Babi na 251-253
***
Ɓangaren Rafiyan Nazára
Rafiyan nazara ya ƙara ƙanƙame littafin yaƙutun izza dake hannunsa wanda Ikenga ya bashi. Ya shafa bangon littafin da hannunsa. Akwai leda samfurin yeniy wadda aka liƙe littafin da ita. Indai yana so yaga kalma ɗaya a ciki to saiya amince da abinda Ikenga yazo masa dashi.
Bayan ɗan lokaci ya ɗago kai ya dubi Ikenga ya ce, "idan na baka Nusi mai zai faru da ita?"
Ikenga wanda ke tsaye yana jiran Nazara yayi murmushi acikin zuciyarsa. Ga dukkan alamu haƙansa zai cimma ruwa. "Bazan ɓoye maka ba; harka ce ta ruhi. Indai na zare ruhinta to babu makawa mutuwa zatai. Amma idan da gaske ka damu da ita akwai hanyarda zan iya dawo da ita. A halin yanzu bani da izzar da zanyi hakan amma da zarar na mallaki ruhin Tarifil-fakta hakan zata faru."
Nazara yayi shiru yana nazari. Bayan sama da mintuna biyar ya ɗago kai ya kalli Ikenga da mutun biyar ɗin dake bayansa. Abin mamakin sai kawai aka ga ya zare ƴar ƙaramar wuƙar dake aljihunsa ya caka a ɗan'yatsansa na ƙafar dama. Ya guntule ɗan'yatsan baki ɗaya, jini yai feshi sama ya ɓata Ikenga.
B. Ururu ya yunƙura a fusace zai sare kan Nazara amma Ikenga ya ɗaga masa.
Nazara ya cije harshe cikin tsananin kafiya da dauriya irin ta shaƙiƙan farko ya ɗaga ɗan'yatsan daya guntule ya cillawa Ikenga tare da littafin kwangilarsa da na yaƙutun-izza. "Wannan ɗan'yatsa dana guntule saboda tunani ɗaya kacal da nayi na yaudarar Nusi ne. Nusi ita ce JININ-ZUCIYA TA. Ina mai tabbatar maka cewa ko duniya zaka bani bazan yaudare ta ba."
Ikenga ya yamutse fuska tsahon daƙiƙu kafin daga bisani ya ce, "kasan waye ni, kasan ruhin da Armad da Bihanzin suke ɗauke dashi na Tarifil-fakta, kuma kasan cewa a YAƘIN-RUHI babu wanda zaiyi nasara banda ni. Domin shi kansa yaƙin an shirya shi ne saboda ni. Amma duk da haka baza kayi mubayi'a ba?"
Nazara ya datse haƙora ya ce, "ni zan zaɓi yadda zan mutu da ranar da zan mutu."
"Idan ka zaɓi Nusi kamar ka zaɓi Armad ne, kana da cikakkiyar masaniyar cewa Zaikid da Taidara da Fatima sune suka kashe ƙaninka ko?"
[idan mai karatu bai mantaba gab da fafatawar jinzidal a littafi ka farko an gano yarima Niyashi acikin jirgin ruwa da gawar ƙaninsa.]
Fuskar Nazara tayi baƙi, tsohon miki ya taso ya cika zuciyarsa. Amma yana buɗe baki abinda akwai ya ce shi ne, "Jinin-zuciya ta."
Ikenga ya gyaɗa kafaɗa ya ce, "ka zaɓi mutuwa a kan rayuwa?"
Nazara ya amsa da cewa, "Jinin-zuciya ta."
"To ai shikenan, mu haɗu a yaƙin-ruhi nan da kwana sittin. Da sannu bawa zai gane waye ubangijinsa."
Ɓangaren Armad
Farar-ƙasa ta rako Armad da Nostaljiya waje inda sukai sallama. A lokacin masallacin ya ɓace ɓat suka nemeshi suka rasa.
Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma Armad ya tari numfashinta da kalma guda ɗaya. "Izza."
Ta kalleshi cikin mamaki. Mai yake nufi?
Armad ya ƙara maimaitawa. "Izza."
"Izza kuma? Kayimin bayani sosai, ta ina zamu fara?"
Armad ya gyaɗa kai. "Izza ita kaɗai ce abinda nake dashi. Koyar sarrafata ita kaɗai ce hanya mai ɓullewa. Bansan meye haƙiƙanin abinda Ikenga da Bihanzin suka kware akai ba amma babu wanda acikinsu yake iya sarrafa izza. Idan ma akwai daga gidana suka ara. Gidan Wilbafos da izza aka san mu, kuma da izza muke yin nasara. Abu na farko da zan kai ƙololuwar kwarewa ashi shi ne izza."
Nostaljiya ta numfasa ta ce, "hakane to amma ina ganin ai tuni ka girmama a harkar izza. Tun a yaƙin sarakunan jinzidal kana iya aron shekarun izza sama da dubu talatin daga Miyurar ka. A yanzu da ka samu zaren izza dole abin zai ƙaru. Kana iya gano fasahar Layar-zana da zaren izza, kana iya tsinka zaren izzar mutun ka katse masa izza baki ɗaya, kana iya zuƙar izza daga sauran mutane...."
Ganin kallon da Armad yake yi mata yasa ta tsaya da bayani.
"Kinji a inda matsalar take: aron izza nake, kamata yayi ace dukkan izzar da aka ajiye acikin Miyura ta a yanzu ta zama tawa dimun-da'iman ba saina ara ba. Kina tunanin a tsakiyar yaƙi Bihanzin da Ikenga zasu bani dama na ari izza ne. Kana ƙifta ido zaka tsinci kan ka a lahira. Matsala ta biyu ita ce bana iya tsinka zaren izzar mutane, ko kuma nace ban taɓa tsinka zaren izzar wani ba saboda ƙarfi na bai kai ba. Eh na taɓa saran zaren izzar Hidaya amma ko kwarzane baiyi ba ballle ya tsinke. Sannan kuma bana iya zuƙar izza daga mutane, kamata yayi ace yadda nake iya zuƙar izza daga miyura haka nake zuƙa daga jikin mutane da aljanu da Dordor dama duk wani abu mai izza. Dole sai nakai matakin da ina bacci zan iya zuƙe izzar duk wanda ya kusance ni da mugun nufi. Kamata yayi ace a duk sanda na ɗaga takobi na izzar abokan gaba ta tarwatse ta rududduge, kai ina buƙatar na wuce haka ma indai ina so nayi nasara a kwana sittin masu zuwa. Wannan kuma ɓangaren izza kenan, dole ta kowanne hali sai na mallaki sabbin fasahohi irinsu Kamalar-ruhi. Ina buƙatar na shiga Deba. Idan na shiga Deba bazan tsaya a Asalin Deba ba, bazan tsaya a Lardin Deba ba, kai tsaye zan wuce mataki na ƙarshe wato Waadin Deba. Daga nan zan wuce gaba izuwa matakin izza na gaba wanda Kuyurussa'ayi ne kaɗai ya taɓa wannan mataki."
Nostaljiya ta ja wani ɗan gajeren numfashi mai cike da kokwanto ta ce, "duk wannan acikin kwana sittin?"
Armad ya gyaɗa kai. "A kwana hamsin da ɗaya. Kafin kwana taran ƙarshe nasan kowa zaiyi ƙoƙarin kammala shirinsa. Ko kuma wani abu ya faru a rage kwana sittin ɗin, idan haka ta faru bana so na zamo ba'a cikin shiri ba."
"Hakane. Amma kace tunda aka shigo kurkukun lokaci ka nemi ruhin Hidaya ka rasa, ta wace hanya kenan zaka shiga matakin Deba?! Shi kaɗai ne ruhin Deba da kake dashi."
"Ta hanyar Miyura ta. Ban sani ba ko zai yiwu amma zan gwada. Kiyi tunani, meye banbancin Sammai da Jemai da Ƙassai da Deba? Yawan izza ne kawai. Idan zan iya ɗaga yawan izza ta yakai matakin Deba ba tare da ruhin Deba ba kinga zan iya shiga matakin Deba kenan."
