Yaƙi na musamman. Yaƙi na bada labari shekaru masu yawa da zasu zo.
A ɓangaren Dul'Ururu kyaftin ne suka jagoranci fitowar. Akwai kyaftin biyar a ƙarƙashin kowane kwamanda wanda hakan ya bada kyaftin ashirin da biyar kenan. A yayinda kwamanda yake harkokin gabansa, ko kuma ya shiga halwar izza, ko kuma yaje doron ƙasa ta farko ziyara, kyaftin ɗin dake ƙasansa sune suke gudanar da rundunarsa. Saboda haka sun saba jagoranci. Sun san kansu, kuma sun san hannunsu. Hasalima acikinsu akwai girma-girma - wannan yana saman wannan. Kafin kace kwabo sun raba rundunar gida ashirin da biyar. Kowanne kyaftin yaja rabonsa. Suna ƙara matsowa gaba suna rabewa.
A ɗaya ɓangaren mayaƙan Maikiro'Abbas sun zubo a guje suna ƙuwa. Lalle zaka iya cewa babu tsari irin na Ururu. Akwai manyan sadaukai wanda suka shige gaba suna jagorantar tafiyar amma basu rabu gida-gida ba kamar na Ururu.
Abu guda da kowane ɓangare suka nuna shi ne rashin tsoro. Kawai azama suke ƙarawa suna ƙara kada makami suna gudu. Kafin su haɗu da juna masu mashi da kibiya daga kowane ɓangare suka fara harbawa. Da dama tun anan suka riga mu gidan gaskiya. Amma babu wata alama dake nuna anyiwa wani ɓangare illa sosai.
A lokacin da suka yi gaba-da-gaba sai da kowa ya ɗauke numfashi. Armad ya runtse ido yana juyo ƙarar fitar ran bil'adama. Jini yayi sama kafin ya dawo ƙasa ya fara kwaranya. Hankakan mutuwa ya fara yawo. Zaren izza yana tsinkewa. Taurari suna duhu. Babu abinda kake ji sai karaji da kururuwa.
Mayaƙan Maikiro'Abbas sun turje sun riƙe takubbansu sunƙi ja da baya. Amma tuni ya bayyana ga Armad an fisu yawa nesa ba kusa ba. Idan kowannensu zai kashe Ururu uku baza su ƙarar dasu ba. Dole ana buƙatar shiri na musamman.
"Armad," inji Najunanu. Armad ya juyo ya kalleshi. "Daɗewa ana yin wannan yaƙi bazai haifar mana da ɗa mai ido ba. Lissafin shi ne mu kwato Fatima da wuri kafin mutanen mu su ƙare."
"Kun tanadi likita?" Inji Armad. Yana ganin dole ana bukatar likita wanda zai ringa warkar da mayaƙansu. Idan ba haka ba kuwa zai zamo an fisu yawa kuma ga rauni.
"Mun tanadi likita, Armad," inji Najunanu.
"Likita? Guda ɗaya ta kenan?" Inji Armad.
Najunanu yayi murmushi.
"Armad, ka kwantar da hankalinka, duk abinda zakai tunani na yaƙi munzo dashi. Anfi mu yawa amma zaiyi wuya a fi mu shiri."
"To ko za'a gayamin shirin?" Inji Armad.
Najunanu yayi shiru kamar yana tantamar gaya masa. Bayan ɗan lokaci ya duka kunnensa yayi masa raɗa.
"Sannan kuma na kware akan kafi," inji Najunanu. "Indai naje kusa da kafin na sami minti guda to zan karya shi. Idan kafin ya sauka to dawa tayi nama."
"Hmm.." Armad ya ɗan ja numfashi. "Na fahimta. To amma baka ganin Ururu zasu yi tunanin zamu yi haka?"
Najunanu yayi murmushi.
