Babi na 40 : Ƙusar tsafi
Alƙalin wasa Ghalee ya kira wasa na gaba. Deniz Bizáya ɗan sarki Deniz Iluru ya fito kan filin wasa tare da abokin karawarsa wato Ikenga O Bayajidda.
Kai daga ganin tsaiwar waɗannan jarumai biyu kasan sun banbanta da sauran.
Sa'ilin nan kuma tsayuwa ce wadda ake gani a jikin jaruman farko waɗanda ƙafafunsu suka ginu a fagen daga.
Fuskokinsu babu tsana ko kallon raini a game da junansu, lamarinda ke nuna cewa kowa acikinsu ya yarda da matsayin Izzar abokin fafatawarsa, amma fa kana ganin idanunsu zaka ga kafiya, irin ta ƙololuwa. Irin wadda lallai idan mutun ya sa abu a gaba, to saiya cimmasa.
Tunda farko dai babban dalilin da yasa Ikenga ya riga kowa zuwa shi ne goron gayyata da Deniz Bizáya ya aika masa na cewa yana jiransa yazo su motsa jini kafin a fara gasar!
Haka kuma akai, Ikenga yazo, shi kuma Bizáya yasa aka buɗe masa ƙofa tun ma kafin lokacin fara gasar yayi.
Kwanansu goma sha uku su na fafatawa a gaban waɗannan giwaye, lamarinda yasa daga ƙarshe suka haƙura aka tashi kunnen doki, dan kowa ya kasa samun nasara.
Kuma a ƙarshen wannan doguwar fafatawa da sukai, kowa acikinsu ya tafi da abu guda ɗaya acikin ransa; cewa indai yana so ya zamo na ɗaya a wannan gasa to saiya ƙara ƙarfin Izzarsa fiye da ɗan'uwansa domin inba haka ba kuwa, sai dai koda sun haɗu a zagayen ƙarshe, a ƙarayin kunnen doki. Dan haka kyautar ma sai dai a raba musu. Wanda kuma wannan abu ne da babu wanda acikinsu ya yarda dashi.
Hakan nema yasa kowa acikinsu yayi amfani da ragowar kwanakin wajen ƙara samun horo. Kuma yanzu gashinan sun haɗu tunma kan aje zagayen ƙarshen.
Deniz Bizáya ne ya fara magana da cewa, "inaga babu buƙatar mu ɓata lokaci a wannan faɗan, dani dakai kowa yasan kowa! Kar tasan kar!
"Kuma jan faɗa a tsakaninmu a wannan mataki, ba abu ne mai amfani gare mu ba. Domin zamu iya gajiya ko kuma mu jiwa juna rauni, kuma ba lalle a bada hutu mai yawa a tsakanin wannan zagaye dana gaba ba.
"Shin mai zai hana muyi wani abu a gaban kowa!"
Yana zuwa nan a zancensa ya rufe idanunsa, bayan kimanin daƙiƙa biyar ya buɗe; yana buɗewa baƙar kwayar idonsa ta ɓangaren dama ta ɓace gaba ɗaya, kuma a wajenta na da babu komai sai hoton wani zane guda ɗaya mai kama da ƙatuwar ƙusa irin wadda ake ginin gidajen aljanu da ita!
Wanda idan ka ɗaga idonka, ka kalli goshinsa dai dai wajenda ya kamata ace Miyura ce, zakai arba da sak irin wannan hoton ƙusa na cikin idonsa, sai dai kawai ya fishi girma.
To idan da a haka abin ya tsaya, to da da sauƙi, amma buɗe idanun Bizaya keda wuya gaba ki ɗayan ilahirin cikin wajen filin ya fara girgiza kamar zai kife.
Can bayan kamar daƙiƙa goma sai komai ya tsaya cak, amma kuma kowa ya samu kansa cikin sakin baki dan mamakin abinda suke gani tsaye cak a bayan Bizaya.
Ba komai bane illa wata ƙatotuwar ƙusa mai malafa ta jan dinare. Tsaye take cak tamkar bata taɓa faɗuwa ba tunda aka shimfiɗa duniya, tamkar kuma baza ta taɓa faɗuwa ba koda duniyar ta ƙare.
Saboda girman ƙusar idan ka ɗaga kai baka iya gano ƙarshenta, sai dai kawai ka hangi malafar ƙusar kawai ta nutse a cikin gajimare.
Ƙasanta kuwa wanda a fiƙe yake, kuma a tsaye a bayan Bizaya, yana cake akan iska.
Kai ta kowanne ɓangare, kuma komai duban mai duba bazai iya gane cewa wannan ƙusa ba'a zahirin gaske take ba. Indai ba zuwa kai ka taɓa ba, sai dai amma idan ka taɓa zaka fuskanci cewa wannan ƙusa hoto ne bawai a zahiri take ba.
Ana cikin haka ne wannan ƙusa a gaban mutane, ta fara rabewa gida biyu! Kan kace meye wannan ta rabe zuwa gida biyu, wanda kuma kowanne rabi ya rabe zuwa gida biyu, inda kowacce ta ƙara rabewa, kai cikin ƙiftawar ido tuni wannan ƙusa ta rabe zuwa gida takwas.
Hakan na faruwa ta daina rabuwa, amma kuma ɓari-ɓarin nata, wanda da kowanne wani ɓangare ne kawai na jikin ƙusar farko, suka fara mulmulewa su na haɗewa, kan kace meye wannan kowacce acikinsu ta zama ƙusa akan kanta. Kuma duk manya, wanda duk da basu kama ƙafar ta farkon ba, amma kowacce tafi zira'i ƙafa sittin!
Duk wanda ya taɓa ziyartar daular Denizawa yasan sunan wannan hoton ƙusa daya bayyana a bayan Bizaya, wanda shi suke kira 'Márakána'.
Bizaya yai wani murmushi mai cike da yadda dakai, gami da ci gaba da cewa, "zan saka dukkan ƙarfin Izza ta acikin wannan Marakana da kake gani, zan kuma sa su kewaye ka.
"Abu ɗaya kacal kawai nake so kayi, ka iya fita daga cikinsu acikin daƙiƙa sittin!
"Indai har kai haka, to ni Deniz Bizáya na yarda kayi nasara akaina!
"Idan kuma ka kasa, to nima kayarda nayi nasara!"
Cikin ƙasa da daƙiƙa ashirin duk wanda ke wajen yaji wannan gasa da Bizaya ya sakawa Ikenga, duk da kuwa ba da ƙarfi ya faɗa ba, amma ya faɗa yadda alƙali Gali zai iya ji, wanda daka ganshi a fili kasan Bizaya yake goyon baya. Ai kuwa yana ji ya fara yayatawa, tayadda kowa saida yaji meke faruwa, a wani yanayi na tabbatar da cewa Ikenga bazai iya cewa a'a ba!
Abin mamakin shi ne, kana kallon Ikenga kasan kai komo yake da zuciyarsa, akan ko ya yarda ko a'a.
Wanda a gaskiya, kowa zaiyi mamakin hakan, musamman duba ga yanayin tsananin buwayar ƙarfi da kowa yasan Ikenga da shi, shi-shi kaɗaine a iyakacin tarihi tsahon lokaci wanda aka taɓa samu ya fafata da Yarima Deniz Bizaya acikin filin horonsa kuma baije ƙas ba.
Amma ganin cewa yana kokwanton amsawa Bizaya wannan abu, sai ya fara bawa mutane mamaki, kuma kan kace meye wannan tuni ƙus-ƙus ya fara tashi akan cewa ko dama Ikengan da ake faɗa da labaran faɗansa da Deniz duk ba gaskiya ne.
Amma acikin wajen manyan baƙi kuwa, tun ɗazu da wannan ƙusa ta jan dinare ta bayyana, a karon fari Asifu yayi wa Sarki Deniz Iluru magana, "lallai Deniz Iluru zanso naga yadda Bizaya zai taso.
"Wataƙila ma yazo ya fika!!"
Maganar da wasa ya faɗe ta, amma acikin idanunsa idan ka kula zaka ga nufaƙa a can ƙasa, kuma da yake shima Deniz ba na yau bane, tuni ya gane hakan, inda kawai ya bashi ɗan ƙaramin murmushi mai ƙunshe bayanai kala-kala.
Amma abinda mutane basu sani ba shi ne duk wanda bai taɓa shiga cikin Marakana ba, to bazai taɓa sanin maike faruwa aciki ba.
A faɗansu na kwanaki da suka wuce, Bizaya ya samu damar saka Ikenga acikin Marakana, lamarinda saida yasha matuƙar wahala aciki kafin ya iya fitowa.
Amma kuma yanzu ga abinda Bizaya ya zo dashi.
Tunda jimawa Ikenga ya rantse da mahaliccin Bayajiddan farko, wadda ita ce mafi girman rantsuwarsa, cewa saiya zo na ɗaya a wannan gasa.
Wanda wannan wani mataki ne na farko acikin tsare-tsaren daya shirya zaibi wajen ɗaukar fansar abinda ya faru da ƙasarsa da danginsa!
To amma kuma ko ma a wanne yanayi ake ciki, yana daga cikin halayen Ikenga shi ne, baya son abinda zai ɓata masa suna ko kaɗan.
Saboda haka yana kallon dariyar dake kan fuskar Bizaya, ya kuma ji abubuwan da ƴan kallo ke faɗa, da kuma yadda alƙali Gali yake ta ƙara zuzuta maganar, cikin isa ya amsa cewa ya yarda.
Lamarinda yasa wajen yai tsit, ana jira aga mai zai faru a gaba.
***
Babi na 41 : Shaibal-shísu (Takun-sarki)
Deniz Bizaya dariya kawai yayi, gami da ƙara taku ɗaya gaba, lamarinda yasa waɗannan ƙososhi guda takwas dake bayansa ɓacewa ɓat daga inda suke a sama kansa. Kafin daga bisani su bayyana a gaban Ikenga, inda suka kewaye shi, kuma suka ci gaba da matsawa suna rufe shi, har saida ya zamo ba'a iya ganin ko da rigar Ikenga, sun rufeshi ruf.
A dai-dai wannan lokaci ne Bizaya yayi wata ƴar ƙaramar dariya gami da cewa, "daƙiƙar ka ta farko ta fara, Ikenga!
"Saura daƙiƙa hamsin da tara!"
ƴan kallo najin wannan batu suka fara shewa su na ihu su na kiran sunan Bizaya.
Acikin zuciyar Deniz Bizaya yana da cikakkiyar amannar cewa indai mutun Izzarsa bata haura shekaru dubu ba, to lallai bazai iya fita daga cikin wannan kurkuru ta ƙusar tsafi ba. Kuma yasan Izzar Ikenga bata haura shekara ɗari ba, saboda haka yana da nutsuwa acikin ransa cewa tabbas yayi nasara. Idan kuma Ikenga ya iya fita daga ciki to lallai abinda mahaifinsa sarki Deniz Iluru ya labarta masa akan tsakanin Ikenga da ƙabilar Ururu gaskiya ne.
