Jirgin ruwa ne kato irin wanda akan daɗe ba'a gani ba. Yawanci idan kaga irin wannan jirgin to a gurin mayaƙan Ururu ne. Ɗakunan dake cikinsa sun isa su ɗauki akalla mutum ɗari. Jikinsa anyi masa fenti da sinadarin yeniy wanda yake kore dodo da sauran muggan namun ruwa.
Armad yana zaune acikin wannan jirgi an ɗaure ƙafafunsa da hannayensa da ankoki. A halin da yake ciki bashi da damar ganin cikin wannan jirgi domin kuwa a kulle yake acikin daki mai duhu. Daɗin daɗawa ga masu gadi ƙarti guda uku tsaye a bakin ƙofa suna jira yayi motsi su afka masa.
To ko tayaya akayi Armad ya tsinci kansa a wannan hali? Amsar sai mun koma kimanin awa daya data wuce. A dai-dai lokacin da Armad yake tare da Liman Umaru a garin Melmusa na sarki Alu dake ƙarƙashin ƙasa.
"Liman, ina so zan koma sama yaya za'ai?" Armad ya ce.
Liman ya girgiza kai. "Ai komawa sama a halin da ake ciki ba abu ne mai yiwuwa ba."
Armad ya yamutse fuska. "Ban gane ba. Mai kake nufi?"
Liman ya gyaɗa kafaɗa. "Ai tunda aka fara wannan dambarwa tsakanin Nusi Wilbafos da Ururu aka hana fita. Daka kula da zaka ga mayaƙan Ururu a bakin ƙofa. Tuni suka saka Kafi tayadda babu wanda zai fita ko kuma ya shigo wannan gari har sai nan da kwana biyu."
Abin da mamaki. Shi kansa Armad bai san akwai wannan gari ba a duniya ba. Kaga kenan yaƙin da ake yi a tsakanin Ururu dashi bai shafe su ba. Ko kuma watakila a wata gudan daya gabata wani abu ya faru.
"Mai yasa Ururu zasu damu daku?" Armad ya tambaya.
"Nima dai bani da tabbas," liman ya ce. "Amma ance akwai ɓarauniyar hanya daga wannan gari zuwa gadar zare wadda daga nan zaka iya shiga doron kasa ta biyu. Babu wanda yasan gaskiyar al'amarin sai sarki Alu mai Sango."
To ba kamar yadda yayi tunani ba ne kenan. Babu alaka a tsakanin Nusi da Alu kuma abinda ya kawo Ururu shi ne su tsare wannan ɓarauniyar da. Abu mafi muhimmanci shi ne akwai hanyar. Koda kuwa jita-jita ce kawai. Dama abinda kawai Gaus yake son ji kenan.
"Ina son naga sarki Alu," Armad ya ce.
"Sai anyi maka iso," Liman ya ce. "Ko ƴan gari basa ganinsa sai sun bi layi. Ina ganin akalla zaka iya samun wata daya zuwa biyu kafin layi yazo kan ka."
Armad bashi da wata guda. Ko kwana guda bashi dashi. Idan baza ayi masa iso yaga sarki ba to ai sai ya sa sarkin yazo ya ganshi har inda yake.
Nan take ya yanke shawara. Ya nemi takarda da alkalami ya rubuta wasika zuwa ga sarki Alu. Ya nin ke ya bawa Liman ya je ya kai wa sarki.
"Hannun ka da nasa zaka bashi," Armad ya ce.
Liman ya tsaya zai fara inda-inda Armad ya bata rai.
"Dakata, Liman Umaru, kada kace min baza ka iya ba, na riga nasan kai mutun ne mai matsayi a garin nan. Idan wannan takardar bata isa ga sarki ba to lalle wani mummunan abu yana gab da faruwa a wannan gari naku. Bana fata amma ka tabbatar takarda nan ta isa wajen sarki kuma ya karanta."
Armad ya miƙe zai tafi. Har ya juya yaga kamar Liman bai dauki maganar da gaske ba sabida haka ya juyo.
"Liman, suna na Armad Wilbafos, idan kaje ka gayawa sarki Alu."
Da wannan ya juya ya fice. Ko kaɗan bai damu da karkarwar da jikin liman yake yi ba a lokacin da yaji sunansa.
