Babi na 140: Ƙabilar Shishirui
Wannan halitta ta runtse ido sannan ta dubi ɗaya kansakalin dake gefenta cikin murna tana magana da harshe bakwai. "Ranbirshishirui, kaji Baƙar wuta suke nema. Ga dukkan alamu zamu ga yaƙi mai ƙayatarwa. Rabona da ganin yaƙi irin wannan tun yaƙin Littafin-takobi."
Acikin muryar wannan halitta akwai farin ciki mabayyani, kai kace anyi mata albishir da dacewa. Kalmominta na ƙara zaƙi suna cika da murna duk bayan kalma ɗaya.
Can bayan ɗan lokaci ɗaya kansakalin ya juye izuwa irin halittar ta farko sai dai kayikansa sunkai goma. Sannan kowanne yana da ƙaho biyu. Wannan halittu biyu wani jinsi ne na daban, suba aljanu ba suba mutane ba kuma suba Dordor ba. Hasalima jinsin su abu ne ɓoyayye ga ilmin bil'adama. Na farkon sunansa Dandirshishirui, na biyun kuma Ranbirshishirui.
Yanbirshishirui ya girgiza kayikansa goma ya ce, "Sarki Wilbafos, sarki Kuyurussa'ayi, sarki Amraikugyu, Tarifil-fakta, dukkan waɗannan zamaninsu ya shuɗe amma sun bar baya da ƙura. Akwai matasa majiya ƙarfi wanda kowa ke ƙoƙarin karɓar mulkin duniya daga hannun Ururu. Idan aka ce na zaɓi ɗaya daga ciki wanda zai iya karawa da Ururu to Baƙar Wuta zan zaɓa."
Dandirshishirui ya fashe da dariyar murna yana cewa. "Amma fa Ranbirshishirui kada ka manta akwai ma'abota haƙiƙanin izza a doron ƙasa. Akwai Ikenga ɗan Odúdúwa jikan Bayájidda. Akwai sarki Maikiro'Abbas mahaliccin fasahar marubutan. Akwai sarakunan Jinzidal. Akwai wannan matashi na kwanannan Armad Wilbafos magajin Eyriyon Wilbafos. Ga kuma uwa uba, ɗan uwanmu, ɗan ƙabilarmu, Banzirshishirui, koda yake yanzu naji ance Bihanzin Mai Dauwamammen Sara suke ce masa. Nidai na zaɓi Bihanzin."
Ranbirshishirui ya ja dogon numfashi ya gyaɗa kayikansa sannan ya ce, "koma dai wanene, nan bada daɗewa ba za'a ware aya da tsakuwa."
Sarki Han'ibal da muƙarrabansa suna tsaye suna sauraron wannan tattaunawa mai cike da hikima. Bayan ɗan lokaci Ranbirshishirui ya juyo da hankalinsa kan sarki Han'ibal. "Ga dukkan alamu Han'ibal burinka ka hana Baƙar Wuta wucewa ta wannan ƙofa idan ta fito daga nahiyar aljanu."
Han'ibal yai murmushi mai cike da izza ya ce, "kayi gaskiya. Kuma nazo wannan waje domin nasan nance kaɗai hanya da za'a iya fitowa daga nahiyar aljanu zuwa ta mutane. Indai Baƙar Wuta ta tsaya acikin nahiyar aljanu bata fito yi mana shisshigi acikin yaƙinmu ba, to nima ba ruwana da ita. Amma indai ta fito sai dai a haifi wata."
***
Babi na 141: Filwa-De-Lisa
~Titin Bayajidda
~Filin yaƙi
Sai da dauwamammen saran Bihanzin ya ɗauki sama da daƙiƙa ashirin suna fafatawa da ƙasar kabarin Rafiyan Daljari kafin ya ɗauke. Ita kuma ƙasar kabarin ta zube ƙasa. Amma abin mamaki idan ka dubi inda saran ya ratsa zaka ganshi a rabe gida. Babu wata ƙasa ko kuma wata izza data isa ta ƙara haɗa wannan ƙasa a waje guda har duniya ta naɗe. Ta riga ta saru sara na har abada.
Bayan ƴan daƙiƙu ƙasa ta daina girgiza, duhun gari ya ɗauke komai ya dawo dai-dai.
Nan take Daljari ya ɗaga hannu sama tare da bawa muƙarrabansa umarni. Domin wannan sara na Bihanzin kamar wani alamu ne na take wasa.
Zaɓaɓɓun nan goma dake rundunar Daljari suka ja rundunar sadaukai dubu goma-goma suka fuskanci rundunar mutun dubu biyar-biyar dake rundunar Bihanzin. Amma duk da haka akwai ragowar sama da mutun dubu hamsin a bayan Daljari.
Daljari da Deniz Iluru da Dandil suka fuskanci Bihanzin da mutun ukun dake bayansa. Su kuma Deniz Bizaya da Yarima Niyashi da Asifu da Jan-doki da kwamandun nan biyu wato Tagwayen-auni suka fuskanci keken dokin da Nostaljiya ke ciki.
Uznu Ururu na gefe yana hange. Kana ganin idonsa kasan wani abu yake nema. Domin idan da ta son ransa ne da tuni ya cimma Armad to amma sauran sarakunan suka ƙi amincewa domin hakan zaisa iyalan Han'ibal acikin sharri.
Duba ɗaya tak zakaiwa filin kasan an ninka rundunar Bihanzin sau huɗu. Babbar dabarar da Bihanzin yayi shi ne saka keken dokin Nostaljiya a tsakiyar rundunarsa sannan kuma yasa ƴaƴansa biyu, Hasanu da Kiru, da kuma manyan kwamandu goma su tsare ta.
Nan take aka buga ƙugen yaƙi. Rundunar mutun dubu goma-goma suka afkawa rundunar Bihanzin. Ƙara da suka da ihun mazaje ya fara tashi. Jini ya fara ambaliya. Cikin ƙanƙanin lokaci banbanci ya fara bayyana. Rundunar Daljari ta fara danna ta Bihanzin. Ko ba komai sun ninka su yawa. Koda ace kowa acikin rundunar Bihanzin zai kashe mutun uku shi kaɗai baza suyi nasara ba.
Damjinu na ganin haka ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban ɗaya daga runduna goman. Ya zaro takobinsa yakai wawan sara. Abin mamaki takobinda bata fi tsayin hannu ba sai gata ta miƙe ta ƙara tsayi cikin daƙiƙa guda. Kan kace meye wannan takobin ta cake mutun na farko dake sauti, tsininta ya hudashi ya shige ta cikinsa sannan ya ƙara huda na bayansa sannan na bayansa. Abin mamaki tana shan jini tana ƙara gudu. Kan kace meye wannan takobin ta tsire mutun ɗari dake kan layi.
Ƴar ƙaramar takobinda bata fi tsayin hannu ba amma yanzu ta ƙaru zuwa nisan sama da kilomita. Damjinu ya motsa hannunsa, lamarinda yasa cikin ƙiftawar ido takobin ta zuƙe ta koma ƙarama babu ko alamu jini a jikinta. Idan baka wajen ƴan daƙiƙu da suka wuce baza ka taɓa yadda ita ce tai wannan aiki ba.
Koda ganin abinda ya faru sai rundunar suka ja daga suka tsaya. Kowa yasan waye ma'aboci wannan takobi a doron ƙasa. Kuma kowa yasan sunan wannan takobi wadda ake kira da FILWA-DE-LISA. Takobin sarkin yaƙin rundunar Bihanzin Damjinu Djinn. Takobinda bata da kaifi ko kaɗan, hasalima zaka iya shekara biyar kana ƙoƙarin yanka kayan miya da ita baka gama ba saboda tsabagen rashin kaifi. Abu ɗaya da wannan takobin take dashi shi ne tsini. Anyi ittafaƙi tsininta zai iya huda duk wani abu dake ban ƙasa, ko dutse ko ƙarfe.
Duk abinda ta huda tana zuƙar ruhinsa ta ƙara tsayi, ta haka take iya yin dogon zango wajen kai saƙo.
Nan take Damjinu ya ƙara miƙa hannu ya kai wani saran inda takobinsa ta tsire mutun ɗari dake gaba. Kan kace meye wannan yaƙi ya ɗau armashi. Ko'ina ka duba jini ke ambaliya.
Zaɓaɓɓu goman dake jagorantar rundunar suka afka kan mutun goma dake jagorantar rundunonin Bihanzin. Sauran sadaukai dake bayansu suka afkawa abokan karawarsu.
