Babi na 230-231
***
A wannan lokaci Armad yazo mataki na ƙarshe a wannan gasa. Yana hawa matattakala ta ƙarshe ya fara jiyo yanayin-izzar Hasanu, abin mamakin shi ne bayajin alamun Ikenga ko kaɗan.
Jim kaɗan ya ƙaraso mataki na shida wanda shi ne mataki na ƙarshe a wannan gasa. A wannan mataki babu komai sai fili fetal. Ƙasar wani wajen rairayi ne wani wajen kuma tsandauri. Baya iya hango ƙarshenta, gabas da yamma, kudu da arewa. Ɗan gaba kaɗan dashi Hasanu ne a tsaye yana riƙe da takobi a zare.
Armad yana kallonsa ya tuna lokacin farko da suka haɗu bayan yabar koriyar duniya. A wannan lokaci ratar dake tsakaninsu tana da yawa, ƙanin Hasanu Kiru shi ne sa'an Armad. Amma a yanzu reshe ya juye, Armad shi ne a sama.
Babu wata magana data gilma tsakanin waɗannan jarumai biyu. Hasanu yayi imani da mahaifinsa da kuma shirinsa, sannan kuma baya nadamar dukkan abubuwan daya aika ta domin a iya tunaninsa sune akan dai-dai. Hasalima Hasanu ya yadda babu wanda yakai Bihanzin sanin ya kamata da ƙoƙarin taimakon na ƙasa domin kuwa shi da doron ƙasa na farko yake rigima. Shi kuma Armad yasan Hasanu da Bihanzin sune suka haɗa baki suka yaudari matarsa har ma sukai niyyar kashe ta a sama da lokaci guda. Bayan nan kuma Hasanu ya dawo yana zaginta. Wannan kaɗai ya isa yasa Armad yai hukunci.
Hasanu ne ya fara ɗaga takobinsa sama. Wani baƙin haske ya kewaye takobin, sannan ya nuna Armad da takobin alamun a shirye yake.
Numfashi kawai Armad ya ja tare da kallonsa a hasale.
Bayan ɗan lokaci Hasanu ya ɗaga ƙafarsa ta dama, ya ƙara danne takobinsa da hannun hagu sannan yai gunjin yaƙi ya afkawa Armad.
Armad na tsaye a inda yake yana jiransa. Taku bayan taku saida Hasanu yai taku ashirin da uku sannan ya ƙaraso wajen Armad. Ya ɗaga takobinsa ya kawo masa sara, amma Armad hannu kawai yasa ya riƙe takobin. Ya matsa dai-dai wajenda ya riƙe lamarinda yasa ta karye gida biyu. Kafin Hasanu ya ankare Armad ya yi amfani da dai-dai saman takobin daya ɓalle ya caka masa aciki. Ta shige ta gaba ta fito ta baya.
Jini yai feshi ta bakin Hasanu da hanci, kafin ya saluɓe ƙasa a hankali ya faɗi cikin jininsa. Gawar tasa Armad ya janye ta cikin duniyar sa.
Bayan ɗan lokaci Armad ya tashi sama ya kewaya cikin filin amma babu Ikenga babu alamunsa. Saida Armad ya shafe sama da sa'a guda yana neman Ikenga amma babu Ikenga babu labarinsa.
To ko ina Ikenga yayi?!?!
Amsar tana ƴan awanni da suka wuce kafin Armad ya fara fafatawa da Ƙaizadu. Idan mai karatu bai manta ba kimanin kwana guda daya gabata sarki Ƙaraiƙisu mai mulkin sashin Ikwatora ya kawo wa na cikin kurkuku ziyara. Abinda ya haɗa da iyalan Armad.
Asalin sarki Ƙaraiƙisu shi ne ya afkawa mutanan Ikenga huɗu wato B. Ururu, Deniz Ururu, Daddaru da kuma Kana. Ƙarfin harin Ƙaraiƙisu yai jifa dasu zuwa kurkukun Bango. Basu zame ko'ina ba sai wajen iyalan Armad. Tun kafin iyalan Armad su fuskanci mai ke faruwa Ƙaraiƙisu ya diro daga ƙasa ta farko, inda yakai hari, ya faɗo kurkukun. Babu wanda yasan mai ya kawo shi, wasu suna ganin iyalan Ikenga ya biyo ya ƙarasa su, wasu kuma suna ganin iyalan Armad ya dirarwa sai dai kuma shi bai san Armad ba kuma bashi da wata matsala dashi. Kai wasu ma suna ganin ɗaya daga cikin hakimansa wato Nusi yazo ɗauka, wasu kuma suna ganin kawai yawon shaƙatawa ne ya kawo shi.
To koma dai meye ga abinda ya faru...
Basamude sarki Ƙaraiƙisu shi ne sarkin samudawa na farko a doron ƙasa, shi ne shugaba mai yaƙi da doron ƙasa na farko, sarki mai iko da kowa a sashin ikwatora, sarkin Dordor da mutane da samudu. Ƙaraiƙisu na dira ya dubi iyalan Ikenga huɗu wanda har yanzu wuta suke ci. Babu wanda acikinsu yake da sauran ƙarfi, har Deniz Ururu wanda shima basamude ne. Ƙaraiƙisu ya girgiza kai ya ja dogon numfashi irin wanda ke nuni da cewa sun bashi kunya. Yayi tunanin ya samu abokan karawa zai ɗan ware hannnayensa amma duka ɗaya sun zube.
Bayan ɗan lokaci ya zuƙe su cikin zobensa sannan ya juyo ga su Babara da Nusi. Hankalinsa na kan Nusi. Abin mamaki sai kawai aka ga yayi murmushi. Baice komai ba ya tashi sama ya juya, Nusi ma bata ce komai ba ta bishi. Da Giwa da sarkin Bai da sauran muƙarrabanta suka bita a baya. Babu wanda a wajen ya iya cewa uffan, kowa ya riƙe numfashinsa saboda tsoro.
Bayan ɗan taƙi Iliyasisi ya tashi sama akan iska ya sha gabansu ya zare takobinsa yai ƙaraji zai afkawa Ƙaraiƙisu. A dai-dai wannan lokaci Cokali ya bugi ƙirji shima ya miƙe, sai Babara da Inara. Sai Lamarudu. Kafin daga ƙarshe Nostaljiya ita ma miƙe.
Bakinsu a haɗe suka ce, "Baza ka tafi da ita ba, amanar sarki Armad ce!!"
Nusi tai sauri idanunta cike da mamaki. Ta je wajen Ƙaraiƙisu ta raɗa masa wasu maganganu a kunne kafin daga bisani duk su biyun su ɓace, babu su babu alamunsu.
**
A wannan ranar Baƙar-guguwa zata zaɓi sabon sarkin Ikwatora. Wanda zai mulki gaba ki ɗayan yankin shekaru sittin masu zuwa. Tunda aka fara wannan zaɓe sama da shekaru dubu a kullum Ƙaraiƙisu shi yake nasara duk da kuwa tarin abokan karawa da yake samu a kowanne lokaci. A wannan lokaci ma haka, Ƙaraiƙisu na zaune kan kujerar alfarma samfurin samudawa. A gefensa na dama akwai kujeru guda biyar, kowacce na ɗauke sarki guda na ikwatora. Akan kujera ta uku Nusi ce zaune tana kallon abubuwan dake gudana. A ɓangaran hagu kuwa kujeru ne sama da arba'in, kowacce na ɗauke da ɗan takara. Daga cikin ƴan takarar da aka fi wayewa dasu akwai waziri Jilani daga sashi na farko da Sarki Tambaɗisu daga sashi na huɗu.
Ana zaune kowa yayi shiru ana jiran Baƙar guguwa. Mutane sama da dubu ɗari na tsattsaye a baya suna kallo. Daga can gabansu duwatsu ne manya-manya wanda a bayansu anan babban ramin da baƙar guguwa take. Kamar kullum wajen duhu ne dashi kuma babu wanda yake iya hangen abinda ke faruwa, sai tsoro da kokwanto dake ƙara shiga zuƙatan duk wanda yake kallon wajen. Wannan tsoro shi ne ya hana kowa cewa komai. Waje yayi tsit kamar mutuwa ta gifta.
Saida aka shafe awa bakwai cikin wannan hali sannan da yammaci guguwa ta taso. Acikinta babu komai sai duhu. Take duk duniyar ta koma dare, wani hayaƙi mai ɗauke da zulumi da rashin-tabbas ya cika ko'ina. Ƴan kallo suka fara jada baya. A dai-dai wannan lokaci a wajaje daban-daban na sashin ikwatora alluna ne ke nuna wannan zaɓe. Wasu suna kiransa da zaɓen jini. Wasu suce zaɓen wanda ya isa. Wasu su ce zaɓen kuraye. Amma mafi yawa an fi cewa zaɓen-guguwa.
Bayan waje ya turnuƙe sai ƴan takara suka miƙe, kowa ya sa kayan yaƙinsa yayi shiri, sannan alƙalin zaɓe yayi busa aka fara zaɓe. Sarki Ƙaraiƙisu yai tsalle ya afka tsakiyar guguwar, wasu daga cikin ƴan takarar suka bishi wasu kuma suka shiga a hankali cikin taka-tsantsan. Alƙali na gefe akan wani dutse, masu sheda kuma sune sarakunan sauran sashen wanda basa cikin gasar.
A har kullum babu wanda yasan me ake gani acikin baƙar-guguwa, kuma babu wanda yasan yanda ake zaɓen. Andai san cewa mutun ɗaya ne ke fitowa a raye. Shi kuma baya faɗar abinda ya faru. Wasu suna ganin kamar sauran sarakunan da alƙalan sun san abinda ke faruwa aciki to sai dai kuma kowanne zaɓe akwai shirin da baƙar-guguwa ke yi. Abin cancanjawa yake.
Lokaci-lokaci akan ji ƴar ƙara da ihu ya taso daga cikin guguwar amma a mafi yawan lokuta shiru ne kawai.
Sai da akai awa ashirin ana abu ɗaya kafin daga bisani ƙura ta lafa, guguwa ta fara janyewa. Alamun wani yaci zaɓe.
