Skip to main content

306-309

 Armad da Iluru na keta hazo sunyi shiru babu mai cewa uffan. Idanun Armad nakan dajin dake ƙasan su inda wasu irin bishiyu tafka-tafka masu fala-falan ganyayyaki suke ta rangaji sun rufe ko'ina, amma kuma hankalin sa na kan Iluru yana lure da duk abinda yake yi. Kai zaka iya cewa ko numfashi Iluru yayi a wannan lokaci Armad na sane dashi yana lissafi. 


Suna tafe tsahon lokaci a haka, shi Armad bai ƙara tambayar Iluru ina zasu ba, shi kuma Iluru bai cewa Armad komai ba. Bayan kimanin awa guda suka iso ƙarshen wannan daji, bishiyun suka fara rage girma a hankali har suka dawo ƴan ƙananu, sannan daga bisani yawan su ya fara raguwa. Har saida Armad ya fara ganin tsandauri wajen da babu bishiya akai, wato dai bishiyun sun koma tsilla-tsilla - wata nan wata can. Ana haka a hankali bishiyun suka ɓace. Tun Armad yana waiwayawa bayansa yana hangosu har suka ɓace ɓat ya daina ganin komai sai tsandauri da ciyawi. A hankali ciyawin suka ɓace, ƙasar ta bushe ta koma baƙa ƙirin kamar wadda aka saukar da azaba akai.


"Mun shigo lardi na biyu." Inji Iluru. "Daga wannan lardi sai babban bango sai kuma Ruwan Bagaja, daga nan zamu ɗauke hanya zuwa doron ƙasa na biyu." 


Armad kawai ƙura masa ido yayi yana ƙoƙarin tsintar aniyar sa ta hanyar amfani da fasahar Kamalar-ruhi amma baiga komai ba. Duk wasu alƙaluma suna nuna gaskiyar zancen Iluru, to amma zuciyar Armad taƙi amincewa. Sabida haka Armad bai saki jiki ba, a haka yaci gaba da bin Iluru cikin shiri. 


Bayan kimanin awa biyar suka wuce wannan busasshiyar ƙasa inda suka fara hango babban bango. Kamar yadda Armad yaji labari bangon jajawur ne wanda aka gina da jan tubali. Ya tashi sama ya tokare da sararin samaniya sannan a ƙasa kuma ya buɗe ya rufe ko'ina babu abinda kake hange saishi. Armad bai tambayi zancen ƙofa ba shi kuma Iluru bai bashi amsa ba. A haka suka isa. Suna zuwa bakin katangar Armad yaja ya tsaya.


Iluru ya juyo ya dubi Armad tare da haɗe gira cikin mamaki. "Kada ka cemin baka da fasahar da zaka iya shigewa ta cikin bangon nan?"


"Ina da ita." Inji Armad. 


"To muje mana. Kana ɓata lokaci kuma lokacin da bamu dashi."


Armad ya ƙara ƙurawa Iluru ido yana ƙoƙarin jin aniyar sa amma babu wani abu dake nuna cuta ko nufaƙa. Bayan ɗan lokaci ya gyaɗa kai, ya ce, "muje, shige gaba."


Iluru ya ɗora hannunsa akan jar katangar inda nan take kewayen dake gaban sa ya fara narkewa kamar an sawa kitse wuta. Kan kace meye wannan ya narke ƙofa ta samu a gaban sa. Ya shige gaba Armad ya bishi a baya. 


Abin mamaki kaurin katangar yafi ƙafa maitan. Saida sukai tafiyar minti goma kyan-kyan sannan suka fara hangen waje. Ai kuwa Iluru da gaske yake, ruwa ne iya ganin ka a wajen. 


Iluru ya shige gaba ya fara fita daga cikin katangar sannan Armad ya bishi a baya. Gangar ruwa ce makekiya iya ganinka. Girman ruwan kaɗai yasa kallo ɗaya kacal zakai masa kaji gabanka na faɗuwa. Babu gida gaba babu gida baya, iyakacin ganin ka ruwa ne mara iyaka. Iskar hunturu mai ratsa ƙashi na kaɗawa ko'ina. 


