Armad ya numfasa ya fara jawabi. "Nima bani da cikakken labarin. Aljanun da suka labarta min sun bayyana min cewa akwai abubuwa da dama wanda suka manta. Al'amarin ya faru ne a tsakanin shekarar 48 zuwa 62 Bayan Amri. A zamanin da sarki Deniz Huhutu shi yake mulkin dukkan doron ƙasashen ƙasa guda shida, haɗe da mutanen da suka zo daga doron ƙasa ta farko wanda tuni sukai mubaya'a ga wannan sarki. A wannan zamani babu wani abu Jinzidal ballantana ma asan sarakunan Jinzidal. Huhutu shi kaɗai ne sarki.
"A shekara ta farko Ururu da suka tashi kawai watso mutane sukai. Babu ruwan su ko su rayu ko su mutu, kai bama su da wata masaniya mai zurfi kan ƙasashen ƙasan, sudai kawai sun watso mutane. Idan ka rayu kan ka, idan ka mutu kan ka. Sudai suna can doron ƙasa na farko suna shagalin su. Akwai kwamandoji da Kuyurussa'ayi ya turo domin su kula da al'amura ta ƙarƙashin ƙasa da kuma wanda ya tura suyi farautar littafin-takobi, amma a zahiri bai juyo da hankalin sa sosai kan ƙasashen ƙasa ba sai a shekarar 48 Bayan Amri.
"Su kuwa iyayen mu da kakannin mu da aka watso tuni sun jima da samun wuri. Suna zuwa suka tarar da ƙasashen nada yalwa da tsari - akwai ƙabilu kala-kala daga mutane da elbis da samudawa, kai harma da dordor masu kai sama da ɗaya. Amma mafi yawan su suna ƙarƙashin mulkin babban sarki guda ɗaya mai suna Deniz Huhutu.
"Ƙabilar Deniz Huhutu samudawa ne baki ɗaya. Kuma suna da wani sirri a jinin su wanda yake basu damar zuƙe hasken rana su ƙara kaurara ƙashin su. Anyi ittifaƙi fatar su kaɗai tafi fiƙar zaƙi tauri kauri.
"Mutun biyu na farko da aka fara turowa daga doron ƙasa na farko su ne Maruta da Haruta. Suna zuwa suka zarce kai tsaye wajen sarki Huhutu suka labarta masa saƙon Jinzidal daga babban sarki Kuyuru. Take sarki Huhutu yasa aka kama su aka ɗaure. Acewar sa 'idan shi Kuyurun ya isa ya sakko yazo da kansa'."
Armad ya ɗanyi shiru yana murza zoben dake hannun sa yana tunani. Bayan ɗan lokaci yai ajiyar zuciya ya kaɗa kai. "Ban san mai ya faru daga tsakanin shakarar 48 zuwa 72 ba, suma aljanun da suka isar da saƙon a gareni basu sani ba, amma sun gayamin cewa a ƙarshen shekarar 72BA, sarki Kuyurussa'ayi ya turo babbar runduna daga doron ƙasa ta farko zuwa ta biyu, inda fadar Deniz Huhutu take, domin a yaƙe shi. Ga yadda yaƙin ya kasance." Armad ya fiddo da kwallon ayrid daga aljihun sa ya cilla sama. Nan take kwallon ya juye izuwa faifan bidiyo inda ya nuna filin yaƙi da Armad yake zance akai.
Acikin filin yaƙin akwai ɓangarori guda biyu. A ɓangare ɗaya wasu mutane ne manya-manya wanda kowanne tsayin sa ya haura zira'i dubu, faɗin sa ya haura zira'i ɗari. Wannan mutanen bawai samudawa bane kawai, a'a sai dai kace musu manyan samudawa. Wato dai a taƙaice idan basamude ya tsaya a gaban su zai iya komawa kamar ɗan jariri. Yawan su yakai dubu ashirin da ɗoriya. Babu ko riga a jikin su banda ɗan bante daya rufe gaban su. Sun jeru suke sahu-sahu sunyi ƙiƙam suna fuskantar abokan gabar su da makamai tsirara.
A ɗayan ɓangaren kuma runduna ce ta zallar Ururu sama da dubu goma. Suna sanye da kayan yaƙi baƙaƙe wanda aka ɗinka da sinadarin yeniy, sinadarin da yafi sulke tauri. Masu jagorantar su sanannun fuskoki ne irin su Dul'Ururu da Haruta da Maruta. Abin mamakin shi ne dukkanin su siffar su iri ɗaya ce da wadda aka sani ayau. Idan ka lura sosai zaka ga baƙin gashin bakin Haruta da farar rigar sa da ɗan siririn sajen sa iri ɗaya ne sak da wanda su Armad suka gani a fafatawar su ta ɗazu. Duk da kuwa wannan yaƙi da suke gani a faifan bidiyo ya afku ne sama da ƙarni goma sha takwas da suka wuce. Towai su wannan mutanen basa tsufa ne?
Sarki Huhutu ya ɗaga al'amudinsa ya fito gaba. Wato Huhutu bajimin ƙato ne. Inuwar sa ta tokare rana. Sulken sa kuwa ya isa yayiwa ɗan ƙaramin gari badala. Yana da dara-daran idanu da kauraran damatsa da ɗan gajeren wuya wanda idan baka lura ba baza ka ganshi ba. Ƙirar sa ta banbanta data sauran samudawan: banda girman jiki daya fisu yana da wasu layi-layi na hatimai a jikin sa wanda suke bada baƙin haske duk sanda ya motsa.