Ba jimawa ya iso bakin kofar garin. A lokacin daya shiga yaga dandazon mayaƙan Ururu sun tare kofar tayadda duk wanda zai shiga sai sun caje shi. Hakan ne ma yasa yayi amfani da fasahar Kaban'shisu ya shige ta cikin katangar tayadda babu wanda ya ganshi. To amma a wannan lokaci Armad ta ƙofar ya bi.
Cikin rabin sa'a layi yazo kansa.
"Kai," ma'aikacin dake caje mutane a lokacin ya daka masa tsawa, "fadi sunan ka da abinda kazo yi garin Melmusa."
"Suna na Armad Wilbafos. Nazo ne domin zuwa doron ƙasa ta biyu."
Sunansa kaɗai ya isa ya jawo masa matsala amma banda shi ya kuma bayyana muradin sa na yin kutse a doron ƙasa ta biyu, a irin wannan hali da ake ciki. Amma a fuskar Armad babu baƙin ciki ko damuwa. Hankalinsa a kwance yake yana kallon su.
Mai tsaron kofar ya haɗe gira. Cikin sauri ya zaro wasu takardu daga aljihunsa masu ɗauke da zanen mutane ya duba.
Ga dukkan alamu abinda ya gani acikin takardar bai yi masa daɗi ba domin kuwa bai ƙara yin magana ba kawai sai gani akai ya jada baya a fusace ya kai wa Armad sara da takobinsa.
Armad ya kauce a nutse ba tare da ya daga ƙafarsa daga inda take ba.
"Armad Wilbafos ne!" Ma'aikacin ya gayawa yan uwansa.
Nan take kowa ya ankare da abinda ke faruwa. Kafin kace kwabo sun manta da caje mutanen dake kan layi sun kewaye Armad. Ragowar mutanen wajen kuwa guje-guje suka fara.
Dukkan mayaƙan sukai kukan kura suka afkawa Armad. Da daman su takobi suke amfani da ita. Wasu yan kaɗan suna da wukake. Sai kuma tsiraru masu fasahar aljanu: wuta ko walkiya ko turbaya.
Gaus ya tsaya cak a inda yake bai motsa ba. Suka sare shi, suka soke shi, suka kona shi, suka binne shi, amma yana nan a tsaye cak bai motsa ba.
Bayan ɗan lokaci suka jada baya suna kallon juna. Yawansu yakai dari. Amma a jikin Armad ko kwarzane babu.
"Ina shugaban ku?" Armad ya ce.
"Kai, mai laifi, karya kake! Mu ma mun ishe ka."
Nan take sukai kukan kura suka ƙara afka masa. Sukai iyakacin yin su amma ko gwarzane babu. Shi kuwa yana tsaye shirim yayi shiru yana kallon su.
Bayan tsahon lokaci ya buɗe baki ya ce, "koda zaku tarar min a lokaci guda, kuma ku kawo min hari a lokaci guda baza ku iya yin nasara a kai na ba."
Mayaƙan suka yamutse fuska. Kalaman Armad sunyi matukar harzuka su. Suka ƙara yin kukan kura zasu afka masa amma a lokacin wani mutum ya bayyana a bayansu.
"Ku rabu dashi," inji mutumin.
Mayaƙan suka dakata amma duk da haka huci suke.
"Koda ka rabu dasu babu abinda zasu iya," inji Armad.
"Kwamanda kaji abinda yake cewa ko? Ya raina ƙarfin Ururu. Ya kamata ka bari muyi masa hukunci."
"Ku rabu dashi, baza ku iya dashi ba," inji mutumin da suka kira da kwamanda.
Armad ya gyaɗa kai. "Gwanda dai ku saurari abinda yake gaya muku. Baza ku iya ba. Koda kuwa na farkon ku dana karshen ku sun taru sunyi taimakekeniya."
Mayaƙan na jin haka suka hasala sukai kan Armad.
"Ku tsaya nace," inji kwamandan. Amma kafin ya rufe baki sun kai ga Armad. A wannan lokaci Armad ya motsa inda jikinsa ya koma walkiya. Suna fara saransa walkiyar tayi tartsatsi tayi sama ta rufe su, kai kace wutar daji ce.
Duk wanda ta taɓa sai kayansa sun kama da wuta. Babu abinda kake ji sai ihu. Ba shiri sahun farko suka yadda makaman su suka fara neman tsira. Amma duk da haka sahu na biyu basu daddara ba, suka ƙara kawo masa sara. Armad yayi tsalle sama ya saukar musu da jaririn hannun Aradu.