Daga waje babu abinda ake gani sai rumfar waɗannan samudawan ƙusoshi. Acikin wannan ƙusoshi kuwa, Ikenga ne ya tsinci kansa acikin wani ɗaki, wanda yake a kewaye da katangu iyakacin ganinsa. Kowacce katanga anyi tane da irin wannan jan dinare na wannan ƙusoshi.
Kuma idan da zaka lissafa, zaka ga a kewaye da wannan ɗaki adadin waɗannan katangu guda dubu takwas ne dai-dai da dai-dai!
Kowacce idan ka ɗaga kai baka gano ƙarshenta!
Kuma babu komai a wajen sai duhu!
Sannna shi kuma gashi acikin ɗaki a ƙulle sannan kuma a sarƙafe da ankoki, waɗanda suma da zai lissafa su da yaga cewa guda dubu takwas ne dai-dai.
Ikenga ya taɓa shigowa irin wajen sak, sai dai a wancan lokacin ankokin daya tarar guda dubu huɗu ne kawai, sannan suma katangun dubu huɗu ne kawai.
Kuma yasan cewa idan yana so ya fita daga wajen saiya sare gaba ɗayan waɗannan katangu, waɗanda tsananin taurinsu bazai misaltu ba!
Amma abin mamakin shi ne, tuni daƙiƙa talatin da uku sun wuce, amma Ikenga na kwance ko motsi baiyi ba!
Idanunsa a buɗe, babu abinda yake sai kallon cikin duhun ɗakin nan, zuciyarsa na tunani.
"Hmmm... yayi kyau da ban nuna masa dukkan fasata a karawarmu dashi a baya ba! Yayi kyau da ban nuna masa fasahar TAKUN-SARKI ba!"
Ikeng ya ci gaba da magana a nutse tamkar babu wani lokaci dake jiransa, cikin ƙasaita tamkar duk duniya shi kaɗai ne sarki, "Lallai dana nuna masa bazai taɓa yarda da wannan gangancin gasar daya saka min ba. Domin kuwa lallai yayi kuskure. Kash... amma koma na nuna masa koma ban nuna masa ba, babu abinda zai canja.
"Gaskiyar kawai ita ce indai baka kai matakin Izza shekara dubu ɗaya ba, to fa lallai baza ka iya tsayawa a gabana ba kai maganar Izza ba. Ballantana ma kace zaka fafata dani."
To ko mai wannan saurayi mai suna Ikenga ya taka da yake wannan cika-baki haka. Bari dai muga gudun ruwansa....
Ikenga ya kira wani ɗalasimi, "Shaibal-shísu!" Wanda idan da mutun yana jin yaren Aldurish to da zai gane cewa fassarar wannan ɗalasimi yana nufin TAKUN-SARKI.
Yana rufe bakinsa, takobin dake bayansa a saƙale ta fara haske, inda ɗakin ya fito fili ya bayyana cewa shima anyi shi ne da jan dinare iri ɗaya da sauran.
Wannan takobi ta fara motsi da kanta, inda ta fice daga cikin ankokin nan tamkar basa wajen. Tana fitowa ta sari ankokin dake hannunsa na dama, inda nan take suka zube ƙas.
Ya ɗaga hannunsa izuwa cikin bakinsa, ya cizi babban ɗan yatsansa, inda jini ya fara ɗiga.
Nan take ya kai hannun goshinsa, inda ya fara zana wani tambari mai kama da Miyura da jinin.
Yana gamawa a dai-dai wajen wata Miyura ta musamman ta bayyana.
Babu komai acikinta sai wasu zanen idanu guda uku, kowanne a kusurwa daban, haɗe da wani jan layi a tsakaninsu!
Wannan Miyura na bayyana yai wata dariya, sannan kai tsaye ya miƙe, ya kuma miƙa hannu ya damƙi takobinsa dake kan iska!
Ya ja dogon numfashi, ya ɗaga ƙafarsa ta dama yai taku ɗaya da ita.
A dai-dai lokacin da yai wannan taku, dukkanin waɗannan ankoki dake ɗaure ajikin sa suka juye suka koma takubba.
Idan ka hango daga nesa, babu abinda zaka gani face wani waje mai ban tsoro, wanda babu komai acikinsa face takubba marasa adadi na jan dinare.
To idan da shikenan, lallai da da sauƙi, amma Ikenga na ƙarasa dire ƙafarsa daga wannan taku na farko, waɗannan takubba suka ɓace ɓat, suna bayyana kowacce na cake a jikin wannan katangu guda dubu takwas da suka zagaye wannan ɗaki.
Abu na gaba kuma daya faru shi ne, fashewa da wannan katangu sukai dukkaninsu a lokaci guda, lamarinda ya bada ƙara mai kashe kunne, da kuma ƙura wadda ta tashi sama, kuma tasa baka ganin komai.
Tana lafawa babu wannan ɗaki da waɗannan katangu ko sama ko ƙasa, kaf sun ɓace ɓat!
A dai-dai wannan lokaci daƙiƙa ta hamsin da ɗaya tayi!
Sai dai kuma da yake na wajen wannan duniya basa ganin abinda ke faruwa, basu ga komai ba sai a daƙiƙa ta hamsin da shida inda suka ga waɗannan ƙososhi dake zagaye da Ikenga sun tarwatse ɗaya bayan ɗaya, har gaba ɗayansu suka ƙare.
A tsaye, idanunsa a rufe, Ikenga ne riƙe da takobinsa tsirara a hannun hagu.
Baiyi magana ba, kuma bashi da niyyar cewa komai, daga ganin yadda ya tsaya! Kai dukkan kamannin sa ma sun canja. Lallai a wannan lokaci idan da zaka kwatanta Ikenga, to zaka ce yafi kama da jan jarumin zaki irin na mutanen farko.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne, Bizaya ya tafa hannu gami da cewa, "ahhhh...ka samu nasara!" Fuskar Bizaya babu damuwa aciki.
Yana tafa hannu ya fara matsowa kusa da Ikenga, ko kaɗan a fuskarsa babu alamun baƙin cikin rashin zuwa zagaye na karshe, lamarin da hatta Gali saida yayi mamaki.
Amma ina kowa idonsa na kansa, babban abinda ya ƙara jan hankalin kowa shi ne yadda suka ga Bizaya na dosar Ikenga, saboda su ga mai zaiyi yayinda yaje kusa da Ikenga.
Amma bisa mamaki babu abinda ya faru, yana zuwa ya ƙarasa kunnen Ikenga yai masa magana acikin raɗa, "dama nayi tunanin akwai abinda kake ɓoyewa a fafatawarmu dakai a baya!Amma.... kana tunanin kai kaɗai ne mai shiri a ɓoye? Hmmm... Bari dai kawai da sannu wataran zamu ƙarasa wannan faɗan!"
Yana gama faɗin haka yai tsalle ya fice daga cikin wajen, mutane kuwa suka bishi da kallo, cikin rashin gane mai ke faruwa, amma ina taku kaɗan yai suka nemeshi suka rasa.
Tuni wajan ya rikice da ƙananan maganganu, akan abubuwan dake faruwa.
Kowa dai ya gani da idonsa Ikenga shi ne yaci wancan gasa data gabata, amma abin mamakin shi ne, yadda Bizaya bai damu ba kwata-kwata, hasalima wasu tuni sun fara raɗe-raɗen yana sane ya bari aka cinye shi.
Toh! Koma dai meye gaskiyar al'amarin bari mu koma kimanin kwana ɗaya kafin fara wannan gasa.
____
KWANA ƊAYA KAFIN A FARA JINZIDAL.
A cikin ƙatoton ɗakin-karatu dake cikin tsakiyar fadar daular Denizawa, sarki Deniz Iluru ne sanye da ƴar shara yana yiwa ɗansa Deniz Bizaya karatun ƙarshe akan gasar da zata gudana a washe garin ranar.
Sarkin ya kasance masoyin tarihi ne matuƙa, domin zaiyi wuya a samu wanda ya kaishi son tarihi da bincikarsa. Hakan nema yasa aka gina masa ƙaton ɗakin-karatun da babu irinsa a ƙasa-bakwai, domin kawai ya ringa tara al'amuran tarihi aciki.
"Bizaya kana ji ko," sarkin yaci gaba da yiwa ɗan nasa bayani, "wannan yaro Ikenga da ka gayyato kuka fafata dashi, na gano acikin tarihi cewa abunda muka daɗe muna nema domin samun damar rayuwa akan doron ƙasa yana da alaƙa da shi. Ko kuma nace yana da alaƙa da abinda ya faru shekaru dubu biyu da suka wuce tsakanin kakanninsa da ƙabilar Ururu.
"Labari ne mai tsayi, amma zan gaya maka kaɗan daga ciki. Abinda kawai nake so dakai shi ne ka gano mana cewa shin wannan Ikenga da gaske shi ɗinne wanda yake da wannan sirri ko kuwa. Indai ka gano haka to yama fi ace kai nasara. Domin lallai zan baka kyautar da baka taɓa zato."
Koda jin kalmar ƙarshe dake magana akan kyauta sai tasa Bizaya ya daina ɓata rai. Domin yasan lallai kyautar mahaifin nasa aba ce maɗaukakiya. Da fari baiji daɗin maganar ba, domin yana so ya samu nasara a wannan gasa ya nuna kansa a duniya. Amma da yaji zancen kyautar baban nasa nan da nan ya amince.
Yazo dai a tarihi cewa asali dole ce tasa daular Denizawa suka koma ƙarƙashin ƙasa saboda wani yaƙi daya afku shekaru aru-aru da suka wuce. Kuma sirrin dalilin wannan yaƙi babu wanda ya sani inba sarki Deniz Iluru ba. Shima saida ya zama sarki ya sani, saboda haka hatta Deniz Bizaya bai sani ba. A ƙa'idar daular Denizawa sai ka zama sarki zaka san wannan sirri. Amma abu ɗaya da duk manyan wannan ƙabila suka sani shi ne su na da buƙatar su dawo rayuwa a saman ƙasa koma ta halin ƙaƙa.
"Saurara kaji kaɗan daga cikin tarihi." Deniz Iluru ya fara labartawa ɗansa kaɗan daga cikin tarihin duniya.
***
Babi na 42 : Takun-sarki (part2)
TARIHIN ƘASA BAKWAI.
Shekara ta 352 Kafin Amri.
Sarki Deniz Iluru ya zaro wani ƙaton littafi daga cikin wata kantar littattafai dake gefensa. Kai daka ganin yadda shekaru sukai sheda akan takardun wannan littafi kasan yayi shekaru aru-aru a duniya.
