Babi na 184-188
***
Ɓangaren Zaikid
***
Zaikid na zaune a tangamemen falon gidan Wilbafos shi kaɗai idanunsa cike da ƙwalla. Yana zaune kan kujera mai lilo wadda ƙe haɗe da teburin cin abincin dake gabansa. Akan teburin akwai ƙaton tire cike da Tairí sannan a gefe kuma ga kwanon miya na tiriri.
Akwai kujeru guda huɗu dake kewaye da teburin. Wannan kujeru kowacce da suna akanta amma babu kowa akai. Ta farko na ansa Taidara, ta biyu ansa Fatima sannan ta Uku ansa Hidaya sai kuma ta ƙarshe ansa Armad. A saitin kowacce kujera akwai kwanon zuba abinci wanda babu komai aciki.
A dai-dai wannan lokaci idan ka kalli Zaikid zaka ga idanunsa sun cika da kwalla. Hasalima kwallar ta fara zuba daga idanunsa na hagu tana shiga cikin abincin dake gabansa.
Dukda cewa babu wani Wilbafos a gidan tsahon lokaci amma akwai ma'aikata wanda ke gidan suna kula dashi ana biyansu. Sai dai kuma tun shekarar da Armad ya fice nemowa mahaifyarsa magani gidan ya zama kamar kango domin Zaikid da Taidara da Hidaya duk basa nan. A saboda wannan dalili ma'aikatan gidan sunyi kwana biyu basu ji albashinsu ba lamarinda yasa da dama suka sallama aikin suka tafi.
A halin yanzu mutun ɗaya ne kacal ya rage wanda shima tsoho ne tukuf da sanda yake yawo. Hasalima a gidan aka haifeshi tunsu Hidaya suna nan. Anan ya girma, anan ya tsufa saboda haka bashi wani wajen zuwa inba nanba. Duk da ba'a biyansa ya gwammace ya mutu a gidan a binneshi a inda aka binne iyayensa. Wannan dattijo sunansa Kalman. Yasan Armad sosai kuma yakan yi masa a lokacin yana yaro. Asali mahaifin Kalman bawa ne wanda Taidara ya siyo ya ƴanta ya kawo shi gidan yake biyansa yana aiki. Saboda haka amana da aminci sosai a tsakanin Kalman da gidan Wilbafos.
A wannan rana kamar kullum Kalman ya fito da sanyi safiya yana gyara shukoki da filawowin dake katafaren gidan. A da can yakan fara daga bayan gidan wanda ya haɗa da katafaren lambu daya kewaye ko'ina amma saboda tsufa gashi kuma shi kaɗai ne yawanci yakan fara daga bakin ƙofar shiga ya biyo ta ƙatotuwar farfajiyar data haɗe ƙofar cikin gidan. Daga nan saiya wuce ɗakunan ma'aikatan gidan wanda suma sunkai ashirin a jejjere. Daga nan saiya ƙara haura barandar dake tsakanin ɓangaren ma'aikatan da kuma haƙiƙanin cikin gidan.
A kullum yana bin ɗakin Armad dana Zaikid da Taidara da Fatima dana Hidaya dalla-dalla. Ya share ya wanke sannan ya goge. Har ila yau ya yanke ciyayi da filawowi ya gyara komai. Ko suna nan ko basa nan a kullum sai yayi wannan aiki.
A yau ma haka yayi. Ya gama ko'ina ɗakin Hidaya ne ya rage. Yana tafe a hankali yana dagirawa ya isa. Yana isa bakin ƙofar ya fara da ƙatuwar kujerar da Hidaya ke zama tayi nazarin izza. Yana cikin goge kujerar ya fashe da kuka. Yayi kuka tsahon lokaci har saida hawayensa ya ƙare. Ya tashi yaci gaba da goge kujerar. A har kullum akwai rubuce-rubuce akan kukerar wanda akayi da yaren Wilburish wanda yake tsallakewa gudun kada ya goge abu amfani. A yau ma haka yayi.
Gabda zai tashi ya fara gyara filawowin dake gaban ɗakin yaji motsi bayansa ya waiwaya yai arba da farfesa Zaikid. Nan take ya faɗi ƙsa yayi gaisuwa.
Zaikid ya ce, "Kalman, kasan abinda Hidaya ta rubuta ajikin wannan kujera?"
Kalman ya girgiza kai ya ce, "a'a."
"WAƘAR-MAƘABARTA! Baitika ne daga cikin waƙar-maƙabarta."
Kalman najin haka ya fashe da kuka domin a matsayinsa na wanda yayi shekara saba'in da ɗoriya a gidan yasan kaɗan daga cikin ma'anar kalmar. Duk da bai san haƙiƙanin ma'anarta ba.
Zaikida ya dube shi ya ce, "akwai ragowar baitika da dama wanda suka ɓace acikin lokaci. Eyriron yayi ƙoƙari ya haɗa wannan baitika acikin littafin-takobi. Ragowar ya rage na Armad ya gano wannan waƙa wadda ake rerawa acikin maƙabarta. Kalman, zanyi tafiya izuwa wani waje mai hatsari bani da masaniya ko zan dawo a raye saboda haka na bar maka amanar wannan gida a hannunka. Duk sanda Armad ya dawo kaceasa kakansa Zaikid yana masa fatan alkhairi. Kuma kace masa idan ya samon Waƙar ina fatan ya saurari baitika na aciki koda sau ɗaya ne. Kaima akwai kyauta dana bar maka a falo ka shiga ka ɗauka.
"Idan da rabo wataran zamu haɗu."
Kalman ya fashe da kuka yasan bankwana Zaikid yake masa.
Zaikid ya bar gidan Wilbafos a shekarar 1861 BA domin aiwatar da wani abu wanda shi kaɗai ya barwa kansa sani.
Ɓangaren Fatima
**
Fatima Bayajidda ita ce mahaifiyar Armad wadda tun a farko ya bazama duniya nemar mata magani. Kamar yadda Babara ya bayyana Fatima tayi fama da Cutar Izza. Hanya sananniya da ake samun wannan cuta ita ce idan aka cutarda izzarka ta hanyar hari. Kamar yadda harin ruhi yake kawo cutar ruhi, kamar yadda harin tunani yake kawo cutar kwakwalwa, kamar yadda harin jiki yake kawo cutar gangar jiki.
Hanya ta biyu da ake iya samun wannan cuta ita ce idan mutun yayi ƙoƙarin shiga matakin Deba ta dole. Misali Deba bai mutu ba amma ma'aboci izza yaga bazai iya jira ba saboda haka ya danna kai ta dole.
Harin izza alama ce ta gidan Wilbafos sannan kuma Fatima ta daɗe da hawa matakin Deba ballantana ace tayi ƙoƙarin shiga Deva ta dole. Abin tambayar anan shi ne wanene ya sawa Fatima Bayajidda cutar izza?!
A dai-dai wannan lokaci Fatima na zaune a wani gidan kiɗan kwarya dake doron ƙasa ta biyu. Gidan hawa biyar ne a kwance kuma yana da faɗi ƙafa dubu. A kowanne hawa akwai mutane daga ƙabilu daban-daban wanda ke sauraren wannan kiɗan kwarya. Wannan kiɗan kwarya kiɗa ne na musamman domin a hawa na biyar ake yinsa amma har zuwa hawa na babu wanda baya jinsa kamar a kusa dashi ake.
Hawa na farko mutane ne gama gari. Na biyu kuma attajirai ne. A hawa na uku akwak sarakuna. A hawa na huɗu akwai Ƙassai. Amma a hawa na biyar babu kowa sai Sammai. Idan ka lura sosai zaka iya tsintar Deba acikin taron.
Mai kiɗan kwaryar yana hawa na biyar. A gabansa akwai shantu akwai kalangu akwai garaya sannan kuma akwai uwa-uba kwarya. A jikin kowanne abin kiɗa akwai hatimin izza wanda yake ƙarawa kiɗan armashi. Bayan mai kiɗan akwai masu amshi guda biyu. A duk sanda masu amshin sukai magana sai kaga zaren izza na fita daga bakinsu yana haɗuwa sautin waƙar. Hakan ne yasa wannan kiɗan da waƙar suke ratsa ruhi sama da duk wani abu da zaka iya tunani. Duk wanda ke cikin wannan gida ji yake yana cikin wata sabuwar duniya. Kamar wanda yake maye. Kai bari, zama ka iya cewa wannan waƙa da kiɗan kwarya sunfi duk wani kayan maye. Wannan waƙa ita ake cewa KIƊAN IZZA.
Ƙatoton ɗakin daya haɗa hawa na biyar yana ɗauke da mutane ashirin da biyar. Ɗaya daga cikinsu ita ce Fatima wadda ke zaune a ƙuryar ƙaton ɗakin. Abin mamakin duk mayen da wannan waƙa ke sawa idanun Fatima na buɗe kar. Ƙwalla ce ke zuba daga idanunta suna kwaranya. Bayan ɗan lokaci ta rufe ido ta shiga cikin WAƘAR-MAƘABARTA tana rera ƴan baitocin da take iya tunawa acikin zuciyarta a hankali.
##
Bayan tsahon lokaci mai waƙa ya kammala waƙarsa lamarinda yasa aka fara buɗe ido a hankali kowa yana dawowa hayyacinsa. Mai waƙar ya rabu da ƴan amshinsa ya nufo inda Fatima ke zaune.
Yana isowa ya ajiye shantun dake hannunsa a gefe ya zauna a kukerar dake gefen Fatima. Fatima ta ɗago kai ta kalleshi ta ce, "Shata Kil-zanki, nazo karɓar ajiya ta."
Mai waƙar wanda akafi sani da Shata ya fito ne daga ƙabilar Kil-zanki. Yana da doguwar fuska da saje siriri wanda ya bawa fuskarsa cikakkiyar kamala. Kayan jikinsa farare ne amma babbar rigarsa tana da ɗan duhu tayadda zata ɓoye takobin dake ɗaure a jikinsa. Ya numfasa ya ce, "lokacin rera waƙar-maƙabarta yazo kenan?!"
Fatima ta gyaɗa kai. "Tuni ɗan-tsoho da ɗansa Taidara sun bani baitocinsu. Hidaya da daɗe da saka nata baitin, baitina kaɗai ake jira. Bazanso ace ɗana yaji wannan waƙa babu kalamina aciki."
Shata ya miƙe ya ce, "minti ɗaya."
Cikin ƴan daƙiƙu ya ƙarasa wajen masu amshinsa yayi musu bankwana. Nan take suka fashe da kukan rabuwa. Shata ya juya yana cewa, "indai an haɗu kamar an rabu ne. Ku rabu dani naje na rubuta babbar waƙa kafin ranaku na su ƙare."
Fatima da Shata Kil-zanki suka tashi sama suka ɓace babu wanda inda suka nufa.
Taidara Wilbafos
***
Abin mamaki Taidara yana kan doron ƙasana farko yana tafe a nutse sanye da hular filani da doguwar riga fara. Ya ɗaure ƙasa tayadda duk taku ɗaya da yayi dai-dai yake da tafiyar shekara ɗaya. Duk sanda ya ɗaga ƙafa ya ajiye sai kaga ya keta birane da tsibirai da tsaunina. Ba jimawa ya iso tsakiyar dogon ƙasa farko. A sama idan ka ɗaga kai zaka hangi zaka hangi Maɗaukakiyar Fada wadda ke lilo akan iska akan bakan-gizo.
A gabansa akwai katafaren ginin babbar jami'ar Ururu wadda girmanta bazai misaltu ba. Kai tsaye Taidara ya nufi wannan jami'a. Yana isa wasu baƙaƙen hatimai suka fara haske a jikin ƙofar shigar suna ƙoƙarin hanashi shiga amma kafin wani ya ankara tuni Taidara ya shige ya ɓace. Ya bayyana acikin ginin shugaban wannan jami'a.
