Skip to main content

342-343

 Ɓangaren Armad


Armad yana tsugunne a bakin rafi. Kewaye dashi daji ne iyakacin ganinka. Ga manya-manyan bishiyu launuka daban-daban suna ta rangaji sabida iskar dake kadawa. Tun daga nesa kana jiyo kukan tsuntsaye abin gwanin sha'awa. A wasu lokuta sai kaga tsuntsu ya sakko kan rafin yasha ruwa sannan yayi fiffike ya koma kan bishiya yaci gaba da waƙa. 


Armad ya ƙarasa wanke rigarsa ya matse ya shanyata a kan bishiyar dake kusa dashi. Babu alamun gida gaba babu alamun gida baya. Zaiyi wuya ace akwai wani ɗan adam a wajen musamman duba da irin dubban namun dawan dake yawo acikin dajin wanda Armad yake jiyo yanayin izzarsu. 


Bayan ɗan tunani Armad ya nemi waje ya gishingida yana jira rigar ta bushe. A lokaci guda kuma ya faɗa cikin kogin tunani akan halin daya tsinci kansa. 


Abu na ƙarshe da yake tunawa shi ne yin amfani da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans. A baya sanda yayi amfani da wannan fasaha tayi cilli dashi shekara biyu gaba wanda hakan yayi sanadiyyar haɗuwarsa da Nusi. A wannan lokaci ma yana da tabbas fasahar tayi jifa dashi acikin lokaci. Abinda bai sani ba shi ne kwana nawa, ko kuma sati nawa, ko kuma wata nawa, ko kuma shekara nawa ya rasa? Ƙarfin izzarsa ya ƙaru matuƙa idan aka kwatanta da wancan lokaci da yayi amfani da fasahar, sabida haka yana ji a ransa cewa lallai yawan lokacin daya rasa bazai kai na baya ba. Amma hanya ɗaya da zai tabbatar shi ne ya samu wani ya tambaye shi idan ya shiga gari. Matsalar kawai bai san a ina garin yake ba? Tun farkon bayyanar sa ya gane cewa bai taɓa zuwa wannan waje ba a tsahon rayuwarsa. Kuma bashi da masaniya ko akwai gari a kusa dashi ko babu tunda ko kaɗan bayan jin yanayin izzar mutun a kusa. 


To koma dai meye Armad ya ƙuduri niyyar yayi gabas yabi hanyar da rafin ya fito. Tunda ance indai kaga ruwa to za kaga mutun. Watakila idan yaci gaba da bin ruwan ya tadda gari. Idan ya gano a inda yake da kuma kwana nawa ya rasa daga nan sai ya fara neman mutanensa domin su shirya yadda zasu tarwatsa daular denizawa. Abinda Iluru yayi masa babu yafewa. Lallai sai ya ɗauki hukunci babba akai. 


Wani hanzari ba gudu ba shi ne Ikenga. Ta bayyana ƙarara cewa Ikenga yana tare da Iluru. Kuma a yadda al'amura suka wakana yaƙi da Iluru kamar yaƙi da Ikenga ne. Amma duk wannan bashi ne abin damuwa ba, babban abin damuwar shi ne har yanzu ƙarfin Armad bai kai ya turmuza hancin Ikenga a ƙas ba, musamman idan mukai duba da sakamakon fafatawarsu wanda ya tursasawa Armad amfani da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans. Fasahar da sau biyu kacal Armad ya taɓa amfani da ita tun bayan fitowarsa daga gida sabida hatsarin ta. Shin hakan yana nuna cewa Armad ya gaza? 