Sarkin yai duba izuwa ɗansa dake durƙushe a gabansa, kana ya fara karanto tarihi daga wannan littafi.
____
Kimanin shekaru dubu biyu da suka wuce, a wata ƙabila da akewa laƙabi da Jidda, anyi wani zamani na wani sarki mai suna Báya Azába.
Asali shima sunan mutun na farko daya kafa ƙabilar aka sakamasa, wato dai bashi ne Azába na farkon da ƴan ƙabilar ke rantsuwa dashi ba.
Wani tarihi babba a game da wannan sarki, wanda baza a taɓa mantawa dashi ba shi ne abinda ya faru a wannan shekara ta 352 Kafin Amri. Kuma wannan al'amari shi yasa aka sakawa wannan sarki suna Báya. Hasalima shi ne asalin dalilin da yasa aka canja sunan wannan ƙabila daga Jidda ta koma Baya+Jidda, wato Bayajidda.
An rawaito cewa a lokacin da aka haifi wannan sarki, a dai-dai lokacinda ya faɗo duniya bai faɗi ƙasa ba, kuma bai faɗo a kwance ba; hasalima da ƙafafunsa ya dira ƙasa, inda akan idon kowa yai taku ɗaya, biyu, har zuwa taku bakwai yana fuskantar gabas, sannan ya faɗi!
A lokacin waɗanda suka halacci wannan haihuwa suka rankaya zuwa ga sarki baban wannan yaro, suka labarta masa. Amma bai yarda dasu ba, hasalima sawa yai a daina zancen, wai acewarsa baya son a ringa yiwa ɗansa kallon wani mai aljanu ko kuma wani mai rauhanai.
Haka wannan magana ta mutu a bisa umarnin sarki.
Amma kuma wani abin mamaki shi ne, sai ya sawa yaron suna Báya, ma'ana bakwai kenan da yaran wannan gari da ake kira da Wilburish.
A kwana a tashi saida wannan yaro mai suna Baya ya girma ya zama hamshaƙin sadauki, ya kuma ɗaga martabar ƙabilar zuwa ƙololuwa aduniya, hasalima ance har gogayya ya yi da mutane irinsu Haruta Ururu da Maruta Ururu, dama irinsu Tarifil-fakta da kansa, da dai sauransu!
Ana nan ana nan, watarana ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴan manya-manyan ƙabilar Ururu. Wadda ake kira Dáya Ururu.
Lallai kowa zaiyi mamaki ace ƴan wata ƙabila sun samu auren maɗaukaka ƴan ƙabilar Ururu. Wanda abu ne da ba'a taɓa yi ba a tarihi hasalima sarki ɓisa doron ƙasa ta farko, wato Sarki Ururu da kansa ya haramta yin hakan. A cewarsa za'a lalata masa jini idan aka sirka shi da wani. Amma a wannan lokaci shida kansa ya amince da wannan aure.
Kowa daga cikin manyan sarakuna sunyi mamaki sosai, hasalima da dana daga cikinsu sun nemi aure daga Ururu tun iyayensu da kakanninsu sama da shekaru dubu amma an hana su. Yau gashi an bawa wannan yaro mai suna Baya ɗan gidan sarki Azába.
Saboda haka hankalin duniya ya tashi, duniya ta girgiza. Babu yadda ba'ai ba a hana wannan biki ba, amma saida ya afku. A ranar wannan biki duk wani wanda ya isa a duniya saida yaje domin ganewa kansa wannan al'amarin mamaki.
Dáya Ururu sanye da baƙaƙen idanuwan ta da kuma farar fata mai walƙiya samfurin jarirai irin wadda bata taɓa ganin ƙura ba. Ta fito sanye baƙar rigar ta kalar idanunta. Lallai ko acikin Ururu, Dáya na daga cikin kyawawa ababen misali. Labaranta na daga cikin waɗanda ake labartawa acikin littattafan mata kyawawa a wannan zamani.
Bayan biki, babban sarki Ururu yasa aka bawa Baya Azaba sarauta kuma aka naɗashi sarki daga cikin daulolin dake ban ƙasa ta farko.
Bayan shekaru uku, Daya Ururu ta haifi ƴan biyu; ɗaya yaro santalele ɗaya kuma mace, ALLAH yasa yana wajen, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓi haihuwarsa, wata ƴar tsohuwa mai yawan farin gashi ita ma na wajen, duk da ta tsufa da yawa a lokacin.
Yaron farko daya fito, babu wani abu na musamman daya faru, amma na biyun yana fitowa ya tsaya cak da ƙafarsa kuma ya fara tafiya, bai tsaya ba saida yayi taku ɗai-ɗai har bakwai.
Wannan sarki na ganin haka, abubuwan da aka gaya masa a lokacin haihuwarsa suka fara dawo masa.
Tun daga lokacin ya sawa wannan ɗa nasa ido, har ya girma, kuma cikin mamaki shima yaron ya girma ya zama shahararre kamar babansa.
Kuma a lokacin wannan ɗa nasa ne aka canja sunan ƙabilar ya koma Báya-Jidda, daga asalinta na Jidda. Wato ya ƙara sunan kakansa wato Báya a farkon sunan ƙabilar.
A haka a haka aka ringa samun ire-iren waɗannan mutane acikin ƙabilar Jidda (Bayajidda), wanda dukkaninsu suke zama shahararru, kuma a ƙarshe su suke zama katangar ƙabilar a zamaninsu.
Ana nan ana nan, abin ya fara yawaita har kusan kowa a ƙabilar yasan da zancen, duk da basu bari maganar ta fita waje ba, amma duk da haka sai suka sawa abin suna 'HAIHUWAR-SARKI', wanda daga nan aka samu sunan 'TAKUN-SARKI!'
Kwatsam sai wani abu ya faru wanda har a wannan rana da Armad zasu kara da Ikenga ba'asan maiya jawoshi ba.
Wani haske ya ringa tashi daga saman wannan ƙabila har tsahon kwana uku. Wanda daga baya ya ɗauke.
Tun daga wannan al'amari aka daina samun waɗannan ƴan baiwa. Aka wayi gari an daina samun irin waɗannan yara kwata-kwata a wannan ƙabila. Har saida akai sama da shekaru dubunnai. Wanda hakan ya jawo cima baya wajen ƙarfi da Izzar ita ƙabilar a tsakanin tsaranta. Harma daga ƙarshe Ururu suka cire su daga layin sirakansa.
Zamanin daya zo daga baya har saida aka manta da wannan al'amari na Takun-Sarki a ban ƙasa.
___
Koda sarkin yazo nan a zancensa saiya rufe littafin, ya kuma matso kusa da ɗan nasa yana cewa, "Inada labari cewa shekaru goma sha an haifi wani yaro, wanda yazo da wannan baiwa ta ban al'ajabi da ake cewa Takun-sarki.
"Kuma an sakawa wannan yaro suna Ikenga! Abinda ban sani ba shi ne ko wannan yaro Ikenga shi ne dai wancan Ikengan da aka haifa da wannan baiwa. Saboda haka nake so ka gano min a yayin faɗanka dashi."
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin sarki Deniz Iluru da ɗansa Bizaya kwana ɗaya kafin a fara wannan gasa.
***
Babi na 43 : Karan-batta
A wannan lokaci, alƙali Gali, cikin ɓacin rai ya sanar cewa Ikenga ne yaje zagaye na ƙarshe, inda zasu kara da Armad.
Da dama dai abin bai musu daɗi ba, musamman tunda yawancin su Denizawa ne, kuma su na so suga nasu yaje zagayen ƙarshe. Amma tunda babu yadda zasuyi, kuma musamman bayanda suka ga shi kansa Bizaya bai damu ba, sai kawai suka ajiye abin a gefe, kuma suka fara zancen zagayen ƙarshe, wanda shi ya kamata ace yafi kowanne ƙayatarwa.
A wannan lokaci ne, alƙali Gali ya sanar da cewa abisa doka, indai babu mai mummunan ciwo acikin waɗanda zasu buga wasan ƙarshe, to cikin awa shida masu zuwa za'a fara wasan ƙarshe.
Da aka tambayi Ikenga ko yana da wani rauni da yake neman a ɗaga lokaci, sai yace shi bazai bar cikin filin bama. Yana nan a inda yake tsaye, lamarinda ya ƙara ɗaga ƙimarsa a tsakanin ƴan kallon nan.
Shi ma Armad da aka tambayeshi, amincewa yayi da lokacin awanni shidan.
Kamar ƙifta ido awa shida ta doso kai!
Acikin wannan awa shida Nusi ta gabatowa Armad da wani labari mai daɗi.
"Armad."
"Na'am yaya Nusi, na shirya fa, ki daina damuwa sosai, kinji." Armad ya amsa mata cikin tsokana, a zatonsa maganar data saba zatai masa. Amma baisan wani abu ne daban ba.
"Kasan mai zance maka ne a'a! Kuma nace maka ka daina cemin yaya." Nusi ta canja fuska haɗe da ɗan murmushi. Ga dukkan alamu su biyun sun fara sabawa sosai. "Indai kaci nasara a wannan fafatawar to lallai muna da damar zuwa garin Shadeniz. Domin kuwa munyi magana da ƴan uwana da muke so mu buɗe garin tare.
"Kai koda bamu samu damar buɗe ƙofar garin ba, lallai zan samo maka labari akan Tarifil-fakta. Kai dai kawai ka dage kayi nasara, kaji!" Nusi ta kammala zancenta tare da miƙa hannu taja jan kyallen dake goshin Armad cikin tsokana, tana cewa, "wai kai tunda ba Miyurar ka cire wannan abun mana."
"Hmmmm.." Armad yaja numfashi yana tunano mai zaice ya tsokani Nusi shima, "indai zaki iya cire ɗankwalinki to nima zan cire. Kin yarda?"
"Me kace?" Nusi ta cije haƙora, kasancewar a ƙabilar su Nusi kowacce mace data haura shekaru sha takwas tana saka ɗan mayafi taɗan rufe gashinta. Kuma sukan ɗauki abun abun tsokana idan bakya yawo da wannan mayafi da ake kira da ɗankwali.
"Zaka iya ƙara wani kyallen ma.... Ni ina ruwana..." Nusi ta haɗe rai tana hararar Armad. Lallai acikin wannan harara akwai abota wadda take ginuwa a hankali a hankali. Ko ina wannan abota zata kaimu, lokaci ne kaɗai zai gaya mana.
Awa shida nayi aka buga ƙugen yaƙi..... Mazaje guda biyu da suka fito zagayen ƙarshe na wannan fafatawar suka bayyana a fagen daga.
Sune waɗanda sukai nasara akan sama da mutun ɗari bakwai da suka fafata a wannan gasa. Kuma yanzu gashi sun haɗu da juna, lallai akwai karan-batta irin wanda ba'a ga irinta ba a baya.