Bayan komai ya lafa surorin ƴan takarar ya bayyana. Sai dai ba kamar yadda aka saba ba, a wannan lokaci babu ko mutun ɗaya dake tsaye. Ƴan kallo suka zuba ido suga waye zai fara motsi domin dole wani yayi nasara, bazai yiwu ace kowa ya mutu ba.
Minti ɗaya, minti biyu, minti uku....
Har zuwa minti goma babu wanda ya motsa. Nan fa alƙali ya dubi sauran sarakunan cikin kokwanto. Suma tattaunawa suke a tsakaninsu. Kowa na mamakin abinda ke faruwa.
Bayan minti talatin hatta ƴan kallo dake wajen dama wasu sassa na sashin ikwatora kowa ya fara bada nasa hasashen. Saboda kada a kawo hargitsi sarakunan suka bawa alƙali dama ya shiga ya duba idan akwai wani mai sauran rayuwa a jikinsa.
Alƙali Kamulu Aldordawi ya sakko daga kan mumbarinsa. Yana sanye da tufafin alharini wanda akaiwa ado da gashin bakin baƙin Dordor. Aldordawi yana da jinin manyan ƙabilu uku dake sashin ikwatora wato mutane, Dordor da samudawa. Mahaifiyarsa da iyayenta jinsin Dordor ne mai kai uku, mahaifinsa kuma yana da jinin mutane ta ɓangaren uba, yana kuma da jinin samudu ta ɓangaren uwa. Wannan shi ne dalilin zamansa alƙali, ana ganin kowanne ɓangare nasa ne. Zaiyi adalci.
Sannu a hankali Aldordawi ya isa fili. Yasa dogon hannunsa, wanda har cinyarsa yake kaiwa idan ya miƙe, ya taɓa gawa ta farko. Babu rai babu alamunsa. Har amfani yayi da hatimin sirri mai gane rayuwa amma baiji komai ba.
Ya girgiza kai ya wuce kan gawa ta gaba, ita ma haka. Nan take ya wuce kan sarki Tambaɗisu na sashi na huɗu. Shi ma ba labari. Abin mamaki sarki Ƙaraiƙisu shi ma ba labari. Waziri Jilani shi ma hakan take.
Da damansu babu manyan raunika a jikinsu amma kamar wani abu ya zuƙe musu rayuwar jikinsu, babu mai ko motsi aciki. Kai wasu ma har jikinsu ya fara canjawa tamkar sun daɗe da mutuwa.
Jiki a mace alƙali Aldordawi ya ƙaraso wajen sarakunan ya raɗa musu abinda ya samu. Sannan kuma ya gaya a kundin-tsarin mulkin ikwatora babu wani hukunci da yayi magana a kan irin wannan yanayi. Dalili kuwa ba'a taɓa samu ba, kuma wanda suka halicci Bakar guguwar sunyi alƙawarin baza a samu hakan ba.
Koma dai meye dalili yanzu an samu, kuma ya rage ya wannan sarakuna da shi alƙalin dasu yanke yadda za suyi.
Nan take wasu daga cikin ƴan kallo suka fara yaɗa maganar. Kan kace meye wannan sashin ikwatora ya fara neman hargitsewa ya shiga cikin ruɗani. Ƴan kowanne sashi suna ganin kawai a bawa nasu ya zama sarki. Alƙali Aldardawi yana ganin a sake saka rana wasu ƴan takarar su ƙara maimaitawa sai dai kuma shi kansa bashi da ƙarfin taso baƙar guguwar ya kawo ta. Koda an samu ƴan takara bashi da amfani idan guguwar bata fito ba. A yanzu zasu iya haɗa baki da sauran sarakunan suyi wa mutane ƙarya dan a samu kwanciyar hankali, to amma kuma gaskiya zata bayyana a hankali. Su kansu sarakunan a tsakaninsu zasu ci dunduniyar juna.
Dole a samu matsaya a wannan lokaci.
Nusi ta daki kujera. "Ayi ƙuri'a kawai, duk wanda yayi nasara shi ne."
Sarkin ƙasa ta shida wanda shi yafi kowa tsufa acikinsu ya ce, "babu wata ƙuri'a, kawai a bawa wanda yafi kowa daɗewa akan mulki. A girmama na gaba."
Sarkin sashi na biyar ya harari na shidan ya ce, "zancen banza kenan, dan kafi kowa daɗewa ina ruwanmu. Kawai ayi fito na fito tsakanin mu huɗun nan, duk wanda yayi nasara shi ne."
Nan fa hargitsi ya rikice. Shi kansa Aldordawi ya kasa shawo kansu. Suna yi magoya bayansu nayi.
Ana haka babu wanda yaga bayyanar wani saurayi a tsakiyar wannan gawarwaki. Saurayin ya dudduba inda idanunsa suka faɗo kan gawar sarki Ƙaraiƙisu. Ya ƙarasa wajen ya ɗora hannunsa akan goshinsa. Bayan ɗan lokaci yayi murmushi sannan ya miƙe ya tsaya a tsakiyar gawarwakin.
Hasken izza ya fara fita daga jikinsa a hankali a hankali, kafin daga bisani hasken ya cika ko'ina.
Aldordawi da su Nusi suka juyo suk fuskanci wannan haske. Suma ragowar mutanen ikwatora masu kallo suka tara hankalinsu. A tsakiyar hasken akwai saurayi tsaye wanda hasken bai hana ganinsa ba.
Idan ka lura sosai wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga.
"Suna na Ikenga Oduduwa Bayajidda, nazo karbar gado na a sashin ikwatora. Amma da farko..."
Ikenga ya ɗaga hannayensa biyu sama inda hasken dake jikinsa ya watsu cikin gawarwakin. Duk gawar da hasken ya taɓa sai kaga ta fara motsi. Cikin ƴan daƙiƙu duk gawarwakin suka buɗe idanunsu suka miƙe. Bawai sun tashi bane a matayin bayi ba, ba kuma sun tashi bane a matsayin matattu ba, a'a, sun tashi ne a matsayin mutane kamar yadda suke a da. An cire mutuwar data ɗauke su, an cire lokacin amma kuma an barsu da sanin abinda ya faru. Kowa acikinsu yasan ya mutu, kuma yasan Ikenga ne ya dawo dashi. Ya rage ya nasu suyi biyayya ko kuma su fanɗare.
Amma alƙali Aldordawi tuni gwiwowinsa suka je ƙasa cikin biyayya yana jin sunan Oduduwa. Sarki na biyu dana uku tuni suma sukai biyayya. Su kuwa ƴan kallo sun shiɗe sun rasa abinda ke faruwa. Ana cikin haka Ikenga ya ƙara ɓacewa ya dawo gasar cin ruhin Deba. Yana bayyana ya tadda Armad na zaune a gefe yana jiransa.
Ikenga ya dira a gaban Armad, fuskarsa babu alamun damuwa ko tsoro ko kokwanto. Ya dubi Armad ya ce, "ko kasan me 'O' ɗin dake suna na take nufi?"
Armad bai ɗago kai ya kalleshi ba ya bashi amsa, "ko kasan me 'W-fakta' dake suna na take nufi?"
Waɗannan jarumai tuni sun saba da juna domin kuwa ba wanne ne haɗuwarsu ta farko ba, sabida haka nan take kowa yai tsayuwar yaƙi suka fuskanci juna.
***
Babi na 232
***
A karo na farko Armad ya samarda takobin Negrinkin zalla. Ita wannan takobin zaka iya cewa ta hayaƙi ce, jan hayaƙi launin Negrinki. Tana da tsayi zira'i uku da faɗi kamu biyu, kaifi biyu. Mariƙin ta na hayaƙi ne.
A ɗaya ɓangaren kuma hasken farin wata ne ya fara taruwa a gaban Ikenga. Daga bisani wannan haske ya dunƙule waje guda ya juye izuwa siffar takobin haske irin ta Armad.
"[Kaban'shisu]."
Armad ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan Ikenga ya kai sara.
"[Rawar-aljanu]."
Shima Ikenga ya kira nasa ɗalasimin ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan Armad. Idan mai karatu bai mantaba a duk sanda Ikenga yayi amfani da fasahar [Rawar-aljanu] ya kan bar hotonsa a wajenda ya bari saboda tsananin sauri. A wannan lokaci ma haka. Takobin Armad ta dira akan hoton Ikenga ta zuƙe shi cikin duniyar Armad. Shima Ikenga ya kawo wa Armad sara da takobinsa ya same shi.
Take jikin Armad ya tsofe kamar ya shekara maitan a lokaci guda. Fatarsa ta yanƙwane sannan ganinsa ya dakushe. Ikenga ya ƙara ɗaga takobin lokaci zai ƙara sararsa amma a lokacin ya fuskanci cewa abinda ke gabansa mutun-mutumin walƙiya ne. Armad na gefe a tsaye.
Ikenga ya kira ɗalasimai; hadari ya taso, ruwan ƙanƙara da walƙiya suka fara ambaliya. Ƙatotuwar dunƙulen walƙiya wadda takai girman [Hannun-aradu] ta dira akan Armad. A ƙasa kuma kogin maliya ya taso daga gabas zai cinye Armad, sannan kuma wani bango mai kama da bangon duniya amma na kankara ya taso daga yamma ya kewaye Armad ya hana masa ƙofar tsira.
Armad na tsaye a inda yake bai motsa ba. Walƙiyar ta dakeshi, ruwan ya cinyeshi sannan kuma ƙanƙarar ta daskarar dashi a ƙasan kogin. Idan ka kalli abin daga nesa zaka hangi ƙatoton kogin ƙanƙara ya binne Armad a ƙasa.
Bayan ƴan daƙiƙu kawai sai aka hangi tsakiyar ƙanƙarar ta fara yin ja, bayan daƙiƙa bakwai sai aka hangi jan ya fara narkewa kafin daga bisani ƙatoton rami ya bayyana a tsakiyar ƙanƙarar. Walƙiya ta fito daga ƙasan ƙanƙarar tai sama ta haɗe da sararin samaniya sannan ta ɗinke dukkan duniya baki ɗaya. Babu wani kogi ko wata ƙanƙanrar Ikenga data rage.
Dukkan wannan walƙiyar ta tattara a waje guda ta dira akan Ikenga.
Ikenga na tsaye bai motsa ba har walƙiyar ta dira akansa. Tun kana hango shi har saida walƙiyar ta cinyeshi. Baga ganin komai sai ambaliyar wuta tana cinye ƙasa.
