Babi na 129: Albishir
Bayyanar rundunar Uznu Ururu keda wuya labari ya fantsama cikin garin Jekis. Saƙo da loko duk inda kabi mutane ne cikin tsoro suna tattauna abinda ka iya faruwa.
A layin kasuwar Zána dake yamma da fadar garin Jekis masu ciniki ne sunyi cirko-cirko suna tofa albarkacin bakinsu.
"Wai da gaske ne Kwamanda Uznu Ururu ne yazo da kansa?"
"Haƙiƙa shi ne, wanda ya gani da idonsa ne ya gayamin. Sannan kuma ya zoda runduna ta Mayaƙan Ururu kusan dubu ashirin."
"To amma ance shi ba yaƙi yazo ba, wai kawai so yake a miƙa masa Armad angon gimbiya. Indai akai haka ba ruwansa da sauran mutanen gari."
"Kai.... To amma wannan ai abu ne da sarki Bihanzin bazai yadda dashi ba. Tunda an ɗaura aure ai shima Armad ya zama jinin sarauta, duk wanda ya taɓa shi ya taɓa sarautar Sisiya."
"Eh.. to. Da wannan dan wannan to amma babu wanda yake son faɗa da Mayaƙan Ururu. Kuma sunce Armad shi ne ya fara takalarsu ƴan kwanaki da suka wuce a garin Dúka. Kaga kamar za'ace laifinsa ne, ko?!"
"Hmm....."
"Duk wannan dai ya rage ga masarauta da sarki Mai-Dauwamammen-Sara."
"Eh lallai kuwa ya rage ya nasu, amma ance dukkan farar-hula dake kusa da badala ya koma tsakiyar gari wajejen fada akwai waje da aka tanada domin killace mutane."
"Ah.. Hakane fa. Muyi sauri tun kafin yaƙi kaure. Naji ance Uznu Ururu ya bada wa'adin sa'a ashirin da huɗu a miƙa masa Armad idan ba haka ba jini yai ambaliya."
Haka irin wannan maganganu suka ringa kewayawa tsakanin al'ummar garin Jekis. Babu wanda yasan mai zai afku, kowa yana cikin ɗar-ɗar.
Jama'a suka bi umarni suka koma tsakiyar birni. A yayinda Uznu ke tsaye a wajen badala yana jira a miƙa masa Armad.
***
Acikin fada kuwa akwai wani sabon ƙerarren gida mai yawan jajayen filawa. Acikin wannan gida akwai mutane biyu rak suna shaƙatawa. Idan da zaka samu dama ka leƙa gidan zaka ga ba wasu bane aciki illa Armad da Nostaljiya suna cin angoncinsu.
Armad ya dubi Nostaljiya cikin tsokana ya ce, "Wai yau kwana nawa?"
Nostajjiya ta haɗe rai cikin shagwaɓa. "Nima na sani!"
Armad ya fashe da dariya yana kallon cikinta lamarinda yasa ta kai masa duka da siririn hannuta. Ya goce sannan ya nufi ƙofa yana mata kwalo. Rai a ɓace Nostaljiya ta biyo shi suka rankaya a guje. Amma duk da haka Armad bai daina dariya da kwalo ba lamarinda yasa Nostaljiya ta fara ɗiban kaya tana jefa masa. To amma bisa mamaki kaf kayan babu wanda nauyinsa ya haura ɗan-taƙi hasalima kayan sawa ne na ciki na mata. Koda duk duniya zata taru ta jefi Armad dasu ko kwarzane bazai samu ba.
Saida Armad da Nostaljiya suka shafe rabin sa'a suna wasan jefe-jefe sannan Nostaljiya ta tsaya tana haki. Armad na ganin haka ya rikice ya juyo da sauri yana lallashinta.
"Kinga ki ringa hutawa. Kinsan ba ƙarfi ne dake ba. Izzarki duk ta juye ta koma kyau!"
Saura taku ɗaya Armad ya ƙaraso kusa da Nostaljiya tayi wuf ta cafi wuyan rigarsa. "Wululu.. Na kama ka, dama wayo nayima."
"Kai ka kai... Harda rinto? Gaskiya ban yadda."
"Ba wani rinto. Ni nace ka dawo? Kawai an kama ka, ka yadda an kama ka. Hukuncin ka shi ne...." Nostaljiya ta ɗan tsaya kaɗan tana kallon Armad cikin ƙissa da kisisina irin ta manyan mata kyawawa, kafin daga bisani ta ƙarasa. "Zaka wanke min kaya na gaba ɗaya! Ahe.. Saura kayi jiƙa-jiƙa."
Kafin Armad ya bada amsa Nostaljiya ta tattaro dukkan kayan dake cikin gidan ta ajiye a gabansa. Sannan ta tsaya ta riƙe ƙugu tana jiransa. "Muje zuwa, ahe!"
Armad ya dubi kayan yaga kaf kaya ne wanda mata su kaɗai suke wanke abinsu. Hasalima bai taɓa arba dasu ba sai bayan aurensa. Cikin kalar-tausayi Armad ya ɗauki kayan ya fara wankewa. Lokaci-lokaci zaka jiyo guna-guninsa ƙasa-ƙasa amma Nostaljiya tayi kamar ma bata san yana yi ba. Waƙarta kawai take.
Da yammacin wannan rana ne Armad yana ƙiris da gama wanki sai suka ji kwankwasa ƙofa.
Cikin zafin nama Armad ya fara ƙoƙarin ɓoye kayan da yake wankewa amma kan ya gama Nostaljiya tasa mayafi ta buɗe ƙofa. Iliyasis ne yai mata sallama sannan ya nemi izni ya shigo. Kai daga ganin fuskarsa kasan akwai damuwa.
Nan take yanayin gidan ya canja. Armad ya dube shi cikin kallo mai cike da tambaya. Iliyasis ya sunkuyar dakai tsahon lokaci kafin daga bisani ya ɗago kai ya dubi Armad ya kwashe labarin rundunar dake wajen gari kaf ya gaya masa.
Iliyasis ya ci gaba da cewa. "Tuni sarkin yaƙi Damjinu Djinn ya gama haɗa rundunar yaƙi kuma suna gabda fita waje domin yin arangama da Uznu. Ance kada a gaya maka amma dani da Cokali da Inara muka ga bai kamata mu ɓoye maka ba tunda kaima kana da haƙƙin ka sani."
Nan take Armad yai zumbur ya miƙe. Dukkan wani wasa da wargi ya fice a fusƙarsa. Walƙiya ta fara rawa acikin idanuwansa. Ba tare da ya ce komai ba ya miƙe ya shiga ɗaki yai shirin yaƙi sannan ya fito ya nufi ƙofa ba tare da ya kalli Nostaljiya ko Iliyasis ba. A zuciyarsa yana ji idan ya kalli idanun Nostaljiya yaga bata so to fa lalle bazai iya zuwa ba saboda haka ya yanke shawarar kada ma ya kalle ta. Iliyasis yana ɗaga ido yaga kwalla na kwaranya daga idanun Nostaljiya. Cikin sassanyar zuciya ya haɗa komatsansa ya bi bayan Armad.
Har sun fice daga ƙofar Nostaljiya tayi ƙarfin hali ta bisu da sauri. Tana fitowa ta kwalawa Armad kira. Armad ya tsaya yana jimamin waiwayowa ya haɗa ido da ita. Har zai juya ya tafi saiya jiyo fitar kwallarta. Nan take Armad ya juyo ba tare da wani tunani ba. Sannan ya rankayo ya dawo gare ta. Iliyasis na ganin haka yai sauri ya basu waje.
"Idan kika ce kada naje to wallahi bazan je ko'ina ba."
Nostaljiya taja dogon numfashi sannan ta amsa cikin shessheƙa da cewa, "nasan mahaifina bashi da matsala, to amma idan baka je ba sauran mutanen gari zasu iya yin mummunar fahimta. Ni nasan gwarzon jarumi na aura.. Kaje ka gama da abokan gaba ka dawo ni kuma zan gaya maka albishir mai daɗin gaske."
*ALBISHIR..* Armad najin haka ya zare ido cikin tunani.
"Wanne albishir zaki gayamin. Kinga gwanda ki gayamin yanzu kada naje filin daga ina tunani."
Nostaljiya tai dariya sannan ta ɗora hannunta ɗaya akan cikinta, ɗaya kuma akan Armad tana cewa. "Kai dai kaje ka dawo. Mai kake ci na baka na zuba."
Armad ya kalli cikinta zuciyarsa na dukan-dukan uku-uku. Koda Nostaljiya ta ga yana neman gane maike faruwa sai kawai ta turo ƙofa tana cewa. "Kaje ka dawo ina nan ina jiranka babu inda zanje. Kuma nasan zaka dawo ka same ni, mijina nawa ni kaɗai."
Nostaljiya da Armad na tsaye ƙofa ta raba tsakaninsu basa ganin juna.
Tsahon lokaci kafin Armad yai ihun murna sannan ya rankaya yabi bayan Iliyasis yana shewar farin ciki. Lallai zaiso yaji wannan albishir duk da yana da kyakkyawan hasashe akansa.
A wannan yammaci Armad ya fita filin daga a karo na farko a rayuwarsa.
***
Babi na 130: Fitar Armad
Sahu-sahu na Mayaƙan-Ururu dubu goma sha biyar na tsaye a bayan garin Jekis ƙarƙashin jagorancin Uznu Ururu. Duk bayan daƙiƙa ɗaya sai kaji wannan runduna ta haɗa baki sun kwala sunan Armad a wani yanayi na nuna buƙatar a miƙo musu shi.
Babu abinda kake ji sai ihu da kiraye-kiraye dake nuna laifinkan Armad a doron ƙasa. Duk sanda wannan runduna sukai magana sai kaji ƙasa ta girgiza, badala tayi ƙuwwa.
Sai dai kuma rundunar sarkin yaƙi Damjinu Djinn na tafe sun kusa ƙarasowa kusa da ƙofar gari inda zasu gwabza da wannnan Mayaƙan masu neman a miƙa musu Armad.
***
A tsakiyar babbar kasuwar wannan gari na Jekis Armad ne tafe dashi da Iliyasis da Inara da Cokali. Duk inda suka ratsa mutanen wannan kasuwa nuna su suke domin kuwa babu wanda baisan fuskar suba. Sannu a hankali Armad ya fara ɗaukar maganganun dake kewayawa a kasuwar.
"Shi ne."
"Su ne."
"Su suka jawo mana."
"Idan gaskiya ne su fita su kaɗai su yaƙi mayaƙan Ururu basai an haɗa da ƴaƴanmu ba."
Ba jimawa waɗannan maganganu suka fara ɓatawa Iliyasis rai. A tsakiyar kasuwa zafin rai ya ɗebe shi ya kaiwa wani gajeren mutun duka da hannu. Da kyar Armad ya bashi hakuri sannan suka rankaya suka fice daga kasuwar ransu a ɓace.
Bayan kimanin rabin sa'a suka fara hango rundunar Damjinu inda suka ƙara azama suka isa gare su.
Koda hangosu sai Damjinu ya bada umarnin a tsaya. Ya dubi Armad cikin mamaki amma ba tare da tambaya ba ya gane yadda akai labarin ya isa ga Armad. Ya buɗe baki ya ce, "Bama buƙatarka anan, ango."
Armad ya dubi Damjinu yai murmushi, "Nasan haka amma kasan mai mutanenku suke cewa akaina?"
Damjinu ya ja dogon numfashi sannan ya gyaɗa kai. "Kada ka zargesu, kaga duk wannan runduna dake baya na ƴaƴansu ne da jikokinsu da ƙannensu da iyayyensu. Dole suyi magana ganin cewa za'a turasu yaƙi saboda kai. Amma kada ka damu, a har kullum umarnin sarki Bihanzin shi ne akan gaba kuma sarki ya ce kada a miƙa ka koda dukkaninmu zamu ƙare."