"Hmm... Kai dai kace baka so ka lalata ruhin Hidaya saboda nace maka sai ruhin Deban ya mutu sannan zaka iya zuƙarsa ka shiga Deba."
"Idan ruhinta yana tare dani a har kullum kamar muna tare ne. Zanji maganar ta zata ji tawa, zamu yi hira mu gana. Amma bazan iya lalata shi kawai saboda na shiga matakin Deba ba. Kuma akwai abinda kika kasa ganewa: akwai Deba da yawa a ban ƙasa, wani yafi wani ƙarfi. Meye yake banbanta su? Yawan izza. Kinga kenan koda ka zama deba kana buƙatar yawan izza wanda shi zai ƙara maka ƙarfi. Ina ganin indai na mallaki dukkan izzar da take cikin miyura ta zan kai wannan mataki."
Nostaljiya ta gyaɗa kafaɗa ta ce, "to naji, amma a halin yanzu a ban ƙasa waye zai koya maka abinda kake nema? Ruhin Hidaya bai shigo kurkukun lokaci ba kuma ga dukkan alamu sai an cire kurkukun sannan zai dawo. Sai dai idan su farfesa Zaikid zaka nema."
Armad ya girgiza kai. "Basu zan nema ba, akwai wajen da zanje."
"Ina?"
"Duniyar aljanu. Akwai baitika da Hidaya ta bari a babinta na waƙar-maƙabarta da wasu shaihunan aljanu data ambata. Su zan kaiwa ziyara. A halin yanzu ke kuma ina so ki koma kurkukun bango ki bayyanawa su Babara abinda ya faru. Ina so kowa ya zama cikin shiri kafin na dawo."
Nostaljiya tai firgigit ta matsa kusa dashi ta ce, "karma kayi tunanin wai kai kaɗai zaka tafi. Duk inda kasa ƙafa ina tare dakai."
Dama Armad yasan za'ai haka amma babu yadda za'ai ya tafi da ita saboda hatsarin tafiyar. Daɗin daɗawa akwai abinda Armad yake son tayi masa wanda kuma ita kaɗai ce zata iya. Kafin ta ankare ya jawo hannunta ya zana wani hatimi akai. Hatimin yana da zanen fuskar mutun da kuma ɗalasimai a dai-dai sai tin idon.
"Mai kake yi...?"
"A halin yanzu ke kaɗai ce zaki iya saka mutane acikin kurkukun lokaci. Duk mutun ɗaya da Ikenga ya saka kema zaki iya saka mana mutun ɗaya. Na yadda dake nasan zaki yi abinda ya kamata. Duk wanda zaki saka kiyi masa bayanin halin da ake ciki da kuma yaƙin da yake tunkaro mu. Idan mutun baya so kada kiyi masa dole. Kamar yadda na gaya miki duk wanda aka saka zai iya koyon fasaha da kuma karɓar horo acikin kurkukun ba tare da ya manta ba idan aka wayi gari. Saboda haka ki zaɓar mana manyan ma'abota fasaha wanda zasu iya karawa da abokan gabar mu."
Sannan Armad ya ciro wani ɗan littafi acikin aljihunsa ya miƙa mata. "Na zaƙulo manya-manyan fasahohi daga cikin waƙar-maƙabarta na rubuta su acikin wannan littafi. Duk wanda kika saka ki bashi su kyauta ya ƙara fasaha. Zan dawo acikin kwana talatin masu zuwa, a lokacin zan futo da dukkan sauran fasahohin da suke cikin waƙar-maƙabarta na raba."
Nostaljiya ta girgiza kai ta ce, "duk wannan bazai saka na bari ka tafi kai kaɗai ba. Kwana uku."
Armad ya haɗe gira, baiyi tunanin duk da haka Nostaljiya zata dage akan sai ta bishi ba. "Kwana uku na me?"
"Ka bani kwana uku zanje na tattaro duk wanda muke buƙata na taho dashi. Nayi alƙawarin baza kayi dana-sanin hakan ba. Kwana uku kacal. Dama kace kana buƙatar nemo ƙofar shiga duniyar aljanun ko? Kaga zai iya ɗaukar kwana uku. Idan bayan kwana uku banzo titin Bayajidda ba ka tafi, na yarda. Kayimin wannan alfarmar saboda Armanos!" Nan take ta fara kwalla tana roƙonsa.
"To." Armad ya faɗa a zuciya.
"Ka yadda?" Kafin Armad ya amsa tayi tsalle ta rungumeshi kamar wata (ƴar-baby). Sannan a wani yanayi mai ban mamaki tai sauri ta hau Ubbaru ta ɓace ko sallama bata yi wa Armad ba saboda tsoron kada ta tsaya ya canja shawara.
Shi kuwa Armad kai tsaye ya nufi bakin gaɓa. Ya ratsa ta cikin bango ba tare da tsaiko ba sannan yabi ta doron ƙasa na bakwai ya wuce zuwa titin Bayajidda. Abinda kowa ya sani shi ne a bayan titin Bayajidda akwai tafiya ta shekaru dubu ɗaya akan ingarman doki kafin a kai ga duniyar aljanu, duk da wasu suna ganin tafiyar bata wuce ta shekara ɗari biyar ba. Idan mai karatu bai mantaba Amraikugyu shi ne ya gina titin Bayajidda, farkon sakkowar mutane daga doron ƙasa ta farko zuwa ƙasashen ƙasa. Amraikugyu shi kaɗai yasan haƙiƙanin dalilin da yasa ya gina titin, abinda jama'a suka sani shi ne tunda aka gina wannan titi aka shinge aljanu da sauran hatsabiban halittu wanda haka ya baiwa duniyar mutane kwanciyar hankali. Idan kaga aljani to yana jikin bil'adama ne kamar yadda idan kaga dordor to akan bango ne ko kuma a sashin ikwatora.
Wani abu da mutane da dama basu sani ba shi ne bayan titin Bayajidda akwai katangar Bayajidda da Amraikugyu ya gina. Ita wannan katanga ita ce abu na gaba da zaka tarar bayan ka haura titin Bayajidda.
A dai-dai wannan lokaci Armad yazo gaɓar doron ƙasa na bakwai, yana kallon titin Bayajidda a gabansa. Titin dai an gina shi da sinadarin Yeniy da kuma wasu abubuwa wanda Armad bai sani ba. Launinsa baƙi ne amma akwai ɗigo-ɗigon ja yayi masa rawaya. Tsayin wannan titi ya ratsa dukkan doron ƙasar tun daga farko har ƙarshe. Akwai izza ta musamman a jikin wannan titi wadda aljanu basa iya ratsawa.
Armad ya miƙa ya tsallake titin ya danna kai gadan-gadan zuwa katangar Bayajidda. Babban abinda ya bashi mamaki shi ne yadda ƙasar wajen take da banbanci da wadda ya baro a baya. Ƙasa ce fara fat kamar an wanke, sannan kuma bata da kwari kai kace toka ce. Duk inda Armad ya taka sai kaga ƙura tana tashi. A haka ya ci gaba da tafiya har saida ya kwana yana amfani da Kabanshisu amma bai fara hangen komai ba. Alfijir ya keto, gari ya waye.
Gari na wayewa aka juya. Ranar farko ta ƙare a banza, saura kwana hamsin da tara.
***
Armad ya farka ya ganshi acikin ɗakin kurkuku a ɗaure cikin farar laya.
"A...Armad..." Wata murya ta kira shi cikin ƙinƙina.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
Nan take kalmomin suka maƙale a maƙogaronsa. Ya tuno duk abinda ya faru jiya da yadda ya gamu da Tarifil-fakta da wa'adin da aka basu, shi da Bihanzin da Ikenga.
Armad ya buga uban tsaki tare da miƙewa tsaye.
"Kaban'shisu."
Ya ɓace daga inda yake ya bayyana a wajen garin inda ya rankaya izuwa titin Bayajidda. Daga nan ya nufi Katangar Bayajidda cikin azama da sauri. Yana cikin tafiya rana ta faɗi dare ya kawo kai. Armad bai tsaya ba sai azama daya ƙara. Wajejen asuba ya fara hango alamun katangar bayajidda amma kafin ya ƙarasa gari ya waye an ƙara juyawa.