Ya kamata mai karatu ya sani cewa akwai sadaukai Sammai dubu saba'in dake gadin wannan jami'a. Dukkansu kowa gab yake daya shiga Deba sannan kuma sun karɓi horo na musamman daga jami'a mafi girma a duniya. Basu da aiki dare da rana sai gadin wannan jami'a, hatta ɓera bai isa ya shigaba saida izninsu.
Acikin wannan jami'a ake yaye maɗaukaka waɗanda ake sawa a hanyar mulki domin su mulki duniya. Duk wani mai kwakwalwa da sanin izza da sanin fannin fasaha a duniya yana cikin wannan jami'a. Kada a manta akwai farfesoshi sama da dubu goma acikin wannan jami'a wanda suka shafe ƙarnika suna koyarda harkokin izza.
Duk da wannan tsaro Taidara ya tsallake kowa ya shige ofishin shugaban jami'ar hankali kwance.
Akwai Deba a tsaye a bakin ƙofar yana gadi amma koshi baiji wucewar Taidara ba.
Ofishin yana da girma sosai amma duk filinsa an cike shi da saƙale-saƙale na izza da kayan tsafe-tsafe. Shugaban wannan jami'a shi ne waziri Tadiyraini Ururu wanda shi kansa ya daɗe da zama Deba. Yaji shigowar Taidara amma bai ɗaga kai ba yaci gaba da rubutu akan jar takardar dake gabansa.
Bayan ya gama ya ɗago kai ya dubi Taidara ya nuna masa takardar ya ce, "kalli kaga."
Ajikin takardar akwai sunaye barkatai.
Tadiyraini ya ci gaba da cewa, "Duk wannan sunayen jira suke su zana Deba. Da dama daga cikinsu izzarsu ta ƙare mutuwa zasu yi nan da ɗan lokaci idan bazu zama Deba ba. Nasan abinda ya kawo ka. Kana so gidan Ururu su ɗauke hannunsu daga harkar ruhin Deban Hidaya ko?"
Taidara bai damu da cewa ba'a bashi wajen zama ba ya fashe da dariya sannan bayan tsahon lokaci ya amsa da cewa, "mutuwar Hidaya ta samarda ruhin Deba wanda mutane suke nema. Amma kuyi sani ruhin Hidaya yafi ƙarfinku. Abinda ya kawo ni daban ne. Nazo ne akan zancen..."
Waziri ya katse shi da cewa, "waye a gidan Wilbafos kake tunanin zai iya kwace ruhin daga garemu? Bari kaji acikin Sammai masu neman shiba Deba akwai yarima Ƙaizadussa'ayi Ururu ɗan yarima Dumaƙisu. Koda kowa zai rasa ruhin ina mai tabbatar maka Ƙaizadu saiya sameshi."
Koda jin sai Taidara yai ajiyar zuciya ya ce, "Ƙaizadu? Shekararsa nawa? Ina ganin zasu yi sheakara ɗaya da ɗana Armad. Naji ance shi ne ɗalibi masa girman kwakwalwa da ƙarfin izza a wannan jami'a. Yana shekara bakwai ya kware wajen harin tunani dana izza dana ruhi dana jiki. Yana ɗan shekara goma ya gano sirrin Farar-laya da sirrin Allon-ruhi. Yana ɗan shekara goma sha uku ya haɗa mutun-mutumi mai matakin Deba. Yana shekara ashirin ya gano sirrin haihuwa wanda ya taimakawa dukkan ƴan ƙabilar Ururu hayayyafa cikin ƙanƙanin lokaci. Ƙaizadu ya kai wani mataki amma duk da haka bai kai matsayinda zai iya karawa da Armad."
Tadiyaraini najin haka ya daki teburin dake gabansa ya miƙe. "Nasan haƙiƙanin waye kai Taidara, kuma nasan waye ɗanka, kuma nasan shirin da kuke na samarda Waƙar-maƙabarta. Kana tunanin bamu shirya muku ba? Da sannu zaku gane kuskurenku. Muna sama muna jiranku duk sanda kuka shirya."
Taidara ya numfasa ya ce, "Nazo nan ne akan maganar Bihanzin Shishirui!"
Waziri najin haka fuskarsa ta canja. Duk wani annuri dya ɓace. Idan ka lura sosai akwai alamu na kokwanto akan fuskarsa. Ankai wani mataki wanda kowa yana tsoron wani abu dazai haɗa su da Bihanzin.
Bayan ɗan jimami waziri ya bawa Taidara kujera ya zauna sannan suka fara tattaunawa akan Bihanzin Shishirui.
***
Ɓangaren Armad Wilbafos
***
Sannu a hankali Nusi da Armad suka shafe wannan dare a tare. Armad ya kwashe dukkan abubuwanda suka afku tun daga gasar Jinzidal har zuwa yaƙin sarakunan jinzidal ya gaya mata. Ita ma ta gaya masa yadda ta zama sarauniya da yadda suka haɗu da Ikenga.
Armad ya dube ta cikin tsokana ya ce, "sarauniya Nusi-ya! Waya ganki akan karaga."
Nusi ta ɓata rai ta ce, "bawannan ba, Ikenga nake maka zance. Ina kyautata zaton shi ne Amraikugyu."
Armad yai shiru tsahon lokaci sannan ya ce, "Amraikugyu? Ikenga? Nayi alƙawari bazan ƙara bari wani nawa ya mutu ba! Nayi alƙawari bazan ƙara faɗuwa a fagen-fama ba. Nayi alƙawari sai naga bayan dukkan maƙiya na kafin naje ƙasa. Akwai yaƙi yana nan tafe. Zanyi shirin yaƙi, amma abokin karawa ta ba Ikenga bane. Kuyurussa'ayi Ururu shi ne abokin karawata."
Armad yana magana ƙarfin izzarsa yana shiga cikin maganarsa yana ratsa iska.
"Gashinka ya koma ja kamar wanda wuta take ci akai..." Nusi ta miƙa hannu ta shafa gashin kan Armad idanunta cike da soyayya.
Armad ya amsa da cewa, "gashi na zai ci gaba da zama jajawur tsahon shekaru har sai sanda na ɗauki fansa akan wanda suka kashe Hidaya."
Armad na faɗar haka ya miƙe. Nusi ta tashi ta tsaya a gefensa.
"Nusi, sai dai kiyimin haƙuri. Daga wannan rana murmushi zaiyi ƙaranci a fuskata. Zan fara shirin yaƙi daga yau har ranar ƙarshe. Idan kina ce baza ki bini ba sarautarki zaki koma bazan zargeki ba. Domin daga wannan rana dukkan haske zai ɗauke daga hanyata. Ina baki haƙuri amma bazan zama Armad ɗin da kika sani ba."
Nusi ta kama hannunsa ta riƙe amma bata ce komai ba. Amsarta tana cikin hannunta. Da jin yadda ta damƙe shi kasan baza ta rabu dashi ba ko a lahira.
"Idan zamu rayu mu rayu a tare, idan zamu mutu mu mutu a tare. Idan ka shiga wuta da ƙafar dama zan shiga da ƙafar hagu. Idan ka shiga yaƙi da takobi ɗaya zan shiga da takobi biyu. Idan kakai sara ta dama zankai ta hagu. Tare muka tare zamu koma. Abu ɗaya kawai nake roƙo a wajenka. Idan na mutu kada ka manta da sunan takobinka Nusi Kil-zanki."
Tana rufe baki ta zare takobi ta dawo bayansa ta tsaya a wani salo irin na bawa da ubangijinsa. Wannan ita ce Nusi Kil-zanki.
Zuciyar Armad ta kaɗa sosai amma ya kasa furta komai. Tsahon lokaci yana tsaye yana kallon gabansa kafin daga bisani ya tashi sama ya nufi wajensu Babara Nusi na biye dashi cikin tsaro. Hatta ƙuda bai isa ya tunkaro shi ba.
Nostaljiya ita ce ta fara jiyo yanayin-izzar Armad. Bata san dalili ba amma nan take jikinta ya ɗau rawa yana karkarwa. Yanayin Armad ya canja ba kamar yadda ta sanshi ba. A zuciyarta ta kasa tantacewa ko tana son gamuwa dashi.
Armad na isowa ya zarce wajenta kai tsaye. Su Babara jmhar sun taso amma da suka fuskanci inda ya dosa sai suka basu waje. Nusi tai jim na ƴan daƙiƙu amma daga bisani ta basu waje.
Bayan sun kaɗaice Armad yayi mata murmushi kamar yadda ya saba. "Nosti..."
Har Armad ya fara magana Nostaljiya ta katseshi. "Duk abinda ya faru ni ce. Ko kasheni kayi bazan zargeka ba. Da ban kawo ka garinmu ba da haka bata faru ba. Da Hidaya bata...."
Armad ya katse ta. "Dani dake babu wanda ya taɓa tunanin Bihanzin zai zama haka. Kema daya samu damj da tuni kina lahira saboda haka baki da abin zargi a wajena kuma bana son ki ƙara tayarda maganar."
Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma Armad ya ɗora ɗan'yatsansa akan bakinta. "Nace bana son jin maganar ya isa haka. A halin yanzu bamu da kowa sai kanmu. Duk duniya maƙiyanmu ne kina ganin zamu iya faɗa a tsakaninmu? Abu na farko da nake so dake shi ne kisa rigar sanyi."
Armad ya ciro rigar jikinsa ya ɗora mata. Nusi na can gefe ta hangi abinda ke faruwa. Fuskarta bata nuna komai ba amma zuciyarta kawai tafasa take itama bata san dalili ba.
Nostaljiya kuwa kasa magana tayu kawai ta tsaya fuskarta tayi jajawur da kunya.
"Abu na biyu da nake so dake ina son ganinki a ɗakina nanda minti goma."
Armad na faɗar haka ya wuce gaba. Nusi da Babara da Lamarudu dasu Iliyasisi suka bi bayansa. Lamarudu ne kan gaba inda ya kaisu dutse mafi girma a wajen. An fafake cikin dutsen inda aka samarda ƙatoton kogo. Cikin kogon an ƙawata tashi da shimfiɗu da kilishi kala-kala tayadda yayi matuƙar kama da fada. Akwai karagar mulki daga ƙuryar kudu. Lamarudu yakai Armad kan kujerar.
Mutane shida wanda suka haɗa da Nusi, Iliyasis, Cokali, Babara, Lamarudu da Nostaljiya duk sun hallara. Kowa ya kama waje suka jere a gaban Armad.
Armad ya fara da gabatarda kowa kafin daga bisani ya wuce kai tsaye dalilin taron.
"Daga wannan rana ta yau na saka ɗan'ba wajen share cinikin bayi a duniya. Idan ka taɓa cinikin bayi kamar ka taɓa doron ƙasa na farko ne haɗe da sarakunan Jinzidal saboda haka duk wanda yasan yana da sauran tsoro ko kuma bashi da wannan ra'ayi yanzu ne lokaci daya kamata mutun yayi magana. Babu takura kuma bazan ga laifin duk wanda ya yace haka ba."
Armad yai shiru yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya amma babu wanda yayi tari sabida haka yaci gaba da jawabi. "Ku shidannan dake ɗakinnan na naɗa ku masu bani shawara, waziraina na musamman. Abinda muke buƙata shi ne runduna ta musamman. Rundunarda zata iya tunkarar dukkan maƙiya ba tare da tayi gezau ba. Anan bamu da Deba ko ɗaya sannan kuma dukkan mutanen dake tare damu basu kai dubu biyar. Da dama daga cikinsu Ƙassai ne. Idan muka tunkari maƙiyanmu a haka bamu da alamun nasara.
"Daga wannan rana zamu fara shirin yaƙi. Neman magoya baya, ƙarfafa izza da samarda sababbin fasahohi da makamai, ƙoƙarin zama Deba ta kowanne hali. Idan kowa a ɗakinnan zai zama Deba sannan mu sam rundunar Sammai dubu ɗari zamu fita yaƙi. A halin yanzu ina da shiri a zuciyata amma kowa ya faɗi shawararsa."