Bayan minti biyu abubuwa sun lafa. Wani wawakeken rami ya bayyana, walƙiyar ta cinye komai amma Ikenga na tsaye akan iska yana lilo kamar farin aljani babu ko kwarzane a jikinsa.
"[Takun-sarki]."
Ikenga yai taku na farko inda wasu dirkoki guda biyu suka bayyana a gefen Armad. Kowacce dirka tana da kaurin mutun dubu sannan ta tokare da sararin samaniya. Sirrin tsafi da tsohuwar izza ya fara fita daga jikin dirkokin. Sannan daga bisani farin hayaƙin Negrinki ya fara fita daga jikinsu yana haɗewa da juna. Armad na tsakiya, yai ƙoƙarin tsalle ya fice amma ya kasa motsawa. Yayi amfani da fasahar Kabanshisu amma batai aiki. Idan ya ɓace sai ya ƙara bayyana a wajen daya bari. Wannan dirkokin sun riƙe duk wata fasaharsa.
Ikenga ya ƙara taku na biyu. A wannan lokaci wasu dirakun guda biyu suka ƙara bayyana, wata a baya wata a gaba. Kowacce na fitar farin hayaƙi. Suka yiwa Armad dabai-bayi suka hanashi motsi sakat.
Kafin Ikenga ya kai taku na uku, a wani salo na fushi da fushin Ikenga ƙasa ta yunƙura ta nannaɗe Armad ta matse shi dashi da walƙiyar tasa. Har saida aka jiwo ƙarar fashewar ruhin Armad a doron ƙasa na farko.
Sai dai kuma a wannan lokaci Fasahar-mutuwa ta fara aiki. Jikin Armad wanda ƙasa ta haɗiye ya dawo ya haɗe. Tsoka da jini suka ci gaba da gudana a jijiyoyinsa. Ruhinsa ya dawo jikinsa. Sai dai kuma saɓanin lokutan baya wanda a duk sanda Armad ya dawo ƙarfinsa ƙaruwa yake a wannan lokaci ƙarfinsa raguwa yayi. Shi kansa mamaki ya cika shi.
Ikenga bai tsaya bayani ba ya ƙara saukarda fasahar Takun-sarki inda ƙasa ta ƙara haɗiye Armad ta halaka shi. Bayan ya dawo ƙarfinsa ya ƙara raguwa maimakon ya ƙaru.
Koda ganin haka sai Ikenga ya fashe da dariya, Negrinkinsa tana aiki.
"Akwai Dafi acikin Negrinki na. Indai na sare ka da ita to ba lahira ba ko'ina zaka je ka dawo dafinta yana tare dakai. Tana ƙara shiga jikinka tana ƙara aiki a akanka. Kaje lahira ka dawo amma duk da haka dafin dana saka a jikinka yana aiki. Kana tunanin zaka iya gujemin? Idan zaka dawo sai ɗari a kowanne lokaci ƙarfinka yana raguwa sai ka gwammace baka dawo ba. Domin kuwa kiyashi ma saiya fika ƙarfi."
Nan fa aka fara. Ikenga ya murƙushe Armad da Takun-sarki shi kuma ya dawo da Fasahar-mutuwa amma a kowanne lokaci maimakon ƙarfinsa ya ƙaru raguwa yake. Sannu a hankali ya faɗo matakin Ƙassai. Daga nan ya ƙara yin ƙasa.
Bayan ɗan lokaci Armad baya iya sarrafa koda fasahar Sikai. Ikenga ya faki idonsa ya saukar masa da fasahar Lokaci inda ya juya shi izuwa tsoho ɗan shekara maitan. Shima Ikenga yasan kashe Armad zaiyi wahala saboda haka yayi amfani da rashin ƙarfinsa ya zuƙe shi cikin zoben sihirin dake hannunsa.
Wani murmushin jin daɗi ya bayyana a fuskarsa. A yau yayi nasara akan dukkan wani sa'ansa a ban ƙasa. Bayan ƴan daƙiƙu ya kasa daurewa ya fashe da dariyar mugunta yana dukan ƙasa da ƙafarsa cikin alfahari. A duk faɗin duniya ana kallonsa amma ko a jikinsa.
Ana haka yaji murya a kunnensa. "Haka ka damu kaga bayana?"
Yana waiwayowa yayi arba da Armad sabo fil a leda. Kafin yayi wani abu Armad ya caka masa takobin Negrinki a ƙirji ya zuƙeshi cikin duniyarsa. Sannan ya janyo zaren izza ya bishi cikin duniyar.
A ɓangarori uku na cikin wannan duniya manyan tsaunuka suna riƙe da Ƙaizadu da Hasanu da Elbinuil. A gefe guda kuma ga ƙarin Ikenga yazo.
Armad ya bayyana a gaban Ikenga wanda tuni yasa ankokin wuta suka ɗaureshi.
"Zan sake ka, idan kaje ka gayawa uban gidanka yazo da kansa idan yana so yai arba dani. A duk sanda zai turo mutun-mutumi nima mutun-mutumi zai gani. Sannan kuma ka labarta masa cewa ina nan tafe zuwa sashin Ikwatora."
Armad ya sare hannayen mutun-mutumin dake gabansa. Ya yanke masa gashi da kunnuwa sannan ya sake shi domin ya koma ya kaiwa ubangidansa Ikenga saƙo.
Tun bayyyanarsa Armad ya gane mutun-mutumi ne a gabansa ba Ikenga ba. Saboda haka shima ya samarda mutun-mutumi ya tura masa ya koma gefe yana kallonsu. Mutun-mutumin Ikenga bashi da ikon ganin Armad.
A wannan ƴar gajeriyar fafatawa Armad ya gano sirrin Negrinkin Ikenga da kuma canjin da aka samu a bisa fasahar Takun-sarki. Ya kuma gane cewa lallai Ikenga shi ne mafi barazana a gareshi sama da duk wani sa'ansa. Lallai haɗuwarsu ta zahiri za'a kai ruwa rana.
Abin tambayar anan shi ne ina ainihin Ikenga yake?
A wannan lokaci gasar cin ruhin Deba tazo ƙarshe. Armad ya mallaki ruhin Hidaya bayan fafatawa da sa'anninsa daga kowanne ɓangare na duniya. Gasar babu shakka ta ƙara haskaka tauraruwar Armad a kowanne saƙo da lungu na ƙasa bakwai.
Armad na fitowa daga ƙofar-asali ya tadda shaihu Babila da sauran ɗaliban makarantar suna jiransa domin tarɓarsa.
***
Babi na 233-236
***
Kwana goma kafin fara gasar Ruhin Deba
Majalisin Masana
Shaihu Babila da Bihanzin da yarima Dumaƙisu da Haruta da Maruta da Taidara da Ƙaraiƙisu da waziri Tadiyraini suna zaune acikin ɗakin taro dake maɗaukakiyar fada a doron ƙasa ta farko. A bayan Bihanzin akwai sarkin-sarki da sauran sarakunan Jinzidal uku. A bayan Taidara akwai Fatima Bayajidda mahaifyar Armad da Zaikid Wilbafos da Shata Kil'zanki. A bayan yarima Dumaƙisu akwai mutun takwas na Tasu'a. Su kuma Haruta da Maruta da waziri Tadiyraini da shaihu Babila suna zaune su kaɗai.
Fada tayi tsit ana kallon-kallo. Ba wannan ne karo na farko da waɗannan mutane suka zo doron ƙasa na farko ba, kuma ba wannan ne karo na farko da suke yin irin wannan taro ba. A duk karshen kowanne Zamani ana aiwatar da shi. Anyi Zamani na farko wanda akewa lakabi da Farkon Lokaci, sannan kuma anyi Zamani na biyu wanda ake kira da Dogon Zaure, sai kuma Zamanin da ake ciki wanda shi ake kira da Rawar Sani.
Taidara ne ya fara magana. "Dukkan alamun taurari da tafiyar rana da wata da sauran alamomi sun nuna munzo ƙarshen wannan Zamani wanda muka sakawa suna Rawar Sani. Majalisin Masana ya kamata ya bayyana matsayarsa. Ni dai matsayata ita ce: daga yau na yanke duk wata alaƙa da wannan majalisi, babu sauran fahimta a tsakaninmu daga yau. Zaku iya yaƙa ta nima zan iya yaƙarku."
Yana rufe baki Bihanzin ya amsa da cewa, "nima na yanke alaƙa." Mutanen dake bayansa suka gyaɗa kai alamun amincewa.
Shaihu Babila ya numfasa ya ce, "wannan ba matsala bace domin dukkaninmu mun yadda ƙarshen Zamani yazo, saboda haka kowa yana da iko yayi abinda yaga dama. Amma akwai zance na cinikin yaƙutun-izza, zamu ci gaba da yinsa ta ƙarƙashin wannan majalisi. Idan akwai wanda bai yadda na yayi magana."
Ya dubi Bihanzin da Taidara amma babu wanda ya nuna alamun rashin amincewa.
Waziri Tadiyraini ya dubi Dumaƙisu ya ce, "Yarima, mai zaka ce game da wannan shawara da Bihanzin da Taidara suka yanke?"
"Fada bata buƙatar komai daga mutane, ku kuka rokemu aka haɗa Majalisin Masana saboda kuna buƙata. A yanzu kuma bakwa buƙata, kuna ganin ƙarfin ku ya kawo. Zamu ci gaba da cinikin yaƙutun-izza daku amma duk wanda ya kauce hanya zai fuskanci hukunci irin wanda ƙabilar Oduduwa ta fuskanta. Sannan kuma daga yau an haramta muku hawo wa doron ƙasa ta farko. Duk wanda muka kama hukuncin kisa ne."
Yana rufe baki ya tashi ya fice, Tasu'a suka bi bayansa.
Ɓangaren Armad
Ƙatoton wajen taro ne wanda girmansa yakai ɗan ƙaramin ƙauye. Duk inda ka hanga kujeru ne da ɗalibai ke ta kai komo wajen hidima. Ana sauke abinci da abin sha ana ƙari. Zaka iya cewa duk wani ɗalibi dake Babila ya halacci wannan walima da ake gudanarwa domin murnar samun nasarar Armad.