Kwana biyu sun tafi a banza, saura kwanaki hamsin da takwas.
**
Armad ya farka ya ganshi acikin ɗakin kurkuku a ɗaure cikin farar laya.
"A...Armad..." Wata murya ta kira shi cikin ƙinƙina.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
Nan take kalmomin suka maƙale a maƙogaronsa. A har kullum idan aka juya Armad yana ɗaukan daƙiƙu biyar kafin kwakwalwarsa ta dawo ya tuno abinda ke faruwa.
**
A wannan rana Armad ya ƙuduri niyyar ko ruwa bazai tsaya sha ba. Saboda haka ya ɗauki hanya cikin hanzari, babu abinda yake amfani dashi sai fasahar Kabanshisu. Daga ya ɓace sai kaga ya bayyana a can nesa sannan ya ƙara ɓacewa ya ninka.
Kimanin ƙarfe uku na dare ya fara hangen katangar. Idan ka lura an samu ci gaba tunda a jiya sai da asuba ta kawo kai ya fara gano ta.
Gabannin asuba Armad ya iso katangar inda ya iske abin mamaki. Girman katangar yakai zira'i dubu a tsaye, a kwance kuwa bata da iyaka domin baya gano ƙarshenta hatta da idanunsa na izza. Gaba ɗaya katangar an gina tane da sinadarin yeniy irin wanda aka gina titin dashi. Lokaci-lokaci zaka ringa hango zanen ɗalasimai suna haske a jikin katangar. Abin mamaki shi ne babu ƙofa ko taga a jikin katangar. Kai ka ce dama ba'ayi ta dan a shiga ba. Amma Armad yasan akwai ƙofa kawai dai sai ya neme ta. Matsalar ita ce bai san a ina ƙofar take ba; dama ko hagu? Idan ya ɗauki ɓangaren dama ya fara tafiya zai iya ƙarar da kwana sittin ɗin yana abu ɗaya bai cimma ƙofar ba, kuma wataƙila ƙofar tana ɓangaren hagu. Koda hagun ya ɗauka ya nufa nisan duk ɗaya ke. Babban tashin hankalin shi ne duk aikin da yayi, koda kuwa yakai ga ƙofar, safiya tana yi zai koma kurkukun Shal. Sai ya ƙara ɗakko hanya ya dawo, sannan ya maimaita.
Wannan ba abu bane mai yiwuwa ba, musamman ga mutumin da mutuwa ke jira.
Nan take Armad ya rufe ido ya faɗa kogon lissafin. Bayan ƴan mintuna ya buɗe idonsa. Babbar matsalarsa ita ce rashin sauri. Fasahar Kaban'shisu ta tsufa, yana buƙatar sabuwar fasahar sauri wadda zata iya ɗakko shi daga inda yake wayar gari wato Kurkukun Shal zuwa katangar Bayajidda acikin rabin daƙiƙa. Wataƙila da yana da irin wannan fasaha da Bihanzin bai cimma sa, domin kuwa a ɗan faɗansu ya gane cewa Kabanshisu ta tsufa. Ana buƙatar canji. Koda yake asalin fasahar kabanshisu sau ɗaya yake iya amfani da ita a shekara, daga baya ne ya gyara ta ta dawo haka. A yanzu ma zai ƙara gyara ta ta hau wani sabon matakin.
Nan take Armad ya nemi waje ya shiga halwar izza. Kafin gari ya waye idanunsa sun cika da sabon haske irin na sabuwar fasaha.
Ya ɗakko ɗalasimin kabanshisu ya zana shi a ƙasa. Sannan yayi masa wasu gyare-gyare wanda suka haɗa da gogewa da ƙarawa. Nan take dai-dai ƙasar wajenda ya zana ɗalasimin ta fara haske. Wata ƴar ƙaramar ƙofar Eycigan ta bayyana a saman wajen. Armad ya koma gefe yaci gaba da kiran ɗalasimai waɗanda da dama daga cikin waƙar-maƙabarta ya same su. Bayan ɗan lokaci ƙofar ta narke izuwa haske, sannan hasken ya dunƙule waje guda ya tunkaro ƙirjin Armad gadan-gadan. Saboda ƙarfin hasken sai da rigar Armad ta yage ta rududduge.
Yana taɓa ƙirjinsa Armad ya dartse haƙora saboda tsananin raɗaɗi wanda yafi na ɗan-bida. Amma abinka da jarumi ko uffan bai ce ba. Dukkan jikinsa ya sauya launi yai jajawur kamar garwashi. Sai da ya kwashe sa'a guda acikin wannan hali sannan jikinsa ya fara dawowa dai-dai. Bayan komai ya lafa sai wani ɗan tambari mai kama da Miyura ya bayyana a tsakiyar ƙirjinsa.
A dai-dai wannan lokaci safiya tayi, saboda haka kafin Armad ya ankara ya gwada sabuwar fasaharsa an ƙara juyawa. Kwana uku sun tafi a banza saura kwana hamsin da bakwai.
***
Armad ya farka ya ganshi acikin ɗakin kurkuku a ɗaure cikin farar laya.
"A...Armad..." Wata murya ta kira shi cikin ƙinƙina.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
***
Daƙiƙa biyar ɗin na cika, bai tsaya magana ba kawai ya kira sabon ɗalasiminsa.
"KABAN'ZISHU!"
Hatimin dake ƙirjinsa yayi haske. Kafin hasken ya ɗauke Armad ya ratsa daga kurkukun garin Ja, wanda yake gefen bango, zuwa titin Bayajidda wannan ɗaya ƙarshen. Sannan ya wuce kai tsaye izuwa katangar bayajidda. A wannna lokaci Armad ya ƙara hawa wani mataki wanda yana ji a jikinsa yafi da sauri sau dubu. Kai a taƙaice zai iya zuwa ko'ina faɗin ƙasa bakwai cikin ƙiftawar ido.
"Kaban'zishu!"
Yana rufe baki ya bayyana a ƙarshen katangar bayajidda ta ɓangaren dama. Ya dudduba bai ga ƙofa ba saboda haka ya juyo ɓangaren hagu.
"Kaban'zishu!"
A wannan lokaci a dai-dai ƙofar ya bayyana inda wasu manyan halittu masu kayika da dama sukai masa sallama irin tasu ta Shishirui.
"Wa nake gani haka?" Inji halittar dake tsaye a ɓangaren dama.
"Kamar jinin Áyubul-laisiy Al-wilbasiy." Inji halittar dake ɓangaren hagu, ɗaya daga cikin kayikansa guda shida suka kwale ido suka kalli Armad kamar suna ƙoƙarin gane shi.
Wannan masu tsaron ƙofa suna tsaye a dai-dai bakin ƙofar sun rufe ta da jikinsu. Ita kanta ƙofar takai zira'i sitttin amma sun shafe ta da jikinsu, baka ganin komai sai su. Kamarsu ɗaya sak sai dai banbancin kayikan kawai. Na daman kai shida gare shi, na hagun kuma biyar. Dukkansu akan wuya ɗaya. Jikinsu a shafe yake da baƙin gashi. Sunyi kama da samudawa ta fuskar girma amma kuma ba samudawa bane.
"Faɗi sunanka, bil'adaman farko." inji na daman.
Maimakon Armad ya basu amsa kawai ya taɓa ƙirjinsa ya ɓace ya dawo titin Bayajidda ya zauna yana jiran Nostaljiya. Yauce ranar da suka yi da ita.
Ai kuwa bai daɗe da zuwa ba wani jirgi mai matsakaicin girma ya bayyana akan titin Bayajidda. Daga inda yake yana iya jin izzar mutanen cikin wannan jirgi. Abin mamakin shi ne banda Babara da Lamarudu da Inara da Nostaljiya akwai Nusi da Cokali da Iliyasisi aciki. Sannan kuma akwai wani ƙarin mutun ɗaya wanda Armad bai taɓa tunanin haɗuwa dashi ba a wannan lokaci.