Wani abin mamaki wannan ruwa yana bada yanayin izza na musamman kai kace mutun ne mai rai ma'aboci izza. Lamarinda yasa Armad ya tsaya cak a sama ya ƙurawa ruwan ido yana jinjina yanayin izzarsa amma baiga komai ba saishi. Duk yadda yayi ruwa ne kawai amma kuma yana jin yanayin izza a jikin sa. 


Iluru ya juyo ya dubi Armad sannan ya kalli ruwan da yake kallo ya ce, "Armad Wilbafos, wannan ruwa da kake gani haka aka halicceshi kamar mutun shima yana bada yanayin izzar sa na musamman."


Armad ya ɗan haɗe gira amma baice komai ba. 


Bayan ƴan daƙiƙu Iluru ya dubi Armad ya ce, "Mu ƙarasa mun kusa zuwa."


Armad bai nuna alamar tsarguwa ba, juyawa kawai yayi yabi bayan Iluru. Saida sukai tafiyar rabin sa'a suna keta hazo akan gangar ruwan sannan kwatsam Iluru yaja ya tsaya. Armad ya bishi da kallo a nutse yana jiran yaji dalilin tsayawar su a tsakiyar ruwa wajen da babu gida gaba ko baya.


"Munzo." Inji Iluru.


Armad ya waiwaya gefe da gefe ya waiga baya ko zaiga wani abu amma baiga komai ba. Dama dai yasan babu komai a wajen (ta hanyar yanayin izzar sa) amma dai kawai ya ƙara dubawa ne sabida ya tabbatar wa Iluru baiga komai ba. 


"Munzo ina?" Armad ya tambaye shi yana ɓata rai. 


Iluru ya gyara tsayuwar sa ya juyo ya fuskanci Armad, ya ce, "kabarin ka."


Maimakon damuwa Armad murmushi yayi. "Kabari na? Hmm. Mai rai da nisan kwana ai baya buƙatar kabari."


Iluru ya canja tsayuwar sa, idanun sa suka kaɗa da azabar yaƙi, sannan ya fara tafa hannu ba tare da jiran Armad ba. Shi kuwa Armad yana tsaye yana kallon sa harya gama bai motsa ba. 


Idan ka kalli Iluru babu canji ko ɗaya a jikin sa duk da ya kammala kiran ɗalasiman sa, amma Armad yana ganin yanayin canji a jikinsa da idanunsa na izza. Duba ɗaya tak zaka ga zaren izzar Iluru ya ƙara jeruwa yayi kauri sannan kuma ya tattare a waje guda, ga kuma wani farin haske yana kewaya shi. 


Iluru ya nuna ɓangaren katangar da suka wuce ya ce, "wai da ƙoƙari nake na gayamaka kabar sahun masu rai tun sanda muka haura wancan katangar." 


"Hmm.." Armad yaja ɗan numfashi ya ce, "wato daman zancen an kama mahaifiyata da kakana ƙarya ce kawai ka shirya dan na biyo ka. Kana tunanin idan na biyoka zaka tarfa ni ka halaka ni sannan ka koma wajen mutane na suma ka ƙarasa su. Hakane?"


Iluru ya kaɗa kafaɗa. "Kakanka da mahaifiyarka an kamasu suna hannun Ururu, ko ka yadda ko kada ka yadda duk ruwan ka. Jawo ka nan da nayi dama na gani wadda zanyi amfani da ita na jefi tsuntsu biyu da tsakuwa ɗaya."