Kai hatta daga sauran sassa na duniya al'ummatai sun zo domin taya Armad murna. Tuni aka shafe awanni ana gudanar da wannan taro. Tun farko dai da kyar shaihu Babila ya shawo kan Armad domin ya tsaya ayi wannan taro dashi. Ya gaya masa a duk sanda aka gudanar da irin wannan gasa ya zama al'ada Babila ta shirya gagarumar walima, kuma a kowanne lokaci wanda yai nasara shi ne babban baƙo na musamman. 'Taron bashi da amfani idan wanda akayi danshi bai ziyarta ba', inji shaihu Babila.
Akwai babban teburi a ajiye a tsakiyar ɗakin wanda aka jera kujerun ɗalibai a jikinsa. Daga sama kuma akwai kujerar ɗalibai da manyan baƙi. Shima Armad yana zaune kan kujera da ɗan ƙaramin teburi a gabansa wanda ke ɗauke da kayan alatu kala-kala. Rigar jikinsa fara ce mai ratsin baƙi sannan kuma tambarin Miyuyar sa ya fito rangaɗaɗau a goshinsa. Yana zaune cikin nutsuwa da kamala, rabin hankalinsa yana ɗakin taron rabi kuma yana wani waje. Hakan nema yasa baiji sanda Shaihu Babila yake yi masa magana ba har saida shaihun ya taɓashi kaɗan a kafaɗa.
"Dukkan ɗaliban nan da mahalarta bayanin ka suke son ji, sun saba jin muryata dani da sauran ƴan'uwa na malamai." Inji shaihun.
Armad yayi murmushi cike da mamakin ƙasƙantar da kai irin nan shaihun. Abu ne sananne hatta Kuyurussa'ayi bashi da ikon yiwa Babila kutse domin kuwa an gwada ba'a cimma ɗa mai ido ba. Kowa nason ya mallaki makarantar mai dogon tarihi amma an buga an kasa. Dole aka barta taci gaba da zama a matsayin ƴan'tacciya.
Armad ya karɓi bututun maganar dake hannun shaihu Babila ya miƙe tsaye ya fuskanci taron. Shidai wannan bututun magana yana amfani da ɗalasimai masu ƙara ƙuwwa da ƙarfin sauti. Duk maganar data shiga ciki za'a ƙara mata ƙarfi taje duk inda ake so.
"Ehem..." Armad yayi gyaran murya inda ɗaliban suka kwashe da tafi da shewa suna kiran sunansa. "Armad! Armad!! Armad!!!"
Armad ya ɗaga musu hannu aka tsagaita sannan ya ɗora da bayani. "Ga dukkan alamu babu buƙatar na faɗi suna na, abinda nake da buƙatar faɗa shi ne cikakken suna na wato Armad WILBAFOS. Cikin kuskure na taso ina ɓoye cikakken suna na wanda hakan yasa da dama basu sanshi ba. Iyalan Wilbafos suna raye kuma ni shaidar hakan ne."
Yana gama faɗar haka ya godewa kowa sannan ya nemi ayi masa afuwa domin bazai samu damar kaiwa ƙarshen taron ba. Bayan ya gaggaisa da manyan baƙi sai shaihu Babila da kansa ya kaishi babban ɗakin karatu na Babila domin nuna masa tsoffin littafan tarihi da sauran ajiyayyun kaya. Ya bawa Armad damar ɗaukan abu ɗaya. Shi dai wannan ɗakin karatu yana da faɗi amma ba wani na kuzo-mu-gani ba, sai dai yana da tsayi wanda bazai misaltu ba. Komin hangenka baka iya hango rufinsa.
Hawa ɗai-ɗai har hawa ɗari shida, kowanne hawa akwai irin tsarin littafan dake kai. Kana ƙara sama ƙimar littafan tana ƙaruwa. Kowanne ɗalibi akwai iyakacin wajenda aka yadda ya hau. Zaka iya cewa babu wani ɗalibi da aka yadda ya haura hawa na hamsin. Malamai ma iyakacinsu hawa na ɗari biyu. Shaihunnai su aka yadda sukai hawa na ɗari huɗu zuwa na ɗari huɗu da hamsin. Amma babu wanda aka yadda ya ziyarci hawa na ɗari biyar zuwa sama sai shaihu Babila indai ba da wani babban dalili ba.
A dai-dai wannan lokaci Armad da shaihu Babila na can ƙololuwa mataki na biyun ƙarshe wato mataki na ɗari biyar da casa'in da tara.
"Dukkan littattafan dake hawan nan babu wanda bai haura shekara dubu ba. Zaka iya ɗaukar littafi ɗaya a matsayin kyauta daga wannan jami'a. Kayi sani cewa duk littafin daka ɗauka babu irinsa a duk faɗin duniya sai a nan."
Armad ya gyaɗa kai cikin godiya sannan ya fara bibiyar littafan.
*Tarihin Oduduwa da sauran shararrun ƙabilu.*
*Sarakunan Ururu*
*Sarakunan Wilbafos*
*Dordor da aljani*
*Canfi da Sihiri*
*Asalin Izza*
Haka dai Armad yaci gaba da dubawa kanta bayan kanta. A lissafinsa akwai littafai sama da dubu maitan a wajen, idan yace zai tsaya lalube da duba kowanne littafi kafin ya zaɓa zai iya yin watanni bai gama ba. Hanya mafi sauƙi ita ce....
Ya juyo ya dubi shaihu Babila ya ce, "littafan da yawa, a matsayin ka na shaihun malami wanne zaka bani shawara na zaɓa?"
Babila yayi murmushi, tuni yayi tunanin haka a ransa. Domin hakan shi ne abinda duk wani mai lissafi zaiyi, kasancewar Babila yana da cikakkiyar masaniyar Armad bai taɓa karanta ko ɗaya daga cikin littafan ba.
"Mene ne burinka a rayuwa?"
Armad ya dubi Babila a nutse, duk da bai tsammaci tambayar ba amma yana da amsarta a ajiye. "Karya cinikin bayi, ɗaukan fansa kan waƴanda suka kashe Hidaya."
Idanun Babila suka yiwa Armad kallon ƙurilla cikin mamaki. "Fansa?!"
Armad ya gyaɗa kai. "Idan kana tunanin zan bar kashe Hidaya ya tafi a banza to ka daina."
Bayan ɗan taƙi Babila ya ja dogon numfashi ya gyaɗa kai. "Akwai mutane da dama dake son karya cinikin bayi, da yawansu sun daƙile a hanya saboda basu san haƙiƙanin mai yasa ake cinikin bayi ba. Bari na baka ɗan misali, mai yasa sarakunan Jinzidal da Bihanzin har yanzu suke cikin cinikin bayi duk da sunyi wa doron ƙasa na farko bore?! Saboda yaƙutun-izza da kayan sihiri da littafan koyon fasaha da sauran abubuwa da dama wanda daga doron ƙasa na farko kaɗai ake samunsu.
"Musamman yaƙutun-izza, a doron ƙasa na farko kaɗai ake haƙarsa. Dashi ake sinadarin Yeniy, dashi ake ƙofar Eycigan, dashi ake ƙara yawan izza, dashi ake haɗa hatimi, dashi ake ƙirƙirar ɗalasimai, dashi akeyin kayan sulke da sauran kayan yaƙi wanda fasaha bata ratsa shi. Idan a yau doron ƙasa ta farko suka daina samarda yaƙutun-izza gaba ɗaya tattalin arziƙin izza karyewa zaiyi a ƙasashen ƙasa. Idan muka sayar musu da bayi sai su bamu yaƙutu, a tunaninka mai yasa tunda can suka barmu muke kula da Jinzidal? Saboda sun san koda Jinzidal ko babu muna buƙatar yaƙutu kuma su kaɗai suke dashi. Mu hana su bayi su hana mu yaƙutu.
"Mutane da dama da sukai ƙoƙarin hana cinikin bayi basu samarwa da mutane wata hanya da zasu samu yaƙutu ba sabida haka aikin banza kawai sukai. Rayuwa baza ta yiwu ba saida yaƙutu, idan kana so ka hana cinikin bayi saika samarda yaƙutu."
Armad yai shiru yana saurare. Labari ne mai amfani to amma mai yasa yake gaya masa shi a yanzu?
"Dalilin da yasa nake maka wannan jawabi shi ne akwai littafi da yayi magana akan yaƙutun izza a hawa na gaba wato hawa na ƙarshe. Hasalima littafai uku ne kacal a hawan ƙarshen kuma wannan littafi yana daga cikinsu. Amma bazan iya baka wannan littafi a kyauta ba, idan kana sonsa to muna buƙatar WAƘAR-MAƘABARTA. Zamu saka Waƙar a hawa na ƙarshe ta zama littafi na huɗu."
Armad ya harari Babila, babu wani dalili da zaisa ya bada Waƙar-maƙabarta saboda yaƙutun-izza. Badan komai ba sabida sirri ne na ƴan gidan Wilbafos kaɗai.
"Wannan hira ce, kaima kasan bazai yiwu ba." Armad ya fara tunanin cewa duk kyautatawar da suke nuna masa dan ya basu Waƙar-maƙabarta ne. Bai masan yadda shaihun yasan da littafin ba.
Shaihu Babila yai murmushi kamar daman yasan haka zata faru. "Kana da lokaci, zaka iya tafiya ka dawo bayan shekaru. A duk sanda ka shirya zaka iya dawo wa. Abu ɗaya da zan faɗa shi ne kamar yadda kake tunanin Waƙar-maƙabarta sirrin gidanku ce shima wannan littafi da zan baka sirrin gidan Oduduwa ne wanda a halin yanzu babu wani mutun dake numfashi a ban ƙasa daya san dashi. Zan iya gaya maka cewa wannan littafi yana daga cikin dalilai da suka sa aka ƙarar da ƙabilar Oduduwa. Kuma wasiyya ce aka rubuta aciki zuwa ga jikokon gidan.
"Shekaru da dama Ikenga yazo yana son littafin amma shima bazai iya bada abinda muka tambaya ba sabida haka ya tafi. Sau uku yana dawo wa yana kawo wasu abubuwan a maimakon abinda muka tambaya amma muka ƙi. Ina kyautata zaton kaima idan ka tafi zaka dawo. Kada kaga kamar na matsa amma idan da bayarwa muke bama karɓa da yanzu mun rasa komai cikin shekaru dubu da suka wuce."