***
Babi na 254-255
***
Sannu a hankali jirgin ya zo ya tsaya a gabansa. Wannan ne karo na farko da Armad ya taɓa yin arba da jirgin ruwa mai tashi sama. Abin mamakin shi ne komai dake jirgin irin samfurin jirgin ruwa ne, tun daga gabansa har zuwa jela. An gina jirgin da itace na musamman wanda yake sheƙi duk da babu fenti a jikinsa. Gabansa yana da tsini da kuma wata ƴar toluwa a samansa ta zama. Idan ka hango jirgin daga sama zaka ga wani ɗan ƙaramin lambu da shukoki masu ƙawa akai, daga nan kuma akwai ƴar matattakala wadda zata kai ka ƙasa, ainihin cikin jirgin.
Tun kafin jirgin ya sauka Nusi ta ɓullo daga kan matattakalar ta futo waje tana hangen Armad. Jirgin na sauka ta rankayo da gudu ta rungume Armad a wani yanayi mai cike da ƙauna. Sannan daga bisani ta fara dudduba jikinsa tana so taga ko akwai ciwo ko rauni. Koda taga babu komai sai idanunta suka cika da fara'a, ta ƙara rungume shi. An kai wani matsayi wanda bata ɓoye soyayyar ta ga Armad ko kaɗan.
A wannan lokaci ne Armad ya fuskanci kowa ya tsaya yana kallonsu. Shi kansa saida ya ɗanji kunya, amma ko a jikinta. Nostaljiya kawai ɗauke kai tayi ta cije haƙora. Dole tana buƙatar ta jawa Nusi kunne.
A kusa da Nostaljiya akwai Babara, sai kuma Iliyasisi da Cokali, da Lamarudu da Inara. Daga can saman jirgin Armad yana jiyo takun wani mutun yana fitowa waje daga cikin jirgin.
Wannan mutun na ƙarasa fitowa ya tsaya a gaban jirgin inda yake hango Armad, shima yake hango shi. Armad bai taɓa tunanin ganin wannan mutun ba.
Lokaci na farko da suka haɗu da Armad a gasar Jinzidal ne, inda suka fafata. Sai kuma lokaci na biyu a yaƙin sarakunan Jinzidal. Yaƙin da yayi sanadiyyar mutuwar babansa Daljari da yayar Armad Hidaya. Abin mamaki, a wannan lokaci sun ƙara haɗuwa da Armad.
Idan ka lura sosai zaka ga wannan mutun ba wani bane illa... Rafiyan Nazara wanda akafi sani da yarima Niyashi.
Armad yayi murmushi ya ɗaga masa hannu. Shima Nazara ya ɗaga masa hannu yayi murmushi, rabin hankalinsa na kan Nusi.
A zahiri dama yarima Niyashi yana daga cikin wanda Armad yake son kawowa cikin tawagarsa. Ko ba komai zasu taimaka wajen yaƙar Bihanzin.
Nan take aka shiga gaishe-gaishe. Bayan an gama aka shiga jirgi aka kama hanya. Kowa ya jeru akan saman jirgin, cikin ɗan lambun da aka tsara domin shaƙatawa. A ƙa'idar kowacce tafiya ana buƙatar shugaba. A wannan tafiya kowa yasan waye shugaba ba tare da buƙatar ambata ba. Wannan tafiyar Armad ce, kowa ya shigo dole yayi masa biyayya.
Duk wanda ke wajen, harda Nazara, suka juyo suka dubi Armad suna jiran umarni.
Armad ya ɗanyi shiru kafin daga bisani ya ɗaga hannu ya nuna gaba. "A ɗau hanya!"
Yadda kasan jirgin sama haka suka tashi sama suka fara keta hazo. Iska tana ɗibansu ta gaba da baya. Bayan ɗan lokaci Nazara ya kira wasu ɗalasimai inda iskar gaba ɗaya ta ɗauke. Kai kace tsayawa sukai, amma ƙara zuba gudu suke.
Tunda Armad ne kaɗai baiga cikin jirgin ba suka jashi suka nuna masa.
Matattakalar da tayi ƙasa ta shiga cikin jirgin bata da tsayi sosai, kana sauka zaka iske ɗan ƙaramin tafki na wanka wanda aka kewaye da gilashi sannan kuma aka saka kifaye masu haske da kyawun gaske aciki. Daga gaba kaɗan akwai ɗakin karatu cike da littafai kala-kala. Daga daman ɗakin karatun akwai ɗakunan kwana na maza, daga hagu kuma akwai ɗakunan mata. Kowanne ɗaki da banɗakin sa. Sai kuma kicin wanda yake daga can gefe haɗe da ɗakin cin abinci. Lallai wannan jirgi ya tsaru. Tambayar farko da Armad ya fara yi ita ce: "A ina kuka samo wannan jirgin?"
Nazara shi ya samarda wannan jirgi ta hanyar fasahar sa ta sarrafa itace. Da mashin hannunsa yana iya samar da bishiya ko kuma itace kowanne iri yake so. Ta haka zai iya gina gida ko jirgi, kai koma meye da itace. Kuma itacensa yana da kwarin gaske. Akwai wanda idan ya haɗa hatta wuta bata cinsa. Akwai mara nauyi shafal-shafal wanda iska take iya ɗiba tayi sama dasu. A wajen gina jirgin yayi amfani da itace mai ƙarfi amma kuma mara nauyi, ta yadda iska zata iya ɗibansa ko ina. Sannan kuma ya saka izzarsa aciki tayadda zai iya sarrafa jirgin da kwakwalwarsa kaɗai, ba tare da direba ba.
Lallai Nazara ma'aboci fasaha ne, kuma a shirye yake ya ɗau fansa akan Bihanzin.
Babbar matsalar wannan jirgi ita ce sauri. Yana da sauri iya nasa amma kuma katangar tana da nisa, hatta Armad sai da ya ƙirƙiro sabuwar fasaha sannan yaje akan lokaci. Sabida haka aka shiga tattaunawa akan yadda za'ayi. Kowa yana kawo tasa shawarar.
"A ƙarawa jirgin sauri." Inji Inara.
Nazara ya amsa da cewa, "Iyakacin saurinsa kenan, musamman duba da cewa yana ɗauke da ƙarin mutane takwas."
"Idan na saka masa jini na zai ƙara sauri." Inji Nostaljiya.
Armad ya girgiza kai. "ba wannan zance, jininki ba mai bane."
"A saka masa farfela." Inji Inara. Dama can Inara babansa sana'ar tuƙi yake saboda haka yasan harkar sosai.
Nazara ya ce, "hakan zai ɗan ƙara masa sauri amma ba irin wanda ake so ba."
Ana cikin wannan kai komo Armad lissafi kawai yake yadda zai juya sabuwar fasahar Kaban'zishu ta ɗauki jirgin baki ɗaya ta kaishi bakin katangar.
Jim kaɗan ya tashi ya ɓace ya bayyana a wajen jirgin, inda ya fara zana wani ƙatoton ɗalasimi a samansa. Yana gamawa jirgin ya ɗau haske kafin daga bisani ya ɓace ɓat. Bai tashi bayyana a ko'ina ba sai a bakin katangar.
Wannan manyan halittu masu kayi ka suka tari jirgin. Kana ganin idanunsu kasan basu da niyyar bashi hanya.
"Ku faɗi dalilin zuwan ku wannan waje?" Inji Dandirshishirui cikin lafazi mai kama da aradu.
Armad ya gabato gaba zaiyi magana amma Dandir na ganinsa ya jada baya a firgice. "Ehmmm... wannan kamar jinin Ayubul-laisiy Al-basiy."
Ranbir ya ƙurawa Armad ido kafin ya matsa baya a tsorace. "Bana son wata alaƙa da masu wannan jini. Mu basu hanya kawai su wuce. Dama sashin su ne."
Dandir yai shiru kamar zaice wani abu yana kallon Armad da mutanen dake bayansa kafin daga bisani ya matsa ya bawa jirgin hanya.