Armad ya haɗe gira gami da gyara zama. Zancen ma ace ya gaza bai taso ba. Kawai dai yana buƙatar ya ƙara shiri ne. A har kullum Armad ya yadda cewa komai daren daɗewa, kuma komai nisan da Ikenga da Bihanzin da kuyurussa'ayi sukai masa tabbas zai kamo su idan yaci gaba da dagewa. Abinda kawai zai sa ya gaza shi ne idan ya karaya. Ja da baya ga rago ba tsoro bane. Ba yau ya fara fafatawa ya faɗi ba. A kullum Armad gwani ne wajen gano matsalarsa da kuma maganin ta. Misali a halin yanzu matsalarsa ta farko ita ce zaren izzarsa baya yi masa abinda yake so. Kwata-kwata bai kamata ace yana zukewa Iluru izza ba amma kuma Iluru yana amfani da fasahar kwangila yana dawo da izzarsa kamar ma babu abinda ya faru. Idan Iluru zai iya haka to ina ga Bihanzin ko kuma Ikenga ko kuma Kuyurussa'ayi. Dole ne ya gyara fasahar tayadda idan ya zuke izzar abokin fadansa to ta tafi kenan. Babu yadda za'ai a dawo da ita. Ta haka koda mutun yana da fasahar kwangila baza tayi aiki ba. 


Shin hakan zai yiwu? Idan zai iya tunawa Hidaya bata zuke izzar Bihanzin ba a lokacin yaƙin sarakunan jinzidal. Shin hakan yana nuna babu wata hanya da za'a iya hana sarakunan jinzidal dawo da izzarsu bayan an zuke ta? Idan kuwa haka ne to lallai fasahar zuƙe izza batai amfani ba. Armad bazai yadda da wannan ba. A ransa ya ƙuduri niyyar koma ta wacce hanya ce sai ya nemi yadda zaiyi ya gano hanyar da zai ringa zuƙe izzar mutane har abada. Domin ta haka ne kadai zai iya cin galaba kan abokan gabarsa. 


Abu na biyu shi ne duniyar Negrinkinsa. Ita ma bata aiki yadda ya kamata. Tsahon lokaci tun bayan sanda Armad ya samu Negrinki yake sarrafa wannan duniya ya kuma kai abinda yake so ciki komai girmansa (ko mutun ko aljan), kuma ya fito da abinda yake so. Shi kansa yakan shiga ko kuma ya fita a duk sanda yake so ba tare da matsala ba. To amma tayaya Armad zai hana abinda yasa acikin duniyar yin layar zana? Bawai Iluru ne na farko ba, akwai Hasanu, da Elbinuil, da Kaizadu, dukkaninsu sun tsere daga cikin duniyar. Kafin su ma ya saka Han'diyuza wanda shima ya tsere har yau bai san inda yayi ba. Shin hakan yana nufin dole idan yasa mutun acikin duniyar zai iya guduwa kuma babu yadda zaiyi ya hana hakan afkuwa? Domin idan mukai duba da yadda Uznu yasa Armad acikin duniyar Kuyurussa'ayi kuma Armad ya samu dama ya fito daga ciki ba tare da yaddar Uznu ba to zamu iya cewa mai yi ne akai masa. Sannan kuma ai Kaizadu ma ya saka Armad a irin duniyar amma kuma Armad ya fice. To wai shin ba'a iya hana ma'abota izza fita daga irin waɗannan duniyoyin?


Armad bai yadda ba ko kaɗan, kuma ya ƙuduri niyyar dole ya gyara duniyarsa tayadda duk abinda yasa aciki bai isa ya fita ba sai da izinin sa. Kuma yana da buƙatar ya hana wani abu shiga cikin duniyar sai da izinin sa. Misali yadda Iluru ya aika masa kogi da daji ciki. Kaga ya kamata ace babu wanda ya isa ya tura wani abu acikin duniyar sai da yaddar Armad. 


Koda Armad yazo nan a tunaninsa sai ya leƙa cikin duniyar Negrinkin domin yaga irin barnar da Iluru yayi masa. 