Armad yaja dogon numfashi ya gyaɗa kai. Lallai ya fahimci yadda abin yake, ko shi ne zai iya yin makamancin hakan. Amma duk da haka bai yadda cewa darajar littafin da shaihun zai bashi takai darajar Waƙar-maƙabarta ba. Kuma idan ya bada waƙar hakan na nuna cewa wani zai iya mallakar sirrikansu. Lallai koda zai duba wannan al'amari to yana buƙatar lokaci. Wani abu daya tsaya masa a rai shi ne ragowar littafai biyu dake hawa na ƙarshen. Babila ya ce masa akwai littafai uku kacal. Ya gaya masa ɗaya yana magana akan yaƙutun-izza amma bai gaya masa sunansa ba, sai kuma ragowar biyun wanda bai faɗa masa ba.
"Baka gayamin sunan littafin ba. Sannan kuma ina son sanin ragowar littafai biyun, idan zai yiwu."
Babila ya kyalkyale da dariya. "Kowa yazo sai yayi wannan tambaya, Sarkin-sarki kaɗai na taɓa bawa amsa saboda ta bani wani abu a maimako. Idan zaka iya bani wani abu a maimako kaima sai na gaya maka sunansu."
Armad ya haɗe gira. "Wai kai malami ne ko kuma ɗan kasuwa? Duk abubuwanka na ciniki ne, ɗazu kace kana son Waƙar-maƙabarta yanzu kuma mai kake so?"
Babila ya gyaɗa kai. "Idan ba'a haka da tuni makarantar Babila ta rushe. Yawan abinda na sani da wanda Kuyurussa'ayi yake tsoron na faɗawa duniya sune suke riƙe da wannan makaranta. Duk abinda aka gayamin ina bada alƙawarin shekara guda kafin na gayawa wani. Zaka iya kwantar da hankalinka cewa babu wanda zai san abinda ka gayamin sai bayan shekara guda."
Armad ya ɗaga kafaɗa. "Amma kasan akwai fasahar da ake iya karanta tunanin mutun ko?"
Babila ya ja dogon numfashi sannan a karo na farko fuskarsa ta canja izuwa kamala da izza. "Ko Kuyurussa'ayi bai isa ya karanta tunani na ba. Ni ne na ƙirƙiro fasahar sarrafa tunani a duk faɗin duniya. Ni ne ABARAI BAYAJIDDA yayan Amraikugyu Bayajidda."
"Abarai?!" Armad ya zare ido cikin mamaki domin tabbas ya taɓa jin wannan sunan amma kuma ya manta a ina. Amma bai manta Amraikugyu da Bayajidda ba.
"Kaima ɗan'uwan Ikenga ne kenan?"
Shaihu Babila ya gyaɗa kai, "a'a, shi Ikenga O. Bayajidda ai ba haƙiƙanin jinin Bayajidda bane. Mutane basu sani ba amma shima ta ɓangaren uwa ya gaji jinin Bayajidda kamar kai. An ɓoye sunan ne saboda kada maƙiya mahaifinsa su cimmasa. Ka taɓa jin sunan Fir'aunu?!"
Armad ya girgiza kai.
"Sunan sarauta ne a yankin gabas. Ni kaina bansan asalin alaƙar wannan sarauta da gidan Oduduwa ba amma duk sarakunan gidan sunansu kenan. Ikenga Fir'aunu Oduduwa, jikan sarkin ikwatora na farko, Fir'aunu na Ɗaya wanda ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴan gidanka a Farkon Lokaci."
Armad ya juyo cikin sauri ya fuskanci Babila. Sunan Babila da kuma kasancewarsa yayan Amraikugyu bai dame shi ba, kasancewar Ikenga ba ɗan asalin Bayajidda ba bai dame shi ba, kasancewar baban Ikenga shi ne tsohon sarkin ikwatora wannan ma bai dame shi. Babban abinda ya dame shi shi ne kakan Ikenga ya auri ɗaya daga cikin mutanensa. Wace ce aciki? Duk cikin mutanensa da mutanen Lamarudu baya iya tunano wata tsohuwa wadda takai ace ta auri kakan Ikenga amma bai sansu sosai ba. Yana buƙatar yasan suna.
"Suna?"
Shaihu Babila ya girgiza kai. "A,a, ai tuni na wuce iyaka ta. Na faɗa maka abubuwanda bai kamata ka sani ba. Indai kana so ka sani sai dai ka bayarda wani abu."
"Mai kake so?"
Wani ɗan hasken farin ciki ya gilma ta idanun Babila. Sai wanda ya nutsu zai gani domin baifi daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace amma duk da haka Armad ya gani.
"Ina so ka bani dama na karanta tunanin ruhin Hidaya."
Armad ya cije harshe. "Amma ka zare ko?"
"Ko ɗaya," inji Babila, "nasan kasan dokar ruhin Deba, baza ta iya gayamaka komai ba kuma baza ta iya baka labarin komai ba. Daga sanda ka haɗe da ruhin zaka shiga Deba amma kuma duk wani abu dake cikin kwakwalwar ruhin zai goge. A taƙaice kaima baza ka samu komai ba, ni na rasa kaima ka rasa. Amma idan ka barni na karanta tunaninta a yanzu kafin ya goge zan sanar dakai abinda na gani. Kaga kowa ya samu."
Armad ya dube shi a hasale ya ce, "kuma mai zai hana ka canja abinda ka gani ko kuma ka gayamin wani abin na daban ko kuma ka rage? Zaka iya ganin Waƙar-maƙabarta aciki kaga baka buƙata ta kenan, wannan shayi ne kawai mara sikari bazai taɓa yiwuwa ba."
"Haka ne, baka da wani dalili da zaka amince min a yanzu amma kaje kayi tunani akan magana ta duk sanda kazo Babila ƙofarmu a buɗe take." Shaihu Babila ya juya zai tafi amma Armad ya sha gabansa.
"Zan bada wani abu amma banda wannan, suna kawai nake so."
Babila ya ja dogon numfashi ya kalli sama tsahon lokaci yana tunani. "Kasan ba ku kaɗai ne kuka ribaci ƙabilar Nára ba, a Farkon Lokaci Eyriyon ya ribaci ƙabilar Nára ya ƙarfafa jininsa. A Dogon Zaure ƙabilar Oduduwa suka ribaci ƙabilar Nára suka ƙarfafa jininsu. A Rawar Sani Bihanzin ya ribaci ƙabilar Nára ya samarda fasahar Jini-Uku. A wannan zamani kaima kabi sahun kakanka Eyriyon kana ribatar ƙabilar Nára. A tunanin ka mai yasa kake da Fasahar Mutuwa wadda hatta sarki Aldaima wanda yafi ka ƙarfin jini bashi da ita? A tunaninka tayaya jininka ya iya ɗaukar Waƙar-maƙabarta a dare ɗaya? A tunaninka tayaya Ikenga ya mallaki fasahar Shaibal'shisu wadda bata gidansu ba? Ƙarfin jinin Nára. Ƙabila wadda bata da ƙarfin faɗa amma duk wanda ya haɗa jini dasu sai yayi suna."
Armad baisan sanda ya cafi kwalar Babila yana haki ba domin ya fara gane inda labarin ya dosa. "Mai kake nufi?!"
Shaihu Babila yai ajiyar zuciya ya ce, "Nostaljiya Nára ita ce matar Fir'aunu na farko wanda hakan zai mayar da ita kakar Ikenga. Idan baka yadda ba ka tambayi Taidara ko kuma Zaikid."
"Amma kai cikakken maƙaryaci ne. Yaushe Nostaljiya ta taɓa zuwa sashin ikwatora? Yaushe harta auri kakan Ikenga!?"
Shaihu Babila ya ɗaga hannunsa cikin bayani. "Ah...baka gane ba, Uzzus, Rafiyan da Nara ai duk suna da sirrin mutuwa. Shi ne abinda yasa ake amfani dasu wajen fasahar Jini Uku. Dukkansu sun gagari mutuwa."
"Kana nufin kace an kashe ta a wancan zamanin ta dawo a wannan zamanin?"
"Kada ka manta baka biya komai ba nake baka wannan labari. Idan kana so kaji asalin labarin sai ka kawo wani abu a bakaci."
Babila ya miƙa hannunsa inda ɗaya daga cikin littafan dake gabansu ya taso ya tsaya akan iska a gaban Armad.
*Ƙabilun Farkon Lokaci*
"Ka karanta wannan a matsayin kyauta, akwai bayani akan Nára. Duk sanda ka shirya ka dawo ina nan akan baka ta."
Armad ya cije haƙoransa yana huci. Ba abun ya rufe Babila da duka ba. Bayan ɗan lokaci ya sakeshi ya fice daga ɗakin karatun. Ba tare da yiwa kowa sallama ba ya fice daga Babila ya nufi sashin Ikwatora.
***
Babi na 237-238
***
Garin Ja
Gefen Bangon Arewa
**
Gari mafi kusanci da Bangon Arewa akan doron ƙasa na shida shi ne wani gari mai suna Ja. Wannan gari yana cikin ƴantacciyar daula kuma yana da kusanci sosai da Bangon tayadda kana hangoshi tun daga tsakiyar garin.
Ja gari ne wanda aka gina shi da jan bulo. Asalin jan bulon anyi shi ne daga jar ƙasar dake bayan garin. Akwai wani makeken rami wanda aka samar dashi sabida haƙar ƙasar da akeyi. Akan hango wannan rami tun daga nisan tafiyar mako ɗaya akan ingarman doki.
A dai-dai wannan lokaci Armad yana hango ramin daga inda yake. A lokaci na farko tun sanda ya ɗauko hanyarsa ta komawa sashin ikwatora ya tsaya yana kallon wannan rami. Zurfinsa yakai yadda ba'a hango ƙarshensa ko kaɗan, faɗinsa kuma yafi girman garin sau uku. Saboda yanayi na damuna da kuma kusancin wannan rami da gari sai zaizayar ƙasa ta fara damun wannan gari, musamman sashin garin dake makwabtaka da ramin. Gashi kuma basu da matsera tunda a bayansu Bango ne.