Da Armad da na bayansa babu wanda yasan waye Ayubul-laisiy, kuma babu wanda yasan dalilin da yasa masu tsaron ƙofar suka tsorata. Amma muhimmin abun sun basu hanya, saboda haka suka wuce kai tsaye ba tare da tsoro. Ita kanta cikin ƙofar waje ne mai ban al'ajabi. Dukkansa da sinadarin Yeniy aka yishi, amma ko'ina ɗalasimai ne wanda aka rubuta da jinin halittu kala-kala. Tsubbace-tsubbace launi-launi. Kana gani zaka ji a jikinka ka bar duniyar mutane.
Armad, Nazara, Nusi, Nostaljiya, Lamarudu, Babara, Iliyasisi, Inara da Cokali.
Wannan mutun tara na tsaye acikin lambun suna kallon jirgin yana wucewa a hankali. Babban abinda ya ɗaurewa kowa kai shi ne a tsarin wajen babu ƙasa, babu wani abu da zaka iya takawa ka tsaya. Iya ganinka kawai duhu ne. Wannan yasa suka fara tunanin yadda zasu yi idan da babu jirgin.
Armad ne ya fara tambaya. "Nazara ka taɓa zuwa wajen nan? Ga dukkan alamu kasan zamu buƙaci jirgi."
Nazara ya gyaɗa kai ya ce, "na taɓa zuwa sau ɗaya. Duniyar aljanu bata da ƙasar takawa. Babara ma ya sani kuma shi ya bada shawarar a gina wannan jirgi."
Armad ya kalli Babara tare da ɗaga masa gira. Ga dukkan alamu abubuwa da dama sun faru a ƴan kwanaki uku da bayanan. Wanda suka haɗa da zuwan Nazara kurkukun Bango da kuma ɗakko Nusi daga sashin Ikwatora. Lallai yana buƙatar yaji bayani.
Koda ganin haka sai Nostaljiya ta amsa da cewa, "sanda na koma kurkukun bango akan Ubbaru tuni Nazara ya isa tare da Nusi. A lokacin Lamarudu da Inara sun shigo kurkukun lokaci, kawai saka su nayi acikin kurkukun yadda kowa acikinsu zai iya koyon fasaha aciki, bayan nayi musu bayanin duk abinda ya faru."
Armad ya juyo kan Nazara domin yaji yadda akai ya san Nusi harma ya ɗakko ta daga sashin ikwatora, abinda su Babara suka kasa.
Nan take labari ya dawo sabo. Nusi ta kwashe duk tarihin dake tsakaninsu da Nazara ta gayawa na cikin jirgin. Shi kuma Nazara ya kwashe abinda ya faru tsakaninsu da Ikenga ya gaya musu. Har yanzu akwai tambaya guda ɗaya da ba'a amsa ba.
"To wai kai Nazara meye alaƙar ka da Nusi? Yar'uwarka ce? Ta yaya ka santa?" Inji Nostaljiya.
Kowa acikin jirgin yana son jin amsar wannan tambaya domin kuwa da mamaki. Haka kawai ba dangin-iya bana baba ace Nazara ya ɗau nauyin Nusi da Cokali da Iliyasisi har suka girma. Dole akwai ayar tambaya.
Nazara yayi murmushi tare da juyowa ya kalli Nusi da wani irin kallo mai cike da ayar tambaya. A zahiri ita kanta bata san amsar wannan tambaya ba, abinda kawai ta sani shi ne Nazara ya basu gida, da ci, da sha, tun suna ƴan shekara shida a duniya har suka girma suka haɗu da Armad. Lallai tana buƙatar amsar wannan tambaya wadda a duk sanda ta tambayi Nazara sai ya ce mata ba yanzu ba. Wataƙila a yau zata ji amsa.
"Amsar wannan tambaya taku... ba yanzu ba."
Nusi taja dogon numfashi. Dama can tasan abinda zai ce kenan. Kuma hakan ne yasa abin yake ƙara ɗaure mata kai.
Duk da wasu daga cikin jirgin kamar su Babara sun matsa akan jin amsa, Armad bai damu ba. Kowa yana da sirrin sa, bai dace, kawai dan Nazara yazo wajensa, ya matsa masa ba. Akwai yiwuwar Nazara baya tare da Armad amma kuma yana tare da Nusi. Ita kuma Nusi tana tare da Armad. Sannan kuma koba komai burin Nazara ya ga bayan Bihanzin wanda hakan zai taimakawa Armad a shirinsa. Ta kowacce fuska Nazara babban taimako ne a shirinsa. Idan zai iya tunawa kafin Daljari ya mutu ya bawa Nazara asusun izzar tsohuwar daular Rafiyawa wadda Daljari ya mulka. Ita kanta wannan izzar zata taimaka wajen shirin da suke.
"Buri na na haura matakin gaba da Deba kafin wannan kwana sittin su ƙare. Kuma duk wanda yake cikin jirgin nan dole ya hau matakin Deba acikin wannan kwanaki." Inji Armad.
Nazara ya gyaɗa kai. "Lallai kayi gaskiya. Tun daga mutuwar baba Dalja nake bincike akan Bihanzin. Na gano cewa yana da mata mai suna sarkin-sarki wadda ke mulkin ɓoyayyiyar daular Elbis. Idan ka taɓa bi ta tsakanin doron ƙasa da ƙasa tabbas kabi ta cikin wasu garuruwa wanda babu kowa aciki. Duk wannan garuruwa suna ƙarƙashin mulkin wannan mata mai suna sarkin-sarki. Ance ƙarfin izzarta yakai na shi kansa Bihanzin, kuma ta taɓa gaba da gaba da Kuyurussa'ayi Ururu. A ƙarƙashinta akwai manya-manyan Deba aƙalla mutun goma. Sannan kuma ita take sarrafa gonar Ayrid da mangwaron Negrinki a ƙasashen ƙasa. Lallai ita ce ƙashin bayan rundunar Bihanzin kuma muna buƙatar yin maganin ta."
Armad ya numfasa ya ce, "ta kaimin hari ana tsakiyar gasar ruhin Deba. Tana iya amfani da kamalar-ruhi, naji ance ita ta ƙirƙiro fasahar sanyin-babban-sihiri. Amma duk da haka bata kai ƙarfin Bihanzin ba. Kamar yadda ka faɗa dole wani acikin jirgin nan ya tare ta idan an fito filin daga, idan ba haka ba ita kaɗai ta isa ta wargatsa mana shiri."
Nusi ta buɗe baki cikin ƙololuwar kafiya ta ce, "nidai ina gefenka, idan sarkin-sarki ta matso zanji da ita."
Kowa acikin jirgin ya juyo ya kalleta. Babu wanda ya ce uffan daga Armad har sauran sabida sun ga babu wasa a idanun Nusi.
Bayan ƴan daƙiƙu Nusi ta katse shirun da cewa, "banda ƙarfin mu akwai ƙarfin rundunar mu. Dole mu haɗa runduna ta musamman domin wannan yaƙin ba iya tsakanin mu zai ƙare ba. Bihanzin da Ikenga duk suna da runduna wadda zasu kira su shigar musu yaƙi amma bamu da ita. Dalilin da yasa nabi Ƙaraiƙisu a baya saboda na tattaro runduna ta ne daga garuruwa na amma tuni Ikenga ya gane hakan, ya toshe duk wata hanya da za'a iya fitarda mutane. A halin yanzu mutun dubu takwas kaɗai na iya fitowa dasu. Zaka iya cewa duk wani mahaluƙi daya rage a sashin ikwatora yana ƙarƙashin rundunar Ikenga."
"Akwai mutanen tsohuwar daular Rafiyawa da nasa kwamanda farin yashi ya haɗa. Amma ba kowa ne yake da ƙarfin halin ƙara fitowa yaƙi ba, duba ga rashin nasarar da muka samu a hannun Bihanzin. Duk da haka ina saran samun sadaukan izza aƙalla dubu goma." Inji Nazara.
Nan take shewa ta ɓarke acikin jirgin. Kowa na cike da fara'a. Samun mutun dubu goma ba ƙaramin abu bane.