"Ku tsaya, tsayuwa irin ta rana. A yau zamu ga bayan tsinannu masu baƙaƙen idanu" Inji Deniz Huhutu. Muryar sa tana da kaushi matuƙa kai kace ƙashi ake gogawa a ƙasa. Yana rufe baki samudawan suka daidaita sahun su suka zare takubba.
Rundunar suka haɗa baki sukai ihu.
"Mun tsaya, tsayuwa irin ta rana!"
"Mun tsaya, tsayuwa irin ta rana!"
"Mun tsaya, tsayuwa irin ta rana!"
A ɗaya ɓangaren kuwa manyan kwamandu Haruta da Maruta da Dul'Ururu sukai kukan kura da kururuwa suka afkawa rundunar samudawan.
Deniz Huhutu ya ɗaga hannun sa sama, ya ce, "Kibbau!" A wani salo na kwarewa dukkan samudawan suka ɗaga kwari-da-bakan su sama sukai shiri. Zaka iya hango gumi na ɗisa ƙasa daga fuskokin kowanne ɓangare.
Rundunar Ururu basu dakata ba ko kaɗan, kai tsaye suka afka wa samudawan.
Sai da suka kusa, tsakanin su baifi zira'i maitan ba, sannan Huhutu ya cilla hannun sa gaba ya nuna su. Ai kafin hannun sa ya sauka kibbau sun fice, fita irin ta burtu, sun tunkari rundunar Ururu da mugun nufi. Kowacce kibiya jiƙe take da mugun dafi mai narka tsoka da fata. Kafin kibban su ƙarasa tuni samudawan sun fiddo da wasu sun ƙara harbawa. A jere a jere sai da suka harba musu jeri uku kafin na farko su isa.
Amma ko kaɗan Ururu basu dakata ba. Maruta da Haruta suka tashi sama kamar tsuntsaye suka shige gaban rundunar inda suka kira wasu manyan ɗalasimai, Maruta ya kalli gabas, shi kuwa Haruta ya kalli yamma. Take jikkunan su suka fara kumbura suna girma, cikin rabin daƙiƙa sun zama samudawa suma sun cika ko'ina sun tare hanyar da kibban zasu wuce. Kowacce kibiya in tazo sai dai ta caki jikin su maimakon ta wuce ta sami wani. Su kuwa sadaukan dake bayansu suka samu dama ta tsakankanin ƙafafunsu suka fara aika musu da saƙon su.
Cikin ƴan daƙiƙu sama da kibbau dubu maitan sun cake jikin Maruta da Haruta, tayadda sai ka lura sosai ma zaka iya ganin fata.
"Hahaha..." Deniz Huhutu ya kyalkyale da dariyar mugunta. "Maruta, Haruta.... Manyan dolaye biyu. Kuna tunanin ban san sirrin ku ba duk tsahon wannan shekaru? Kai Maruta ance ka ga ranar da zaka mutu da idon ka amma baka san wajen ba, kai kuma Haruta ance kasan wajen da zaka mutu amma baka san ranar ba. To duk baku ga dai-dai ba. Yau ne ranar da zaku mutu, kuma nan ne wajen."
Yana rufe baki kibban da suke cake a jikin Maruta da Haruta suka rabu gida biyu: rabi suka juye izuwa mutane, kowanne riƙe da igiyar wuta da takobin walƙiya suka hau sara da sukan su; rabi kuma suka juye izuwa ƙusar mairakana. Kan kace meye wannan Maruta da Haruta sunje ƙasa. Rundunar Huhutu suka afka kan ragowar mayaƙan.
Ana zuwa nan sai bidiyon ya ɗauke.
"Iyakacin sa kenan. Suma aljanun iyakacin abinda suka samu kenan." Inji Armad.
Iliyasis ya kaɗa kai cikin nazari, ya ce, "To amma idan haka ne ai Huhutu shi yake da alamun nasara a yaƙin. Ya akai Ururu sukai nasara? Ya akai Haruta da Maruta suka rayu? Akwai ayar tambaya."
Armad ya gyaɗa kai. "Tambayar kenan. Tunda dai gashi nan a fili Ururu sune sukai nasara, to mai ya faru da Huhutu? Sannan kuma a wancan zamani duk wani badenize basamude ne, mai yasa yanzu suka koma ƙananun mutane kamar mu? Mai yasa jikin su ya daina zuƙar hasken rana kuma ya daina girma? Meye dalilin tura su ƙarƙashin ƙasa? Abu ne a fili mun san cewa zuƙar hasken ranar da suke yi shi ne yasa suka gagari duniya, shi ne yasa suka zama samudawa, kaga indai zan samu wannan sirrin zan iya yin amfani dashi wajen haɗawa Hidaya jikin da zai iya ɗaukan ruhin ta."
Nan take kowa ya fuskanci hikimar Armad. Wato wancan sirri da Denizawa sukai amfani dashi a baya suka zama samudawa shi yake nema domin ya ƙarfafa fasahar sa ta haɗa mutun-mutumi ya dawo da Hidaya. To amma abun da kamar wuya, idan ba haka ba mai ya hana kowanne badenize sake komawa basamude?
Nusi ta ɗora hannunta akan taswirar dake kan teburin ta kalli Armad, ta ce, "Wai ni kaɗai ce nake mamakin Haruta da Maruta a wannan faifan bidiyon da muka gani? Ɗaya ance yasan ranar dazai mutu amma bai san wajen ba, ɗaya kuma ance yasan wajen amma bai san ranar ba, yau naga hatsabibai!"
Nan fa aka fara kallon-kallo. Hankalin kowa ya dawo kan Haruta da Maruta.
Comments
Post a Comment