Armad yayi shiru yana tunani acikin ransa. Tabbas dabara ce mai kyau a wajen Iluru daya rabashi da tawagar sa, to amma shima Iluru ya raba kansa da tawagar sa, kaga kenan duk sunyi anko tanan ɓangaren. Kuma Iluru yasan Armad zai iya turawa mutanen sa saƙo ya gaya musu halin da ake ciki. Idan ma bazai iya turawa su Nusi saƙo ba sabida nisa ko kuma wani Tsarin tsafi to ai zai iya turawa Ayubu komai nisan dake tsakanin su, badan komai ba sabida Ayubu daga tsokar jikin sa ya halicce shi. Sai dai kuma kawai idan Iluru yana ganin zai iya hallaka shi cikin sauri kafin ya samu damar tura saƙo ya sanarda mutanen sa dake fadar Iluru halin da ake ciki.


Armad ya ƙara duban Iluru cikin matuƙar nutsuwa ya ce, "kace zaka jefi tsuntsu biyu da tsakuwa ɗaya, ban dani wane tsuntsun ka kama?" 


"Wannan bai shafe kaba?" Inji Iluru. A lokaci guda ya nuna Armad da ɗan-yatsa inda wani haske yai fitar burtu yai kan Armad.


Acikin hasken akwai manyan ƙusoshin mairakana na tsafi guda ɗari. Kowacce tsininta yafi na mashi. Suna juyawa suna haske suna ƙara gudu. Shi kuma hasken ya kewaye su ya dunƙulesu waje guda kai kace taron masu aka jera. 


Dunƙule hannu Armad yayi ya daki iska. Take wani basamuden hannun aradu ya fice daga hannunsa ya tari gaban ƙusoshin. Suna haɗuwa wata ƙara ta tashi. Iskar dake kewayen ta fara ci da wuta. Ruwan dake ƙasansu ya fara tafasa yana zaɓalɓala. Abin mamaki kawai sai ƙusoshin suka zame suka wuce ta cikin hannun aradun Armad suka nufi Armad. 


Armad sauri yayi ya buɗe taga zuwa duniyar Negrinkinsa domin aika wannan ƙusoshi can. Amma koda ƙusoshin suka matso kusa suna gabda shiga ciki sai kawai aka ga Armad yayi sauri ya rufe tagar. Cikin tsananin sauri da kwarewa ya gocewa ƙusoshin suka wuce. Amma kafin ya ankara sun shawo kwana sun juyo sun nufo shi ta baya. Ya ƙara dunƙule hannu ya aika musu da hannun aradu amma haka suka shanye suka ƙara afka masa ko gezau basu yi ba. 


"Armad Wilbafos!"


Armad ya kira ɗaalasimi mai sunansa. Nan take taga ta buɗe akan iska ya zira hannu ya finciko takobin sa ta Wilbafos daga ciki.


Nan take taurari huɗu reras suka bayyana kan iska a dai-dai tsinin takobin. Wani nauyi mai kama da nauyin duniya ya saukarwa ƙusoshin. Wani wawan rami ya bayyana a kewayen ƙasan Armad sabida nauyin takobin. 


Armad ya yunƙura yakaiwa ƙusoshin sara. Takobin sa ta haɗu da ƙusoshin. Nan take layin farko na jerin ƙusoshin wanda ya haɗa ƙusoshi wajen guda goma ya tarwatse ya rududduge. Su kuma ragowar ƙusoshin suka tsaya cak suka daina motsi sabida tsabagen nauyi. Armad ya ɗaga takobin sa ya ƙara kai musu sara. Takobin ratsawa tayi ta cikin su ta shige kamar tana yanka kabewa. Tana wucewa komai ya tarwatse. Ƙusoshin suka juye suka murmushe suka juye izuwa koren haske. 


Abin mamaki kawai sai koren hasken ya fara dunƙulewa a guri guda. Kafin Armad ya juyo hasken ya haɗe guri guda sannan ya rarrabe izuwa ƙusoshin, kowacce ta dawo dai-dai kamar ma babu abinda ya same ta. 