Armad ya hangi wasu mutun bakwai sun tsaya a bakin ramin suna zana hatimin izza. Bayan sun gama sai wani ƙatoton allo na haske ya taso ya shiga tsakanin ramin da garin. Daga can bayan wannan mutane akwai wasu dakaru sama da mutane ɗari suna rangadin wannan katanga. Da yawansu masu gadin Bango ne suka gangaro.
Ana cikin haka Armad ya gilma ta saman wannan allon haske da niyyar wucewa ta saman garin amma yana gilmawa sai bangon ya fara girgiɗi yana rawa. Cikin daƙiƙa kaɗan ya daddare ya ɓace kamar ba'a taɓa yin sa ba. Armad bai ankare ba sai kawai ganin wannan mutun bakwai yayi sun sha gabansa. Armad ya ja ya tsaya yana kallonsu suna kallonsa.
"Mai jan gashi," inji na tsakiyar, "baka san an hana wucewa ta saman wannan gari ba. Gashi ka rusa mana abinda mukai sati muna ginawa."
Armad yaja numfashi a hankali, babu dalilin da zaisa ya firgita Sammai. "Ban sani ba kuyi haƙuri." Yana rufe baki ya juya zai wuce amma suka ƙara shan gabansa.
"Malan mai jan gashi baka gane girman laifinka ba..."
"Kaban'shísu!"
Armad ya ɓace daga inda yake bai bayyana a ko'ina ba sai a cikin garin. Babu wanda a cikinsu yaga kyallin Armad ko kuma inda yayi.
Armad ya bayyana a gefen wata kasuwa inda nan take ya nufi wani ƙaton shago na siyarda fura da nono. Ya nemi kujera ya zauna.
Wani mutun ya nufo inda yake ya miƙa masa takardar bayani akan abincin da ake siyarwa a wajen. Armad ya duba a hankali kafin ya zaɓa. Ya kula cewa mutumin yana ta kallon Miyurarsa da kuma kamanninsa amma Armad bai damu ba yaci gaba da zamansa yana shan iska.
Bayan ɗan lokaci mutumin ya dawo da kwaryar fura da kwanon nama a hannunsa. Yana ajiyewa Armad ya gano cewa an saka maganin bacci aciki amma ko a jikinsa, ya ɗaga furar ya kurɓa sannan ya bita da nama.
"Kai," Ya kira mai wajen, "a kawomin farin yaji."
Armad yana dangwalar yaji yana cin naman sannnan yana korawa da furar. A ɗaya hannunsa yana karanta littafin da Abarai ya bashi.
Can bayan ƴan daƙiƙu ya fara jin bacci sabida haka ya maida littafin aljihu ya gishingiɗa ya rufe ido.
***
Bayan tsahon lokaci ya farka ya ganshi acikin ɗakin kurkuku a ɗaure cikin farar laya.
"A...Armad..." Wata murya ta kira shi cikin ƙinƙina.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal!"
Asalin sunanta Shaldisa amma tun suna yara Armad yake tsokanarta yana ce mata Shal. Maimakon taji haushi daɗin sunan take ji. Sunyi makaranta tare da Armad kuma badan Zaikid ya hana ba da tare zasu zana jarabawar ɗaukan aikin Mayaƙan Ururu. Shaldisa ita kaɗai ta zana wannan jarabawa kuma taci wanda shi ne asalin rabuwarsu da Armad tun suna ƴan shekara tara. Aka kaita doron ƙasa na shida shi kuma Armad yaci gaba da rayuwarsa a doro na uku. Yau shekararsu sama da goma basu haɗu ba.
"Shal, anan kike aiki?"
"A kullum idan na ganka a jarida sai nayi mamaki, ban taɓa tunanin zaka juyawa Mayaƙan Ururu baya ba yadda kake son su."
Armad yai ajiyar zuciya, akwai wani lokaci da bashi da buri sai ya zama kwamanda a rundunar Mayaƙan Ururu. Badan komai ba saboda sulkensu mai sheƙi, baƙi da ratsin fari. Sulken da aka gina da ruwan yaƙutun-izza ziryan. A lokacin suna ƴan shekara bakwai Armad da Shaldisa sukan laɓe akan hanya su kalli kayan kwamandojin idan zasu wuce. Irin wannan kaya sune sak a jikin Shaldisa. Tun daga inda yake yana hango sheƙinsu da walwali irin na yaƙutu. Shaldisa ta ɗaure dogon gashinta inda ta fito dashi ta ƙasan hular sulken dake kanta.
"Kin cika burinki na zama kwamanda, dama wannan kaya kike son sawa tun kina ƙarama. Ko waiwayar garin Kanyu bakya yi."
"Kaima kana so. Ajiye wannan a gefe, ka ɗauki hanya kana so ka halaka kanka. Nice ta hannun daman Haruta Ururu kuma a yanzu idan nace ayi maka afuwa zaka dawo cikin mu zai yadda. Ka daina wannan rigimar... kaji Armadsan." A ƙarshe ta sassauta muryarta.
Maimakon ya bata amsa sai ya haɗe gira cikin tsokana ya ce, "Armadsan? Ki ka ce kin daina faɗar sunan nan."
Shal ta fashe da dariya a karo na farko, "kaima ai kace ka daina faɗar 'Shal'."
Bayan ɗan lokaci Shaldisa ta kori masu gadin dake wajen ta buɗe ƙofar kurkukun ta shiga ta zauna a kusa da Armad. Bayan ɗan lokaci ta ja gashin Armad a hankali sannan ta hura shi da iskar bakinta. "Yaushe gashinka ya koma ja. Kafi kyau a da. Kuma a yaushe ka daina ɗaura jan kyalle? Ka tuna sanda na kwance kyallen kana bacci a gidanmu?"
Maimakon ya bata amsa sai ya ƙara canja zancen ya ce, "ina mama?"
Shal ta ja dogon numfashi ta sunkui da kai, "hehe... har yanzu tana nan tana maganar auranmu dakai."
Armad ya fashe da dariya ya dubi Shal ya ce, "duk sanda tai maganar sai fuskarki tayi jajawur. Har yau na rasa kunya ce ko kuma yarinta?"
"Kaji dashi. Har Hidaya ka gayawa kana so na ai ta gayamin..." Nan take ta tsaya ta riƙe hannun Armad cikin kwalla. "Ya haƙurin Hidaya? Har gidanku naje nayi gaisuwa amma babu kowa sai ɗan tsoho. Nayi zaton zan samu dattijo Zaikid."
"Haƙuri da godiya."
Bayan ɗan lokaci Armad ya tsinke ankokin dake jikinsa ya cire Farar-layar ya miƙe. "Na gane yanayin-izzarki, daga yau zan ringa kawo miki ziyara."
Shal ta miƙe ta taka a hankali, idanu cike da kwalla, ta rungume Armad. "Ina kewar yarinta. Kowa acikinmu yayi nasa waje. Shekaru shida banga Shinal da Adam ba, Aji da Zabari duk sun zama ƴan kasuwa. Kada ku mutu ku barni ni kaɗai, ku bari na fara mutuwa, kunji."
Armad yai doguwar ajiyar zuciya sannan a wani salo na tsokana ya jada baya ya dube ta ya ce, "Shal, wai har yanzu kina so na?"
Kafin ya rufe baki ta dake shi da ƙafa a gabansa. Ba shiri cikin Armad ya ƙulle ya jada baya yana harararta. "Dama can kin saba, halinki ne."
"Kaima halinka ne."
Bayan tsahon lokaci Armad da Shal sukai sallama Armad ya ci gaba da tafiya izuwa kurkukun Bango.
***
Kamar yadda ya biyo ta Tsohuwar Daula a sanda zai taho haka yanzuma ya dawo ta ciki. Garin yana nan kamar yadda yake babu kowa acikinsa, duk mutanen ciki sun ɓoye. Armad ya ratsa garin a kan iska har zuwa ƙofar inda ya gangaro ya futo waje ta ƙofar daya shiga.
Kamar yadda ya tsammata dukkan jama'arsa na tsaye suna jiran dawowarsa. Akan gaba Inara ne da Babara da Nostaljiya da Lamarudu. Daga bayansu kuma sauran mabiya ne wanda ke tsaye cikin nishaɗi da murnar dawowarsa.
Abu na farko da Armad ya fara ganewa shi ne babu Nusi babu alamunta. Babu Cokali babu Iliyasisi. Nan take fuskarsa ta canja ya dubi Nostaljiya, Nostaljiya ta sunkui da kai. Ya dubi Babara wanda shima ya sunkui da kai. Inara da Lamarudu dama can kansu a sunkuye yake babu mai niyyar magana acikinsu.
Cikin sauri Armad ya wuce fadarsa ta dutse suka bi bayansa. Suna shiga Armad ya zauna akan karagarsa sannan ya umarci a rufe ƙofa.
Babara yai ƙarfin hali ya zube a ƙas ya kwashe dukkan abinda ya faru Nusi ta tafi ya gayawa Armad tun daga zuwan sarki Ƙaraiƙisu har ƙarshe.
"Sannan daga baya Cokali da Iliyasisi suka bi bayanta." Babara ya ƙarasa bayaninsa.
Armad yai ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye. Babu buƙatar yayi musu faɗa akan abinda basu da iko. Yasan cewa babu wanda acikinsu zai iya tunkarar Ƙaraiƙisu ko kuma ya hana Nusi tafiya.
"Nayi tunanin zan huta kwana biyu kafin na ƙara shiga wani yaƙin." Inji Armad.
Nostaljiya ta tari gabansa da sauri ta ce, "akwai matsala, sarki Armad. LOKACI YA CANJA."
Armad ya kalleta cikin mamaki. Abu na farko da yazo ransa shi ne 'kishi kumallon mata' amma yai shiru ya bata dama tayi bayani. A zahiri ita kanta bata san ta ina zata yi masa bayani ba saboda haka ta dubi Babara ya kawo mata agaji.
Babara ya numfasa ya ce, "haƙiƙa LOKACI YA CANJA. Dani da sarauniya Nostaljiya mu kaɗai muka ankare da canjin amma lallai lokaci ya canja."
Armad ya daka musu tsawa a fusace. "Wai mai kuke nufi ne?! Kamar yaya LOKACI YA CANJA??!!"
Nostaljiya ta girgiza kai tare da buɗe baki zatai bayani amma kalmonin suka maƙale a wuyanta ta kasa cewa komai. Shima Babara yayi ƙoƙarin bayani amma ya kasa. Ga dukkan alamu Inara da Lamarudu basu da masaniya akan abinda ke faruwa domin suma neman bayani suke yi.
