Skip to main content

BABI NA 77 -89: Horo

 Babi na 77: Mubayi'a ta farko 


"Kurkuku?!" Armad ya faɗa cikin ɓacin rai. Yana niyyar ƙarewa Babara tanadi sai wani abu ya faɗo masa. 


Nan take ya ce, "idan a kurkuku nake to ai kaima a kurkuku kake kenan?"


Babara yai murmushi inda dattijon takarsa ta ƙara bayyana. "Lallai kayi gaskiya. Idan kana kurkuku to nima ina kurkuku. Ko a baya dana gaya maka cewa na taɓa keta rabin wannan Bango a zahiri bawai Bangon na keta ba. Mu kanyi amfani da manya-manyan hatimai wanda ƙungiyar duba ta duniya ta samar domin kawo yara wannan duniya ta bango domin muyi musu horo. Amma a zahiri hatimin yana canja taswirar waje tare da mutanen dake kai, a saboda haka bawai cikin nan muke kawo suba. A taƙaice dai ni kaina wannan shi ne zuwa na wannan waje na farko."


Koda Armad yaji haka saiya haɗe gira yana mamaki. Nan take zare ido gami da tambayar Babara. "Idan baka taɓa zuwa ba to tayaya kake niyyar fita daga wannan waje?"


Babara najin tambayar ya sunkui da kansa ta yadda Armad bazai iya karanta halinda fuskarsa ke ciki ba. 


Lokaci ya fara tafiya, gari na ƙara duhi, sanyin dusar ƙanƙara na keta ruhin Armad yana sashi rawar ɗari. Can daga bisani Babara ya zube akan gwiwowinsa, kansa na kallon ƙasa cikin miƙa wuya.


Abu na farko da Armad yayi tunani shi ne sanyi ne ya yiwa Babara yawa, ko kuma wataƙila ciwon ciki yake. Amma kafin Armad ya kaiwa Babara ɗauki yaga Babara ya zare doguwar wuƙa daga aljihunsa, ya yanki tafin hannunsa, inda jini ya fara kwaranya. Sannan yayi amfani da hannunsa mai jini ya cake sandar tsafinsa a ƙas.


Armad ya rasa mai zaiyi tunani sai kawai yaji muryar Babara a kunnensa. "Ni Babara Bayajidda nayi mubayi'a ga sarkin mutane da aljanu Armad Wilbafos na uku." 


Idan ba daban tsananin imani da kafiya da Armad yaji a muryar Babara da lallai zai ɗauka wasa yake. Amma duk da hakan Armad bai gane abinda ke faruwa ba, nan take ya buɗe baki ya ce, "wai maike faruwa ne? Lallai kana sani ina jin kunya, kuma idan wannan ɗaya ce daga cikin dabarunka na horo bai bada ma'ana ba."


Babara ya ja ɗan ƙaramin numfashi tare da ƙara sunkui da kansa yana cewa, "lallai wannan ba wata dabara bace. Ni Babara na bar muƙami na sarkin duba na dawo gefenka domin ganin cewa ka zama sarki wilbafos na uku. Ina fatan zaka karɓi mubayi'a ta."


Armad yai farat ya ce, "to saboda me? Ni bance ina son na zama sarki wilbafos na uku ba. Sannan kuma ni ban masan abinda hakan ke nufi ba."


Babara ya amsa a nutse, tamkar dama yayi tunanin Armad zaice hakan. "Zama sarki Wilbafos na uku ba abu ne da zaka iya zaɓa ba koda kana so. Abu ne da mutane su zasu gani su naɗa ka, kamar yadda yanzu nai amanna acikin raina cewa ka cancanci wannan muƙami. Kamar yadda na labarta maka a baya sarki Wilbafos na farko wato Aldaima Wilbafos da Wilbafos na biyu wato Eyriyon Wilbafos sune mutane na farko da suka taɓa yin yaƙi domin rusa rukunan Jinzidal da Amri. Kaima yaƙin da kake da rukunin Jinzidal yasa kabi sahunsu. Sannan kuma daɗin daɗawa kaima ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Na daɗe ina ƙin jinin siyarda marasa ƙarfi da ake a ban ƙasa a matsayin bayi dasa hannun manyan sarakunan duniya, amma ƙungiyar duba suka nuna min basa son shiga rigima da sarakunan Jinzidal dana Ururu domin a cewarsu babu wata nasara da zata futo daga ciki. A saboda haka na zaɓi na bi sahunka domin ganin an daina wannan kaba'ira ta siyarda mutane a matsayin bayi."


"Hmmmm...." Armad yaja dogon numfashi Babara na durƙushe a gabansa yama rasa mai zaice. 


Can bayan tsahon lokaci ya ce, "to amma idan na fuskance ka kana da wani dalili na musamman da yasa kake ganin zan iya aiwatar da wannan abu. Domin dai baza ka ajiye babban muƙamin ka na sarkin duba ba kawai ka dawo ɓangare na ba tare da wannan ba. Zanso naji mene ne."


Babara ya fara da murmushi wanda daga bisani ya juye izuwa dariya sannan bayan ɗan lokaci ya tsagaita tare da cewa, "lallai kamar yadda ake haifar duk wani ɗan ƙabilar Wilbafos ko Bayajidda ko Ururu ko kuma ƴaƴan sarkunan Jinzidal da Izza ta musamman kaima kana da taka ta musamman. Amma bazan ɓoye maka ba, lallai abu ɗaya tak da yasa nayi mubayi'a shi ne manufarka ta cimma Jinzidal. 


"Kada ka manta akwai wani yaro wanda aka haifa da baiwa irin taka kuma ɗan ƙabila ta. Nasan ka gamu dashi. Ana ce masa Ikenga O. Bayajidda. Lallai Ikenga yana da ƙarfin da zan iya yi masa mubayi'a to amma manufarsa ba irin tawa bace. Hasalima Ikenga tuni ya farkar da fasahar gidan mu ta Byajidda wato Takun-sarki, wadda Izza ce wadda ke matakin Ururu. Amma a halin yanzu kai baka farkar da fasahar gidanku ta Wilbafos ba ballantana asan wacce irin fasaha zaka samu. 


"Sanin irin fasahar da zaka samu shi ne zai nuna ko zaka iya karawa da Ururu da sarakunan Jinzidal. A taƙaice dai ina gaya maka ni Babara na ajiye muƙamina na sarkin duba a duniya nayi maka mubayi'a ba tare da sanin wacce irin fasaha zaka samu ba. Kuma na biyo ka cikin wannan kurkuku ba tare da sanin irin fasahar da zaka samu ba. Kai sani cewa irin fasahar daka samu ita ce zata nuna ko zamu iya fita daga wannan waje ko kuma anan rayuwarmu zata zo ƙarshe."


Armad yai shiru yana sauraren Babara. Babara ya gayawa Armad cewa fasahar sa ta Ɗorawa da Wilbafosiyan-siwod-dans da Al-yaya duk ba nasa bane na aro ne. Da farko Armad bai yadda ba, amma daga bisani Babara ya labarta masa cewa kowanne kabila suma da tarin fasahohinsu. Amma kadan daga cikin yan kabilar suna iya farkarda fasaha ta musamman wadda zata zama tasu. Hakan bawai yana nufin wasu baza suyi amfani da ita ba. Sai dai kawai duk wanda zaiyi amfani da ita to kamar da aro zaiyi, kuma bazai taba kaiwa asalin karfin masu ita ba. 


Ya gaya masa fasahar Dorawa ta Hidaya ce ta ara masa, sannan kuma fasahar Wilbafosiyan-siwod-dans ta kakanka ce Zaikid. Hatta fasahar Al-yaya wadda bai taba amfani da ita ba ta aro ce, asalin ta daga gidan Maikironomada ta fito. 


A saboda haka Armad yana da bukata ya farkarda fasaharsa ta musamman tasa shi kadai. 


***

Babi na 78: Yanayin Izza


Armad ya numfasa tare da duban Babara cikin mamaki ya ce, "To amma duk da haka baka bayyana min dalilin da yasa ka zaɓi wannan kurkuku a matsayin wajen da zamu yi horo ba."


Babara yai murmushi yana cewa, "sannu a hankali zaka ga dalili, ya shugaba na."


Armad najin kalmar 'ya shugaba na' ya haɗe rai. A ganinsa irin kalmomin nan ne da yakan ji aljanu na faɗawa iyayen gidansu acikin littattafan yaƙi. Amma haka dole Armad Wilbafos ya karɓi mubayi'ar sarkin duba Babara, duk da cewa bai san haƙiƙanin mai hakan ke nufi ba. 


Washe gari suka cire tanti tare da nausawa cikin dusar ƙanƙara suka nufi gabas.


Suna ƙara nausawa waje na ƙara duhu, ba daɗewa Armad ya gano cewa tsananin duhu ne yasa baya iya hango abinda ke gabansu. 


Babara ya dubi Armad ya ce, "A ganinka taya ya mutun ɗan adam yake iya yaƙar aljanu? Kasan dai ba'a ganin aljanu indai basu suka bayyana maka kansu ba."


Armad najin tambayar ya tuno abinda Babara ya gaya masa akan yayarsa Hidaya wadda ke can tana yaƙar aljanu a wata duniya ta daban. Lallai kuma haka ne, tunda sai kana ganin abu zaka iya yaƙarsa. 


Armad ya girgiza kai alamun bashi da amsa, inda Babara yaci gaba da cewa, "To wannan shi ne dalilin da yasa na gaya maka cewa cikakken ma'aboci Izza bada idonsa yake gani ba. Kuma horonka na farko zai fara daga wannan."


Babara na faɗar haka ya tsaya a tsakiyar dusar ƙanƙarar nan tare da kirawo waɗandu ɗalasimai a zuci, lamarinda ya bayyanarda aljaninsa. "Zaka fara horo da aljanina mai suna Ji-Inara."


Aljanin ya kasance jinsin muridi, yana da farar haɓa doguwa da koren gashi wanda ya futo akan ƙahonsa guda ɗaya. Hannayensa kuwa ƙananu ne ƴan gajeru kamar na jariri sabuwar haihuwa. Amma ƙafunsa sunkai tsayin zira'i sittin. Yana sanye da farar alkyabba ta ƙasaita, kana ganin yadda yake ɗaukar kansa kasan wannan aljani yana ji da kyau. 


Koda rufe bakin Babara sai aljanin ya rusuna tare da miƙa gaisuwa. Sannan kafin ya ɓace wani ƙaton al'amudi ya bayyana a hannunsa.


Babara ya numfasa ya ce, "Kada ka damu, bazai kashe kaba amma zaka sha wahala. Kayi duba izuwa Tsarin-ruhinka, yanayin me kake ji idan ka kalli Izzarka?


Armad ya girgiza kai yana cewa, "ba wani yanayi da nake ji."


Babara ya ce, "a'a dai ƙara dubawa da idon basira."


Armad na niyyar cewa a'a amma wata zuciyar tace ya duba. Saboda haka ya rufe idonsa yayi duba izuwa Tsarin-ruhinsa inda yai tsinkaye da abubuwan nan guda uku: Izza da takobi da kuma wannan mutun-mutumi mai idanu ruwan ƙasa wanda shi ne a matsayin aljanin Armad da Uznu ya kashe.


Armad ya maida hankalinsa akan Izzarsa domin jin wannan irin yanayi Babara yake faɗa amma baiji komai ba. Yana niyyar buɗe ido ya bayyanawa Babara sai yaji wata iska mai zafin gaske na tashi a hankali daga inda izzarsa take. Nan take ya fara mamakin shin dama wannan iska tana nan ne ko kuma yanzu ta bayyana, domin kuwa dai bai taɓa ganinta ba.


"Naji iska mai zafi na tashi."


Babara yai murmushi tare da cewa, "wannan iska ita ce yanayin Izzarka. Kayi sani cewa akwai yanayin izza da dama. Amma wanda aka fi sani sune yanayin zafi, yananyin hunturu, yanayin kaka, yanayin rani, da kuma yanayin damuna. Kamar kai kana da yanayin zafi ni kuma yanayin rani ne dani.


"Irin wannan yanayi da kake ji ajikin shekarunka na Izza shi zaka yi ƙoƙari kaji ajikin wannan aljani nawa tunda baza ka iya ganinsa ba. Zan tafi nayi bincike akan sharrikan dake cikin wannan kurkuku da kuma hanyoyin da zamu iya ficewa, kai kuma zaka tsaya anan ka koyi jin yanayin Izza da aljani na Ji-Inara."


Armad ya kyaɗa kai tare da amincewa. Lallai yasan cewa ba ƙaramin ƙarfi zai samu ba idan ya koyi wannan al'amari na Izza, domin hakan na nuna cewa zai iya faɗa da mutun ko aljan koda kuwa idanunsa a rufe suke. Indai zai iya jin Izzar dake jikinsu yadda yake jin Izzar dake jikinsa to lallai koda baya ganinsu zai iya sanin inda suke da kuma motsin da suke da kuma yadda zasu yi motsin. Ta haka babu wani abu da zai ɓoye masa.