A lokacin tabbas sun ga mutuwar su a fili, sun kuma ɗebe haso. To amma a lokacin mutumin mai suna kwamandan yayi tsalle ya shigo gaba ya tare walkiyar da wani hatimi dake hannunsa.
Mayaƙan tuni sukai dana sani da gaggawar da suka aikatawa kansu a lokacin da suka ga gunguman walkiyar ta dososu gadan-gadan. Hakan yasa nan take suka maida wuƙar su suka jada baya. Sun yadda wannan faɗa yafi karfinsu.
"Armad Wilbafos," inji kwamandan. "Suna na Lilut Nimaya'u - kyaftin na ɗaya a karkashin rundunar kwamanda Yurba Ururu. Nayi mamakin ganinka anan wurin. Wata guda kenan babu ko alamun ka duk kuwa da abubuwan da suke faruwa. Waye zaiyi tunanin kana ƙarƙashin ƙasa ka buya?"
"Nima nayi mamakin ganin ku anan wurin," inji Armad. "Mai kuka zo yi nan?"
Kyaftin yayi murmushi. "Ga dukkan alamu baka fahimta ba. Ai ba zuwa muka yi ba. Dama can muna nan. Akwai rundunar mayaƙan Ururu wadda take aiki a ƙarƙashin ƙasa. Watakila shi yasa mayaƙa na basu san ka ba sosai."
Armad ya gyada kafada. "Duk da haka dai baka yimin bayanin mai kuke yi anan ba. Ko nan ne shalkwatar ku?"
"A'a," inji kwamandan. "Ba nan ne shalkwatar mu ba. Idan kana so kaji dalilin daya kawo mu nan sai ka gaya min dalilin daya kawo ka."
Armad yana ɗan numfasa kaɗan. Har ya buɗe baki zai gaya masa cewa shi ma bai san yadda akai yazo ba sai wata dabara ta fado masa. "Na gaya muku ai tun da fari. Nazo ne neman hanyar zuwa doron ƙasa ta biyu. Ance akwai ɓarauniyar hanya ta wannan gari. Da zaka nuna min inda take da naji daɗi."
Kyaftin yayi murmushi. "Dama kwamanda Yurba yayi tunanin haka shi yasa ya ajiye mu anan," Lilut ya ce. "Kada ka damu domin kuwa munzo ne domin hana ka wucewa."
Kaga wannan ya tabbatar da maganar Liman cewa akwai hanya. Kuma duk inda wannan hanya take Alu zai sani.
"Ina ragowar rundunar ka?" Inji kyaftin Lilut.
"Suna aljihuna," Armad ya ce.
"Hmm." Kwamandan yaja ɗan numfashi. "Idan muka kama ka ai zakai mana bayani, ko?"
Armad ya yamutse fuska. Abin mamaki ne yadda mutum mai matsayin kyaftin yake tunanin zai iya kama shi. To amma ba'a ƙwacewa yaro garma.
Kyaftin Lilut ya kira ɗalasimi wanda yasa hatimin dake hannunsa ya juye izuwa takobin walkiya. Kwamandan yayi kan Armad yakai masa sara. Armad yayi tsalle sama ya kauce. Wani abin mamaki kawai sai wasu digo-digon ja suka fara fita daga cikin takobin suna watsuwa ko'ina. Duk abinda suka taɓa sai kaga ya kama da wuta. Cikin kankanin lokaci katangar garin ta kama da wuta.
Armad yayi mamaki. Shi dai yasan walkiyarsa bata haka. Koma meye acikin hatimin nan to ya sauya walkiyar kuma a yanzu shi kansa Armad bai san meye acikin ta ba.
Lilut ya ƙara kawo wa Armad sara ta sama. Armad ya karkace gefe akan iska. Ƙarfin walkiya ya shige cikin garin ya fara kona gidaje da mutane. Kafin kace meye wannan ƙara da hayaniya ta cika garin.
Lilut yaci gaba da kawowa Armad sara da takobin walkiya shi kuma Armad yana kaucewa. A duk sanda ya kauce sai kaga wajen da saran ya samu ya kama da wuta. Ba jimawa garin Melmusa ya dau harama.
Awa guda da fara wannan dambarwa wani dattijo ya bayyana akan alfadari. Yana da idanu ruwan ƙasa irin na ƴaƴan Wilbafos. Alfadarinsa yana lilo akan iska kai kace tsuntsu ne. Shi kuma yana riƙe da wani littafi a hannunsa na dama.