Bayan tsahon lokaci ana kai-komo da dambarwa: Nostaljiya da Babara sun kasa bayani su kuma su Armad sun dage sai anyi musu bayani. Daga ƙarshe Armad ya kai zuciya nesa ya wuce turakarsa. Yana zuwa ya hau kan ƙatoton gadon da aka tanadar masa na alfarma ya hau nazari. Lalle akwai wani mashahurin abu dake gudana wanda Babara da Nostaljiya ne kaɗai suka sani amma kuma suna tsoron faɗa, ko kuma baza su iya faɗa ba.
Abubuwa da dama suka gilma ta kwakwalwarsa. Shin Nusi ce ta gamu da wata lalura? Wani ne ya mutu? Sarkin-sarki ce ta kawo hari? Bihanzin ne ya kawo farmaki? Sai dai kuma amma duk wannan abubuwan basu yi kama da bayanin jimlar 'lokaci ya canja' ba. Bayan ƴan daƙiƙu Armad ya ɗakko kalmar ya fara yi mata 'fassara mara ƴanci'. Shin lokaci ne ya ƙaru ko kuma ya ragu. Misali ace awa ɗaya ta dawo awa biyu ko kuma uku. A labarun daya karanta yana yaro akwai bayanai akan wasu ƙofofin Eycigan wanda suke ƙara yawan lokaci; awa goma acikin wannan ƙofofi bata fi awa ɗaya ba a waje. Da dama daga cikin ƴaƴan sarakunan wancan lokaci sukan shiga cikin wannan ƙofofi domin koyon horo kala-kala acikin ƙaramin lokaci.
Amma irin wannan ƙofofi na Eycigan a labari kaɗai ya taɓa jinsu, babu su a gaske.
Yana cikin tunani sai Nostaljiya ta shigo. Fuskarta akwai yanayi na kokwanto da wasu-wasi irin wanda a fasahar Wasu-wasi kaɗai ake gani. Bata ce masa komai ba ta kwanta a gefensa tare da yin fulo dashi. Armad ya ɗago kai ya kalleta na ƴan daƙiƙu kafin daga bisani ya koma aiki. Idan baza su gaya masa ba shi zai gano da kansa.
A lokacin isha ta kawo kai, ba jimawa gari yai tsit dare ya nutsa, taurari suka bayyana a sararin samaniya. Abinka da wanda yai kwana da kwanaki bai rintsa ba, bai san sanda bacci ya ɗauke shi ba. Nostaljiya ta tashi zaune ta ɗora kansa akan cinyarta sannan ta ɗakko muhuci ta hau fiffita.
A haka suka kwana cir ko rintsawa batai ba. Ketowar alfijir kedawuya, ƙarfe huɗu saura minti takwas. Komai da kowa ya tsaya cak. Da mai bacci da mai aiki da mai tafiya da mai hira da mai lissafi da mai fiffita kowa ya tsaya.
***
Armad ya farka ya ganshi acikin ɗakin kurkuku a ɗaure cikin farar laya.
"A...Armad..." Wata murya ta kira shi cikin ƙinƙina.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
Nan take kalmomin suka maƙale a maƙogaronsa. Irin wannan yanayin sak shi ne abinda ya faru jiya a lokacin da yake dawowa gida.
"Armadsan..." Inji Shal.
Armad ya haɗe gira. Komai da komai maimaita kansa yake kamar yadda ya faru a baya. Shin ranar aka dawo da ita baya ko kuma shi ne ya dawo baya. Domin yana tuno komawarsa gida da bayanin su Nostaljiya akan cewa Lokaci ya Canja. Wai shin dama abinda suke nufi kenan da lokaci ya canja? To amma maike faruwa?
Shal ta fashe da dariya a karo na farko, "naga ka haɗe gira, idan baka so naci gaba da cewa Armadsan to ka daina cewa 'Shal'."
Hirar ta ci gaba kamar yadda Armad ya santa a jiya. Bayan ɗan lokaci Armad ya zabura yai sallama da Shaldisa a gaggauce ya nufi kurkukun bango. Nostaljiya da Babara su kaɗai suke da cikakken bayanin mai ke faruwa. Shin wace irin canjawa lokaci yayi?!
***
Babi na 239-240
***
Kamar yadda ya biyo ta Tsohuwar Daula a jiya haka yanzuma ya dawo ta ciki. Garin yana nan kamar yadda yake babu kowa acikinsa, duk mutanen ciki sun ɓoye. Armad ya ratsa garin a kan iska har zuwa ƙofar inda ya gangaro ya futo waje ta ƙofar daya shiga.
Kamar jiya dukkan jama'arsa na tsaye suna jiran dawowarsa. Akan gaba Inara ne da Babara da Nostaljiya da Lamarudu. Daga bayansu kuma sauran mabiya ne wanda ke tsaye cikin nishaɗi da murnar dawowarsa. Babu wanda acikinsu ya san anyi irin wannan rana da lokaci sak a jiya sai Babara da Nostaljiya.
Armad ya wuce fada suka bishi a baya. Suna zuwa ya sallami kowa banda Babara da Nostaljiya. Inara yai ƙoƙarin tsayawa amma daga bisani yai ajiyar zuciya ya fice. Har yanzu baya son yayi nisa da Armad.
Babara ne ya fara magana. "Kullum ta ALLAH da asubahin fari ƙarfe shida sai na farka a dai-dai cikin ƙofar Tsohuwar daula, dai-dai wajenda nake a safiyar jiya."
Nostaljiya tai ajiyar zuciya ta ce, "kullum sai na farka a banɗaki ina wanka ko a ina na kwanta kuwa."
Armad ya haɗe gira, ga dukkan alamun wani babban al'amari wanda zai iya rikita duniya ya afku. "Kwana nawa kenan?"
Babara ya kalli Nostaljiya suka ƙara yin ajiyar zuciya. "Ni kwana tara, Babara kuma kwana shida. Da farko ni na fara gano cewa Lokaci ya Canja, sannan bayan kwana biyu sai Babara. Sai kuma kai..."
Maimakon amsar Nostaljiya ta samar masa da nutsuwa sai ƙara ɗaure masa kai tayi. Akwai tambayoyi marasa iyaka. Shin mai ya jawo wannan Canji? Ko kuma ace wane ne ya jawo? Shin duk duniya abin ya shafa ko kuma wasu wajaje ne ƙaiyadaddu? Kwana ɗaya kafin wannan rana Armad yana Babila, kuma ga dukkan alamu canjin bai shafi Babila ba domin kuwa babu cikas a gasar da akayi....
Ehmmm! Armad yai ajiyar zuciya yana tunano fuskar ragowar mutanen dake rundunarsa. Babu wanda acikinsu yake da masaniya akan yana maimaita rana. Wanda hakan ke nuna cewa wataƙila ita kanta gasar cin ruhin Deba an maimaita ta sau da yawa ba tare da ya sani ba. Akwai matuƙar kokwanto acikin alamuran. Babu wanda hankalinsa bazai gagarumin tashi ba idan ya gano cewa yana maimaita rana ɗaya a rayuwarsa ba tare da ya sani ba.
"Ace wani ne ya samarda wannan Canjin Lokaci to saboda me? Idan kuma ba kowa bane to mai ya faru? Mutun ɗaya dana sani yana iya sarrafa Lokaci shi ne Ikenga, kuma shima yana cikin gasar. Sai dai ban sani ba ko tun a lokacin yana sane da Canjin." Inji Armad.
Nostaljiya tayi ajiyar zuciya ta ce, "wai kana nufin Ikenga ne ya aikata wannan abu?"
Armad ya girgiza kai, "a'a fa, har yanzu babu tabbas, zata iya yiwuwa shi ne ko kuma ba shi bane. Zata iya yiwuwa ba aikin mutun bane, domin kuwa ban taɓa gani ko jin irin wannan gagarumar fasaha ba ko a cikin Littafin-takobi."
Babara ya gyaɗa kai cikin amincewa ya ce, "eh na yadda to amma mu ɗauki mafi munin sakamako, ace Ikenga ne ya samarda wannan fasaha kuma burinsa ya mulki sashin ikwatora da duk wani wanda ke ciki. Meye manufarsa?"
Armad ya ƙunduma cikin nazari. A duk tsahon lokacin da yasan Ikenga har yau yana jin bai gane waye Ikenga ba. Hasalima ya gano cewa a duk fafatawarsu ta baya da mutun-mutumi suke yi. Waishin waye Ikenga? Wannan tambaya ita tasa Armad ya ji cewar wataƙila zata iya yiwuwa Ikenga ne sanadiyyar abinda ke faruwa. To amma kuma idan shi ne to meye manufarsa tayin hakan?
"Ya samu lokacin horo." Armad ya amsawa kansa a fili. "Kuyi tunani, idan aka ce kullum zakai ta maimaita rana guda ɗaya tak a rayuwarka. Kaga baza ka tsufa ba. Idan kasan kana maimaita wannan rana guda ɗaya zaka yi ƙoƙari ka samu horo aciki har sai inda ƙarfinkaya ƙare. A duk lokacinda ka fito..."
Babara ya tari numfashinsa da sauri ya ce, "nayi ƙoƙarin yin hakan a rana ta uku amma duk wata fasaha daka koya a banza take. Ana juyawa zata tafi, sai ka sake sabuwa. Abu ɗaya kacal da muke riƙewa shi ne ilmin mu na kasancewar Canjin amma komai tafiya yake. Waye yasan daɗewar da akai ana cikin wannan KURKUKUN LOKACIN kafin ma mu ankara. Akwai yiwuwar fasahar ta daɗe tsahon shekaru, kuma mune sai a yanzu muka tsinkaye da ita."
"Idan har baza mu koyi fasaha acikinta ba to ta zama Kurkuku, kuma ya zama wajibi mu tarwatsa ta." Inji Armad.
"To amma tayaya? Har yanzu bamu da masaniya akan abinda ya jawo fasahar, bamu san yaya fasahar take ba, bamu san da ina da ina ne suka kamu ba, to tayaya zamu lalata ta?" Inji Nostaljiya.
