Skip to main content

BABI NA 278

A lokacin da Suwainah ke ƙoƙarin haɗiye Inara da ƴan-goma, a ɗaya ɓangaren kuma Hanibal ne ya fiddo da wani sabon salon. Nazara, da taimakon Nusi, ya samu damar binne shi a ƙarƙashin ƙasa, to amma kawai sai ji sukai iskar bayan wajen ta ƙara ɗaukan zafi. Kafin su ankara dunƙulen wuta ya haɗiye su. Sarkin aljanu Wut-Naru ya bayyana acikin wutar ɗauke da masu uku na wuta. Kowanne mashi da sunan ɗaya daga cikin su a kai. 


Kafin su shirya wasu sabbin hannaye guda uku sun bayyana a ƙirjin Wut-Naru. Kowanne hannu ya riƙi mashi guda ya kaiwa ɗaya daga cikin su suka. 


Wani abin mamaki shi ne hannayen wannan aljani kawai miƙewa suke suna ƙara tsayi kamar ana jan taliya. Asalin jikin aljanin yana waje guda a tsaye bai motsa ba, amma hannayen nasa kawai ƙara tsayi suke suna tunkarar su. 


Nazara ya daki ƙasa da ƙafar sa, lamarin da yasa manyan rassan bishiyar kaɗanya uku suka bayyana. Kowanne sanda ya juye izuwa hannun basamude ya riƙe hannayen aljanin. 


Nusi da Farin Yashi sukai ajiyar zuciya. Domin aljanin yaso ya shammace su, badan taimakon Nazara ba da tuni....


"Aaarghh..."  Farin yashi yai ƙara. Yana duba ƙirjin sa yaga mashi ya faso ƙirjin ya fice ta baya. Ko ya akai aljanin ya fincike daga riƙon da rassan sukai masa? Wannan babu wanda ya sani.


Nazara da Nusi sun kaucewa nasu masun duk da kuwa cewa a lokaci guda suka gan su da Farin Yashi. Wataƙila sabida taimakon halwar da sukai a duniyar aljanu.


Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su da aljanin. A gefe guda Farin Yashi yana kwance a ƙasa cikin jini. Nusi tana so taje kan sa ta shafa masa magani domin tsayar da jinin, to amma a halin da ake ciki tana ɗauke idon ta daga kan aljanin labari zai sha ban-ban. Suna cikin wannan hali suka ji murya a bayan su.


"Hmmm... Sama da shekara ɗari nake sarkin Jinzidal." Inji Hanibal. Abin al'ajabi yana tsaye kan ƙafafun sa, jikin sa ya dawo dai-dai babu alamar ciwo, kamar bashi aka tatsile yanzu ba. Wani abu daya ƙonawa Nazara rai shi ne Hanibal na zaune akan aljanin sa Bil-Bishiyaini, ya maida shi kujera. 


Hanibal ya ci gaba da bayani ba tare da kula cewa Nazara yaji haushin zama akan aljanin sa ba.  "A ƙarƙashi na akwai dakaru ma'abota izza marasa adadi. Nayi shekaru ina wasa wuƙa ta. Kuna ganin zai yiwu kuci galaba a kaina da shirin ƴan kwanaki? Sannan kuma..."


Hannun ƙashi ya fito daga ƙarƙashin ƙasa ya caki marar Hanibal ya yaga fatar ya shige cikin sa. Take Hanibal ya faɗi ƙas kan gwiwowin sa, idanun sa cike da mamakin yadda wannan hari ya same shi ba tare da yaji tahowar sa ba. 


Shi dai wannan hannu ɓarangwal ne. Launin sa baƙi-ƙirin, yana kyalli kamar an shafa masa mai. Ƴan'yatsun suna bada wani haske kamar an shafa musu zaiba. Ga kuma wasu farata masu tsayin gaske. Kowanne farce a fiƙe kamar takobin. Lallai ko wanne ɓarangwal ne ke da wannan ya jima bai yanke farce ba. Zaka iya cewa rainon faratan yake idan ka duba yadda ya fiƙe fasalin su izuwa fasalin takobi.


*Tari*Tari* 


Tari mai haɗe da aman jini baƙi-ƙirin ya kwacewa Hanibal. Ya miƙa hannu ya ɓalle hannun, sannan ya zare ragowar ƙashin dake tsire a cikin marar sa ya jefar. Fitsari da jini suka fara ɗisa daga marar sa.


"Naji kana cewa aljanu basa ciwo, ko?" Inji Nusi. 


Hanibal ya cije baki. "Kin gano sirri na cikin ƙanƙanin lokaci. Lallai kin cancanci yabo. Ba a banza Nazara ya ceto ki daga bara da yankan aljihu ba." 


Nusi ta gƴaɗa kafaɗa, ko kaɗan abinda ya faɗa bai dame ta ba. "Kana zigani da yawa. Fasahar taka ai ba wata ingantacciya ba ce. Babu wani mutun da yake iya narkewa baki ɗayan sa banda shugaba Armad. Hatta masu amfani da fasahar Laidan idan ka yanke zaren shikenan. Kai kuwa a duk sanda zaka narke dabara kawai kake yi ka tara kurwar ka da izzar ka a mara (mtsww.. kamar wata mai ciki) sannan sai ka narka ragowar. Abinda ban gane ba shi ne: bayan mun tatsile ka ɗazu ina kurwar ka da izzar ka suka tafi. Na tabbatar har marar ka muka tatsile." Nusi ta ɗanyi shiru tana tunani kafin taja dogon numfashi. "Ah... Na gane. Da farko ne kawai kake buƙatar ka kula da kurwar ka. Jikin ka yana fara narkewa, kurwar ka dake ajiye a mara zata narke izuwa tsoka da jini ta sake gina wani jikin sabo. Wanda bai lura ba sai yaga kamar jikin kane na da. Amma a zahiri sabon jiki ne. Mtsww.. wai mai yasa dakai da Bihanzin kuke ƙoƙarin kwaikwayon fasahar Sikai ta shugaba? Ku baza ku ƙirƙiro sabon abu ba." 


