Skip to main content

344-345

 "Kaban'shisu!"


Armad ya bayyana acikin wannan gari. Yana bayyana ya ji jiri yana neman ɗibansa alamun a jikin katangar daya gifta akwai Tsari. Armad ya girgije ya kuma dawo hayyacinsa. Abu na farko daya fara yi shi ne juyarda rigarsa ta koma zilaika sabuwa irin ta mutanan wannan gari, sannan kuma ya samar da rawani ya naɗa kamar yadda yaga kowa yana yi. Ance idan ka shiga gari kaga kowa da jela kaima ka ɗaura taka, ko babu komai ka saje da mutan garin. 


Bayan Armad ya tabbatar zaiyi wuya a iya banbance shi daga sauran mutanen garin sai ya wuce cikin wannan gari. Ya wuce ta wani filin dambe inda ya tarar da maza an kwabe ana gabzar juna, ga yan kallo a gefe suna ta ihu da nishadi. Yaci gaba da tafiya inda ya hango wani ƙatoton gini mai toluwa a samansa da kuma farfajiya mai girman ta kewaye shi ta ko'ina. Yana ganin wannan gini ya tuna da masallacin da ya haɗu da Tarifil-fakta aciki. Irin gini ɗaya ne dasu babu wani banbanci. Hatta fentin kore ne iri ɗaya sak.


Armad yaci gaba da tafiya yana zagaya gari. Gashi dai yaga mayaƙan Ururu a tsaye a bakin ƙofar shiga amma kuma babu wani alamun tashin hankali acikin garin. Kowa sabgar gabansa kawai yake yi.


Bayan ɗan lokaci Armad ya gaji da zagayawa inda ya nemi waje ya zauna. Meye abinyi? 


"Malam, da ALLAH ina da tambaya?" Armad ya tsayar da wani mutum da zai wuce.


Mutumin ya juyo ya tsaya yana sauraro.


"Ina zan samu gidan jarida?"


Mutumin ya ɗan haɗe gira cikin mamakin. "Idan jarida zaka siya ka tare yara a hanya mana sabida gidan jaridar da nisa fa." Inji mutumin.


Mutumin bashi da masaniyar cewa nisa ba matsala bane idan kana da Kaban'shisu.


"Zan iya samun jaridar wata guda a gurinsu?" Armad ya tambaya a hankali. Shima idan zai samu a wajen na bakin hanyar yafi masa sauki. 


Mutumin ya girgiza kai. "A'a, gaskiya, ta yau da jiya kawai suke ajiye wa. Kabi wannan layin ka miƙe sosai zaka tadda yar kwalbati tayi gabas. Idan kabi ta zaka tadda titi. Kabi titin kayi ta tafiya. Idan baka gane ba ka tsaya tambaya."


Armad yayi godiya ya kama hanya. Ba jimawa ya iso kwalbatin. Da tambaya ya samu ya isa inda zashi - wato kamfanin jaridar Addeen.


Kai tsaye ya sayi duk wata jarida data fito tun daga wannan rana har zuwa wata guda daya wuce. Ya fito ya fara neman otal ɗin dazai kwana domin tuni dare ya fara yi. 


Yana cikin tafiya yazo masallacin daya wuce a baya. A lokacin yaga mutanen garin suna ta sauri sun wanke fuskokinsu da ƙafafunsu suna shiga cikin masallacin. Bayan ɗan tunani, Armad ya samu waje ya zauna yana kallon ikon ALLAH. Ko mai ake yi acikin masallacin? 


Yana zaune akayi kiran salla aka tada ikama. A hankali yaga an durkusa anyi sujuda sannan yaga an ɗago an ƙara tsayawa. Haka har saida aka yi sau uku. Bayan an kammala, mutane suka fara fitowa kowa yana yin nasa waje. Wasu yan tsirarun suka ci gaba da zama aciki suna maimata irin durkuson da suka gama yi a tare, amma a wannan lokaci sau biyu sukai suka katse. Ga dukkan alamu wani sirri ne na izza wanda bai sani ba, sabida haka koma mai ake ciki akwai wani mutun guda daya shige gaba ya jagoranci wannan al'amari na izza shi Armad zai tambaya. Watakila akwai izzar da zai koya a wannan gari mai ban al'ajabi. 