Armad ya miƙe tsaye cikin nutsuwa ya ce, "to ai munsan akwai ta, kuma munsan tana aiki acikin kurkukun bango, munsan cewa duk bayan awa ashirin da huɗu ake juyawa, sannan kuma idan an juya ana barin mu da ilmin mu, sabida haka sai muyi amfani da abinda muka sani wajen gano abinda bamu sani ba. Babban shirin shi ne mu gano mai yasa mu muka san da Canjin amma sauran basu sani ba. Mai yasa muka gano ta a lokaci daban-daban? Shin akwai yiwuwar wasu su gano anan gaba? Iya yawan mutanen da suka sani iya damar mu ta gano abinda ke faruwa, saboda haka tanan zamu fara."
Nostaljiya tayi ajiyar zuciya. Abu mai kamar wuya yiwa jaki kwalliya. Su kansu basu san tayaya suka gano Canjin Lokacin ba saboda haka bata da masaniya akan yadda za'a gano abin. "Ta ina za'a fara?"
Armad ya dubi Babara ya ce, "har yau tambayar da ban taɓa yi maka ba ita ce meye tsarin fasahar ka? A ina ka kware? Nasan akwai al'amarin Duba da buga ƙasa amma kuma wannan baiyi kama da fasahar Hari ba, a wane fannin ka kware?"
Babara yai murmushi ya ce, "zanso sarki Armad ya ɗan bani lokaci yaga fasaha ta a fagen daga. A yanzu dai na kware a harkar duba da gano abinda ya faru da wanda zai faru."
"Kamar fasahar Saɓani kenan?"
"Eh... kamar ita. Amma kuma ina da sandar tsafi wadda nake iya sarrafawa duk yadda naso. Kuma anan sirrin Hari na yake."
Nostaljiya ta dubi Babara ta ce, "to mai zai hana ka Duba mana me ake ciki ko ma ga waye ya samarda wannan fasaha."
"Kina tunanin banyi hakan ba? Tuni na duba duk wata tauraruwa amma babu bayani. Duk wani abu daya faru kafin yau ya goge, hatta gasar ku ta cin Ruhin Deba. Sannan kuma ba'a ganin komai a abinda zai faru gobe, kai kace an yanke samuwa da faruwa. Da farko kafin na gano Canjin nayi tunanin ƙiyama ce zata tashi."
Armad najin bayanin ya rankaya izuwa cikin duniyar Negrinkinsa ba tare da ya ce musu komai ba. Ai kuwa babu kowa aciki, babu Hidaya babu Ƙaizadu babu Hasanu babu Randuil. Tabbas akwai babbar hatsaniya wadda ta girmi ƙaramin lissafi.
Yana fitowa yayi musu bayani. Abin mamakin shi ne suna sane da duk abinda ya faru a gasar Jinzidal domin kuwa basu manta abinda suka gani a hoton bidiyon ba. Lallai akwai rikita-rikita. Domin kuwa idan suna iya tunawa to lallai anyi gasar Deba to amma kuma idan anyi to ina mutanen daya ajiye tare da ruhin Hidaya suka tafi?
Dukkansu suka nutsa cikin tunanin kowa yana tunanin mafita. Bayan ɗan lokaci Nostaljiya ta numfasa ta dubi Babara ta ce, "ina ganin ina da mafita, ni bani da ƙarfin fasaha to amma jini na yana da ƙarfi. Yawancin fasaharku ta Duba tana amfani da surkulle ne da kayayyakin sihiri. Idan na ɗisa maka jini na akan kayayyakin ka na duba ina da tabbas ƙarfin fasahar zai ƙaru da adadi da dama. Idan ka shirya sai mu gwada. Wataƙila ka gano mana wani abun."
Kafin Babara ya amince sai da ya dubi Armad yana neman umarni. Armad ya gyaɗa kai alamun amincewa.
Babara ya daki iska da sandarsa inda wani ɗan sumulmulallen dutse ya bayyana akan iska. Babara an kware a harkar duba, sabida haka da dutse kaɗai yake amfani saɓanin sauran masu Duba da zaka gansu cikin tarukuce kamar mahaukata. Babara gajeren tsoho ne mai yawan furfura. Kuma tun sanda yayiwa Armad mubayi'a ya aske gemunsa dubuzu-dubuzun gashin fuskarsa. A har kullum yakan saka ƴar shara doguwa ya rataye sandar tsafinsa a kafaɗa.
Nostaljiya tana ƙoƙarin yanka hannunta Armad ya bayyana a kusa da ita ya kirawo wasu ɗalasimai daga cikin Waƙar-maƙabarta.
"Fasahar Kashe-zafi."
Nan take dai-dai hannunta wajenda Armad ke riƙe dashi ya dusashe ya daina jin komai kamar anyi masa allurar kashe zafi. Sannan cikin soyayya da kyautayi Armad yai amfani da walƙiya ya yanka tafin hannunta daga gefe ɗan kaɗan. Ya ɗisa jinin akan dutsen sarkin Duba Babara.
Ɓangaren Rafiyan Nazára(yarima Niyashi)
A can doron ƙasa na shida sashin kudu a wani gari mai suna Bílas taro yai taro a ƙofar babbar laburarin wannan gari. Mutane daga kowanne sashi na garin sun zo domin jin tattaunawar da jaridar aminiya zatai da yarima Niyashi. Tun kwanaki huɗu da suka wuce labari yake ta kewayawa akan wannan tattaunawa. Da dama sun yadda cewa za'a tattauna batutuwa akan tsohuwar daular Banfiriya, daular sarki Daljari mahaifin yarima Niyashi. Akwai kuma batutuwa akan manyan jarumai irinsu Armad wanda kuɗinsu yai sama sosai.
A dai-dai wannan lokaci da jama'a ke ta shewa yarima Niyashi na zaune kan kujera acikin wani ɗaki dake laburarin. Maimakon jan gashi da aka san shi dashi a yanzu ya koma baƙi. Sannan kuma ya yanke shi ya rage masa tsayi. Fuskarsa tana nan da yarintar ta amma kuma duk da haka kana ganin idanunsa kasan akwai nutsuwa aciki da ilmi aciki. Ƴar rigar dake jikinsa ta saƙa ce da ɗan dogon wando fari.
Ɓangaren da yake zaune babu mutane aciki sosai, ɗakin da yake ciki an killace shi a can sama a wata ƙurya keɓantacciya. Tunda garin Bilas ɗaya ne daga cikin garuruwan da ada suke ƙarƙashin mulkin Rafiyawa kafin Bihanzin yaci su da yaƙi, saboda haka Daljari yana da alfarma a wajen.
Tsahon lokaci Nazara ya daɗe yana kallon rufin ɗakin wanda aka yishi da farar azara, bayan ɗan lokaci fararen idanunsa suka bar kan rufin suka sakko kan teburin dake gabansa. Shi kansa teburin yakai faɗin rabin ɗakin. Akansa akwai hotunan mutun uku wanda suke cikin mutun bakwai da Majalisin Ururu suka ƙarawa kuɗi a satin. A jikin kowanne hoto daga ƙasa akwai kuɗin sa aka sakawa kowanne.
Hoto na farko hoton Armad ne da zanen kuɗi Ayrid miliyan ɗari tara da hamsin (A950,000,000), sai kuma hoto na biyu na Ikenga da zanen kuɗi Ayrid miliyan ɗari tara da tamanin da takwas (A988,000,000). Hoto na uku shi ne hoton Nusi da zanen kuɗi Ayrid miliyan ɗari huɗu (A 1.2 billion).
A gaban hotunan akwai sabon littafi wanda babu komai acikinsa sai jajayen takardu bugun Farkon Lokaci.
Bayan dogon nazari Nazára yai ajiyar zuciya tare da buɗe littafin. Ya ɗora alƙalaminsa a shafin farko ya fara rubuta ɗumɓin abubuwan da zai gayawa mutanen dake jiransa a waje.
Ikenga O. Bayajidda
Dogon bincike da nazari ya nuna cewa an haifi Ikenga a garin Hurairah dake sashin ikwatora saɓanin yadda ake tunanin an haifeshi a garin Jíha. Binciken ya nuna cewa ba'a shekarar 1833 aka haifi Ikenga ba, an haifeshi a Shekarar Miciji 122BA. Babbar tambayar anan ita ce ya akai aka ga Ikenga a jariri a garin Jíha a shekarar 1833? Menene ma'anar jinin da aka bawa Ikenga na magajin wilbafos a lokacin yana jariri? Idan ba Shísu O Bayajidda ne asalin mahaifin Ikenga ba to waye? Wacece mahaifiyar Ikenga? Menene alaƙar Ikenga da gidan Ururu? Menene alaƙar Ikenga da gidan Wilbafos? Menene alaƙar Ikenga da gidan Bayajidda? Wannan sune kaɗan daga cikin tambayoyin da zamu amsa dangane da Ikenga.
Nusi Kil'zanki
Dogon bincike da nazari ya nuna ita ma Nusi an haifeta ne a Shekarar Miciji (122 Bayan Amri). Meye dalilin da yasa na ceci Nusi a lokacin tana ƴarinya? Shin meye alaƙa ta da ita? Kaɗan kenan daga cikin tambayoyin da zan amsa akan Nusi Kil'zanki amma kafin nan ina so na bayyana cewa Hidaya bata da alaƙa da zaman Nusi sarauniya a sashin Ikwatora. Dalilin da yasa Nusi ta zama sarauniya shi ne dalilin da yasa tafi Armad da Ikenga yawan kuɗi. Ko menene dalili?
Armad Wilbafos
Abu mafi girma da nake son na bayyana a yau shi ne Armad Wilbafos ba ɗan cikin FATIMA BAYAJIDDA BANE, BA ƊAN TAIDARA BANE, KUMA BA JIKAN FARFESA ZAIKID BANE. Hakan yake nuna cewa Hidaya Wilbafos ba yayarsa ba ce, basu haɗa ciki ba.
A yau zan baku hujjoji bayyanannu akan dukkan abubuwan dana faɗa. Amma kafin muje ga wannan ina so na bayyana muku cewa nima ba ɗan cikin sarki Daljari bane....
Haka dai Nazara yaci gaba da rubutu kafin daga bisani ya rufe littafin ya fito waje domin fuskantar wanda suke jiransa. Ko me da me Niyashi yake niyyar faɗawa duniya a yau?
***
Comments
Post a Comment