Armad na cikin tunani Babara ya ɓace ya barshi da aljani Ji-Inaru. Koda ganin haka sai aljanin yai dariyar mugunta tare da ɓacewa. Abu na gaba da Armad ya sani shi ne saukar wannan al'amudi a bisa doron kansa, ba tare da yasan daga ina ba. Ƙarfin dukan ya tayarda iska wadda tayi cilli da Armad cikin dusar ƙanƙara.


Yana tashi yaga jini na tsiyaya daga cikin kansa. Babu aljani Ji-Inaru babu alamunsa. Kafin Armad ya gane maike faruwa yaji wata gudumar ta sauka a bayansa. Nan take yaji wata ƙara mai nuni da cewa bayansa ya ɓalle. Ba shiri ya zare takobi ya fara kai sara ko'ina da ina amma a banza, ko sau ɗaya bai samu aljani Ji-Inara ba. Baya ganinsa ballantana yasan inda yake. 


Nan take Armad ya gane haƙiƙanin abinda Babara yake so ya koya. Inda ya rufe idonsa ya kuma yi ƙoƙarin jin yanayin Izzar dake tashi daga jikin aljani Ji-Inaru. Armad baiji komai ba a karo na farko, lamarinda yasa ya ƙara karɓar wata gudumar. 


Koda Armad ya tabbatar aljanin nan baida imani kuma zai iya karairaya shi indai baiyi da gaske ba, saiya ƙara zage damtse. A kwana na goma bayan kimanin kowanne ƙashi na jikinsa ya ɓalle sau kamar biyu sai kwatsam Armad yaji wani abu mai kama da ruwa sanyi yana tunkaro shi ta ɓangaren dama. Nan taje yakai sara ɓangaren. Ai kuwa nan take yaji ya daki ƙarfe, saiga al'amudin aljani Ji-Inaru ya bayyana. Armad yai ihun murna tare da ƙara rufe idonsa, yana neman wannan yana yi. Amma kawai sai ji yayi al'amudin ya ƙara sauka a kansa. 


Amma duk da haka Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, ya tashi tare da ci gaba da neman wannan yanayi na Izzar aljanin. A haka dai Armad yai ta fama, wani lokacin yaji wani lokacin yasha tafka har saida ya gane haƙiƙanin mai ake nufi da jin yanayin Izza.


A haka saida Armad yai wata uku yana faɗa da wannan aljani kafin Babara ya dawo. Lokaci lokaci aljanin zai bayyana ya tausayawa Armad tare da koya masa abu ɗaya ko biyu akan Izza kafin ya ƙara ɓacewa yaci gaba da tafkarsa. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan aljani Izzarsa ce mai wannan yanayi na hunturu. 


Ana haka sai Babara ya dawo, ai kuwa abu na farko da Armad yayi shi ne fara jin yanayin Izzarsa inda yaji ta da yanayin kaka, gab da saukar damuna. 


"Lallai kayi ƙoƙari." Babara ya ce cikin farin ciki. "Na gano mana hanyar fita, amma lallai saika farkarda fasaharka zamu iya wannan aiki. Saboda haka yanzu abu na gaba shi ne farkarda fasaha."


Armad yai murmushi tare da cewa, "muje zuwa."    


***

Babi na 79: Magajin Wilbafos


Tuni Babara ya zaunar da Armad a tsakiyar wani hatimi, a ƙoƙarin farkarda haƙiƙanin fasahar Armad. Armad na zaune ido a rufe, wasu ɗalasimai na haske suna kewayashi. 


Lokaci yaci gaba da tafiya a haka. Tuni hankalin Armad ya gushe babu abinda yake gani acikin kansa sai haske. Ana haka wannan ɗalasimai suka fara cinye ƙasar dake kewaye da Armad. Ba jimawa sukai wani ƙaton rami mai kama da rijiya, inda Armad ya rufta ciki. Amma duk da haka Armad bai buɗe idonsa ba. Daga nan sai kawai wannan ɗalasimai suka kama da tsawa da walƙiya wanda suka juye izuwa aradu. Ba jimawa wannan aradu ta fara cinye jikin Armad. 


Armad na zaune ko motsi baiyi ba. Hasalaima tamkar ba jikinsa ke ƙonewa ba. Ƙafafunsa ne su suka fara cinyewa izuwa toka, sannan sai gangar jikinsa, kafin daga bisani hannayensa da wuyansa da kansa. Armad ya ƙone ƙurmus acikin wannan rijiya amma ko tari baiyi ba. Shima Babara na zaune a wajen rijiyar bai motsa ba. 


Anma duk da haka wannan ɗalasimai masu bada walƙiya da aradu basu tsagaita ba. Hasalima juyewa sukai izuwa launin ja, sannan nan take walƙiyar ta fara tsiri tana sama har saida ta taɓo sararin samaniya. Ba shiri wani baƙin hadari ya taso mai ɗauke da aradu launin ja. Samaniya ta fara rugugi tana kaɗawa tamkar za'a saukar da ruwan azaba. Amma duk da haka Babara bai motsa ba.


Nan take ruwa ya ɓarke tamkar da bakin kwarya. Duk bayan daƙiƙa biyar sai aradu ta sauka mai ƙarfin gaske. Ba jimawa wannan ruwa ya fara haɗuwa zafin aradun dake sauka suka fara narka wannnan dusar ƙanƙara data cika wannan kurkuku. 


Kwana uku cir aka ɗauka ana zabga ruwa kafin dukkan wannan ƙanƙara ta narke. Wannan kurkuku ta bayyana a fili. Ashe acikin wannan dusar ƙanƙara manya-manyan duwatsu ne na wuta wanda aka fafake cikinsu akai gidaje. Kana ganin wannan gidaje zasu tuna maka da ƙissar samudawan farko irin wanda akan bayyanasu da cewa suna ɗumamen safe da zafin rana. 


Waɗansu halittu ne sanye fatun namun dawa suka fara ambaliya daga cikin wannan gidaje na dutse da wani irin sauri tamkar na aljanun farko. Kafin ƙiftawar ido da bismillah sama da wannan halittu dubu uku sun bayyana sun kewaye Babara a inda yake zaune. Ga dukkan alamu ya tayar dasu daga baccinsu. Fuskokinsu a rufe suke da fatar farin zaki amma hakan bai hana tsananin ƙiyayya dake tashi daga cikin idanuwansu bayyana ba. Wata irin iska mai ɗauke da marmarin yaƙi na fita daga jikinsu. Sannan suna bada gunji mai amo kai kace samarin kuraye ne. Sahu-sahu sukai tare da tunkaro Babara a inda yake zaune, lallai babu ko tantama niyyarsu suyi watanda da naman Babara. Matsalar ɗaya na bayan ba lalle su samu ba.


Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Idanunsa na cike da imani da dogaro da fasahar da Armad Wilbafos zai farkar.


Ba jimawa tokar naman jikin Armad ta fara haɗewa tana curewa waje ɗaya acikin wannan rijiya wadda tuni ta cika da ruwa. Ba jimawa wata tsawa ta sauka acikin rijiyar wadda ta ƙone duk ruwan dake ciki. Babu abinda yai ragowa acikin wannan rijiya sai tokar Armad.


Ana haka wannan toka ta juye izuwa siffar Armad Wilbafos. Armad yai wani gunji mai firgitarwa wanda yasa dukkan wannan halittu jada baya. Wani taku irin na jaririn aljani ya fara fitowa daga cikin wannan rijiya. Inda daga bisani sabon saurayi ɗan kimanin shekaru sha tara ya bayyana daga cikin wannan rijiya, a jikinsa babu komai sai ɗan bante. 


Yana bayyana Babara ya buɗe ido tare da miƙewa ya kawo gaisuwa. Koda ganin haka sai waɗannan halittu suka fusata tare da rabuwa izuwa gida uku. Kaso na farko suka ɗaga hannunsu sama, inda wasu masu, masu ci da wuta suka bayyana. Kaso na biyu kuwa bakunansu suka buɗe, inda suka fara yin aman ruwan narkakken dutse wanda zafinsa zai iya ƙona wuta ita kanta. Kaso na uku kuwa wani baƙin ruwa ne ya fara ambaliya daga hannayensu, idan da Armad yana gani zai gane ruwan irin ruwan da Dordor suke amai ne.


Dukkaninsu sukai ƙaraji tare da sakar wannan hare-hare izuwa Armad. Babara yai tsalle da niyyar shiga tsakani amma Armad ya ɗaga masa hannu. Ba shiri Babara yai gefe. Lallai koda aljanun farko sai sun tsorata da wannan hari na wannan halittu, wanda ke ɗauke da tsantsar rashin imani. Domin kuwa idan ka kalli samaniya zaka ga masu, masu cida wuta sama da dubu, haɗe da guma-guman ruwan narkakken dutse sama da dubu, tare da wani baƙin ruwa mai alamun mutuwa. Kuma abu na farko da zai fara zo maka shi ne waɗannan hare-hare ana niyyar halaka gari ne dasu, babu wanda zaiyi tunanin wai mutun ɗaya ake so a halaka.


Armad ko gezau baiyi ba, hasalima ko motsa ɗan-yatsa baiba. Yana tsaye waɗannan guma-guman azaba suka saukar masa. Wata ƙara mai firgitarwa ta tashi, sannan ƙura ta turnuƙe. Lallai ko wanda ke tsaye kimanin nisan tafiyar shekaru dubu zai iya jin wannan ƙara, kuma zai iya ganin wannan ƙura. 


Babara yai ƙaraji saboda ɓacin rai ya afka cikin wannan hargitsi domin ceto Armad. Amma ba jimawa yaji wani irin yanayin Izza mai firgitarwa irin wanda bai taɓa ji ba a duk tsahon shekarunsa. Ba shiri ya fara jada baya kaɗan da kaɗan kafin wannan yanayin izza ya ƙara dukansa, lamarinda yasa ya harɗe tare da faɗuwa a ƙasa. Haki sarkin duba Babara ya fara, badan komai ba sai dan saboda ƙarfin izzar da yake ji.


Amma waɗannan halittu basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara fara shirin wani harin. Sai dai a wannan karan girman kaba'irar da suke nufin Armad da ita ya ƙaru. Domin kuwa kowa acikinsu girman harinsa ya ƙaru da sama da sau uku. 


Suna niyyar afkawa Armad sai ƙura ta lafa inda surar Armad ta futo fili. Sai dai ina, kwata-kwata ba irin Armad ɗin da aka sani bane. Babu komai a jikinsa face walƙiya. Amma abin mamakin bawai irin yanayin walƙiyar dake kewaye Armad bace a lokacin da yake amfanin da ɗalasimai irinsu Kaban'shisu. Wannan walƙiyar daga cikin tsoka da jinin Armad take. Hasalima zaka iya cewa naman jikin Armad ne ya juye baki ɗaya izuwa gundarin walƙiya. 


A wannan lokaci Armad ya zare wani mashi wanda ya nutse acikin ƙirjinsa. Amma babu komai ajikin mashin daya shafi jini ko fatar ɗan-adam. Lallai a wannan lokaci zaka iya cewa Armad wilbafos ya zama walƙiya, walƙiya kuma ta zama shi. Armad ya ɗaga hannusa sama ya dubi gundarin walƙiyar data haɗa hannunsa. Sannan daga bisani ya juyarda hannun nasa ya koma izuwa tsoka da jini. Sannan sauran jikinsa shima ƴa koma yadda yake. 


Koda ganin haka sai Babara ya zube a ƙas yana gaisuwa. "Ina ƙara jaddada mubayi'ata magajin wilbafos."


Abin mamaki sai waɗannan halittu suka cire fatar dake rufe da fuskarsu inda suka bayyana a matsayin mutane. Sannan suka zube a ƙas suna gaisuwa tare da mubayi'a.


"BARKA DA ZUWA MAGAJIN WILBAFOS, MAGAJIN SARKI EYRIYON, MAGAJIN SARKI ALDAIMA. Ka yafe mana rashin ɗa'ar mu, lallai mun cancanci kisa!!!"


A dai-dai wannan lokaci duk wani wanda yasan sirrin dake ɗauke cikin jinin MAGAJIN WILBAFOS yasan an farkar dashi.


***

Baba na 80: Tsohuwar daula


Sai da aka shafe rabin sa'a waɗannan halittu na risune a ganan Armad Wilbafos sannan Armad ya basu umarnin su tashi. Daga bisani aka kai Armad da Babara ƙasaitaccen masauki. 


Suna zaune Armad hankalinsa a kwance yana kallon irin zubi da tsari na ƙaton ɗakin da aka sauke su wanda ya kansance anyishi da zallar dutse, shi kuwa Babara har yanzu bakinsa a buɗe yake yana kallon Armad tamkar yana kallon mutuwa.


Can dai Armad ya gaji ya kada baki ya ce, "Wai mene ne?"


"E...eh?" Babara ya fara da ƙinƙina. "Wai kasan mai ka aikata kuwa har waɗannan mutane sukai maka mubayi'a?"


Armad ya girgiza kai, "a'a."