Waye zaiyi nasara? Waye zai je ƙas? Waye zai nunawa duniya ya isa? Waye zai mallaki dubunnan bayin da aka tara?
____
Armad na tsaye a gefe guda da takobinsa a rataye a kafaɗarsa, yana karantar Ikenga wanda ke gabansa a tsaye, idanunsa a rufe.
Kuma abin mamakin shi ne anfi minti uku da kaɗa musu ƙugen yaƙi, amma babu wanda ya motsa acikinsu.
Can daga bisani Ikenga ya buɗe ido ya kalli Armad, inda dubansa ya kafe akan jan kyallen dake ɗaure a goshin Armad, nan take kaifafan idanununsa, wanda ga dukkan alamu zasu iya gani har hanji, suka ƙurawa wajen ido cikin mamaki, kafin daga bisani ya buɗe baki ya fara magana cikin tsananin girman kai da taƙama da ƙarfin Izza, "a wannan rayuwar na tsani mutane da dama!
"Amma daga cikin waɗanda nafi tsana akwai matsorata masu jin tsoron bayyana kosu su waye!!
"Da farko nayi niyyar mutunta jarumtarka ta zuwa zagayen ƙarshe, na nuna maka fasaha ta mai suna 'Takun-Sarki', wanda hakan nema yasa tunda nayi takun farko ban matsa daga nan ba, da niyyar zan ɗauki taku na biyu na halaka ka dashi. Domin kaga idan ka mutu ta wannan hanyar zakai alfahari a lahira, saboda kana daga cikin kaɗan da suka mutu daga maɗaukakiyar fasahar 'Takun-sarki'.
"Amma ina, ka ɓata min lokaci kawai! Lallai duk wanda ke tsoron bayyana cewa shi Magajin-wilbafos ne to bai cancanci Takun-sarki ba. Ko kana tunani dan babu Miyura a goshinka idanu na zasu kasa gane ka. Lallai inaga baka da masaniyar cewa wannan idanu nawa su na ganin hatta safa-da-marwar mutuwa a lokacin da take ɗaukar rayukan bil-adama."
Yana gama faɗar haka bai jira komai ba, ya nufi kan Armad da takobinsa a hannun dama tsirara. Jikinsa na sassarfa irin ta mazajen aljanu.
Yana isa ga Armad ya kai masa wawan sara da niyyar tsinke kansa, amma a wannan lokaci Armad ya farfaɗo daga cikin mamakin da yake na yadda akai Ikengan ya gano shi ne Magajin Wilbafos, ya kuma kare wannan sara da tasa takobin.
Takubban biyu na haɗuwa Ikenga yayi amfani da tsananin kwarewa ta fasahar takobi ya zame takobinsa daga jikin ta Armad, ya kuma kai masa wani saran da ita ta ƙasan hannunsa.
Cikin tsananin zafin nama Armad yayi amfani da walƙiya mai ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya ya ƙarawa kansa ƙarfi domin zamewa wannan sara. Yai tsalle izuwa gefe guda tare da mayarwa da Ikenga martanin sara mai ɗauke da shekarun Izza biyar. Lamarinda yasa dole Ikenga yayi amfani da Izzarsa sannan ya iya kaucewa ta hanyar yin tsalle ya koma baya.
Armad ya bishi da kallo riƙe da takobinsa, inda shima ya kalleshi yana mai yamutse fuska.
Lallai ɗan wannan bata kashi na ƴan daƙiƙu daya wakana tsakanin wannan ma'abota Izza biyu ya girgiza ƴan kallo domin kuwa babu abinda kake ji sai shewa da ife-ife.
"Hmmmm...." Armad yaja numfashi cikin yarda dakai yana mai cewa, "shin kana ganin dan ka fita daga cikin Mairakana da Bizaya ya saka ka aciki shi ne ka isa. To ya kamata ka canja tunani, domin lallai sai nayi nasara a wannan fafatawa. Kuma wani abu guda ɗaya da baka sani ba, koda kasan ni ne Magajin Wilbafos ko baka sani ba, ko kana ganin mutuwa ko baka gani duk bai shafe ni ba. Domin lallai koda zan mutu saina fito daga kabari na nemo Tarifil-fakta nan da wata shida. Kai koda dukkaninku zaku haɗu na farkon ku dana ƙarshenku, baza ku iya hana ni nemar mata lafiya ba."
"Hmm.." Ikenga yayi murmushi tare da tafa hannayensa biyu ya kuma kira sunan ɗalasimi acikin ransa, sannan ya ci gaba da cewa, "Da takobi kaɗai, ba tare da aljani ba, ba kuma tare da fasahar Takun-sarki ba zan halaka ka. A matsayinka na zuri'ar Wilbafos koba komai ka cancanci na nunawa duniya ƙarfin Izza ta akanka. Kayi sani cewa a irin wannan rana ta yau Wilbafos-na-uku ya rasu. Kuma kaima yau ita ce ranar da zaka isa magabatanka a lahira."
Armad ya haɗe gira cikin mamaki domin bai taɓa jin wani Wilbafos-na-uku ba. Kuma ga dukkan alamu Ikenga ba ƙarya yake ba, sai dai kuma yasan koya tambaye shi bazai gaya masa wani abu ba. Saboda haka kawai ya share zancen, kawai abinda ke ransa shi ne ya zaici nasara akan Ikenga.
"Bari muga har tsahon daƙiƙa nawa zaka iya zama akan zancenka naƙin yin amfani da aljaninka." Armad na faɗar haka ya zuƙo shekaru biyar na Izza a matsayin ƙawanyar walƙiya biyar, ya kuma aikawa da Ikenga su.
Ikenga ya kaɗa takobinsa a sama, sannan yayi tsalle tare da kaiwa ɗaya daga cikin wannan walƙiya sara. Nan take takobin tasa ta ratsa cikin walƙiyar, kafin daga bisani ta tarwatsa ta ta ɓace acikin iska.
Lamarinda ya jawo shewa mai ƙarfin gaske acikin ƴan kallo. Kowa yasan cewa ba ƙaramin ƙarfin fasahar takobi ake buƙata ba kafin mutun ya iya tarwatsa harin aljani da takobinsa, amma ga Ikenga akan iska ya tarwatsa ɗaya cikin kwanciyar hankali.
Tun ma kafin shewar ƴan kallo ta mutu Ikenga ya ƙara ratsa walƙiya ta gaba, sannan ta gabanta. A haka a haka har saida ya gama da guda biyar ɗinnan hankalinsa a kwance. Sannan ya dira ƙasa yana kallon Armad.
Nan Armad take Armad ya duba yaga yana da kimanin ragowar shekarun Izza arba'in, sabida haka nan take yasan maiya kamata yayi.
Armad ya zuƙo shekaru goma nan take, sannna ya haɗa ƙatotuwar ƙawanyar walƙiya da ita. Ya ɗora ta a saman hannunsa na dama sannan yai ƙaraji ya afkawa Ikenga.
Yana zuwa yakai masa duka da ita, inda shi kuma yasa takobinsa ya kare. Sai dai kuma shima Ikenga yasan babu yadda za'ai ya iya kare shekaru goma na Izza a haɗe, da takobi kawai. Koda kuwa ya iya karewa, zata iya fancala ta gefe ta ƙona shi.
Saboda haka nan take ya ɗaga hannunsa sama ya kira ɗalasimi, inda wata takobin ta ƙara bayyana akan ɗayan hannunsa. Nan take ya kawo wa Armad sara da ita.
Dama Armad yayi tunanin haka zata iya faruwa, saboda haka ya shirya mata. Takobin na fitowa wata ƙawanyar wuta mai ɗauke da shekaru sha biyar na Izza ta bayyana ta tare ta. Sannan kuma a lokaci guda wata ƙawanyar mai ɗauke da wasu shekaru sha biyar ɗin ta ƙara bayyana ta yiyo kan Ikenga ta baya.
Da farko Ikenga ya kasa riƙe ƙawanya mai ɗauke da shekaru goma, a dalilin hakan ya kira wata takobin, amma kuma Armad ya shiryawa hakan, inda shima ya ƙara aika masa wata ƙawanyar mai shekaru sha biyar har guda biyu; ɗaya ta gaba ɗaya ta baya. Lallai Armad ya kware a harkar sarrafa aljaninsa yadda yake so. Kuma ga dukkan alamu kullun ƙara kwarewa yake.
***
Babi na 44 : Aljani Gal-Iyyu
"Hmmm...." Ikenga ya ja dogon numfashi tare da girgiza kai, "eh lallai ka cancanci kaga aljani na, na janye abinda na faɗa a baya. Amma kayi sani cewa duk abinda ya faru dakai, kada ka zargi kowa ka zargi kanka."
Yana rufe baki ya tafa hannayensa biyu tare da faɗar wasu ɗalasimai ƙasa-ƙasa, kana daga bisani ya kira sunan aljaninsa, "Gal-iyyu!"
Faɗar hakan keda wuya wannan filin wasa ya fara girgiza yana neman rugurgujewa. Waɗannan manya-manyan ƙawanyu na walƙiya ɗauke da shekarun Izza dake tunkaro shi suka fara girgiza kafin daga bisani su tsaya cak tamkar ansa wani bango an tare su.
Sai dai idan ka lura zaka ga cewa bawai haka kurum waɗannan ƙawanyu suka tsaya ba. Wani baƙin abu ne mai kama da hadari yayi musu hijabi tsakaninsu da Ikenga. A zagaye da wannan baƙin abu akwai wani jan layi daya kewaye dukkaninsa. A tsaye wannan baƙin abun da kaɗan ya haura Ikenga, amma a kwance yana da faɗin daya kewaye shi ya kuma kare shi daga sharrin wannan walƙiya dake neman halaka shi. Wata irin Izza mai saka firgici na tashi daga jikin wannan abu. Kallo ɗaya kacal zakai ka tabbatar da cewa akwai ƙarfin maɗaukakin aljani a jikin wannan abu mai kama da hadari. Kai idan ma ka nutsu ka ƙara matsawa kusa zaka iya jin ƙarfin Izzar baƙin Rauhanin aljani na tashi daga ciki.
Babu abinda kake ji sai ajiyar zuciya da ƙara kwale ido daga ƴan kallo, domin ga dukkan alamu har yanzu babu wanda ya gano haƙiƙanin me wannan aljani na Ikenga mai Gal-iyyu yake sarrafawa.
Wasu ƴan kallo daga ɓangaren kusurwar arewa suka fara bada hasashe kan mai suke tunani akan wannan aljani. Ɗaya daga cikinsu ya ce, "ina ganin aljanin duhu ne, ko?"
Ɗayan kuma ya girgiza kai, "a'a, ni ina ganin aljanin hadari ne."
