Armad bai saurari abinda Zaikid yake faɗa masa ba, ya taka ya koma wajen gadon aba'in. Ganin dawowarsa Haruta ya kyalkyala dariya. "Daka sani kaji abinda kakan ka ya faɗa maka baka dawo ba."
Haruta ya ɗaga ƙafa ya ƙara yin cilli dashi. Zaikid ya ƙara maimaita masa irin maganar daya faɗa a baya amma Armad baiji ba, ya ƙara dawowa. Haruta ya ƙara buga shi. Armad ya ƙara dawowa. Kololuwar taurin kai da kafiya irin ta mutanen farko. Tuni Armad ya daina jin tsoron mutuwa ko rauni, indai yasa abu a gabansa tofa sai ya cin masa. Haka ya ringa komawa Haruta yana cilli dashi har saida takai-ta-kawo baya iya miƙewa ya tsaya akan ƙafafunsa. Da rarrafe ya ƙara dawowa.
A nasa ɓangaren kamar yadda Armad bai gaji ba, haka shima Haruta bai gaji ba. Sai da akai haka sau goma.
A zuwa na goma sha ɗaya Haruta ya ɗaga takobinsa ya cake ta a ƙirjin Armad. Jini ya fara malala. Ya zare takobin zai tsinkewa Armad kai amma Zaikid yayi kururuwa yayi tsalle ya ture Armad gefe takobin ta dira a kafaɗarsa. Jini yayi feshi sama. Haruta yayi tsaki ya sa ƙafa ya ture Zaikid gefe sannan ya taka a hankali inda Armad yake kwance yana kakarin mutuwa. Yana zuwa ya ɗaga takobinsa da hannu ɗaya ya saukar da ita a wuyan Armad. Babu wani tauri ko kafi da yake iya tare wannan takobi. Yadda zata yanka albasa haka zata yanka ƙashi. Kan Armad ya gutsire daga gangar jikinsa ya faɗi ƙasa. Haruta ya goge takobinsa a jikin gangar jikin Armad sannan ya maida ita cikin kufen ta. Yasa ƙafa ya tura gangar jikin Armad ƙasa. Duk abinda ke faruwa da Shata da sadaukan dake fafatawa hankalin su nakai kuma suna gani amma babu wanda acikinsu yayi ƙoƙarin yin wani abu.
Yana gamawa da Armad ya juyo kan Zaikid wanda ke kwance hawaye yana zuba daga idonsa. Ya daga takobinsa ya kawo sara da niyar datse wa Zaikid kai. Zaikid yana kwance bai motsa ba. Sai da takobin tazo gaf da wuyansa sannan ta tsaya cak akan iska. Abin mamaki Haruta ƙoƙari yake ya danna takobin amma taƙi motsawa. Yana cikin kiki-kaka da takobi yaji daga bayansa anyi masa magana. Ya gane muryar amma kuma bai taɓa tsammanin ƙara jinta ba. Dolensa ya waiwaya baya inda yaji muryar. Armad ne tsaye ya riƙe hannun takobinsa ta baya. Ya juya ya kalli inda ya tura gangar jikin Armad. Abin mamaki tana nan kamar yadda ya barta ɗazu, kan Armad daya guntule shima yana nan a ƙasa inda ya barshi. Kafin ya gama fahimtar abinda ke faruwa Armad ya dunkule hannunsa ya saukar masa da hannun aradu. Haruta ya saki takobinsa yayi tsalle gefe domin ya kaucewa walkiyar, amma a lokacin Saif-Al-Barzak ta bayyana ta sama ta kawo masa sara.
"Tuladan-nan-Galak!"
