Skip to main content

282: Mafarauci ya sauka (2)

 Babi na 282: Mafarauci ya Sauka (2)

***

Idan muka dawo wannan rana ta yau kuma, a dai-dai wannan lokaci Nostaljiya, Babara, Cokali da Iliyasisi suka dira a garin Faideba.


A wannan karan Babara ne ya shige gaba. Kowa ya nuna fasahar sa banda shi, sabida haka suna shiga garin ya afka kan sadaukan nan biyu masu suna Tagwayen-auni wanda suke fafatawa da Lamarudu. Asalin Babara sarkin Duba ne, kuma zaka iya cewa izzar sa tafi karkata zuwa sihirin duba saɓanin na hari. To amma hakan bashi ke nuna a fagen daga bashi da ta cewa ba. A baya munga yadda ya koyawa Armad amfani da yanayin-izza, mun kuma ga yadda ya farkar da fasahar Armad ta Sikai. A yanzu lokaci ne da shi ma zai nunawa duniya shirin sa. 


Babara ya ɗaga sandar sa sama ya daki ƙasa, lamarin da yasa hayaƙin Negrinki ya fita daga jikin sandar ya shige cikin ƙasa. Ganin abinda Babara yayi yasa kowa ya dawo hayyacin sa. Amma kafin su ankara ƙasar wajen ta fara girgiza tana darewa. Farin hayaƙin Negrinki ya fara fita daga cikin ramikan. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar ta juye izuwa taɓo mai tsananin danƙo. Taɓon ya kama ƙafafun su ya haɗiye. 


Ɗan wadan aljani mai farin kwalkwal ya bayyana a gefen Babara ya ɗora hannun sa akan taɓon, inda nan take taɓon ya fara cin jikin su. Ba jinawa ƙafafu suka fara murmushewa suna komawa yashi. Tun ana jin ihu har sai da aka daina ji. 


Bayan minti biyu babu komai sai taɓo.


Sunan aljanin Babara aljani Kilma'ata. Shi ne aljanin daya bawa Babara damar sarrafa ƙasa: ya buga ta ya gano abinda zai faru na gaibu, ya samar da taɓo daga yashi, ya juyarda tsoka izuwa ƙasa kamar yadda yakan iya samar da tsoka daga ƙasa. Yana kuma iya ɗaure ƙasa yayi tafiya doguwa cikin lokaci ƙanƙani. Kai anyi ittifaƙi indai faɗa a ƙasa za'ai to Babara ne zaiyi nasara. Da haka ya zama shugaban ƙungiyar duba ta duniya, kuma da haka a halin yanzu yake ƙoƙarin juya akalar yaƙin da ake. 


Sai dai zaka iya cewa akwai wani abin al'ajabi dake faruwa: kwamandun nan biyu da ake kira da Tagwayen-auni sun cika bujen su da iska. Kowannen su ƙoƙari yake ya arcewa na kusa dashi. Wasu mutun-mutumi na taɓo guda biyu na bin su da gudu a baya kamar jela. 


Babara ya zama jan gwarzo. A hannun sa na hagu akwai farin hayaƙin Negrinki yana juyawa, a daman sa kuma akwai aljani Kilma'ata, sannan a gaban sa kuma akwai wata ƴar fadama cike da taɓo. Acikin abubuwan nan uku kowanne zai iya cinye runduna. Lallai Babara ya cancanci kasancewa acikin tawagar Armad. 


Ana haka aka jiyo muryar mutanen Lamarudu na kiran sunan Babara cikin yabo da godiya. 


"Babara! Babara!! Babara!!!"


Da dama suna ganin da ace tun farko Babara yana wajen da yaƙin bai ɗau lokaci ba. 