"A'a anya kuwa, ka taɓa ganin hadari da yakai baƙin wannan? Lallai ni inaga ba hadari bane.. Ko kuma wataƙila ma aljanin ƙasa ne ko kuma na......" Sai dai kafin ya rufe bakinsa ya haɗiye ragowar maganarsa domin abinda ya gani na faruwa a wannan filin daga.
"Kaiiiiii.... Ai kuwa aljanin hadari!!!" Yai ajiyar zuciya tare da kallon abokin hasashen nasa. "Duba kaga yadda yake zuƙe walƙiyar dake kewaye da dashi. Aljanin hadari shi kaɗai ke iya zuƙe walƙiya a iya sani na."
Ai kuwa abinda ke faruwa kenan. A kewaye da Ikenga wannan abu ya fara rage shekarun dake ɗauke acikin wannan ƙawanyu na walƙiya. A gaban idon kowa na suka fara rage yawa tamkar wasa.
Nan take Armad yai tsalle izuwa baya tare da haɗe fuska, acikin ransa yasan lallai akwai matsala. Domin shima kamar sauran ƴan kallon ya gano cewa wannan aljani na hadari ne. Domin yana da cikakkiyar masaniyar shi kaɗai ne zai iya zuƙe walƙiyar sa haka.
Ikenga ya ɗaga hannunsa na dama yana nuni da Armad, "Kayi sani cewa tun daga lokacin da aka hallicemu aka rubuta nayi nasara akan ka. Kai koda ma ba haka aka rubuta ba, lallai yanzu al'amari zai canja. Koba komai zaka yi alfahari idan kaje lahira kana daga cikin waɗanda suka mutu ta hannuna. Domin lallai abin alfahari ne a gareka, ace ka mutu a hannun sarkin ƙabilar Bayajidda."
Armad ya ja numfashi gami da murmushi, "kayi dai ka gama surutun ka. Ni dai nasan lallai bazan bari naje ƙas ba a wannan fafatawa. Ko da aljani ko babu!"
Ikenga najin wannan magana ya ƙara tafa hannayensa, lamarinda yasa wannan baƙin hadari ya ƙarasa zuƙe dukkanin walƙiyar dake kewaye dashi. Sannan nan take ya aikawa da Armad wannan hadari da niyyar ya halaka shi dashi.
Armad yai tsalle ya kaucewa hadarin ta hanyar yin gefe. Amma tunma kafin yaje ƙas wannan dunƙulen hadari yayiwo kwana ya ƙara tunkaro shi da ƙarfin tsiya. Saboda ƙarfin gudunsa har wata iska ce ke tashi tana bada gunji tamkar ana ƙuga ruwan sama.
Armad yai sauri ya baje a ƙas inda wannan hadari ya wuce ta saman kansa da kaɗan. Lallai bada ban yayi dabarar yin sauri ya kwanta ba da tuni wannan hadari ya dunƙule shi. Duk da cewa hadari ne kawai amma tsananin ruɗani da ƙarfin Izza dake tashi daga jikinsa yana da matuƙar tsoratarwa, lamarinda yasa Armad ya san lallai bai kamata ya bari wannan hadari ya riske shi ba. Haka dai suka ci gaba da kai komo; Armad yana ta zillewa hadari, shi kuma Ikenga yana ƙarawa wannan hadari ƙarfi da gudu. Amma duk da haka Ikenga bai samu damar riskar Armad.
Armad na tsalle yana lissafi acikin ransa, "saura daƙika ashirin da ɗaya."
Dama dai duk guje-gujen da Armad yake so yake aljaninsa ya tara masa wata walƙiyar. Kuma yasan dai-dai lokacin da zai ɗauka kafin hakan ta faru, saboda haka ya yanke shawarar yaci gaba da guje-guje zuwa sanda zai iya sarrafa wata walƙiyar.
Amma a ɓangaren Ikenga kuwa, koda ganin babu yadda zaiyi ya iya kama Armad da hadarinsa saiya canja taku.
Nan take ya tafa hannayensa ya kuma ƙara kiran wani ɗalasimin, "Samá'u!"
Yana rufe baki wannan baƙin hadari dake bin Armad ya tsaya cak. Sannan daga bisani ya fara yin sama. A hankali a hankali har saida yakai kimanin ƙafa ashirin sannan ya tsaya. Yana tsayawa kuma ya fara buɗewa yana ƙara girma. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba wannan hadari ya gama karaɗe saman wannan filin gasa.
Armad ya buɗe baki yana kallon abin mamaki. Hadari ne baƙi-ƙirin ya rufe saman wajen baki ɗaya. Babu abinda kake gani face shi.
To amma idan da shikenan al'amarin toda da sauƙi, amma a dai-dai wannan lokaci ne wannan hadarin ya fara rugigi, sannan tsawa ta karaɗe ilahirin wajen.
Nan take aka fara tsuga ruwa kamar da bakin kwarya.
Ikenga ya ɗaga hannunsa yai nuni ga Armad, lamarinda yasa dukkan wannan ruwa dake saukowa ya tunkari inda Armad yake da wani gudu irin na walƙiya.
Kafin ma Armad ya motsa tuni wannan ruwa ya zagaye shi ya jiƙa shi sharkaf.
"Kana da masaniyar cewa daga hadari akan samu ruwa." Ikenga ya fara magana cikin girman kai, tamkar babu wani ma'abocin Izza daya kaishi a ban ƙasa.
Sai dai duk wannan abu bai tsorata Armad ba, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci da yake tunanin zaiji wani canji kamar zafi ko kuma wani abu a yayinda ruwan ya taɓa shi baiji komai ba. Saboda haka ya ɗaga tafin hannunsa yana nazarin wannan ruwa daya jiƙa shi. A dai-dai wannan lokaci ne Armad yaji motsi a saman kansa. Amma kafin ya ɗaga kai wata ƙatotuwar ƙawanyar walƙiya mai ɗauke da ƙarfin Izza na shekaru ɗari ta fito daga cikin wannan hadari ta tunkaro shi. Kafin yayi koda tunanin kaucewa ta cimmasa. Inda nan take ta daki ruhinsa ta zagaye jikinsa tana neman tarwatsi shi.
To da yake koda kana da aljanin walƙiya indai wannan walƙiya ba daga aljaninka ta fito ba saita yi aiki a kanka. Saboda haka nan take rauni ya cika jikin Armad. Da kyar ya iya zuƙo ƙawanyar walƙiyar da bata fi ta shekarun Izza biyu ba ya kare kansa. Abinda shi kaɗai ne yasa jikinsa bai tarwatse ba.
A dai-dai lokacin ne ya ƙara jin muryar Ikenga, "shin kasan cewa daga cikin hadari akan samu walƙiya?" Wata dariyar mugunta ta cika fuskar Ikenga a yayinda ya ƙara ɗaga hannunsa ya ƙara kiran sunan wani ɗalasimin, "Sainówi!"
Yana rufe baki dukkan ruwan dake kewaye da Armad ya juye nan take izuwa farar ƙanƙara. Cikin ƙiftawar ido da bismillah wannan ƙanƙara ta kewaye Armad ta rufe shi ɗaki ɗaya.
Kai daga nesa idan ka hango Armad kace wani gunki ne da aka sarrafa da farar ƙanƙara. Ga baki ɗaya jikinsa ya ƙanƙare baki ɗaya, kai ko fatar jikinsa ba'a gani.
Ikenga ya gabato inda ƙanƙararren Armad yake a tsaye yana taku ɗai-ɗai na ƙasaita, "Shin kasan daga cikin hadari akanyi ruwan ƙanƙara. Lallai ni Ikenga saina mulki duniya, kuma zan fara ta halaka ka, na kuma nunawa duniya ƙarfin Izza ta da ƙarfin aljani na Gal-iyyu, aljanin Hadari!"
A wannan lokaci ne wata iska mai cike da tsoro da firgici ta tashi daga cikin ƴan kallon. Lallai a wannan da dama daga cikinsu suka san an fara gasar Jinzidal.
***
Babi na 45 : Ɗorawa
SHEKARA ƊAYA KAFIN ARMAD YA FITO NEMO WA MAHAIFIYARSA MAGANI.
"Armad daga yau ya kamata kwata-kwata ka daina amfani da wannan fasahar takobin." Mahaifiyar Armad ce zaune a kusa dashi take lallashinsa a cikin ɗaki.
Ga dukkan alamu dare ne kuma Armad bai jima da dawowa daga karɓar horo daga kakansa ba, domin ko kayan jikinsa bai cire ba.
"Kaga duk amfanin da zakai da takobi zaka iya amfani da aljaninka na walƙiya kayi. Amma dai amfani da takobi haka ba tare da kasa walƙiya ba ina ganin a daina. Duk amfani ɗaya kana ƙara rage kwanakin da zakai a duniya. Kana kuma ƙara kusantar mutuwarka. Lallai bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya same ka. Saboda haka ka daina kawai. Walƙiya ta ishe ka duk abinda zakai. Kuma hatta yayar taka Hidaya data bar maka takobin nasan da tasan haka zata faru da bata bar maka ba."
"To mama naji. Na daina fa!" Armad ya faɗa cikin jimami da tuno wahalar da yasha kafin ya koyi wannan fasahar takobin amma gashi ala dole ya daina amfani da ita. Shekaru kimanin biyar kafin wannan rana ya gaji wannan takobi daga yayarsa mai suna Hidaya. Kuma tun daga wannan rana ya kwallafa ransa akan amfani da ita duk da cutar da jikinsa da take. Yakan ce takobin ita kaɗaice abarda tafi tuno masa da yayar tasa.
Ita dai yayar Armad wato Hidaya ita ta sawa wannan takobi sunan ƊORAWA. Da dama mutane sukan yi tunani kodan saboda launin yalo na takobin shi yasa tasa mata sunan, amma ba haka bane. Dalilin ta shi ne ƙaninta Armad yakan bata sautu ta taho masa da ɗorawa a duk lokacin da zata tafi wata ƙasar. Armad dai masoyin ɗorawa ne, kuma tun yana yaro ya kwallafa a ransa cewa kan ya mutu saiya sha ɗorawar kowacce ƙasa dake duniya, tun daga kan doron ƙasa ta farko har zuwa ta bakwai.
___
A dai-dai wannan lokaci Armad ya ji sanyin wannan ƙanƙara yana neman lalata masa jiki. Saboda tsananin sanyi yana ji tamkar ana soya fatarsa. Hatta ganinsa ya fara komawa dishi-dishi, kuma tuni ya daina jin muryar Ikenga saboda ƙanƙarar data kewaye shi.
Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa da Miyurarsa tana nan zai iya amfani da fasaharsa ta Wasu-wasi ya tarwatsa wannan ƙanƙara ya kuma saukarwa da Ikenga sara kafin ya farga. To amma yanzu babu. Kuma lallai idan ya ci gaba da zama a cikin wannan ƙanƙara to lallai ya faɗi wannan gasa, kuma Ikenga yayi nasara. Lamarinda ke nuni da cewa hanya ɗaya tak da yake da ita a wannan lokaci ta nemo Tarifil-fakta ta ɓace. Wanda kuma lallai abu ne da bazai amince ba, tunda baifi saura wata shida ne ya rage masa ya nemo wannan mutun ba.