"Armad kenan... To ai saboda sauƙin shirin shi yasa Ururu baza su taɓa tunanin zamu yi hakan ba. Na tabbatar suna lissafin wasu manya-manyan shirye-shirye da suke tunanin zamu yi. Babu wanda acikinsu zaiyi tunanin zamu shige su gaba da gaba. Kafin su ankara mun kwace Fatima mun fice."
"Ni zanyi gaba," inji Armad.
"Tsaya," inji Najunanu. "Kafin ka tafi mai zai hana kayi bayanin fasahar da kayi amfani da ita dazu?"
"Haaa... Wai baka mantaba?" Armad yayi murmushi. Ya fuskanci babu wata hanya da zai gujewa yin bayanin kansa domin kuwa fasahar ta ja hankalin mutane. "Eh... Kasan kowace rai akwai girman tsarin ruhinta. Kuma kuma kowanne tsarin ruhi akwai iyakacin adadin izzar da zai iya diba. Ni kaga tuni na cika wannan ka'ida. Ruhi na bazai karbi wata izza ba har sai na rage wadda take ciki. To yaya kake gani idan naƙi ragewa na kuma ci gaba da ƙara izza a jiki na?"
"Hakan zai sa tsarin ruhinka ya cika," inji Najunanu. "Idan ya cika ya batse baka daina tura izza ba sai ya...."
Najunanu ya haɗe gira. Ya fahimci abinda Armad ya aikata amma kuma ya kasa gane yadda abin yake.
"Armad, idan tsarin ruhinka ya cika ya batse fashewa zaiyi. Hakan zai sa ruhinka yayi bindiga ya fashe. Dole ka mutu. Babu wani mahaluki da zai iya ceto ka. Kada kace min haka kayi?"
Armad ya kaɗa kafada.
"Ai kuwa haka nayi, sai dai ba tsarin ruhina na fasa ba, na mutun-mutumina na fasa. Kaga idan ka kai kololuwa wajen sarrafa mutun-mutumi zaka iya haɗa shi da jikinka kasa ya maye gurbinka ba tare da kowa ya kula ba. Kafin nazo filin nan sai da na haɗa mutun-mutumi da ruhi na. Akwai bambamcin izza a tsakanina dashi saboda haka a duk sanda na saki izzata sai ta ringa fita tana shiga jikinsa. Da tsarin ruhinsa ya cika shi ne yayi bindiga."
"Amma hakan zai cutar dakai tunda jiki ɗaya kuka haɗa," inji Najunanu. "Watakila ya tarwatsa ruhinka ma. Ance a duk sanda ruhi ya fashe ƙarfin halitta yana fita wanda zai iya kashe komai."
"Eh hakane," inji Armad. "Shi yasa kafin ya fashe nake gudawa na barshi. Amma tunda mutun-mutumin yana da hankali da tunani dole sai na jira yazo gab da fashewa kafin na fita. Idan na fita da wuri to zai kare kansa ya saki izzar ta fice. Shi yasa bana son amfani da fasahar domin ina samun rauni a duk sanda nayi."
Najunanu ya ƙurawa Armad ido yana jimanta abun. Bayan ɗan lokaci ya zare takobinsa.
"Ba kai kaɗai zaka bada ranka akan Fatima ba, Armad," inji Najunanu. Da wannan Najunanu yayi sama ya dira a tsakiyar abokan gaba.
Armad ya juyo wajen su Nusi.
"Tunda sun tari juna gaba-da-gaba mai zai hana mu kai musu hari ta can gefen?" Armad ya nuna can gefen filin jiri inda Ƙaraiƙisu ya faɗa. "Ta haka zamu raba musu hankali sannan mu raba ƙarfin rundunarsu."
"Ta yaya zamu ratsa wannan filin?" Inji Nazára, ya nuna filin yaƙin inda aka kacame. "Sai dai idan da Aiban'shisu zaka kai mu."