"Kyaftin Lilut, bazan yafe muku ba idan kuka ci gaba da kona min gari," inji mutumin.
Lilut yaja da baya ya daina kai wa Armad sara. Abin mamakin kawai nishi kyaftin yake yi duk kuwa da cewa ko hari ɗaya Armad bai kai masa ba.
"Alu Mai Sango," Inji kyaftin Lilut, "wannan shi ne makiyin mu Armad Wilbafos. Ina fatan ba zuwa kayi ka shigar masa ba."
Mutumin da aka kira da Alu Mai Sango ya ƙurawa Armad ido tsahon lokaci kafin ya juya ga kyaftin Lilut ya girgiza kai. "Ko kaɗan, nazo ne na saurari kowane ɓangare sannan nayi hukunci."
Armad yayi murmushi. Tabbas Alu ya samu sakon sa.
"Alu sunan ka ko?" Armad ya ce. "A matsayinka na wa zaka yi min hukunci?"
"A matsayina na sarkin garin nan," inji Alu. "Mai ya kawo ka gari na, Armad Wilbafos?"
"Hanya ce ta kawo ni," inji Armad.
"Ko zaka iya gaya mana inda zaka je?" Alu ya tambaya.
"Doron ƙasa ta biyu," Armad ya ce.
Alu ya zare ido cikin mamaki.
"Kaji abinda na gaya maka ko?" Kyaftin Lilut ya ce.
Alu ya gyaɗa kai alamun amincewa. "Muje fada na saurari kowane ɓangare nayi hukunci."
Ba musu Armad da Lilut suka bi bayan Alu zuwa cikin garin.
Suna isa fada, Alu yasa aka kawo masa ankwa ya miƙawa Armad. "Ina bukatar ka saka wannan a hannunka. Domin hakan zai bawa mutane na da abokaina na sama kwanciyar hankali."
Armad ya karbi ankwar ya saka a hannunsa ba tare da musu ba sannan suka wuce ciki. Alu ya hakimce akan karagarsa ta mulki sannan kowa ya hau layi.
"Kyaftin Lilut," Alu ya ce. "Kace Armad abokin gabar ka ne to amma hakan bashi zai baka damar ka kawomin hari a kofar gari na ka ɗagawa mutane na hankali ba."
"Nasa ni, Alu," Lilut ya ce. "To amma wannan mutumin yana da hatsari matuka yadda baka tsammani. Yana faɗa da ikon mutanen dake sama a doron ƙasa ta farko. Ba lalle ka iya gane halin da ake ciki ba kuma a yanzu babu lokacin da zan tsaya nayi maka bayani."
Alu ya juyo wajen Armad. "Malan Armad, ana tuhumar ka da laifi wajen jada ikon mutanen dake sama. Ka amsa laifin ka?"
"Na amsa," Armad ya ce.
Alu yayi ajiyar zuciya. "To idan kuwa haka ne to dole hukunci ya hau kanka, malan Armad. A duk inda mutun sama da guda zasu taru to dole a samu shugaba idan ba haka ba kuwa to baza a samu ka'ida ba. Mutanen dake sama shugabanni ne. Shi kuwa shugaba babu kyau ayi masa tawaye. Kuma ni a dabi'a ta bana son masu tawaye."
"Yauwa, Alu," Lilut ya ce. "Baza mu manta da gudummawar daka bayar ba. A yanzu ina so ka ƙara masa ankoki kamar guda bakwai sannan ka bani shi na tafi dashi domin a hukunta shi. Zan miƙa batun ka zuwa sarki bisa doron ƙasa ta biyu. Tabbas zamu kawo maka agaji a yayin faɗanka da Bihanzin."
"Naji daɗin jin wannan batu daga gareka," Alu ya ce. "To amma a tsarin addini na bana miƙa mai laifi hannun wanda yake tuhumar sa. Ni da kai na zan kaishi Gadar Zare na miƙa shi a hannun hukuma. Ina fatan zaka mutunta shawarar dana yanke."
Lilut ya haɗe gira. Kamar zai ki amincewa amma ya juya sukai kuskus da mutumin dake bayansa.
"Na amince," ya ce. "Amma dole na raka ka da kaina. Kasan halin da ake ciki saboda haka idan ma kaje ba lallai su barka ka shiga ba."