A gefe guda Damjinu kawai aiki yake. Sai dai kuma har yanzu a runduna ta farko yake. Kuma akwai ragowar runduna tara wadda babu abinda suke sai ƙara matsawa kusa da keken dokin da Nostaljiya ke ciki.
Ganin ya rage yawan runduna ta farko, Damjinu ya koma kan runduna ta biyu.
Sai dai kuma a gefe guda Deniz Bizaya ya jagoranci fitattu shida wanda suka haɗa da Niyashi da Jan-doki da Asifu da Kalhari da kuma kwamandun nan biyu na daular Han, wato Tagwayen-auni, suka tunkari keken dokin. Saboda ruguntsumi babu wanda ya gansu. Sannan kuma sunyi amfani da Farar-laya tayadda babu wanda zai iya jin yanayin izzarsu. Suka salallaɓa suka shige cikin ƙura suka ɓace. Kan kace meye wannan sun iso kusa da inda suke iya hangen keken dokin.
A dai-dai wannan lokaci Bihanzin yaji yanayin-izzarsu ya waiwaya cikin sauri zai kai sara wajen amma sarki Daljari ya tare shi yana cewa, "baka tunanin saika gama damu kafin ka tafi? Kada ka manta bayan ni akwai Deniz akwai Dandil sannan kuma ga Uznu Ururu."
Nan take Bihanzin ya juyo a fusace yana kallon Daljari. Mutun biyu dake bayansa, Naƙata da Dinandul suka zare takubbansu suka fuskanci sarakunan Jinzidal.
Nan take idanuwan Bihanzin suka kaɗa. Ya dubi Daljari ya ce, "banyi niyyar kashe ka ba amma idan baza ka matsa ba babu yadda zanyi." Yana rufe baki takobinsa ta fara ɗaukan zafi tana fitarda baƙin hayaƙi. A wannan lokaci fuka-fuki biyu baƙaƙe suka bayyana a bayan Bihanzin. Kafin wani ya ankara ya tashi sama ya tunkari wajen keken dokin.
Shi kuwa sarki Daljari wani baƙin al'amudi ya zaro daga cikin zobensa. Al'amudin bashi da girma amma kana ganinsa zaka fara jin rawar ɗari na shiga jikinka kamar kana kana zazzaɓi. Sannan ya murza kwangilarsa ta ƙasa, lamarinda yasa gaba ɗaya ƙasar da yake kai ta ɓamɓaro ta tashi sama dashi inda taje tasha gaban Bihanzin.
Ga ɗaya da baƙaƙen fuka-fuki irin na hankaka ga ɗaya yana tsaye akan faifan ƙasa akan iska. Lallai fafatawa tsakanin sarakunan Jinzidal babban al'amari ne.
Wakilin sarki Han'ibal wato Dandil ya hau kan Dinandul, shi kuma sarki Deniz Iluru ya afkawa Naƙata.
A yayinda sarakunan Jinzidal biyu wato Bihanzin da Rafiya suka baje fili za'a ware raini shi kuwa Uznu Ururu nazarin yaƙin kawai yake yana rubuta ƙarfin kowa kamar yadda shugabansa Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu, ya aiyana masa.
Daman sun daɗe suna so su tabbatar da maganar da ake cewa fasahar Bihanzin ta Yanayin-izza tafi ƙarfin Farar-laya amma sai yau ya gani da idonsa. Domin kuwa a gabansa su Bizaya suka rufe kansu da farar-laya amma duk da haka saida Bihanzin ya gano su.
A gefe guda kuma yasan sarki Deniz zai iya gamawa da Naƙata cikin ƙanƙanin lokaci domin babu wani mahaluƙi daya taɓa karawa da sarkin Jinzidal yai nasara sai Ururu. Sai dai kuma yaƙi tsakanin Naƙata da Dandil sai an tashi. Shima tsakanin Bihanzin da Daljari sai an tashi.
Nan take Uznu Ururu ya fara aikawa da Dul'Ururu saƙon wannan yaƙi ta wata irin fasaha mai amfani da idanuwansa na Ururu. Wannan fasaha ana kiranta da suna SHANKIL.
Ta hanyar fasahar Shankil ma'aboci Ururu zai iya nunawa ɗan'uwansa ma'aboci Ururu yaga abinda yake gani komai nisan dake tsakaninsu. Abinda ka gani shima ya gani kamar yana wajen.
***
Babi na 142: Farkawa
Kan kace meye wannan su Bizaya sun ƙarasa kusa da keken dokin, abinka da fitattun ma'abota izza. Nan take su Hasanu suka kewaye keken dokin tare da zare makamansu. Nan fa aka ja daga.
Filin yaƙi ya rabu kaso uku. A ɓangare ɗaya rundunar dubunnan sadaukai na fafatawa, a inda sarkin yaƙi Damjinu yake ƙoƙarin tare su. A wani ɓangaren kuma sarakunan jinzidal ne ke fafatawa, a yayinda Uznu Ururu ke nazarin izzar kowa acikinsu. A ɗaya ɓangaren kuma yarima Bizaya ne da mutanensa ke kewaye da keken dokin suna niyyar afka masa.
Babu abinda kake ji sai kururuwar mazaje da ƙarar takubba da masu.
Hasanu Sisiyu ya dubi Bizaya a hasale ya ce, "kai yanzu saboda tace bata sonka shi ne kake so ka kashe ta kowa ya rasa? Lallai ka cika butulu, musamman duba ga cewa ƴar uwarka kake so ka kashe."
Abu ne sananne matar Bihanzin wato babarsu Hasanu ƴar asalin ƙabilar Deniz ce wato badeniziya ce. Saboda haka a har kullum akan dubi ƴaƴan sarautar daular Sisiya a matsayin ƴan uwan Denizawa na nesa.
Bizaya najin haka ya kyalkyale da dariya ya ce, "Koma mai zaka ce bakin alƙalami ya riga ya bushe. Lokaci yayi." Yana gama magana ya tafa hannayensa tare da kiran ɗalasimai. Lamarinda yasa manyan ƙusoshin yaƙi biyar suka bayyana suka zagaye keken dokin.
Hasanu na ganin haka ya zaro takobinsa ya kai sara kan ƙusoshin, inda wata guguwa, launin ja, ta tashi daga jinin takobin ta cimma ƙusoshin. Suna haɗuwa wata wuta ta miƙe sama, ƙasa ta fara girgiza. Kan kace meye wannan ƙusoshin sun zuƙe iskar suma sun ɓace.
Bizaya yai tsalle yakai sara kan Hasanu amma Hasanu ya tare da tasa takobin shima ya mayar masa. Kan kace meye wannan sun fara ɗauki ba daɗi. Cikin ƙanƙanin lokaci sun kaiwa juna sara da suka sama da ashirin.
Rafiyan Nazára wanda akafi sani da yarima Niyashi yai kan yarima Kiru da suka da mashinsa inda shima Kiru ya zare takobinsa da akafi sani da Farar-takobi ya maida martani. Kiru na zare takobinsa walƙiya ta cika wajen, suna haɗuwa da mashin wata ƙara mai kama da saukar aradu ta tashi kai kace ana fasa dutsen uhudu. Sannan kuma ƙura ta biyo baya inda ta turnuƙe sararin samaniya. Dukkan wannan abubuwa sara ɗaya ne kacal, lallai da Armad yana nan da kallo ɗaya tak zai gane wannan takobi, domin kuwa ita ce takobin daya fafata da ita a haɗuwarsu ta farko da Nostaljiya. Nan take suka kaure da azababben yaƙi. Kowa na neman yadda zai kashe ɗan'uwansa.
A gefe guda, Kalhari da Tagawayen-auni ne suka afkawa sadaukan nan takwas dake gadin keken dokin. To abinka da banbancin izza, cikin ƙanƙanin lokaci Kalhari da Tagwayen-auni suka halaka mutun bakwai cikin takwas. Koda yake idan ka duba zaka ga cewa ba matsayinsu ɗaya ba, domin kuwa Kalhari matsayi ɗaya yake da sarkin yaƙi Damjinu kuma matsayi ɗaya suke da Tagwayen-auni, su kuwa wannan kwamandu takwas basu kai ba.
A dai-dai wannan lokaci Asifu wanda ake kira da Ruwan-bala'i da kuma kwamanda Jan-doki suka rufarwa keken-dokin.