Babara yai murmushi tare da ɗora hannu aka cikin alhini yana cewa, "tunda aka halicci duniya ba'a taɓa samun mai irin wannan Izza taka ba sai mutun ɗaya koda kuwa acikin magabatanka Magada Wilbafos. Wannan mutun kuwa ba kowa bane illa Sarki Eyriyon Wilbafos, ɗan sarki Aldaima Wilbafos. Ina mai tabbatar maka cewa koda kai magajin wilbafos ne waɗannan mutane baza su ɗaga maka ƙafa ba, abu ɗaya daya sa sukai maka mubayi'a shi ne fasahar sarki Eyriyon da suka gani."


Babara na zuwa nan a zancensa sai kawai zuciyarsa ta raya masa cewa har yanzu Armad bai gane girman wannan fasaha ta sarki Eyriyon daya samu ba, saboda haka ya miƙe tsaye ya fara sabon bayani. "Kaɗau misali ace jikina ne ya koma walƙiya, hakan na nuni da cewa babu wani hari da zai iya yimin rauni ko ya cuceni, domin babu jini ko tsoka a jiki na. Duk inda aka daka zan iya mai dashi izuwa walƙiya. Kaga babu wani mahaluƙi da zai iya cin galaba akan jikinka. Da wannan fasaha sarki Eyriyon ya mulki duniya. Ya kai shugabana Armad Wilbafos, lallai al'amarinka ya girmama,." 


Can dai Armad ya fuskanci cewa Babara bazai daina bayanin falalar fasahar daya samu ba indai bai nuna masa ya fahimta ba saboda haka ya ce, "eh na fuskance ka, kuma lallai wannan fasaha ta ɗaukaka. Amma abinda ke gabana shi ne ya zan sarrafa idanuwa na domin na ceto mahaifiyata. Yau ya kamata mu fara horo akan wannan."


Babara ya kyaɗa kai yana cewa, "Eh, lallai kayi gaskiya. Fasahar marigayi sarki Eyriyon ce ta ɗauke min hankali. Amma bari na kira shugaban wannan mutane muji bayani akansu da kuma bayani akan wajen horo idan suna dashi."


Babara ya fice kuma ba jimawa sai gashi ya dawo da wani ɗan yaro wanda baifi shekaru ashirin ba. Suna shigowa yaron ya zube a ƙas ya fara bayani. "Sunana Lamarudu Wilbafos, ɗan gidan Indimi-ƙiƙi Wilbafos. An haifeni acikin wannan kurkuku, amma iyaye na sadaukai ne a rundunar sarki Eyriyon Wilbafos. Bayan kammala juyin mulkin da Ururu sukai wa ƙabilar Wilbafos sai aka ƙulle iyayenmu a wannan kurkuku. Yau shekaru dubu ɗaya kenan da ɗari takwas da kawo su wannan waje."


Koda yazo nan a zancensa sai Babara ya dakatar dashi yana mai cewa, "sadaukan sarki Eyriyon Wilbafos dole suna da babbar izza wadda zata basu tsahon kwana a duniya, bana tunanin dukkanin iyayenku da aka fara jefowa wannna kurkuku sun mutu."


Lamarudu ya amsa da cewa, "eh lallai hadimi Babara kayi gaskiya kuma idan sarki Armad bazai damu ba zamu je na nuna masa wani abu."


Babara ya kalli Armad domin neman amincewarsa kafin daga bisani ya amince su bi Lamarudu zuwa cikin tsakiyar wannan gari na cikin kurkuku.


Garin lallai bai kama da gari ba, koda yake dama wane gari za'a samu acikin kurkuku. Babu komai sai manya-manyan duwatsu wanda aka fafake izuwa gidaje, sannan duk mutanen wajen sun ɓoye acikin gidajen su na duwatsu suna tsoron kada su fito Armad ya halaka su saboda laifin da suka aikata masa.


Ba jimawa suka bayyana a gaban wata ƙofa mai ban mamaki. Ƙofar dai idan ka zagayo ta bayanta abin mamaki babu gida ko ɗaki a wajen, babu komai sai fili. Amma ta gaba idan ka kalli cikin ta zaka ga wata matattakala akan iska tayi sama. A kewaye da matattakalar akwai hatimai da rubuce-rubuce na ɗalasimai. Sannan cikin wajen kuma yayi kama da duhun tsohuwar rujiya. 


Armad na cikin nazarin wannan matattakala yaji muryar Lamarudu a kunnensa. "Acikin wannan waje akwai tsohuwar daular wilbafos, kuma aciki sirrin fita daga wannan kurkuku yake. Dukkan iyayenmu da kakaninmu suna ciki suna neman hanyar fita. Babu wanda yasan yadda wannan daula tazo wannna kurkuku, wasu suna cewa sarki Eyriyon ne ya kafa ta kafin ya mutu wasu suna cewa dama tana nan. Amma dai a haƙiƙanin gaskiya babu wanda yasan tayaya. Abu ɗaya da muka sani shi ne baza mu fita daga wajen nan ba har sai sanda iyayenmu suka fito daga ciki. Sannna kuma akwai sirrika da fasahohi na musamman wanda aka ajiye su acikin wannan tsohuwar daula wanda dasu zamu yi amfani mu fita daga wajen nan."


Armad ya numfasa ya ce, "To naji bayaninku amma ni yanzu wajen samun horo nake nema idan kuna dashi."


Lamarudu ya amsa da cewa, "Wajen horo? Sarki Armad ma yana buƙatar wani horo..." Yai shiru kamar yana jiran amsa amma Armad baice komai, saboda haka ya ci gaba, "Eh akwai wajen horo. Amma idan sarki Armad yana so ya shiga cikin wannan tsohonuwar daula ta Wilbafos domin samun fasaha da hatimai baza mu hana shi ba. Akwai manyan aljanu da zaka iya mallaka na musamman duk aciki. Sai dai kawai zamu gaya masa bazai iya fitowa ba sai yayi aƙalla sati ɗaya acikin, sannan kuma duk kwana ɗaya aciki kimanin shekaru goma ne a duniyar mu."


Armad yai murmushi tare da cewa, "kada ma ku damu. Ba saina shiga ba, kudai kawai ku nunamin wajen da zan ci gaba da horo na zuwa nan da wani lokaci."


***

Babi na 81: Kwangila 


Haka Lamarudu Wilbafos ya kai Armad cikin wani shinge wanda aka kewaye shi da manya-manyan jajayen duwatsu. Daga saman duwatsun kuma ruwa ne ke gudana zuwa ƙasa tayadda suka samarda wata ƴar ƙasaitacciyar ƙorama a ƙasa. Lamarinda yasa wajen yake bada wani irin sanyi mai inganci. Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wai shin wajen horo aka kawoshi ko kuma wajen shaƙatawa. Amma kafin ya tambaya sai Lamarudu ya ɗora hannunsa akan wani dutse inda wasu hatimai suka bayyana suka kewaye dutsen. Nan take wata ƙofa ta buɗe a wajen.


Lamarudu ya shige ciki sannan su Armad suka bishi a baya. Suna shiga wani ƙasurgumin daji mai kama da kasuwar muridan aljanu ya bayyana a gabansu. Babu komai sai manya-mayan bishiyun kuka wanda kowacce ɗaya tafi tsayin zira'i ɗari. Abin mamaki shi ne wasu manyan ƙayoyi dake kewaye da rassan wannan bishiyu a matsayin ganyayyaki.


Lamarudu ya ce, "ga wajen koyar horo. Ga kuma ɗalasimin dazai fitar daku a yayinda kuka gama." Ya miƙa musu wata takarda mai ɗauke da hatimi. Har ya juya zai fita saiya waiwayo ya ce, "dajin nan an rabashi izuwa gida uku. Dajin kuma acike yake taf da jinsin Dordor dana aljanu masu cin naman biladama. Indai har mutun baya iya jin yanayin-izza to lallai bazai iya rayuwa aciki ba. 


"Kaso na farko na dajin yana ɗauke da abubuwanda izzarsu take tsakanin dubu ɗaya da dubu biyar. Kaso na biyu suna ɗauke da izza tsakanin dubu biyar da dubu goma. Amma kaso na uku duk abinda ka gani aciki izzarsa ta haura dubu goma. Lallai duk hatsabibancinmu bama shiga yanki na uku. A fito lafiya." Ya juya ya fice ya bar Armad da Babara a wajen.


Bayan ya fita Babara ya tambayi Armad, "kaga irin kallon da wannan mutane ke yima?"


Armad ya amsa da, "eh."


Babara ya ɗanyi shiru naɗan taƙi kamar baya so ya faɗa amma daga ƙarshe ya ce, "Sunyi imani dakai kuma suna yi maka kallon zaka cece su. Hakan shi ne ma dalilin da yasa suka nuna maka waccan tsohuwar daula. Kada ka manta iyayensu sunyi wa kakanka sarki Eyriyon bauta, wanda hakan ne yasa aka ƙullesu. Cetonsu da zakai kamar ramawa kura aniyarta ne. Kuma idan ka yadda ka shiga cikin wannan daula zaka samu fasahohi da bayi na aljanu wanda zasu taimake ka a hanyarka ta zama cikakken sarki Wilbafos. Nidai ina ganin ya kamata ka shiga wannan tsohuwar daula."


Armad dama yasan tuntuni Babara bai amince da rashin shigarsa wannan tsohuwar daula ba, saboda haka tuni ya tanadi amsa. "Duk na yadda da abinda kake faɗa amma kai sani cewa bazan iya sauka daga manufata ba. Kuma lallai indai ba ganin mahaifiyata ta samu lafiya nayi ba bazan iya tsayawa acikin wannna kurkuku ba. Saboda haka inaga mu fara horo kurum."


Haka dai Babara ya haƙura dole. Sannan ya zana wasu hatimai guda uku a kewaye da Armad kafin ya bawa Armad umarnin ya zauna a tsakiya, sannan daga bisani ya fara karanta wasu ɗalasimai. 


Can bayan sa'a ɗaya ana cikin wannan hali sai fuskar Babara ta canja, inda nan take ya daina karanta ɗalasiman ya garzayo gaban Armad inda ya ɗebi kaɗan daga jininsa ya zuba acikin wata kwalba mai ɗauke tsumi. Armad dai ya ji wani abu amma yai shiru baice komai ba ya ƙurawa Babara ido.


Can Babara ya kalli Armad cikin alhini yana cewa, "dama nayi tunanin haka, amma ina ta addu'a ya zama hakan bata faru ba."


Armad yai zumbur ya ce, "ban gane ba. Mai kake nufi da dama kayi tunanin haka?"


Babara ya fara bayani, "labarin daka bani na ɓacewar Miyurarka bawai Miyurarce kaɗai ta ɓace ba, harda wani ɓangare na ruhinka. A sakamakon haka bazaka iya amfani da idanuwanka ba har sai ka nemo wannan ɓari na ruhinka."


Armad ya zare ido. "Eh?!"


Babara ya ce, "bari mu gani idan zan iya gano inda ɓarin ruhin naka yake." 


Nan take ya ƙara ɗiban wani jinin daga hannun Armad ya kuma yaryaɗar dashi akan ƙasa, inda ya zana wasu hatumai masu rikitarwa akansa. Can daga bisani jinin na Armad ya fara yin haske, kafin daga bisani ya kama da wuta. Nan take sukai tsalle gefe, amma kafin suyi wani abu tuni jinin ya ƙone ƙurmus.


Babara ya dubi Armad ya ce, "ruhinka yana katange acikin wata sihirtacciyar ƙasa amma saboda ƙasar na kewaye da Tsari baza a iya gane wacce bace."


Armad yama rasa mai zaice, domin kaf maganar a baibai yake jinta. Wai ruhinsa ya ɓalle? Bayan kuma gashi nan da rai da lafiya. A iya saninsa ma wannan ba abu bane mai yiwuwa ba. 


Yana cikin tunani yaji muryar Babara, "nasan mai kake tunani, kuma kayi sani nima wannan shi ne karo na farko da naga mutun ruhinsa ya rabe kuma ya ci gaba da zama da rai. Amma dai maganar tana nan cewa bazaka iya yin amfani da idonka ba har sai ka nemo ɓangaren ruhinka."


Armad ya kalli zoben dake ɗan yatsansa inda mahaifiyarsa ke ajiye. Can bayan tsahon lokaci Armad ya yanke shawara, inda ya numfasa ya ce, "idan za'a fara bada tarihi na, za'ace na fara ne daga nemo ɓangaren ruhina daya ɓalle. Saboda haka inaga zaman mu a wannan kurkuku yazo ƙarshe, lallai inada mahaifiyata a gabana bazan tsaya neman suna acikin wannan kurkuku ba."


Babara ya rusunar dakai alamun girmamawa sannna ya ce, "ya shugaba na akwai wata hanya banda idanuwanka da zaka iya bawa mahaifiyarka izza da ban gaya maka ba."


Armad najin haka yai zumbur cikin murna ya ce, "ko? Kamar ya fa?"