"Wannan ba wani abu bane," Alu ya ce. "Zarar na miƙa shi a hannun hukuma nasan aiki na ya cika. Kawai so nake abi komai kamar yadda doka ta tanada."
Wannan shi ne abinda ya faru Armad ya tsinci kansa acikin jirgin ruwa. Daga garin Melmusa akwai wasu ramuka na ƙarƙashin ƙasa wanda zaka bi su fito dakai waje daidai bangon arewa. Daga nan kwamanda Lilut ya ɗauke su a jirgin mayaƙan Ururu yayi sama dasu zuwa Gadar Zare.
***
Armad na zaune ya tankwashe ƙafa acikin kurkuku. Ga wata busasshiyar gurasa a gabansa. Ɗaya daga cikin masu gadin da aka bari a gurin ya leƙa yayi dariyar mugunta.
"Kaci gurasa idan zaka ci," mai gadin ya ce. "Shi ne abincin ƙarshe da zaka gani."
Armad bai ce masa uffan.
Haka suka ci gaba da tafiya akan bangon arewa tsahon awanni hudu kafin su iso.
Zai yi wuya ka samu ɗan asalin ƙarƙashin ƙasa ko kuma wanda yake rayuwa a doron ƙasa ta uku zuwa ta bakwai wanda ya taɓa ziyartar doron ƙasa ta biyu.
Kamar yadda kabilar Ururu suke gadin doron ƙasa ta farko haka suke gadin doron ƙasa ta biyu. Hakan ne yasa suka gina wani katafaren gini a tsakanin doron ƙasa ta biyu data uku wanda indai zaka wuce sai ka bi ta cikinsa. Sunan wannan gini gadar zare. A gari banza Ururu basa barin mutane su wuce ta cikin gadar zare ballantana a wannan lokaci da ake ɗari-ɗari. Zaka iya cewa a kowanne lokaci Ururu suna tsammanin Nusi Wilbafos ta kai musu hari. Wanda hakan yasa aka ƙara tsaurara tsaro a gadar zare.
Armad yana kasan jirgin ruwan a ɗaure saboda haka bai samu damar ganin yadda ƙofar shigar take ba. Yana zaune yaji an buɗe ƙofar ɗakin da yake ciki haske ya shigo. Ma'aikata biyu sanye da bakaken kaya suka shigo suka janyo shi waje.
Idan mai karatu bai mantaba a tsakanin bango da kowane doron ƙasa akwai rami wanda ya raba su. Zurfin ramin shi ne kwatankwacin kaurin doron ƙasar wanda hakan shi kaɗai zai iya nuna maka girman ramin. A lokacin da Babara ya fara kai Armad kurkukun bango Armad ya leƙa ramin amma bai ga komai ba. Haka bayan wannan lokacin ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba Armad ya sha leƙawa cikin ramin a duk sanda zai wuce ko zai ga wani abu acikin amma babu komai sai duhu iyakacin hange. Armad bai taɓa bi ta ciki ba sabida haka wataran ya tambayi masu tukin jirgin ruwa wanda suka taɓa ratsawa ta wajen. Abinda suka gaya masa shi ne rami ne kawai wanda babu komai acikinsa sai duhu da kuma dodo. Iskar wajen tana da bambanci data waje sannan kuma akalla ana iya yin wata guda ana tafiya kafin a fita daga ciki.
A tsakanin doron ƙasa ta biyu data uku akwai katanga wadda Ururu suka gina. Ba'a yadda wani mahaluki ya kusanci wannan katanga ba tare da izini ba. A saman katangar an sa Gadar Zare.
A dai-dai sanda aka fito da Armad jirgin su yana tsaye a ƙofar wannan katanga ana caje su kafin su shiga.
Alu da kyaftin Lilut suna gaba suna magana da masu gadin. Bayan ɗan lokaci masu gadin suka zo suka ƙara caje Armad a karo na goma sha.
"Ku shiga dashi," shugaban masu gadin ya ce bayan ya kammala cajen.
Aka bude musu kofa jirgin su ya shiga. Akwai fitilu a kofar shigar amma duk da haka duk inda ka kalla duhu ne. Alu da Lilut suka kama Armad da hannunsu suka shiga dashi ciki takan wata gadar ƙarfe mai raga-raga. Armad yana jin yanayin izzar manya-manyan dodo irin wanda bai taɓa ji ba suna yawo a kasan gadar.