"Hmmm..." Armad yaja dogon numfashi mai haɗe da ɗan murmushi ya ce, "Amma ai baice idan zan fita akan kaina ku hanani ba?"
Damjinu ya gyaɗa kai. A zahirin gaskiya Bihanzin baice su hana Armad fita ba amma dai ya hanasu miƙa shi ko kuma yi masa dole. Saboda haka yai shiru yana tunanin maiya kamata.
Bayan ɗan lokaci ya dubi Armad ya ce, "mai kake so ayi?"
Armad ya amsa da cewa, "ina so ku bar rundunarku anan ku bani dama na fita na fuskanci Uznu dan naji dalilin da yasa yake nema na. Ko naga idan akwai wanda ƙarfin izzarsa takai ya iya cutar dani acikinsu."
Nan take kace-nace ya ɓalle tsakanin Damjinu da Armad.
Damjinu ya ƙeƙasa ƙasa ya ce, "Ko ƙaɗan bazan amince da wannan batu ba."
Armad ya tari numfashin sa. "Lallai ni kaɗai zan fita na fuskanci Uznu kuma bawai na raina agajinku bane sai dai kawai bana buƙatarsa a yanzu."
Nan take su Iliyasis sukai ca akan Armad suna nuna rashin yaddarsu akan wannan shawara da ya yanke. Amma ina, tuni Armad ya riga ya yanke shawara.
"Kada ku damu. Ni Armad nayi muku alƙawarin zan dawo da rai da lafiya."
Har Armad ya juya baya ya nufi ƙofar gari sai Iliyasis da Inara suka bi bayansa. Ya juyo da sauri ya ce, "Ina zaku je?!"
Iliyasis ya kada baki ya ce, "kamar yadda bamu isa mu hanaka fita ba muma baka isa ka hana mu biyo ka ba."
Inara ya girgiza kai alamun amincewa. Murmushi kawai Armad yai suka nufi bakin ƙofa. Shi kuwa Cokali juyawa yai ya nufi fada gadan-gadan, bai zame ko'ina ba sai sabon gidan da Armad ya tare da Nostaljiya. Yana isa ya gaya mata abinda ke faruwa. Kafin Cokali ya hattama labarinsa tayi shiri ta fito ta nufi wajen gari domin dakatar da Armad.
***
Acikin wannan sihirtaccen fili da mahaifiyar Armad ta karɓi shekarun izza sarki Bihanzin ne ke zaune yana nazarin wani tsohon littafi dake gabansa. Babu kowa a wajen sai aljaninsa yana masa ƙidayar izza. Acikin wannan waje lokaci bashi da ma'ana, domin kuwa sai yadda Bihanzin yayi dashi. Sannu a hankali sa'o'i da dama suka wuce, sarkin yana ta nazarin wannan littafi baice uffan ba. Kwatsam sai ya miƙe zumbur ya ɓace daga inda yake.
Yana bayyana sai gashi acan tsakiyar fada a gaban Nostaljiya da Cokali a yayinda suke ƙoƙarin fita daga fadar.
Duk su biyun suka ja da baya da sauri, fuskokinsu cike da mamaki. Can bayan sun dawo hayyacinsu sai suka durƙusa sukai gaisuwa. Sarki Bihanzin ya gyaɗa kai sannan ya wuce gaban Nostaljiya ya tsaya.
"Ƴa ta, ina zaki je?"
Nostaljiya tai gyaran murya sannnan ta kwashe abinda ke faruwa ta gaya masa.
Bihanzin yai shiru tsahon ƴan daƙiƙu kafin daga bisani ya ce, "yau tauraruwarki na ɗauke da wani yanayi wanda ban taɓa jinsa ba. Ban san mai hakan yake nufi ba; alkhairi ko sharri, amma ina ganin ki zauna a fada kusa dani yadda zan iya kare ki idan wani abu ya taso."
Nostaljiya tayi murmushin girmamawa sannnan ta ce, "ya mahaifina, lallai babu abinda zai faru. Kuma nayi maka alƙawarin zan dawo na same ka lafiya-lafiya. Kawai dai so nake naga ko zan iya canja zuciyar mijina. Idan ma hakan bai faru ba ina so naga fafatawarsa da idona. Kuma sarkin yaƙi Damjinu yana wajen, lallai zai iya kare ni daga dukkan sharri."
Bihanzin yai murmushi tare da dafa kafaɗar Nostaljiya ya ce, "duk da haka dai zuciya ta na kokwanto. Amma na fuskanci dalilinki, kije amma kiyimin alkawari baza ki shiga faɗan ba ko mai rintsi komai wuya."
Nostaljiya ta gyaɗa kai. "Nayi alƙwari."
***
A ƙofar gari sadaukai goma ne suka buɗewa Armad da Iliyasis da Inara ƙofar garin. Jaruman uku suka rankaya suka nufi rundunar Uznu Ururu kai tsaye.
Kan kace meye wannan tuni labari ya bazu akan matakin da Armad ya ɗauka na fuskantar rundunar Uznu shi kaɗai. Wannan gayawa wannan labari ya gama gari. Ana haka sai mutane suka fara tahowa wajen badala domin ganewa idonsu koda gaske ake. Idan har da gaske ne to lallai zasu so suga wannna fafatawa tsakanin mutun ɗaya da Mayaƙan-Ururu dubu goma sha biyar. Ƙiftawar ido da bismillah bayan gari ya fara cika duk da ƙoƙarin jami'an tsaro nasu hana mutane zuwa amma hakan ya gagara.
Dubunnan jama'a sun taru domin ganin wannna al'amari mai kama da al'mara.
***
Babi na 131: Gajeriyar Fafatawa
Armad, Iliyasis da Inara suka hau dawakai suka durfafi wajen rundunar Mayaƙan-ururu.
Koda wannan runduna suka hangosu sai suka zare takubbansu suna jiran umarnin.
Uznu ya dube su yana murmushin mugunta. Saida ya rage saura taku bakwai su Armad su isa gaban rundunar sai Uznu ya ɗaga hannu yai nuni izuwa Armad yana cewa. "Ku kama minshi Mayaƙan-Ururu. Duk wanda ya kamo shi zan ɗaga matsayinsa sau bakwai na kuma yi masa kyautar duk abinda yake so guda ɗaya."
Koda jin haka sai wannan runduna suka haɗa baki sukai ƙaraji lamarinda ya girgiza ƙasar wajen. Sannan suka tunkaro su Armad a sukwane. Kafin su ƙaraso sai suka zagaya suka saka su Armad a tsakiya. Sannan suka bisu da ruwan masu da kibbau tun kafin su ƙaraso. A fusace Armad ya karanci abinda ke faruwa sannna ya bada umarni. "Iliyasis ka riƙe dama kai kuma Inara ka riƙe ɓangaren hagu. Ni kuma zan ratsa ta gabansu domin cimma Uznu."
Ba tare da musu Iliyasis ya cafi akalar hagu shi kuma Inara ya tsaya a dama. Armad ya buɗe bakinsa yai feshin farar walƙiya wadda nan take ta ƙone dukkan masu da kibbau da aka harbo. Sannan a wani saƙo na kwarewa ya dunƙule hannunsa na dama ya juyar dashi izuwa walƙiya sannna ya saukar da Hannun-Aradu akan wannan mayaƙa dake tunkaroshi.
Wata walƙiya mai yawan ambaliya da ƙuwwa ta fita daga hannun Armad ta dunƙule sannan ta rufe ɓangaren dama inda ta haɗa da duk wani mahaluƙi dake tsaye a wajen. Kan kace meye wannan duk wanda ke wajen ya ƙone ƙurmus babu abinda kake ji sai ƙarar wayyo da neman taimako. Armad ya ƙara saukar da wani harin a ɓangaren dama lamarinda ya bawa Iliyasisi da Inara damar ɓullewa sukai nasu harin. Shi kuwa Armad amfani yai da rikicin dake faruwa yai kan Uznu yai gadan-gadan.
Dubban mutanen dake hango Armad takan katanga sai ƙaruwa suke. Acikinsu hadda gimbiya Nostaljiya da Cokali wanda sukai amfani da rawani da hirami suka ɓoye fuskokinsu.
Kowa na ganin abinda ke faruwa. Duk inda Armad yai sai dai kaga maza na zubewa sun ƙone ƙurmus. Wani jan hadari mai yawan rugugi ya fara bayyana a sararin samaniya dai-dai kan Armad. Alamun Kwangila.
Armad kashe jaruman yake yana ƙoƙarin ƙarasawa wajen Uznu amma kamar ƙara yawa suke sunƙi ƙarewa.
Wasu mutun ɗari sukai ƙuwwa suka afkawa Armad ta ɓangaren dama, amma Inara yakai musu sara da takobinsa mai ɗauke da fasahar walƙiya wadda ya samu daga Armad. Kana gani kasan babbar kwangila yake amfani da ita.
Ta ɓangaren hagu kuwa Iliyasis shima ba'a barshi a baya ba, duk wanda ya kawo wa Armad hari sai yaga bayansa. Shi kuwa Armad kawai ƙone hanyarsa yake zuwa gaba. Ihu da ƙaraji ne kawai ke tashi kai kace acikin wuta ake.
Duk wannan abu dake faruwa Uznu na gefe yana kallo baiyi motsi ba har saida ya tabbatar Armad zai iya ƙarar masa da dukkan mayaƙa cikin ƙanƙanin lokaci idan baiyi da gaske ba.
Armad ya ɗaga hannu sama zai ƙara saukarwa da mayaƙan Hannun-aradu sai kawai gilmawar wata takobi ya gani ta gefen idonsa ta ɓangaren hagu. Yana dubawa ya ga Iliyasis ne ya tare saran Uznu Ururu da takobinsa lamarinda yasa takobin ta ɓalle tayo kan Armad.
Uznu ya ɓace daga kusa da Iliyasis ya ƙara bayyana a kusa da Armad ya kawo masa sara. Armad ya zare takobinsa a karo na farko inda ya rufe jikinta da walƙiya sannan ya tare takobin Uznu. Wata ƙara mai haɗe da ɗimbin ƙura ta tashi sama.
Kan kace meye wannan waje yayi tsit kowa hankalinsa ya dawo kan wannnan mutane biyu.
Armad ya ɗaga hannunsa na dama ya saukarwa da Uznu Hannun-aradu. Amma sai wani baƙin haske nai ɗauke da ratsin yalo ya futo daga idanun Uznu ya tare hannun Armad inda ya bada wata ƙarar.
Armad ya ƙara kawowa Uznu sara amma Uznu ya kauce. Kan kace meye wannan waje ya rikice da faɗan manya.
A gefe guda Armad da Uznu da wasa jini a ɗaya gefen kuma Inara da Iliyasis na fafatawa. Akan katangar na n kuwa Cokali ne ya dubi amarya ya ce, "bari naje na taimaki ƴan'uwa na kinga yawan mutanen sun musu yawa. Ki tsaya anan dan ALLAH kada kije ko'ina kinga amana aka barmin."
Nostaljiya ta gyaɗa kai alamun amince sannan ta bashi umarni ya je.
Ana tsaka da fafatawa jama'a suna kallon abin mamaki sai kawai aka ga wani ƙaton saurayi ya dira a filin hannunsa ɗauke da ƙaton littafi. Kan kace meye wannnan saurayin ya fara rubutu acikin littafin yana fito da wasu mahaukatan zaku na daga ciki.
Iliyasis ya waiwayo ya dubi Cokali yana murmushi ya ce, "Barka da zuwa ma'aboci fasahar marubutan farko"
Shi kuwa Inara kallonsa kawai yai yayi murmushi sannan suka ci gaba da aiki.
Waje ya turnuƙe da ƙura da ƙarar sadaukai. Hankakan mutuwa ya fara yawa yana ɗiban rayuka. Mutanen gari nakan katanga suna kallon abin mamaki. Kowa da abinda yafi ɗaukan hankalinsa. Wasu fasahar Armad ta Hannun-aradu ce wasu kuma fasahar cokali ta marubutan farko. Wasu kuma kwangilar Iliyasis da Inara.