Ai kuwa haka akai, Armad ya jira har sai da wannan mutum ya fito ya nufi gida, shi kuma ya bishi a baya. Har suka isa gidan mutumin bai ga Armad ba. Kai har sai da Armad ya gaji ya bayyana kansa.


Mutumin fari ne mai dogon gemu wanda aka yiwa ƙunshi ya koma jajawur. Juyowa yayi a hankali ya kalli Armad a nutse ya ce, "sannun ka dan'uwa, akwai abinda kake buƙata?"


Armad ya ɗan ɗaga gira a hankali kafin ya matsa kusa ya ce, "wacce irin izza kake koyawa mutanen ka acikin gidan can?"


"Izza?" Mutumin yayi murmushi. "Ba komai ne izza ba. Wannan abu da kaga muna yi shi ake kira da 'salla' a addini na. Amma kai baƙo ne ko?"


Armad ta gyaɗa kai. "Ban daɗe da zuwa ba idan haka kake nufi."


"Lale marhaban, bakanka da zuwa garin Melmusa na ƙarƙashin ƙasa. Daga wacce nahiya kake?"


"Doron ƙasa ta uku."


Mutumin ya haɗe gira. "Daga SAMA kake?" 


Armad ya gyaɗa. 


Mutumin yayi shiru yana tunani kafin ya buɗe ƙofar gidansa yaja Armad ciki. "Shigo ciki."


Armad ya bishi suka shiga gidan. 


"Ka taɓa zuwa ƙarƙashin ƙasa ko wannan ne zuwanka na farko?"


"Na taɓa zuwa, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Menene?"


"Wanne ɓangare kake zuwa?"


"Daular denizawa nake zuwa. Ban taɓa zuwa nan ɓangaren naku ba," 


Mutumin ya turo baki a hasale. "Ah, haka zaka ce, ai ɓangaren denizawa baya cikin asalin daular ƙarƙashin ƙasa. Daga baya aka gina shi aka jona shi damu bayan anyi kamfen na farko a shekarun ƙarshe na Farkon Lokaci. Kaga asalin daular ƙarƙashin ƙasa ai garuruwa bakwai ne. Da Melmusa da Zurill da Da'if da Kumafta da Shunsa da Shadeniza da kuma Abindal. An rufe Shadeniza da Abindal amma Bihanzin ya buɗe su. A halin yanzu sarki Alu yana mulkin Melmusa da Zurill da Kumafta. Shi kuma Bihanzin yana mulkin Shadeniza da Shunsa da Abindal. Garin Da'if yana tsaka-tsaki: rabi mu, rabi Bihanzin. Acikin ƙauyuka goma sha ɗaya dake cikin garin mun ci bakwai da yaƙi, saura huɗu."


Armad yayi kasake yana sauraro. Wato a ƙarƙashin ƙasa akwai babbar dambarwar da take faruwa a yayinda kwata-kwata na sama basu san ana yi ba. To amma tun yaushe Bihanzin yake mulki a ƙarƙashin ƙasa? Shin tun yana sarkin jinzidal yake yi, ko kuma sai bayan ya sauka? Zaiyi wuya ace daga saukar sa daga muƙaminsa na sarkin jinzidal har ya kafu a ƙarƙashin ƙasa haka.


Mutumin ya dakko tasa ya dubawa Armad shayi shima ya zuba. Bayan sun zauna ya dubi Armad ya ce, "mai ya kawo ka garin mu? ALLAH yasa dai ba leken asiri kazo ba. Domin kuwa idan haka to dole na miƙa ka wajen sarki."


"Ba leken asiri nazo ba. Kuma zanyi murna idan kuka ci Bihanzin da yaƙi."


Mutumin yayi jim yana tunani. Can ya ɗago ya kalli Armad ya ce, "amma yaya akai ka iya huda Tsarin da aka saka aka raba duniyar sama data ƙasa har ka shigo nan? Kasan ko denizawa basa iya zuwa wannan yanki sabida Tsarin da aka saka aka raba mu dasu. Shi yasa ma da dama muke musu kallon suma mutan sama ne."


Armad ya kaɗa kafaɗa. "To nima dai bansan yadda akai nazo ba. Kawai nayi amfani da wata fasaha ce na bude ido na ganni anan."


Ba wannan ne karo na farko da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans tayi jifa dashi acikin lokaci ba. Zaka iya cewa wannan karan da sauki ma.