Nan take ya yanke shawara, "Idan ana zancen taimakawa iyaye a lokacin da suke cikin buƙata, idan ana zancen nemawa mahaifiya lafiya, to ai rasa shekaru ɗaya ko biyu koma goma na tsahon rayuwa ba matsala bane. Wanda zaiyi shekara hamsin ai zai iya haƙuri da arba'in!"
A wannan lokaci Armad ya kira ɗalasimin da aka hanashi amfani dashi a rayuwarsa. Ɗalasimin da yake buɗe ƙofar amfani da takobin tarihi mai suna Ɗorawa. Takobin ita kanta Hidaya gada tayi daga mahaifinsu Wilbafos.
Wannan ɗalasimi dai anyi amfani dashi ne wajen sihirce wannan takobi acikin wani shinge na tsafi. Wanda babu wanda ya isa yaje ko mutun ko aljan. Kuma wannan ɗalasimi an haɗa shi ne da ruhin Armad da kuma jinin zuciyarsa, saboda haka nema sunan wannan ɗalasimi, "Armad-Wilbafos!"
Ai kuwa Armad na cewa, "Armad-Wilbafos!" Wata walƙiya mai ruwan ɗorawa ta fara ɓulɓula daga jikinsa. Nan take wannan ƙaton akwatin ƙankara dake kewaye da Armad ya fara narkewa.
Ikenga ya juyo cikin mamaki, amma kafin ya ƙarasa juyowa tuni dukkan ƙanƙarar tasa ta narke. Abinda kawai ya tarar shi ne walƙiya mai ruwan ɗorawa na kewaye da jikin Armad. Sannan kuma a gaban Armad akwai wani dogon haske shima ruwan ɗorawa, wanda ya bada siffar takobi mai tsayin gaske.
Kafin Ikenga ya gama tunani ko takobi ce ko ba takobi bace tuni dukkan yalon hasken ya ɗauke kuma wata doguwar takobi mai launin ɗorawa ta bayyana a gaban Armad. Tsayinta ya haura tsayin Armad da kamu uku da rabi, amma kuma siririya ce bata fi rabin tafin hannu ba. Dukkan jikin ta ruwan ɗorawa ne.
Amma babban abun mamakin shi ne wata tauraruwa ruwan ɗorawa guda ɗaya data tsaya a saman wannan takobi ta kuma ƙi ɓacewa. Girman wannan tauraruwa baifi kamu ɗaya ba, amma tana fitarda wata irin Izza mai ban mamaki.
Irin Izzar da baza ta misaltu ba, sai dai kurum wanda yake cikin wannan fili kuma yaji ta a jikinsa shi ne kawai zai iya fassara ta. Amma dai akwai kalma ɗaya da zata yi kama da wannan Izza wato MUTUWA. Lallai wannan Izza na kama da irin ƙanshin mutuwa wanda mutumin dazai mutu shi kaɗai ke ji.
Bayyanar wannan takobi keda wuya da dama daga cikin manyan baƙin da ke tare da Uznu Ururu da sarki Deniz suka miƙe tsaye suna buɗe baki. Kai hatta Uznu Ururu saida ya haɗe fuska cikin mamaki. Ga dukkan alamu waɗannan mutane sun san wannan takobi. Ko kuma dai a ƙalla sun taɓa ganinta.
'Takobin Wilbafos!' Wannan shi ne kawai abinda Uznu Ururu ya ce acikin ransa. Abinda ya nuna cewa yasan takobin sosai, kuma har sunanta ya sani.
A wannan lokaci ya zira hannunsa a aljihu ya fiddo da wannan allon tsafi, ai kuwa sai ganshi yana haske. Abin mamaki yadda allon yake haske da aka fito da Littafin-takobi haka yanzu ma yake haske. Kana ganin fuskar Uznu Ururu kasan ya gama yanke shawara cewa lallai Littafin-takobi yana tare da Armad.
Duk da wannan abubuwa dake faruwa ko a jikin Armad, miƙa hannu kawai yayi kan takobinsa ya kuma ɗaga ta sama, sannan cikin kwarewa da sabawa ana yi ya juya ta a sama ya kuma yiwo kan Ikenga.
Nan take Ikenga yai nuni da ɗan yatsansa sama, lamarinda yasa wannan hadari dake sama ya fara rugugi kafin daga bisani a fara ruwan manya-manyan al'amudan ƙanƙara guda uku. Ya ƙara tafa hannayensa waɗannan al'amudai suka juye izuwa mutun-mutumi.
Kowanne ɗaya daga wannan mutun-mutum ya juye izuwa siffar mutun sak irin Ikenga, harda kayan jikinsa.
Ikenga ya ƙara tafa hannu, waɗannan mutun-mutumi suka buɗe bakunansu a tare. Abu na gaba daya faru shi ne wata ƙuwa da sauti masu rikita zuƙata da suka fara tashi daga bakin wannan mutun-mutumi uku.
Ba komai ya jawo wannan ƙara ba illa wata dusar ƙanƙara mai tiriri dake fita daga bakin mutun-mutumi na farko, da kuma aradu mai ɗauke da jar walƙiya dake fita daga bakin mutun-mutumi na biyu, da kuma ruwan zafi dake fita daga bakin mutun-mutumi na uku.
Dukkaninsu kan Armad suka yi gadan-gadan suna neman halaka shi.
A wannan lokaci Armad ya juya doguwar takobin dake hannunsa. Wannan tauraro dake samanta ya kaɗa a sama. Sannan Armad ya aika wawan sara izuwa Ikenga.
Nisan dake tsakaninsu ya fi taku biyar kuma babu yadda za'ai takobin takai inda Ikenga yake, kai ko inda wannan walƙiya da ruwa da dusar ƙanƙara suke ma baza ta taje ba.
Amma bisa mamaki sai kawai wata walƙiya ruwan ɗorawa ta fice daga jikin takobin a matsayin saran da Armad yayi, ta kuma tunkari waɗannan abubuwa uku dake gabato shi. Wato dai a taƙaice saran da Armad yayi ya fice daga jikin takobin tamkar abu mai rai, ya kuma tunkari Ikenga. Irin wannan fasahar takobi aba ce maɗaukakiya a wannan zamani, kuma ita akewa laƙabi da fasahar takobi mai tafiya. Wasu kuma sukan kira ta Fasahar takobi mai Tafiya.
A dai-dai wannan lokaci ƴan kallo suka fara firgita da al'amuran da suke gani. Lallai basu yi kama dana masu shekarun Izza ƙasa da dubu ba.
Babu abida kake ji sai, "Kunga Armad yana iya amfani da fasahar takobi mai tafiya!"
Wasu kuma su na cewa, "Kunga aljanin Ikenga SARKI RAUHANI ne." To ko mai ake nufi da aljani SARKI RAUHANI?
To aljanu gama gari dai su ake rabawa izuwa ƙabilar baƙi, fari da kuma ja.
Aljanu maɗaukaka kuma ana raba su ne Izuwa ƙabilar Rauhani, Muridi, Shaiɗani da kuma Ifiritu. To ko acikin waɗannan ɗin ma akwai maɗaukaka na sahun farko, wanda ake musu laƙabi na musamman. Misali asalin sunan aljanin Ikenga shi ne IYYU, amma saboda kasancewarsa maɗaukaki na sahun farko shi yasa ake ce masa GAL-IYYU. Wato dai 'GAL' ɗin da aka ƙara wata lambar girma ce.
Babban banbanci tsakanin waɗannan aljanu shi ne ƙarfi da kuma yawan sihirin da zasu iya
sarrafawa.
Misali aljani gama-gari ɗan ƙabilar Fari, ko Baƙi, ko kuma Ja, baya taɓa mallakar fasaha sama da ɗaya; dole sai dai ko ya zama aljanin wuta, ko na ruwa ko na walƙiya ko na ƙanƙara ko kuma dai wani abu amma dai abu guda ɗaya kurum.
To shima jinsin Rauhani da Muridi da Ifiritu da Shaiɗani abu ɗaya kurum suke iya mallaka, sai dai banbancin shi ne su basu da ƙa'ida. Misali aljanin Wuta ɗan ƙabilar Fari ko Baƙi ko Ja yana da adadin wutar da zai iya sarrafawa a kowanne lokaci, kuma indai ta ƙare saiya jira ta taru. Amma wutar aljanin wuta na ƙabilar Rauhani ko Muridi ko Ifiritu ko Shaiɗani bashi da ƙa'ida, wato zai iyai ta samarda wuta har abada. A kowanne lokaci idan kai duba acikin ɗan taƙin dake tsakanin ruhin irin waɗannan aljanu da masu su zaka ga wuta bata ƙarewa.
To sai kuma aljani maɗaukakin Rauhani, wanda shima fasaharsa bata ƙarewa kamar duk wani Rauhani, sannan kuma yakan mallaki fasaha sama da ɗaya. Yawanci biyu. Amma ƙasa da kaso ɗaya acikin ɗari sukan samarda fasaha sama da ɗaya kamar aljanin Ikenga kenan.
Irin wannan aljanu su ake kira da SARKI, sai a ƙara kalmar sarkin a farkon sunansu. Wato dai a taƙaice shi ne abinda ƴan kallon can suke nufi da cewa aljanin Ikenga SARKI RAUHANI ne.
***
Babi na 46 : Nauyi da Lokaci
•Suna : Armad
•Ƙabila : Wilbafos
•Aljani : Ji-daime
•Fasaha : Farar Walƙiya
•Fasaha ta musamman : Miyura
•Fasahar takobi : Ɗorawa
•Izza : shekara 51
____
•Suna : Ikenga
•Ƙabila : Bayajidda
•Aljani : Gal-iyyu
•Fasaha : Jar walƙiya, ruwa, ƙanƙara
•Fasaha ta musamman : Takun-sarki (shaibal-shísu)
•Fasahar Takobi : Lokacin alfijir
•Izza : Shekara 100
***
"Hmmm...." Armad baiko tsaya kallon saran takobin daya aikawa wannan ƙanƙara da ruwa da walƙiya ba, domin yasan lallai saran sa na takobi mai tafiya ba sa'an waɗannan mutun-mutumi bane. Saboda haka ya yiwo kan Ikenga ta ɓangaren dama.