A can gefe guda kuwa Armad me tsaye cak yana fuskantar Uznu a wani salo nayin nazari. Bayan ƴan daƙiƙu Armad ya ce, "Uznu na taɓa fafatawa dakai kuma nasan wannna ba shi ne iyakacin ƙarfinka ba. Idan har da gaske kama ni kazo yi to saika ƙara.zage dantse."
Uznu tai shiru yana kallon Armad baice komai har tsahon daƙiƙa bakwai. Sannnan daga bisani ya ce, "Zamu haɗu nan bada daɗewa ba mu fafata fafatawa ta musamman. Amma a yanzu na cimma abinda ya kawo ni, sai anjima."
Uznu na gama faɗar haka ya tafa hannayensa tare da kiran wasu ɗalasimai sannnan ya ɓace tare da rundunarsa. Hatta gawarwakin da suka mutu bai bari ba. Cikin daƙika ɗaya tak waje yai tsit kamar ba'a taɓa mutun ba a wajen.
Abin mamaki ya hana kowa magana. Armad ya dubi Iliyasis da Inara da Cokali amma duk cikinsu babu wanda yasan maike faruwa. Baki a buɗe cike da mamaki haka aka buɗe musu ƙofa suka dawo cikin gari. Suna shiga Cokali ya ce, "Ina zuwa ina da uzuri." Da niyyar yai sauri ya mayarda Nostaljiya gida ba tare da Armad ya sani ba.
Ya nufi inda yabarta gadan-gadan amma yana zuwa babu ita babu alamunta.
Da farko ya ɗauka canja waje tayi amma bayan awa guda yana dubawa ya tabbatar akwai wani abu a ƙasa. Ba shiri ya kira Iliyasis ya sanar dashi. Sannan suka sanar da Armad abinda ake ciki. Dukkansu suka rankaya fada hankali a tashe suna tunanin ko can ta koma amma babu Nostaljiya babu alamunta.
***
Babi na 132: Titin Bayajidda
Babu wanda yasan tayaya amma labari ya gama baza ko'ina cewa an sace amarya.
Washe garin ranar da abun ya afku jaridar Jinzidal ta rawaito wani labari da ɗumi-ɗuminsa. Duk inda ka kewaya a faɗin duniyar ƙasa bakwai wannan labari kawai ake tattaunawa.
Jaridar dai ta rawaito cewa sarakunan Jinzidal sun yankewa gimbiya Zahra da Armad Wilbafos hukuncin kisa saboda haɗa hannu da ƙarfe da sukai wajen kawo cikas ga gasar Jinzidal da kuma ƙin karɓar hukunci cikin sauƙi da sukai. Jaridar ta ci gaba da cewa Armad Wilbafos shi ne magajin wilbafos wanda ya gaji fasahar marigayi sarki Eyriyon. Jaridar ta bayyana cewa an kama gimbiya Zahra kuma za'a yanke mata hukunci a TSIBIRIN JALJUS dake kan titin Bayajidda na doron ƙasa ta uku. Sannan kuma duk wanda ya kamo Armad, a mace ko'a raye, zai karɓi kuɗin Ayrid miliyan ɗari biyu da hamsin.
A dai-dai wannan lokaci Armad na tsaye gaban sarki Bihanzin hannunsa riƙe da takobi fuskarsa baƙi-ƙirin. Bayan Armad dasu Iliyasis akwai kwamandu bakwai da sarakuna talatin da ɗaya a wannan fada. Kowannensu na tsaye cikin sulken yaƙi. Kallo ɗaya kacal zakaiwa fadar kasan cikin shirin ko a mutu take.
Kowa yayi tsit ana jira. Armad ne ya fara fitowa gaba yayi magana. "Zanyi gaba. Zanbi ta titin Bayajidda kamar yadda aka tsara. Zan tsaya a mararraba."
Armad na gama faɗar haka bai jira umarni daga kowa ba ya fice. Iliyasis da Inara da Cokali haɗe da wasu mutun goma suka bi bayansa. Kowannesu na sanye da jajayen sulke hannayensu riƙe da takobi.
Suna fitowa suka hau dawakansu wanda tuni suke jira a bakin fada sannan suka bazama sashin ƙofofin Eycigan wanda tuni aka gama gyara su aka ƙayata su domin amfani dasu wajen wannan yaƙi. Tun daga ranar da Armad ya nemi matarsa ya rasa bai ƙara dariya ba. Bai cewa kowa komai ba akan batun amma kowa yasan maike faruwa duk da cewa babu wanda yasan taƙamaimai halinda zuciyar Armad ke ciki sai shi kaɗai.
Idan ka dubi taswirar ƙasa bakwai zaka ga kowacce ƙasa tana da iyaka ta ɓangaren dama da hagu. Idan ka dubi ƙasashen da ke sashin arewa zaka ga a ɓangaren dama sunyi iyaka da ruwan Bango da kuma sashin ikwatora. To amma ta ɓangaren hagu kuma zaka ga babu komai a wajen sai fili.
Kaɗan ne daga cikin rayuka, bil-adama ko aljanu suka taɓa zuwa wannan sashe kuma suka gano menene aciki. Wasu sunce ruwa ne wasu sunce katangar ƙarfe ce wasu kuma sunce babu komai sai daji. Abinda kawai aka sani shi ne akwai katafaren titi wanda ya raba tsakanin ƙasashen da kuma wannan waje. Wannan titi shi ake kira da titin Bayajidda.
A doron-ƙasa ta uku akwai wani ƙaton tsibiri wanda ya fito tun daga doron ƙasa ta uku zuwa titin Bayajidda. Kuma wannan tsibiri shi ne sansanin mayaƙan sarki Han'ibal, sarki bisa doron ƙasa ta uku.
Wannan tsibiri yana da tsohon tarihi. Hatta sarki Amraikugyu Bayajidda da yazo gina titin Bayajidda bai taɓa shi ba. Kuma babu wanda yasan haƙiƙanin daɗewarsa a doron ƙasa, hasalima da dama suna ganin tunda aka halicci ƙasa bakwai wannan tsibiri yake.
Abu ɗaya sananne shi ne zuwa wannan tsibiri nada matuƙar haɗari kuma ba'a banza mayaƙan sarki Han'ibal suka maida shi sansaninsu ba. Ga ragowar mutanen duniya babban abin sharri ga wannan tsibiri shi ne yawan hazo. A sau da dama akanyi hazo mai kaurin gaske wanda yakansa ko tafin hannu ba'a iya gani. Amma banda wannan akwai sauran sihirce-sihirce dake gudana akan wannan tsibiri.
Bayan sace Nostaljiya kai tsaye aka tafi da ita wannan tsibiri aka sata a kurkuku. Sannan kuma cikin ƙanƙanin lokaci rundunar sarki Deniz Iluru data sarki Han'ibal data sarki Rafiya kai harma da mayaƙan Ururu suka bayyana a wannan tsibiri. Bayan doguwar tattaunawa, shugabanninsu suka yanke shawarar yankewa Armad da Nostaljiya hukuncin kisa. Inda suka buga labaran a babbar jaridar Jinzidal kuma suka yaɗa ta a faɗin duniya.
Duk da Armad yasan Uznu Ururu nada sa hannu wajen sace matarsa amma saida jaridar ta bayyana sannan yasan taƙamaimai abinda ke faruwa.
A yanzu babu abinda zai hana yaƙi tsakanin ɓangaren sarki Bihanzin da ɓangaren sauran sarakunan Jinzidal. Tuni aka buga ƙugen yaƙi kuma aka saka ranar da za'a yankewa Nostaljiya hukunci.
Armad yayi shirin yaki kuma yayi azama dashi da mutanensa sun nufi tsibirin Jaljus. Babu komai a ransu sai azabar yaƙi.
***
Babi na 133: Tsibirin Jaljus
Akan tsibirin Jaljus akwai wani ƙaton fili wanda aka kewaye da bishiyun dabino. Daga nesa idan ka hangi wannan waje baza kaga komai ba saboda kakkauran hazo daya lulluɓe ko'ina, amma idan ka matso kusa zaka ga manyan gine-gine masu yawa wanda zaka iya yi musu kallon ƙaramin ƙauye.
Wannan gine-gine ba komai bane illa gidajen ma'aikatan dake kula da wannan tsibiri da kuma sojojinsu. Ko akan ingarman doki akanyi sati guda cif kafin a isa cikin gari daga wannan tsibiri. Kuma saboda yawan nisan dake tsakanin tsibirin da cikin gari shi yasa aka gini ɗan ƙaramin birni akan tsibirin domin jin daɗin ma'aikata.
Ana kiran wannan ɗan ƙaramin birni da Goruja.
A ɗaya daga cikin gine-gine na birnin Goruja wasu manya-manyan masu faɗa aji ne suke tattauna mas'alar wannan yaƙi da kuma yadda zasu kawarda sarki Bihanzin da Armad, magajin Wilbafos.
Dukkansu suna zaune akan kujeru wanda suka zagaye ƙatoton teburi da aka gina da jan ƙarfe. Mutun goma sha ɗaya. Daga ɓangaren dama akwai Uznu Ururu da jarumai biyu wanda fuskarsu a rufe suna tsaye a kansa. A gefensa akwai sarki Deniz wanda ɗansa Bizaya da kwamanda Deniz Kalhari ke tsaye akansa. Sannan sai kuma sarki Rafiya wanda kwamanda Asifu Ruwan-bala'i da kuma kwamanda Jan-Doki ke tsaye a kansa. Sannan sai kuma mutun biyu wanda ke wakiltar sarki Han'ibal wanda tuni ya tafi taren Baƙar-wuta. Wannan mutun biyu sanannu ne sosai a doron-ƙasa ta uku kowa yasan su. Ana kiransu da Tagwayen-Auni.
Uznu yai gyaran murya gami da murmushi yana duban takardar dake kan teburin wadda akanta suka tsara dukkan wata hanya da zasu samu nasara a wannan yaƙi. "Kamar yadda nayi alƙawari na kawo muku gimbiya Zahra. Yanzu sai naku ɓangaren alƙawarin. Nidai zan kasance cikin jira."
Uznu na faɗar haka ya tashi ya fice ba tare da jiran amsarsu ba. Sarakunan biyu da wakilan sarki Han'ibal suka kalli juna suka gyaɗa kai.
***
Ranar 14 ga watan bakwai, 1858
***
Tuni filin da aka tsara za'a yankewa Nostaljiya hukunci ya ɗau harama. Ba abinda kake ji sai ihu da shewar mayaƙa wanda yawansu yakai dubu ɗari biyu.
Acikin birnin Goruja wani ƙatoton allo ne wanda aka sarrafa da kwallon Ayrid mai mataki na bakwai ke bada bidiyon abinda ke faruwa a filin. Dubban mutane sunbi layi suna kallon wannan bidiyo. Ga dukkan alamu sauran sarakunan Jinzidal suna so su nunawa duniya dukkan abinda zai faru a fagen daga. Da kuma yadda zasu samu nasara.
Filin dagar an tsara shi zuwa ɓangare huɗu. Ɓangare na farko dubban mayaƙa ne wanda yawansu ya haura dubu ɗari biyu. Ɓangare na gaba zaɓaɓɓun sadaukai ne wanda aka tsinto daga kowacce daula wanda yawansu yakai dubu. Kowanne acikinsu yana da izza data haura ɗari biyu.
Ɓangare na uku ƴaƴan sarakuna ne su Deniz Bizaya wanda zafin kishi yasa yake so yaga bayan Nostaljiya. Dasu yarima Niyashi da manyan kwamandu biyu daga kowacce daula. Kwamanda Deniz Kalhari daga daular Denizawa da Kwamanda Asifu Ruwan-bala'i da Kwamanda Jan-Doki daga daular Rafiya sai kuma kwamandu guda biyu masu wakiltar sarki Han'ibal wanda ake kira da Tagwayen-Auni.