"Kamar yadda ka sani kowanne ɗan adam yana samun ƙayyadaddun shekarun izza lokacin daya farkarda izzarsa, kuma wannan adadi a ƙa'ida baya taɓa canjawa. Koda kaima dalilin da yasa naka suka canja daga hamsin da ɗaya zuwa dubu ɗaya dan kawai baka farkarda izzarka ta haƙiƙa bane da farko.


"Amma akwai wasu hanyoyi guda biyu kacal wanda ake iya ƙara yawan izza. Hanya ta farko na riga na gaya maka ita. Ita ce ta amfani da sirrin dake cikin idanun ƴaƴan Wilbafos. Hanya ta biyu wadda ban gaya maka ba ita ce hanyarda ake kira da KWANGILA!!"


***

Babi na 82: Kwangila 


Saida Babara ya tabbatar hankalin Armad na kansa sannan ya ci gaba da bayani. "Baza ka fahimci haƙiƙanin mai ake nufi da Kwangila ba sai ka fahimci yadda alaƙa take tsakanin aljanu da mutane. Sudai aljanu kayi sani cewa da damansu suna da girman kai kuma ba a son ransu bil'adama ke amfani da fasahohinsu ba. Amma ana amfani da izza wajen danne su, domin su miƙa wuya.


"Saboda haka wannan alaƙa an raba ta mataki ɗai-ɗai har shida. Mataki na farko shi ne mafi ƙanƙanta, mataki na shida mafi girma: fasahar da mai mataki na biyu zai iya amfani da ita mai mataki na ɗaya bazai iya ba. Haka fasahar da mai mataki na uku zai iya na biyu bazai iya ba. 


"Matakai ukun farko su ake kira da BAUTARWA, ukun ƙarshe kuma su ake kira da MALLAKA. Wato dai a taƙaice duk wanda yake da alaƙa da aljaninsa a mataki na ɗaya zuwa na uku kawai yana bautarda wannan aljani ne, amma wanda yake a mataki na huɗu zuwa na shida ya mallaki wannan aljani har abada. Banbancin ƙarfin izza da fasaha dake tsakanin wannan matakai guda biyu tamkar sama da ƙasa ne. Kaɗan daga ciki shi ne duk wanda yakai matakin Mallaka yana iya fito da aljaninsa waje ya sashi aiki, kamar yadda na haɗa ka da aljani na Ji-inara ya koya maka yanayin izza. 


"Idan nace zan fassara maka banbanci tsakanin matakai biyu kwana ɗaya ma bazai ishemu ba, amma bari mu dawo kan abinda nake so ka sani wato Kwangila.


"Ita dai Kwangila wata fasaha ce wadda kaɗai waɗanda suka kai mataki na shida a fannin alaƙa da aljanu suke iya amfani da ita. Duk wanda ya mallaki wannan fasaha to bawai kaɗai aljaninsa ya mallake ba, hatta fasahar aljanin tasa ya mallake ta kuma ta zama tasa har duniya ta naɗe sai dai in mutuwa yayi. Kuma duk wani mahaluƙi da yake son yin amfani da ita to sai ya biya wani kaso na izzarsa. Wannan kaso aljaninka shi yake ɗauka daga cikin izzarka ya biya aljanin wannnan ma'aboci izza daya mallake wannnan fasaha. Hatta kaima lokacin daka fara yin amfani da fasahar walƙiya na tabbatar saida aljaninka marigayi Jidaime ya biya wannan da shekarunka na izza. Amma ba lallai ka gane ba tunda ba wani kwarewa kayi a fannin izza ba, sannan kuma daga abinda ka gayamin aljanin ba shiri kuke yiba saboda abinda Hidaya tayi masa. 


"Kayi sani cewa ta hanyar wannan fasaha aka gina manyan daulolin daka sani guda biyar a doron ƙasa. Ɗauki daular Han ta doron ƙasa na uku wanda shugabanta sarki Han ya mallake fasahar wuta. Kuma duk wanda zaiyi amfani da ita saiya biya wannnan kaso na izza a lokacin daya fara. Daular Denizawa su suke da mulkin walƙiya. Daular Sisiya ta sarki Bihanzin mai dauwamammen sara su suke da Iska. Daular Maikironomada ta sarki Maikiro Abbas su suke da Ruwa da ƙanƙara. Daular Infiriya waɗanda akafi sani da Rafiyawa su suke da fasahar kasa da turɓaya.


"Ka hango miliyoyin mutanen da suke amfani da aljanu, kuma ka hango cewa kowa acikinsu ya biya wannan kaso na izza kafin ya fara amfani da fasaharsa. Sannan kayi tunani akan irin yawan izzar da waɗannan dauloli suke dashi a ajiye tun daga sanda aka kafa duniya har izuwa yau. Sai kuma ka tambayi kanka mai suke da wannnan izza. Kayi sani cewa wannan dalili shi yasa daulolin nan guda biyar baza su taɓa faɗuwa ba domin kuwa suna da tsananin ƙarfinda hatta Ururu babu yadda zasu yi dasu idan suka haɗa kai. 


"Dalilin da yasa nake maka wannan bayanin shi ne zaka iya tambayar Nostaljiya sisiya acikin rumbun izzarsu ta bawa mahaifiyarka wani kaso. Daga yadda kayimin bayaninta ina ganin kamar baza taƙi ba. Amma duk da haka zamu iya nemo ɓarin ruhinka ka koyi fasahar idanuwanka, amma dai gaskiya ina ganin tunda abin yazo da haka gwanda a gwada wannnan hanya. Domin yanzu wa yasan lokacinda za'a ɗauka kafin ka gano ruhinka. Amma dai ban san meye shawararka ba."


Armad yai shiru yana sauraren Babara har saida ya tsaya sannan ya numfasa ya ce, "Nostaljiya? Eh gaskiya tana daga cikin mutanen da nafi yadda dasu amma bana son na ɗora mata nauyi. Amma fa wannnan tsarin na kwangila yana da ban tsoro, kuma lallai zai bawa daulolin nan ƙarfi mai firgitarwa. To amma ni yanzu da nake amfani da fasahar walƙiya ba tare da aljani ba yaya kenan?"


Babara ya numfasa ya ce, "to ai ya shugaba na wannan shi ne mafi girman falalar dake cikin fasaharka ta Eyriyon. Domin dai kaga kai yanzu babu ruwanka da tsarin kwangila, sannnan duk abubuwa wanda suke ɗaure aljanu irinsu Farar-laya da sanyin-babban-sihiri baza suyi aiki akanka ba. Sannnan kuma duk wani mai amfani da aljani saiya jira aljanin ya tara masa wannan walƙiya ko wuta koma dai meye, kamar yadda kaza take yin kwai a ɗiba. To amma kai baka buƙatar wani aljani domin kuwa kai kake samarda walƙiyar ka."


Koda jin haka sai wani murmushi yazo fuskar Armad. Shima yasan lallai a halin yanzu mai iya cinye shi a fagen izza saiya shirya. 


Haka dai Babara yaci gaba da yiwa Armad bayanai akan fasaharsa har zuwa wani lokaci kafin daga bisani Armad ya yanke shawarar fita daga wannan kurkuku. Kodai ya nemo ruhinsa ko kuma ya tambayi Nostaljiya. Saboda haka suka karanta wannnan ɗalasimai ƙofa ta buɗe suka futo daga cikin wajen horon. 


Sai dai kuma abu na farko da suka tarar a bakin ƙofar saida yasa suka jada baya. Dukkanin mutanen wannna kurkuku sun jeru sun durƙushe a bakin ƙofa. A jere suke sun ɗaga hannu sama suna addu'a. Hasalima da dama kuka suke yi. Koda ganin haka sai Armad ya jada baya cikin mamaki yana tambayar Babara mai ke faruwa.


Babara ya amsa da cewa, "Addu'a suke. Ƴan addinin Amraikugyu Bayajidda ne, ana kiransa da addinin musulunci. Naji labari cewa wasu daga cikin ƴaƴan Bayajidda da ƙannan sarki Eyriyon, ƴaƴan sarki Aldaima sun karɓi addinin."


Wannna ne karo na farko da Armad ya taɓa jin wata kalma wai musulunci, hasalima dai wanda suke da addini a doron ƙasa bakwai ƴan tsirari ne, kuma suma din da yawa Ɗalasimai suke bautawa.


A wannna lokaci Armad ya gano cewa da yawa daga cikin wannan mutane yara ne, kuma lallai kamar yadda Babara ya gaya masa duk da ƙarfinsu amma sun dogara da Armad tun bayan ganin fasaharsa. Ga dukkan alamu koma meye acikin wannan tsohuwar daula yafi ƙarfinsu kuma suna neman agaji. Saboda haka nan take Armad ya juyo ya dubi Babara ya ce, "Ina umartarka daka shiga wannan tsohuwar daula a maimako na. Kuma duk wani taimako da suke buƙata kayi musu a yayinda bananan." 


Koda rufe baki sai Armad ya fito da Ubbaru daga cikin zobensa ya kuma yanki hanya. Domin ya fara ji acikin ransa idan yaci gaba da zama acikin mutanan nan to zasu shiga ransa su hanashi fita nemowa mahaifyarsa magani.


***

Babi na 83: Bango


Duk da gudun dokinsa Ubbaru saida Armad yai kwanaki goma sha ɗaya yana tafiya sannan ya fara hango Bangon arewa. Gangar ruwa iyakacin ganinka ta shafe kudu da yamma gabas da arewa, tana ta kwaranya izuwa ƙasa amma babu ko halitta ɗaya a samanta. Koda Armad ya hangi wannan sai yaja linzami ya tsaya, inda ya buɗe zoben sihiri da Nostaljiya ta bashi domin ya futo da mahaifiyarsa. 


Babara ya gaya masa duk bayan kwana biyu akwai wani tsumi da zai ringa bata har zuwa lokacinda zai samu wannan shekarun Izza ya bata. Shi dai wannan tsumi shi ne abinda Babara ya ringa bata tsahon shekarunda Armad yayi bayanan kuma har ya dawo ya same ta cikin ƙoshin lafiya. A lissafin Babara mahaifiyar Armad tana buƙatar aƙalla shekarun izza dubu goma kafin ta warke. Wannan shekaru ba wani abu bane a wajen sarakunan jinzidal masu fasahar kwangila, saboda haka Armad ya gama yanke shawara kai tsaye wajen Nostaljiya zaije. Kuma tunda a hannunsa akwai wani ɗalasimi daya karɓa daga wajen Babara wanda zai iya gano masa inda ruhinsa yake zai iya yin aiki biyu a lokaci ɗaya, yana neman ruhinsa kuma yana neman Nostaljiya.


Amma koda wannnan tunani ya gilmawa Armad a rai saiya tuno cewa ai bama abu biyu ba, lallai abu uku zaiyi a lokaci ɗaya. Domin kuwa akwai alƙawari daya ɗauka na kawarda cinikin bayi a ban ƙasa, wanda kuma bai manta dashi ba. Koda tunanin haka sai Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya shiga inda ya samu waje ya rubuta sha huɗu ga wata tara shekarar 1855 Bayan Amri. Wato dai a wannan rana ce Armad ya fara shirinsa na rusa rukunin Jinzidal. 


Bayan ya gama kallon wannnan kwanan wata saiya juya izuwa ɗakin daya ajiye mahaifyarsa, inda ya shiga ya same ta a kwance, idanunta a rufe kamar tana bacci. Mahaifiyar Armad tana bada yanayin kwarjini matuƙa wanda saboda haka ba kowanne ma'aboci izza bane zai iya tunkararta ba a hakan da take a sume. Gashin kanta na nan baƙi, kuma kamar yadda wannnan cuta ta izza take a har kullum alamar kawai shi ne mutun zai zamanto a sume, amma banda haka babu wani abu dazai nuna rashin lafiya kamar irinsu tari ko zazzaɓi. 


Koda zama a gefenta sai kawai wani hawaye ya fito daga idonsa, babu abinda yake tunawa sai lokutan da yana yaro da kuma lokaci na ƙarshe daya ganta da lafiya. Tsahon lokaci a haka kafin ya buɗe bakinta ya ɗisa mata wannan tsumi dake cikin wata ƴar kwalba. Sannan ya taso ya futo idanunsa cike da kwalla. Lallai akwai abubuwa da dama da yake so ya tambayeta idan ta farka. Saboda haka babu wani abu dazai tsaya a gabansa. Har Armad yaje bakin ƙofar wannan zobe zai fita sai ya tsaya ya juyo inda ya durƙusa yayi alƙawari, ƙololuwar alƙawarinsa cewa a wannan fita kozai rasa ransa bazai dawo ba sai mahaifiyarsa ta warke. 


Yana fitowa ya rufe ƙofar wannan zobe sannan bayan yaci abinci ya mayarda Ubbaru cikin zobensa ya kuma nufi wannnan bango a ƙafa. 


Yana isa gaban wannan bango wata izza irin wadda bai taɓa jintaba ta dakeshi tayi cilli dashi gefe. Yana faɗuwa yaga jikinsa ya fara narkewa, fatarsa tana ɓanɓarewa. Nan take Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya. Wanda hakan ne ya cetoshi tunda hatta wuta bata isa ta ƙona walƙiya ba. 