Mutumin yayi shiru yana tauna maganar. Akwai kokwanto a fuskarsa amma bai ƙaryata Armad ba.


"Ya sunan ka?"


"Armad Wilbafos suna na. Kai fa?"


"Umarul Abisi. Zaka iya kira na da Liman. Amma 'Wilbafos' tsohon suna ne. Ko a littafan mu zaka daɗe baka ji an ambace su ba. Idan banda abinda ƴar ƙabilarka ta aikata a ƴan kwanakin nan da zan iya cewa da dama an manta daku."


Armad ya kifta ido sau biyar a jere. Wacece ƴar ƙabilarsa? Hidaya? A'a, bazai yiwu ace Hidaya bace. To wace mace ce ta rage a ƙabilar sa?


"Ƴar ƙabilar Wilbafos kuma?"


"Eh mana, nasan ba lalle ka santa ba tunda dan kuna ƙabila ɗaya da mutun ba shi ne yake nuna dole kunsan juna ba."


Armad ya cafi hannun mutumin da sauri. "Gayamin, yaya sunanta?"


"Sunan ta Nusi Wilbafos."


Take Armad ya miƙe tsaye. "Nusi Wilbafos kuma?!"


"Eh mana, ko ka santa?" Mutumin ya miƙe ya zaro jarida a adakar dake bayansa ya nunawa Armad. "Kasan babar ta da kakan ta Ururu suka kama suka bayar a matsayin bayi ga wanda yayi nasara a wannan jinzidal ɗin da akai a doron ƙasa na biyu."


Armad ba sauraron abinda mutumin yake cewa yake ba. Idonsa na kan hoton Nusi dake damfare a shafin farko na jaridar. 


Daga ƙasan hoton an saka:


Nusi Wilbafos ta umarci a dawo mata da iyayenta ko kuma ta tarwatsa gasar jinzidal da za'ai ta bana. Ta bada wa'adin kwana uku; ko a dawo mata da iyayenta ko kuma ta hau sama ta zubar da jini.


Daga can ƙasa ga hoton Fatima da Zaikid nan a durkushe akan gwiwowinsu suna jira a bayar dasu ga duk wanda yayi nasara a gasar. To amma wani abu da yaja hankalin Armad shi ne kwanan watan jaridar. Idan akayi la'akari dashi to tuni an wuce ranar da aka tanada za'a gudanar da gasar jinzidal ɗin.


Liman ya tari numfashin sa ya ce, "tuni an gama gasar jinzidal kuma sarki ƙaraiƙisu shi ne yayi nasara."


"Tsaya-tsaya," Armad ya katse shi, "wane ƙaraiƙisun? Badai na sashin ikwatora ba?"


Liman ya gyaɗa kai. "Shi mana, wai kai duk baka san abinda ya faru ba? Ko baka duniyar ne. Muma da muke ƙasa labari yazo mana ballantana kai."


"Liman Umaru, ka ɗauka kawai duk abinda ya faru a wata guda daya wuce ban sani ba. Domin kuwa hakan ne, babu abinda nake iya tunawa a wata guda daya wuce. Kada ka tambaye ni dalili."


Liman ya ƙura masa ido cikin al'ajabi. Can bayan ɗan lokaci ya numfasa ya ce, "idan haka ne baka ma san abinda ya faru ba kenan bayan an gama gasar jinzidal ɗin?"


Armad ya gyaɗa kai tare da zaro jaridun daya siya daga aljihunsa ya ɗora su akan teburin ɗakin. "Ban san ma anyi gasar jinzidal ɗin ba. Shi yasa na siyo wannan jaridun ko zan samu bayani aciki. Gayamin, mai ya faru?"


Liman ya gyara zama. "Da farko kowa yayi tunanin da wasa Nusi Wilbafos take yi da tace zata kai farmaki, amma ana kammala gasar ta kai hari. An ɗanyi bata-kashi tsakanin ta da Haruta amma daga ƙarshe aka koro ta ƙasa. Bamu san hakikanin mai ya faru ba, watakila sabida harin da ta kai musu, sarki Dul'Ururu ya yanke shawarar ya kashe Fatima da Zaikid. Saboda haka ya siye su har kuɗin ayrid miliyan dubu daga hannun ƙaraiƙisu. Ance acikin yarjejeniya sai da Dul'Ururu ya yadda zasu bawa sashin ikwatora dama su ci gaba da cin gashin kansu. Daga ƙarshe dai ƙaraiƙisu ya siyarwa da Dul'Ururu Zaikid da Fatima kuma jibi ne ranar da za'a sare musu kai."