Babara ya numfasa ya ce, "ban san haƙiƙanin lamarin ba amma lallai Taidara da Zaikid da Fatima suna da shirinsu, zaka iya cewa suna da rundunarsu ta kansu kafin Hidaya ta mutu. Kuma har yanzu wannan runduna tana nan."
Inara ya ce, "nima nasan ma'aikatan jirgi, abokan mahaifina wanda zasu iya taimakawa."
"Muna da mutun dubu biyar ma'abota izza a cikin kurkuku, ƴan tsohuwar ƙabilar Wilbafos." Inji Lamarudu.
Armad yaji daɗin ganin cewa kowa yana nasa tanadin. Domin hakan na nuna masa lallai kowa a shirye yake. "Nima ina son da zarar mun gama da duniyar aljanu na kaiwa sarki Maikiro'Abbas ziyara. Akwai baiti da Hidaya ta bari akansa. Wataƙila ya dawo ɓangaren mu."
A dai-dai wannan lokaci suka fito daga cikin ƙofar suka tsunduma cikin duniyar aljanu.
Abu na farko da suka tarar ya basu matuƙar mamaki.
***
Babi na 256-258
***
Sannu a hankali jirgin su Armad ya sauka a duniyar aljanu. Duniya daban da irin ta mutane.
Abinda ya basu mamaki shi ne babu doron ƙasa a wannan duniya. Jirigin na sauka ya fara lilo a kan iska. Armad ya leƙa ƙasa iyakacin hangensa amma baya hango komai sai rami da farin gajimare. A ƙasan gajimaren akwai hayaƙi mai duhun gaske, sannan kuma a ƙasan hayaƙin akwai iska abar kaɗawa da ƙugi da rugugi. A ƙasan iskar akwai duhu wanda bashi da ƙarshe.
Armad yana da tabbas duk wanda ya faɗa wajen sai dai a haifi wani. Kasancewar aljanu fuka-fukai ne da su basa buƙatar ƙasa. Hasalima koda basu da fika-fiki yanayin girabiti dake wannan duniya ya banbanta da na duniyar mutane. Zaka ga gida ƙatoto ko kuma wajen cin abinci amma yana lilo akan iska babu ruwansa.
[Girabiti - gravity]
Idan ana maganar gidaje abin a bayyane yake. Suna dira sukai arba da ƙatotuwar barikin soja a gindaye a bakin ƙofar. Sojijin aljanu launi-launi suna ran gadi. Wasu baƙaƙe, wasu farare, wasu kuma jajaye.
Sanye a jikinsu akwai yunifom ruwan ɗorawa mai ratsin baƙi.
Yawancin aljanu launinsu yana da banbanci da juna. Ba kamar mutane ba wanda zaka ce jinsin su kowa yana da kai da wuya da gangar jiki da ƙafafu da hannu. Aljanu zaka iya samun wa da ƙani, uwa ɗaya uba ɗaya amma ɗaya yana da jela ɗaya bashi da ita. Wani nada hannaye biyar wani nada huɗu.
Sannan kuma saɓanin a duniyar mutane da suke ɓuya, a duniyar su a bayyane suke. Kowa na kallon kowa.
Jirginsu na bayyana idanun aljanun dake gadin ƙofar ya juyo kansu. Sama da aljanu ɗari bakwai ne ke gadi a wajen, kai kace wata ƙaramar runduna ce.
Jirgin su Armad ya tunkari wajen aljanun ya tsaya.
Abinka da aljanu, maimakon su fara yi musu tambaya kawai sai suka zare takubbansu, kamar kura taga ragon layya.
Armad da mutanensa na tsaye a farfajiyar jirgin suna kallonsu. Hankali kwance.
"Akwai Rauhani, Muridi, Shaiɗani ko kuma Ifiritu acikin ku? Ko akwai Sarki-rauhani? Ko Sarki-ifritu, ko Sarki-shaiɗani, ko Sarki-muridi?" Inji Armad.
Aljanun suka ja tunga na ƴan daƙiƙu. Suka kalli juna kafin daga bisani su fashe da dariya. Babara da Nazara wanda sun taɓa zuwa wannan duniya kuma sun san sharrin aljanu suka zare makamansu tare da raɗawa Armad magana a kunne.
Wani baƙin aljani ya nuna Armad ya dubi ƴan'uwansa ya ce, "wai Sarki-rauhani take nema, ina mamakin girman kan ƙananun halittu."
Armad yai tsalle ya fito daga cikin jirgin ya tsaya akan iska ya fuskanci aljanun. "Gaba ɗayanku na siya. Indai akwai wanda ya fini sauri ko ya fini iya sarrafa takobi ko ya fini iya samarda walƙiya to zamu koma mu bar muku duniyar ku."
Kafin Armad ya rufe baki aljanu ɗari sun kewaye shi. Wasu ɗari suka ware fuka-fukansu sukai sama inda suka fara kawo masa hari ta sama.
Na ƙasan suma ba'a barsu a baya ba. Duk inda ka duba ƙawanyar walƙiya ce ko kuma dunƙulen wuta ko na ƙanƙara ko na ruwan zafi suke zuba. Kai harma da takubba na iska da walƙiya. Al'amarin ya juye izuwa ƙasurgumin filin yaƙi cikin ƴan daƙiƙu.
Armad na tsaye a tsakiya bai motsa ba. Sai da hare-haren suka rage saura ɗan taƙi su tadda shi sannan ya kira sabuwar fasahar sa.
"Zaren Mayu."
Nan take zarurrukan izza adadin yawan hare-haren sukai fitar burtu daga cikin miyurar sa suka dira akan fasahohin. Duk zaren daya taɓa hari sai kaga izzar dake ɗauke cikin harin ta zuƙe. Idan babu izza babu hari, kuma kowanne hari yana ɗauke da izzar sa. Iyakacin yawan izzar dake cikin hari iyakacin ƙarfin harin. Armad na zuƙe izzar dake cikin hare-haren suka ɗauƙe kamar ba'a taɓa yinsu ba.
Amma maimakon aljanun su ja baya sai suka ƙara azama wajen aikawa Armad saƙo. Duk inda ka duba hari ne. Armad na tsaye a gaban jirgin sa yana wasa da zaren izza. Aljani fari ko baƙi ko ja duk ƙananun aljanu ne, a matakin da Armad yake a yanzu bashi da lokacin ɓatawa akansu. Wanda yake hangen Ƙuyurussa'ayi da Bihanzin da Ikenga ina zai tsaya ɓata lokaci akan yaran aljanu.
Armad ya raba duk fasahansa zuwa gida uku: wanda suke ƙarƙashin miyura da wanda suke ƙarƙashin walƙiya da wanda suke ƙarƙashin takobi. Fasahar Zaran Mayu na daga cikin fasahan dake ƙarƙashin Miyura. Ita wannan fasaha aikin ta zuƙe izza; kama daga kan izzar dake cikin hare-hare zuwa izzar dake jikin ma'abota izza, mutun ko aljan.
"Zaren Damuna!"
Duk izzar da Armad ya zuƙa ta fasahar Zaren Mayu, maimakon ta shige miyura, sai ta shige zuwa tsarin ruhinsa kai tsaye. Sabida Armad ya gaji da kayan aro.
Zaren damuna wani ɗan tafki ne da Armad ya samar acikin tsarin ruhinsa a tsakanin jiya da yau. Acikin wannan tafki akwai ruwa mai danƙo wanda duk izzar da Armad ya zuƙa ta zaren mayu zata shige kai tsaye zuwa tsarin ruhinsa ta ɓoye acikin wannan tafki. A hankali har ya zuƙe ta zuwa jikinsa tabi jini. A yanzu zaka iya cewa Armad kawai farauta yake yana ƙara yawan izzarsa.
Kamar yadda aka sani Ƙassai suna da izza ƙasa da dubu. Jemai suna da izza ƙasa da dubu biyar. Jemai suna iya amfani da Negrinki. Deba maɗaukaka ne.
Izzar Armad tasa ta kansa banda ta aro har yanzu a dubu take. Amma cikin daƙiƙu kaɗan izzar sa ta tashi sama daga dubu zuwa dubu da ɗari uku.