A ɗaya ɓangaren kuma Lamarudu baiji daɗin hakan ba. Dashi da Babara duk matsayin kwamanda suke a tafiyar. Abinda zai bayyana wanda yafi wani shi ne gudunmawar daka bayar a fagen daga. Zaka iya cewa Babara taimakawa Lamarudu yayi, to amma Lamarudu zai so ace shi ne da kansa yayi nasara ba tare da an kawo masa agaji ba. Koba komai Armad ne da kansa ya saka shi ya jagoranci ƙungiyar sadaukai dubu goma sha biyar, badan komai ba sabida ya yadda dashi.


"Kayi ƙoƙari." Nostaljiya ta gayawa Lamarudu. Tana jin tunanin da yake yi kamar da baki yake faɗa. "Da badan kana nan ba da mun rasa mutane da yawa."


Nan take akai wani kallon kallo tsakanin Lamarudu da Babara. A zahiri wannan ba wani ɓoyayyen abu bane acikin kwamandun Armad guda takwas. A lokacin suna halwa kowa ƙoƙari yake ya wuce wani. Kowanne yana so ya zama mafi kusanci da Armad wanda hakan ya janyo goga kafaɗa a wasu lokutan. Armad baiyi magana ba sabida abin bai kai yawan da zai buƙaci ya shiga ba (yawancin irin wannan abubuwa idan babba ya shiga ƙara rikicewa suke), sannan kuma Armad yana gani gasa tsakanin ɗalibai tana ƙara hazaƙa. 


Amma a zahiri matsalar ta samo asali ne daga Nusi da Nostaljiya. Nostaljiya tana ganin ita ce mafi kusanci da Armad, kuma a lokuta da dama takanyi ƙoƙarin juya kwamadojin, lamarin da Nusi take ganin bazai yiwu ba. Kan kace kwabo Nusi ta janye Iliyasisi da Cokali da Nazara zuwa ɓangaren ta. Ita kuma Nostaljiya ta janye Inara da Lamarudu. Babara shi ne kaɗai baya tare da kowanne ɓangare: wato yana kan katanga. 


Wannan ɓangaran ci da Armad ya gani shi ne yasa ya haɗa Nostaljiya dasu Cokali, ita kuma Nusi ya haɗa ta da Inara da Lamarudu. Sannan ya jefa Babara a ɓangaren Nostaljiya sabida daidaito, shi kuma Nazara ya barshi tare da Nusi. 


"Muje ciki mu taimakawa su Nusi, nasan anan ma zaka ƙara nuna hazaƙa." Inji Nostaljiya. Kana jin sautin maganar ta kasan da wata a ƙas. Tirƙashi, kaji mata, a fagen yaƙi ma kishi suke.


***


A dai-dai lokacin da iyalan Armad ke ta ƙoƙarin burge shi, a tsakanin doron ƙasa ta biyu data uku wani dattijo ne ke kwance kan iska ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin kwanciyar hankali, kai kace kwance yake kan gadon sa. Wani dunƙulen hadari ya taru a ƙasan kansa yayi fulo dashi. 


Idan ka dubi ƙasa babu komai sararin samaniya mara iyaka ɗauke da hadari yana kewayawa. Idan kuwa ka ɗaga kan ka sama babu abinda zaka hango face filin sararin samaniya cike da taurari da gajimare suna iyo ta ko'ina. Lokaci-lokaci idan tauraruwa ta ɗauki hankalin dattijon sai kaga ya miƙa hannu ya damƙeta yana wasa da ita: ya fasa wata, ya kyale wata. Kai a wasu lokutan ma sai kaga ya zuƙo ruhi daga taskar ruhin sa ya saka acikin wata tauraruwar, lamarinda zai ƙarawa tauraruwar ƙarfi, ko kuma ya zuƙi ruhin tauraruwar ya ƙara a taskar sa. Idan kai duban tsanaki zaka fuskanci dattijon ba wani bane illa sarki Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu.


Hohoho... Da ace bayi sun san yadda ake wasa da ruhin su da basu yi jayayya ba.

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...