Suna ganin abinda ke faruwa, Hasanu da Kiru suka bar inda suke suka dawo gefen akwatin suka tsaya a wani salo na ko'a mutu ko'ai rai. Kana ganinsu kasan sun shirya mutuwa akan ƴar'uwarsu.
Koda ganin haka sai su Bizaya suka fashe da dariya. Domin sun san babu yadda za'ai mutun biyu kaɗai su iya tare su.
A dai-dai wannan lokaci manyan sarakunan Jinzidal na tsaye sun ɗan dakata da fafatawarsu suna kallon abinda ke faruwa a gefen keken dokin.
Sarki Daljari yai murmushi yana cewa, "kaɗan ka gani Bihanzin. Bari kaga aiki da cikawa." Yana rufe baki ya bawa dakarun dake tsaye a bayansa umarni su afkawa rundunar Bihanzin.
Nan take mutun dubu ɗari sukai kuwwa suka afka kansu. Kan kace meye wannan an haɗiye rundunar Bihanzin ko alamunsu ba'a ganowa. Idan ka gano wata bajinta to sarkin yaƙi Damjinu ne ke aiki. Cikin ƙanƙanin lokaci yaƙi ya canja salo. Gashi ana gabda kama Nostaljiya, gashi rundunar Bihanzin na gabda ƙarewa, gashi kuma Bihanzin da Naƙata da Dandil basu da damar kai agaji domin sarakunan Jinzidal na gabansu.
A gefe guda Uznu Ururu na nazarin al'amura. Ga dukkan alamu yaƙin bazai ɗau lokaci ba kamar yadda yai tunani a farko.
***
Acikin wani kogo dake can nesa da filin daga, Armad ne kwance yana jinya. Inara da Iliyasis da Cokali tare da muƙarrabansa goma na zaune a gefe suna jiran farkawarsa.
Har zuwa yanzu babu alamun farkawarsa. Kana kallonsu kasan kowa yana cikin alhini domin tuni labarin abinda ke faruwa a filin daga ya zo musu. Lallai ana buƙatar agajinsu sai dai kuma basa so su bar Armad kwance acikin wannan hali.
Iliyasis ya tunkari inda Armad ke kwance ya zauna a gefe. Bayan ɗan lokaci ya dubi Armad cikin kokwanto sannan daga bisani ya fara jawabi. "Mai ɗakinka Zahra na cikin mawuyacin hali a filin daga. Mai ɗakinka Zahra na cikin mawuyacin hali a filin daga. Mai ɗakinka Zahra na cikin mawuyacin hali a filin daga."
Bayan ya maimaita sau uku saiya rufe ido yaci gaba da bayani. "Idan baka farka ba lallai rayuwarta zata iya salwanta. Na yanke shawarar zuwa na taimaketa. Zan fita filin daga nayi yaƙi na kare ta a maimakon ka, idan ka farka ina nan da rai shikenan, idan kuma an halaka ni a filin yaƙi wannan ita ce bankwana ta a gareka, aboki na, Armad Wilbafos."
Koda gama wannan jawabi sai Iliyasis ya saɓa takobinsa ya nufi ƙofar kogon. Sai da yakai gabda bakin ƙofar ya waiwayo ya ce, "duk wanda ya shirya mutuwa a yau ya biyoni. Wanda keson mutuwa gobe ya zauna yayi jinyar Armad. Nidai na tafi filin daga." Koda jin haka mutanen cikin kogon suka zare ido cikin mamakin maganganunsa. Amma Iliyasis ko'a jikinsa, juyawa kawai yai ya nufi ƙofa.
Yana gabda ficewa Armad ya buɗe idanunsa yaja dogon numfashi. Sannan ya miƙe zaune. Da farko idanunsa sunyi kalar bacci amma ba jimawa suka wartsake. Ya ɗaga hannunsa na hagu ya gwada juyar dashi izuwa walƙiya, inda hannun ya juye. Koda ganin haka sai Armad yasan lallai izzarsa ta dawo. Nan take ya miƙe ya fara shirin yaƙi ba tare cewa komai ba.
Kowa ya ƙame ya kasa magana. Hatta Iliyasis bakinsa a buɗe yake saboda mamaki. Ana cikin haka Cokali yai tsalle ya rungume Armad yana dariyar murna yana cewa, "barka da dawowa sarki Wilbafos."
Nan take kogon ya cika da shewa. Iliyasis ya dawo ya tsaya a tsakiyar kogon yana kallon ikon ALLAH. Can bayan Armad ya gama shiri ya dube shi ya ce, "barka da dawowa. Amma ai ka tambaye mu maiya faru bayan ka suma ko?"
Armad ya gƴaɗa kai cikin murmushi ya ce, "hakane, amma kasan ba lokaci. Kuma nasan akan hanya zaku bani labarin komai."
A wannan lokaci Armad da tawagarsa sukai shirin yaƙi suka nufi filin daga.
**
Babi na 143: Salsa
Katangar Yaljadu katanga ce mai dogon tarihi. An gina ta tun a lokacin mulkin sarki Aldaima Wilbafos kafin zuwan sarki Eyriyon. Ita dai wannan katanga ita ce ta raba tsakanin duniyar mutane da aljanu. Babu wanda yasan dalilin da yasa sarki Aldaima gina wannan katanga kuma tunda aka gina ta ya zamanto babu wani aljani da zai iya shigowa duniyar mutane saita hanya ɗaya kacal. Wannan hanya ita ce aljanin ya kasance a jikin ɗan adam. Misali aljanin Armad, Jidaime, kasancewarsa tare da Armad shi ya bashi damar shigowa duniyar mutane. Amma duk aljanin da baya jikin mutun bai isa ya haura wannan katanga ba.
Tsayin katangar a tsaye ta tokare da sararin samaniya tayadda komai hangen mai hange bashi iya hango ƙarshenta. Sannan tana da kauri wanda yakai ƙafa dubu. A ƙasan wannan katanga akwai ƙofar shiga guda ɗaya tak sannan kuma akwai ƙofar fita guda ɗaya tak. Masu gadin wannan ƙofa sune Ranbirshishirui da Dandirshishirui. Daga tsakanin ƙofar shiga zuwa ƙofar fita an rarake doguwar hanya wadda ta haɗe ƙofofin guda biyu.
Ita dai wannan katanga tana bayan Titin Bayajidda. Daga ita sai duniyar aljanu, duniyar da mutane kaɗan ne suka taɓa ziyarta.
A dai-dai wannan lokaci acikin wannan hanya wadda ta haɗa tsakanin ƙofar shiga da fita wasu mutun uku ne ke tafiya. Maza biyu sun saka mace ɗaya a tsakiya. Suna sanye da fararen kaya wanda aka yiwa kwalliya da gashin fararen aljanu. Cikin hanyar akwai duhu amma bisa mamaki haske na fita daga jikin namijin dake tafe a ɓangaren dama. Hasken da ya haskaka cikin hanyar.
Gaba ɗaya hanyar an simince ta wata irin ƙasa mai launin jini. Babu wata hanyar iska acikin wajen sabida haka zafi ba'a magana. Kakkaurar yana da ƙasusuwan mutane sun rufe ko'ina acikin wajen. Kana gani kasan anyi shekaru ba'a wuce ta hanyar ba.
Macen tana da duhun fata kuma tana kama da Armad sosai amma mazan guda biyu farare ne. Ɗaya acikinsu yana da kamannin girma da yawan farin gemu. Idan ka dube shi sosai zaka ga ba wani bane illa kakan Armad wato Zaikid. Shi kuma ɗayan bai taɓa bayyana ba amma yana da yawan saje da dogon gashi. Sannan kuma abin mamaki gashinsa ja ne jajawur kamar na ƙabilar Rafiya. Wannan mutun ba wani bane illa mahaifin Armad Taidara Wilbafos. Macen ta tsakiya ba wata bace illa Hidaya Wilbafos wadda akafi sani da Baƙar wuta.
Hidaya ta dubi gabansu ta hango doguwar hanyar dake gabansu tai tsaki ta ce, "na tsani jira. Wannan hanyar tana cimin tuwo a kwarya. Ina kyautata zaton zan rushe ta wataran."
Taidara yai murmushi ya ce, "kada ki damu ai mun kusa."