Babara ne mutun na farko daya fara magana. "Shugaba Armad, ina ganin akwai duk abinda muke nema acikin Tsohuwar daula wadda ka tura ni ciki a shekarun baya. Bazan ce komai ba domin yafi kyau ka gani da idonka ya shugabana."
Lamarudu wanda yaga abinda ke cikin tsohuwar daular da idonsa ya gyaɗa kai ya ce, "lallai sarki Armad zakai farin ciki da abinda ke ciki."
Nusi ta numfasa ta ce, "koma meye acikin wannan Tsohuwar daula da kuke zance bana jin zai kai matsayin sashin ikwatora baki ɗaya da miliyoyin mutanen dake ciki da dukiyoyinmj da fasahohinmu. Lallai ina ganin Armad kamata yayi ya fara da kama sashin Ikwatora. A kwanaki kaɗan masu zuwa akwai zaɓe da za'ayi, ta hanyar wannan zaɓe na zama sarauniya. Lallai idan Armad ya gwada shima zaiyi nasara."
Cokali ya gyaɗa kai alamun amincewa.
Iliyasis ya ce, "duk da ban taɓa zuwa sashin ikwatora ba amma na daɗe inajin labarinsa. Sannan kuma wannan Tsohuwar daula baza ta gudu ba. Ina ganin mu fara da can."
Nostaljiya tayi kasaƙe, akwai abinda take son faɗa amma har yanzu ta kasa sakar jiki. Armad ya daɗe da gano ta saboda haka ya ƙura mata ido. Baice komai ba amma tasan abinda yake so saboda haka ta numfasa ta ce, "akwai littafi dana taɓa gani a ɗakin karatu na Jekis wanda yayi magana kan ƙabilu da aka ɗaure cikin kurkukun nan. Akwai aƙalla ƙabilu hamsin. Bansan a ina suka ɓoye ba domin zaiyi wuya ace dukkansu sun mutu. Idan kuwa suna cikin kurkukun nan to lalle mu nemosu domin da dama an ɗauresu ne sabida ƙin cinikin bayi. Saboda haka zamu samu goyon bayansu cikin sauƙi. Saɓanin mutanen ikwatora wanda kowa yake rasuwarsa cikin jin daɗi, basu san wani abu cinikin bayi ba saboda haka baza su bada haɗin kai cikin sauƙi ba koda kuwa kaci zaɓen. Waye zai ydda yana zaune cikin zaman lafiya a kawoshi yaƙin da bai shafeshi ba?"
Nan take Nusi ta daka mata harara. A fili babu wani ɓoye-ɓoye ita ma ta rama. Babu wani abin sirri a soyayyar da Nusi ke nunawa Armad. Ita kuma Nostaljiya tana ganin mijinta ne. Armad na ganin abinda ke faruwa yaji ciwon kai. A zahiri Armad bashi wata alaƙa da sashin ikwatora. Mutane ne wanda ke zaune lafiya babu ruwansu da Ururu saboda haka baya son ya zuƙosu cikin wannan faɗa wanda zai jawo asarar miliyoyin rayuka. Amma kuma yana buƙatar mayaƙa sannan kuma ba lallai ya samu isassu ba acikin kurkukun.
Babban abin shi ne da damar zaɓar Nusi akan Nostaljiya ko kuma Nostaljiya akan Nusi.
Babara ta fuskanci abinda ke faruwa saboda haka yai gyaran murya ya ce, "kowa ya gayawa sarki Armad shawararsa. Yanzu lokaci ne da kowa zai tafi a bawa sarki dama ya zaɓi abinda yafi."
Babara ne ya fara miƙewa ya fice. Iliyasis da Cokali da Lamarudu suka bi bayansa. Nusi da Nostaljiya babu wadda ta motsa. Armad ya tashi ya fice ya barsu a wajen. Yana da cikakkiyar masaniyar ko ƙiyama mata sayi kishi, shirin yaƙinsa bazai hana su komai ba.
##
Armad na futowa ya nemi Lamarudu da Babara suka gaya masa abinda ke cikin Tsohuwar-daular. Bayan yaji haka Armad ya yanke shawarar abinda zaiyi amma kafin nan akwai abinda yake so ya aiwatar.
"Lamarudu wajennan na horo da nayi amfani dashi a baya yana nan?!"
Lamarudu ya gyaɗa kai, "yana nan kuma tuni muka gyarashi dominka."
Lamarudu yakai Armad wajen dutsen daya rufe ƙofar shiga filin horon. Ya zana hatimi akan dutsen lamarinda yasa dutsen yayi haske sannan ya tashi sama ƙofa ta bayyana a bayansa. Ta cikin ƙofar Armad yana hango duwarwatsu da dazuka. Ya danna kai ciki kai tsaye. Babara da Lamarudu sun san Armad yana buƙatar fili saboda haka babu wanda ya bishi acikinsu.
Akwai fasahohi da dama da bincike-bincike akan sihiri da Armad yake so yayi amma duk wannan daga baya ne. Babban abinda yake cizonsa shi ne MOSTIN LITTAFIN-TAKOBI da yake ji acikin ruhinsa tun bayan sanda ya farkarda Negrinkinsa. Wannan motsin yana da banbanci matuƙa da irin motsin da yaji a baya lokacin gasar Jinzidal. Yana jin motsin kuma yana jin tafiyar littafin acikin jininsa. Take Armad ya juye izuwa walƙiya sannan ya danna hannunsa cikin ƙirjinsa dai-dai inda yake jin motsin.
Abu kamar wasa sai gashi Armad ya zaro littafin a hannunsa kamar zare gashi acikin mai. Armad ya tuna da irin wahalar da Uznu yasha wajen ƙoƙarin zaƙulo littafin amma ya kasa. Nan take ya gane cewa littafin shi ne yake so Armad ya ganshi bawai Armad ne ya nemo shi ba.
Take Armad ya haye kan wata bishiyar kwakwa ya samu reshe ya tankwashe ƙafa ya fara karatu. Takardun cikin littafin ruwan ɗorawa ne amma rubutun da jini akayi shi. Saboda daɗewa jinin ya koɗe matuƙa izuwa baƙi-baƙi. Kowanne shafi baifi girman tafi ba amma akwai kalmomi a rubuce a ko'ina ajiki. Bangon littafin fari fat da zanen takobi guda ɗaya. Akwai hasken tsafi ajikin bangon wanda yasa duk da daɗewa littafin bangon bai koɗe ba ko kaɗan.
Yaren dake cikin littafin shi ne yaren dake jikin Miyurarsa saboda haka Armad bai iya gane haƙiƙanin mai ake cewa ba duk da kuwa yana iya karanta baƙin.
Amma bisa mamaki yana gamawa karantawa sai yaji murya acikin kansa tana cewa, "SUNANA ALDAIMA WILBAFOS. NA SAMARDA FASAHA WADDA DUK WANI ƊAN ƘABILAR WILBAFOS ZAI IYA SAKA ILMINSA DA FASAHARSA ACIKIN TASKAR TSAFI KAFIN YA MUTU SABODA JIKOKINMU SU GADA. WANNAN TASKA ZATA RAYU HAR GABAN ƘARSHEN DUNIYA INDAI AKWAI RAGOWAR WILBAFOS A DORON ƘASA. IDAN KA SAMU WANNAN FASAHA KAYI SANI CEWA SUNANTA WAƘAR-MAƘABARTA. KAYI ADDU'A GA DUK WANDA YABAR MAKA BAITI ACIKI. NI DAI GA NAWA BAITIN...."
Nan Armad yaga duniyar ta juye masa baki ɗaya. Ya tsinci kansa acikin Tsarin-ruhinsa. Wani ƙaton littafi mai ɗauke da fasahar sarki Aldaima da duk wata fahimtarsa akan izza ya bayyana. Take Armad ya hau karatu. Yana cikin haka ya ji wata muryar ta ƙara bayyana.
"SUNANA HIDAYA WILBAFOS, GA BAITI NA. INA SA RAN ƘANINA ARMAD SHI NE ZAI KARANTA WANNAN BAITIN KUMA AKWAI ABUBUWANDA NASA NE KAƊAI SABODA HAKA IDAN BA SHI NE BANE KADA KA WUCE BAITIN FARKO. HIDAYA."
Nan take ƙaton littafin Hidaya ya bayyana acikin Tsarin-ruhin Armad. Take Armad ya ajiye littafin Aldaima ya buɗe nata. Kafin ya ƙarasa buɗewa yaji wasu muryoyi da yawa sun fara shigowa.
"SUNANA EYRIYON WILBAFOS, GA BAITI NA..."
"SUNANA ALƘALI WILBAFOS, GA BAITI NA..."
"SUNANA BANTUL-BAITA WILBAFOS, GA BAITI NA..."
"SUNANA AZARA'ILU WILBAFOS, GA BAITI NA..."
"SUNANA SHÁWEE WILBAFOS, GA BAITI NA..."
Miliyoyin muryoyi kowacce da baitinta da kuma littafinta. Cikin ƙanƙanin lokaci Tsarin-ruhin Armad ya cika da ilmi na shekaru miliyoyi. Babban abin al'ajabin shi ne da Armad ya buɗe littafi sai duk ilmin ya shige kansa cikin ƴan daƙiƙu kaɗan. Kan kace meye wannan Armad yasan komai a jiya da yau da gobe da shekaran-jiya.
***
Babi na 189-192
***
Shekarar 14 BA
Doron ƙasa na farko
Garin Kaldizmi
Babban ɗakin-karatun Ururu
Ɗakin karatun ya girmama wajen ƙayatuwa. Anyi ginin da jan dutse mai ɗaukan ido. Kowacce katanga faɗinta yakai kamu tara. A tsaye kuwa ba'a hango ƙarshen ginin. Faɗinsa yakai tsayinsa sannan kuma ko'ina acike yake da littafai daban-daban. Wani irin yanayi na daɗewa da shekaru na tashi daga jikin ginin sabida yawan shekaru.
Acikin wani ɗakin karatu Uznu Ururu ne ke zaune yana nazari. Kasancewar ɗakin da yake yana cikin keɓantancan waje babu kowa a wajen sai shi. Kafin yaƙin duniya na farko Uznu ya shafe yawancin shekarunsa na samartaka cikin wannan ɗakin karatu yana bincike kan fasahohi da izza.
Watarana yana zaune yana nazari da yammaci sai waziri Tadiyraini ya shigo. Yana shigowa yayi wajen Uznu yana cewa, "Ko wata ɗaya ba'ai da gama yaƙin duniya na farko ba. Da gudunmawarka mun rusa daular Wilbafos mun tabbatarda rukunan Amri da Jinzidal. Idan ka ɗauke masu gine-gine kowa hutawa yake yana shan iska amma maimakon haka a kullum kana cikin wajennan kana nazari, ko meye dalili?"
Uznu yaja dogon numfashi ya dubi waziri ya ce, "bazan iya amfani da fasahar [Taskar-ruhi] ba saboda ni ba ɗan asalin Ururu bane, sannan kuma ruhi na ya kasa shiga Deba. Hanya ɗaya da nake ganin zan jera kafaɗa da sauran ƴan'uwana na Ashura shi ne idan na mallake dukkan fasahohin dake cikin wannan waje."
Uznu yai nuni da kantar dake gabansa ya ce, "akan wannan kanta akwai littattafai dubu tamanin da ɗoriya. Acikin kowanne littafi akwai fasaha sama da dubu. Kowacce fasaha zata ɗauki watanni zuwa shekara kafin na mallaketa. Shekara nawa nake buƙata kafin na mallake dukkan fasahohin dake cikin wajennan? Kaga kuwa bani da lokacin hutu domin ta wannan hanyane kaɗai zan jera kafaɗa da sauran Ashura."
Waziri najin haka ya fashe da dariya ya ce, "dama nasan haka zaka ce saboda haka na taho maka da wani labari. Mutane kaɗan ne suka san wannan labari."
Uznu ya rufe littafin dake hannunsa ya juya ya kalli waziri da kunnuwansa biyu a buɗe.