"Hahaha...." Hanibal ya bushe da dariya. "Kina tunamin da Baƙar Wuta. Kinyi wayo da yawa. Sai dai kada ki manta masu wayo irin ku da wuri suke mutuwa. Ina da tambaya: shin tayaya kika ga kurwa ta? Bawai a fili na barta yadda kowa zai iya gani ba. A'a, a ɓoye take sosai tayadda hatta Ururu basa iya ganin ta. Zaka iya cewa kurwa tama fi ruhi wahalar gani. Amma tayaya..."


Nazara ya katse shi. "Bamu da lokacin hira dakai, wataƙila bayan an gama yaƙin ruhi, amma yanzu muna buƙata ka miƙa wuya. Yanzu-yanzu, cikin tsananin zafin nama ka fito da duk bayin dake garin nan, ka kuma biya kowa bautar da yayi maka ta shekaru."


"Da gaske?" Hanibal ya wage baki cikin mamaki. "Acikin gari na, ina kewaye da Salsa na, ina tare da runduna ta... ku huɗu kacal ku yi nasara akai na, mutun yana ganin ko da babu Ururu hakan baza ta taɓa faruwa ba. Wai shin kun san walƙiyar nan ta ɗazu mecece?!"


Ƴan mintina da suka gabata anga walƙiya da tsawar aradu wadda ta garwaye ko'ina a faɗin duniya. Bayan ƴan daƙiƙu komai ya ɓace ya koma dai-dai. Tsakanin Nazara da Nusi da Farin Yashi babu wanda yasan daga ina walƙiyar take. Kuma tunda ana tsaka da fafatawa babu wanda ya damu ya tambaya. Amma ga dukkan alamu Hanibal yana da masaniya akan zancen. 


"Ashura... A'a, Tasu'a ne suke fafatawa da manyan ku wato Fatima, Taidara da Zaikid." Inji Hanibal.


Nusi ta kalli Nazara sukai jim. Akwai bayanai da suka gayawa juna ta cikin wannan kallon wanda babu wanda zai gane sai su. 


Nusi ta dubi Hanibal ta ce, "kada ka ce min yanayin izzar ka ne ya kai ka ga wannan faɗa, domin nasan bai kai ba, sabida haka labarin ka yafi kama dana ƙanzon-kurege. Zan fi yadda da zancen ka idan kace min hasashe kake. Kana ganin Ashura zasu sakko su kare jinzidal, su kuma su Fatima da Taidara zasu tare su."


"Ƙanzon-kurege? Hahaha... Wataƙila yanayin izza ta bai kai ba, wataƙila kuma ya kai, meye banbanci? Muhallish-shahid anan shi ne babu wanda zai kawo muku agaji. IBRAHAM NIL da kansa ya sakko ƙasa domin ganin bayan duk wani ɗan ƙabilar Wilbafos da yai saura wanda basu kashe ba a yaƙin Rukunai Biyu."


Ibraham Nil?! Nusi ta kalli Nazara cikin wasu-wasi. Ita bata san sunan ba, amma shi Nazara ya sani.


"Ibraham Nil shi ne shugaban wata ƙaramar jami'ar kimiya da bincike ta doron ƙasa ta farko. Ya taɓa zuwa a lokacin da aka hana baba Dalja cinikin ɗalasimai a shekarun baya. Ƙassai ne a lokacin. Nasan duk saurin sa bazai wuce Deba ba a yanzu." Inji Nazara. 


A sanin Nazara Ibraham Nil ba wani ƙasaitacce bane. 


Kamar an basu amsa sai Suwainah ta dira a gaban su kamar an jefo ta. 


Hanibal na ganin ta ya fashe da dariya. "Da sannu zaka gane waye Ibraham Nil." Ya nuna Suwainah ya ce, "Ga ɗaya nan daga cikin aikin sa."

Comments

Most Popular

297-300

 Armad da Nostaljiya na tsaye a gefen titi. Wata budurwa ƴar kimanin shekaru bakwai na tsaye a gaban su tana kallon ƙasa. Armad dai na sanye da jar riga yar-shara da baƙin wando. Tambarin Miyura na ɗamfare a goshin sa, sannan kuma, kamar kullum, idanun sa na hagu a rufe da audugar jamsiƙa. Ita kuwa Nostaljiya na sanye farar riga doguwa. Kanta babu ɗan-kwali tayadda gashin kan nata ya kwanto gadon bayanta. Duk inda ta motsa sai kaga gashin yana yalali yana haske abin sha'awa da ƙawa. Fatar jikin ta, kamar kullum, haske take bayarwa a duk sanda rana ta haska.  Amma duk wanda ya lura sosai zai gane cewa babban abin jan hankali shi ne wannan budurwa dake gaban su Armad tana kallon ƙasa. Rigar jikin ta baƙa ce dunɗum. Fatar ta ja ce jajawur kamar gashin kanta. Idanun ta kuwa wasu iri ne, maimakon alamar baƙin ido dake tsakiyar idon kowa ita takobin ce a tsakiyar idon ta. Kai hatta idon nata samfurin takobi ne - a fiƙe yake yake kallon doron ƙasa ta farko yanai mata izgili. Wani abi...