"Akwai hatsari wajen amfani da Aiban'shisu tare daku," inji Armad. "A gidan abokan gaba muke. Watakila sun saka kafi a ko'ina. Idan muka shiga muka maƙale shikenan. Ni zan iya fita to amma ku fa?"
Asifu yayi murmushi.
"Armad, kada ka damu, duk wanda ya fito filin yaƙi ai yasan hatsari ya fito nema. Idan mun maƙale ka tafi ka barmu."
Nusi ta gyaɗa kai cikin amincewa. Lallai akwai yiwuwar Ururu sunyi kafi acikin filin yaki. Abinda kawai suke jira mutun ya shiga su kaddamar da kafin. To amma ko kaɗan hakan bazai tsorata su ba. Idan sun maƙale Armad ya tafi ya bar su.
"Bazan tafi na barku ba," inji Armad. "Sai dai ku yadda idan mun maƙale to mun maƙale a tare. Mu shiga tare, mu fita tare."
"Armad," inji jan doki. "Ban taɓa tunanin zan shigar maka yaƙi ba, amma yau gashi nazo. Bani da masaniyar zan koma ko bazan koma ba. Amma abinda ya kawo ni shi ne na kubutar da Fatima. Idan na mutu akan hanya a tafi a barni."
"Idan na tafi na barka waye zai taimaka min na yaƙi waɗancan?" Armad ya nuna inda su Dul'Ururu suke tsaye. "Ba wannan ne karo na farko dana shiga yaƙi ba. Na fahimci mai kuke nufi. Sai dai ban yadda kowa ya mutu a yau ba. Kuyi sani ina buƙatar ku bayan yau. Yadda muka zoa tare haka zamu koma."
Suka kalli juna sannan suka kalli Armad. Kowa ya buɗe baki zaiyi magana sai ya fasa idan suka haɗa ido da Armad.
Giwa ta matso kusa da Nusi ta ce, "Ran sarauniya ya daɗe, na fara fahimtar mai yasa kike girmamashi."
Nusi tayi mata murmushi. Indai halin Armad na dattaku ne ai Giwa bata ga komai ba.
Armad ya taka ya fara tafiya. Nusi, Cokali, Giwa, sarkin Bai, Inyaya, Shísu, da Barilu suka tsaya a ɓarin damansa. Nazára, Asifu Ruwan Bala'i da kwamanda jan doki suka tsaya a hagu. Mutun goma-sha-ɗaya wanda amana ta haɗa. Dukkansu sun aminta da tafiyar Armad. A wannan rana sunyi shirin yaƙi domin gidan Wilbafos.
"Aiban'shisu!"
Armad ya kira ɗalasimi. Ƙasar dake ƙarƙashin ƙafafunsu ta fara haske. A wani yanayi mai ban al'ajabi ƙasar ta ɓubɓugo tayo sama. Tarin fasassun duwatsu ya maye gurbinta. A can gaba kuma Armad ne ya bayyana tare da mutanensa a dai-dai inda Ƙaraiƙisu ya fado. Ƙasar dake ƙasan ƙafarsu ta maye gurbin katangar data fadi. Daga inda suke ratar dake tsakaninsu da inda Fatima take bata da yawa sosai. Sai dai tarin mayaƙan Ururu marasa adadi.
Armad ya duba gefen dama da hagu baiji kafi ba.
"Ku duba gefenku ko akwai kafi," inji Armad. Zaiyi mamaki ace Ururu sun bar wajen babu kafi musamman duba ga cewa wajen yana kusa da inda Fatima take. Idan shi ne to zai binne kafi a gurare daban-daban wanda zasu hana kowa wucewa.
"Babu kafi anan," inji Nusi.
"Nima babu anan," inji Nazára.
Dukkansu suka kalli juna. Wata zuciyar tana gaya musu akwai matsala. Babu yadda za'ai Ururu suƙi kare gidansu.
"To yanzu jira zamu yi ko kuwa mu afka musu," inji Inyaya.