Waziri yaci gaba da cewa, "fasahar [waƙar-maƙabarta]. Aldaima ya samarda wata fasaha wadda dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos matattu suke barin fasaharsu domin ƴan bayansu. Bansan haƙiƙanin yadda abin yake ba amma nasan Eyriyon ya gaji wannan fasaha kuma da ita yayi shura. Kuma na tabbatar kafin ya mutu ya barwa ƴan'bayansa su gada. Hakan nema yasa muka sa masa ido a lokacin yaƙin. Ile kuwa ya barwa sarkin Bai da kwamandan runduna ta huɗu da kuma wani mutun wanda bamu san waye shi ba wasiyya. Wannan mutane uku sun bazama sun shiga ƙasashen ƙasa bamu san inda sukai ba.
"Na farko dai wannan wasiyya ba wani abu bane illa fasahar waƙar-maƙabarta da kuma wasu sirrikan da har yanzu bamu tantance ba. Na biyu dolene mu kama wannan fasaha mu hanata isa ga wani Wilbafos idan ba so muke mu ƙara samun wani Eyriyon ɗinba. Na uku kuma idan muka ƙwato wannan fasaha zamu yi bincike akanta mu gano yadda Aldaima ya haɗa ta. Ta haka sai muyi ƙoƙarin haɗa tamu. Kaga indai mukai nasara ba kada buƙatar ka ƙara karanta komai anan.
"Babban sarki Kuyurussa'ayi ya bada umarnin tura ƴaƴansa manya guda biyu subi wannan mutane uku. Idan kana buƙata zanyi musu magana su tafi dakai."
Uznu najin haka ya miƙe zumbur cikin murna. Sarki Kuyurussa'ayi shi ne wanda ya ɗorashi akan matsayin Ashura duk da kuwa mutane da yawa sun fishi cancanta. Saboda haka ya daɗe yana so yayi wani abu gagarumi dazai saka masa. Wannan dama ce ya samu.
"A shirye nake waziri yaushe za'a tafi."
Daga wannan rana Uznu ya haɗu da manyan ƴaƴan Kuyurussa'ayi guda biyu suka sauka ƙasashen ƙasa domin neman wasiyyar da Eyriyon ya bari.
Bayan shekaru biyu suna kai-komo a shekarar 16 BA sukai arba da wannan mutun uku a wani daji dake doron ƙasa ta biyu. Inda Ƴaƙin littafin-takobi ya biyo baya. Ƴaƴan kuyurussa'ayi Ururu da wannan mutun uku dake ɗauke da littafin-takobi suka mutu. Uznu shi kaɗai ne ya rayu saboda yanayin sirrin gidan Uzzus dake cikin Negrinkinsa.
Kurkukun Bango
Ɓangaren Armad Wilbafos
Armad na zaune kan reshen bishiyar kwakwa yana nazari. Tuni kwana biyar suka wuce. Kwana bakwai, sati biyu, sati uku Armad bai futo ba. Nusi da Nostaljiya dasu Babara duk sun shigo cikin wajen domin duba lafiyarsa kuma sunga halin da yake ciki saboda haka suka juya. Inara ya dawo daga aikin da Nostaljiya ta turashi na binciko dukkan ƙabila da ƙungiyoyi dake cikin kurkukun.
A wajen Inara matar ubangidansa ubangidansa ce saboda haka duk umarnin Nostaljiya kamar na Armad yake.
Bayan Nostaljiya ta gama haɗa labaran daya kawo mata sai ta nemo Babara ta nuna masa. Sannan ta nemi iznin zasu tafi tare da Inara ta duba da kanta. Babara ya amince ya haɗa su da mutun goma masu kwangilar Armad.
Bayan cikar wata ɗaya Nusi ta kasa daurewa ta koma cikin wajen horon domin duba lafiyar Armad. A hannunta akwai ƙoƙon nono da abinci.
Tana shiga ta duba kan reshen da Armad yake taga babu kowa.
Ina yayi? Kar dai kura ta cinyeshi?
Take kwaryar dake hannunta ta zame ta faɗo ƙasa. Amma bisa mamaki sai Armad ya bayyana a ƙasanta ya tallafe kwaryar.
Yai ajiyar zuciya ya ce, "Hmmm... Dama yunwa nake ji amma a baki za'a bani."
Nusi ta haɗe gira. "Dama dan ka tsorata nine ka ɓace to bazan baka a bakin ba."
"Nusi-ya..."
"Kaimin shiru kafin na kutufeka."
"Hehe... idan kika kutufeni hannunki zaiyi ciwo ai."
"Ehh.. ai ba komai. Idan hannun yai ciwo akwai ƙafa da haƙora da..."
Armad ya kalleta irin kallon nan na tsokana ya ce, "Ai bansan kin iya kokwawa ba kwata-kwata. Naji tsoro na daina tsokanarki daga yau."
Nusi ta cije baki ta kawo masa duka da ƙafa. Armad ya tashi sama ya kauce. Take suka fara guje-guje acikin dajin. Armad yana mata dariya da kwalo ita kuma tana kawo masa duka ta ko'ina. Abin mamakin har yanzu kwaryar abincin da nonon na hannun Armad basu zube ba.
Haka suka wanzu suna tsalle daga wannan bishiya zuwa wannan tsahon lokaci. Kan kace meye wannan tuni yamma ta kawo kai duhu ya fara yi. A dai-dai wannan lokaci sun iso ƙarshen wannan daji.
Abu na farko da Nusi ta fara kula dashi shi ne dukkan namun dajin dake dajin sun ɓuya a gidajensu. A yanayin izzarta bata jin tsoron namun dawar koda kuwa sun ninka haka. Amma abin mamakin shi ne tasan ƙarfin izzarta bai kai tasa namun dawan su gudu ba saboda haka ta dubi Armad cikin tambaya.
"Kardai kacemin ka fara amfani da [SAIKIKA]?"
Armad ya fashe da dariya ya ce, "[Saikika]? Hoho... Ai wannan tsohon zancene. Zo na nuna miki wani abu."
Take Armad yayi amfani da fasahar Kaban'shisu ya ɗauki Nusi ya ɓace daga inda yake ya bayyana acan nesa cikin dajin. A dai-dai inda ya bayyana akwai ƙatoton kogo wanda ba'a iya ganin ƙarshensa. Ya tsaya ya kirawo wasu ɗalasimai. Take wani ƙatoton Aljanin-zaki mai ƙahunhuna biyu ya futo.
Da farko zakin yana ta hanƙoro yana kurari. Yana ganinsu yai tsalle ya afka musu. Amma kafin ya ƙaraso ya fara haɗa gumi. Nan take yaci birki ya turje a gaban Armad. Bayan daƙiƙa biyar yai wata ƙara mai cike da tsoro sannan ya faɗi ƙasa a sume.
Idanun Nusi ya cika da firgici da mamaki. Ta hanyar fasahar [Saikiku] tana iya saka tunani a zuciyar abokin gabanta. Wannan tunani zai iya yin tasiri a zuciyar wanda aka sawa sannan kuma zai iya karyewa. Ya danganta da ƙarfin mai yin da wanda akayiwa. A hannu ɗaya fasahar [Saikiku] tana iya saka tunani ɗan mitsitsi a zuciyar mutun wanda bai wuce wasu-wasi ba amma a ɗayan hannun takan iya saka tunani maɗaukaki na tsoro da firgici. Wannan tsoro idan yayi yawa yakan saka mutun ya suma anan take. Kafin mutun yakai wannan mataki saiya taka babban matakin izza.
"Haba Nusi ta tawa ni kaɗai... Meye kike wani kallona kamar kinga baƙo. Tukunna ai baki ga komai ba."
Take Armad ya ƙara ɗaukanta suka nufi wani sashi na daban acikin dajin ya ƙara nuna mata wata fasahar. Saida suka wuni cir Armad yana nunawa Nusi fasaha daban-daban har saida yawun bakinta ya ƙafe.
Da yammaci suka nufo hanyar futowa suna tattauna lamura.
Armad ya ce, "Harin Tunani shi ake kira da [Saikikù]. Harin ruhi shi ake kira da [Sóru]. Harin izza shi ake kira da [Lanjabiti]. Harin jiki shi ake kira da [Jikkaida]. Amma hare-hare hanya ɗaya ne kurum na dabarun yaƙi. Akwai hanyoyi da dama wanda suke nuna ƙarfin runduna. Misali harkar magani da likitanci. Ta wannan fanni akan iya karya rundunar abokan gaba kafin su ƙaraso a saka musu wata cutar. Sannan kuma ta wannan fanni ake kula da wanda suka faɗi a fagen fama. Ina so na naɗa ki shugabar kula da magani da marasa lafiyan sabuwar rundunar Wilbafos."
Nusi tai tsam tana tunani kafin daga bisani ta gyaɗa kai. "na amince, dama can a harkar magani da sarrafa fatalwa na kware."
Armad yayi murmushi ya ce, "yauwa kinga zan naɗa Babara shugaban ƴan-duba da aika saƙo na wannan runduna tawa. Sauran muƙamai da suka rage suna da yawa: kwamandan noma da kiwo, kwamandan koyarda yaƙi da takobi, kwamandan koyarda Saikika, kwamandan Soru, Kwamandan Lanjabiti, kwamandan Jikkaida, da dai sauransu."
Nusi ta amsa da cewa, "Ina ganin da ƴar wayewata a harkar mulki zan iya taimakawa da wannan."
A dai-dai wannan lokaci suka iso bakin wajen horon. Armad ya zana hatimin dake jikin ƙofar cikin kwanciyar hankali. Nan take ƙofar dutsen ta buɗe. Nusi na niyyar tambayarsa ya akai ya san yadda ake zana hatimi hasken waje ya shigo ya haske musu ido.
Dubban mutanen Lamarudu wanda dukkansu zuri'ar Wilbafos ne wanda aka ƙulle suna tsaye sahu-sahu suna jiransu. A gaban wannan mutane akwai Babara da Lamarudu da Cokali da Iliyasisi da Nostaljiya da Inara wanda tuni suka dawo daga shawagin da suka tafi. Armad yaja dogon numfashi. Taron wannan mutane ba wani abu suke so ba illa suji muryarsa, suji jawabinsa. Kowa acikinsu dashi ya dogara. Kowa a wannan waje yayi mubaya'a. Abinda kawai suke jira shi ne shugaba. Wannan shugaba ba wani bane ba illa Armad.
Armad ya hau kan mumbari sannan ya juyo ya kallesu.
"Suna na Armad Wilbafos. Kusan dukkaninku da kuke nan kunsanni a fuska ko kuma kun taɓa ganina. Da dama daga cikinku sunaimin kallon magajin wilbafos, magajin sarki Eyriyon. Hakan ne. To amma kuyi sani ba nine kaɗai magajin wilbafos ba.
"A doron ƙasa babu wani zalunci daya wuce cinikin bayi. Eyriyon yayi faɗa da zalunci kuma ta haka ne ya rasa ransa. Iyayenmu da kakanninmu sunyi faɗa da zalunci kuma ta haka ne suka rasa rayukansu. Dukkan wanda aka ƙulle a cikin wannan kurkuku yayi faɗa da zalunci kuma dalilin haka ne yasa aka ƙulleshi.
"Matsafa da masu sihiri suna neman jinin magajin wilbafos domin suyi tsafi dashi. Abokan gaba masu assasa cinikin bayi suna neman magajin wilbafos domin su kasheshi. Idan ka tambayeni waye magajin wilbafos zan gaya maka ba kowa bane illa dukkan wani mai yaƙi da cinikin bayi. Nima magajin wilbafos ne, kaima magajin wilbafos ne, kema magajin wilbafos ce, dukkanninku magajin wilbafos ne.
"An kashe mu, an ɗaure mu, an sakko damu ƙasashen ƙasa badan komai ba sai dan munƙi cinikin bayi. Idan dai wannan ne dalilin da yasa ake ƙinmu to bama buƙatar soyayyar. Suci gaba da ƙinmu, daga wannan rana duk wani magajin wilbafos yasa ɗan'ba na ƙiyayya dasu. Daga wannan rana zamu fara shirin yaƙi. A gaya musu muna nan tafe!"