Ɓangare na gaba wanda shi ne na ƙarshe yana ɗauke da dogon dutse wanda aka saƙale ankwa a samansa. Akan wannan dutse za'a ɗora Nostaljiya yayinda za'a yanke mata hukunci. Daga gaban dutsen akwai kujeru guda huɗu wanda aka ajiye amma babu kowa akai. Ana jiran sarki Deniz da sarki Rafiya da wakilin sarki Han'ibal da kuma Uznu Ururu.
**
Acan cikin wani ɗaki mai kama da kurkuku Nostaljiya ce a kwance cikin sarƙa tana kallon rufin ɗakin. Yauga gimbiya wadda tafi kowa kyau a ban ƙasa ɗaure cikin ankwa. Ko shimfiɗar tabarma babu ballantana katifa. Bisa mamaki idan ka kalli idanunta zaka ga babu nadama ko kaɗan aciki. Indai akan Armad ne komai zai faru da ita baza ta taɓa damuwa ba.
Babu abinda ke ranta sai mijinta Armad. Ga mahaifinta sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Lallai idan ba wani ƙadaru na ubangiji ba gagarumin yaƙi wanda zai canja duniya na gabda afkuwa.
Nostaljiya bata so a zubar da jini akanta. Amma a halinda ake ciki babu abinda zata iya.
Waima ya akai haka ta faru? Ya akai aka kamata? Abu na ƙarshe da take iya tunowa shi ne kallon Armad takan katanga yana saukarda Hannun-Aradu akan mayaƙan-ururu. Sai kawai ta ganta acikin taurari tana yawo kamar tsuntsuwa. Daga nan sai hankalinta ya gushe bata tashi ganinta ba sai acikin wannan ɗaki.
Idan zata iya tunawa akwai wanda acikin mayaƙan ururu aka ce yana iya sarrafa taurari amma duk da haka zuciyarta taƙi yadda wani ɗan'adam yana da ƙarfin izzar da zai iya aiwatar da haka.
Yau kwana biyu kenan a ɗaure kuma duk da ana ziro mata abinci da abin sha ta taga ta fita a hayyacinta. Babu abinda take so sai taji dalilin da yasa aka kawo ta wannan waje.
Daga inda take tana hango inuwar masu gadi mutun biyu tsaye cak a bakin ƙofa kamar gumaka. Idan da bata taɓa jinsu suna magana ba da tace gunkaye ne.
Bayan dogon tunani ta yanke shawarar tayi musu magana. "Nasan a matsayinku na masu gadi an hana kuyi min magana. Amma nasan zaku iya gayamin waye ya kawo ni nan kuma meye dalilin da yasa ake tsare dani."
Masu gadin ko motsi basu yi ba ballantana su bata amsa. Can dai ta fusata tayi tsaki ta rabu dasu.
A rana ta uku aka buɗe ƙofar ɗakin haske ya shigo. Saboda daɗewar da Nostaljiya tayi rabonta dashi saida ta rufe ido. Kafin ta wartsake masu gadin guda biyu wanda fuskokinsu a rufe suke sun shigo.
Na ɓangaren daman ya ce, "ki tashi ki biyomu. Yau ne ranar da za'a yanke miki hukuncin kisa ta hanyar fille kai."
Nan take Nostaljiya ta cika da mamaki. Hukuncin kisa kuma? Aduk abubuwan da take tunani babu wannan. Kama ta kaɗai ya isa ya janyo mummunan yaƙi ballanta ace za'a kashe ta. Lallai ba wani abu suke nema ba banda yaƙi.
Nostaljiya ta dube su ta ce, "kuna tunanin mahaifina da mijina zasu tsaya suna kallonku?"
Masu gadin suka ɗanyi shiru kamar baza su amsa mata ba sai daga ƙarshe ɗaya daga cikinsu ya ce, "tuni aka sanar a jaridar Jinzidal. A halin yanzu duk duniya babu wanda bai sani ba amma har yanzu saura awa uku lokaci ya cika amma babu mijinki babu mahaifinki babu alamunsu."
Nostaljiya najin haka ta fahimci abinda ke faruwa. Idan buƙatarsu su kashe ta zasu iya a kowanne lokaci amma saboda suna so Armad yazo su haɗa dashi shi yasa suka sanar a jaridu suka kuma saka rana suna jira saboda su kamasu a tare. Ga dukkan alamu ganin fasahar sarki Eyriyon a tare da Armad tasa darajarsa da kuma son a kashe shi yayi matuƙar ƙaruwa.
Ba musu Nostaljiya ta shige gaba suka bita a baya. Tana tafe cikin doguwar riga ruwan ƙasa wadda wahala ta ƙarawa duhu. Duk taku ɗaya sai kaji ƙarar ankwa.
Ba jimawa Nostaljiya ta ƙure soron dake gabanta. Tana tafe bata san inda take dosa ba, abubuwa da dama na gudana acikin kanta. Kwatsam sai taga ta bayyana a wani ɗan fili. A gabanta mutane ne fululu kamar kiyashi. Kowannensu na riƙe da makamai daban-daban, suna ganin tahowarta suka rikice da iface-iface, suna zaginta da kalmomi marasa daɗin ji.
Abu na farko daya tsorata Nostaljiya shi ne dukkan wannan mutane so suke su kashe ta. Gata gimbiya gata kyakkyawa amma a yau kowa ya tsane ta. Nan take idonta ya ciko da kwalla mai zafi. Tunda take bata taɓa fuskantar tsana ba. Kowa sonta yake, kowa so yake ya haɗa kansa da ita amma a yau sama da mutun dubu ɗari sun taru suna so ta mutu.
Wannan masu gadi guda biyu suka tafi da Nostaljiya saman ɗan dutsen da aka tanada sannan suka durƙusar da ita cikin wulaƙanci. Ana haka wani basamuden mutun wanda shi ne haunin da aka tanada ya bayyana ɗauke da gatari ya tsaya a bayan Nostaljiya yana jiran umarni. Nostaljiya ta sunkuyar da kanta babu abinda take sai kwalla. Tama rasa mai zatai.
Ana haka sai taji ihun mayaƙan ya canja ya koma na yabo. Tana ɗago kai taga sarki Deniz da sarki Rafiya da wazirin sarki Han'ibal da Uznu Ururu sun shigo. Sai ihu da yabo ke tashi.
Suka ƙaraso suka zauna cikin isa da ƙasaita akan kujerun dake ƙasan dutsen da aka ajiye Nostaljiya.
Mataki na farko mayaƙa sama da dubu ɗari biyu, mataki na biyu zaɓaɓɓun mayaƙa sama da dubu ɗaya, na uku ƴaƴan sarakuna da manyan kwamandu wanda kowa acikinsu izzarsa ta haura dubu biyar. Sai kuma mataki na ƙarshe inda sarakunan guda huɗu ke zaune. Duk wanda ke son cetar Nostaljiya sai yabi ta wannan matakai. Ko wanne mataki Armad zai ɗauka?
***
Babi na 134: Shirin Armad
Ɓangaren Armad
Awanni kaɗan bayan fitar Armad suka iso doron ƙasa ta uku ta hanyar ƙofar Eycigan. Sai dai kuma bisa mamaki daga inda suke tsaye ana iya hangen ruwan Bango a bayansu wato dai bata ɓangaren titin Bayajidda suka fito ba.
Doron ƙasa ta uku ɓangaren arewa yana daga cikin daular sarki Han'ibal wanda tuni ya fice domin taren Baƙar-wuta a wani shiri na kota-kwana. Amma duk da haka wannan yaƙi an kawo shi ƙasarsa saboda yadda da sihirin dake ɓoye akan tsibirin Jaljus wanda shi ne sansanin mayaƙan wannan nahiya.
Idan ka dubi wannan nahiya zaka ga tana da manyan garuruwa guda goma sha tara. Kowanne acikin wannan garuruwa yana da ƙauyuka daban-daban. Misali ƙauyen da Armad ya taso yana ƙarƙashin babban garin Fijja ƙarƙashin mulkin sarki Jarfi wanda shima yana ƙarƙashin mulkin babban sarki Han'ibal.
Cikin sauri Armad da Iliyasis da Inara da Cokali haɗe da sauran mutun goman dake biye dasu suka ɗau azama suka nufi babban birnin wannan nahiya wato garin sarki Han'ibal wanda ake kira da Ɗaurisa.
Dukkaninsu na ɗauke da murtukakkiyar fuska amma Armad babu komai a fuskarsa sai kafiya. Idanunsa na tsaye kuma har yanzu bai cewa kowa komai ba. Hakana suma su Iliyasis basu ce masa komai ba. Tafiya kawai ake ba'a cewa uffan.
Sannu a hankali suka iso bakin garin Ɗaurisa. Tun daga nesa zaka ga alamun yaƙi. Sojoji ne kawai suke safara a bakin ƙofar babu wanda ake bari ya shiga ko fita daga wannan gari. Ƙatuwar katangar data kewaye garin taɗan so ta ɗara katangar garin Jekis girma. Sannan kuma a samanta akwai mayaƙa ɗauke da kibbau suna kallon hanya ko wani zai iso, kai kace acikin wannan gari za'ai yaƙin.
Suna bayyana, Armad ya ɓace inda ya bayyana a saman katangar. Kan kace meye wannan masu tsaron katangar sukai yo kansa da ruwan kibbau amma Armad ya tsaya cak ko motsi baiba. Dukkan wannan kibbau suka shige ta jikinsa a yayinda ya zama walƙiya. Koda ganin haka sai tsoro ya shiga zuƙatansu. Wasu daga ciki suka fara jada baya wasu kuma suka ƙara harbo wasu kibban amma kafin su ƙaraso Armad ya dunƙule hannunsa na dama ya saukar musu da Hannun-Aradu. Wata ƙatuwar ƙawanyar walƙiya wadda girmanta yakai dutsen dala ta fita daga hannun Armad tai kansu. Masu gudu suka fara gudu. Masu rabon ganin baɗi sune wanda sukai tsalle suka faɗa ƙasa tare da samun karayu. Ragowar kuma tuni suka ƙone acikin hasken aradun Armad.
Armad ya ƙara saukarwa da ita kanta katangar Hannun-Aradu lamarinda yasa katangar ta tarwatse gami da bada wata ƙara mai ɗaukar hankali. Duk cikin garin Ɗaurisa babu wanda baiji wannan ƙara ba. Nan take ragowar sadaukan da aka bari a garin suka ɗaura ɗamarar yaƙi suka nufo inda su Armad suke.
A dai-dai wannan lokaci kuma Armad da mutanensa sun shigo cikin garin Ɗaurisa ta sashin katangar da Armad ya rusa. Kai tsaye suka nufi ɓangaren fada cikin gaggawa.
Akan hanyarsu sukai arba da mayaƙa wanda sun haura dubu uku. Kowannesu ɗaure da sirdi da kayan yaƙi. Sai dai kafin su ƙaraso Iliyasis da Cokali da Inara da sauran mutun goma dake tare dasu suka tafa hannayensu tare da kiran ɗalasimai kala ɗaya lamarinda yasa wata walƙiya tai fitar burtu daga hannayensu tai kan wannan mayaƙa.
Suma mayaƙan basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen aiko da tasu kwangilar ta wuta. Kan kace meye wannan walƙiya da wuta sun haɗu inda suka bada wata ƙara mai ɗaukar hankali gami tartsatsi da haske wanda ake ganowa a duk faɗin garin da kewaye.
Ana cikin haka Armad ya sulluɓe cikin rububi ya nufi fada ya barsu suna fafatawa anan.
Cikin daƙiƙa hamsin kawai sai jin muryar Armad akai a lasifika ta game duk gari. A duk inda kake kana ji.
"Mun kama fada gami da iyalan sarki dake ciki. Idan kuna so kada mu fara kashe su ɗaya bayan ɗaya ku ajiye makamanku."