"Ai mun riga mun janyo hankalinsu," inji sarkin yaƙi Barilu yana nuna mayaƙan Ururu da hannu wanda kawo yanzu sun kewayesu.
Kowa ya juyo wajen Armad yana jiran umarni.
Armad ya zare takobi yayi tsalle kan abokan gaba. Nusi da Nazára suka bi bayansa. Sauran mutanen suka rufa musu baya.
A halin yanzu zaka iya cewa rundunar Maikiro'Abbas ta rabu gida biyu. Ɓangaren su Armad wanda suke gab da wajen da Fatima take. Da kuma asalin rundunar wanda suke baya suna fafatawa da mayaƙan Ururu.
A wannan ɓangare akwai Armad. A wancan ɓangaren kuma Najunanu ne yake sharafinsa. Maikiro'Abbas da salsansa suna tsaye suna nazarin yaƙin kamar yadda Dul'Ururu yake baya yana kallo.
Armad ya danna cikin mayaƙan Ururu suka tunkari Fatima. Mayaƙan Ururu sukai kukan kura suka tare su. Armad ya ɗaga hannu zai kawar dasu sai Inyaya ya shige gaba.
"A barni dasu, sarki," inji Inyaya. Kafin ya rufe bakinsa ya saukar da takobinsa akan wuyan sadaukin dake gaban Armad yana ƙoƙarin kai masa sara. Takobin ta shige wuyan sadaukin. Jini yayi feshi sama inda sadaukin ya yanke jiki ya faɗi. A wani salo na kwarewa sai Inyaya yasa ɓarin takobinsa ya mari jinin kafin ya zuba a ƙasa. Jinin ya rarrabu dunkule-dunkule yayi kan abokan gaba kamar an watsa tsakuwa.
Mutun na farko da jinin ya taɓa sai da yayi tsalle sama sannan ya faɗo ƙasa tim a sume. Duk wanda jinin ya taɓa sai kaga yayi sama ya faɗo ƙasa a sume. Babu rauni a fili amma ta ciki ƙasusuwa sun ɓalle. Cikin ƴan dakiku hanya ta samu.
Armad ya kalli Inyaya takobin jini ya jinjina masa ta hanyar gyaɗa kai. Ba tare da cewa komai ba tawagar Armad suka danna kai. Inyaya yana gaba yana aiki. A duk sanda mayaƙan Ururu sukai ƙoƙarin tare musu hanya sai kaga ya sare kan guda ɗaya sannan yayi amfani da jini ya tarwatsa su.
A haka suka yi tafiyar minti guda. Ba jimawa wata tawaga ta tari gabansu.
Sarkin yaƙi Barilu ya dirar musu. Babu makami a hannunsa amma kuma shiga gabansu kaɗai da yayi sai da suka tsaya.
"A wannan yaƙi anfi ƙarfinku," inji Barilu. "Anfi ku yawa, anfi ku ƙarfi, mai zai hana bazaku juya ku gudu ba, ko kuma kuje ku tari dai-dai ku?"
Abin mamaki sai kawai mayaƙan Ururu suka fara kallon juna. A idanunsu akwai kokwanto. Wasu daga cikinsu sun yadda da maganar Barilu. Wasu kuma suna ganin akwai gyara aciki. Amma dai babu wanda yake ganin karya Barilu yayi.
"Hakane," inji Barilu. "Abinda na faɗa gaskiya ne. Anfi ƙarfin ku. Abinda yafi dacewa shi ne ku tari dai-dai daku. Ga waccan rundunar ta bayan mu ita ce dai-dai daku." Barilu ya nuna rundunar Maikiro'Abbas dake baya.
Abin mamaki sai kawai wasu daga cikin mayaƙan suka fara juyawa suna yin baya.
"Ku mahaukata," shugaban tafiyar ya daka musu tsawa. "Kada ku saurare shi. Ku kashe su."
