane irin canji kuma?"
Armad yayi murmushi. "Dabarar ita ce a samu ɗalasimin da zai iya canja muhalli. Kinsan dai kowane abu yana bukatar muhalli. Ko a yanzu dani dake duk acikin muhallin mu muke. Idan na ɗauki muhallin da kike na musanya shi da muhallin da nake ciki kinga zaki dawo inda nake, ni kuma na koma inda kike. A duk sanda nayi amfani da Kaban'shisu muhallin da nake shi nake canjawa da wani muhallin. Hakan yake bani dama na ɓace na bayyana a wani gurin. Da Kaban'shisu da Kaban'Zhisu duk irin wannan canjin muhallin suke amfani dasu.
"Fasahar Aiban'shisu ita ma canjin muhallin take yi, amma kuma iyakacin muhallin da ƙafar ka take kai banda na ragowar jikin ka. Misali, maimakon gaba ɗayan inda kike ya canja, sai iyakacin inda ƙafafunki suke ya canja. Ta haka na ragewa ɗalasimin aiki, a lokaci guda kuma na ƙara masa ƙarfi. Kin fahimta?"
Nostaljiya ta ɗanyi shiru tana lissafi a zuci kafin ta gyaɗa kai.
"Na fahimta," inji Nostaljiya. "A takaice dai maimakon izzar ka tayi aiki a gaba ɗayan jikinka sai ka tara ta a iyakacin ƙafarka wanda hakan yake ƙara maka sauri, ko?"
Armad ya gyaɗa kai.
"To na fahimci wannan," inji Nostaljiya. "Amma meye amfanin ita wannan sabuwar fasahar mai suna Aiban'shisu ƙarni na biyu?"
"Amfanin wannan fasahar shi ne taimakon akan lokaci kuma ba tare da ɓata lokaci ba," inji Armad. "Yaya zanyi idan na gamu da abokin faɗa mai tsananin sauri wanda yafi Aiban'shisu sauri? Misali ace an samu wanda yake iya tafiya cikin abinda bai kai rabin dakika ba. Nasan zaiyi wahala a samu hakan amma kada kiyi mamaki idan Ikenga ko Bihanzin ko Dul'Ururu sun samu irin wannan sauri. Kinga ita Aiban'shisu ƙarni na biyu bata da bambamcin sauri da asalin Aiban'shisun. Sai dai kurum tana da alaƙa da halin da nake ciki. Duk sanda aka kawo min hari zuciya ta zata buga da ƙarfin gaske. Fasahar Aiban'shisu ƙarni na biyu zata sa kai tsaye jiki na ya ƙaddamar da Aiban'shisu ba tare da na sani ba. Kamar dai kawai na bawa fasahar dama ne ta ƙaddamar da kanta a duk sanda na shiga matsi. Domin akwai lokacin da baza ka samu damar kiran ɗalasimin ba."
"Hakane?" Nostaljiya ta gyaɗa kai cikin fahimta. "Wato dai ka mayar da ita fasaha mai zaman kanta. A duk sanda aka kawo maka hari kawai zaka ɓace. Kayi dabara. Ina ganin fasahohin sauri sun ishe ka haka saboda..."
"A'a," Armad ya ɗaga mata hannu da sauri. "Ko kusa ko kaɗan basu isa ba. Duk wannan sharar fage ne kawai. Har yanzu akwai sabuwar fasahar da nake son na kirkiro. Tashi zaune na baki labarin izza."
Tuni Nostaljiya ta fara firgita da himmar Armad. Babu wani alamun zai taɓa tsayawa ya ɗan huta. A hankali ta tashi zaune ta rungume shi ta baya.
"Faɗa min naji," inji Nostaljiya.
Armad yayi gyaran murya ya fara jawabi. "Da farko dai akwai izza. Shekarar izza guda zata iya samar da ƙawanyar walkiya guda. Idan ka ƙarawa walkiyar shekara guda suka zama biyu sai girman walkiyar da ƙarfinta ya ƙaru. Kamar haka ƙawanyar da aka samar da shekara hamsin ta ninka wadda aka samar da shekara ɗaya ƙarfi sau hamsin. Wadda aka samar da shekara ɗari ta haura wadda aka samar da shekara casa'in da tara ƙarfi. A haka ƙassai da jemai suka tafi kan wannan tsari. Yawan izzar su ƙarfin su.