Armad ya ƙara maimaita maganarsa sannan daga bisa yasa ɗaya daga cikin matan sarkin tai magana domin ya tabbatar da aniyarsa.
Da dama daga cikin masu tsaron fadar jikinsu yai sanyi. Wasu kuma suna kokwanto amma duk da haka suka haƙura suka ajiye makamansu. Iliyasis da sauransu suka samu hanya suka shige izuwa fada.
Daga bisani bayan sun jere mutanen dake cikin fadar sai suka kira shugaban masu tsaron fadar domin bashi saƙo.
Armad na zaune kan karagar sarki Han'ibal yana muzurai. Ya dubi mutumin mai yawan ƙasumba da faɗin fuska ya ce, "Ya sunanka?"
Mutumin ya amsa cikin karkarwa. "Han'Fasumu."
"Han'Fasumu, saƙo zan baka zuwa tsibirin Jaljus. Kaje ka faɗi duk abinda ya faru anan kuma kace nanda sa'a ɗaya zamu fara kashe iyalan sarki. Duk minti biyu zamu kashe mutun ɗaya."
Fasumu najin haka wani sanyi mai haɗe da firgici ya shiga jikinsa. Ya dubi Armad yana karkarwa ya ce, "to amma mai kuke so? Mene ne buƙatarku?"
Armad ya gyaɗa kai ba tare da kallonsa ba ya ce, "ba komai. Lokacinka ya fara daga yanzu. Bayan awa ɗaya zamu kashe mace ɗaya ko namiji biyu."
Fasumu najin haka ya ƙara firgita da lamarin Armad da irin rashin wasa da yake gani a fuskarsa. Nan take ya tashi ya ɗauki ɗamara ya bazama zuwa tsibirin Jaljus wajen da ake shirin gwabza yaƙi.
***
Acan tsibirin Jaljus dubban mayaƙa ne keta iface-iface. Kowa ya hallara: sarki Rafiya sanye da jar riga mai buɗaɗɗen hannu, sarki Deniz sanye ƴar shara ruwan ƙasa. Uznu Ururu sanye da fatar zaki. Sai kuma wakilin sarki Han'ibal sanye babbar riga wadda rabinta a ƙone yake.
A dai-dai samansu Nostaljiya ce durƙushe akan dutsen tana kuka bata ko iya ɗago idonta. A gabansu kuma su yarima Bizaya da Yarima Niyashi da kuma manyan kwamandun nan wato Jan-doki da Ruwan-bala'i daga Rafiya da kuma Kalhari daga Denizawa da kuma Tagwayen-auni daga daular Han ta sarki Han'ibal.
A gaban wannan fitattun kwamandu runduna ce ta zaɓaɓɓu sama da dubu wanda kowa izzarsa ta haura ɗari.
Sai kuma filin gama garin mayaƙa wanda yawansu ya haura dubu ɗari biyu.
Ana haka sarki Rafiya ya miƙe ya fara jawabi. "Kowa yasan laifin da wannan gimbiya ta aikata wanda bisa tsari muka zauna muka yanke mata hukuncin kisa kamar yadda zamu yankewa kowa. Wannan shi ne adalci. Duk wanda ke wajen nan yayi amanna da wannan mataki saboda haka zamu zarce mu yanke wannan mataki."
Yana zuwa nan a zancensa ya kalli sarki Rafiya da sarki Deniz inda suka gyaɗai kai alamun amincewa, sannan daga baya ya ɗaga hannu ya bawa hauni umarni. Hauni ya gyaɗa kai sannan ya gabato kan Nostaljiya. Yana zuwa ya ɗaga takobinsa ya nunawa sama, a lokacin waje yai tsit sannan ya saukar da ita kan wuyan Nostaljiya.
A dai-dai wannan lokaci dai-dai inda Nostaljiya take wani haske ya bayyana. Lokaci ya tsaya cak. Sannan Nostaljiya ta ɓace. Armad ya bayyana a dai-dai wajen. Maimakon takobin hauni ta wuce ta wuyan Nostaljiya sai ta wuce ta wuyan Armad.
Anan fa kallo ya koma sama.
***
Babi na 135: Zaran-Gwana
Doron-ƙasa na huɗu
Garin Jekis
Awa ɗaya bayan sace Nostaljiya
Armad ne tafe sauri-sauri gudu-gudu yana haki kamar wanda yai gudun fanfalaƙi. Jikinsa duk ƙurar yaƙi ko canja kaya baiyi ba. Yana isa fada ya zarce gidansa ya fara haɗa kayan yaƙi domin tuni ya gama yanke shawarar fita neman Nostaljiya da kansa duk da kuwa baisan inda take ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci Armad ya haɗa abinda yake buƙata ya fito ƙofar gida da niyyar bazama neman matarsa. Sai dai a wannan lokaci ne yai arba dasu Iliyasis sun ƙaraso ƙofar gidan. Kowa acikinsu ƙoƙari yake ya tsayar da Armad tare da yi masa bayanin ya kamata abi abu a hankali amma sun rasa ta ina zasu ɓullowa Armad. Shi kuwa Cokali wanda aka barwa alhakin jire Nostaljiya kunya tasa ya koma gefe bama yaso su haɗa ido da Armad.
Armad ya dube su ya ce, "nidai zan bazama neman mata ta."
Iliyasis yai ƙarfin hali ya numfasa ya ce, "niko ina ganin kaɗan yi haƙuri mu zauna mu tattauna maganar, wataƙila ma tana cikin garin nan ba nisa tayi ba. Ina jin ko sarki bai san maike faruwa ba."
Armad yai farat ya tsayar dashi. "Kwata-kwata bana jin yanayin-izzarta a kusa kuma a gaskiya bazan iya zaman jira ba bayan bansan halinda mata ta take ciki ba."
Armad na rufe baki ya nufi hanya, sai dai a lokacin ne ya ƙara yin arba da kwamanda Damjinu ya shawo kwana ya nufo inda suke gadan-gadan. Yana zuwa gaban Armad ya fara magana cikin sauri. "Sarki Bihanzin na jiranka a fada."
Armad ya haɗe gira. A wannan lokaci babu abinda yaƙi jini face a tsayar dashi amma tunda sarki ne babu yadda za'ai. Nan take yabi bayan kwamanda sukai fada. Suna zuwa shi kansa kwamandan a bakin ƙofa ya samu waje ya tsaya ya tura Armad ciki.
Armad na shiga ya tarar da Bihanzin zaune kan karagarsa a nutse amma rataye da takobi. Sannan akan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye teburin dake gaban Bihanzin wani mutun ne zaune baya ko motsi. Amma fuskarsa cike take da murmushi.
Bihanzin ya fara jawabi bayan Armad ya zauna. "A matsayinka na ma'aboci izza kuma shugaban gobe ya kamata ace a lokuta irin wannan ka samu nutsuwa fiye da kowa. Ta hakane kaɗai zaka iya saita kan mabiyanka."
Sarki Bihanzin na magana a nutse amma cike da izza kana ji kasan akwai shekaru da kwarewa aciki.
"Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu shi ne ya sace Nostaljiya. Nima ban san ya akai haka ta faru ba, amma gabda hakan zata faru naga tauraruwar Nostaljiya na ɗaukan zafi fiye da ƙima sannan kuma tana motsi tana barin wajenta. Hakan nema yasa naje nayi ƙoƙarin hana ta fita daga gida amma ta dage saita ga fafatawarka. Yanzu dai an riga an ɗauke ta, abinda ya rage shi ne mai zamu iya yi mu dawo da ita?"
"Dul'Ururu, Uznu Ururu, Han'ibal, Deniz Iluru, Rafiyan Daljari. Waɗannan sune mutanen da zamu fuskanta a wannan yaƙi. Daga ni mahaifinta sai kai mijinta, mai zamu iya yi mata?"
Armad yai ajiyar numfashi gami da gyaɗa kai. Ga dukkan alamu bayanin Bihanzin ya shige shi. "Abinda ya kamata muyi na farko shi ne mu gano inda take. Daga nan zamu tsara matakin da zamu ɗauka na gaba."
Bihanzin yai ɗan ƙaramin murmushi tare da cewa. "Eh wannan haka yake. Sai dai tuni nasan inda take. Tana kan doron ƙasa na uku, a tsibirin Jaljus."
Koda jin haka sai Armad ya tuno da labarin ƙarfin fasahar Yanayin-izzar sarki Bihanzin ya haɗiyi yawu. Yana niyyar yin magana Bihanzin ya tari numfashinsa. "Kamar yadda akai amfani da fasahar taurari aka sace ta nima akwai fasahar da zanyi amfani da ita na dawo da ita. Kuma wannan fasaha tana buƙatarka. Wannan shi ne dalilin da yasa nace a kira ka."
Nan take Armad ya gyara zama. "Ina saurare."
"Rabonda nayi amfani da wannan fasaha sama da shekaru ashirin kenan badan komai ba saboda indai nayi amfani da ita to har sai wanda nayi amfani da ita akansa ya mutu sannan zan ƙara iya amfani da ita. Dubi wannan."
Bihanzin ya nunawa Armad mutumin dake zaune akan kujerar. Wanda a lokacin Armad ya lura cewa mutumin gawa ce.
"Sunansa Abir Sisiyu. Ɗaya ne daga cikin mayaƙa na wanda muke tare tsahon lokaci tunma kafin na zama sarkin Jinzidal. Ya kashe kansa ne saboda ya bamu damar yin amfani da wannan fasaha wajen ceto gimbiya. Idan ka yarda zanyi amfani da wannan fasaha akanka domin kuɓuto da matarka daga inda take."
Armad har izuwa wannan lokaci idanunsa nakan wannan mutun yana kallon idanunsa da doguwar fuskarsa wadda ke ɗauke da murmushi. Kana gani kasan bai mutu cikin baƙin ciki ba.
"Yaya wannan fasaha taka take aiki?"
Bihanzin ya amsa da cewa, "Sunan fasahar ZAREN-GWANA. Zan jefa ruhinka izuwa inda ruhinta yake a lokaci guda kuma na dawo da ruhinta inda naka yake. Idan nayi amfani da ita a yanzu zaka bayyana a inda take sannan ita kuma ta bayyana anan. Fasaha ce wadda na gada tun iyaye da kakanni kuma a haƙiƙa bama bawa kowa wannan fasaha sai ɗan zuri'a. Abu guda da zan gaya maka shi ne tana da hatsari akan mutanen da za'a canja. A sau da dama jikin mutun yakan rududduge ya tarwatse kafin ƴa ƙaraso. Kuma duk da jikinka na walƙiya ne bani da tabbas akan irin illar da zatai maka. Saboda haka bazan yi wannan fasaha akanka ba har sai ka amince ɗari bisa ɗari."
Armad yai sauri ya ce, "Na amince."
***
Filin yaƙi
Tsibirin Jaljus
**
Nan take kallo ya koma sama. A wajenda ya kamata ace Nostaljiya ce Armad ya bayyana.
Wani dunƙulalle aman jini ya fito daga bakin Armad bawai dan takobin haunin ba sai dan ƙarfin fasahar da Bihanzin yai amfani da ita.
Armad ya miƙe tsaye dakyar ya dubi gabansa amma baya iya ganin komai sai hazo-hazo. Nan take jiri ya ɗauke shi ya ƙara faɗuwa ƙasa. Bakin kowa a buɗe sun rasa mai zasu ce domin tuni abin ya shallake tunaninsu.
Abokin kishinsa yarima Bizaya shi ne ya fara ambatar sunan Armad baki a buɗe. "A...ARMAD?"
Shima yarima Niyashi wanda rabonsa da Armad tun a gasar Jinzidal ya ce, "wancan ai Armad Djinn ne! Maike faruwa? Maiya kawo shi nan? Ina Zahran take?"
Shima Uznu da dukkan sauran mutanen dake wajen kawai sunan Armad suke ambata.
"Armad!"
"Armad!"
"Armad!"
Ana cikin haka mai tsaron gida Fasumu ya danno kai filin daga da saƙon Armad.