Mayaƙan suka yi firgigit suka fara sosa idanunsu kamar wanda suka farka daga barci. A lokacin suka fara tambayar kansu mai ya faru. Wai tayaya suka ji maganar abokin gaba? Har ma suke ƙoƙarin guduwa. Wannan wace irin izza ce?
"Kai ƙaramin bil'adama," shugaban tafiyan ya dakawa Barilu tsawa. "Izzar ka bata aiki a kaina." Ya juya wajen mayaƙansa. "Ku kashe shi."
"Anya kuwa," inji Barilu yana gyaɗa kafaɗa. "Ni kuwa ina ganin kamar fasaha ta tayi aiki a kanka domin ga abokaina can sunyi gaba." Barilu ya nuna tawagar su Armad wadda tuni tayi gaba.
Shugaban tafiyar ya haɗe gira tare da sosai ido. Ko kaɗan bai kula da sanda su Armad suka wuce ba. Watakila a ƙoƙarinsa ya hana mayaƙansa tafiya abokin faɗansa yayi amfani da damar ya yaudare shi. Koma dai yaya ake ciki bazai yadda da wannan cin mutuncin ba.
Yayi kururuwa ya kawowa Barilu sara da fafalo.
"Ni ne kyaftin Tangile. Ƙarya kake kayi nasara akaina."
Barilu ya kauce ta hanyar sunkuyawa. Sai dai kafin ya dira ya lura cewa fafalon baki biyu ne dashi. Ya juya ta ƙarfin tsiya a sama. A sakamakon haka ya tade da ƙafarsa ta baya ya hantsila ya buge kai.
Kyaftin Tangile yayi dariyar mugunta. Yau ya kama nama.
"Tsaya-tsaya," Barilu ya ɗaga hannu cikin miƙa wuya. "A zahiri ni ɗin ba wani ƙarfi ne dani ba. Tabbas ban kai matsayin yin faɗa da kyaftin ba." Yana magana yana ja da baya.
Kyaftin Tangile ya wage baki. Ya rasa dariya zaiyi ko kuka.
"Kaga fa dalilin da yasa suke kirana da sarkin yakiBarilu ba wani abu bane saboda ina da baki. Duk abinda na faɗawa mayaƙa a filin daga zasu yi. Amma a zahiri Sarkin Bai shi ne sarkin yaƙin garin mu. Kana yiwa ALLAH kada ka kasheni."
"Mtwsss..." Tangile yaja wani dogon tsaki. A hankali ya sauke fafalonsa ƙasa. "Baka cancanci ka mutu a hannu na ba." Ya juya wajen mayaƙansa. "Ku sare kansa."
Mayaƙan wanda daman a fusace suke suka yi kan Barilu. Kafin su ƙarasa wasu jajaye tsakuwoyi suka saukar musu. Idan ka lura zaka fuskanci kowace tsakuwa jini ne kawai ya dunkule.
"Mai yasa ka daɗe?" Inji Barilu yana kallon Inyaya wanda ya bayyana a gabansa.
Inyaya ya nuna bayansa inda ya baro. A kwance a wajen mutane ne sun kai hamsin wanda Inyaya ya kaɗe. Barilu ya haɗiyi yawu.
"Yanzu meye abinyi to?" Inji Barilu.
"Abinyi muje mubi bayan Nusi-ya," inji Inyaya. Duk harin daya zo ta baya mu kare mata shi.
"Hmm.. Inyaya kenan, kana tunani wannan mutanen dake tsakanin mu da ita zasu bari mu wuce?"
Barilu ya nuna dubunnan mutanen da suka shiga tsakaninsu dasu Armad a ɗan lokacin daya wuce. Inyaya ya jinjina mutanen.
"Da wannan dan wannan kuma fa," inji Inyaya. "Amma haka aka bada umarnin. Mu buɗe hanya sannan mu bisu a baya. Bamu da lokacin tsayawa muyi faɗa dasu baki ɗaya."