Armad ya ɗaga hannu sama ya dunƙuleshi ya maimaita jimlarsa ta ƙarshe da ƙarfin tsiya. Tare da yin amfani da fasahar [Kiɗan Izza] wajen ƙarawa sautinsa ƙuwwa.
"MUNA NAN TAFE!"
Dukkan wanda ke cikin wajen ya ruɗe da amshi.
"Muna nan tafe! Muna nan tafe!! Muna nan tafe!!!"
Shugaba ya samu, saura shirin yaƙi.
Babara, Nusi, Nostaljiya, Cokali, Iliyasisi, Inara da Lamarudu na bayan Armad gab-da-gab. A bayansu akwai mutun goma da suka karɓi kwangilar Armad a jere.
Bayan sun isa fada sai mutun goman da suka karɓi kwangilar Armad suka tsaya a ƙofa suka kewaye ƙofar suna gadi. Hatta kiyashi baza su bari ya shiga ba saida izini.
Armad ya juyo ya dubi ragowar mutun bakwai dake tare dashi ya ce, "na yanke shawara da tsohuwar daula zamu fara. Iliyasisi zaka zauna tare da sauran mutun goma masu kwangila kuyimin ƙidayar duk jama'ar da muke dasu a yanzu da kuma fasahar da kowa yake da ita da gudunmawar dazai iya bayarwa. Ina dawo wa dashi zamu fara aiki. Zamu raba rundunarmu gida-gida musa kowa a inda ya dace. Lamarudu kaima zaka zauna domin kafi kowa sanin mutanenka sai kuyi aikin tare da Iliyasisi.
"Nusi da Nostaljiya duk bazan tafi tare daku ba. Duk wanda ke ɗakin nan ya sani cewa na naɗa Nusi shugabar haɗa magani da kula da marasa lafiya a wannan runduna tawa. Wannan muƙami zai ci gaba dabinta har zuri'arta har izuwa ƙiyama. A halin yanzu bani da kambu ko kuma wani sanda na shaida da zan baki amma kiyi sani tuni an riga an rubutaki. Na baki dama ki sawa wannan sarauta taki duk sunan da kika ga dama."
Nusi ta manta da muƙaminta ta durƙusa a gaban Armad. "Ina godiya sarki Wilbafos. Ina so na gayawa sarki cewa na shigo wannan sashi da mutun goma sha huɗu. Dukkansu sunkai matsayin Sammai kuma a sashin ikwatora na shida suna daga cikin manyan ma'abota izza. Acikinsu uku suna sarrafa fasahar [Turɓuya]. Da wannan fasaha zasu iya gina mana ɗan ƙaramin gari da badala cikin wata ɗaya a wannan waje. Na sadaukar dasu ga wannan tafiya domin ina ganin lallai sarki kamarka yafi ƙarfin ya ringa rayuwa acikin duwatsu. Sannnan kuma sashina na ikwatora da nake mulki na sadaukarwa wannan tafiya."
Armad ya sakko daga kan karagarsa ya tsaya a kanta ya ce, "idan kowa zai durƙusa banda ke. Daga yau na haramta miki durƙusawa wannan karaga."
Armad ya jata ya tsayar da ita a gefen kujerarsa. Sannan ya juyo ya dubi Nostaljiya ya ce, "Ga wanda basu sani ba Nostaljiya matata ce. Bana so na sata aiki saboda tana ɗauke da juna biyu acikinta. Inara ka zauna a kusa da ita, ka kula da ita yadda zaka kula dani kafin na dawo."
Lallai idan da ba'a gaban mutane ake ba da Nostaljiya ta ce a'a amma bata so taja masa a gaban mabiyansa saboda haka ta gyaɗa kai. Zancen ciki kuwa dama tuni Nusi ta sani tunda ita ma mace ce. Ragowar ƴan fada suka gabato gaban Nostaljiya suka kwashi gaisuwa. A halin yanzu ta zama sarauniya mai ɗauke da ɗan sarki. Yadda za'ai wa sarki biyayya haka za'ai mata a fannoni da dama.
Armad ya miƙe ya saka ɗamarar yaƙi. "Babara dakai da Cokali daku zamu shiga wannan tsohuwar daula muga mai take ciki."
Kowa ya buɗe baki yana mamakin dalilin da yasa aka zaɓi Cokali. Idan an zaɓi Babara ba matsala bane domin kuwa Babara shi ne mafi girman shekaru da izza acikinsu. Sannan kuma idan ka ɗauke Lamarudu babu wanda yasan meye acikin daular saishi. To amma Cokali bashi da wani banbanci da zaisa a zaɓeshi. Armad ya fuskanci abinda suke tunani to amma bai basu amsa ba kawai ya shige gaba ya nufi ƙofar tsohuwar daular.
Ƙofar dai anyi tane da wani sinadari mai kama da narkakken ƙarfe amma kuma idan ka ƙura masa ido zaka fuskanci ba ƙarfe bane. Yafi kama da dutse amma kuma ba dutse bane. Armad ya dubi Babara da Cokali ya ce, "sunan wannan sinadari Yéniy, dashi ake haɗa kayayyakin tsafi kamar su Alkadar da Farar laya da ƙofar Eycigan dama sauransu."
Armad ya kalli Cokali ya ce, "Kasan meye dalilin da yasa na zaɓo ka?"
Cokali ya girgiza kai.
"Na taho dakai ne domin a duk wanda nake tare dasu babu wanda jikinsa ya dace da sarrafa sinadarin Yéniy sai kai. Zan koya maka fasaha ta musamman wadda zaka fara sarrafa Farar-laya da ƙofar Eyricigan."
A dai-dai wannan lokaci suka iso bakin ƙofar. Abin mamaki shi ne ƙofar tana tsaye sama da shekaru dubu amma babu alamun tsufa ko kaɗan a tare da ita. Idan ka kalli cikinta zaka hangi matattakala tayi sama ta haɗe da gajimare amma kuma idan ka dawo ta baya zaka ga babu komai a bayan ƙofar sai iska. Lallai wannan ƙofa tana da abin mamaki amma ko kaɗan bata firgita Armad da mutanensa ba. Kai tsaye suka shige cikin ƙofar.
Gefensu babu komai sai duhu. Babu abinda ake gani sai matattakalar. Armad da Cokali da Babara suka hau kan matattakalar sukai sama.
Bayan tsahon lokaci suna tafiya sai suka fara hango hasken rana daga can nesa. Hatta Armad da Babara da ƙarfin yanayin-izzarsu basa jiyo meye a wajen hasken sai dai hasashe.
Ba jimawa suka ƙaraso. Suna fitowa suka hangi rana a sama ta haske ko'ina. A gabansu akwai fili fetal wanda ya haɗe da sama. Daga can karshen filin ana hangen ganuwar gari. Take suka nufi wannan ganuwa cikin sauri.
Abin mamaki suna isowa suka fara jiyo muryoyin mutane. Suka fara hangen fitulu da haske na tashi. Bayan tafiyar wuni ɗaya wani ƙasaitaccen gari ya bayyana a gabansu. Ƙofar garin a buɗe take amma basa hango komai aciki. Babara ya dubi Armad ya ce, "akwai irin wannan garuruwa guda biyar a sassa daban-daban na wannan waje. Idan ka matsa kusa zaka iya jin hayaniya da wani irin yare na daban wanda bamu gane mai ake cewa.
"Abu ɗaya dana sani shi ne duk wanda ya shiga cikin wannan garuruwa baya taɓa fitowa. Anan kakannin su Lamarudu suka ɓace. Nima dani da Lamarudu dan bamu shiga bane shi yasa muka samu damar dawowa."
Koda jin haka sai Armad yai shiru na ɗan lokaci kafin daga bisani yai murmushi ya ce, "muje zuwa to. Tunda wannan shi ne gari na farko bari mu fara ta kansa."
Kai tsaye Armad ya shige gaba ya nufi ƙofar garin. Ya shige kai tsaye cikin ƙofar Cokali da Babara suna biye dashi.
Abu na farko da suka fara ji shi ne wata ƙara a kunnuwansu mai kama da ana goga tsohon ƙashi akan dutse. Sannan kuma kansu yai nauyi kamar an tsoma su acikin ruwa. Bayan ɗan lokaci komai ya ɗauke suka bayyana acikin garin.
Abinda suka gani yayi matuƙar basu mamaki.
***
Babi na 193-197
***
Wata irin iska mai ƙarfi ta ɗebe su ta watsa su bakin wata unguwa. Dogayen gidaje ƙirar aljanu sun kewayesu ta ko'ina. Armad ya baza [Yanayin-izza]rsa amma baiji kowa a kusa ba. Tuni Babara ya zaro sandar tsafinsa, Cokali kuma ya zaro littafin fasahar marubutan farko da alƙalaminsa zai fara rubutu.
Armad ya dubesu ya girgiza kai, "bakwa buƙatar wannan. Ku biyoni."
Armad ya tunkari ɗaya daga cikin gidajen. Ginin anyi shi da farin dutse sannan kuma anyi masa fenti da wani koren abu wanda babu wanda ya taɓa gani acikinsu. Tsayin kowanne gida yakai zira'i maitan. Duk da wasu gidajen sunfi wasu tsayi amma dukkansu a jere suke a layi da ƙayyadajjen faɗi a tsakaninsu. A kowanne layi akwai bishiyoyi na Ayrid da ƴaƴan itatuwa. Komai a tsari. Ƙasar garin gaba ɗaya fara ce fat kai kace Farar-ƙasa ce.
Armad yai ajiyar zuciya sannan ya tashi sama akan iska ya kalli kudu da yamma, gabas da arewa. Acan tsakiyar garin ya hango dandazon mutane sun kewaye wani abu mai haske. Take Armad ya fara iyo kan iska ya nufi wajen wannan haske ba tare da tsoron komai ba. Babara ya zare sandar tsafinsa yabi baya tare da Cokali.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso tsakiyar garin. Tun kafin su iso Armad yai amfani da [Yanayin-izza] yaga babu kowa a wajen.
Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Ana nufin babu kowa a garin?
Suna isa Armad ya saita idonsa akan hasken dake tsakiyar wajen.
Hasken na tashi daga Ayrid mai mataki na ashirin da uku. Yana ɗauke da hoton bidiyo na mutun biyar. Abin mamaki hoto na farko hoton Hidaya ne. A ƙasansa akwai hoton wasu mutane huɗu. Dukkan wannan mutane guda huɗu ƙoƙarin cimma wannan hoto na Hidaya suke. Mutun biyu daga cikin mutun huɗu dake bin hoton Hidaya duk Armad ya sansu.
Ikenga O. Bayajidda da kuma Hansirshishirui wanda akafi sani da Hasanu Sisiyu ɗan sarki Bihanzin. Ragowar mutun biyun ɗaya yana da idanuwan Ururu ɗaya kuma yana da dogayen kunnuwa kamar zomo.
Armad yai duba izuwa Tsarin-ruhinsa ya zaƙulo ɗaya daga cikin baitikan da Hidaya ta bar masa. Take ya gane mai yake faruwa. Hoton Hidaya yana ɗauke da ruhin Deba ɗinta. Ikenga da Hasanu da ma'abocin Ururun da mai dogon kunnen duk suna ƙoƙarin ƙwace ruhin ne ya zama nasu.
Zuciyar Armad ta buga bugawa mai ƙarfi. Marmarin yaƙi mai tsanani ya kaɗa a idanuwansa. Armad yasan mai ya kamata yayi saboda haka nan take ya zare takobinsa ya tashi sama ya nufi bakin ƙofar garin daya shigo.
Saboda tsananin gudun da Armad yake saida iska ta fara darewa tana ƙara tana kamawa da wuta. Tuni yabar Babara da Cokali a baya. Yana zuwa bakin ƙofar ya ɗaga takobinsa ya tsarge bakin ƙofar inda wani tsohon mutun ya bayyana a gabansa. Iskar da ke tashi daga jikin mutumin tana nuni da yakai matsayin Deba. Tsohon ya rufe fuskarsa da baƙin kyalle.