A ƙarshen gadar wata ƙatuwar ƙofa ce ta katako. Aka buɗe musu suka shiga inda suka iske wasu kofofi na ƙarfe masu raga-raga guda biyu a jere a bayan ta katakon. Kowacce akwai masu gadi aƙalla goma a tsaye.
Kai tsaye aka bude musu suka shiga ciki. Wani mutum ya ɗauke su izuwa dakin caje.
Armad aka fara dubawa.
"Cire kayan ka," mai gadin ya ce masa.
Ba tare da gardama ba ya cire. Akwai irin ayrid a kowacce kurya acikin dakin wanda ke nuna hoton bidiyo na abinda ke faruwa acikin dakin. Sabida haka su Alu dake waje suna ganin komai.
Bayan an kammala caje Armad sai Alu da Lilut. Wato su kansu ba'a yadda dasu ba sai da aka caje su.
Bayan nan aka shiga da su wajen shugaban gadan.
Katon ofishi ne da kujeru na taryar baƙi. Suna shiga suka iske shi a zaune kan kujerar sa yayi tagumi yana kallon ƙasa.
"Barka da aiki, kwamanda Kamus," Lilut ya ce.
Kamus ya ɗago kai a hankali ya kalleshi. "Lilut...? Ya akai?"
Armad bai taɓa ganinsa ba. Ƙatoton gardi ne wanda ko a zaune yafi Armad tsayi. Yana da kasumba wadda tayi futu-futu kai ka kace bai taɓa wanke taba ballantana ayi maganar tajewa. Gashin kansa ma haka yake amma ya ɗan aske gemun sa kaɗan. Rigar jikinsa tayi kama data Ibraham Nil.
Lilut ya kalli. A ganinsa Alu shi ne ta kamata yayi magana tunda shi ne yace a kawo Armad wajen.
Alu yayi gyaran murya. "Suna na Alu Mai Sango, a kundin tsarin mulkin da aka bamu ance idan mun kama mai laifi wanda baza mu iya ajiye wa ba mu kawo shi nan." Ya nuna Armad. "Wannan mai laifi ne. Kyaftin Lilut ne ya kama shi da laifin tawaye da sabawa manya."
Kamus ya kalli Armad a hasale sannan ya ɗauke kai. "Waye shi?" Ya tambaya.
"Wannan shi ne Armad Wilbafos wanda ake shirin hukunta iyayensa a doron ƙasa ta farko," Lilut ya ce.
Kamus ya ƙara duban Armad a karo na biyu. A wannan karon ya ɗan daɗe yana kallon sa kafin yayi ajiyar zuciya ya ce, "ku kaishi ku sashi a ɗakin da muka kulle Deniz Ururu. Alu mun sallame ka."
Alu ya ƙara kallon Armad a karo na ƙarshe sannan ya fice.
Kamus yasa ma'aikatansa suka ɗauki Armad suka shiga dashi ciki. A yayinda ya tsayar da kyaftin Lilut domin su tattauna.
Gini yakai gini, kai baza kace akan ruwa ake ba. Ko'ina Armad ya duba mutane ne a kulle. Wasu suna ihu wasu kuwa ko maganar ma basa iyawa. Suna tafe sautin ankwar dake ƙafarsa yana janyo hankalin na cikin ɗakunan. A haka har suka iso. Masu gadin suka buɗe dakin suka zira Armad aciki suka kulle. Sannan suka juya suka tafi tare da fitilar da suka zo da ita.
Babu abinda ke tashi sai hayaki da warin matattun dodonni da mutane. Kai sabida kaurin hayakin hatta duhun wajen bai hana a ganshi ba. Armad yana jiyo yanayin izzar mutun uku dake gefensa amma bisa mamaki baya jin sauran mutanen dake wajen duk kuwa da ya gansu da idonsa a yayin zuwansa.
Yana kwance cikin ankoki yana lissafi. Bayan ya tabbatar masu gadin sunyi nisa sai ya rarrafa gefe ya kwankwasa bangon dakin dake kusa dashi.
"Waye acikin dakin nan?" Ya tambaya.
Bai samu amsa ba sabida haka ya ƙara kwankwasawa har sau uku.
"Suna na Armad Wilbafos. Nazo ne domin na fitar daku daga wannan waje. Idan akwai wanda yake ji na ya amsa. Suna na Armad Wilbafos."
Comments
Post a Comment