Ɗalasimin yana barin bakinsa tambarin miyurarsa ya bayyana akan iska yayi kan Haruta. Idan ka hangi Haruta daga nesa zaka ga bashi da hanyar tsira: ta sama Saif-Al-Barzak, ta gabansa Hannun-Aradun Armad da kuma miyura. Amma saboda kwarewa ta tsohon ma'aboci izza a sama akan iska Haruta ya juya sannan ya dawo da baya ya kaucewa hare-haren. Kafin ya dira miyurar ta ɓace ta bayyana a ƙasansa dai-dai inda yake kokarin saka ƙafa. Dole Haruta ya dira akanta. Nan take izzar sa tayi kasa, rubuce-rubucen dake jikin miyurar suka zagaye jikinsa suka ɗaureshi kamar igiya. A dai-dai wannan ɗan taƙin walkiyar Armad da takobin Saif-Al-Barzak suka sauka akansa. Armad bai jira ya ga sakamakon hare-haren ba ya ƙara kiran takobin Wilbafos ya afkawa Haruta da sara da suka da fasahar Ɗorawa Abada.
Kamar duk wannan bai isa ba ya ƙara kiran wani ɗalasimin.
"Gidan gizo-gizo!"
Koda kiran wannan ɗalasimi sai zarurruka suka bayyana a saman Haruta suka samar da saƙa irin ta gizo-gizo.
"Zaren Babbar Mutuwa!"
Zarurrukan suka juye izuwa jajaye, Negrinkin Armad ta fito ta rufe
su, sannan a wani salo na zafin nama zarurrukan suka sakko ƙasa suka ƙara ɗaure Haruta tamau.
Armad ya koma yana jira ƙura ta lafa domin yaga halin da Haruta yake ciki da kuma abinda hare-haren sa suka aikata. Zaka iya cewa wannan sune mafi girman hare-haren da Armad yake dasu. Domin idan ka dakko fasahar Tuladan-nan-Galak za kaga cewa gaba ki ɗaya miyurar Armad take fitowa da ita ta ɗaure jikin mutum ta zuƙe izzarsa baki ɗaya sannan ta bawa Armad. Fasahar Saif-Al-Barzak aure ne tsakanin Armad da takobi. Takobi mafi sauri da kaifi, takobi wadda ya gada acikin littafin-takobi, takobi wadda shi kansa har yanzu bai san iyakacin ƙarfinta ba. Duk wani lissafi ya nuna cewa kaifin takobin Saif-Al-Barzak zata iya tare dauwamammen sara bama takobin Haruta ba. Zaiyi wuya ace Haruta ya tsallake daga sharrin ta. A lokaci guda kuma ga hannun aradu ya tare masa ƙofar tsira. Ga gidan gizo-gizo na Zaren Babbar Mutuwa wanda zai zuƙe izzarsa ya kuma zuke jikinsa izuwa duniyar Negrinkin Armad. Ga Ɗorawa Abada. Hakan yasa Armad kawai jira yake ƙura ta lafa domin yaga nasarar da yayi.
Ba jimawa ƙura ta lafa inda surar Haruta ta bayyana. Kayan jikinsa sun ƙone a wajaje da dama amma kuma banda wannan babu alamun rauni a tattare da shi. A wannan lokaci Armad ya tabbatar da cewa acikin gadar zare akwai wani sirri da yake rage ƙarfin fasaharsa sannan kuma ya ƙara ƙarfin fasahar Haruta, kamar yadda Shata ya bayyana masa a baya. Kuma dama ya gaya masa gadar zare wani yanki ne daga cikin duniyar Kuyurussa'ayi. Hanya ɗaya da zaiyi nasara shi ne yayi amfani da Negrinkinsa ya karya wannan duniyar kamar yadda yayi a baya. Amma kuma matsalar ita ce Haruta bazai bashi isasshen lokacin da zai tara Negrinkinsa har ya maimata abinda yayi a baya ba. Dole ne yana buƙatar wanda zai taimaka masa ya bashi lokacin daya ke bukata. Koda wannan tunani ya zo masa sai ya juya ya kalli Shata. Har yanzu ana tsaka da fafatawa kuma baya tunanin nan kusa faɗan zai ƙare. Ya juyo wajen Zaikid wanda ke zaune cikin ankwa. Indai zai samu ya tsinke ankwar to ya gama da Haruta.