Aljanun suka ƙara azama. Shi kuwa na tsaye yana jin daɗinsa. Duk inda ya motsa ƴan'yatsunsa sai kaga zare yana yawo. Sannu a hankali duk taurin kan aljanun suka gane cewa harinsu a banza yake tafiya. Maimakon Armad ya gaji ƙarfi yake ƙarawa.
Suna gabda canja tsari Armad ya aike musu da sabon ɗalasimi.
"Zaren Manyan Mayu."
Zarurrukan dake aiki akan fasahohinsu suka koma kansu. Kowanne aljani yaja tunga a inda yake ya tsaya cak, bawai dan suna so ba sai dan sun kasa sarrafa jikinsu.
Zaren Mayu ya zuƙe izzar fasaha, shi kuma Zaren Manyan Mayu ya zuƙe izzar ma'abota izza.
Nan fa izzar Armad ta ci gaba da yin sama.
1,500
1,600
1,700
1,800....
Mafi ƙanƙantar aljanin dake wajen Jemai ne. Sabida haka kamar wani rumbu Armad ya samu na izza. Domin shi a wajensa farauta yazo duniyar aljanu. Shi kuwa mafarauci baya raina nama.
2,100
2,200
2,300
2,400
2,500....
Wanda izzar sa takai dubu biyar kuma yake iya sarrafa Negrinki to ya zama cikakken sammai wanda ke gabda shiga Deba. To amma Armad yana da ɗan banbanci; tun yana shekara dubu yake iya sarrafa Negrinki.
Shaihunnai da dama sun yadda da cewa matakin Deba bashi da wata ƙa'ida. Wani zai iya kaiwa har matakin izza dubu hamsin amma bai shiga Deba ba. Wani kuwa zai iya shiga Deba a dubu goma. Ana ganin ƙarfin Negrinki da ƙarfin ruhin Debar da mutun ya zuƙa na daga cikin abinda yake taimakawa wajen isa Deba da wuri. Haƙiƙanin al'amarin shi ne babu wanda yasan gaskiya.
4,000
4,200
4,400
4,600
4,800
5,000...
Daƙiƙa hamsin da farawa amma har yakai matakin dubu biyar. A dai-dai wannan lokaci tsarin-ruhin Armad ya canja ya koma ruwan ƙasa. Izzar na ƙara yin sama tsarin ruhin na yin fari har saida ya dawo fari fat.
10,000
15,000
20,000...
Izzar na ƙara yin sama ƙarfin zaren mayu na ƙaruwa. Kai kace zarurrukan sun samu abinci ne. Sun ƙara kauri sun zama murtuka-murtuka. Ruruwa kawai suke suna gurnani kamar jan zaki.
20,000
30,000
40,000...
Lissafi ya canja. A yanzu izzar Armad da dubu goma-goma take ƙaruwa. Idanuwan Armad sukai jajawur kamar garwashi. Gashin jikinsa ya tattashi yai miƙe kamar ƙayar kifi.
Fatarsa tai jajawur tana fitarda wani haske mai tsoratarwa. Hasken yai sama ya haɗu da hasken watanni biyu dake sararin samaniya. Idanuwan Armad suka bayyana acikin watannin dake sama suna kallon ƙasa a wani yanayi mai nuna isa.
Shekaru 50,102.
A wannan lokacin tuni Armad ya zuƙe dukkan izzar wannan aljanu masu tsaron ƙofa. Amma bai ƙoshi ba.
Armad ya koma cikin jirgin ya nemi waje ya zauna ba tare da ya cewa kowa komai ba ya rufe ido. A hankali ya ringa kewaye wannan izza daya zuƙa izuwa kowanne saƙo da loko na jikinsa har saida tabi jikinsa.
Yana buɗe abinda ya fara cewa shi ne, "ina buƙatar izza."
Nostaljiya ta dafa kafaɗarsa ta ce, "shekaru nawa ka samu?"
"Dubu hamsin da kaɗan. Amma har yanzu bana jiyo ƙanshin Deba. Sannan ina buƙatar izzar da zan baku. Dole ina buƙatar izza mai ɗumbin yawa."
"Dubu hamsin acikin ƴan mintuna?! Kasan mai kake cewa kuwa? Wannan fa rumbun izzar wasu ƙasashen ne." Inji Nusi.
Babara yai dariya ya ce, "wannan shi ne dalilin da yasa ake tsoron ƙabilar wilbafos. Ana cikin faɗa suke ƙara ƙarfi. Iya daɗewar faɗa iyakacin ƙarfinsu. Basa gajiya kuma basa faɗuwa; iyakacin ƙarfin abokin gaba iyakacin ƙarfinsu."
Nazara na daga gefe yai gyaran murya ya ce, "ina da rumbun izza a waje na wanda baba Dalja ya barmin. Zan iya shiga Deba dashi kuma na taimakawa Nusi da wasu mutun biyu su shiga. Saboda haka kaji da kanka da sauran mutun huɗu da suka rage."
Armad ya gyaɗa kai.
Babara ya matso kusa ya ce, "nima ina ganin a cire ni a lissafi. Domin nima duk da ban zama cikakken Deba ba zan iya zama a kowanne lokaci. Inara, Cokali da Iliyasisi sune wanda zaka ji dasu. Babban abin kai muka fi damuwa dashi."
Armad ya ƙara gyaɗa kai. A zahiri ba wani jinsu yake ba. Hankalinsa da tunaninsa da lissafinsa na kan yaƙin dake gabatowa. Bihanzin, Ikenga da Kuyurussa'ayi sune a gabansa.
Armad ya ɗaga hannu ya nuna gabansu ya bada umarni a ci gaba da tafiya.
Bayan tafiyar awanni sai suka fara shigowa cikin gari. Kamar duniyar mutane anan ma akwai ƙofar gari da katanga wanda duk suke lilo akan iska.
Tuni labarin zuwansu Armad ya isowa masu tsaron ƙofar.
Duniyar aljanu daban data mutane. A wannan duniya mai ƙarfi shi ne sarki. Mara ƙarfi sai dai ALLAH ya isa. Zakai tunanin suna ganin su zasu far musu amma abin mamaki sai kawai suka zube sukai gaisuwa.
Aka buɗewa jirginsu ƙofa. Ba tare da tsoro ba suka shige ciki.
Mutane kamar aljanu kowa na harkokinsa. Wasu suna kasuwa wasu suna tafiya wasu suna hira. Tsarin gidajensu a rarrabe yake tayadda kowanne gida zaune yake da gindinsa kuma akan iska yana lilo. Duk inda suka wuce sai kaga ana kallonsu. Na farko dai su mutane ne, na biyu kuma sun halaka duk masu tsaron ƙofar garin.
Abu ne sananne akwai manyan aljanu ma'abota izza wanda ke gadin wannan ƙofa amma dukkansu sun halaka.
Armad da mutanensa suka shige kai tsaye zuwa cikin garin inda suka tsaya a bakin wani gidan cin abinci.
Akwai wani dogon turke wanda duk inda ka zaka a garin zaka gani. Shidai wannan turke ba kamar sauran gidajen yake ba, yana da tsayi harya sauka ƙasa ya shige cikin hadarin dake yawo a ƙasan duniyar. Ga dukkan alamu duk abinda zaka ajiye saika ɗaure shi a jikin wannan turke idan ba haka ba ya gudu.
"Rilya biyu kuɗin ajiya." Inji aljanin dake gadi a bakin wajen.
Aljanu da wani irin kwankwalati mai suna Rilya suke amfani maimakon ayrid.
Armad ya kalli Babara da Nazara domin su kawo agaji. Su kaɗai ne suka taɓa zuwa wannan duniyar. Wataƙila a zuwansu sun yi guzuri.
Nazara da Babara suka girgiza kai.
Armad ya kalli aljanin ya ce, "Bamu da kuɗi amma zamu iya biya da izza. Ka yadda?"
"Izza?" Aljanin ya zare ido cikin mamaki. Bayan ƴan daƙiƙu ya gyaɗa kai.