Abu na farko da Armad yayi arba dashi shi ne waɗannan tsibirai guda shida wanda suke lilo akan iska sun tarwatse sunyi daga-daga. Kogin da Iluru ya aiko ya rufe wutar dake ci a ƙasa ya maida ita ruwan sanyi. Kai hatta nauyin da kake ji idan ka shigo a yanzu babu shi. Kana gani kasan an tashi duniyar daga aiki. Ko'ina ka duba sai konannun bishiyu da ƙasa da kuma narkakkun duwatsu. 


Armad ya fito daga cikin duniyar rai a ɓace. Ya zama dole yayi aiki akan Negrinkinsa domin bata da amfani idan ya zamana kowa zai iya cilla masa shirme da shashanci ciki. 


Yana cikin wannan hali ne yaji ƙara daga bayansa. Yana waiwayawa yaga ƙura ta tashi, bishiyoyi suna zubewa ƙasa kamar fari. Wani zabgegen aljanin zaki yai tsalle ya fito daga cikin dajin yayi kansa gadan-gadan. Armad kawai lashe baki yayi amma zakin yaci birki a tsorace. Kafin zakin ya gane mai ke faruwa walkiya ta sauka a kansa. Dama Armad ya kwana biyu bai ci komai ba saboda haka ya hau kan zakin ya aikata shi. Bayan ya gama yayi godiya sannan ya janyo rigarsa daya shanya ya saka ya nufi gabas yana bin gefen rafin.


Banda Negrinki da miyura Armad baya jin akwai sauran matsala a fasahohinsa na yanayin izza, sauri, da kuma tsaro. Idan ana zancen tsaro yana da sikai da kuma sabuwar fasahar sikai. Idan ana zancen yanayin izza to fa a yanzu yakai matsayin ƴan ƙabilar elbis wato su Sarkin-sarki kenan. Idan kuwa ana maganar sauri to bayan Aiban'shisu akwai Aiban'zhisu. Banda wasu shirye-shirye da suka kulla da Hidaya. Zaka iyacewa ko kaɗan Armad bai karaya ba duk kuwa da yadda faɗansa da Ikenga ya kasance. 


Yana cikin tafiya kawai baiyi aune ba sai jin kibiya yayi ta shigo shingen yanayin izzarsa. Kafin ya ankara kibiyar ta fara ƙoƙarin tsire shi a wuya. Armad yayi tsalle gefe inda kibiyar ta wuce ta caki bishiyar dake bayansa. Yana dira wasu kibban guda uku suka tunkaro shi. Yayi tsalle ya haye bishiyar dake gefensa dan ya gano ta ina ake harbinsa. Wani abin mamaki shi ne yadda bishiyar da kibiyar ta samu tayi bindiga. Komai ƙarfin kibiya ai bai kamata ace ta saka bishiya tayi bindiga ba sai dai idan akwai wani sirri da Armad bai sani ba. 


Yana ɗaga kai ɓangaren da kibban suka fito ya hangi wasu mutane uku daga can nesa kusan tafiyar awa guda daga inda yake. Abin mamaki shi ne yadda har suka ganshi duk da nisan dake tsakaninsu har kuma suka iya harbinsa. 


Maimakon wani abu kawai sai Armad ya bayyana a gabansu ta hanyar Aiban'shisu. Suna ganinsa suka firgita. Mazan sukai tsalle baya inda suka faɗo daga kan bishiyar da suke kai. Ita kuwa macen kasa motsi tayi. Armad kawai tsayawa yayi yana kallonsa, ko kaɗan bai damu da halin da suke ciki ba, a ransa kawai jira yake yi su nutsu yaji dalilin da yasa suke harbinsa. 


Ɗaya daga cikin mazan da suka faɗa ƙasa yayi ta maza ya ja kwari-da-bakansa zai harbi Armad. 


"Ajiye kibiyar ka nemi waje ka zauna," inji Armad. Abin mamaki kawai sai mutumin ya ajiye kibiyar ya jada baya ya nemi waje ya zauna a ƙasa kamar yaro mai ladabi. Ɗayan namijin yayi kansa yana kurari akan mai yasa ya ajiye makaminsa. Armad ya dube shi ya ce, "kai ma zauna."