A gabansa kuwa tuni wannan sara ya haɗu da wannan ƙanƙara da wuta da walƙiya. Haɗuwar tasu keda wuya gaba ki ɗayan abubuwan nan guda uku suka tarwatse suka ɓace, tamkar ba'a taɓa yinsu ba. Sannan saran yaci gaba da tafiya yayi kan wannan mutun-mutumi gadan-gadan. Amma suma basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da aikowa da wannan sara saƙon bala'i. A haka suka samu suka tsayar dashi kafin ya isa gare su. Ai kuwa saran na tsayawa duk su ukun sukai kan Armad suka hanashi ƙarasawa kan Ikenga wanda ke tsaye a gefe na ganin maike faruwa.
Suka saka Armad a tsakiya, sannan suka fara aika masa da saƙon ruwan zafi, walƙiya da dusar ƙanƙara. Suna niyyar halaka shi ta kowanne ɓangare. Amma ina, Armad a tafe ya kwana. Domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne ya fusata ya juya takobinsa da karfin tsiya, sannan ya kaiwa waɗannan mutun-mutumi uku sara, inda ya tsinke musu kai nan take. Wata iska mai zafi ta fice daga jikin takobin tasa sannan ta daki jikin mutun-mutumin suka juye izuwa toka. Cikin ƙiftawar ido Armad ya bayyana a gaban Ikenga ya kuma kai masa wawan sara.
A dai-dai wannan lokaci babu wata kalma da zaka iya yin bayanin Armas da ita illa kace yayi kama da matashin bajimin aljani ɗan fari. Babu alamun tausayi ko yafiya a tattare da idanunsa, lallai a kowanne lokaci Ikenga zai iya ziyartar lahira.
Sai dai ana cikin haka ne Ikenga yaga babu sarki sai ALLAH yai zafin nama ya tafa hannayensa tare da kiran ɗalasimin Takun-sarki, "Shaibal-shísu."
Acikin wani yanayi na ban al'ajabi gaba ki ɗaya lokaci ya tsaya cak, ya kuma bawa Ikenga damar yin taku bakwai da ƙafafunsa kafin saran Armad ya cimmasa. Yana ajiye ƙafa a takun ƙarshe wani duhu irin na farkon ketowar alfijir ya bayyana ya maye gurbin hasken da da ke cikin filin kallon. Hatta ƴan kallon dake cikin filin basu samu damar ganin abinda ke faruwa ba a dai-dai wannan lokaci.
Bayan kimanin daƙiƙa biyar wannan duhun ya sarara, sannan haske ya dawo. Ai kuwa sukai arba da Ikenga sanye da wata rigar tsafi ruwan dinare, sannan kuma riƙe da wata takobi mai kyalli ita ma ruwan Dinare.
Armad kuwa na can gefe a tsaye shima riƙe da takobinsa ruwan ɗorawa. Babu alamun ciwo ko rauni ko gajiya a jikin kowannensu, amma ga dukkan alamu iskar dake kaɗawa a tsakaninsu ta canja, kuma lallai yanzu ne za'ai faɗan ƙarshe. Kana gani kasan kowa acikinsu yai rantsuwa daya faɗi ƙasa a wannan wasa a gaban idon duniya kwara ya mutu.
"Fasahar Ɗorawa ko?" Ikenga ya kalli takobin Armad cikin nazari sannan yaci gaba da cewa, "lallai babbar fasaha ce. Kuma idan da ba dani ka haɗu ba, to da lallai zaka iya yin nasara akan kowa. Amma kayi sani cewa ƙarfin dake cikin ruhi da jini na ya wuce gaban lisaafin ka, kuma yanzu zan nuna maka dukkan ƙarfina. Zan nuna maka fasahar takobi dana sakawa suna Lokacin Alfijir. Ina mai baka shawara idan har kana da wani shiri a ɓoye, to ka fito dashi."
Yana rufe bakinsa yai kan Armad cikin zafin nama tare da kaɗa wannan takobi ruwan dinare dake hannunsa. Ai kuwa nan take wani duhu irin na alfijir ya fito daga jikin ƙarfen takobin ya kuma yiwo kan Armad.
Duk inda wannan duhu ya gifta sai kaga wajen ya tsufa nan take kuma ya murmushe tamkar wanda yayi shekara dubu a ajiye. Kan kace meye wannan tuni filin da suke fafatawa akai ya tashi daga sabo mai kyalkyali ya koma izuwa tsoho tamkar wanda akai shekara dubu da sarrafa shi.
Armad na ganin haka ya ja da baya da sauri ya tafa hannayensa ya sa tsinin takobinsa ya caki hannunsa, sannan ya shafa jinin akan takobin. Kafin wannan sara na Ikenga ya ƙaraso tauraruwa ɗaya dake saman takobin Armad ta fara ƙoƙarin rabewa izuwa biyu. Amma ina, kan ta ƙarasa rabewa wannan sara ya iso, inda ya daki jikin takobin Armad da ƙarfin tsiya sannan ya ɓace. Yana ɓacewa Armad ya kalli hannunsa yaga yayi furfura ya tsofe ya yamushe tamkar wanda yayi shekara dubu a raye. Cikin ɓacin rai ya maida takobin hannun dama, inda lokacin tauraruwar ta koma biyu. Dukkan wani ƙarfi dake jikin Armad da takobinsa ya koma izuwa biyu. Nan take wani tsananin nauyi mai ban tsoro ya fara fita daga jikin Armad yana yiwo wa kan Ikenga.
Kan kace meye wannan wajen da suke tsaye ya fara lotsawa cikin ƙasa, tamkar wanda aka dunƙule nauyin dala da kwauron dutse aka ɗora masa. Ikenga yaji ƙafafuwansa sun fara ƙara suna neman karyewa saboda wannan nauyi. Amma a lokacin ya ƙara kaɗa takobinsa ruwan dinare, lamarinda yasa wannan nauyi ya tsofe nan take, tamkar yayi shekara dubu. Lallai ba nauyi ba koma mene ne zai ƙare idan yayi shekara dubu.
Ana cikin haka ana kallon kallo aka ji muryar Ikenga, "Hmmm.... wato kana da takobin da take sarrafa nauyi. Ta ƙarashi ko kuma ta rage shi. Lallai kaima ma'aboci Izza ne, amma duk da haka baza ka iya tsayawa a gaban fasaha ta Lokacin alfijir ba. Takobi ta ta duhun alfijir tana sarrafa lokaci. Kuma duk abinda na sara da ita a lokacin take yake tsufa na shekara ɗari. Ko yaro ne anan take zai tsofe tamkar yayi shekara ɗari. Lallai saina mulki duniya da fasaha ta takun sarki. Kayi sani cewa indai na sare ka koda sau ɗaya ne, kuma komai ƙanƙantar saran sai ka tsufa na kimanin shekara ɗari nan take."
Yana rufe baki yai kan Armad da takobinsa gadan-gadan, shima Armad kawai fusata yaƙara yi ya kuma yiwowa kansa. Duk inda Armad ya gifta sai wajen ya nutse a ƙarƙashin ƙasa tamkar an haƙeshi da kimanin ƙafa ɗari. Shi kuma Ikenga duk inda yayi sai kaga wajen ya tsufa.
Suna haɗuwa suka kaure da azababben yaƙi, ƙura ta turnuƙe, iska ta tsofe, haske ya ɗauke. Ƴan kallon basa jin komai sai ƙarar takubba. Cikin daƙiƙa ashirin kawai su biyun sun isarwa da juna sara sama da hamsin. Duk sanda saran Ikenga ya yiwo kan Armad, Armad zaiyi amfani da nauyi ya danne shi izuwa ƙas ya hanashi zuwa wajensa. Shi kuma Ikenga kawai tsofantar da saran Armad yake kafin ya isa gareshi.
Haka wannan yaƙi yaci gaba tsahon kimanin mintuna bakwai, kafin daga bisani a daina jin komai. Kowa acikin ƴan kallo yayi tsit acikin filin wasan. Jira kawai ake aga ƙurar ta lafa domin aga maike bayan wannan ƙura.
Bayan minti ɗaya ƙurar ta lafa, akai arba da Ikenga da Armad a kwance cikin jinin shane-shane, babu wanda yake iya motsi acikinsu. Lallai duk su biyun sunkai ƙarshe wajen ƙarar da ƙarfin jikinsu. Kai hatta ɗan yatsa basa iya motaswa. Amma duk da haka basu daina yiwa juna kallin tsana da azabar yaƙi ba. Kansu na tsaye suna kallon juna, kuma da da yadda zasu yi da tuni sun ƙara tashi sun afkawa juna.
Ana cikin haka alƙali ya rasa wa zai bawa nasara, kawai sai Armad yaga wani dattijo mai yawan farin gashi bayyana akan Ikenga ya dafa shi. Haka na faruwa dukkan Izzar Ikenga ta dawo tamkar yanzu aka fara faɗan.
Yana ji Ikenga ya ce, "Bayajidda, karfa wani ya ganka."
Sannan kuma yana ji dattijon da aka kira da Bayajidda ya amsa, "Ai ko Uznu Ururu dake cikin can bai isa ya ganni ba. Saboda dalili guda biyu, na farko dai ƙarfin Izzarsa bai kai ya ganni ba, sannan kuma koda ƙarfinsa yakai babu wanda zai iya gani na sai jinin Bayajidda."
Armad ya buɗe baki zai gayawa alƙali da ƴan kallon cewa Ikenga zaiyi fasha, amma hatta bakinsa ma yaƙi motsawa saboda tsananin gajiya da ƙarewar ƙarfin Izzarsa baki ɗaya. Kai hatta idonsa ma ya kasa ƙiftawa.
Tunani kaɗai yake iya yi acikin ransa, 'wai mai wannan tsohon yake nufi da babu wanda zai iya ganinsa sai jinin Bayajidda, gashi ina ganinsa. Kuma yana nufi Uznu Ururu ma bai kai ƙarfinsa ba. Koma dai meye lallai bazan yadda ba, wannan ai fasha ce!'
***
Babi na 47 : Hidaya Wilbafos
Armad na ganin wannan ruhi mai girman Izza daya bayyana ya taimaki Ikenga babu abinda ya faɗo masa acikin rai sai ƴar uwarsa mai suna Hidáya Wilbafos.
___
1847 Bayan Amri
Kaɗan daga cikin tarihin Armad da ƴar uwarsa.
"Armad wallahi zan dake ka! Wai baza ka maida hankali ba!" Wata budurwa mai matuƙar kama da Armad tayi masa tsawa a yayinda suke tsaye a filin horo.
A wannan shekara ta 1847 Armad yana ɗan shekara takwas, kuma tun a wannan lokaci aka fara koyar dashi al'amuran Izza.
Wannan budurwa na tsaye sanye cikin jar alkyabba irin ta mutanen farko. Kimanin shekarunta zai kai ashirin da biyar koma fiye da hakan. A rataye da kafaɗarta ta dama akwai doguwar takobi mai zanen taurari ruwan ɗorawa. Budurwar doguwa ce wadda a ƙalla zata yi zira'i uku a tsaye. Kamanninta akwai kamala da nutsuwa da jarumta aciki, lallai akwai ƙarfin Izza a tattare da ita.