Armad ya tafa hannayensa ya kira ɗalasimi.
"Zaren Layya."
Nan take zaren izza ya tashi daga jikin Armad ya taɓa aljanin. Kwanakin izza ɗari suka tashi daga jikin Armad suka shige jikin aljanin.
Aljanin ya cika da mamaki amma bai ce komai ba. Ya karɓi jirgin ya ɗaure musu.
Suna shiga suka iske ƙaton ɗaki da kujeru da kanta. Aljanu na zaune ana shaye-shaye ana mai da zance. Suna shiga wajen yai tsit aka juyo ana kallonsu.
Armad da mutanensa suka wuce izuwa wani teburi da babu kowa akansa.
Shi kansa na kan kantar na zaune ya wage baki yana kallonsu ya rasa mai zaice.
"Ni fura nake so." Inji Armad.
"Nima haka." Inji Nusi.
"Nima haka." Inji Nostaljiya.
"Kunu wanda ya fara tsami." Inji Babara.
"Koko mai ɗumi da nama da tsinken sakace." Inji Cokali.
"Tuwo." Inji Iliyasisi.
Nan dai kowa ya faɗi abinda yake so. Bayan ɗan lokaci aljanin dake bayan kantar bai motsa ba. Armad ya daka masa tsawa. "Wai bakwa siyar da komai ne? Muna jira."
"Koko? Fura? Tuwo? Kunu? Menene su?" Inji aljanin dake bayan kantar. Ga dukkan alamu abincin aljanu da na mutane sun banbanta sosai.
"Amma muna da tsutsotsi farare wanda aka samar daga kwanannan kashin bil'adama. Muna da jan zawo mai sanyi da mai ƙanƙara. Muna da ruɓaɓɓan ƙashin kabari da ruwan ciwo mai wari. Akwai hanjin mage wanda aka haɗa da yawun tsohon kare. Muna da..."
Nazara ya daki tebur yai ashar. "Kut.. baku da abincin mutane? Taya zamu ci kashi ko tsutsa. An gaya ma a kabari muke?"
"Shekaru ɗaruruwa rabon mu da mutane. Bamu da abincin su." injin aljanin.
Armad ya waiwayo ya kalli mutanensa. A zahiri tunda ya mallaki fasahar Sikai bashi da buƙatar abinci, idan kaga yaci to saboda sha'awa ce kawai amma mutanen dake tare dashi ba haka suke ba. Idan basu samu abinci ba to akwai matuƙar yiwuwar mutanensa su mutu da yunwa.
"Amma akwai wasu wajajen cin abincin a can ƙasa. Wataƙila ku samu ajiyayyiyar fura ƴar shekara maitan."
"Wajen kwana fa?" Inji Nusi.
"Wajen kwana kuma? Saboda me zamu gina wajen kwana muda bama bacci?" Inji aljanin.
Ba shiri suka tashi suka ƙara gaba.
Har sun nufi bakin ƙofa farin aljanin yai ta maza ya tsayar dasu. "Wai da gaske kune kuka ƙarar da masu tsaron babbar ƙofa?"
Armad ya waiwayo ya kalle shi. Ga dukkan alamu labarin abinda suka aikata ya zaga ko'ina.
Ba tare da bashi amsa ba suka fice.
Jirginsu na ajiye a jikin turken da suka barshi. Suka nufi cikin gari domin neman abinci da wajen kwana.
Gidajen aljanu ba irin na mutane bane. Yawancin su kamar toluwar masallaci suke: sirara masu tsayin gaske ba faɗi. Kai kace ɗaki ɗaya ne kacal acikin gidan. Sai dai kuma kusan hakan ne; a gidajen babu banɗaki babu ɗakin bacci saboda basa buƙata. Kai hasalima da dama daga cikin aljanun basu da gida. Suna yawonsu ne akan titi saboda basa buƙatar bacci.
Ba jimawa magariba ta kawo kai. Dare ya fara yi. Babu abinci babu wajen kwana. Duk aljanin da suka gamu dashi sai kaga ya arce a guje. Babu wanda yake tsayawa yayi musu magana.
Bayan ɗan lokaci suka yanke shawara su shiga ɗaya daga cikin gidajen. Wataƙila sa samu abinda suke nema.
Kwankwankwan.
Armad ya kwankwasa ƙofar.
Kwankwakwan.
Kwankwakwan.
Kwankwakwan.
Bayan tsahon lokaci babu labari sai yayi amfani da yanayin izza ya leƙa ciki. A tsaye bayan ƙofar akwai mutun uku; mata da miji da jaririn aljani suna magana ƙasa-ƙasa. Dukkansu sun yadda kada a buɗe ƙofar, harda jaririn. Hasalima lissafin yadda zasu gudu suke.
Armad ya tura ƙofar a hankalin inda sukai arba da aljanun. Ai kuwa suna ganinsu suka arce suka jefar da jaririn anan.
Armad ya numfasa ya ce. "Wai aljanu matsorata ne dama?"
A haka dare yayi suna neman abinci da gurin kwana amma babu sa'a.
***
A dai-dai wannan lokaci dasu Armad suke neman wajen kwana a can wani ɓangaren duniyar aljanu yaƙi ake tafkawa tsakanin ɓangaren aljanu da ɓangaren Dordor.
Sama da mayaƙa miliyan ne ke cikin wannan filin yaƙi. Babu abinda kake ji sai ƙarar mazaje a yayinda rayukansu suke fita da ƙarar fashewar ababan fashewa. Da walƙiyar fasahai maɗaukaka.
Hankakan mutuwa ya yawaita. Jini ya kwarara ya rina hadarin dake duniyar izuwa jajawur.
Acikin manyan ƙasashen aljanu shida a yanzu wannan yaƙi yaci huɗu. Aljanun dake wannan garuruwa sunyi gudun hijira sun dawo garuruwan dake bayansu.
Kamar yadda aka bayyana a baya wannan yaƙi shi ne yaƙin da Hidaya tayi a duniyar aljanu. Tambayar anan ita ce mai ya kawo Hidaya wannan yaƙi? Menene alaƙar ta da yaƙin? Shi kansa yaƙin meye asalinsa? Mai yasa aljanu suke yaƙar Dordor duk da ba duniyar su ɗaya ba?
Wani zai iya cewa saboda fasahar aljanu da Dordor suke so su kwace to amma tuni sun kwace wannan. A yanzu yawancin mutanen dake ban ƙasa wanda ke amfani da fasahar aljanu an musanya musu da fasahar Dordor. Mai yasa har yanzu ake tafka wannan yaƙi?
A filin wannan yaƙi babu rago kuma babu wanda yake ƙasa da matakin Sammai. Sammai ne kawai da Deba. Zaɓaɓɓu mazajen fama ba irin matsoratan da Armad ya tarar a wancan gari ba.
Wani abu da Armad bai sani ba shi ne duk wani mai ƙarfi a jikinsa ya tafi filin yaƙi. Duk wanda ya gani a garin mata ne da masakai da masu lalura wanda baza su iya fita filin daga ba.
Wuta ce kawai take tashi a kowanne sashi na filin, kai kace a maƙerar Farkon Lokaci kake.
A ɓangare guda akwai sarakunan aljanu biyar wanda kowanne ke riƙe da ɓangare ɗaya na fasahar aljanu wato wuta, ruwa, iska, walƙiya da ƙasa.
Wannan sarakunan guda biyar sune aljanu mafi ƙarfi a ban ƙasa. Tunda aka fara yaƙin suke tsaye a filin dagar basu matsa ba, suna sahun gaba. Dasu aka ga jiya dasu aka ga shekaran jiya. Babu rauni a jikinsu amma kuma babu launin jinin da babu a jikinsu.
Sun kashe ƴan adawa har sun kasa ƙirgawa.
A dai-dai wannan lokaci wannan aljanu guda biyar suka tsaya cak suka kalli dai-dai saitin inda Armad ya shigo duniyar.
Bayan ɗan lokaci dukkansu suka gyaɗa kai. Lokacin da aka alƙawarta yazo. Sarkin da ake jira ya iso.
Comments
Post a Comment