Armsd ya kaɗa takobin sa. Nan take taurarin suka rikiɗe daga huɗu suka koma bakwai. Abin mamaki kawai sai samaniya ta fara kaɗawa tana juyawa. Ƙarfin nauyin dake jikin takobin ya miƙe zuwa sararin sama lamarin da yasa sama ta fara rugugi. Kafin ma Armad yayi wani abu ƙusoshin sun rududduge sun murmushe. 


A dai-dai wannan lokacin aka ji dariyar Iluru, "haha... Ƙusoshi na na daban ne. A ganin ka dame nake haɗa su? Kana tunanin kawai dan ka kaɗe su sau ɗaya tafiya zasu yi?" Kafin ma Iluru ya rufe baki ƙusoshin sun ƙara haɗewa sun nufo kan Armad. A haka abu kamar wasa Armad yana gamawa da ƙusoshin su kuma suna dawowa saida aka shafe mintina biyar. Armad ya mayarda takobin sa cikin gidanta ya daina saran ƙusoshin. Suma kuma ƙusoshin kamar suna jiran suga mai zai aikata sai suka koma gefe suka tsaya suna kallonsa.


Armad ya haɗe gira ya dubi Iluru ya ce, "na kasa turawa Ayubu saƙo."


Iluru ya taɓe baki kamar wanda aka gwaɓawa magana. "Wai muna tsaka da fafatawar kake ƙoƙarin turawa mutun-mutumin ka saƙo? Gaskiya ka rainani."


Armad yaja da baya ya gyara tsayuwarsa sannan ya dubi Iluru ya ce, "Ina Ayubu? Bazan ƙara tambaya ba." Yana rufe baki ya ɗaga hannayensa sama ya haɗe su guri guda. Ya kira ɗalasimi a zuci sannan ya kira wani a bayyane, "Gidan Gizo-gizo!"


Koda faɗar haka sai kawai zaren izza ya bayyana a saman su yayi musi rumfa kamar tanti. Sannan ya buɗe ya fara girma. Kafin kace meye wannan ya haɗiye komai duk inda ka ɗaga kai babu komai sai zaren yana haske yana ɗisar da walƙiya kamar zaren azaba. Kamar abun bai isa haka ba sai kawai zaren ya fara sakkowa ƙasa yana sarƙewa da juna yana haɗewa yana samarda wani irin gida irin na gizo-gizo. Kafin kace meye wannan babbar saƙar gizo-gizo ta sauka ta rufe su. 


Zuwa wannan lokaci idanun Armad sunyi jajawur. Tuni ya gane abinda ke faruwa da kuma rashin kyautawar da Ayubu yake shirin yi masa.


Abin mamaki Iluru ko a jikin sa. Duban Armad yayi ya ce, "Idan baka jinsa kaga baza ka iya yi masa kamai ba kenan. Dama tsoron mu ace kana da wani shirin da zaka iya cimmasa duk da nisan dake tsakanin ku shi yasa muka kawo ka nan."  


"Wai, Iluru, kana tunanin na haɗa mutun-mutumin da hannuna kuma zai gagare ni ne? Gayamin, mai kuka yi masa alƙawari daya sa ya bijiremin? Mulki? Kuɗi? Izza? Mata?"


"Babu ko ɗaya." Inji Iluru. "Abinda kawai muka bashi shi ne rayuwa. Abinda kai kuma kake ƙoƙarin kwace masa. Idan zan iya tunawa da jikinsa kake ƙoƙarin amfani ka dawo da Hidaya, hakane?"


Armad ya nuna Iluru da ɗan'yatsa ya ce, "kuma duk da ka gayamin wannan kana tunanin zan barka ka rayu ka koma gida? Ko kuma zan bar Ayubu ya sha da abinda yake niyyar aikatawa?"


Armad ya dunƙule hannu yana niyyar afkawa Iluru amma Iluru yayi murmushi ya ce, "Nusi.."


Armad yaci birki ya kalleshi cikin rashin fahimta. "Nusi kuma? Kada ka sake ka taɓa ko gashi kwaya ɗaya a jikinta. Idan ba haka kuwa bayan na kashe ka saina haɗa da duk wani badenize dake ban ƙasa." 