Zaikid ya gƴaɗa kai ya ce, "iskar da take kaɗawa a duniya ta fara sauyawa. Lalle akwai canje-canje da zasu afku bayan wannan yaƙi. Hidaya, ke kaɗai kika karanta Littafin-takobi kuma ke kaɗai kika san meye aciki. Ya kike ganin wannan yaƙi zai kasance?"
Hidaya ta juyo da sauri tana ajiyar zuciya ta ce, "mai nake tunanin zai faru? Mutane da dama suna farauta ta saboda na karanta Littafin-takobi kuma nasan meye aciki. Abinda basu sani ba shi ne akwai wani mutun ɗaya wanda shima ya karanta Littafin kafin ni. Kuma sanin hakan nema ya sa bai shiga wannan yaƙin ba. Ina tabbatar muku yana nan tafe yana shiri. Burinsa ya mallaki garin ƙarƙashin ƙasa na Seerisha."
Taidara ya shafa takobinsa ya ce, "Hmm.. Maikiro'Abbas?"
Hidaya tai shiru tana tunani kafin daga bisani ta numfasa ta ce, "rigimar dai ita ce waye zai mallaki ƙasashen ƙasa. Wanda ya mallaki ƙasashen ƙasa shi kaɗai zai iya yaƙar Ururu. Akwai mutane da dama masu burin wannan matsayi amma babu wanda yake da ƙarfin izzar da zai iya mallakar ƙasashen."
Zaikid ya ja dogon numfashi ya ce. "Han'ibal na waje yana jiran mu. Naji ance burinsa ya mallaki fasahar takobin Bihanzin?"
Taidara ya ɗaga hannu yana yamutse fuska ya ce, "Rabu da Han'ibal, abinda yafi damu na shi ne Fatima. Naji labari Bihanzin ya bata shekarun izza kuma...."
Zaikid yai sauri ya dakatar dashi ya ce, "kada ka damu da Fatima tana tare da Armad kuma Hidaya tayi alƙawarin dawo da ita. Kasan dole mu dawo da SALSA kafin faɗuwar rana."
Taidara yaja dogon numfashi yana gyaɗa kai. Salsa suna ne mai ma'ana. A zamanin da kowanne sarki yana da jarumai fitattu guda uku wanda zasu shimfiɗa rayuwarsu kafin wani abu ya same shi. Wannan jarumai uku su ake kira da Salsa. Taidara da Zaikid da Fatima suna tare da Hidaya a har kullum tun daga ranar da Hidaya ta fara gwagwarmaya. Sune iyayenta kuma sune Salsa ɗinta.
Han'ibal yana tare da mutun uku: Wutar Daji, Wutar Ruwa da kuma Wutar Jini.
Shima Bihanzin na tare da mutun uku: Damjinu da Nakata da Dandil.
Haka dai zaka ga yawancin shahararru suna tafe da Salsa.
***
Acan wani sashen duniya Iliyasis ne ke labartawa Armad duk abubuwan da suka faru tun bayan sumansa. Koda Iliyasis yazo ƙarshe a labarinsa sai Armad ya ce, "zanyi amfani da Kaban'shìsu ku same ni acan."
Nan take Armad ya ɓace ya nufi filin yaƙi a yayinda yabar su Iliyasis akan dawakai suna gudu.
***
Babi na 144: Fushin Armad
***
~Titin Bayajidda
~Filin yaƙi
***
Ana tsaka da yaƙi sai kwatsam gari ya fara duhu, hadari ya fara haɗowa, sararin samaniya tai baƙi-ƙirin. Sannu a hankali duhun ya ringa ƙaruwa har saida takai ba'a iya ganin tafin hannun mutun. Dole ba shiri rundunonin dake filin suka fara shiga taitayinsu, kuma duk da ba'a tsaya da yaƙin ba amma da dama sun daina yin gaba. Wasu daga ciki suka fara shan jinin jikinsu suna neman mafaka.
Ba jimawa sai sama ta fara rugugi, hasken walƙiya ya fara bayyana. Kan kace meye wannan ƙarar tsawa ta fara sauka kafin daga bisani ilahirin filin ya rincaɓe da ƙarar aradu.
A wannan lokaci kowa ya tsaya cak da yaƙin yana kallon sama domin abinda ke faruwa ya wuce ace haka kawai ne.
Can bayan ƴan ɗaƙiƙu sai wani farin haske ya fara tasowa daga samaniya. Kafin mutanen dake filin yaƙin su ankara an fara ruwan sama, amma fa na walƙiya. Wani basamuden hannun walƙiya wanda shi kaɗai ya rufe sararin samaniya ya sakko akan rundunar abokan gaba.
Yana sauka dukkan abinda ke ƙasansa ya rududduge ya koma toka. Sama da sadaukai dubu ashirin ne suka mutu lokaci ɗaya. Da ganin hasken da saukar hannun baifi daƙiƙa ɗaya ba. Nan take filin yaƙin ya rikice, rundunar sarki Daljari suka fara jada baya cikin firgici da tsoro domin da dama daga cikinsu suna ganin ubangiji ne yai fishi dasu.
Sai dai kuma suna cikin wannan hali suka tsinci wani haske tsaye a bayansu ya tare musu hanyar wucewa. Wannan haske dukkaninsa walƙiya ne kuma idan ka dubeshi sosai zaka ga ya ɗauki siffar mutun. Wannan mutun ba wani bane illa Armad Wilbafos. Yana tsaye cikin ƙololuwar fushi da ɓacin rai.
Kafin wannan runduna su ankare Armad ya dunƙule hannunsa na dama ya aika musu da Hannun-aradu. Nan take ya baje filin tare da kashe sama da mutun dubu biyar.
Sama da sadaukai dubu hamsin suka kewaye shi. Dukkaninsu suka kawo masa hari a lokaci ɗaya. Wasu da masu wasu da kibbau, kai kace ruwan sama ake idan ka kalli yawan kibban da suka yiwo kan Armad. Amma ko gezau bai yiba. Haka ya tsaya cak suka zo suka cake shi suka wuce. Babu ciwo babu alamar ciwo, jiki ne na walƙiya.
Cikin ɓacin rai irin wanda aka daɗe ba'a gani ba Armad ya ƙara ɗaga hannu zai saukar musu da Hannun-Aradu amma a lokacin sarki Daljari ya dubi Uznu Ururu ya ce, "dama shi kake jira. Na baka dama ka kashe shi."
Cikin murna Uznu ya ɓace daga inda yake, amma abin mamaki baiyi kan Armad ba sai yai kan keken dokin da Nostaljiya ke ciki. Koda ganin haka sai Armad ya bar inda yake ya nufi keken dokin. Yana zuwa ya afka kan Uznu. To amma abin mamaki a dai-dai wannan lokaci sai kawai tauraruwar Uznu Ururu tai haske, lamarinda yasa ya ɓace daga inda yake ya bayyana akan iyakar doron ƙasa na farko dana biyu. Wato dai-dai kan dutsen nan da ake kira da Hajarul-Ururu, inda aka kama ruhin Armad.
Daga nan aka ɗauki Uznu Ururu cikin tafiyar taurari aka tafi doron ƙasa ta farko dashi.
Shi kuwa Armad yana ganin Uznu ya ɓace yai tsaki ya ƙarasa kan keken dokin. A wannan lokaci Kwamanda Asifu da Jan-doki na gabda cimmasa amma ganin bayyanar Armad suka jada baya. Nan take Kiru da Hasanu suka dawo gefen Armad suka tsaya suna fuskantar su yarima Niyashi da Bizaya da sauran kwamandun.
Kiru yai dariya ya ce, "Armad, ban taɓa tunanin zanyi farin ciki da ganinka ba kamar yau."
Armad yai murmushi ya gyaɗa kai.
***
~Doron ƙasa na farko
~Fadar sarki Ururu
~Majalisin Ashura
***
A dai-dai lokacinda ake tsaka da wannan yaƙi a kan doron ƙasa ta farko yarima mai jiran gado da waziri Tadiyraini Ururu sun kira taron gaggawa domin tattauna matsalolin mulki.
Irin wannan taro akan yishi a shekara sau biyu amma idan wani muhimmin abu ya taso akan yishi a kowanne lokaci.
Shidai wannan taro shi ake kira da Majalisin Ashura, kuma zaka iya cewa a halin yanzu babu wani taro da yakai shi muhimmanci a duniya, domin kuwa a shi ne sarakunan duniya suke tattauna yadda zasu tafiyarda duniya.