Nan take Armad yai murmushi tare da cire zoben dake hannunsa ya cilla a baki sannan ya ɗaga hannunsa sama ya kirawo ɗaya daga cikin ɗalasimansa daya daɗe baiyi amfani dasu ba wato Kaban'shisu. Idan mai karatu bai mantaba wannan ɗalasimi ana iya amfani dashi ayi tafiya acikin lokaci daga wani waje zuwa wani. Matsalarsa kawai ita ce sai ɗaya kacal ake iya amfani dashi a shekara. Tuntuni dai Armad yayi tunanin amfani da wannan ɗalasimi ya fice daga cikin wannan kurkuku to amma bai gama abinda ya shigo dashi ba, sannnan kuma baya son yabar Babara anan. 


Nan take ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, inda ya ɓace daga inda yake. To amma a wannan lokaci maimakon ya tsinci kansa a bayan wannan bango sai kawai ya ganshi acikin tsakiyar bangon, kewaye dashi wani ruwa ne mai tsananin danƙo. Abu na gaba daya biyo baya wasu abubuwa ne manya-manya guda biyu suka bayyana a gaban idon Armad. 


Ɗaya daga cikinsu yana kama da wata daren goma sha uku, ɗaya kuma yana kama da rana saidai dukkaninsu baƙaƙe ne wuluk. Waɗannan abubuwa suka ƙura masa ido tamkar wasu idanun mayunwaciyar kurar da taga abinci. Nan take Armad yaji ya fara rawar ɗari. A lokacin ne ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya jikinsa ya narke babu abinda ya rage face ƙoƙon kansa. Kuma wai a hakan ma dan ya riga ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ne, lallai da tuni ya tsinci kansa a lahira. 


A wannan lokaci ya fuskanci abubuwa guda biyu. Na farko dai bawai a waje ɗaya yake tsaye ba, hasalima mugun gudu yake acikin wannnan bangon saboda ɗalasiminsa na Kaban'shisu. Wanda hakan ya nuna masa cewa saɓanin fahimtarsa da ɗalasimin bawai ɓacewa yake yiba a lokacin da yayi amfani dashi, kawai dai saboda tsananin sauri ne kawai yake ganin kamar ɓacewa yayi. 


Abu na biyu daya fuskanta shi ne wannnan abubuwa guda biyu dake kama da rana da wata ba wasu abubuwa bane illa idanuwa guda biyu na Ururu. Kuma hatta rawar ɗarin da yake ji daga su ne. 


A take Armad ya gane cewa lallai koda ya taho da Babara lallai bazai iya wucewa dashi ba. Domin ba daban jikinsa na walƙiya ba da tuni ya mutu aƙalla sau ɗari zuwa wannan lokaci. Sannan kuma ya gano cewa yayi dabara daya saka zobensa acikin bakinsa domin da tuni ya narke. 


Ana cikin haka wannnan idanuwa guda biyu suka fara haske suna fitarda wani yanayi mai firgitarwa. Ba shiri Armad yaji tamkar ana caccaka masa allurai acikin kansa. Abin mamaki sai kawai ya ganshi ya tsinci kansa a tsakiyar filin yaƙi, kewaye dashi sarakunan Ashura ne guda goma. Kowanne acikinsu yana riƙe da baƙar takobi. Kafin Armad yai wani motsi su goma sunyi tafiya acikin lokaci sun cake masa wannnan takubba acikin ƙirjinsa. Ko motsi baiyi ba ya faɗi matacce. Abin mamaki a gaske ma a wannna lokaci hankalin Armad ya gushe, babu wanda ya sani ya mutu ko kuwa yana raye.

---------

A dai-dai wannan lokaci acan doron ƙasa ta farko sarakuna goma mafi girma a duniya, wanda aka fi sani da ASHURA, ne suke jin wata sarewa mai alamar ƙugen yaƙi tana kaɗawa. Wannan sarewar nada ban mamaki tayadda duk wanda yaji ta kawai zaiji sarewa ne amma banda sarakuna goma na ASHURA. Su saƙo suke ji akan wani mutun da yayi ƙoƙarin ficewa daga kurkukunsu. Amma acewar wannan murya, idanuwan sarki Ururu Kuyurussa'ayi, idanuwanda suka yaki sarki Eyriyon Wibafos, sun halaka wannnan mutun har lahira.


***


Babi na 84: Ɗan-Baiwa


Bayan gushewar hankalin Armad dukkan jikinsa saiya fara juyewa daga walƙiya yana komawa toka. Kafin ƙiftawar ido da bismilla Armad ya juye izuwa toka. Nan take wannan toka ta narke acikin wannan ruwa kafin daga bisani ayi watsi da ita ta dawo cikin wannan kurkuku. Idan da zaka ga yadda akai watsi da wannan toka zaka fuskanci cewa hatta ragowar tokar ba'a yadda ta fita daga wannan kurkuku ba. Lallai abinda ake faɗa na cewa indai ka shigo ka shigo kenan haka yake. 


Amma ba jimawa ƙarfin fasahar Armad ta ƙara warewa, wannan toka ta kama ci da walƙiya. Sannnan daga bisani ta juye izuwa surar Armad, kafin daga bisani ta juye izuwa Armad a kwance a sume yana aman jini.


Haka Armad yaci gaba da kasancewa acikin wannan hali baisan inda kansa yake ba har tsahon kwana biyar. A kwana na biyar ɗinne wasu mutane sanye da kayan farar fatar raƙumi su biyu suka iso wajen. Dukkaninsu suna kan ingarmar dawakai, sannan kuma suna riƙe da takubba. 


Na damansu ne ya fara sakkowa inda ya zunguri Armad da ƙafa domin ya gano da rai ko ba rai. Kafin daga bisani ya ɗaɗɗaure shi a jikin dokinsa kafin su koma da Armad inda suka fito. 


Armad bai san yadda akai ba, kuma bai san kwana nawa yai ba, kawai dai ya farka ya tsinci kansa a cikin wata ƴar bukka shishi kaɗai. Yai shiru yana tunano abubuwan da suka faru dashi acikin bango, inda nan take wata tambaya ta faɗo masa. Shin ya fita daga kurkukun ko kuwa har yanzu yana ciki. Abu ɗaya daya sani shi ne idanda da matsala da lallai acikin ankwa zai ganshi, amma gashi nan a sake akan gado.


A wannan lokaci yaji surutan mutane a waje saboda haka nan take ya gano cewa hanya ɗaya dazai samu amsar wannan tambaya shi ne ya fita waje ya tambayi ɗaya daga cikin mutanenda yaji suna magana a wajen tantin. Saboda haka ba tare da tunanin mai zai faru ba Armad ya buɗe ƙofa ya danna kai waje. Abin mamaki yana fitowa yaga babu ko mutun ɗaya dake gadinsa, suma masu wannan magana suna can gefe kuma kallo ɗaya sukai masa suka ɗauke kai suka ci gaba da hira. 


A kewaye da wajen duk irin wannan bukkoki ne sama da hamsin. Daga gaba garesu kuma akwai wannan ruwa da ake kira da bango, lamarinda yasa Armad ya gano cewa lallai akwai matuƙar yiwuwar haƙarsa bai cimma ruwa ba. Ajikin bangon akwai wani baƙin ƙarfe wanda yai sama sosai tayadda ba'a iya gano ƙarshensa.


Akwai mutane a wajen amma basu da yawa, kuma abin mamaki ba ruwan kowa da kowa, kowa harkarsa kawai yake. Can dai Armad ya kasa daurewa ya tare wani mutun sanye da jallabiya ya tambayeshi, "Malan da ALLAH ina ne nan?"


Mutumin ya kada baki ya ce, "baka ma san inda kake ba. Kaine wanda aka ce yayi ƙoƙarin shiga ta cikin bango kai tsaye ko?" Mutumin na faɗar haka ya wuce gaba ba tare da amsawa Armad tambayarsa ba.


Armad ya haɗe rai yana niyyar finciko mutumin baya sai yaji murya a gefensa. "Kana shalkwatar ƴan-daban ƊAN-BAIWA."


Armad ya juyo da kansa ɓangaren inda yaji muryar inda yai arba da wani saurayi kalar larabawan yamma mai yawan dogon gashi mai launin ja da fari. "Shalkwatar ƴan-daban ƊAN-BAIWA? Wane ne ɗan-baiwa kuma?"


Saurayin ya ja dogon farin gashin dake kansa tare da yin murmushi yana cewa, "kamar yadda ka sani wannan kurkuku an rabata tsakanin ɓangarori guda uku. Shekara ɗaya baya, ɓangare ɗaya basa ƙoƙarin guduwa daga wannan kurkuku, amma dama can ɓangarori biyu sun daɗe suna ƙoƙarin guduwa. Amma a yanzu hatta wannnan ɓangare ƙoƙarin guduwa suke. Wanda hakan ya jawo sauye-sauye da dama acikin wannann kurkuku. Da dama ana ganin wannan canji yana faruwa ne saboda bayyanar wannan mutun da ake kira da ƊAN-BAIWA, duk da babu tabbashi akan wannan maganganu amma lallai a yanzu sama da kaso sittin na wannan kurkuku suna biyayya ga wannan mutun mai suna ɗan-baiwa. Babu wanda yasan daga inda yake ko kuma tayaya ya shigo wannan kurkuku amma bisa mamaki tuni jama'a suka naɗashi a matsayin sarkinsu. Suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Ni ne na ceto ka daga inda ka suma." Wannan mutun ya kammala  bayaninsa da miƙawa Armad hannu su gaisa.


Abubuwa da dama Armad bai fahimta ba saboda haka yai shiru yana tunanin mai zaice masa. Baima kula da dogon sunan wannan saurayi ba. Koda saurayin yaga haka sai yai tunanin ko Armad bai yadda dashi ba ne, saboda haka ya ce, "Kada da damu, dani da abokina muka ceto ka. Kuma a wannan waje babu wanda ya damu dakai, sai dai kawai kai sani cewa muna zaune Tsarin dake jikin bangon nan ya fara haske irin wanda ke nuna cewa wani yayi ƙoƙarin guduwa. Hakan ne yasa akai ƙungiya ta mutun bibiyu domin su kewaya su gano inda abin ya faru. Ta haka ne dani da wanda aka haɗani muka gano ka."


Armad ya numfasa ya ce, "nagode. Amma ina da tambayoyi da yawa. Da farko dai wanne sunanka acikin sunayen daka gayamin?"


Saurayin yai murmushi tare da cewa, "suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Kada ka damu a hankali zaka riƙe su. Da dama sukan ɗau lokaci."


Armad yaja numfashi mai tsayi kafin ya girgiza kai. "To amma menene manufar wannan shugaba naku mai suna Ɗan-baiwa? Sannan kuma shin zan iya tafiya idan ina so?"


Wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Eh zaka iya tafiya mana, amma idan har kana so kaga Ɗan-baiwa to ka tsaya domin kuwa yau zai biyo ta wannan waje."


Armad ya tsaya yana tunani kafin daga bisani yai ajiyar zuciya. Babban abin shi ne duk wata tambaya da Armad yayi wa saurayin bao amsa masa ita ba kai tsaye. Hasalima har yanzu bai masan taƙamaimai meke faruwa ba. Daɗin daɗawa jikimsa bai gama warewa ba. 


Yana cikin tunani yaji muryar wannan saurayi a kunnensa yana cewa, "zo kaga zanensa kafin ya ƙaraso." Saurayin yaja Armad izuwa wata kwana. Suna isa wasu mutane ne guda shida suke ta kallon wani ƙaton zane dake kafe a jikin bango.


Suna matsawa kusa sai Armad ya fara jin abinda suke cewa. "Shi ne Ɗan-baiwa. Yadda ka ganshi a jikin hoton nan haka yake a gaske. Kana ganinsa kasan jarumi wanda zai iya canja duniya."


Koda Armad yaji wannan kalamai sai ya ƙara azama domin yaje ya ga wannan ɗai-baiwa da idonsa. Amma yana isa ya tararda hoton wanda ya sani kamar tafin hannunsa ajikin wannan zane.


Wannan dai ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda.


Koda ganin wannan zane sai Armad yaja da baya cikin tsananin mamaki da ɗimuwa. Ya dubi wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Wannan ne ɗan-baiwan?"


Saurayin ya kyaɗa kai, "Eh shi ne. Kasan shi ne?"


***

Babi na 85: Ƙabilar Nára


Koda Armad yaga wannan zane na Ikenga sai zuciyar ta yamutsa, ya rasa abinda ke masa daɗi. Abin mamakin shi ne fafatarwarsu da Ikenga a shekarar data gabata ita ce take ta dawo masa. 


Yana cikin haka yaji muryar wannan saurayi  a gefensa. "Kasan ɗan-baiwa ne?"


Nan take Armad yai sauri ya farfaɗo daga zurfin tunanin daya shiga. "Eh... a'a! Na dai taɓa gamuwa dashi a wajen kurkukun nan."


Koda jin wannan amsa sai saurayin ya haɗe gira cikin mamaki, kafin daga bisani ya numfasa ya tambayi Armad. "Ya akai kuka haɗu? Ko kaima mabiyinsa ne a wajen wannan. kurkuku?"