Yana cikin wannan tunani Haruta ya kawo masa sara, ya kauce sannan ya mayar masa. Suka kaure da azababben faɗa. Cikin ƴan dakiku sunyi musayar sara sama da talatin. Duk wani harin Armad yana tare da Ɗorawa Abada. Amma wani abin mamaki Haruta ko a jikinsa. Gashi dai takobinsa babu wata alamar izza ta musamman a jikinta amma kuma a haka yake tare takobin Armad.
Bayan ɗan lokaci su kayi tsalle suka rabu suna kallon juna kowa yana auna ƙarfin kowa.
"Armad," inji Haruta. "Kasan cewa akwai wasu mutane da zaka gamu dasu a rayuwa komai iyakacin ƙoƙarinka da dagewarka baza ka taɓa cin musu ba? Ko a makaranta idan ka tara yara sama da goma sai ka sami wani wanda yafi kowa ƙoƙari, sannan kuma sai ka samu wanda yake ƙoƙarin ya cin masa amma kuma komai zaiyi bazai taba cin masa ba. Toh, Armad, kamar haka misalinka yake dani. Koda zaka tattaro duk wata fasaha da take gidan Wilbafos ba zaka samu nasara akai na ba."
Armad yayi murmushi. "Lokaci ne kawai zai nuna gaskiyar maganar ka. Lokaci ne zai nuna waye zai kasance a ƙasa a ƙarshen wannan fafatawa. Amma ka daina zancen ƙoƙari bayan ka laɓe anan ana ƙara maka ƙarfi."
"Toh shikenan," inji Haruta. "Bari na janyo lokacin na nuna maka abinda zai faru."
Haruta ya ɗaga hannayensa sama ya yarda takobinsa ya kira ɗalasimi. "Duniyar Takobi!"
Yana rufe bakinsa filin dake tsakaninsa da Armad ya fara haske, wani layi ya bayyana a ɓangaren hagunsu da damansu. Hasken yana ƙaruwa abinda yake cikinsa yana bayyana. Bayan dakika goma alamun takobi ya fara bayyana acikin hasken. Bayan dakika ashirin takubba hamsin sun bayyana. Bayan dakika talatin takubba ɗari sun bayyana. Haruta ya nuna Armad da hannayensa guda biyu. Kamar wanda yake bawa takubban umarni gaba dayansu suka tashi sama a lokaci guda sukayi kan Armad. Kafin su ƙarasa ko wacce takobi ta rabe zuwa biyu, sannan ko wacce ta ƙara rabewa zuwa huɗu, sannan suka ƙara rabewa. Tun Armad yana iya lissafi har ya kasa. Kafin su ƙarasa ko wacce ta kama da wuta lamarinda ya ƙara musu wani mahaukacin sauri. Kamar masifar bata isa haka ba, Haruta ya daki ƙasa da ƙafarsa, nan take ƙasar ta juye izuwa takubba. Takubba ta gaba, takubba ta ƙasa. Wasu takubban suka zagaye suka dawo ta baya, wasu kuma ta gefe. Ta ko'ina an kewaye shi. Kafin ya motsa takubban sun haike masa. Wasu suka cake shi, wasu kuma su kayi bindiga dashi. Kafin kace meye wannan Armad yayi daga-daga.
Haruta ya juya ɓangaren Zaikid. "Farfesa, baka bawa yaron nan horo daya kamata ba."
Zaikid yayi murmushi. "Ni kuwa ina ganin kai ne baka samu horon daya kamata ba, Haruta."
Haruta ya haɗe gira. "Ko?"
"Eh mana," inji Zaikid. "Domin har yanzu baka gane cewa da mutum-mutumi kake faɗa ba."
Haruta ya yamutsa fuska. Shi dai yasan akwai wani abu wanda ba dai-dai ba a tattare da Armad ɗin da yake faɗa dashi, toh amma kuma ya kasa gane menene. "Haba, Farfesa, bafa yau muka fara harkan nan ba, nasan mutum-mutumi. Kana gayamin akwai wata fasahar mutum-mutumi a gidan Wilbafos da bazan iya ganewa ba?"