Fadar sarki Ururu ita ce a tsakiyar doron ƙasa na farko, kuma a saitin ƙasanta dutsen Hajarul-Ururu yake. Ita kanta fadar an gina tane da dutse mafi daraja wato dutsen Yalfinji. Fadar tafi komai tsayi a dukkan faɗin doron ƙasa ta farko kuma ana iya hangota daga ko'ina a faɗin ƙasar komai nisa.
Acikin babban ɗakin taro dake wannan fada anan ake gudanar da wannan majalisi. Tuni kowa ya hallara, dama kawai Uznu Ururu ake jira domin yana daga cikin sarakuna goma na Ashura.
A halin yanzu akwai mutun goma sha ɗaya acikin wannan ɗaki zaune kan kujeru. Kowa ka kalla zaka ga baƙaƙen idanuwa masu tsantsar izza da buwaya.
Mutun biyu fuskarsu a buɗe take; ɗaya Uznu Ururu ne ɗaya kuma yana sanye da ƙaramar riga baƙa da baƙin wando yana da dogon gashi baƙi mai sheƙi. Fuskarsa na bada alamun rashin tsufa da kuma tsufa duk a tare. Wato irin yanayin nan da zaka kasa gane shekarun mutun. Gashin girarsa bashi da yawa amma yana da surar takobi. A kafaɗarsa akwai takobi a rataye wadda ke ɓoye cikin kufenta. Wannan mutun shi ake kira da Tadíyraini Ururu kuma shi ne wazirin sarki Kuyurussa'ayi Ururu.
Sauran mutun tara dake wajen kaf fuskokinsu a rufe suke da baƙin hirami kuma sune ragowar sarakuna goma na Ashura kamar haka:
1)Gidan Kuyurussa'ayi Ururu: Ɗa ɗaya
2)Gidan Dumaƙisu Ururu: ƴaƴa ashirin.
3)Gidan Dul'Ururu Ururu: ƴaƴa tara.
4)Gidan Jushai Ururu: ƴaƴa talatin da uku.
5)Gidan Ƙilbaru Ururu: ƴaƴa sha tara.
6)Gidan Jidda Ururu: ƴaƴa bakwai
7)Gidan Nasára Ururu: Ƴaƴa huɗu
8)Gidan Shiysui Ururu: ƴaƴa shida
9)Gidan Fayziy Ururu: ƴaƴa sha ɗaya.
Waziri Tadiyraini yai gyaran murya ya fara jawabi. "Na kira kune domin tattauna matsaloli kamar haka: Armad Wilbafos, Hidaya Wilbafos, Banzirshishirui, da kuma Ikenga O. Bayajidda."
***
Babi na 145: Majalisin Ururu
***
***
~Doron ƙasa na farko
~Majalisin Ururu
***
Mutun goma sha ɗaya wanda ke rike da mulkin duniya baki ɗaya sun hallara.
Waziri Tadiyraini Ururu ya dubi Uznu ya ce, "ina ganin kafi kowa cancanta kayi bayani akan wannan yaro da ake kira da Armad Wilbafos mai amfani da SIKAI."
Uznu yaja numfashi sannan ya gyara zama ya fara bayani. "Gani na dashi na farko a gasar Jinzidal ne wadda ta gabata, a garin Denizawa na ƙarƙashin ƙasa, Shadeniza. A lokacin ya shiga gasar da sunan Armad Djinn saboda haka hankali na baya kansa. Abu na farko daya kai ido na kansa shi ne motsin Littafin-takobi dana ji a jikinsa. A wannan lokaci nayi ƙoƙarin kwace Littafin amma Littafin ya shige cikin ruhinsa. Saboda haka na ɗauke shi na tafi dashi izuwa shalkwata domin zaƙulo Littafin amma hakan ya gagara.
"Bayan ɗan ƙaramin bincike na gano cewa koda kashe shi nayi Littafin bazai fito daga ruhinsa ba. Hanya ɗaya data rage shi ne mu rabi da Littafin ya fito da kansa a sanda yaga dama. Nasan cewa Littafin yana da ruhi na kansa kuma indai yana jin Ururu a kusa dashi bazai fito ba, saboda haka nasa aka siyar da yaron a matsayin bawa sannan nasa manyan hadimai na biyu, Kalkutu da Netti, su samin ido akansa.
"Amma Zahra ƴar Bihanzin ta kashe su ana tsaka da cinikin bayi wanda hakan yasa na rasa ido akan Littafin. Tun daga wannan lokaci nake neman Armad amma bamu haɗu ba sai a wannan yaƙi. Amma nayi alƙwarin bazan bari ya ƙara kuɓucemin ba face na kwace shi."
Dukkanin sarakunan dake zaune na sauraren bayanan Uznu. Bayan ya kammala sai waziri Tadiyraini ya ce, "ka manta baka bayyana mana cewa a lokacin daka kama wannan yaro ruhinsa a tsage yake ba."
Uznu yai gyaran murya ya ce, "eh lallai a lokacin ruhinsa a tsage yake, kamar an datsa gida biyu. Amma har muka rabu ban san inda ɗaya ɓarin ruhin yake ba. Watannin baya naji ance jikar Ƙilbaru Ururu mai suna Suwainah ta kama wani ruhi yana neman hawowa kasa ta farko wanda shima a tsage yake kamar wancan. Saboda haka nayi tattaki izuwa Hajarul-Ururu. Abin mamaki wannan ruhi irinsu ɗaya sak da ruhin Armad a lokacin dana kama shi. Ina ganin koma dai ya ake ciki ruhin nan dake jikin Hajarul-Ururu a yanzu shi ne ɓarin ruhin Armad Wilbafos."
Waziri Tadiyraini ya gyaɗa kai ya ce, "meye burinsa? Mai yake so ya cimma a duk wannan abubuwan da yake yi?"
Uznu ya amsa da cewa, "Eh to.. Da farko burinsa ya samarwa mahaifyarsa lafiya amma yanzu naji ance shima ya ɗau gaba da rukunin Jinzidal."
Waziri Tadiyraini ya tari numfashinsa da cewa, "hakan ba abin mamaki bane tunda mahaifyarsa ita ce Fatima Wilbafos babar Hidaya Wilbafos. Mahaifinsa Taidara Wilbafos. Dukkansu ragowar Eyriyon ai dole su yaƙi Jinzidal."
Ɗaya daga cikin sarakunan wanda ke zaune fuska a rufe ya tsoma baki. "Kuna ganin abinda Armad yake Hidaya ce ta saka shi?"
Waziri Tadiyraini ya amsa da cewa, "ko ita ce koma ba ita bace dukkansu jininsu ya halatta. Shima Banzirshishirui jininsa ya halatta. Kuma koda ya rayu a wannan yaƙin mun cire shi daga jerin sarakunan Jinzidal."
Nan take Uznu Ururu ya ce, "amma ya kamata mu kalli wannan yaƙi ta fuska da dama. Mun san waye Bihanzin duk da bamu san meye shirinsa ba, amma ba abin mamaki bane idan yai nasara. Saboda haka ima ganin babban abinda ya kamata mu lura shi ne kare sarautar sarakunan Jinzidal. Idan muka bari Bihanzin yai nasara to lallai rukunin Jinzidal yana cikin matsala domin kuwa Bihanzin da Hidaya zasu iya hallaka dukkan sarakunan Jinzidal ɗin dake filin yaƙin nan."
Waziri ya ja dogon numfashi ya ce, "a farkon lokaci muka saukar da ragowar halittu zuwa ƙasa. Kuma a lokacin muke kula da rukunin Jinzidal wajen tabbatar dashi. Bayan shuɗewar shekaru muka ga ya kamata mu bar mazauna ƙasashen nan suci gaba da gudanar da harkar rayuwarsu saboda haka muka ƙirƙiro da sarautar Jinzidal. Duk wanda muka yaba da izzarsa zamu kai masa goron gayyata, idan ya amince da ƙa'idojinmu mu naɗa shi idan bai amince ba mu halaka shi. Ƙa'idojin sune zai kula da gasar Jinzidal kuma zai tabbatar ba'ai mata kutse ba. Zai rinƙa karɓar haraji kyauta, sannan kuma baza mu saka masa baki acikin abubuwansa ba. Bazamu shiga iyakarsa ba shima bazai shiga tamu ba. A bisa wannan ƙa'ida muka samu sarakunan Jinzidal har guda biyar: daga na farko wato Maikiro'Abbas har zuwa na ƙarshe Bihanzin.