Cikin sauri Armad ya amsa da cewa, "a'a, ni ban san ma yana da mabiya ba ballantana na zama ɗaya daga cikinsu. Shi kuwa meye manufarsa ta haɗa mabiya? Yaƙi yake shiryawa ko kuma me?"


Wannan saurayi yai murmushi, "Eh.. lallai wannan ita ce tambayarda kowa yake tayi a tsahon shekara ɗayannan da ɗai-baiwa ya shigo wannan kurkuku. Sai dai kuma babu wanda yake da amsarta sai shi kansa da kuma manyan kwamandojinsa guda biyar dake haɗa masa jama'a. Kamar dai yadda na gaya maka ana saka ran ɗan-baiwa zaizo nan yau, kuma koda baizo yau ba lallai acikin satin nan zai bayyana domin yiwa mabiyansa bayani akan manufofinsa."


Koda jin wannan jawabi sai Armad ya yanke shawarar lallai ya kamata yaji wannan manufofi na Ikenga. Domin kuwa duk da Armad baisan Ikenga sosai ba amma fafatawar da sukai tasa yana ji a ransa cewa akwai wani sirrin Izza a tattare dashi. Sannan kuma babban abinda ya tsayawa Armad a rai shi ne maiya kawo Ikenga wannan kurkuku, domin kuwa a lissafi shekarar Ikenga ɗaya cir da zuwa wannan kurkuku. Wanda hakan ke nuna cewa Ikenga yazo kurkukun lokaci kaɗan bayan gama fafatarwarsa dashi a gasar Jinzidal. Lallai da sake. Akwai wani abu dake faruwa a ƙasa. 


"Sailári, shin kana ganin nima zan iya shiga naji wannnan manufa ta Ikenga?" 


Wannan saurayi najin wannan tambaya ya fashe da dariya yana cewa, "Sailári? Wato a duk sunaye na guda biyar biyar shi ka riƙe. To ba komai, hakan ma yayi. Amma dole na gaya maka cewa Sailari suna ne da kishiyar babata ta saka min, saboda haka mahaifiyata bata faɗarsa. Kai sani cewa ina da wata ƙanwa mai suna Ranâ-Ƙísa-Hurura-Inshala-Yaƙa-Dása. Ita wannan ƙanwa tawa indai tayi laifi babarmu ta dake ta to ranar baza ta faɗi kowanne suna ba sai Sailári, wai itama ta rama saboda tasan maman mu bata so." 


Saurayin ya ƙara yin dariya yana tuno da, kafin daga bisani ya amsawa Armad tambayarsa. "Eh zaka iya zuwa mana. Mabiyan ɗan-baiwa suna da yawa, babu wanda ma zai gane kai baƙo ne."


Armad ya kyaɗa kai ya ce, "to indai haka ne kuwa zanje. Amma mai yasa dakai da ƙanwarka kuke da sunaye har guda biyar? Inzan iya tunowa sunanka Indimi-Iyka-Sailari-Citta-Abati."


Saurayin ya amsa da cewa, "A kabila ta duk yaron da aka haifa yakan samu sunaye daga ɗaya zuwa ɗari. Dalili kuwa shi ne haƙƙin saka suna yana kan duk wanda suke zaune gida ɗaya da wannnan yaro da aka haifa. Misali a gidanmu mu biyar ne sanda aka haifeni. Babata ta saka min Indimi, babana ya saka min Abati, kakata ta saka min Iyka, Kishiyar babata ta saka min Sailari, sannan sai kuma yar aikinmu ta saka min Citta. Shi yasa ƙanwata kuma sunanta ya zama guda shida saboda nima na ƙaru sanda aka haifeta." 


Saurayin na zuwa nan ya ja Armad izuwa tantinsa yana cewa. "Muje mu shirya kafin ɗai-baiwa yazo." 


Sai dai suna cikin tafiya ya fashe da dariya kamar wanda ya tuno wani abu. Armad yai niyyar tambayar mai yasa yake dariya amma ya fasa. Can dai Sailari ya kada baki ya ce, "na tuno wani aboki da aka haifa a gidan yawa. Sunayensa guda saba'in da bakwai ne. A lokacinda muka shiga makaranta akan ɗauki rabin awa ana kiran sunayensa idan akazo kiran suna."


A zuciyar Armad ya ce lallai akwai al'ada kala-kala a duniya. Idan kaji wata ma saika riƙe baki.


Suna shiga Sailari ya jefowa Armad ɓarin gurasa yana cewa, "satinka ɗaya baka ci abinci ba amma jikinka bai nuna yana jin yunwa ba, lafiya kake kuwa?"


Armad najin haka ya zare ido tare da kallon gurasar. Lallai kuma haka ne. Abin mamakin shi ne saida ma akai magana sannan ya tuna, domin kuwa da daida kwayar zarra baya jin yunwa ko ƙishirwa. Lallai ba lafiya ba. Amma ba daɗewa Armad ya tuna da cewa ashe fa dukkan jikinsa ya juye izuwa walƙiya, saboda haka baya buƙatar yaci abinci dan yunwa sai dai kawai dan marmari. Amma a haƙiƙa wannan ba abu bane da zai iya gayawa kowa kai tsaye ba. Domin wannan sifa ce ta manyan sarakunan aljanun, kuma zaiyi wahala a yadda cewa ba aljani bane shi indai aka ji. Saboda haka yai murmushi kawai tare da jefa gurasar a bakinsa amma bai bawa Sailari amsarsa ba. Shima Sailarin bai damu ba kawai yaci gaba da hirarsa. 


A wannan rana saida Armad yasan kusan komai akan ƙabilar Nára, wadda ita ce ƙabilar su Sailari. Amma Ikenga baizo ba, washe gari ma haka, har saida akai kwana uku. Magana ta tabbata cewa mutumin daya haɗa kan fursunonin wannnan kurkuku suke masa biyayya acikin shekara daya kacal, wanda akafi sani da ɗan-baiwa zaizo wannan yankin na ƴan-daban warure, kuma anan zai bayyana manufofinsa. Saboda haka kullum wajen ƙara cika yake da mutane. Kullum Armad zai kewaye ya nuya yana gwada fasahohinsa domin ƙara kwarewa, sannan kuma yana nazarin Bango domin ganin hanyar guduwa. Amma hakan bai hana Sailari yin hira dashi ba ta sama da awa biyar a kowacce rana.


A rana ta biyar Armad ya haƙura da ganin Ikenga yana niyyar tafiya sai kwatsam ƴan shela suka fara yin shelar cewa ɗan-baiwa ya bayyana. Nan take fursunonin nan suka fara ambaliya suna tururuwa izuwa ga ɗan-baiwa. Armad na tsaye daga gefe tare da Sailari suna kallon. Sai a lokacin Armad ya gane lallai akwai mutane da yawa a wajen. 


Ba jimawa saiga Ikenga nan ya bayyana sanye da jajayen kaya samfurin alkyabba, rataye da takobinsa. Abin mamaki sai Armad yaga duk da cewa ga kama nan amma kamar Ikenga ya ƙara girma da faɗi sosai da sosai. Ba jimawa ya gane cewa ƙarfin Izza ne kawai ba wani abu ba. Koda gano haka sai Armad ya rufe idonsa domin jin yanayin-izzar Ikenga. Amma bisa mamaki babu komai, tamkar Ikenga baida wata izza. Ya tuno da abinda Babara ya gaya masa na yadda wasu manyan ma'abota izza suke ɓoye yanayin-izzarsu domin kada kowa yasan halin da suke ciki. 


Armad na cikin tunane-tunanensa yaji hayaniya, Ikenga ya bayyana.


***

Babi na 86: Ikenga da Armad


Mutane sun jejjeru iyakacin ganinka a gaban dakalin da Ikenga ke tsaye shi da tawagarsa. Kuma saboda da ragowar hasken rana kowa na ganin kowa tar-tar. Babu murmushi ko ɓacin rai a fuskar Ikenga saɓanin mabiyansa wanda keta murna da shewa. 


Koda bayyanar Ikenga sai wannan taron jama'a suka ƙara ruɗewa da shewa. Babu abinda kake ji sai sunan ɗan-baiwa. A dai-dai bayan Ikenga wani tsoho ne a tsaye, wanda ba wani bane illa wannan mutun mai suna Kána dake tare da Ikenga. A bayan Kána wasu sadaukai ne sanye da kayan yaƙi daban-daban susu biyar. Dukkaninsu ba'a ganin fuskokinsu.


Armad najin yanayin-izzarsu ya gane cewa babu wanda acikinsu bai haye izza dubu ba. Amma ko a jikinsa. Abinda kawai ya dami Armad shi ne yaji manufar Ikenga ya bar wajen. 


Ana jira Ikenga ya fara jawabi kawai saiya juya ya koma inda ya fito. Lamarinda yasa nan take wajen yai tsit, kowa ya fara kalle-kalle yana tunanin maike faruwa. Ana cikin haka shima Kána tare da mutun biyar ɗin dake bayansa suka bi bayan Ikenga. 


Koda ganin haka sai Armad yai tsaki gami da juyawa izuwa tantinsa domin  yin shiri ya kama gabansa. Saboda haushi ko Sailari bai yiwa magana ba. Amma bisa mamaki a lokacin ne yaji muryar Ikenga a kunnensa. 


"Idan kana so kaji manufata to ka rufe idanunka kayi tafiya kimanin taku hamsin a jikin bango kana fuskantar gabas kana kiran ɗalasimin 'Shaibal'shísu' zaka bayyana a fada ta."


Koda jin wannan batu sai Armad ya haɗe gira yana mamakin yadda Ikenga ya iya shiga kansa yayi magana ba tare da ya bashi izini ba. Amma kawai ya share yai kamar baiji ba. Inda ya nufi tantinsa ya haɗe kayansa ya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya saka su aciki. Abu ɗaya ya rage kafin ya bar wannan waje, shi ne sallama da Sailari. 


A wajen tantin jama'a ne barkatai suke ta tattaunawa akan dalilin da yasa ɗan-baiwa baice komai ba, amma bisa mamaki babu wanda ya juyawa ɗan-baiwa baya duk da haka. Hasalima wasu da dama daga cikinsu suna ganin abinda yayi ya dace da girman izzarsa.


Armad na fitowa ya fara laluben Sailari acikin tantinsa, amma babu shi babu labarinsa. Saboda haka ya nufo cikin taron jama'ar nan inda ya barshi. Duk da ruɗani da yawan jama'ar dake wajen ba jimawa sukai ido huɗu da Sailari a tsaye yana jimamin rashin jin muryar Ikenga. 


Armad ya jashi wajen mutane ya ce, "kai yanzu Sailari baka damu da abinda Ikenga... ɗan-baiwa yayi ba?" 


Koda jin wannan magana sai Sailari yai murmushi ya ce, "ai wannan ba wani abu bane. Mutun biyar ɗin da ka gani a bayansa sune manya-manyan ma'abota Izza acikin wannan kurkuku kafin bayyanar ɗan-baiwa. Mutane kamar mu basu isa suje kusa dasu ba ballantana su gansu. Ai ganin ɗan baiwa kaɗai da mukai falala ce." 


Koda jin wannan magana sai Armad ya fara gane yanayin yadda ake rayuwa a wannan kurkuku; mai ƙarfi kamar wani abin bauta ne. Sannan kuma Armad ya tabbatar cewa Sailari zai iya dagewa saiya bishi idan yaji cewa zai tattauna da Ikenga. To amma Armad bai san yanayin yadda zata kaya ba. Ƙazamin faɗa zai iya rincaɓewa tsakaninsa da Ikenga saboda haka bazai iya tafiya dashi ba. 


Nan take Armad ya fasa gaya masa inda zaije. "Au haka abin yake... Ai ban sani ba. Bari naje na dawo ai kana nan ko?"


Sailari ya kyaɗa kai, yana niyyar tambayar Armad mai yasa yake kiran ɗan-baiwa da Ikenga amma ya fuskanci sauri Armad yake saboda haka ya fasa. 


Haka Armad ya bi ta tsakankanin wannan taron jama'a ya ratse can nesa izuwa shiyar da Bangon yake. Yana isa ya nufi gabas tare da fara lissafa adadin takun da yake. Babu wani tsoro ko kuma tunanin mai zai faru da yake. Yana jin cewa Ikenga bai isa ya cutar dashi ba a yanayin ƙarfin izzarsa.


Ba jimawa Armad ya cika adadin wannan taku da Ikenga ya bashi, inda ya buɗe idonsa ya tsinci kansa a wata ƴar ƙaramar farfajiya kewaye da rafi. Komai dake wajen dai-dai yake idan ka ɗauke launin ruwan dake cikin wannan rafi. Ja ne jajawur, hasalima da dama zasu yadda idan aka ce jini ne ba ruwa ba.


Armad na bayyana ya iske Ikenga shi kaɗai a zaune kan kujera ta ƙasaita. A gaba dashi akwai wata kujerar wadda ba kowa akai, sannan a tsakiyarsu akwai ɗan teburi ɗauke da abin sha irin na mutanan farko. Ikenga yai wa Armad nuni daya zauna akan wannan kujera, sannan ya miƙa masa abin sha.