Zaikid yaja ankokin dake jikinsa ya gyara zama ya fuskanci Haruta. "Girman kai shi ne zai kashe ka. A kullum kana ganin kasan ko wacce fasaha bayan kuma a zahiri ba haka bane."
"Ƙarya kake, Farfesa, wannan ba fasahar mutum-mutumi bace. Domin kuwa idan fasahar mutum-mutumi ce idanuwa zasu gane ta."
"Ruwan ka; ko ka yarda ko kada ka yarda."
Duk da cewa Haruta bai gama yarda da abinda Zaikid ya faɗa ba to amma kuma bashi da wani bayani akan dalilin da yasa yake ta kashe Armad yana dawowa. To wai idan mutum-mutumi ne ina Armad ɗin gaskiyar yake? Yaushe, kuma a ina yake samar da mutum-mutumin ba tare da Haruta ya gani ba?
Yana cikin wannan tunani Armad ya ƙara bayyana a saman kansa ya kawo masa suka, Haruta ya kauce amma duk da haka sai da takobin ta gogi gefen fuskarsa. Nan fa fafatawa ta dawo sabuwa. Armad bashi da niyar yiwa Haruta bayanin mai yake faruwa saɓanin Zaikid. Bayan kimanin minti biyar ana wannan fafatawa, Haruta ya ƙara kirawo Duniyar Takobi ya halaka Armad.
Abu kamar wasa, daga ɗaya zuwa biyu, daga biyu zuwa uku, a haka har saida Haruta ya kashe Armad sau tara, amma Armad yana dawowa. A lokacin ya tabbatar da cewa mutum-mutumi yake faɗa dashi. Babbar tambayar itace ina Armad ɗin gaskiyar yake?
Watakila amsar tambayar tana wajen da Shata yake tsaye. Idan ka lura za kaga wani Armad ɗin a tsaye yana yiwa shata magana a yayin da shi kuma Haruta yake faɗa da wani Armad ɗin. Lamarin daya ƙara tabbatar wa da Haruta cewa da mutum-mutumi yake faɗa. Kafin ya yanke shawarar mai zaiyi Armad da Shata sun haɗa ƙarfi-da-ƙarfe sun saukarwa da rundunar azaba. Cikin kankanin lokaci suka gama da rundunar sannan suka rankayo suka dawo wajen da Haruta yake faɗa da ɗaya Armad ɗin. Suna ƙarasowa suka shiga fadan. Armad guda biyu da Shata, shi kuma Haruta shi kadai. Shata ya ɗakko sabuwar garaya daga cikin jakar tsafinsa ya fara kaɗawa. Armad ɗaya yaci gaba da faɗa da Haruta. Ɗayan kuma ya nemi waje ya koma gefe ya tankwashe ƙafa ya fara tara Negrinki.
Ko da ganin haka sai Haruta ya gane abinda suke shirin yi. Cikin sauri ya ƙara kiran Duniyar Takobi domin ya halakasu a lokaci guda. Amma kafin hakan ta faru yawan Negrinkin Armad takai matakin da zai iya janyo duniyarsa ta shigo cikin wannan duniyar. Yayi ƙoƙarin yin hakan amma kamar a baya hakan bata faru ba. Sai dai kuma ya rage ƙarfin duniyar Kuyurussa'ayi wanda ya rage karfin fasahar Haruta, ya kuma bawa hare-haren da ɗayan Armad ɗin da Shata suka kai dama suka samu Haruta.
Wani abin mamaki kiɗan da Shata yake yi sai ya fara danne fasahar Haruta. Takubban sun bayyana sun kuma kawo musu hari, amma kuma basa sauri. Kai kace bacci takubban suke ji. Suna ƙara kusantar inda Shata yake kaɗa garayar suna ƙara rage sauri. A ɗaya ɓangaren kuma Saif-Al-Barzak ta samu bayan Haruta ta sara. Duk da bata tsarge shi gida biyu ba amma ta ratsa fatarsa domin kuwa ga jini nan a kanta.