Kamar an cire masa laka shima ya tafi a hankali ya zauna yayi cilli da kwari da bakar dake hannunsa. Dukkaninsu suna cike da mamakin yadda akai jikinsu yake biyayya ga wannan mutun duk kuwa da cewa zukatansu basa so. 


Armad ya dubi budurwar dake gabansa, ya ce, "ke fa?"


Cikin karkarwa macen ta sakko ƙasa ta zauna ta jeru da yan'uwanta, kai kace yara aka jera ake bawa tarbiyya.


Armad ya sakko daga kan bishiyar ya nemi waje daga kusa dasu ya jingina da wata bishiya. "Tunda mun fuskanci juna yanzu waye acikinku zai gayamin kwanan wata da shekara?


Cikin sauri duk su ukun suka daga hannu. "Ni."


Armad ya nuna macen. "Ke faɗi."


"Yau bakwai ga watan tara, shekarar 1861."


Armad yayi shiru yana tunani. Tabbas a watan daya gabata aka kammala kurkukun lokaci, kuma a watan yaje daular denizawa harma sukai faɗa da Iluru da Ikenga. A sakamakon haka dole yayi amfani da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans wadda ta cillo shi nan. Idan aka lissafa ya kama wata guda kenan da kwana biyar ya rasa.


Armad yayi ajiyar zuciya. Tunda ya rasa wata guda bari kuma yaji a ina aka cillashi. "Wanne gari ne wannan?" 


"Garin Melmusa na sarki Alu mai Sango dake ƙarƙashin ƙasa."


"Ƙarƙashin ƙasa? Hajiya kada ki raina min hankali, babu wani gari mai suna Melmusa a ƙarƙashin ƙasa?"


Macen ta firgita matuƙa da jin wannan batu. Ko kaɗan ba ƙarya take ba, abinda ta faɗa gaskiya ne, kololuwar gaskiyar ta. Amma kuma tana jin tsoron tankawa Armad. 


Armad ya ɗanyi shiru yana tunani kafin daga bisani ya miƙe tsaye. "Muje garin na gani da kaina." 


Sadaukan uku suka miƙe ya tasa ƙeyarsu a gaba zuwa wannan gari mai suna Melmusa. 


Sai da suka ƙara wuce wani dajin sannan suka iso wannan gari mai suna Melmusa. Tun daga nesa Armad yana hango ƙasaitacciyar katangar garin wadda aka gina da jajayen duwatsu. Tsayinta har ya haura ta garin Jekis. Ga wata ƙofar shiga ta baƙin karfe a tsakiya. Armad ya hango mutane sanye da bakaken kaya sun jejjeru a bakin ƙofar garin. 


"Su waye wadancan?" 


Macen ta amsa da cewa, "mayaƙan Ururu ne."


Nan take Armad ya janyo ɗalasiman sa kusa dashi. "Meye alaƙarku dasu?"


Namijin yayi sauri ya fara bayani. "Sarki Alu mai Sango ya taɓa kulla yarjejeniyar zaman lafiya dasu. Amma yanzu bamu san meye ya kawo su ba. Yau kwanan su uku anan sunki tafiya."


Armad ya yamutse fuska. Duk wani abu daya haɗa da Ururu baya haifar da ɗa mai ido. Musamman duba ga cewa bai san abubuwan da suka faru a watan daya gabata ba. Wani abin haushi shi ne suna ganinsa zasu gane shi tunda ance hotunan Armad ake raba musu kowa ya haddace.


Bayan ɗan tunani Armad ya yanke shawarar ya sallamesu ya shiga garin da Kaban'shisu. 


"Ku koma wajen gadinku amma ku tabbatar babu wanda kuka gayawa labari na ko waye. Kunji?"


Suka risuna a tsorace. "Munji."


Suka juya suka arce jiki na karkarwa.


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...