"Sarakunan Jinzidal suke kula da Jinzidal a bisa umarnin mu, idan wani ya taɓa su kamar ya taɓa mu ne. Dole baza mu bari wani ya tarwatsa su ba.
"Ƙilbaru kai ne da alhakin kula da Banzirshishirui, ya kake ganin zamu ɓullo masa?"
Nan take sarki Ƙilbaru ya cire abinda ya rufe fuskarsa. Idanuwansa baƙaƙe ne kamar na kowa amma kansa babu gashi ko ɗaya. Akwai gashin baki mara yawa da kuma ɗan gemu. "Lokaci na farko da muka fara saka ido akan Banzirshishirui lokacin Yaƙin-ɗalasimai ne. A ƙarshen yaƙin mukai masa muƙamin sarkin Jinzidal, amma ba jimawa muka gano cewa yana da wata manufa ta musamman. Uznu bamu labari akan sunansa daka gani acikin Littafin-takobi."
Uznu Ururu yaja dogon numfashi ya ce, "a lokacin yaƙin Littafin-takobi mun samu damar karanta shafin farko na wannan littafi, kuma anan naga sunan Banzirshishirui da tsarin-ruhinsa. Lallai shi ne ya canja sunansa zuwa Bihanzin saboda ɓadda kama."
Ƙilbaru ya gyaɗa kai sannan ya ɗora da cewa, "banda wannan, mun gano cewa Bihanzin da Maikiro'Abbas suna da alaƙa amma har yanzu bamu san meye a tsakaninsu ba. Shekaru ɗari biyar da arba'in da ɗaya kafin Bihanzin ya gamu da Rafiyan Daljari an gano su suna koyon dabarun izza a wajen mahaifin mai tsaron ƙofa Ranbirshishirui. Ina ganin yadda muka sauke Bihanzin shi ma mu sauke shi, domin lalle akwai abinda ya taka."
Waziri ya juya ɓarinsa na dama ya dubi ɗaya daga cikinsu ya ce, "Fayra Ururu, kaine da alhakin kula da Hidaya. Taya kake ganin zamu ɓullo mata?"
Shima Fayra Ururu ya cire rufin fuskarsa ya fara jawabi. "Hidaya a har kullum burinta ta kawarda Jinzidal saboda haka sai tafi kowa farin ciki idan sarakunan Jinzidal suka je ƙas. Za'a iya cewa wannan yaƙi wata hanya ce mai kyau da burinta zai cika idan mukai duba da cewa zarar Bihanzin yai nasara sarakunan Jinzidal guda uku zasu iya rasa ransu da daulolinsu.
"A halin yanzu tana tare da Salsa ɗinta, kuma ina ganin zasu iya cin nasara akan Han'ibal duk da kuwa za'a iya kai ruwa rana. Hanya mafi kyau da za'a shawo kan al'amarin shi ne mu sanar da ita mun kama ruhin ƙaninta. Wannan zai raba mata hankali ya kuma bawa Han'ibal dama."
Waziri ya gyaɗa kai cikin dogon numfashi ya dubi mutumin dake damansa ya ce, "Yarima Dumaƙìsu mai za'ai?"
Yariman wanda shi ne mai jiran gado ya amsa da cewa, "Bihanzin, Daljari, Deniz, Maikiro'Abbas da Han'ibal duk suna da buri da suke so su cimma. Kuma acikinsu babu wanda yai mubayi'a ɗari bisa ɗari ga Jinzidal. Kawai dai suna neman kariyar mu ne. Hakan ne yasa a lokuta irin wannan muke samun matsala dasu. Hanya ɗaya da zamu tabbatar rukunin Jinzidal bai ƙara shiga wannan hali ba shi ne juyin mulki."
Nan take waziri yai farat ya tari numfashinsa ya ce, "juyin mulki, kamar yaya?"
Yarima yai murmushi mai cike da sanin makamar aiki ya ce, "Han'ibal kaɗai muke buƙata acikinsu amma ragowar canja su zamu yi. Tuni inada sababbin ƴan takara a raina."
Nan take ɗakin taron yai tsit kafin daga bisani su shiga ƙus-ƙus da maganar kowa na tunani akan maganar. Abu ɗaya dai shi ne babu wanda ya isa ya tanka zarar yarima yai magana hatta wazirin.
Yarima yai gyaran murya waje yai tsit sannan ya ɗora da cewa, "Uznu Ururu na baka dama kai amfani da dukkan ƙarfin izzarka da idanuwanka ka kashe wannan yaro Armad Wilbafos. Ka kawomin ruhinsa ni zan zaƙulo Littafin-takobi daga ciki. Waziri Tadiyraini ka saki DENIZ URURU daga kurkuku. Dul'Ururu, akaiwa Han'ibal kundin fasahata ta takobi wadda na samar a ƙarni na uku. Naji ance burinsa yafi kowa ƙarfin takobi aban ƙasa. Ana kammala wannan yaƙi zan sauya tsarikan duniya. ZANYIWA KOMAI GARANBAWUL DOMIN NAGA AL'UMMAR ƘASASHEN ƘASA SUN FARA MANTAWA DA WAYE URURU."
***
Babi na 146: Ƙabilar Uzzus
***
Acan wani tsohon zamani kafin zuwan Amri da Jinzidal, kafin zuwan Ururu, a lokacin mulkin sarki Eyriyon Wilbafos anyi wata ƙabila mai suna Uzzus. Asalin wannan ƙabilar suna rayuwa akan wani tsibiri dake ruwan maliyan da Ururu suka bi suka zo ɓangaren gabas.
Ƙabilar Uzzus na da mutun dubu bakwai kacal. Abin mamakin shi ne anyi ittafaƙi sunfi kowacce ƙabila daɗewa a ban ƙasa amma basa haihuwa kamar sauran al'umma. Daga lokacin da mace ta ɗauki ciki akanyi shekara dubu kafin ta haihu.
Banda wannan akwai wani sirri wanda ke ƙunshe cikin ruhin wannan ƙabila. Wannan kuwa ba wani abu bane illa rashin tsufa. Zancen tsufa babu shi domin kuwa duk ƙabilar tsofaffi uku ne kacal. Saboda haka ba'a mutuwa saboda tsufa a wannan ƙabilar. Hasalima mutun talatin da uku ne kaɗai suka taɓa mutuwa acikin ƙabilar.
Sarkin wannan ƙabilar yaro ne saurayi, kyakkyawa mai yawan jan gashi. Abin mamaki idanunsa baƙaƙe ne wuluk kamar na Ururu. Sunansa sarki Uznu Uzzus.
Watarana sarki Uznu ya fito shan iska saiya hangi wata ƙatuwar tawaga wadda ke ɗauke da jiragen ruwa aƙalla dubu ɗari biyu. Kowanne jirgi yana ɗauke da sadaukai sama da dubu, da dawakai da makamai na musamman. Nan take sarki yasa aka buga ƙugen yaƙi, aka kirawo sadaukai suka hau layi. Sarki ya shiga sulke.
Bayan wannan runduna sun ƙaraso sai suka bayyana cewa sunansu Ururu kuma ba yaƙi ne ya kawo suba kawai wucewa zasu yi.
Sarki Uznu ya bada umarnin a ajiye makamai a basu hanya lamarinda yasa sarkin yaƙinsa ya juyo cikin mamaki ya kalleshi. Amma sarki Uznu ya dage akan a buɗe musu.
Wannan ne lokaci na farko da ƙaɓilar Uzzus da sarkinsu Uznu Uzzus suka haɗu da wannan ƙabila mai suna Ururu.
Sarki Uznu yai matuƙar farin ciki da ganin cewa akwai mutane masu irin idanunsa a duniya. Cikin ƙanƙanim lokaci suka saba da wannan ƙabila. Ya basu wajen zama da abinci da komai da suke buƙata.
Bayan wata ɗaya ƙabilar Ururu suka bayyana aniyarsu ta barin wannan tsibiri domin suci gaba da tafiya. Sarki Uznu baiji daɗin wannan zance ba domin har ya fara sabawa dasu. Bai taɓa jin daɗin haɗuwa da wasu bil'adama ba irinsu.
Da dare sarki ya kasa bacci saboda tunanin rabuwa da wannan ƙabila, saboda haka ya tashi ya fito daga gidansa yabi dare ya shiga masaukin wannan ƙabila. Burinsa yaga sarkinsu ya roƙeshi su ƙara koda kwana ɗaya ne. Abin mamakin shi ne bai taɓa ganin sarkin wannan ƙabila ba, kullum sai ace masa bashi da lafiya.