***
Babi na 136: Canjin Filin Yaƙi
Koda bayyanar Armad sai yarima Niyashi da yarima Bizaya da kwamanda Asifu da kwamanda Jan-doki da kwamandun nan guda biyu da ake kira da Tagwayen-auni sukai tsalle daga inda suke zuwa kan dutsen suka zagaye shi. Yana cikin wannan hali mai tsaron gida Fasumu ya kwashe dukkan abinda ya faru gayawa wazirin sarki Han'ibal, sadauki Han'Dandil.
Koda jin wannan labari sai aka fara kallon-kalo. Armad ya kama iyalan sarki Han'ibal kamar yadda aka kama matarsa. Sannan kuma yayi musanyar kansa a maimakon matar tasa. Idan suka cutar dashi akwai matuƙar yiwuwar iyalan sarki Han'ibal su halaka a hannun mutanensa wanda abu ne da Han'Dandil bazai taɓa yadda dashi ba. Yin hakan ka iya tarwatsa haɗin kan dake tsakanin sarakunan.
Sarki Rafiyan Daljari ya ɗagawa su yarima Niyashi hannu alamun su dakata da aikata Armad. Sannan ya ja sauran sarakunan dake tare dashi zuwa cikin wani tanti domin su gana a sirri.
Har izuwa wannan lokaci Armad bai daina aman jini ba. Ko tsayawa da ƙafafunsa ya kasa saboda tsabagen karkarwa da suke. Sannan kuma ga ƙadamusawa a kansa. Sauran mayaƙa dake ƙasa shewa kawai suke suna nuna goyon bayansu akan a sare Armad.
Acikin tanti, waziri Dandil ne ke magana. "Dole ne mu sa iyalin sarki a gaba da komai kamar yadda inda yana nan za'ai. Ina ganin muyi yarjejeniya akan sakar Armad indai zai saki iyalin sarki."
Uznu ya tari numfashinsa. "Amma kasan ko an sake shi babu tabbas zai rabu da wanda ya kama ba cutarwa. Sannan babban abinda ya kamata mu saka a gaba shi ne yadda akai Zahra ta ɓace da kuma ina ta tafi domin dole mu tsayar da hankalinmu akan wannan mutane guda biyu wanda sune ginshiƙin nasarar wannan yaƙi. Idan muka rasa su to lallai akwai matsala."
Sarki Deniz da Rafiyan Daljari suka dubi juna sukai ajiyar zuciya. Lallai suna tsaka mai wuya: abinda Uznu ya faɗa dai-dai ne to amma kuma barin iyalin sarki Han'ibal su halaka shima babbar matsala ce. Nan dai aka ci gaba da kace-nace tsakanin Uznu da Dandil kowa yana kare ɓangarensa. Kan kace meye wannan magana ta ɗau zafi. Da ƙyar sarki Rafiyan Daljari ya tsayar dasu tare da kawo ƙarshen hayaniyar.
"Yaƙi lissafi ne. Dukkanmu muna jirgi ɗaya. Zamu ceto iyalan sarki Han'ibal sannan kuma zamu saki Armad to amma hakan bashi ke nuna cewa mun rasa duk biyun ba. Kada ku manta dama can mun riga mun shirya yaƙar Bihanzin gaba-da-gaba ba tare da yin garkuwa da ƴarsa ba, saboda haka kawai zamu koma wancan tsarin ne. Sannan kuma kada ku manta mu muke da runduna guda huɗu ta manyan sarakuna wanda kowanne acikinsu dai-dai yake da Bihanzin."
Koda yin wannan bayani sai hankalinsu ya dawo jikinsu suka tuna dama can wannan tsari na sato Zahra ayi garkuwa da ita shawarar Uznu Ururu ce kuma kasancewar bata ɓulle ba ba shi ke nuna basu da wani tsarin ba.
Sarki Deniz ya numfasa ya ce, "Ina kyautata zaton Bihanzin yayi amfani da fasahar Zaren-gwana wajen musayar ƴarsa da Armad. Wannan fasaha bata da nisan zango sosai. A faɗin tarihi mafi dogon zango da aka taɓa samu anyi tafiya da mutun ta hanyar wannan fasaha shi ne tsahon tafiyar wuni ɗaya. Daga nan zuwa garin Bihanzin yakai tafiyar shekara ɗaya a ingarman doki saboda haka ina ganin har yanzu muna da damar kamo Zahra kafin ta ƙarasa daular Sisiya."
Uznu ya gyaɗa kai yana cewa. "Lallai haka ne. Kamar yadda na faɗa a kwanan baya yin yaƙi acikin garin Jekis shi ne babban abinda zai bamu matsala domin kuwa sunfimu sanin sirrin garinsu. Kamar yadda muma inda anyi yaƙi a wannan tsibiri muke da sa'a. Saboda haka tunda sun ɗauke Zahra kuma sun kama iyalan Han'ibal kunga damar da muke da ita ta kawo yaƙinnan wajenmu ta gwace saboda haka sai muyi ƙoƙarin hana faruwar yaƙin a garinsu. Zanyi duba izuwa taurari na gano inda wannan yarinya take."
Koda jin haka sai kowa yai na'am. Nan take sarki Daljari ya raba aiki a matsayinsa na shugaban tawaga. "Uznu kaine da alhakin gano mana inda Zahra take da kuma hanata isa gida. Kai kuma Deniz idan ya gano inda take kaine da alhakin jagorantar mayaƙanmu domin isa wajen domin mayaƙan Bihanzin zasu zamo tare da ita.
"Kai kuma Dandil ka ɗauki Armad ka kaishi kurkuku ka kuma duba yiwuwar kuɓutar da iyalan Han'Ibal. Ni kuma zan jagoranci zaɓaɓɓun mayaƙanmu mu tare hanyar shiga ƙasar Sisiya saboda tsaro. Na bawa kowa sa'a guda kacal ya gama aikinsa daga nan zan turo muku saƙon inda nake ta Ayrid domin dukkaninmu mu haɗu a waje ɗaya. Ga dukkan alamu wannan yaƙi babu wanda yasan inda za'a yi shi."
Koda gama wannan bayani sai suka fito daga tantin kowa acikinsu ya kama aikinsa. Uznu ne ya fara ɓacewa sannan Dandil da kwamandu biyu da ake kira Tagwayen-auni suka cafi Armad sukai kurkuku. Har a wannan lokaci Armad bai dawo hayyacinsa ba.
Shugaban tawaga, sarki Rafiyan Daljari, yaja kwamandunsa guda biyu; Rafiyan Asifu da Rafiyan Jan-doki da kuma ɗansa yarima Niyashi da wannan zaɓaɓɓun ma'abota izza guda dubu dake mataki na uku suka nufi kan iyakar ƙasar Sisiya domin tsare hanya.
Sarki Deniz yaja ɗansa Bizaya da kwamandansa Kalhari suka fara haɗa kan mayaƙan dake wajen suna jira umarni.
***
Akan titin Bayajidda, dai-dai iyakar doron-ƙasa na huɗu dana uku wata tafkekiyar runduna ce mai ɗauke da sadaukai dubu hamsin ke tsaye suna jiran umarni. Idan kai musu duba na tsanaki zaka ga ba wasu bane face mayaƙan Sisiya na sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Suna sanye da kayansu mai yalo da ratsin baƙi ko motsi basa yi. Tsit kamar mutuwa ta gifta.
A gabansu akwai wasu sadaukai sanye da alkyabba guda uku. Na tsakiyar babban kwamanda Damjinu ne amma na gefensa guda biyu wannan ne karo na farko da aka gansu. Ɗaya dogo ne mai faffaɗar fuska da yawan gemu ɗayan kuma ƴar gajeriyar fuska ce dashi ƴar firit mai kama da mage.
A gabansu sarki Bihanzin ne zaune akan ingarman dokinsa sanye da doguwar riga ƴar shara wadda akaiwa ado da bezar baƙin hankaka. Rataye a wuyansa takobin da akewa laƙabi da dauwamammen sara ce. Ko gida takobin bata dashi tana buɗe tsirara tana burin shan jinin mai ƙarar kwana.
Suna tsaye sai ga wata tawaga ta mutun tara sun doso inda suke. A gabansu akwai keken doki ne.
Suna isowa sarki Bihanzin da kansa ya buɗe ƙofar keken dokin yai arba ƴarsa gimbiya Zahra. Cikin sauri ya juyo zai bada umarnin a juya a koma gida amma anan ne rundunar sarki Rafiyan Daljari ta bayyana a gabansu.
Ana dara ga dare yayi!!
***
Babi na 137: Buɗe Labulen Yaƙi
Rundunar sarki Bihanzin da ta sarki Rafiyan Daljari suna tsaye suna kallon juna anyi cirko-cirko. Kwatsam saiga sarki Deniz da ragowar tawagarsu sun danno tare da Uznu Ururu da Waziri Dandil. Ƙura ta turnuƙe ta tokare sararin samaniya. Ga Bihanzin da tawagarsa ga kuma ragowar sarakunan Jinzidal. Kowa ya hallara banda Armad.
Umarni na farko da Bihanzin ya fara bayarwa shi ne a kula da Nostaljiya wadda ke kwance cikin keken dokin anyi mata allurar bacci. Mutun biyu dake tsaye a gaban keken dokin suka cire hular ƙarfen dake rufe da fuskarsu tare da gyaɗa kai. Ba wasu bane illa yarima Kiru da yarima Hasanu.
Bihanzin ya ƙara jaddada musu. "Duk yadda yaƙi zai kasance ku zamanto kuna tare da ita." Sannan daga bisani ya juya izuwa kwamandu uku dake bayansa ya ce, "Damjinu, dakai da NAƘATA da DINANDUL kuna tare dani. ƳAN GOMA, kowa acikinku zaija rundunar sadaukai dubu biyar ya jagoranta a ƙarƙashin umarni na."
Bihanzin na rufe baki kwamanda Damjinu da mutun biyu dake gefensa suka dawo bayan Bihanzin. Sannan wasu mutun goma suka fito daga cikin sahun farko suka raba kansu kowa yaja sadaukai dubu biyar suka kewaye keken dokin dake ɗauke da Nostaljiya. Bihanzin da manyan kwamandunsa uku suka tsaya gaban wannan runduna.
A ɗaya ɓangaren kuma sarki Rafiyan Daljari ne ya jagoranci lissafin. "Uznu Ururu, Deniz Iluru, Dandil kuna baya na. Niyashi, Bizaya, Jan-doki, Asifu, Kalhari da Tagwayen-auni kune da alhakin kama wancan keken doki da Zahra ke ciki saboda haka ku tsaya daga gefe ku nemi hanya."
Sannan ya zaɓo mutun goma daga cikin zaɓaɓɓun nan dubu ya basu aikinsu. "Ku raba rundunar mu izuwa mutun dubu goma-goma kowa ya ɗauki kaso ɗaya ku tsaya cikin sahu. Ragowar mayaƙan inaso ku tsaya a baya tare da ragowar zaɓaɓɓun sadaukanmu ku jira umarni. Idan Bihanzin ko ɗaya daga cikin mutun uku na bayansa ya shigo fili ko ni ko Iluru ko Ururu ko Dandil wani zai tare shi. Idan wancan mutun goma suka shigo ɗaya daga cikinku zaɓaɓɓu goma ya tare. Idan kuma gama garin mutane ne, ragowar mayaƙanmu sun isa. Kada ku manta, Niyashi, Bizaya, Tagwayen-auni, Asifu, Jan-doki, Kalhari, kune da aiki mafi muhimmanci. Aikinku shi ne kama wancan keken doki da Zahra ke ciki. Mun ninkasu yawa aƙalla sau huɗu. Nasara tana a garemu indai munbi wannan tsari."
Nan take dubunnan muryoyi suka haɗa baki suka amsa. "Munji munbi."
Sannan kowa yabi layi aka hau sahu-sahu.