"Nusi zamu aura masa mu haɗa masa da matarka Zahra." Iluru ya karasa magana a nutse. 


Wani dunƙulen abu ya daki zuciyar Armad sannan ya taso wuyan sa ya tsaya ya shake shi. Ba komai bane illa baƙin ciki. Ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa. Jikinsa na rawa ya tashi kan iska ya juya zai koma fadar Iluru. Amma a lokacin ruwan da suke kai ya fara girgiza yana ambaliya. A wani salo mai kama da almara wasu manyan gumaka suka fara tasowa daga ƙasan ruwan suna tasowa sama. Dole Armad ya nemi waje ya tsaya.


"Wannan shirin tsohon shiri ne, Armad. Tun daga sanda Shugaba Deniz Curu-curu ya ceto Ikenga yana yaro muke yin sa. Ikenga da magabantansa da sashin ikwatora kai har dama baƙar guguwa duk suna tare damu. Kayi haƙuri, amma ta kanka zamu taka mu haye doron ƙasa ta farko. Lokacin Denizawa da Oduduwa da Bayajidda yazo."


Armad ya daki iska yai karaji yai kururuwa. "Zaren Babbar Mutuwa!!"


***


ƁANGAREN NUSI.


Jikinta a sanyaye ta miƙe ta nufi ƙofar ɗakin ba tare data cewa Armad komai. Shima bai ƙara cewa komai ba kuma bai hanata fita ba. 


A hankali taja ƙofar ta rufe. Har ta fara tafiya ta ƙara juyowa ta kalli ƙofar tayi doguwar ajiyar zuciya. Zaiyi matuƙar wahala a gane meye acikin zuciyar Nusi duk da kuwa idanun ta na nuna alamun mamaki amma fuskarta a nutse take tana ɗauke da alamun kafiya. 


A haka ta tsaya a bayan ƙofar bayan ta rufe ta tsahon rabin minti kafin daga bisani ta wuce zuwa ɗakin ta. A wannan rana babu wanda ta gayawa komai. 


Washe gari da safe kowa ya hallara a falo zasu tattauna. Dukkan su suna zaune a kewaye da teburin cin abinci an jere musu kwanuka irin na jiya amma har yanzu babu wanda ya fara cin abincin. 


Nostaljiya ce ta fara magana. "Wai har yanzu Iluru bai dawo ba ne? Nifa ban yadda da mutanen nan ba." 


Nusi da Armad suka kalli juna, Nusi ta sunkui da kai kafin shima yaji kunya ya ɗauke kai. Nostaljiya ta kalli Armad sannan ta juya ta kalli Nusi sannan ta ɗauke kai bata ce komai ba. 


"Shirin mu yana nan." Inji Armad. "Iluru yace a kwana biyu zai dawo min da mahaifiyata da kakana. Idan ya saɓa alƙawari to magana ta tashi. Amma kafin nan mu bashi kwana biyun mu gani." Yana magana ya miƙa hannu kan cokalin dake gaban su ya fara yagar wainar da aka kawo musu yana sawa a baki. 


Cokali ya numfasa ya ce, "amma Iluru awa uku yace zaiyi, kuma gashi har gari ya waye bai dawo ba. Ni a gani na hakan ma saɓa alƙawari ne."


"Hakane, Cokali, to amma ka gane duk abin mai sauƙi ne. Dukkanin mu nan babu wanda ya yadda da Iluru sabida haka tuntuni muna cikin shiri. Sannan kuma kada ka manta ba'a banza mukai horo acikin kurkukun lokaci ba, da ƴan tsirarun ma'abota izzar da suke dasu acikin daular nan baza su iya kai mu ƙasa ba." Inji Inara.


Lamarudu ya gyaɗa kai alamun amincewa da maganar Inara.