Armad bai tsaya ba ko kaɗan yaci gaba da tunkarar ƙofar. Tsohon ya jada baya ya zare takobinsa.
Jar Negrinki ta fara ɓulɓula daga hannun Armad tana kewaye takobinsa. Gashin kansa ya miƙe sama ya ƙara yin jajawur kamar ana kunna masa wuta. Samaniya ta fara juyawa tana rugugi. Nan take hadari ya haɗo ya tokare gabas da yamma kudu da arewa. Tamkar sama tana yiwa Negrinkin Armad biyayya ta juye izuwa launin ja. Taku ɗaya tak Armad yayi iskar dake kewaye dashi ta dare ta tarwatse. Armad ya bayyana a kusa da wannan tsoho mai matakin Deba.
Tsohon ya lissafa zuwan Armad saboda haka ya kewaye jikinsa da Sirrin Deba. Takobinsa ta fara ci da wuta sannan ya kirawo aljaninsa na wuta ya bayyana a bayansa. Ya daki ƙasa da ƙafarsa inda ƙasa ta dare wuta ta fara ambaliya. Narkakken dutse ya fara ambaliya yana ƙoƙarin haɗiye dukkan duniya. Sirrin Deba ya cika sama da ƙasa. Deba sun banbanta. Da sama da ƙasa da iska da ruwa komai biyayya yake yiwa Deba.
Dukkan duniya ta koma ɓangaren wannan dattijo tana bin bayansa tana juyawa Armad baya. Walƙiyar da Armad ya kirawo ta ɓace ɓat. Sama ta dawo dai-dai tana mai kore Negrinkin Armad. Iska da ƙasa da sammai komai yayo kan Armad yana neman haɗiye shi. Dattijon ya buɗe baki ya ce, "Na manta sunanka amma na gane ruhinka."
Kalma bakwai ya faɗa amma kowacce ta juye izuwa babban ɗalasimi sannan ɗalasimin ya juye izuwa al'amudin wuta yayo kan Armad ta kowanne ɓangare.
"Mutu kawai. Ka mutu kawai. Ka mutu kawai."
Armad yaji muryar duniyar da yake ciki tana juya masa baya tana ALLAH wadai dashi.
Irin wannan abu shi ake cewa sirrin Deba. Sirrrin da yake bawa Deba damar sarrafa duniyar da suke ciki. Saboda wannan sirri faɗa da Deba kamar faɗa da duniya ne baki ɗaya. Idan kana faɗa da Deba duniya baza ta baka walƙiyarta ba, baza ta baka wutarta da iskarta da ƙasarta ba. Idan baka da wani abu sai wannan tun anan an cinyeka da yaƙi.
Armad na tsaye bashi da komai sai Negrinkinsa da takobinsa. Amma abin mamaki babu tsoro ko ƙaɗan a fuskarsa. Kai kace kwance yake akan gadonsa yana hutawa. Lokaci yayi dazai bayyana fasahar dake cikin Negrinkinsa.
Ya ɗaga takobinsa sama ya kawo sara. Jan hayaƙi ya fara ambaliya daga jikin takobin. Cikin daƙiƙa ɗaya ya gauraye ko'ina.
Abu na gaba daya faru yasa tsoro da firgici ya bayyana a idanun wannan dattijo mai taƙama da matakin Deba.
Negrinkin Armad ta kewayeshi ta kowanne ɓangare. Dukkan masifun da suka yiwo kan Armad suka daki Negrinkin. Abin mamaki sai kawai Negrinkin ta zama kamar wani ƙaton kogo ta zuƙe komai. Cikin ƙiftawar ido duk al'amudan wutar da suka kewaye Armad suna neman halaka shi suka ɓace ɓat. Babu abinda kake gani sai Negrinkin Armad tana haske kamar wuta mai ruruwa.
Negrinkin ta zuƙe hatta [Sirrin Deba] da yasa duniya ta juyawa Armad baya. Iska, ruwa da komai ya ɓace. Walƙiyarsa ta dawo. Babu komai sai Armad da ikonsa. Jan sarki mai jan gashi da jan Negrinki.
A ɗaya gefen kuma wannan dattijo mai taƙama da [Sirrin Deba] yasha dakyar. Negrinkin Armad ta zuƙe takobinsa. Babu komai a hannunsa sai ƙota. Kayansa sunyi daga-daga. Sashi da dama na kayan sun ɓace ɓat babu alamunsu. Fuskarsa ta bayyana a fili domin Negrinkin Armad ta zuƙe hijabin daya rufe fuskar.
Ga duk wanda yaga fafatawar Armad ta farko bayan fitowarsa daga gida nemawa mahaifiyarsa magani zai gane wannan mutun kai tsaye.
"Han'Diyuza?"
Dattijo Han'Diyuza ya kalli Armad cikin mamaki. Bayan tsahon lokaci yai ajiyar zuciya ya ce, "baka manta sunana ba kenan. Ka shammaceni da Negrinkinka ba daban na ankare da wuri ba da tuni ka illatani. Kayi sani cewa duk wanda ya shigo garin nan baya fita. A matsayina na mai tsaron ƙofa aikina ne gadi. Kada ka zargeni cikin aikina."
Armad ya numfasa yai ajiyar zuciya. Shima kansa ganin Han'Diyuza ya shammaceshi. "Dattijo Han'Diyuza mai tsaron ƙofa, ganinka ya tunamin abubuwa da dama. Ko kaine mai gadin duk wata ƙofar sirri dake doron ƙasa?"
Han'Diyuza yai murmushi tare da amsawa da cewa, "ba gaskiya bane kuma ba ƙarya bane."
Armad ya yatsine fuska tare da aikawa tsohon kallo mai cike da tambaya.
Han'Diyuza ya amsa da cewa, "Koda zanyi maka bayani baza ka gane ba."
Waɗannan kalmomi takwas da dattijon ya furta suka juye izuwa ɗalasimai. Kowanne ɗalasimi ya juye izuwa hatimi. Hatiman takwas suka kewaye Armad. Huɗu suka zama al'amudin wuta sannan huɗu suka zama al'amudin ƙanƙarar [Sanyin-Babban-Sihiri]. Suka tunkaro Armad gadan-gadan suka ƙaraji da ƙuwwa tamkar zasu ci babu. Sanyin ƙanƙara haɗe da zafin ruruwar wuta suka haikewa Armad ta kowanne ɓangare.
Armad ya ɗaga hannunsa na hagu sama ya dunƙuleshi inda ya juye izuwa [Hannun-Aradu]. Ya daki iska sau takwas a jere. Kowanne duka ya samarda [Hannun-Aradu] guda ɗaya. Sannan Armad yayiwa kowanne [Hannun-Aradu] fenti da Negrinkinsa.
[Hannun-Aradu] takwas suka tunkari al'amudan Han'Diyuza takwas. A lokacinda suka haɗu babu ƙara ko rugugi ko kaɗan. Babu wata alamar yaƙi kawai Negrinkin Armad ce ta zuƙe dukkan al'amudan takwas a yayinda itama ta ɓace tabar walƙiyar mai ɗauke da [Hannun-Aradu] sukai kan Han'Diyuza zasu murƙusheshi.
Han'Diyuza ya kai musu sara da takobinsa inda koriyar wuta ta futo tana ambaliya.
Armad yana ganin koriyar wutar ya gane ta. [Jukisu]. Sai dai kuma a yanzu ƙarfinta ya ƙaru matuƙa ba kamar sanda Armad ya ganta ba.
Da [Jukisu] da [Hannun-Aradu] suka kashe juna.
Kowanne ɗaya daga cikin wannan hare-hare zai iya rusa runduna guda amma da Armad da Han'Diyuza ko a jikinsu. Hirarsu kawai suka ci gaba. Faɗan manya sai manya.
Han'Diyuza yaci gaba da bayani. "Sarkin sarki, sarki a sama, sarki a farkon lokaci."
Yana rufe baki dukkan kalmomin daya faɗa suka koma ɗalasimai wanda suka juye izuwa hare-hare sukai kan Armad. Armad ya sare su cikin kwanciyar hankali.
Armad ya ce, "Wa kake nufi da kace sarkin-sarki?"
Han'Diyuza ya amsa da cewa, "idan na gaya maka wannan sai dai na kasheka."
Armad yai shiru yana kallonsa. Bayan ɗan lokaci yai tsaki sannan ya ce, "zaka kashe ni? Kayi kuskure da kayi wannan kalami. Saboda abinda kayimin a baya na baka dama ka ɓacemin da gani. Idan ba haka ba duk abinda ya same ka kada ka zargeni."
A dai-dai wannan lokaci su Cokali da Babara suka iso suka ga abinda ke faruwa.
"Akwai ASALIN DEBA wanda shi ne mataki na farko a Deba. Na gabansa shi ne LARDIN DEBA. Bayanshi akwai WAADIN DEBA wanda shi ne ƙololuwar izza. Ni Han'Diyuza nakai matakin Lardin Deba. Kana tunanin duk da haka zaka iya cimmin?"
Armad bai bashi amsa ba kawai ya juyo ya dubi Babara da Cokali yayi musu inkiya suja da baya.
Take Negrinkin Armad ta fara tsattsafowa daga jikinsa tana ambaliya. Cikin daƙiƙa goma ta cika wajen. Dukkan abinda ta taɓa sai kaga ya ɓace ɓat babu shi babu alamunsa. Gidaje da duwatsu da katangar garin da dukkan wani abu ya fara ɓacewa. Babu wanda yasan inda abubuwan da suka ɓace suke tafiya hatta shi kansa Armad. Han'Diyuza ya jada baya ya ware dukkan shekarun izzarsa sannan ya kirawo dukkan manyan fasahohinsa ya afkawa Armad.
Wata ƙatuwar rana wadda aka haɗa ta da zunzurutun kuriyar wuta ta dunƙule a bayan Han'Diyuza inda ya afkawa Armad.
Armad ya afka masa kai tsaye.
Ƙasa tai girgiza sama tai duhu. Dukkan ilahirin garin ya fara girgiza. Idan ka hangesu daga nesa zaka ga duniyar ta rabu gida biyu. Ɓangare ɗaya kore ɗaya kuma ja. Koriyar wutar Han'Diyuza tana ɓulɓula tana ambaliya kamar baza ta ƙare ba, ita ma Negrinkin Armad tana ta ɓulɓula ta cika ko'ina. Abu kamar wasa Negrinkin Armad ta zuƙe sama da rabin gidajen garin.
Manyan gine-gine da akayi da jan dutse da bishiyoyin Ayrid da suka cika garin komai ya ɓace ɓat. Babu komai sai fili da Farar-ƙasa.
Sannu a hankali Negrinkin Armad ta fara haikewa koriyar wuta. Da farko abin bai bayyana ba amma bayan sa'a biyu ba'a ganin komai sai ja. Jajawur ko'ina. Kai kace wani ƙaton kogi ne na jini. Armad yana tsakiyar kogin. Bakin kogin ya hangame yana hanƙoro zai cinye Han'Diyuza.
A lokacin da Han'Diyuza ya gano cewa ba Lardin Deba ba koma me zai samar Negrinkin Armad cinyeshi zatai sai kawai ya canja shawara. Ya juya baya zai gudu.
Armad ya ce, "hmm.. kana tunanin zan bari ka gudu? Daina mafarki."
Armad yai amfani da Kaban'shisu ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban Han'Diyuza. Negrinkinsa ta haɗiye tsohon kai tsaye. Babu Han'Diyuza babu koriyar wutarsa. Babu rabin garin. Komai ya ɓace, Negrinkin Armad ta zuƙe.
Babara da Cokali da kyar suka sha. Suka bayyana a gaban Armad suna haki.
Cokali yana haki ya ce, "Sarki wacce fasaha ce wannan? Sauran ƙiris mu halaka."