Suna cikin wannan tattaunawa sai Armad ya bayyana a gabansu.
"Sunana Armad 3," inji mutun-mutumin. "An haifeni bayan an haifi Armad 2. Sannan kuma bayan Ni akwai Armad 4. Aikina na ɗebi mutane na kai su duk inda suke so a filin yaƙin nan. Ina kuke so na kai ku?"
Inyaya da Barilu suka tsaya suna kallon ikon ALLAH. A kullum kada mai karatu ya manta fasaha da izza abubuwa ne wanda basu yawaita ba a sashin ikwatora. Hakan yasan idan mutanen ikwatora suka ga babbar fasaha sai kaga sun cika da mamaki.
Inyaya ya juya wajen rundunar Maikiro'Abbas wadda yake can baya suna fafatawa da mayaƙan Ururu.
"Mai zai hana ka ɗauko gaba ɗayan rundunar mu ka kawo ta nan? Idan kayi hakan zaka fi taimakawa wajen raba hankalin Ururu saɓanin ace mu kaɗai ka ɗiba."
Armad 3 ya girgiza kai.
"Bazan iya amfani da fasahar Aiban'shisu ba balle na ɗibi mutane da yawa," inji Armad 3. "Kaban'Zhisu kaɗai nake iyawa. Sai dai idan ɗaya bayan ɗaya zan ɗakko su. Kada dai ku manta duk sanda nayi amfani da izza a jikin Armad ake ɗiba. Yace na gaya muku kada ku saka ni aiki sai dole domin a duk sanda muke aiki izzarsa tana raguwa."
Inyaya yayi ajiyar zuciya. Ga dukkan alamu lissafin dayake bazai yiwu ba.
"To," inji Barilu. "Ɗauke mu ka kai mu wajen su Armad."
"To," inji Armad 3. Ya matso zai ɗora hannu a kansu sai Inyaya ya ɗaga masa hannu. "Kada ka ƙarasa damu wajen su, a dai-dai bayansu zaka ajiye mu."
Armad 3 ya gyaɗa kai. Sai dai kafin ya taɓa su kyaftin Tangile ya kawo musu sara.
"Kuna tunanin barin ku zanyi ku tafi?"
Inyaya da Barilu suka dare saran ya faɗo a ƙasa. Hannun Armad 3 ya sauka akan Inyaya. Kafin kowa ya ankare Inyaya da Armad 3 sun ɓace. Aka bar Barilu da fusataccen kyaftin Tangile da kuma mayaƙan Ururu a kewaye dasu.
Barilu yaji kamar yayi kuka dan baƙin ciki.
"Ni ya kamata ka fara ɗauka, Armad 3," inji Barilu.
Tangile ya kawo masa sara. Ya kauce amma duk da haka sai da ya goge shi a kafaɗa.
Wasu mayaƙa huɗu suka zare kibiya zasu harbe shi.
"Ku tsaya," inji Barilu. "Ni ba abokin gabar ku bane."
"Ku harbe shi nace," inji Tangile. "Kada ku bari yayi magana. Inda dama ku saka wani abu ku toshe kunnen ku."
Da farko maharban sun ɗan fara kokwanto amma jin muryar Tangile yasa suka saki kibiyar a fusace.
A lokacin Barilu ya ɗebe haso daga wannan duniya. Tabbas bashi da ƙarfin kubuta daga wannan waje da kansa. Saboda haka ya rufe ido kurum yana jiran tsammani.
"Kaban'Zhisu!"
Armad 3 ya bayyana ya ɗauke shi. A lokacin daya buɗe ido bai ga kyaftin Tangile ba, bai kuma ga kibiya ba, a kusa dashi Inyaya ne a tsaya yana kallonsa. A gabansu kaɗan tawagar su Armad ce take ƙara tafiya tana kusantar inda Fatima take.
"Armad 3," inji Barilu. "Nan gaba ni zaka fara ɗauka ba Inyaya ba, kaji?"