Nostaljiya ta miƙa hannu ta riƙe Armad sannan taci gaba da cewa, "jiya dana dawo kayi bacci. Naje na kewaya cikin fadar domin na duba tunanin kuyangi da bayi da kuma wasu daga cikin sadaukan fadar amma babu wanda yasan mai ake ciki. Yawancin su basu yadda damu ba, kuma a zahiri babu wanda yake farin ciki da zuwan mu duba ga irin ƴan abubuwan da suka faru a tsakanin mu. To amma dai Bizaya ya basu umarnin kada wanda ya takale mu. Ina ganin zamu iya jira mu gani zuwa kwana biyun. Idan har a lokacin Iluru bai cika alƙawarin sa ba to alƙawari ya tashi."


Armad ya gyaɗa kai ya ce, "daɗin dadawa bana jin Ururu zasu halaka mama ko kuma farfesa Zaikid, da zasu yi hakan da tuni sun yi. Dole akwai abinda suke buƙata. Sabida haka a halin yanzu babu abinda zamu yi banda mu jira. Amma duk da haka Iluru yana damuna. Eh, na amsa masa idan ya kawo min iyayena zamu shirya, to amma maganar bata kai zuci ba. Bana niyyar saɓa alƙawari amma bazan ƙara haɗa kai da wani kamar Bihanzin ba. Sannan kuma bana so na karya asirin da akai musu domin hakan zai zamanto tufka da warwara kenan matuƙar ban san asalin tarihinsu ba da kuma dalilin da yasa akai musu asirin. Kamar yadda Iluru ya faɗa da bakinsa denizawan asali naman mutane suke ci, kada kuyi mamaki hakan shi yasa aka taru akai musu asirin. Amma tabbas dai da lauje acikin naɗi."


Koda Armad ya faɗi haka sai kowa ya shiga kogon tunani. Tabbas hakane. Karya asirin zai iya zamowa duniya matsala. Kuma bai kamata a matsayin Armad na wanda yake ƙoƙarin taimakon marasa ƙarfi ba ya zamanto kan gaba wajen janyo musu matsala, kawai sabida yana son ya dawo da Hidaya. 


Lamarudu yayi gyaran murya ya ce, "idan na fahimta muna da abubuwa kamar haka: na farko, karɓo mahaifiyar sarki Armad da kakan sa Zaikid; na biyu, dawo da Hidaya ba tare da mun karya asirin denizawa ba; na uku, fita daga daular nan lafiya ba tare da sun kashe mu ba."


Armad ya gyaɗa kai. "Haka." Sannan ya ɗaga ƴan-yatsun sa biyu na dama sama ya ce, "Kwana biyu. A kwana biyu rak zamu kammala waɗannan abubuwa. Yanzu saura kwana ɗaya da rabi."


Dukkansu suka amince. Kwana biyu kamar yau ne.


Nostaljiya ce ta numfasa ta ce, "yanzu kawai zaman jira zamuyi kenan har ya dawo?"


Armad ya girgiza kai. "A'a, yau ma zamu ƙara shiga gari mu zaga wataƙila mu gano wani abun. Duk wanda yake son zuwa ya shirya." Yana magana ya miƙe ya nufi ɗakinsa. "Nanda awa biyu zamu fita."


A wannan lokacin kowa yayi ɗakinsa domin shiryawa. 


Nostaljiya tana zuwa ɓanɗaki ta wuce domin yin wanka ta canja kaya. Banɗakin da aka tanadar mata bashi da girma sosai amma kuma komai daka sani na manya daga bututun ruwa mai amfani da izza zuwa kan bahon tangaran da ake kwanciya acikin sa ayi wanka duk akwai. Daɓen banɗakin shima na izza ne kuma duk abinda ya zuba ƙasa zuke shi yake yi, saboda haka ko rariya babu a banɗakin.


Kai tsaye ta cire doguwar rigar dake jikinta ta karata a jikin bangon banɗakin. Abin mamakin rigar na taba bangon sai kawai ta manne ta makale kamar an saka karo an manna. 