Armad yayi murnushi ya ce, "fasahar dake cikin Negrinki na ce. Wancan tsoho mun taɓa fafatawa dashi farkon lokacin dana fito daga gida. Sunansa Han'Diyuza ɗan ƙabilar Hán. Babara, farkon saukarku ƙasashen ƙasa kun tararda ƙabilar Hán?"
Duk da Babara bai gane dalilin tambayar ba ya amsa da cewa, "a wancan lokaci gaskiya babu ƙabilar Hán. Idan zan iya tunawa mafarin ƙabilar shi ne Han'Kalámu mahaifin sarki Han'Ibal wanda akafi sani da Han-na-ɗaya. Shi ne wanda ya fara kaiwa matakin Deba ya ɗaga matsayin ƙabilar a doron ƙasa."
Armad yai shiru yana nazarin amsar da Babara ya bashi kafin daga bisani ya ce, "idan ba ƙabilar Hán ba to wacce ƙabila kuka tarar? Zaiyi wuya ace baku tararda kowa ba sai fili."
Babara ya amsa da cewa, "a gaskiya bamu tararda kowa ba. Sai dai kuma mun tararda garuruwa da manyan gine-gine a wajaje da dama kamar wannan gari. Anyi ta bincike kan wannan gine-gine amma daga ƙarshe ba'a ga komai ba. Idan zaka iya tunawa hanyar da kabi lokacin dana buɗe maka ƙofar Eycigan akwai garuruwa irin waɗannan acan."
Armad yai shiru yana tunani. Akwai abubuwa da dama wanda da bai kula dasu ba amma yanzu daya samu fikirar littafin-takobin tunaninsa ya canja.
"Dole akwai al'ummar da suka rayu a doron ƙasashen-ƙasa kafin mu? Tambayar ita ce ina wannan mutanen suka tafi? Meye labarinsu? Meye shirinsu?"
Armad yana cikin magana yaji iskar dake kewaye dashi ta canja. Ya ƙarfafa [Yanayin-izza]rsa amma baiji komai. Ya waiwaya ya dudduba amma baiga komai ba. Babara da Cokali suka dubeshi suna niyyar tambayarsa mai yake nema kawai suka ji wani abu ya daki kansu duk su ukun a tare. Kan Cokali da Babara ya dare jini ya fara zuba. Akai jifa dasu gefe guda. Armad shi kaɗai ne ya tsaya a inda yake bai motsa ba.
Iskar dake kewaye dashi ta ƙara canjawa inda ya ƙara jin abin ya gwari kansa da ƙarfin da ya ninka na baya. Armad bai motsa ba. Yana tsaye ƙiƙam kamar sararin samaniya. Idanunsa suna bin motsin iskar da yake ji. Can ya ƙara jin iskar dake kewaye dashi ta canja. A wannan lokaci abubuwa uku suka daki kansa ta ko'ina. Kowanne daga cikinsu yafi ƙarfe tauri.
Armad ya miƙa hannunsa yakai wafta kan iska. Abin mamaki sai gashi ya riƙo wani abu. Ba'a ganin abinda ya riƙo amma kuma yana jinsa a hannunsa.
Ya wujijjigashi sannan ya fyaɗashi da ƙasa. Duk da haka Armad bai sake shi ba ya ƙara fyaɗa shi da ƙasa har saida ƙasar wajen ta dare gida biyu. A lokacin wata halitta ta bayyana a hannunsa a sume bata san inda kanta yake ba.
Armad ya cillawa Babara halittar. "Saka masa Farar-laya ka ɗaureshi."
Sannan ya juyo gabansa. Yana da cikakkiyar masaniyar cewa akwai ragowar irin waɗannan halittu guda biyu dake tsaye a gefe suna kallonsa.
Armad ya ƙurawa iskar gabansa ido. Baya ganinsu kuma baya jin [Yanayin-izza]rsu amma yana ganin motsin iska a duk lokacinda sukai motsi. Suna gefe su kuma suna kallonsa suna tsoron motsawa domin sun san suna motsawa zai gane inda suke.
Bayan ƴan daƙiƙu Armad ya dube su ya ce, "idan zaku bayyana kanku ku bayyana idan kuma zaku ci gaba da tsaiwa kuci gaba."
Ɗaya daga cikinsu ya juya ya fita da gudu. Armad yaga motsin iskar dake wajen saboda haka ya yunƙura zai bishi amma kuma ɗayan ya bayyana a gabansa.
Zabgegene mai dogon gashi fari yana jan ƙasa. Yana da ƙatoton kai wanda yafi komai girma a jikinsa. Kafin Armad yayi wata-wata ya yiwo kansa yana ƙaraji yana cewa, "[Kan-Kada Mai Ƙwari]"
Kan halittar ya kumbura, wasu ƙayoyi irin na kada suka bayyana a jikinsa. Kunnuwansa suka ƙara yin tsini. Ya jada baya kamar rago sannan ya afkawa Armad da kansa.
Armad ya jada baya ya ce, "[Ƙashin-Wilbafos Farkon-ƙarni]!"
Yana rufe baki kansa ya koma baƙi-wuluk. Ya jada baya sannan ya gwarawa halittar kansa. Koda kayikansu suka haɗu sai wata ƙara mai kama da an buga dutse akan dutse ta tashi. A lokacin Armad ya fuskanci cewa abinda ya daki kansa a baya kai ne ba ƙarfe ba. Ƙarfin karon yai wurgi dasu baya. Ɗigon jini ya bayyana a kan Armad a dai-dai inda sukai karon.
Armad ya kai hannunsa ya taɓa wajen sannan ya ɗago kai ya dubi halittar mai ƙaton kai ya ga ita ma akwai jini akanta.
Halittar mai kama da mutane ta buɗe bakinta ta ce, "kai ne na uku a jinsin bil-adama daka taɓa tarar fasahar [Kan-kada Mai Ƙwari] gaba-da-gaba kuma ka rayu. Amma bari na nuna maka fasahar da mutun ɗaya ne kacal a jinsin bil-adama ya taɓa gamuwa da ita kuma ya tsira."
Armad yana jin yaren da wannan halitta mai kama da mutane suke yi saboda BAITIN WAƘA da Heeda ta bar masa cikin Littafin-takobi amma Cokali da Babara babu abinda suke ji. Sunan wannan yare Elburish.
Cokali ya yamutse fuska yana kallon halittar dake hannun Babara a ɗaure cikin ankwar Farar-laya. Komai nata yana kama dana mutane sai dai banbance-banbance a wasu abubuwa kamarsu kunne, fata, da gashi. Shi kuwa Babara miƙawa Cokali halittar yayi sannan ya miƙe ya nufo inda Armad yake fafatawa da halittar domin kawo ɗauki.
A dai-dai wannan lokaci halittar dake fafatawa da Armad ta ƙara kirawo wsta fasahar. "[Kan-gwanki Mai Rangwangwan]."
Kansa ya juye izuwa farin dutse. Idanuwansa suka ɓace, gashinsa ya koma ciki babu komai a jikin kan sai dagayen kunnuwa a fiƙe suna kallon sama. Ya tunkaro Armad da gware. Halittar dake hannun Cokali ta buɗe tana murmushi ta ce, "yanzu kan ɗan uwanka zai tarwatse. Zai gamu da [Kan-gwanki Mai Rangwangwan]."
Cokali baya jin mai yake cewa saboda haka ya daka masa tsawa yayi shiru.
Armad ya ƙara buɗe Baitikan dake cikin Tsarin-ruhinsa ya zaƙulo wata fasahar. "[Ƙashin Wilbafos Ƙarnin-ƙarshen]."
Dukkan jikin Armad ya juye izuwa baƙin ƙarfe. Ya tunkaro halittar ya gwara mata kansa. Banbancin wannan fasahar da fasahar farko da Armad yayi amfani da ita shi ne ƙarnin. Fasahar farko an samar da ita ne a ƙarnin farko na mulkin Aldaima. Tun daga wannan lokaci ake ta gyarata ana ƙara ƙawatata har zuwa ƙarnin ƙarshe na mulkinsa inda aka samarda fasahar ta biyu.
Inda sukai gware ya kama da wuta kafin daga bisani kan ya halittar ya tarwatse gida biyu ta faɗi ƙasa matacciya. Idanun ɗaya halittar ya zaro saboda firgita. Fasahar [Kan-gwanki Mai Rangwangwan] tana daga cikin fasahohi mafiya ƙarfi na ƙabilarsu amma gashi wannan mutun ya tarwatsata. Abinda bai sani ba shi ne Armad ya tsallake rijiya da baya saboda jikinsa gaba ɗaya walƙiya ne. Hari na jiki baya aiki a kansa.
Armad ya dubi halittar dake ƙasa a kwance ya ce, "babban kuskurenka shi ne bayyana kanka da kayi. Daka gudu ko kuma ka tsaya a ɓoye kamar ɗan'uwanka da ka tsira da ranka."
Armad ya juyo ya dubi su Babara ya ce, "ɗayan ya gudu nasan zai dawo da wasu. Dole mu bar wajennan mu ɓuya a wani wajen domin muyi nazarin abinda ke faruwa da kuma yadda zamu ɓullowa masa."
Babara da Armad izzarsu takai dubu saboda haka suka tashi sama kai tsaye suka nufi daji mafi kusa dasu. Shi kuwa Cokali har yanzi bai kai matsayin tashi ba saboda haka ya zana shirwa acikin littafinsa da fasahar [Marubutan-farko] sannan ya hau kai ya bisu.
Ba jimawa suka isa dajin daya kewaye garin suka sami wani kogo suka ɓoye. Babara ya cire yanar data rufe ƙofar kogon sannan ya shafa kan sandar tsafinsa lamarinda yasa kan sandar ya juye izuwa hasken fitila ya haskaka cikin kogon. Abu na farko da suka fara gani shi ne ƙasusuwan mutane bajaja a ƙasa. Wasunsu suna riƙe takubba wasu littafai daban-daban. Babu tayadda za'ai a gane su waye wannan mutane domin komai nasu ya narke ya koma ƙashi. Hasalima babu yadda za'ai a gane yawan shekarun da sukai acikin kogon. Wasu daga cikinsu suna ɗauke da zobe a ɗan-yatsansu irin na Armad mai ajiye kaya.
Armad yayi wa Cokali inkiya daya ɗebar musu duk wani abu mai amfani. Sannan dashi da Cokali suka danna cikin kogon ko zasu ga wani abu.
Kogon yana da faɗi da farko sannan sai kuma wata ƴar siririyar hanya data miƙe izimuwa ciki. Babu komai aciki sai duhu da ƙura. Babara ya gyara musu waje suka zauna.
Armad ya dubi halittar da suka kama. Kunnuwanta dogayene matuƙa kamar na zomo sannan kuma a fiƙe suke suna kallon sama. Fatarta fara ce sosai kamar ta Nostaljiya. Tana da kyawun fuska da madaidaicin jiki. Armad ya lura akwai tudu akan ƙirjinta saboda haka ya ɗauka macece. Bayan Baitin da Heeda ta bar masa na yaren Elburish akwai Baiti akan sunan ƙabilar wannan halitta dake gabansa. Sunan ƙabilar ELBIS. Amma abin mamaki babu komai banda wannan. Shin Hidaya ita ma bata san wannan ƙabila sosai bane ko kuma ta sani amma bata son gaya masa?
"Ya sunanki?"
Halittar ta dubi Armad cikin mamakin ya akai ya iya yarenta. "Suna na Dinanduil Sanfuil. Amma sanin suna na bazai maka amfani ba."
Armad ya dube ta tsahon daƙiƙa biyar sannan yaci gaba da cewa, "zanyi miki tambayoyi idan kin amsa dai-dai zan sakeki ki tafi. Kiyi sani cewa ina da fasahar dazan gane idan kin amsa min tambayoyina gaskiya ko kuma kinyi ƙarya." Armad ba ƙarya yayi ba. Hidaya ta bar masa fasahar [Saikika] wadda zai iya ganewa idan mutun yai ƙarya.