Inyaya yayi dariya. Shi kuwa Armad 3 kyada kai yayi cikin amincewa.
"Barilu," inji Inyaya. "Idan ka huta akwai aiki a gaban mu." Ya nuna masa dubunnan mayaƙan Ururu dake kewaye dasu a fusace.
Barilu ya miƙe cikin shiri. Tabbas bai shirya mutuwa a yau ba, kuma hanya guda dazai tabbatar bai mutu ba shi ne ya kaɗe abokan gaba.
"Ku tsaya cak a inda kuke. Ni sunana Barilu. Asali na ɗan ƙabilar Shantu ne saboda haka ni ba abokin gaba bane."
A yayin da Inyaya da Barilu suke tare bayan su Armad, ta gaba mai unguwa Shísu shi ne yake sharafinsa. Komai yawan kibban da aka harbo musu sai kaga sun kauce musu da zarar Shísu ya ɗaga hannu. Hannunsa ya zama kamar wani mayan ƙarfe wanda yake tare duk abin da aka harbo masu.
Zuwa wannan lokaci tuni mayaƙan Ururu suka fuskanci harbi ko suka bazai yi aiki akan su Armad ba zarar Shísu yana tare dasu. Hakan yasa suka yanke shawarar su fara ɗauke Shísu. Mutun ɗari suka haɗa hannu guri guda suka samar da wata bulala ta wuta.
Suka cillota kan Shísu.
Sarkin Bai ya zare wuƙa daga ɗamararsa ya tunkari bulalar. Shin wuƙa wadda aka samar daga ƙarfe zata iya yanka bulalar da aka samar daga wuta? Ai kamar misalin ƙarfe da wuta ne. Wuta ita ce zata narka ƙarfe amma ƙarfe bazai iya yanka wuta ba. Haka al'adar take.
Duk da haka dai su Armad basu tsaya ba. Haka kuma Shísu da sarkin Bai basu tsaya ba. Kamar zaka iya cewa mayaƙan Ururu ƙoƙari suke yi su tsayar dasu domin su hana su zuwa gurin da Fatima take. Su kuma su Armad sunƙi tsayawa.
Bulalar wutar tana matsowa kan Shísu tana ƙara ruruwa. Su kuma mutun ɗarin da suka samar da ita suna ƙara kiran ɗalasimai domin su ƙara mata zafi. Sarkin Bai ya shiga gaban bulalar ya kai mata sara da wuƙarsa.
Bulalar ta haɗu da wuƙar. Abin mamaki sai kawai dai-dai inda suka haɗu ya tarwatse tabi iska. Sarkin Bai ya matsa gefe kada hayaki ya ɓata shi. Sannan a wani salo na kwarewa ya sari gindin bulalar. Dai-dai inda ya sara ya ɓace. Mutun ɗarin da suka samar da wutar suka buɗe baki cikin mamaki suna kallon ikon ALLAH. Kafin su farfaɗo sarkin Bai ya bayyana a kusa dasu da ƴar ƙaramar wuƙarsa.
Da sauri ya cake wuƙar a wuyan na farko. Kafin jini ya fito ya zare ta ya caka ta a wuyan na gaba, sannan na gaba. Cikin sauri wanda ya saɓa da al'ada kafin jini ya fito a wuyan mutun na farko daya soka tuni ya cake mutun goma. Wasu sadaukai fusatattu masu marawa wanda aka soka baya suka ɗana baka suka harbo masa. Shísu ya shiga gaba ya ɗaga hannu. Take kibiyoyin suka dare suka basu hanya. Kafin su ƙara ɗana wata kibiyar sarkin Bai ya gama dasu.
Wani abin sha'awa shi ne ko tsayawa basu yi ba balle su Armad su wuce su. Kana gani kasan sarkin Bai da Shísu sun saba fita fili a tare.