Armad kai tsaye ya zauna ya kurɓi wannan abin sha wanda bai taɓa ganinsa ba sannan ya dubi Ikenga da wani kallo mai cike da tambayoyi. Koda ganin haka sai Ikenga yai murmushi tare da cewa, "kana da tambayoyi da dama amma kayi sani na kira ka nan ne domin na baka dama wadda baza ka ƙara samun irinta ba. Saboda haka tambayoyinka sai dai su jira.


"Zan fara kai tsaye. Ina so a matsayinka na Magajin Wilbafos kayimin mubaya'a. Ni kuma zan arzutaka da abubuwa guda huɗu."


Koda Armad yaji wannnan magana saiya fashe da dariya yana cewa, "ni zanyi maka mubayi'a ko kai zakai min?"


Amma bisa mamaki sai Ikenga yaci gaba da bayani tamkar baiji me Armad ya faɗa ba. "Abubuwa huɗu dazan arzutaka dasu sune; na farko zan gaya maka inda ɓarin ruhinka yake, na biyu zan gaya maka labarin mahaifinka, na uku zan baka ɗalasimin dazai fitar dakai daga wannan kurkuku, sannan na huɗu zan kare ka daga wani babban sharri dazai faru dakai acikin wannan shekarar mai zuwa."


***

Babi na 87: Alƙiblar Armad 


Koda Armad ya ga lallai Ikenga da gaske yake saiya canja fuska tare da kyara zama. Ya dubi Ikenga ya ce, "Idan zan iya tunowa lokaci na farko da na ganka akan wani tsibiri ne ana rigimar Littafin-takobi. Kuma a wannan rana ta dalilinka na rasa Miyura ta tare da ɓarin ruhi na.


"Lokaci na biyu dana gamu dakai ƴar uwata Nusi ta gano hanyarda zan samo Tarifil-fakta na ceto mahaifiyata amma bisa sharadin sai nayi nasara a gasar Jinzidal. Kai ne sanadiyyar rashin samun nasara ta da kuma faɗawa hannun Uznu Ururu da nayi, sannan kuma da rasa ƴar uwata Nusi wadda har yanzu ban san inda take ba.


"To yanzu gashi mun kara gamuwa dakai a lokaci na uku. Sai dai kuma a wannan lokaci kazo da wani sabon salo na buƙatar mubayi'a. Kai sani cewa ban damu da me kake ciki ba, ban damu me kake ƙullawa ba, ban damu da yadda ka shigo wannan kurkuku ba, ban damu da ko kana da hanyar fita ba ko baka da ita ba, ban damu da mai yasa kake haɗa mabiya acikin wannan kurkuku ba, ban damu wani hasashenka na wani sharri dazai faru dani ba, ba damu ko kasan inda ruhi na yake ba. Amma abu guda ɗaya dazan gaya maka, ni Armad Wilbafos saina kawarda Jinzidal a ban ƙasa kuma saina samowa mahaifiyata lafiya koda sama da ƙasa zasu haɗu. Idan kana tunanin kana da karfin izzarda zaka iya hanani to ka gwada. Wannan shi ne kashedi na farko kuma na ƙarshe da zan baka."


Koda Armad yazo nan a zancensa saiya ɗauki wannan kofi ya ƙara kora abinsha. Sannan yaja kujerarsa baya ya miƙe da niyyar tafiya. Amma a wannan lokaci Ikenga shima ya canja fuska ya kuma fara bawa Armad jawabi.


"Ni Ikenga O Bayajidda saina mallaki wannan duniya koda kuwa mutane da aljanu da Ururu zasu haɗa kai su yaƙe ni. Domin tun a ranar da aka haifeni tauraruwa ta take bada hasken sarauta. Bari na baka kaɗan daga cikin tarihi.


"Kafin zuwan Ururu, kafin zuwan Wilbafos, kafin zuwan Bayajidda, akwai taurari a sararin samaniya. Wannan taurari su suke tsara tafiyar lokaci da zamani a yadda aka sanshi. Bayan juyin mulki da Ururu sukaiwa ƙaɓilarka sai wannan taurari suka dusashe. A shekarar da aka haifeni wannan taurari suka ƙara bayyanar da haskensu, kuma tun daga wannan rana alƙalami ya riga ya bushe cewa sai na mallaki duniya. 


"Tun ina yaro nake iya karanta tafiyar taurari na gano abinda zai faru na gaibu dama wanda ya riga ya faru. Ina ɗan shekara bakwai na fara amfani da taurari ina sarrafa lokaci, wanda ta haka ne takobi na take iya tsofantar da duk abinda na sara ta hanyar zuƙe shekarun dake jikin wannan abu. Babu wanda yasan tayadda na rayu bayan yaƙin daya halaka gari na amma da wannan fasaha na kuɓuta daga hannun Ururu a wannan yaƙi.


"Gamuwa dakai da nayi a lokaci na farko kawai kaciɓis ne da kuma ƙaddara, amma kafin lokacin ban taɓa sanin dakai ba a duniya. A gamuwa ta dakai ta biyu na gano cewa ajikin ka akwai wani sirri na musamman, amma kuma akwai inuwar mutuwa dake tattare da ruhinka. Wanda indai ka shallake ta to lallai zaka zamanto magajin wilbafos da ba'a taɓa gani ba. Nayi niyyar kashe ka a faɗan da mukai a Jinzidal dan kada ka kawomin cikas, amma na canja shawara.


"Nayi tunanin idan ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a dani dakai zamu iya kawarda da daular Ururu da kuma sarakunan Jinzidal mu kawo tamu daular. Saboda haka a wannan lokaci na ɗora ɗalasimai masu aiki da tafiyar taurari acikin wannna filin daga da muka fafata tayadda koda wani abu ya faru zan iya ceto ranka. 


"Bayanda Uznu ya bayyana aniyarsa a fili ta halaka ka saina ƙara ƙarfin wannan ɗalasimi, amma sai bayan na ɓace sai taurari suka bayyana min cewa Uznu neman littafin-takobi yake bawai taƙamaimai kai yake so ya halaka ba. Saboda haka sai na juyo izuwa wannan fili da niyyar na canja fasalin wannan ɗalasimi, amma duk da nayi amfani da hasken taurari na ɓoye kaina saida idanun Uznu Ururu suka ganni, lamarinda yasa matsala ta faru a yayinda nake canja yanayin wannan ɗalasimi. Daga nan ni kaina ban san maiya faru ba, amma Uznu yayi amfani da wannan ɗalasimi da nasa domin kare ka ya cillo ƴar uwarka izuwa wannan kurkuku. 


"Bayan komai ya lafa na ƙara yin bincike akanka na gano cewa ruhinka ya rabe gida biyu, sannan kuma na gano cewa zaka bayyana acikin wannan kurkuku duk da cewa lokacin da zaka zo bai bayyana a gareni ba. Saboda haka na yanke shawara wannan kurkuku ita ce waje mafi dacewa da kayimin mubayi'a sannan kuma mu fara shirin yadda zamu mulki duniya.


"A saboda haka ne nazo wannan kurkuku tun waccan shekara na jira ka amma baka zo ba sai yanzu. Acikin shekarar data wuce na gano cewa shi kansa Uznu yayi kuskure, maimakon ya jefo Nusi zuwa wannan kurkuku sai ta zarce izuwa sashin Ikwatora. Ban san mai take ciki ba amma lallai bata cikin matsala kuma tauraruwarta tana bada haske na lafiya.


"Nayi amfani da wannan dama ta kasancewa a wannan kurkuku na fara haɗa kan mabiya a wannan kurkuku. Bawai dan ina buƙatar su ba, domin kuwa kai kaɗai ne abinda ya shigo dani wannan kurkuku, kuma a kowanne lokaci naga dama zan iya fita cikin sauƙi. Alƙawarurruka na guda huɗu suna nan, abinda kawai kake buƙatar kayi shi ne ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a."


Armad yai shiru yana sauraron Ikenga, abubuwa da dama sun ɗau hankalinsa acikin bayanan Ikenga. Akwai yiwuwar ƙarya Ikenga yake akwai kuma yiwuwar gaskiya ne. Bayan tsahon lokaci yana tunani sai yayi murmushi sannan ya bawa Ikenga amsa a nutse.


"Manufarka mulki, manufa ta ceto wanda basu da ƙarfi daga tafarkin cinikin bayi, lallai alƙiblarmu ba ɗaya bace. Sannan kuma ina so ka sani koda alƙiblarmu ɗaya ce kaine zakai mun mubayi'a ba nine zanyi maka ba. Kakana Eyriyon wanda na gaji fasaharsa sarki ne na duniya baki ɗaya. Ƙabila ta mulki dukkan duniya. Ina da ƙarfin fasahar da jikina bazai taɓa halaka ba, bana buƙatar ci ko sha. Ina da ɗalasimai wanda sun girmi lissafinka. Bama kaiba Ikenga, babu wanda ya isa nayi 

masa mubayi'a a wannan zamani. Kamar dai yadda na gaya maka a farko, idan kana ji zaka iya hanani aiwatar da manufa ta, to ka gwada.


Armad na rufe baki ya juya ya fice.


***

Babi na 88: Sabuwar fasaha


Lallai akwai raini acikin abinda Ikenga yayi wa Armad, domin duk wanda ya nemi kayi masa mubayi'a to lallai yana nuna cewa yafi ka ƙarfin izza. Wannan shi ne abinda yake ta kai-komo a zuciyar Armad tun bayanda suka rabu da Ikenga. 


Babban abinda yafi ɗaukewa Armad hankali shi ne yadda Ikenga yake nuni da cewa yana iya shiga da fita ta cikin Bango ba tare da matsala ba. 


A halin yanzu Armad baida lokacin tsayawa yayi nazari akan labaran da Ikenga ya bashi, ko gaskiya ko ƙarya. Saboda haka ya yanke shawara zai ƙara gwada ficewa ta cikin wannan bango. Idan ya wuce shikenan, idan kuma bai wuce ba saiya koma izuwa Babara da mutanen Lamarudu Wilbafos. 


Amma Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa ƙara shiga Bango ba tare da wani shiri ba lallai halaka ne, saboda haka tuni Armad yai amfani da kwakwalwarsa ya gano wata sabuwar fasaha. Hasalima akan hanyarsa yake ta gwada wannan fasaha. 


Wajenda Armad yake tafiya yayi nisa da Bango sannan yana da ƙarancin ƙanƙara. Amma wata irin iska ce mai ƙarfin gaske take kaɗawa. Babu gida gaba babu gida baya, babu wani rai a wannan waje face Armad. Tuni Armad ya alkinta kansa da kayan sanyi daga cikin zoben da Nostaljiya ta bashi. Yana tafiya yana ƙara sauri, yasan dai-dai inda zashi.


Lallai wannan kurkuku ta musamman ce, domin babu wanda ake ƙullewa acikin ɗaki ko kuma a bayan kanta. Fili ne kawai fetal iya ganinka. Kowa yana da damar yayi yawo acikin ta, yayi gini ma idan yana so, ya haihu ya rayu, yayi duk abinda yaga dama. Amma dai bazai fita daga cikinta ba har abada. Wannan shi ne sharaɗin wannan kurkuku. Tuni Armad ya samu taswirar wannan kurkuku a hannun Sailári, wanda da ita ya gano dai-dai wajenda yafi ko'ina sharri acikin kurkuku. Wajenda mutanen cikin kurkukun basa ko ziyara.


Shi kuwa Armad wannan waje nan ya tunkara da niyyar gwada sabuwar fasahar da yake ƙoƙarin amfani da ita domin fita daga wannan kurkuku.


Ba jimawa Armad ya bayyana a tsakiyar bishiyu dogaye masu kama dana tsamiya. Abu na farko daya fara yi masa sallama shi ne kukan Dordor da aljanu. Koda jin haka sai Armad yai murmushi tare da cusa kai cikin duhuwar dajin dake gabansa. Ai kuwa yana shiga wata ƙatuwar damisa wadda tafi girman duk wata damisa daya taɓa gani ko ji ta bayyana a gabansa. Babu alamun jira ko haƙuri a tattare da ita a yayinda ta afko masa da saurin gaske tana dalalar da yawu. 


Armad ya rufe idonsa domin banbance wacce irin damisa ce. Kasancewar duk jinsin dabbar da suke iya amfani da izza an ware su, kuma su ake kira da ALJANUN-DABBOBI, misali idan wannnan damisa tana iya amfani da izza sai ace mata aljanar-damisa. Aljanun dabbobi suna da matuƙar banbanci da sauran dabbobin dawa wanda basu da izza a wajen sauri da tsananin ƙarfi da rashin imani. Kuma da yawansu abincinsu shi ne naman mutane. Wannan aljanun-dabbobi su ne dalilin da yasa jama'ar wannan kurkuku suke gujewa wannan daji. 