Kan kace meye wannan sarki Uznu ya rataya Farar-laya ya ɓoye yanayin-izzarsa. Sannan yai amfani da fasahar sauri ya wuce masu gadin ya isa tantin sarkin. Kai tsaye ya buɗe ya shiga.
Sai dai kuma yana shiga ya iske mutun tara a tsattsaye sun juya masa baya suna fuskantar ɗaya bangon ɗakin. Nan take ya cake yana ƙoƙarin juyawa amma yaga mutanen ko motsi basuyi ba, kamar ma basu san ya shigo ba. Yana ɗaga kai ya fuskanci cewa wannan mutane tara kallon wani mutun suke. Nan take ya yanke shawara mutumin shi ne sarkin saboda haka ya kewaya ta gefe ya shige gaba.
Yana shiga yai arba da fuskar babban sarki Kuyurussa'ayi Ururu. Kallo ɗaya tak ruhin Uznu ya kama ci da baƙar wuta. Shekarunsa na izza suka fara ƙonewa. Kan kace meye wannan jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Ba komai ne ya jawo wannan ba illa tsananin ƙarfin izza da buwaya na sarki Kuyurussa'ayi. Mutane kaɗan ne suka taɓa ganinsa kuma suka rayu saboda ruhi baya iya jure gamuwa dashi.
Abin mamaki sarki Uznu ya girgije ya daddagira ya tsaya. Sannan yana kakarin jini ya buɗe baki ya ce, "w..waye kai.. Waye kai.."
Wannan ragowar mutun tara suka dubi sarki Uznu cikin tsananin mamaki. Domin kuwa Uznu shi ne mutun na farko wanda baɗan asalin ƙabilar Ururu ba dayai ido huɗu da sarki Kuyurussa'ayi kuma ya rayu.
A wannan rana sarki Kuyurussa'ayi ya karɓi Uznu a matsayin ɗa. Kuma ya canja masa suna zuwa Uznu Ururu.
Uznu ya amince da wannan mataki domin bai taɓa ji ƴan ƙabilar Uzzus ƴan'uwansa bane musamman saboda kalar idanunsa. Amma kallo ɗaya ya amince da amince da sarki Kuyurussa'ayi. Yana sarki ɗan sarki amma ya ajiye muƙaminsa yabi sarki Kuyurussa'ayi badan komai ba saboda tsananin ƙarfin izza daya gani. Yasan a duniya babu wani mahaluƙi mai irin izzar sarki Ururu.
A lokacin mutanen sarki Uznu suka nemi a naɗashi ɗaya daga cikin sarakuna tara na Ururu wanda ake kira da TASU'A. Sarki Kuyurussa'ayi ya bayyana cewa Tasu'a mutum tara ne. Dole indai Uznu yana so a naɗa shi sai dai ya kashe mutun ɗaya daga cikin Tasu'a ya maye gurbinsa.
A lokacin aka samarda ƙawanya. Sarki Uznu ya shiga ciki yana jira abokin fafatawarsa. Dukkan rundunar Ururu sun halacci wajen domin ganin wannan fafatawa. Amma duk da haka sarakuna tara na Tasu'a fuskokinsu a rufe suke. Shi kuwa sarki Kuyurussa'ayi yana zaune cikin tantinsa domin zarar ya fito to dukkan wanda ya ganshi mutuwa zaiyi.
Ɗaya daga cikin sarakunan Tasu'a, Sarki Jailan Ururu, ya fito ya tsaya a gaban Uznu.
Duk da fuskarsa a rufe take amma Uznu ya dube shi cikin izza ya ce, "kaine sarki Jailan Ururu ɗan sarki Ashiraini Ururu. Shekarunka na izza dubu arba'in da bakwai da ɗari uku da hamsin. Sunan tauraruwarka YSKEZAI. Kuma kana amfani da fasahar idanuwa da kuma takobi.
"Sa'a ɗaya data wuce kana tare da ƴan'uwanka na Tasu'a kuna tattauna yadda zaku kashe sarkin duniya Eyriyon Wilbafos. Kaine ka ce ku fara kashe ɗansa mai suna Wilbafos Juniyo.
"WANNAN IDANUWA NAKA, ME KAKE IYA GANI DASU? Shi ne abinda zaka ce min nanda daƙiƙa biyu."
Abin al'ajabi bayan daƙiƙa biyu dai-dai sai sarki Jailan ya buɗe baki ya ce, "WANNAN IDANUWA NAKA, ME KAKE IYA GANI DASU?"
Sarki Uznu ya bushe da dariya yana cewa, "a duk faɗin duniya babu wanda zai iya nasara akaina. Idanuwana suna ganin abinda zai faru daƙiƙa biyu kafin ya faru. Wannan fasaha na saka mata suna SAƁANI. Sannan kuma ina iya karanta taurari na gane waye abokin gabata da ƙarfin izzarsa da fasaharsa. Wannan fasaha ita na kira da HAƘIƘA. Sannan kuma ina ganin abinda abokin gabata ya aikata sa'a ɗaya kafin mu haɗu ta hanyar ƙarfin idanuwa na. Ina kiran wannan fasaha da suna BAYANI."
Abinda Uznu bai sani ba shi ne wannan fasahohi daya bayyana sun samo asali ne daga baƙaƙen idanuwansa. Wanda hakan ke nuna cewa duk wanda ke cikin rundunar Ururu yasansu.
Ururu basu da abin bauta banda idanuwansu saboda haka suna ganin fasahar Uznu suka zube ƙasa cikin bauta suna cewa:
"
*Sarki Mai Urürü{Namibi yâ Urürü}
A Tun Farkon Urürü {Damshïsh Urürü}
A Har Ƙarshen Urürü {Jímbíl Urürü}*
"
Sarki Kuyurussa'ayi yana ganin abinda ke faruwa ta hanyar fasahar SHANKIL ta idanuwan babban ɗansa yarima Dumaƙìsu Kuyurussa'ayi Ururu.
A wannan lokaci ya bada umarnin a tsayarda wannan fafatawa. Sannan ya naɗa Uznu sarauta, ya kuma canja sunan sarakunan Ururu daga Tasu'a zuwa Ashura.
Wannan al'amari ya faru tun kafin Ururu suzo daular sarki Eyriyon. Bayan Ururu sun iso gabas saida suka shafe sama da shekara ɗari kafin su fara yaƙi da Eyriyon. Yau anyi shekara sama da dubu ɗaya da ɗari takwas da hamɓarar da daular Wilbafos. A duk tsahon wannan lokaci Uznu Ururu ƙarfafa fasahar idanuwansa yake.
Saboda sirrin rashin tsufa da bijirewa mutuwa da ƴan ƙabilar Uzzus ke dashi Uznu Ururu ya gagari mutuwa har a yaƙin Littafin-takobi.
A halin yanzu babu wanda yasan iyakacin izzar Uznu Ururu. Abu ɗaya sananne shi ne Uznu baya tsufa kuma baya mutuwa. Sannan kuma idanuwansa suna ɗauke da duk wata fasahar Ururu. Kuma a dalilinsa aka canja sunan sarakunan Ururu daga Tasu'a zuwa Ashura.
A dai-dai wannan lokaci Uznu ya dawo Titin-Bayajidda, filin yaƙi. Yana sanye da baƙin sulke, rataye da baƙar takobi. An yaye hijabi kuma an bashi cikakkiyar dama ya buɗe izzarsa ya afkawa Armad. Ranar da zai nuna kansa a wajen sarki Kuyurussa'ayi tazo.
Abin mamaki wata mace ce mai idanu ruwan ƙasa irin na ƴaƴan Wilbafos a tsaye tare da Uznu. Duk su biyun Idanuwansa suna kafe kan Armad wanda ke tsaye a jikin keken dokin Nostaljiya.
***
Babi na 147: ArmaNos
***
***
Ranar-kewaye
***
Akwai wani abu daya faru Ranar-kewaye wanda ba wanda ya sani daga Armad sai Nostaljiya.
Nostaljiya na goye a bayan Armad sai yaji tana masa tafiyar tsutsa a wuya. Armad yai kamar baiji ba yaci gaba da tafiya yana gaisawa da mutane. Jim kaɗan sai Nostaljiya ta fara ja masa gashi da ƙarfi. Armad ya dake yai kamar baiji ba yaci gaba da ɗagawa mutane hannu. Amma bayan wannan sai kawai Nostaljiya ta fara caka masa farce a baya. Tun yana daurewa har saida ya waiwayo ya harare ta.