Lokaci guda Armad yaji wani jiri yana ɗibansa. Akwai abubuwa da dama da suka faru acikin wata guda kacal da baya nan. An gudanar da gasar jinzidal a doron ƙasa ta biyu. Da waye da waye suka taka rawa? Yaya akai ƙaraiƙisu wanda yake sashin ikwatora yazo ya taka rawa a gasar harma yayi nasara? Wai ana nufin ace anci ikwatora da yaƙi ne? Mai ya faru da Nusi? Ina ragowar mutanen sa da matarsa Nostaljiya? Wata guda kurum yayi bayanan amma komai ya rincabe. A wannan lokaci Armad ya yanke shawarar ya ajiye komai a gefe ya dawo da hankalin sa kan abu guda mafi muhimmanci wato zancen kashe mahaifiyar sa da kakansa da za'ai jibi. 


Armad ya dubi Liman yana haki. "Daga nan zuwa doron ƙasa ta biyu tafiyar kwana nawa ce?"


"Ai ba hanya," inji Liman, "dama can kasan doron ƙasa na biyu ba wajen zuwan na ƙasa bane. Dalilin da yasa a baya ita ma Nusi Wilbafos ta samu damar shiga sabida an sassauta takunkumin shigar ne saboda jinzidal ɗin da akai. Amma ana saka ranar yankewa Fatima da Zaikid hukunci aka rufe ko'ina. Babu wanda ya isa ya shiga ko ya fita daga doron ƙasa ta biyu. Tsaron yama fi na da. Naji jita-jitar Nusi tana haɗa runduna amma bata da amfani idan bata samu damar shiga doron ƙasa na biyu ba."


Armad yayi shiru ya rufe ido. Abin mamaki a wannan lokaci kawai sai yaji wata nutsuwa tazo masa. Saɓanin Armad ɗin da aka sani a baya wanda zai tashi hankalin sa ya rude a irin wannan yanayin, wannan Armad ne komawa yayi ya zauna ya nutsu ya fara tunani. Da ALLAH yaga dama to da bazai buɗe ido ba har sai an yanke hukuncin. Tunda kuwa ALLAH yasa ya farka kafin a yanke hukuncin to kuwa dole bazai bari wannan abu ya faru ba. Amma dole ne yayi tunani mai zurfi. Abokan faɗansa ba yara bane irin wanda ya fafata dasu a baya a gasar jinzidal ba. Abokan faɗansa manyan arna ne wanda suka daɗe suna yi, yana ji a ransa cewa suna sane suka sanar da kashe Fatima a jaridu domin kowa yaji. Domin kuwa da sun ga dama da zasu iya kashe ta a salin-alin babu wanda yaji. Kai da ace so suke su kashe ta to da tun farko zasu kashe ta ba tare da sun saka ta a matsayin kyauta a gasar jinzidal ba. Dole akwai wani makirci a ƙarƙashin ƙasa dake gudana wanda idan baiyi da gaske ba zai iya faɗawa ramin da suka haƙa masa. Dole bazai bari a kashe iyayensa yana gani ba. Komai wuya komai wahala, komai rintsi komai tsanani, sai ya kubutar dasu. To amma ta wace hanya ce zai bi ya aiwatar da hakan? Abu na farko da yazo ransa shi ne ya haɗu da Nusi domin yaji takamaiman mai ya faru. A zahiri ba komai aka rawaito a jarida zaka yadda dashi ba. 


Kamar yadda ba duk abinda Liman Umaru ya gaya masa zai yadda. Idan ma duk abinda Liman ya faɗa gaskiya ne to ai Liman a jarida ya gani domin dai bai je sama ya gani ba. Kuma zai iya kasancewa akwai abubuwa da dama wanda jaridar basu bayyana ba, ko kuma basu sani ba. Dole ya samu Nusi tunda ita ce a tsakiyar abin. Idan suka haɗu zaiji yadda akai aka haihu a ragaya. Daga nan sai su shirya abinda zasu yi.


"Liman, ina so zan koma sama, yaya za'ai?"


#






Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...