"Sai kuma Sammai wanda suke iya amfani da sinadarin dake cikin izza su samar da hari. Kamar misalin gyaɗa da man dake cikinta, Negrinki tafi izza gamsarwa. Yunit ɗaya na Negrinki dai-dai yake da izza goma zuwa ɗari zuwa sama. Ya danganta da irin izzar mutun. Kamar yadda aka riga aka sani izza kala-kala ce, kuma abinda yake banbanta su shi ne Negrinkin dake cikinsu.
"Kamar ni yanzu duk yunit ɗaya na Negrinki na dai-dai yake da izza ɗari da uku. Kinga idan ina da izza dubu dai-dai take da yunit goma na Negrinki kenan. Watakila zaki iya tambayar mai yasa nake miki wannan bayanin, ko? Dalilin shi ne ina so na bayyana miki na samo fasahar da bani da yawan izzar da zan gudanar da ita."
Nostaljiya ta zare ido cikin mamaki. Kamar Armad ace an samu fasahar da bashi da izzar dazai iya ƙaddamar da ita? Ba'a daɗe ba ya basu kyautar izza dubu goma-goma. Kuma yana iya zuƙar izzar mutane da kuma ta hare-harensu duk ya ƙara a jikinsa. Ta yaya za'a ce bashi da izzar da zata gudanar da hari?
"Wai yanzu izza nawa ce acikin tsarin ruhinka?" Ta tambayeshi.
"Ina da izza dubu ɗaya ta kaina," inji Armad. "Sannan kuma ina da izza barkatai ta mutane dana ɗiba na ajiye a tsarin ruhi na."
"Barkatai?" Inji Nostaljiya.
Armad ya gyaɗa kai.
"Kuma duk da haka kace akwai fasahar da baka da ikon amfani da ita saboda tsadar ta?"
Armad yaja ɗan numfashi ya runtse ido.
"Abinda mutane basu sani ba kenan," inji Armad. "A zahiri gidan Wilbafos muna da nakasu wanda babu wanda muke gayawa. Eh, tabbas muna iya zuƙar izzar mutane muyi amfani da ita mu ƙarawa kan mu shekaru. Sannan muna iya amfani da izzar da muka zuƙa mu kai hari. To amma izzar da muka zuƙa bata taɓa yin Negrinki. Misali, ni yanzu bazan zuƙi izzar ki kuma nayi tunanin zan samu Negrinki na aciki ba, domin kuwa kowacce izza tana da Negrinkinta. Sai dai zan iya amfani da izzarki na samar da harin izza amma bana Negrinki ba. Kin gane?"
"Hmm.. to, na gane amma kuma har yanzu ban gane mai kake so kace ba," inji Nostaljiya cikin tunani. "Kace duk izzar ka ɗari da uku tana yin yunit ɗaya na Negrinki. Ita kuma waccan izzar daka zuƙa bata yin Negrinki amma kuma zaka iya amfani da ita ka kai hari. To ai ni banga wata matsala ba anan, sai kurum kayi ta tara izzar mutane kana amfani da ita koda baza ta koma Negrinki ba."
Armad yayi murmushi. "Nima da farko abinda nayi zato kenan kuma ban taɓa sanin hakan bazai yiwu ba sai da nazo kan wannan fasahar." Armad ya juyo ya fuskance ta. "Wato, Armanos, akwai adadin izzar da tsarin ruhi na zai iya ɗauka. Kamar yadda kema akwai adadin da ruhinki zai iya ɗauka. Idan muka haura hakan, tsarin ruhinmu zai fashe mu mutu. Ni tsarin ruhina zai iya daukan adadin shekara dubu ɗari da uku. Duk abinda ya haura haka to bazai zauna acikin tsarin ruhi na ba, idan kuwa na takura ya zauna to zai fasa min ruhi."
Nostaljiya tayi shiru tana tunani. Tabbas hakan ya sauya abubuwa da dama. Maimakon yadda a da take tunanin Armad bashi da iyaka, a yanzu tasan yana da ita. Tunda dole idan tsarin ruhinsa ya cika ya tsaya da zuƙar izza. Watakila zai iya zuƙa ya raba, amma shi dai bazai yi amfani da ita ba. Hakan yake nuna akwai adadin fasahar da zai iya amfani da ita a kowane lokaci.