Ta juyo izuwa bahon wankan wanda yake bangaren yamma. Akwai wasu zanen dalasimai a samansa wanda Nostaljiya ta ɗora hannunta akai. Nan take ruwa ya fara bulbulowa daga cikin bahon. Gab take data cire kananun kayan dake jikinta ta fada cikin bahon taji motsi a bayanta. Cikin mamaki ta waiwaya wajen data ji motsin. 


Abin mamaki wata mace ce tsaye acikin banɗakin a bayan Nostaljiya. 


Nostaljiya ta hade rai. "Nusi, kuma meye ma'anar hakan...?"


Nusi ta ɗora hannu kan bakinta tana yi mata alamar tayi shiru. "Shushsh..." 


Kallon-kallo aka shiga tsakaninsu. Nusi tasan mai ya kawo ta to amma Nostaljiya na cikin wani yanayi: rabi haushi rabi kuma mamaki da kokwanton dalilin daya kawo Nusi banɗakin ta.


Takarda Nusi ta zaro daga cikin rigarta ta nunawa Nostaljiya rubutun dake kai.


Nostaljiya ta kara yamutse fuska tana kallon Nusi cikin rashin fahimta. 


Nusi ta daga takardar tana nuna mata. 


A hasale Nostaljiya ta fara karanta rubutun, a jiki Nusi ta sa: "akwai matsala. Ina tunanin wani abu ya faru da Armad."


Nostaljiya ta bude baki zata bata amsa amma Nusi ta girgiza kai sannan ta mika mata alkalami tana nuna mata gefen takardar wajen da zata rubuta abinda take son fada. 


Nostaljiya ta karbi alkalamin da takardar ta rubuta: "wai mai kike so kice?"


Nusi ta karbi alkalamin ta rubuta: "ina tunanin wannan Armad din da muka gama tattaunawa dashi ba Armad bane."


Nostaljiya ta hade gira ta rubuta: "Ban gane ba. Armad din ne ban sani ba ko kuma mijina ne bazan gane ba."


Nusi ta rubuta: "shi yasa nazo wajenki kai tsaye sabida na yadda duk duniya babu wanda yasan Armad sama dake. Wannan hasashe na ne kawai amma watakila wanda muka gama tattaunawa dashi yanzu Ayubu ne ko kuma wani mutun-mutumin na Armad amma dai ina tunanin ba Armad bane."


Nostaljiya ta jada baya a tsorace. "Eye..."


Nusi tayi sauri ta rufe mata baki sannan ta rubuta: "ko kin manta da yanayin izza ne? Idan mukai magana koma waye ya canji Armad zaiji. Tsorona kada iska ta dauki sautin ta kai masa. Ko kuma zaren izza ya kai masa. Shi yasa na biyo ki banɗaki."


Nostaljiya ta gyada kai alamun ta gane sannan ta karbi alkalamin ta rubuta: "amma mai yasa kike tunanin ba Armad bane? Kin san dai Armad din yanzu bana da bane, babu yadda za'ai yana tsaye ya bari Ayubu ko kuma wani ya canje shi. Kuma tayaya Ayubu zai bari a yiwa Armad haka, kada fa ki manta idan Armad ya mutu shima ya mutu tunda ruhi daya suke amfani dashi."


Nusi ta danyi jim tana tunanin abinda Nostaljiya ta ce. Bayan ɗan lokaci ta rubuta: "da wannan dan wannan amma dai ina so ki karanta tunanin sa ki tabbatar mana ko shi ne ko ba shi bane."


Nostaljiya ta rubuta: "hmmm.. tunanin Armad din zan karanta? Ai bazai yiwu ba, koda zai yiwu zai gane na duba tunanin sa. Kuma ni gaskiya har yanzu ban gamsu da maganar ki ba."


Nusi tayi ajiyar zuciya ta rubuta: "nima ban yadda ba da kaina ba hasashe ne kawai, amma kuma abu ne da zai iya yiwuwa duk da kuwa yana da wahala. Kiyi tunani, watakila lokacin da muka baro Armad a fada muka shigo aka canja shi."