Armad na rufe ido yaji yanayin-izza a tattare da wannan ƙatuwar damisa, lamarinda yasa ya tabbatar cewa aljanar-damisa ce. Amma bisa mamaki duk da wannan damisa tana gab da cimmasa Armad bai motsa daga inda yake ba, kuma bai maida jikinsa walƙiya ba. 


Suna yin arba da wannan damisa ya buɗe baki ya kira ɗalasimin KABAN'SHÍSU. Lamarinda yasa ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan wannan damisa. Yana ɓacewa yaji wannan damisa taci birki tana laluben inda yake. A dai-dai wannan lokaci Armad yaji shekarun Izzarsa dubu sun girgiza, nan take ya fara ganin dishi-dishi yana jin jiri. Yaji wani tari mai ƙarfi ya taso masa, kafin yai wani abu ya fara tari yana aman jini. Wannan damisa najin tarinsa ta juyo izuwa gareshi da mugun nufi.


Armad dai yasan maiya taka, domin tunda yake bai taɓa karya dokar da kakansa Zaikid ya ɗora masa ba akan ɗalasimin Kaban'shísu, wato bai taɓa yin amfani dashi sama da sau biyu a shekara ba. Amma a wannan lokaci yayi amfani dashi sau biyu a wata ɗaya.


Armad na cikin wannan hali wannan damisa ta ƙara cimmasa, amma ya rufe ido ya ƙara kiran ɗalasimin Kaban'shísu. Inda ya ƙara ɓacewa ya bayyana a bayan wannan damisa. Nan take jini ya fara fita daga idanunsa da kunnuwansa. Armad yai wata ƙara saboda tsananin zafin da yake ji, tamkar ana jera garwashi akan fatarsa. Amma wannan damisa ta ƙara yiwowa kansa, inda yai ƙaraji tare da ƙara kiran wani ɗalasimin a karo na uku. Nan take yaji mutuwa ta fara yi masa sallama, ba shiri ya juye izuwa gundarin walƙiya. Amma duk da haka saida ya faɗi ƙasa sumamme. 


Wannan damisa ta faɗa kansa da niyyar tsinke masa kai, amma koda hasken walƙiyarsa ya dake ta saita jada baya. Bayan tsananin ɓacin ran rasa abincinta ta ɗanyi turje-turje da gurnani kala-kala kafin ta bar wajen. 


Armad yaci gaba da zama a wannan halin tsahon kwanaki shida, inda bayan ya farka ya tsinci kansa a kewaye da aljanun-zakuna farare masu jajayen idanuwa. 


Koda tashinsa saiya fuskanci jiransa kawai suke ya juye izuwa mutun su cinye namansa. Tunda baza su iya cinyeshi a haka ba to bari su jira. 


Armad yai murmushin izza tare da juyewa izuwa mutun. Wannan aljanun-zakuna guda uku suka nufo shi gadan-gadan. Armad ya ƙara kiran ɗalasimin Kaban'shísu ya bayyana a nesa dasu kimanin taku goma. Yana bayyana ya ƙarajin irin raɗaɗi da tashin hankalin da yaji a baya. Su kuwa wannan zakuna suka ƙara yiwowa kansa. Armad ya ƙara kiran ɗalasimin ya ƙara ɓacewa ya bayyana ƙafa goma gaba da inda yake. Wannan zakuna suka ƙara fusata suka tisa shi.


A haka a haka saida Armad ya kira ɗalasimin Kaban'shísu sau biyar sannan ya faɗi ƙasa sumamme. Wannan zakuna sukai iyayinsu su halaka shi amma tuni ya juye izuwa walƙiya haka suka haƙura. 


Bayan kwanaki ya ƙara farkawa ya ƙara maimaita irin sak abinda yayi. Sannan ya ƙara maimaitawa. Ba jimawa Armad ya kai tsahon kimanin wata uku a wannan daji yana gwada amfani da wannan ɗalasimi. Bayan ya samu nutsuwa ya koyi abinda ya kawo shi saiya juya izuwa Bango domin jarraba wannan fasaha. 


Ita dai wannan sabuwar fasaha ta samo asali ne daga ilmin Armad na ɗalasimin Kaban'shisu da kuma ƙarfin fasaharsa ta walƙiya. Da ita zai iya tafiya cikin tsananin sauri daga wani waje zuwa wani tayadda za'a ga kamar ɓacewa yai. Tun a sanda ya shiga Bango a karo na farko ya gano cewa shi kansa ɗalasimin Kaban'shísu bawai ɓatarda mutun yake ba, yana saka mutun yai tafiya cikin tsananin sauri tayadda za'a ga kamar ɓacewa yayi. To idan kuwa haka ne, idan ɗalasimi guda ɗaya ya wutar dashi rabin hanya an watsoshi waje, to idan yayi amfani da ɗalasimi goma a lokaci ɗaya zai iya wucewa. 


Daɗin daɗawa wannan sabuwar fasaha ta Armad zata bashi damar cin galaba akan abokan fafatawarsa cikin sauƙi. Domin kuwa komin sharrin daya tunkaro shi zai iya ɓacewa ya dauje masa. Sannan zai iya bayyana a bayan abokin fafatawarsa ya aiwatar da harinsa ba tare da an ankara ba. 


Armad yayi niyyar sakawa wannan fasaha sabon suna amma daga ƙarshe ya yanke shawarar yaci gaba da kiranta da Kaban'shìsu.


***

Babi na 89: Hannun-Aradu 


Armad na tafe yana goge takobinsa, rabonsa da amfani da takobi an kwana biyu. Kai hatta harin ƙawanyar-walƙiya an daɗe rabonda yayi amfani dashi. A iya tunaninsa tun bayan fafatawarsa a gasar Jinzidal. A halin yanzu hannunsa ƙaiƙayi yake, saboda haka maimakon ya kewaya ya zagaye wannan daji sai ya yanka ta tsakiyarsa. 


Ai kuwa ko taku goma bai yiba Dordor uku masu kai ɗai-ɗai da wasu aljanun-shirwa guda biyar suka tunkaro shi. Dordor suna kawo masa hari ta ƙasa, shirwa na kawo masa hari ta sama. Armad yai murmushi tare da dunƙule hannunsa na dama. Sannan ya juyarda dashi izuwa walƙiya ya daki iska dashi yana cewa, "HANNUN-ARADU."


Haka na faruwa wata farar walƙiya mai layin kore-kore ta fara ɓulɓula daga hannunsa tare da afkawa wannan shirwowi da Dordor. Wannan shi ne karo na farko da Armad yayi amfani da wannan fasaha mai suna Hannun-aradu, wadda ta banbanta matuƙa da ƴar walƙiƴar daya saba amfani da ita ada. Idan ka kalli dunƙulen hannunsa na dama zaka ga ya juye izuwa walƙiya sannan kuma walƙiya tana ɓulɓula daga cikinsa tamkar ana ambaliyar ruwa. Duk abinda wannan walƙiya ta taɓa saita narkar. Babu wani abu dake tsaye a gabanta face Armad Wilbafos. Bayan daƙiƙa bakwai Armad ya saki hannunsa ya ɗauke walƙiyar sannan yai duba izuwa abinda ya aikata. 


Dukkan abubuwan dake gabansa sun ƙone ƙurmus, babu shirwa babu Dordor babu koda bishiyu da suka rage. Babu komai sai ƙarfin izzar Armad wilbafos. Wannan daji ya ƙone  ƙurmus tamkar ba'a yishi ba. Daga inda Armad ke tsaye yana hango Bango. 


Armad yai murmushi tare da tunkararsa. Tuni dai ya gano wata hanya da zaiyi amfani da ita domin ƙirƙiro sabuwar fasahar takobi amma ba sauri yake ba zata iya jira. Saboda haka ya tunkari wannan Bango gadan-gadan. Yana isa ya juye izuwa walƙiya sannan ya kira ɗalasimin Kaban'shísu. 


Armad ya tsinci kansa a tsakiyar wannan ruwa mai kauri wanda ke narka jikin ɗan adam. Yana bayyana ya ƙara ido biyu da wannan baƙaƙen idanuwa na Ururu. Amma tuni Armad ya shirya musu, kafin wani abu ya faru tuni ya ƙara kiran wani ɗalasimin, ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaba da inda yake. Wannan idanu suka ƙara bayyana suna neman haɗiye amna Armad ya ƙara ɓacewa da taimakon sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu.


A haka saida Armad yayi amfani wannan ɗalasimi sau goma, a kowanne lokaci yana ƙara kusantar ƙofa amma wannan idanu suna ƙara cimmasa. Armad yasan iyakacinsa ɗalasimi goma, kuma indai ya wuce haka to a take zai fara aman jini ya sume. Amma babu yadda zaiyi, baiyi tunanin ɗalasimi goma baza su isa ba. Saboda haka ya rufe ido ya ƙara kiran wannan ɗalasimi a karo na goma sha ɗaya. Abun mamakin shi ne duk da yana walƙiya amma hakan bai hanashi aman jini ba da jin zafi da radaɗin wannan ɗalasimi ba. 


Gabda Armad zai sume ya ga wani haske ya rufe masa ido, bashi da tabbas mene ne amma yana fatan hasken fita daga kurkukun ne.


**

A can doron ƙasa na farko kuwa wannan sarewa dake gadin wannan kurkuku ce ke ƙara bada labarin wani mai ƙoƙarin ficewa daga cikin kurkuku. Amma a wannan karan ya samu damar fita, sannan kuma abin mamaki irin ruhi ɗaya ne sak da wancan mutun da yayi ƙoƙarin fita a watan baya. 


Nan take wannan sarewa ta bada umarnin ayi maza-maza a kamo wannan mutun sannan a gane mene ne alaƙarsa da wancan mutun da yayi ƙoƙarin guduwa a watan baya. Shin duk mutun ɗaya ne bai mutu ba ko kuma wani ne mai irin ruhinsa. 


Gidan Uznu Ururu shi ne gidan da aka ɗorawa alhakin kamo wannan fursuna.

**      

Al'ada ce sananniya kwararrun matuƙa jirgin ruwa sukan sakawa jiragensu sunaye. Wani suna kawai na sha'awa ne wani kuma yakan dace da tsarin jirgin. A dai-dai wannan lokaci wani madaidaicin jirgin ruwa ne ke tafiya akan Bangon arewa ya nufi doron ƙasa ta huɗu, daular Sisiya. Sunan wannan jirgi Fataken-dare. Yakan ɗauki jama'a aƙalla ɗari biyu da hamsin zuwa ɗari uku, kuma shaidar safararsa tana tsakanin doron ƙasa ta uku data huɗu. 


Duk da kasancewar yawan ƙofofin Eycigan da ake tafiya ta cikinsu amma duk da haka masu sana'ar jirage basu rasa abinci ba, indai ka yiwa jirgin ka shaidar kariya ta hukumar tafiye-tafiye ta sarakunan jinzidal to zaka samu fasinja. Rashin yin shedar na nuna kana daga ɓata gari ku kuma ɓarayin ruwa.


Jirgin Fataken-dare na tafiya sannu a hankali iska na kaɗashi izuwa hanyarsa. Fasinjojin wannan jirgi na harkokin gabansu cikin kwanciyar hankali, sun san nan da wata ɗaya mai zuwa zasu isa garuruwansu a daular Sisiya.


Shi kuwa kyaftin ɗin wannan jirgi sunansa Bisaiya Sisiyu. Asalinsa ɗan daular Sisiya ne kuma tunda ya taso yake yin sana'ar kwandasta a irin wannan jirage, yanzu gashi a ɗan shakara talatin ya mallaki nasa jirgin. Duk da bashi da izza amma yana da ma'abota izza guda shida dake aikin tsaro a jirginsa. Kuma ko a wannan lokaci mutun biyu daga cikinsu na tare dashi.


Bisaiya ya dubi ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ce, "idan iska ta bamu dama nanda kwanaki ashirin zamu isa. Shi yasa dole saina ɗauki ma'abocin aljanin iska aiki."


Mutumin sanye da fararen kaya ya gyaɗa kai yana cewa, "gaskiya ne, kyaftin Bisaiya. Amma duk da haka ina tunanin zamu isa a yadda muka tsara." 


Bisaiya baice komai ba, kawai yaci gaba da kallon gangar ruwan dake gabansu. Yana sane da cewa ƙaro wani ma'aikacin dole zai jawo ya kori ɗaya daga cikin ma'aikatansa shida dan bazai iya biyansu ba, amma dole yana buƙatar wanda zai ringa ɗaure masa 'iska' a yayin tafiyarsu.


Yana cikin wannan tunani ne sai ya hango wani abu kwance a gaban jirginsu. Abun yana ta iyo yana sama da ƙasa kamar ƙirgin itace. Da farko Bisaiya bai ɗauki wani abu ba saida yaga abin yana motsi kamar ɗan adam. Nan take ya haska fitilar jirgin saitin abun domin ya tabbatarwa da idonsa. Ai kuwa wani saurayi ne kwance a sume ba kaya a jikinsa. 


Abu na farko daya fara zuwa ran Bisaiya shi ne wannan ɗaya ce daga cikin dabarun ƴan fashin ruwa. Domin ka tsaya ceto suyi maka fashi.

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...