Sarki Rafiyan-Daljari na tsaye saitin Bihanzin suna kallon-kallo. Kowa acikinsu nada ɓoyayyiyar tsana ta musamman da yake yiwa ɗan uwan.
Bihanzin ne ya fara magana. "BABA DALJA. Shekaru da dama rabonda mu gana. Bai kamata ace bayan duk wannan shekaru mun haɗu a fagen yaƙi ba. Kuma wai ace ƴarka Zahra kake so ka halaka. Lallai anyi faɗuwar baƙar tasa. Kama fi hankali da dattaku a lokaci kana saurayi."
Kana jin muryar Bihanzin da yadda yake bayani kasan akwai zaulaya da cin fuska aciki. Rafiyan Daljari ya dunƙule hannunsa cikin ɓacin yana cizon harshe. Idan yana da wani buri guda ɗaya kacal daya rage a duniya bai wuce ya halaka Bihanzin ba. Kasancewar su biyun suna da tsohon tarihi mara daɗi wanda ya faru sama da shekaru casa'in da suka wuce.
Daljari yai murmushi mai cike da baƙin-ciki tare da haɗiye abinda ke ransa ya amsa da cewa. "Ai ɗan halak shi ake son gani ba ɗan tsiya ba. Waye zaiso ya haɗu da ɗan ƙabilarka? Bari dai na damƙe ka a hannuna. A yau zan gayawa duniya sunan ƙabilarka da kuma meye asalinka bayan na turmuza hancinka a ƙasa na sare maka wuya."
Bihanzin najin haka ya haɗe rai. Sauran jama'ar dake wajen suka fara ƙus-ƙus suna tambayar me Daljari ke nufi da 'asalin Bihanzin'.
A wannan lokaci Bihanzin ya fusata ya zare takobinsa sannan ya aikawa da sarki Rafiyan Daljari sara akan iska. Kai daga ganin yadda Bihanzin ya juya takobin da yadda ya lanƙwasa ta kasan akwai tsananin kwarewa da daɗewa anayi. Wani baƙin haske mai kama da mutuwa ya fice daga kaifin takobin sannan yai kan Daljari yana ƙugi.
Hatta iskar dake kewaye da saran saida ta fara ƙonewa tana kuka tana darewa. Cikin ƙanƙanin lokaci duk wani abu dake kan hanyar wannan sara ya kauce, babu komai a tsakaninsu sai Rafiyan Daljari. Ƙasar wajen ta fara girgiza tana bada amo.
Uznu Ururu ya haɗe gira yana cewa. "Wato wannan shi ne dauwamammen saran da ake faɗa. Ban taɓa ganinsa ba sai yau."
Shima sarki Deniz tofa albakacin bakinsa yayi. "Wato wannan shi ne saran da ya tsorata sarki Maikironomada yaƙi shiga wannnan yaƙi?! DAUWAMAMMEN SARA!"
Shima Dandil matsawa da baya yai tare da cewa. "Sarki Han'ibal ya bani labarin wannan baƙin haske dake tashi daga jikin dauwamammen sara. Ance hatta mutuwa tana tsoro yin gamo dashi! Lallai banga laifin sarki Han'ibal da yake son ya mallaki wannan fasaha ba."
Shi kuwa sarki Rafiya tafa hannunsa yayi ya kirawo ɗalasimai a zuci, lamarinda yasa wata tafkekiyar katanga mai ɗauƙe da ƙasar kabari ta bayyana daga ƙarƙashin ƙasa ta tsaya a gabansa. Idanun sarki Daljari suka fara haske da hasken taurari.
Baƙin hasken mai ɗauke da saran Bihanzin ya haɗu da katangar inda nan take ya raba ta biyu. Amma kafin ya wuce wata katangar ta ƙara bayyana a bayanta. Hasken ya ƙara raba ta biyu amma a lokaci guda shima yana raguwa. Katangar ta ƙara bayyana a gaban hasken. A haka saida katanga huɗu ta faɗi kafin hasken ya tsaya. Duk da haka saida akai sama da daƙiƙa biyar kafin ƙasa ta daina girgiza.
Haka na faruwa sadaukan dake ɓangaren sarki Daljari wanda babu abinda suke tsoro banda dauwamammen sara duka fara ihu suna cewa. "Ai muna da sarakunan Jinzidal, babu abinda zai same mu. Muke da nasara."
Da wannan sara aka buɗe labulen yaƙi na farko a wannan ƙarni.
***
Akan Bangon arewa, dai-dai iyakar doron ƙasa na huɗu dana uku wani jirgin ruwa ne ya sauka. Acikin jirgin ruwan Ikenga ne dashi da su Kana da kuma wannan yaro mai ɗauke da idanun Ururu. Suna sauka suka nufi ƙofar Eycigan.
Kána ya dubi mai aiki a wajen ya ce, "titin Bayajidda zamu je, nawa zamu biya gaba ɗayanmu?"
Mai tsaron ƙofar najin haka ya ware ido ya ce. "Titin Bayajidda? Ku yara, kunsan yaƙin dake shiri ɓarkewa kuwa a wannan waje? Ina baku shawara kada ku ratsa ta wannan hanya a yau."
Babu wanda ya ce masa uffan. Wannan ɗan ƙaramin yaro shi ne kawai ya buɗe baƙaƙen idonsa ya harare shi. Nan take yaji ƙirjinsa ya ƙulle yayi aman jini ba shiri. Kan kace meye wannan ya buɗe musu ƙofar sun shige.
Bayan sun iso sai wannan yaron ya dubi Ikenga ya ce, "ina mamakin dalilin wannan yaƙi. Nasan dai mu kallo zamu je. To amma idan ka duba sarki Deniz yana da buƙatar a kashe Armad sabida kwantiraginsa na walƙiya, kaga yana da dalilin shiga wannan yaƙi. Sarki Han'ibal yana so ya mallaki fasahar takobin Bihanzin shima yana da dalilin shiga. To amma har yanzu na rasa meye dalilin da zaisa sarki Rafiyan Daljari da Uznu Ururu su shiga wannan yaƙi!"
Koda jin haka sai Ikenga yai murmushi ya ce, "naji labari ance ɗan uwanka Uznu yana da alaƙa mai ƙarfi da Armad Wilbafos, wai ance saboda Littafin-takobi. Amma bani da tabbas ko haka ne. Sai dai kuma akwai mummunan tarihi a tsakanin sarki Rafiyan Daljari da sarki Bihanzin shekaru casa'in da biyu da suka wuce. Bari na baka labari akan hanyarmu kafin mu ƙarasa inda zamu kalli wannan yaƙi."
***
Babi na 138: Mai Dauwamammen Sara
~Shekara ɗari da arba'in da biyu da suka wuce (shekarar 1716)
~Ranar Asabar
~Daular Rafiyawa
A wannan rana akwai hadari gagarumi a sararin samaniya. Sarki Rafiyan Daljari yana tsaye a bakin harabar fada dashi da ɗansa Rafiyan Nazára wanda aka fi sani da Yarima Niyashi. Sannan kuma a ɓangaren hagu akwai wata kyakkyawar budurwa mai yawan dogon gashi. Dukkan su ukun gashin kansu jajawur ne mai kyalli.
A wajen harabar dawakai ashirin ne sunbi sahu-sahu da mahaya a kansu suna jiran umarnin sarki.
Wannan rana rana ce ta fita rangadi da shaƙatawa a wajen sarki Rafiyan Daljari sai dai kuma ga hadari yana neman hanashi fita.
Bayan ɗan lokaci sarki Rafiya yai ajiyar zuciya ya ce, "tuni an rubuta zan fita wannan rangadi kuma ruwa zai sakko akan hanyarmu ta dawowa saboda babu yadda za'ai. Ku ɗaura sirdi."
Sarki na faɗar haka suka ɗau azama suka bi bayan gari inda suka ratsa ta cikin babbar gonar data zagaye garin suka nufi daji.
Kamar yadda sarki ya labarta haka ya faru. Bayan sun dawo daga wannan rangadi akan hanyarsu ta dawo wa ruwan sama ya tsuge. Aka sawa sarki lema aka ci gaba da tafiya.
Suna cikin tafiya suka iso wajen wata duhuwa dake tsakanin wasu manyan duwatsu biyu. Saboda tsayin duwatsun idan ruwan sama ya taru akai yana zubowa ƙasa sai kaji kamar ambaliyar ruwa ce ke afkuwa. Hanyar gaba ɗaya ta cika taf babu hanyar wucewa. Ɗaya daga cikin jaruman dake tare da sarkin ya shige gaba ya tafa hannu gami da kiran wasu ɗalasimai. Lamarinda yasa ruwan daya taru ya fara ƙafewa yana shigewa ƙarƙashin ƙasa. Kan kace meye wannan hanya ta samu.
Sarki ya shige gaba suka wuce. Duk da ruwan yana zubowa amma inda zasu taka a ƙafe yake. Suna gabda wucewa sai sarki ya ja linzami ya tsaya. Sannan yayi wa sadaukan dake tare dashi nuni da bayan wani dutse.
Ana ɗauke dutsen sai ga wani saurayi mai yawan dogon gashi jajawur kamar na kan sarkin da ƴaƴansa.
Sadaukan biyu suka zare takubba suka tsare shi. Amma sarki Daljari ya ɗaga musu hannu yana mai cewa. "Ku dube shi karkarwa yake cike da tsoro ku ajiye takubbanku."
Sarkin ya matsa kusa ya sauka daga kan dokinsa ya isa wajen yaron. "Yaro, ya sunanka?"
Yaron ya kalli sarki ya ce, "Suna na Bihanzin."
Sarki ya numfasa ya ce, "Bihanzin! Anan nahiyar bamu da irin wannan sunan. Amma muna da irin gashinka. Ina iyayenka? Kai mutumin wacce ƙasa ne?"
"Nazo daga Ƙissƴɓui. Iyayena sun mutu akan hanya."
"Ƙissƴɓui?!" Ɗaya daga cikin masu tsaron suka dakawa Bihanzin tsawa. "Sarkin Jinzidal ne ke tambayarka idan kai mana ƙarya kwananka ya ƙare. Duk faɗin ƙasa bakwai babu wata ƙasa da ake cewa ƘISSƳƁUI!"
Sarki Rafiya ya ɗagawa bafaden hannu. "Rabu dashi ya ƙarasa ga dukkan alamu ba ƙarya yake ba. Yaro mai kake anan?"
"Nazo ne ɗabbaƙa addinin takobi."
A wannan lokaci Niyashi ne ya amsa masa. "Addinin takobi? Mai kake nufi?"
Bihanzin ya amsa da cewa, "Kunce kar nayi ƙarya shi yasa nake gaya muku gaskiya. Nima haka mahaifina ya gayamin kafin ya mutu amma har yanzu ban san mai yake nufi ba."
Sarki ya dubi Bihanzin sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga bisani ya numfasa ya ce, "yaro idan baka da wajen zuwa ka biyo ni gidana nayi maka sutura."
Bihanzin yai sauri ya amsa da cewa. "Da gaske? Muje. Dama yunwa nake ji."
Sarki ya fashe da dariya sannan ya nuna Nazara da budurwar dake gefensa ya ce, "Wannan ƴaƴa na ne, Nazara da Hilhusa. Nazára, ɗorashi akan dokinka. Daga yau ya zama abokinka."
Ba musu Nazara ya ɗauki Bihanzin a bayan dokinsa suka nufi cikin gari.
A wannan shekara ta 1716 sarki Rafiya ya ɗauki Bihanzin a matsayin maraya zuwa gidansa.
***
SHEKARAR 1720
***
Acikin fada yarima Niyashi ne zaune da mahaifinsa sarki Rafiya.
Niyashi ya dubi mahaifin ya ce, "Baba Dalja, yau shekara huɗu kenan da ɗakko wannan yaro Bihanzin amma har yau baka faɗamin dalili ba."