Nostaljiya ta rubuta: "wai sai ki ringa cewa an canjashi kamar wani Kassai ko Jemai. Kinsan waye Armad amma kuma duk da haka kike tunanin zasu iya yi masa wani abu. Harma ace wai an sace shi an canjashi da wani ba tare da mun sani ba. Gaskiya zaiyi wahala."


Nusi ta rubuta: "hakane. To amma kiyi tunani. Bawai lallai karfi aka saka masa ba, watakila amfani sukai da mahaifiyar sa da aka ce an kama suka yaudareshi suka tafi dashi sai kuma daga baya suka zo suka musanya

shi da Ayubu."


Nostaljiya najin haka ta zare ido. A zahiri tasan Armad sarai kuma tasan yana da rauni indai abu ya haɗa da danginsa. Shi mutun ne wanda bai damu da sharrin da zai same shi ba indai akwai yiwuwar zai taimaki iyayen sa. Ko a baya sanda yana Kassai haka ya fito ya shiga duniya da izza shekaru hamsin da daya kacal.


Nostaljiya ta gyada kai. Lallai ta fara aminta da bayanin Nusi. Ta rubuta: "yanzu meye abinyi?"


Nusi ta rubuta: "ki yaudare shi ki duba mana tunanin sa."


Nostaljiya ta yamutse fuska. "Wacce irin yaudara kenan kike nufi?"


"Ba sai nayi miki dogon bayani ba, amma dai yau da daddare ina so kije a matsayin matarsa. Idan ya saki jiki dake saiki shiga tunaninsa bai sani ba."


Nostaljiya ta yamutse gira. "A haba dai, Nusi. Ana tunanin ba Armad bane kuma kike kokarin sawa na kwanta dashi. Meye yake damunki?"


Nusi ta dunkule hannunta ta cije hakora. Kana ganin idonta kasan akwai kafiya da shirin ko a mutun ko ai rai. "Saboda Armad... Saboda Armad har akwai abinda za'ace baza ki iya yi ba?"


Nostaljiya ta girgiza kai. "Ai Sabida kare mutuncin Armad din ne yasa bana son aikata hakan. Yaya kike tunanin zaiji idan ya dawo yaji abinda ya faru?"


Nusi ta ɗora hannunta akan kafadar Nostaljiya tayi murmushi mai cike da ciwon rai. "Nostaljiya, nima fa mace ce. Nasan mai kike tunani kuma duk da nace kiyi. Amma idan bakiyi abinda na gaya miki ba to akwai yiwuwar da Armad, dake, da ɗan da yake cikin ki, dani, da kowa da kika taɓa sani mutuwa zamu yi. Kiyi tunani amma kada ki dau dogon lokaci domin ko a yanzu da muke magana bamu san a halinda Armad yake ciki ba." Da wannan Nusi ta juya zata fice amma Nostaljiya ta riko ta. 


"Kada fa ki manta akwai yiwuwar duk wannan hasashen da muke karya ce kawai. Watakila da Armad din gaskiya muke tare bawai jabu ba."


Nusi ta juyo ta karbi alkalamin ta rubuta: "watakila, amma bana so nayi sanya wani abu ya sami Armad. Idan hakan ta faru bazan taba yafewa kaina ba." Ta dago ido ta kara kallon Nostaljiya sannan ta kara ɗora alkalaminta ta rubuta: "nidai duk amsar da kika samo da ita zanyi amfani. Idan kika ce armad ne to armad ne, idan kika ce Ayubu ne to Ayubu ne. Domin kuwa nasan baza ki taba yin abinda zaki cuci armad ba."


Da wannan Nusi ta juya ta fice daga banɗakin. Ita kuma Nostaljiya tsayawa kawai tayi ta kasa wankan domin kuwa ta faɗa cikin zuzzurfan tunani.




Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...