Tana buɗe baki sai tace masa, "idan kaci gaba da dariya da murna da farin ciki lallai zuciyata zata buga na faɗi ƙasa matacciya."
Armad ya turo baki cikin tsokana yana cewa, "ohh, shi yasa kike cakamin farce dan naji zafi na daina dariya ko. Lallai ma. Ai kuwa saina rama. Kuma..."
Armad na cikin magana yaja baki yai shiru saboda hawayen da ya gani suna zuba daga idanunta. Nan take ya rikice ya ce, "mai ya faru? Mai ya saki hawaye?"
Cikin shessheƙa ta amsa da cewa, "Ba komai."
Jikin Armad yai sanyi bai ƙara cewa komai ba yaci gaba da tafiya yana ta tunane-tunane akan abinda take nufi. Yana cikin wannan hali ne yaji muryarta a kunnensa tana cewa, "zaɓi ɗaya, ArmaNos ko ArmaZah?"
Armad najin haka ya gane cewa sunansa da nata ta haɗa. Cikin farin ciki ya amsa da cewa, "ArmaNos."
Nostaljiya tai murmushi tace, "kowanne suna yana da ma'anarsa. Kaga ArmaNos yana nufin kayi alƙawari idan na mutu baza kai zaman kaɗaici ba zaka ƙara aure."
Armad ya juyo rai a haɗe ya ce, "hmm.. idan na zaɓi ArmaZah kuma fa?"
Nostaljiya ta fashe da dariya. "Ai maganar farko da ita sarki yake amfani. Ka riga ka zaɓi ArmaNos."
Armad ya canja murya ya ce, "kina tunanin zan bar mutuwa ta ɗaukeki? Tare zamu rayu, tare zamu mutu, abadan dani dake zamu zauna."
Nostaljiya ta hau wani mataki na musamman akan soyayyarta da Armad. Son da take masa baya buƙatar dalili. Kuma koda zaice ya daina sonta wannan bazai taɓa sawa ta rage sonsa ba. Hasalima bata damu da kanta ba, abinda kawai take dubawa shi ne farin cikin Armad. Idan taga Armad yana farin ciki ko dariya to ita ma anan farin cikinta yake. Idan yana baƙin ciki anan baƙin cikinta yake. Tun ma kafin a ɗaura musu aure tunanin ta kawai kada ya shiga kaɗaici idan bata nan.
Ƙololuwar ƙauna.
***
~Titin Bayajidda
~Filin yaƙi
***
Armad ya dubi jaruman dake gabansa, ya kuma dubi fafatawa tsakanin Bihanzin da Daljari sannan kuma ya kalli keken dokin da Nostaljiya ke ciki. Nan take ya yanke shawarar abinda zaiyi. Yai tsalle ya shiga cikin keken dokin.
Babu komai aciki sai ɗan ƙaramin gado wanda Nostaljiya ke kwance akai a sume. Tare da Armad Nostaljiya ta suma saboda fasahar Zaren-gwana to amma jikin Armad na walƙiya ne saboda haka tuni ya farfaɗo.
Armad ya dube ta, kallo mai cike da soyayya da tausayi. Kyawun fuskarta yana nan amma duk alamun duka da ciwuka sun lalata mata tsari. Fatar ta tayi fari fat kamar babu jini a jikinta. Hannayenta sun dundunƙule kamar na matacce. A wannan lokaci Armad ya kula da wata ƴar takarda dake dunƙule acikin hannunta na dama. Cikin sauri ya buɗe hannun ya zaro takardar.
Rubutun ciki anyi shi ne da jini. Yana ganin rubutun ya san rubutun matarsa ne. Nan take ya fara karanta saƙon inda yaga an saka:
***
*ArmaNos*.
***
Koda Armad ya ga wannan rubutu saiya fashe da kuka. Ko a halin ƙunci da mutuwa babu abinda Nostaljiya take tunani sai shi. Babu abinda take tunani sai kada ta barshi cikin kaɗaici bayan ta mutu.
Duk soyayyar mace babu ruwanta da farin cikinka indai akan ƙara aure ne. Amma tuni soyayyar Armad da Nostaljiya ta wuce matakin bil'adama. Tunaninsu kada ɗaya daga cikinsu yai kaɗaici.
Armad yai kururuwa, yai ƙaraji. Wani hawaye mai zafi ya fara kwaranya daga idanunsa. Nan take samaniya ta kaɗa tai jajawur. Kamar tana tsoron fushin Armad. Armad ya ƙara yin ƙaraji mai firgitarwa, lamarinda yasa dawakai suka fara haniniya suna arcewa da gudu. Ya ƙara yin ƙaraji, lamarinda yasa keken dokin ya juye izuwa toka. Gadon da Nostaljiya take kai shima ya juye izuwa toka. Armad ya cafi matarsa suka faɗo ƙasa tana kan hannayensa.
Ƙafafuwan Armad na taɓa ƙasa dukkan ƙasar wajen ta juye izuwa walƙiya. Sannan kuma duk abinda walƙiyar ta taɓa sai kaga ya juye izuwa toka. Armad ya ƙara yin ƙaraji mai tsoratarwa wanda duk yafi na baya. Nan take wasu mutun-mutumi guda goma sha biyu na walƙiya suka bayyana a bayansa. Kowannensu na ɗauke da al'amudin wuta. Jikin Armad ya juye izuwa walƙiya. Ya buɗe ƙofar zobensa ya saka matarsa aciki. Sannan ya juyo izuwa su Bizaya da Niyashi da Asifu da Jan-doki da Kalhari da Tagwayen-auni ya ce, "idan akwai wanda yake son uwarsa ta haifi wani ya matso kusa."
Kallo ɗaya kacal zakaiwa Armad kasan a wannan rana bashi da niyyar barin wani mahaluƙi a raye. Idan kuwa ka matsa kusa zaka fuskanci cewa Armad yafi kama da hatsabiban shaiɗanun nan wanda suka gallabi mutan farko.
An taɓa iyalan sarakunan duniya. A wannan lokaci babu abinda ya shafi Armad ko duniyar ce zata ƙare bai damu ba. Kawai Nostaljiya.
Koda ganin sabuwar siffar Armad sai kowa ya fara jada baya. Armad ya fara tafiya cikin izza yai tsakiyar filin yaƙin. Duk abinda ya taɓa sai kaga ya juye izuwa toka. Hatta iskar data taɓa jikin Armad toka take komawa.
Kan kace meye wannan Armad ya bayyana a tsakiyar filin dagar. Amma abin mamaki sai kowa ya dare aka bashi waje. Armad yai kururuwa yai kurari. Sannan ya dubi sarakunan Jinzidal ya ce, "zan tafi da mata ta, idan akwai wanda ya isa ya biyo ni." Yana rufe ya tafa hannayensa zaiyi amfani da fasahar Kaban'shìsu ya ɓace amma a lokacin ne sarkin Ashura, Uznu Ururu ya bayyana a tsakiyar filin yaƙin. A bayansa wannan mace mai idanuwan gidan Wilbafos na tsaye.
Uznu Ururu ya ce, "DAMA NA DAƊE INA SO NA TAMBAYEKA INA KA JEFA ƳAR'UWATA NUSI. Shi ne abinda zaka ce."
Abin mamaki bayan daƙiƙa biyu sai Armad ya ce, "dama na daɗe ina so na tambayeka ina ka jefa ƴar'uwarta Nusi."
Uznu ya ƙara cewa, "zaka kawomin sara da takobin ka ta dama."
Abin mamaki bayan daƙiƙa biyu sai Armad ɓace daga inda yake ya kawowa Uznu sara da takobinsa. Amma tuni Uznu ya daɗe da ɓacewa daga inda yake saboda haka Armad ya sari iska.
Nan take Armad ya tsaya cikin mamaki. Armad bai san maike faruwa ba amma ya gane cewa Uznu yana sanin abinda zaiyi kafin yayi.
A wannan lokaci filin yaƙi yai tsit. Kowa ya tsaya aka zuba musu ido.
Yaƙi tsakanin wanda yasan abinda zai faru kafin ya faru da kuma wanda jikinsa gaba ɗaya na walƙiya ne. Lallai akwai fafatawa wadda aka daɗe ba'a gani ba a duniya.
***
Comments
Post a Comment