Sarki Rafiya yai murmushi ya ce, "Kaga yadda kake da jini mai ƙarfi wanda yake hana ka tsufa, to shima wancan yaro naga wani jini mai ƙarfin gaske a tattare dashi. Har yanzu bansan wanne iri bane amma inaji a raina shima yana da gudunmawar da zai bayar a wannan duniya."
A dai-dai lokacin da sarki Rafiya yake tattaunawa da ɗansa, a wani sashi na fada Bihanzin ne ke koyon faɗa tare da ƴar sarki Rafiya wadda ake kira da Hilhusa. Sarkin yaƙi Kabaru shi ne yake kula da wannan aiki.
Sarkin yaƙin ya ce, "wannan ita ce karawa ta farko a tsakaninku wadda na bawa kowa dama yayi amfani da dukkan ƙarfinsa. Saboda haka kowa ya kiyaye."
Yana gama bayani suka ɓarke da faɗa. Sai dai a musaya ta farko Bihanzin ya zame cikin kwarewa ya daki ƙasan hannun Hilhusa da niyyar tunkuɗe takobin dake hannunta. Amma yana dukan hannun nata wani baƙin hayaƙi ya fita daga jikinsa ya daki ƙashinta. Nan take hannun yai ƙara ya ɓalle gida biyu.
Daga Bihanzin har sarkin yaƙin dake wajen babu wanda bai buɗe baki ba cikin mamaki. Wannan shi ke karo na farko da Bihanzin ya taɓa ganin wannan baƙin hayaƙi.
Nan take aka ɗauki Hilhusa aka nufi asibiti.
Bayan sati ɗaya aka sallamota ta dawo gida. Jama'a da dama a fada sunso su halaka Bihanzin sabida abinda yai wa Hilhusa amma sarki ya hana. Yana cewa, "ai duk wanda yaji ciwo a fagen daga laifinsa ne."
Tun daga wannan rana Bihanzin ya fara girmama sarki Rafiya yana ganin ƙimarsa fiye da komai. Daga haka shima ya fara ce masa Baba Dalja kamar yadda ƴaƴansa suke faɗa masa.
Sati biyu bayan Hilhusa taji ciwo jini ya fara zuba daga wajen. Aka koma asibiti inda likita ya bayyana cewa karayar ce bata haɗe ba. Aka ƙara ɗora ta aka kwantar da ita a asibiti tsahon kwana uku sannan aka sallamo su. Abin mamaki bayan sati ɗaya karaya ta ƙara ɓallewa. Aka ƙara komawa asibiti. A haka saida aka ɗora Hilhusa sau ashirin da huɗu. Amma duk da haka karaya bata ɗoru ba.
Babban likitan fada ya bayyanawa sarki cewa Hilhusa ta samu DAUWAMAMMIYAR KARAYA wadda baza ta taɓa ɗoruwa ba kuma baza ta taɓa gyaruwa ba, abadan abidina.
Karayar Hilhusa ita ce al'amari na farko daya fara bayyana daga cikin shaiɗancin Bihanzin.
***
Babi na 139: Baƙin Maraya
Shekaru biyar bayan fara rashin lafiyar Rafiyan Hilhusa ta rasu. Sarki Rafiya yai kuka matuƙa da rasa ƴarsa kwaya ɗaya tak amma daga bisani ya yafewa Bihanzin. Hasalima hanawa yayi a yaɗa zancen wanda hakan yasa da yawa daga cikin al'umma basu san dalilin mutuwar gimbiyar ba.
Shekaru sha ɗaya bayan rasuwar Hilhusa sarki Rafiya ya naɗa Bihanzin muƙamin kwamanda na biyu a daular. Hakan na nuna duk faɗin daular sarkin yaƙi ne kaɗai yafi Bihanzin acikin wanda basu da jinin sarauta.
Saida Bihanzin ya shafe shekaru sha tara a wannan muƙami wanda a lokacin ya samu nasara a yaƙu ka da dama har saida sunansa ya watsu a doron ƙasa.
A ƙarshen wannan shekara Ururu suka samu matsala da sarki Rafiya akan al'amuran cinikin ɗalasimai a kasuwar duniya.
Kowa ya sani sarki Rafiya shi ne kan gaba wajen kasuwancin ɗalasimai a ƙasashen ƙasa amma rana tsaka Ururu suka dakatar da wannan cinikayya. A wannan zamani daular Rafiya ita ce mafi girman daula badan komai ba saboda wannan ciniki. Harma jama'a suna ganin za'a iya zuwa wani lokaci da Rafiyawa zasu kamo Ururu. Kuma wasu suna ganin hakan ne yasa Ururu suka dakatarda kasuwancin.
Koma dai menene dalili sarki Rafiya baiyi amanna da wannan hukunci ba kuma hakan ya jawo sarki Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa na biyu, ya yo ayari na sadaukai dubu ashirin ya kawo hari daular Rafiyawa.
Abu kamar wasa yaƙi ya fara da kaɗan-kaɗan. Al'ummar ƙasa bakwai suka sawa wannan yaƙi suna YAƘIN ƊALASIMAI.
Sai da akai shekaru bakwai ana yaƙin amma ba wanda yaci nasara. A wannan yaƙi ne Bihanzin ya fara nuna fasaharsa ta Dauwamammen sara. Sarki Dul'Ururu ya fuskanci yana rasa jama'a kuma idan aka ci gaba a haka wankin hula zai kaishi dare. Saboda haka ya duba mutun kwaya ɗaya tak wanda yafi ci masa tuwo a kwarya a yaƙin. Mutun guda ɗaya wanda ya hanashi samun nasara. Wannan mutun ba wani bane illa Bihanzin.
Babu wanda yasan yadda akai amma sarki Dul'Ururu ya samu dama ya gana da Bihanzin kuma yayi masa alƙawarin kujerar sarkin Jinzidal indai zai bari aci su da yaƙi. Bihanzin ya amince wanda hakan ne sanadiyyar karya daular Rafiya a wannan zamani. Daga wannan rana aka nemi Bihanzin aka rasa.
Dole sarki Rafiya ya amince da daina cinikayyar ɗalasimai a doron ƙasa. Ance sarki Rafiya ya tsinewa Bihanzin kuma a dalilin haka ne gashin kan Bihanzin ya juye daga ja zuwa zuwa fari.
Jama'ar ƙasa bakwai da suka shaida abinda ya faru suka koma kiran Bihanzin da BAƘIN-MARAYA. Amma ance wannan suna baiyi wa Bihanzin daɗi ba saboda haka yai amfani da wasu ɗalasimai. Ance duk wanda ya bada wannan labari ko kuma ya kira Bihanzin da Baƙin maraya a ranar da daddare zaiyi mafarki da baƙin hankaka kuma washegari da safe jikinsa zai kumbura ya fashe. Hakan ne yasa aka daina wannan zance kwata-kwata a ban ƙasa.
Koda Ikenga yazo nan a zancensa sai wannan yaro mai ɗauke da idanun Ururu yai farat ya ce, "Ikenga akwai yiwuwar kaima ka tashi da safe gobe jikinka a kumbure."
Koda jin haka sai Ikenga da Kána suka fashe da dariya. Ko amsa basu bashi ba.
Jim kaɗan Kána ya nuna wani daji dake gabansu ya ce, "naji ance har cikin wannan daji Jan-doki da Asifu Ruwan-bala'i suka rarako Bihanzin Baƙin maraya."
Yaron ma'aboci Ururu ya haɗe gira ya ce, "wato kaima Kána baka jin tsoron kai mafarki da baƙin hankaka yau da daddare ko?" Suka fashe da dariya.
***
A dai-dai lokacin da su Ikenga suke tattuuna tarihin Bihanzin da Rafiyan Daljari, akan tsibirin Jaljus Armad ne da muƙarrabansa. Tuni muƙaddashin sarki Han'ibal ya fanshi iyalan sarki da Armad. Lamarinda yasa su Iliyasis suka amshi Armad kuma suka saki iyalan.
Har izuwa wannan lokaci Armad bai farfaɗo ba sosai. Saboda haka suka sami wani tsohon kogo suka ɓuya. Iliyasis ya zaro ƙatuwar sarƙa da aka sarrafa da Farar-laya ya saka a bakin ƙofar kogon. Amfanin ta hana wani jin Yanayin-izzarsu.
Cokali na zaune yana haɗa gumi, can dai ya kasa daurewa ya buɗi baki ya ce, "wai dan me yasa bamu ce su bamu nama ba indai suna so mu saki matan sarkin. Aƙalla nasan kowacce mata takai kuɗin raƙumi hamsin. Gashi yanzu yunwa nake ji."
Iliyasis ya dube shi ya ce, "ka fita waje kai farauta."
Nan da nan wani gumin ya ƙara ketowa Cokali. "FARAUTA? So kake na mutu. Kasan hatsabiban abubuwan da suke cikin hazon nan?"
Nanfa musu ya kaure tsakaninsu, Cokali na ganin ya kamata Iliyasis ya samo musu abinci shi kuma Iliyasis ya ce zai iya zama da yunwa har zuwa wani satin. Mutun goman dake tare dasu kawai dariya suke tunda dai daman an saba irin wannan kace-nace tsakanin Cokali da Iliyasis. Yawanci in sunayi Nusi ce kaɗai ke iya tsayar dasu.
A gefe guda Inara ne zaune a kusa da Armad wanda har yanzu idonsa a rufe yake yana numfashi ƙasa-ƙasa. Ga dukkan alamu fasahar Zaren-gwana babban al'amari ne.
Ana cikin haka suka ji muryar Armad yana kakari. "N...nos...tal..jiya... Nos..."
Kowa ya kasa kunne yana jin mai Armad yake cewa.
***
Acan wata uwa duniya sarki Han'ibal ne tafe cikin kayan yaƙi. A bayansa akwai manyan kwamandun yaƙinsa uku. Abin mamaki gagarumar dusar ƙanƙara ke zuba ko'ina hatta gabansu basa iya gani amma a duk lokacinda ƙanƙarar ta taɓa jikinsu sai kaga ta narke.
Suna tafe a hankali a hankali kowa yai shiru sun buɗe fasahar Yanayin-izzarsu suna duba ko'ina saboda tsaro.
Kwatsam sai suka tsaya cak kowa acikinsu yakai hannunsa kan takobinsa.
Duhun ƙanƙarar dake wajen ya fara yayewa. A gabansu wani gagarumin bango wanda ba'a iya gano ƙarshensa ya bayyana. Abin mamaki a jikin bangon babu ko ɗigon ƙanƙara, abu ɗaya kacal da ake iya gani shi ne wata ƙatuwar ƙofa ta jan ƙarfe da kuma wasu diraku guda biyu a gefe.
Suna tsaye cikin shiri sai ɗaya daga cikin dirakun ya motsa inda siffarsa ta juye izuwa wata baƙar halitta mai fuka-fuki bakwai da kayika bakwai. A riƙe a hannunta akwai dorina da sasari irin ƙirar aljanun farko. Wannan halitta ta buɗe baki ta ce, "su waye ku? Kuma maiya kawo ku BANGON-KISRA, bangon daya raba tsakanin duniyar aljanu da mutane?"
Sarki Han'ibal ya amsa da cewa, "nine sarkin Jinzidal, sarki Han'ibal ɗan sarki Han'Harùnu, nazo nan ne domin yaƙar Hidaya Wilbafos."
Sauran mutun uku dake bayansa suma suka bayyana kansu. "Nine Han'Adamul Kanzubuƙ wanda akafi sani da WUTAR DAJI. Nazo ne domin yaƙar Hidaya Wilbafos"
"Nine Han'Rabilu Dùna wanda akafi sani da WUTAR RUWA. Nazo ne domin yaƙar Hidaya Wilbafos"
"Nine Han'Inki Ru'az wanda akafi sani da WUTAR TOKA. Nazo ne domin yaƙar Hidaya Wilbafos"
Koda jin haka sai halittar ta gyaɗa kai ta ƙara maimaita sunan cikin mamaki. "Hidaya Wilbafos?!"
Comments
Post a Comment