"Idan da ace zan iya maida izzar dana zuƙa ta koma Negrinki," Armad yaci gaba da bayani. "To da zan iya matse izzar komai yawanta na maida ita Negrinki. Ta hakan sai na sami ƙarin fili acikin tsarin ruhi na. To amma bazan iya haka ba. Duk izzar dana zuƙa tana da Negrinkinta. Bazan iya amfani da wannan Negrinkin ba tunda ba tawa ɓace saboda haka dole na haƙura nayi amfani da izzar a yadda take ba tare da zuƙi Negrinkin cikinta ba.
"Kinga a halin yanzu idan kika haɗa da izza ta dubu ɗaya da kuma wadda na zuƙa dubu ɗari da uku, zaki ga gaba ɗaya izza dubu ɗari da huɗu nake da ita. Bazan taɓa haura wannan mataki ba tunda a haka aka halicci tsarin ruhi na. Fasahar da nake so nayi amfani da ita tana buƙatar yunit ɗin Negrinki biyar duk rabin dakika, ko kuma nace adadin izza ta ɗari biyar kenan. Kinga yunit goma (shekara dubu) da nake dashi dakika ɗaya kacal zan samu. To idan da ace izzar da nake zuƙa takai ƙarfin tawa, to da kinga izza shekara dubu ɗari da uku zata bani dakika ɗari da uku kenan. To amma ina, har yanzu ban taɓa samun wanda izzarsa takai ɗaya bisa goman ƙarfin tawa ba. Kinga duk waccan tulun izzar har ta shekara dubu ɗari da uku? Bata wuce ƙarfin izza ta dubu goma ba. Kuma a haka izzar aljanu ce wadda tafi ta sauran mutane ƙarfi. Idan na koma duniyar mutane izzar zata rage ƙarfi. Daga abinda na lissafi bazan samu sama da dakika huɗu ba koda an haɗa da yawa izzar."
Sai a yanzu Nostaljiya ta gane mai Armad yake cewa. A takaice dai bashi da izzar da zata ishe shi ya aiwatar da wannan shiri. Sannan kuma Armad yana da iyaka. Akwai abubuwan da sunfi gaban ikonsa. Sai dai Nostaljiya har yanzu tana ganin akwai mafita.
"Mai zai hana ka ɗebi izza daga miyurar ka?"
Armad ya haɗe gira cikin mamaki.
"Daga miyura ta? Wacce izza ce kuma ta rage a miyura ta?"
"Wadda tun farko kake zuƙa? Wadda kace min ta iyaye da kakanni ce? Kaga dole zata fi sauran da zaka zuƙa ƙarfi. Ko yaya kake gani?"
Jin haka Armad ya fashe da dariya.
"Nostee, ai wannan izzar da nake zuƙa tun a baya dama ta wasu mutane ce, babu wasu iyaye da kakanni. To wane iyaye da kakanni wanda tuni sun daɗe a lahira? Dama farfesa ne yace min izzar iyaye da kakanni ce, ina ganin a lokacin yana ganin idan ma yayi min bayanin zaren izza bazan gane ba. Amma a yanzu na fahimta da kaina. Izzar da nake Arab a da ana zuƙo ta ne daga zarurrukan izzar dake cikin miyurar. Amma kamar yadda kika sani wannan izza bata zama tunda tsarin ruhi na bazai ɗauka ba."
Nostaljiya tayi turus. Wai shin ana nufin duk abinda suka taso suka yadda dashi akan miyura ba gaskiya bane? Kaga fa matsalar ma'abota izza kenan, sun fiya kulle-kulle.
"Amma idan haka ne Hidaya ta Farkon lokaci aljana ce ta musamman," inji Nostaljiya. "Na gani a yayin faɗan ka da ita a Babila yadda take iya canja launin Negrinki ya koma yadda take so, harma tana iya kwafar Negrinkin. To kaga kuwa idan haka ne duk izzar data zuƙa zata iya zuƙe Negrinkin dake cikinta tayi amfani da ita. Ta haka tsarin ruhinta bazai taɓa cika ba komai izzar data ɗiba. Sannan kuma zata iya amfani da duk wata fasaha a faɗin duniya."
Nostaljiya tayi shiru tana hakaito abin a ranta.
"Lallai Hidaya ita ce mafi ƙarfin bayi dana taɓa yin tsinkaye dasu."