Sunan wannan budurwa Hidaya Wilbafos. Kuma yayar Armad ce ta jini duk da kuwa ratar shekarun da ke tsakaninsu.
Armad na sanye cikin farar ƴar shara ɗaure da jan kyalle a goshinsa. Daga ganin yadda yake ɓata rai kasan dole tayi masa, amma lallai da zata kyaleshi da bazai yi wannan horo ba.
"Shikenan, idan baza ka dage ka koyi al'muran Izza ba to ba ruwa na da kai. Idan bana nan wa zai kare ka?
"Ehmmm..." Hidaya ta ja dogon numfashi tare da girgiza kai. "gaka da tsokana amma baka san dagewa ka koyi al'muran Izza, sai muga idan bana nan wazai ringa hana yaran da kake tsokana suyi maka duka. Zo mu tafi gida, kuma gobe ma sai mun dawo ka ci gaba. Ai ko kana so ko baka so saika zama ma'aboci Izza."
Hidaya ta juya zata tafi amma Armad ya tsaya yaƙi binta, fuskarsa cike da shagwaɓa irin ta ƙananun yara.
"Ka taho mana...." Hidaya ta waiwayo tai masa magana.
"Ni.....ni fa ƙafa ta ciwo take!" Armad ya haɗe fuska kamar zai fashe da kuka.
"Hmmm....." Hidáya taja numfashi gami da gyaɗa kai. Domin tuni ta gano abinda Armad yake nufi. Sau da dama idan suka fita tare yakan ce bazai iya tafiya ba saita goyashi shi a bayanta. Kuma a wannan lokacin ma abinda yake nufi kenan.
"Indai baka dage ba ai daina ɗaukan ka zanyi." Cikin sanyin zuciya da tausayi irin na ƴan uwa ta juyo izuwa Armad. Inda ta durƙusa ta goya shi sannan suka kama hanya.
Ba jimawa suka fara fita daga cikin duhun manyan bishiyun goriba da suka kewaye wajen. Hidaya ta numfasa tare da ci gaba da nunawa Armad muhimmancin ya dage da horonsa. Ga dukkan alamu baza ta haƙura ba indai Armad bai maida hankali yayi ba.
"Kaga ina so na koya maka duk wasu fasahohi na sarrafa aljanu da suka shafi zuri'ar gidan wilbafos kafin lokaci ya ƙure. Amma kaƙi maida hankali, towai mai kake so ka zama ne, gayamin naji?"
Armad na kwance a bayanta cikin shagaɓa irin wadda yayar tasa ita kaɗai yake yiwa, ya fara da cewa, "kinsan me yaya, ni dai abinda nake so a rayuwa shi ne zaman lafiya ya wanzu. Ko wa ya zamanto acikin kwanciyar hankali. Idan na girma na zama kamar ke nayi aure, idan na kara girma saina haifi ƴaƴa guda uku duk masu kama dake, sannan idan na tsufa saina mutu akan gado na akan cinyarki tare da mama da Abba da ƴaƴa na duk sun kewaye gadon da zan mutu. Shikenan inna mutu sai kuyi kuka sannan kuma ku ringa tunani na...." Koda yazo nan a zancensa sai yai shiru tamkar wani abu ya gilma acikin ransa, inda cikin tsoro irin na yara ya ɗaga kai ya dubu yayar tasa Hidaya. Idanunsa a wangale ya ce, "Ai zaki ringa tunani inna mutu ko Yaya?"
Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta juyo da kanta ta ƙura masa ido tana mai mamakin wannan abu daya faɗa. Badan komai ba sai dan cewa ita ma kanta shekaru da dama da suka wuce burinta kenan. Tamkar ƙanin nata Armad ya shiga ranta ya gani, duk da kuwa cewa bata taɓa gayawa wani mahaluƙi wannan buri nata na yarinta ba har zuwa wannan lokaci.
Saboda haka sai kawai tayi murmushi tare da cewa, "eeh, zan tuna ka."
Amma ga dukkan alamu wannan magana kaɗai ta faranta wa Armad rai, inda ya ƙara maƙalewa a bayanta tamkar yana tsoron wani abu zaizo ya raba su da ita.
Murmushi kawai tayi taci gaba da tafiya tana yin tunane-tunanen ya zatayi ta kare wannan ƙani nata wanda baya son koyon al'amuran Izza ko kaɗan.
Tana cikin tunani ne taji muryar sa yana cewa, "ehmmm... Kinsan me? Mu ɗaura alkawari cewa duk wanda ya riga mutuwa ɗayan zai ringa tuna shi."
Tun kafin ya rufe bakinsa ya ziro ɗan ƙaramin ɗan yatsansa ta gefen kunneta da niyyar su ɗaura. Babu abinda tayi face ajiyar zuciya sannan kuma ta kama hannun nasa da niyyar ta yarda.
Kamar zaiyi shiru, amma abu na gaba daya faɗa shi ne, "to indai da gaske kin yarda toki ɗakko min ɗaya daga cikin filawar dake wancan lambun." Armad yai nuni da wani katafaren lambu kimanin taku dubu daga inda suke tsaye.
Babu abinda kake gani daga nesa sai baƙin duhuwar wannan daji da wasu manya-manyan baƙaƙen bishiyu waɗanda lallai koda basu yi shekaru dubu a raye ba to kaɗan ne babu. Tsayin kowacce bishiya yakai zira'i maitan da ɗoriya. Kai lallai har sai hular mai kallo ta faɗi ƙasa saboda ɗaga kai amma bai gano ƙarshen wasu daga cikin bishiyun ba.
Lambun daban yake da wanda su Armad ke ciki, kuma an kewaye shi sannna kuma ansa shedar sarki Hanibal Sarkin ƙasa ta uku akai. Sarki Hanibal shi ne sarki mai mulkin doron ƙasa ta uku, sannna kuma yana ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal biyar.
Koda jin wannan magana sai Hidaya ta canja fuska, "Armad ka fasan cewa duk abinda ke cikin can wajen na Hanibal ne kuma ya hana shiga."
"Eh na sani, amma fa ta sama zamu bi kawai mu ɗauki guda ɗaya ai ba wanda zai sani fa. Kinji Yaya, kinji... Kinji daga wannan fa shikenan."
Tai murmushi tare da ajiƴar zuciya, "To muje amma karka taɓa komai kaji."
Armad ya kyaɗa kai.
A dai-dai wannan lokacin Hidaya ta tafa hannayenta ta kuma kira wani ɗalasimi a zuci, sannan tai tsalle ta tashi sama tamkar tsuntsu mai fuka-fuki. Abu ne sananne cewa duk wanda ya haura shekaru dubu na Izza to zai iya tashi yayi tafiya a sama ba tare da matsala ba. Kuma hasalima Armad bawai filawar ce ta dame shi ba, sai dai kawai yana so ƴar uwar tasa ta tashi sama dashi, saboda yasan lallai indai zasu shiga dajin to saisun tashi saman.
Ai kuwa suna tashi sama Armad ya ƙara saƙale hannunsa ta ƙirjinta tamau, sannan ya saki ɗayan akan iska yana ihun farin ciki. Duniya tayi masa daɗi domin a wannan lokaci babu abinda yake so face tashi sama a bayan yayar tasa.
"Wuuuuuu...." Tun daga nesa zaka iya jiwo ihun Armad a saman.
"Dama nasan abinda kake so kenan. Ka riƙe ni dai sosai karka faɗo." Tana cikin magana suka dira acikin tsakiyar wannan daji. Inda ta ajiye Armad ta kuma juya tana hangen imda filawar take.
"To ka tsaya anan, ga wata can bari na ɗauko maka." Nan take ta ƙara tashi sama ta nufi wani surƙuƙi a ɓangaren arewa.
Bayan daƙiƙa ashirin ta dawo da wata filawa yaluwa mai kyawun gaske.
Amma tana sauka a gaban Armad taga hannunsa na ɗisa da jini.
"Waye ya ji maka ciwo?" Shi ne kawai abinda ta tambaya.
Tun kafin Armad ya bata amsa siffarta ta canja baki ɗaya. Wani yalon haske ya fara fita daga jikin takobin dake rataye a kafaɗarta. Wata baƙar wuta ta fara ci acikin idanunta. Nan take iskar wajen ma ta canja ta ƙara nauyi, sannan kuma wani sauti ya fara tashi daga cikin wannan daji. Lallai inda akwai mai fassara maganar tsirrai da yaji cewa haƙuri waɗannan bishiƴoyi ke bawa Hidaya. Amma ina, tuni ta toshe kunnenta tsahon lokaci. Kai hatta alkyabbar dake jikinta ta canja launi izuwa baƙa, lallai a wannan lokaci Hidaya tayi kama da siffar mutuwa kanta.
Amma a wannan lokaci shi kamsa Armad karkarwa yake yana matsawa baya ganin yadda yayar tasa ta canja kama. Yana ji tamkar wutar dake cikin idanunta zata soya naman jikinsa nan take.
Bai san lokacinda bakinsa da kansa ya fara magana ba ba tare da ya bashi umarni ba. "Wancan ƙayar dake jikin wancan bishiyar ce." Ya nuna wata bishiyar ƙaya a kusa dashi yana karkarwa.
"Wato har akwai wanda ya isa ya jiwa ƙanina ciwo ina wajen! Lallai yau ba Hanibal ba, koda wannan dajin na sarkin Ururu ne a bisa doron ƙasa ta farko saina rusa ku." Tanan rufe baki ta zare takobinta, inda nan take wasu taurari guda uku suka bayyana a kewaye da takobin.
Ai tunma kafin ta juya takobin dukkanin wannan lambu ya kama da wuta. Wanda idan da zaka kula zaka ga irin wutar dake ci acikin idonta ce.
A dai-dai wannan lokaci Armad ya sume a wajen. Babu abinda yake iya tunowa sai tashi dayayi washe gari ya ganshi akan gadonsa Hidaya na gefensa tana shafa kansa.
To a wannan shekara ne da kakan Armad mai suna Zaikid da yayar tasa Hidaya suka tafi wani aiki wanda Armad yayi-yayi amma suka ƙi bayyana masa ina zasu. Daga ƙarshe ya haƙura.
Bayan wata biyu da wannan tafiya tasu, dattijo Zaikid ya dawo shi kaɗai. Babu Hidaya amma akwai takobin ta mai taurari ruwan ɗorawa a hannunsa.
Armad ya taho da gudu yana tambaya ina take, amma kakan nasa baice komai ba sai kawai takobin daya miƙa masa. Armad na karɓa ya fashe da kuka ganin alamun jini a jiki.
Tun daga wannan lamari Armad ya ɗau takobi ya kuma shiga koyon horo da alamuran Izza.
Comments
Post a Comment