Har yanzu dai babu abinda ya iya tare su Armad. A kowanne lokaci suna ƙara kusantar inda aka ajiye Fatima.
A can baya kuwa yaƙi ya rincabe. Wajen aƙalla mutun dubu hamsin ne suka rufarwa mutun dubu goman da Maikiro'Abbas yazo dasu. Babu imani babu tausayi. Kawai jini ne yake kwaranya.
Wani abun mamaki shi ne ya kamata ace kawo wannan lokaci an kai al'ummar Maikiro'Abbas ƙasa. Ko babu komai yawan ba ɗaya ba. Sannan kuma mayaƙan Ururu a gida suke. Sun saba faɗa a filin sun kuma san yadda yake. Sun san duk wani tudu ko kwari. Babu zancen ace zasu yi tuntube ko su fadi.
Wani ayarin mayaƙan Ururu goma-sha-ɗaya sun danno kai rundunar Maikiro'Abbas. Duk inda sukai sai dai kaga jini yana zuba. Kayukan bil'adama suna tsalle sama.
Abin mamakin wannan ayari ba kan Maikiro'Abbas suka yi ba. Hasalima gefe suka nufa hanyar fita daga filin saɓanin ragowar mayaƙan Ururu wanda suka rabu gida biyu: rabi sunyi kan Maikiro'Abbas, rabi kuma suna ƙoƙarin tare Najunanu su hanashi zuwa wajen Fatima.
Wannan ayari na mutum goma sha ɗaya suka ci gaba da tafiya. Ba jimawa suka ƙaraso inda zasu je. A hannun daman shugaban wannan ayari takobi ce fara, a hannunsa na hagu kuma farar iska ce wadda ta bayarda ƙawanya. Babu abinda iskar take yi sai ƙugi da ƙara. Tana kaɗawa kamar guguwar damuna.
Shugaban tafiyar ya ɗan karkato ƙasa daga kan dokinsa ya saka takobinsa ya sare kan wata mata dake durkushe a ƙasa tana shafawa wani mayaki magani a hannunsa inda aka sare shi.
Kan matar yayi sama. Jini ya feshe ko'ina. Mayaƙan Maikiro'Abbas dake gurin sukai ihu saboda razani. Babu abinda kake ji sai kiraye-kirayen sunan 'Rabi' da ake yi.
"Rabi!"
"Rabi!!"
Wani fusataccen sadauki yayi tsalle kan shugaban ayarin daya sare kan matar ya kai masa sara. Takobinsu ta haɗu da juna. Abin mamaki sai takobin shugaban ayarin ta shige cikin takobin sadaukin ta yanka ƙarfen sannan ta wuce ta samu hannunsa. Yayi ƙoƙarin sakar takobin domin ya tsira daga kaifin takobin Lilut amma hakan bai samu ba. Saurin Lilut ya kere nasa. Takobin Lilut ta sare yan-yatsu uku daga jikin hannun sadaukin. Ya buɗe baki zaiyi ihu amma Lilut ya danna masa iska a baki. Yana haɗiya kansa ya kumbura ya fashe.
Dole ragowar sadaukan suka ja baya suka bawa ayarin guri.
Shugaban ayarin ya sakko daga kan dokinsa ya fara zagaye jikin matar daya sarewa kai. Wani abun mamaki shi ne duk da an sare mata kai amma bata fadi ba.
A hankali sabuwar tsoka da jini da jijiya suka fara fitowa a wuyan matar. Cikin dakiku kaɗan sabon wuya ya bayyana. Sannu a hankali kokon kai ya fito. Sannan ƙwaƙwalwa ta samu. A hankali fata ta fito ta rufe komai. Sabon kai ya bayyana akan wuyan.
Shugaban ayarin da mutanen dake gurin duk babu wanda ya nuna alamun mamaki. Matar ta miƙe tsaye. A hankali ta juyo ta kalli shugaban ayarin wanda yayi dariya.
Comments
Post a Comment