Armad yayi murmushi. Tun tuni ya gano hakan. Wato kafin Hidaya ta kwafi Negrinki tana gano tsarin Negrinkin da duk wani sirrinta, ta yadda zata iya amfani da ita idan tana so. Kuma kamar yadda Nostaljiya ta faɗa babu wani mutum guda da Armad ya taɓa gani wanda yake da irin wannan iko na Hidaya a duk faɗin sama da ƙasa.
A wannan lokaci su biyun suka shiga bayani akan falalolin Hidaya har sai da maraice ya kawo kai.
"Ehmmm.. Armad," inji Nostaljiya. "Har yanzu baka gayamin wace fasaha ce kake so ka samar ba wadda take buƙatar izza da yawa haka. Ko sirri ne?"
Armad yayi murmushi. Ya zata baza ta tambaya ba.
"Sirri ne," inji Armad. "Amma tunda ke sanyi ido nace zan gaya miki."
Nostaljiya tayi murmushi mai sanyi tana kallon Armad kamar wanda taga baƙo.
"Sanyi ido kaɗai?" Inji Nostaljiya.
Armad ya fashe da dariya.
"Kina ji ko, Armanos, ita wannan fasaha bana so kowa ya santa sai a faɗan ƙarshe. Da ita nake so nayi nasara akan abokan gaba."
"Faɗi ina jin ka," inji Nostaljiya.
Armad yayi gyaran murya ya fara bayani.
"Kin san da Kaban'shisu da Kaban'Zhisu da Aiban'shisu duk muhalli suke canjawa kamar yadda nayi miki bayani, ko? To sai nayi wani tunani, mai zai hana, a dai-dai sanda ake samun canjin muhallin na tsayar da ɗalasimin. Ke kin taso daga inda kike zaune, nima na taso daga inda nake zaune, ɗalasimin ya ɗauke mu da niyyar ya musanya mu. Mai zai faru idan na tsayar da ɗalasimin akan hanya? Ke baki ƙaraso ba, ni ban ƙaraso ba, duk muna kan hanya."
Nostaljiya ta haɗe gira cikin rashin fahimta. "Hakan zai yiwu?"
Armad ya gyaɗa kai. "Mai zai hana? Sai dai tsada da kuma ba'a san mai zai faru ba."
"To ka gwada?" Inji Nostaljiya.
"Na gwada mana," inji Armad. "Da ban gwadaba da ban san tsadar fasahar ba. Na gwada da Kaban'shisu, na gwada da Kaban'Zhisu, sannan ma gwada da Aiban'shisu. A kowane lokaci komai na duniya yana tsayawa cak ya ƙame. Babu wani abu dazai motsa sai ni kaɗai kwallin-kwal. Har zuwa sanda izza ta zata ƙare sai ɗalasimin ya dawo yaci gaba da aiki. Na kan ganni a sama kan iska na bayyana. Ni zan iya motsawa tsahon dakikun da nake dasu, amma babu wanda zai motsa sai ni. Hasalima babu wanda yasan abinda yake faruwa a wannan lokaci sai ni. Zan iya ɗaukan abu na canja masa waje. Zan iya kai hari ko kuma nayi koma mai nake so. Amma kuma komai a izza ta. Kinga idan nayi amfani da fasaha mai ƙarfi zan rage yawan ƴan dakikun da nake dasu. Har yanzu dai..."
Armad ya dakata da bayani ganin bakin Nostaljiya yaƙi rufuwa.
"Kana nufin kana iya tsaida lokaci kenan?" Inji Nostaljiya da ƙarfin tsiya. Armad yana da tabbas har su Cokali dake ƙasan tsibirin sai sun ji mai tace.
"Eh...to," inji Armad. "A zahiri kamar hakan ne. Ina ganin fasahar tana tsayar da dakika ne ta kuma hana dakikar gaba zuwa. Kamar ace tsakanin wannan dakika da wannan an samu wasu dakikun wanda ni kaɗai nake da iko acikinsu. Idan nayi amfani da ɗalasimin Aiban'shisu tsadar fasahar tana ƙaruwa, amma kuma ƙarfinta yana ƙaruwa. Ina ganin Aiban'shisu tana raba dakika ɗaya gida biyu. Sannan a tsakanin ɓari biyun sai ta bani lokaci nayi abinda nake so matuƙar ina da izza. Sunan wannan fasaha Aiban'Zhisu, babban ƙarni."
Comments
Post a Comment