Shata ya kyalkyale da dariya. "Wato Armad maganarka haka take, fakewa kawai yake da duniyar yana tare hare-haren ka, amma a waje bai isa ba. Kuma indai zaka karya alkadarin duniyar da Negrinkinka to kuwa zamu iya halaka shi."
Ga dukkan alamu shima Haruta ya fuskanci hakan domin kuwa cikin tsananin zafin nama yayi wajenda Armad yake zaune yana amfani da Negrinki. Shata ya shigo gabansa da niyar tare shi amma ya zille masa ya bayyana a gaban Armad. Cikin kwarewa ya ɗaga takobi ya tsarge shi gida biyu. Nan take duniyar ta koma dai-dai. Ƙarfin Haruta ya dawo
Sai dai kuma wani abu da Haruta bai kula ba shi ne: a dai dai lokacin daya ɗauke idon sa daga kan Zaikid, a lokacin wani Armad ɗin ya bayyana a inda Zaikid yake. Yasa hannu ya tsinke ankokin dake jikinsa. Kawai ƙarar dirar ankwar a ƙasa Haruta yaji. Yana waiwayowa ya hangi Zaikid ya miƙe tsaye babu ankwa a jikinsa.
Cikin tsananin fushi Haruta ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban Armad ɗin da yake kusa da Zaikid ya tsinke masa kai. Sannan ya juyo wajen Shata ya kai masa sara. Kafin takobin ta dira ya sake ta ya koma wajen Zaikid inda ya samar da wata takobin ya kai masa sara. Zaikid ya tare saran da tasa takobin. Sabon faɗa ya kaure. Wani abun mamaki da takubban Haruta shi ne: suna iya kai sara da kansu. Misali takobin da Haruta yayi amfani da ita akan Shata. Da kanta ta ƙarasa ta sauka akan Shata, kuma har yanzu faɗa suke yi bata haƙura ba. Ba daban Shata yayi sauri ya tare da jitar dake hannunsa ba da tuni ta tsinke masa kafaɗa. Da yake Shata ba gwanin faɗa da takobi bane, kuma zaka iya cewa yafi kwarewa a fannin faɗa na nesa tunda da kayan kiɗa yake amfani, sabida haka haka takobin Haruta ta hana shi sakat. Tabbas idan aka ci gaba a haka zata iya raunata shi.
Ana cikin haka ƙofa ta bayyana akan iska Armad ya fito ta ciki. Shata da Zaikid sukai tsalle suka dawo gefensa. Shima Haruta tsalle yayi ya koma baya suka fuskanci juna.
Haruta ya dubi Armad fuska a murtuke. "Wato a duniyar Negrinki ka ɓuya. Kana ciki kana aiko da mutun-mutumi suna yi maka aiki."
"To akan me zanyi faɗa dakai bayan taimakon ka ake yi?" Armad ya tambaye shi. "Ana rage min ƙarfe kai kuma ana ƙara maka. Amma yanzu kaga tayi dai-dai tunda mun zama mu uku."
Haruta ya yadda takobin dake hannunsa ya zaro wata daga cikin jakar tsafinsa ya fuskance su. "Kuna tunanin dan kun zama ku uku zaku ci nasara akai na?" Ku canja shiri."
"Duniyar Takobi!"
Kafin takubban Haruta su gama bayyana Zaikid ya shige gaba ya karɓi ragamar faɗan.
"Armad, koma gefe. Yi ƙoƙari ka ragewa duniyar ƙarfi ta hanyar Negrinkin ka. Shata, kai kuma ka zagaya ta baya ka jira dama."
Ba musu Armad ya nemi waje ya zauna. Shata ya zagaya ta bayan Haruta. Shi kuma Zaikid ya zare takobinsa ya kira fasahar da Armad ya daɗe yana so ya koya.
"Wilbafosiyan-Siwod-dans!"
Comments
Post a Comment