"A ina ƙabilarki ta Elbis suke rayuwa banda wannan gari? Kune ƙabilar da kuka rayu tun kafin Amri a doron ƙasashen ƙasa? Menene sirrin wannan gari naku da ba'a iya fita idan an shigo? Hoton bidiyo dana gani a tsakiyar gari mai yake nufi? Menene alaƙarku da dattijo Han'Diyuza? Sannan kuma tambaya ta ƙarshe menene alaƙarku da tsohuwar daular Wilbafos?"
Daga cikin Baitikan da sarki Eyriyon ya barwa Armad yaga cewa shi ne ya haɗa Tsohuwar-daula. Ya saka albarkatu na sihiri da abinci da kayan izza wanda zasu isa mutanen dake ciki rayuwa tsahon shekara dubu biyar masu zuwa. Eyriyon yayi hakan ne domin tseratarda iyalansa da sauran mutanensa yara da mata da tsoffi marasa ƙarfi. Eyriyon ya sakawa wannan duniya suna Tsohuwar-daula sannan ya sakko da ita ƙasashen ƙasa ana tsaka da yaƙin Rukunai Biyu. Idan yayi nasara ya ɗakko duniyar ya dawo da ita sama doron ƙasa na farko idan kuma baiyi nasara ba ya barsu a ƙasa.
A duk Baitikan da Eyriyon ya bari babu zancen ƙabilar Elbis saboda haka Armad yasan daga baya ƙabilar Elbis suka shigo cikin wannan Tsohuwar-daula. Tambayar ita ce ina asalin mutanenda Eyriyon ya saka acikin Tsohuwar-daular? Su waye ƙabilar Elbis kuma menene manufarsu?
Ɓangaren Han'Diyuza
A dai-dai lokacinda Armad yake ƙoƙarin zaƙulo bayani daga fursunan daya kama dattijo Han'Diyuza ya tsinci kansa a wata duniya ta musamman. Duniyar bata da ƙarshe. Wani wajen ƙanƙara wani wajen wuta wani wajen walƙiya. Dashi da wutarsa da Negrinkin Armad ta zuƙe duk wannan duniya ta cillosu.
Abu na farko da Han'Diyuza ya fuskanta shi ne ɓacewar izzarsa. Bashi da wani ƙarfi ko kaɗan ko motsi da gyar yake yi. Sannu a hankali ƙasa ta fara kama ƙafarsa tana haɗiyewa. A wannan lokaci ya fuskanci cewa yayi kuskere daya takali Armad. Wannan Armad ɗin ba irin wanda ya gamu dashi bane mai shekara hamsin da ɗaya.
Duk da daɗewarsa a duniya da sanin sirrin ƙasashen ƙasa bai san wacce duniya yake ba. Ba kuma shida hanyar tsira.
"Yanzu haka rayuwata zata ƙare..."
Yana cikin wannan tunani yaga hannu ya bayyana ta sama ya fincikoshi daga ƙasa. Hannun yana taɓa shi ya sume. Bai san inda knasa yake ba kuma abu na ƙarshe daya gani shi tsintar da yayi a fadar 'Sarkin sarki, sarki a sama, sarki a farkon lokaci'.
Fadar gaba ɗayanta akan iska take. Akwai Deba wanda tuni suka wuce makatin Lardin Deba suka kai matsayin Waadin Deba guda goma a tsaye suna jiran umarni. Kowanne acikinsu zai iya kashe Han'Diyuza da ɗan'yatsa. Biyar suna tsaye a ɓangaren dama biyar suna tsaye a ɓangaren hagu. Akwai wasu dattijai guda biyu a zaune kan ƙaramar kujera sun saka karagar mulkin a tsakiya. Akan karagar akwai wata kyakkyawar budurwa wadda idan ka ganta baza kace ta haura sha takwas amma a zahiri ta girmi yaƙin Rukunai-biyu. Tana da kunnuwa dogaye da farar fata mai haske irin na ƙabilar Elbis.
Akanta akwai kanbum mulki na ayrid mai mataki na ɗari (100). Abinda babu wanda ya taɓa gani a wannan zamani. Kai hatta Deba idan ka tambayesu zasu ce maka babu Ayrid mai mataki na ɗari. Amma akan kanbum mulkin wannan sarauniya irin wannan Ayrid suna jere a layi. Kayan jikinta na shuɗin haske ne wanda ya rufe mata tsiraici kuma a lokaci guda ya ɗaukaka darajarta. Idanunta nada ban mamaki: farin idon ya koma baƙi shi kuma baƙin ya koma baƙi. Acikin farin akwai zanen takubba bakwai.
Wannan mace ita ce shugabar Han'Diyuza kuma ita ce ta sakashi aikin gadin ƙofofi wanda duk ita ta haliccesu. Babu wanda yasan ainihin sunan wannan mace amma wanda suka santa sun san ana ce mata 'Sarkin sarki, sarki a sama, sarki a farkon lokaci'. Eh... mace ce amma kuma sarki ake ce mata. Ita ce take mulki a doron ƙasashen ƙasa tun Kafin Amri.
Han'Diyuza ya faɗi ƙasa yai gaisuwa sannan ya buɗe baki zaiyi magana amma dattijon dake zaune a ƙaramar kujerar dake hannun daman 'Sarkin-sarki' wanda akafi sani da wazirin-dama ya ɗaga masa.
"Koma gefe Mai-gadi Diyuza muna da baƙi."
Yana rufe baki sai ƙofar fadar ta buɗe. Ita kanta ƙofar takai tsayin zira'i dubu a tsaye da kwance. Anyi tane da baƙin dinare ziryan. Sannan kuma anyi mata ado da Farar-laya.
Mutun goma sha uku suka shigo. Mutun uku farko mai karatu ya sansu. Ba wasu bane illa Bihanzin da Maikironomad da Han'Ibal. Sauran sarakunan Jinzidal ɗin biyu sun saka Han'Ibal a tsakiya. Mutun goman dake bayan Bihanzin dukkansu Baƙaƙen Hankaka ne suka juye izuwa mutane. Babu wanda acikinsu bai kai matsayin Deba ba. Bihanzin yayi amfani da sabuwar fasahar jini-uku ya mai dasu Deba wanda zasu rikiɗewa izuwa mutane.
Suna shigowa suka tsaya a tsakiyar fadar. Bayan ƴan daƙiƙu Bihanzin ya wuce gaba izuwa karagar da Sarkin-sarki take kai. Deban dake tsaye suna gadin ta suka motsa amma tayi musu inkiya da babu ruwansu.
Sai da Bihanzin yakai dai-dai karagar sannan ya tsaya a kusa da ita. Gwiwarsa tana taɓa gwiwarta. Akai wani kallon-kallo mai cike da isa kafin duk su biyu su fashe da dariya.
Sarkin-sarki ta buɗe baki tayi magana da Elburish, "a lokacin kana yaro ɗan shekara ashirin da uku kazo neman aurena a wajen mahaifina ya ce maka baka kai ba. Yace idan ka mallaki fasaha mai girman izza ka dawo. Ka fiya naci Bihanzin. Gashi ka ƙara dawowa. Amma tunda ka takura zan aureka amma sadaki na shi ne karagar doron ƙasa ta farko. Kujerar tsohon can Kuyurussa'ayi. Ya tsufa kasheshi a yanzu bazai maka wahala ba ko?"
Bihanzin ya fashe da dariya ya ce, "kafin muje ga Kuyurussa'ayi ya kamata mu fara da share doron ƙasashen ƙasa. Dama can naki ne kuma yanzu zan dawo miki dasu."
Sarkin-sarki ta haɗe rai tsahon lokaci kafin daga bisani ta ce, "tsoron Kuyurussa'ayi kake ji?"
Bihanzin ya ɗora hannunsa akan cinyarta ya ce, "Ikwatora, Kurkukun Bango da kuma ɓangaren Kudu da Arewa na doron ƙasashe inda ake bautar Jinzidal zamu gama dasu a kwana sittin masu zuwa. Na gama tsara komai da komai a rubuce."
***
Babi na 198-200
***
Kwana bakwai kafin shigar Armad Tsohuwar-Daula....
•Sashin Ikwatora
•Ɓangaren Ikenga
Bayan gama ƴar gajeriyar fafatawa tsakanin Ikenga da Nusi Ikenga bai koma masaukinsa ba. Kai tsaye ya wuce izuwa wani daji kimanin tafiyar kilomita dubu tara daga inda yake. Wannan daji dai ba baƙo bane domin kuwa a nan ake aiwatar da gasar Baƙar-guguwa wadda ke zaɓar wanda zaiyi shugabanci a sashin ikwatora. A wajen aka zaɓi Nusi ta zama sarauniyar sashin ikwatora na shida.
Tun daga nesa zaka hangi ma'aikata sanye da kakin sojoji fari mai ratsin baƙi suna ta kai-komo. Babu wani mahaluƙi da yake da lasisin zuwa wannan guri ko waye. Hatta sarakunan ikwatora an ƙayyade musu lokacin zuwa. Sannan kuma idan suka zo sai an caje su matuƙa kafin su shiga. Abu ne sananne an hana shiga sashin wajen da makami saboda haka ko wuƙa babu wanda zaka gani da ita sai ma'aikatan su kaɗai. Suma kuma ma'aikatan basa shiga ainihin cikin wajen da makami. Idan zasu shiga sai dai su ajiye a waje.
Abin mamaki Ikenga na dira a kusa da wajen kai tsaye ya wuce ta tsakankanin mutanen babu wanda yace masa ƙala.
Wajen an rabashi gida uku. Akwai waje na farko wanda ya haɗa da manyan bishiyu na darbejiya a jere a layi sun yiwa waje na biyu ƙawanya. Waje na biyun bashi da faɗi sosai kuma yawancin ƙasar wajen akwai zanen hatimi akanta wanda yake hana duk wata halitta wucewa. Akwai haske dake tashi lokaci-lokaci daga wannan hatimai. Hasken yana bada launi-launi; wani baƙi wani fari wani ja wani shuɗi.
Waje na uku shi ne a tsakiya, yana da faɗin zira'i dubu. Wani irin ƙaton dutse ya tokare kowacce ƙurya; gabas da yamma, kudu da arewa. Saboda girman duwatsun ba'a ganin abinda ke gabansu sosai. Ikenga ya ƙuƙuta ya wuce dukkan masu tsaron wajen ba tare sun ganshi ba sannan yabi ta tsakankanin duwatsun ya shige ciki.
A tsakiyar wajen wani wawakeken rami ne ba'a gano ƙarshensa. Wata irin iska baƙa-ƙirin tana juyawa acikinsa. Idan ka ƙurawa iskar ido sai kaji tana janka ciki kamar mayan-ƙarfe. Sauti mai firgitarwa yana tashi daga ciki.
Ikenga ya riƙe ɗaya daga cikin duwatsun ya tsaya. A ransa yana cewa Ko ni idan na ƙarasa kusa halaka zanyi.
Can bayan ɗan-lokaci ya zaro wani kyalle daga aljihunsa. Idan ka lura da wannan kyalle zaka fuskanci ɓangarene daga rigar da Nusi ta saka a lokacin fafatawarsu da Ikenga. Babu wanda yasan yadda akai amma Ikenga ya faki idonta ya yagi rigar.
Kyallen na bayyana ya bada haske ruwan ɗorawa.
Ikenga yayi murmushi sannan ya ɗakko wata Farar-laya a ɗaya aljihunsa. Layar tana bayyana ita ma ta bada haske ruwan ɗorawa.
Wani murmushi na murna ya bayyana a fuskar Ikenga. Nan da nan ya maida kyallen aljihunsa ya juya ya ɓace. Ba jimawa ya dawo masaukinsu inda ya tararda Deniz Ururu aciki.
Ikenga ya dubeshi ya ce, "baka fita bane?"
Deniz Ururu ya gyaɗa kai a hasale ya ce, "mutanan garin nan ƴan ƙauye ne. Sun fiya kallo."
Ikenga yai shiru yana kallonsa kafin daga bisani ya fashe da dariya. "Baba Deniz, ai dole su kalleka sunga basamude. A wannan zamani babu samudawa irinku da yawa duk wanda ya ganku dole ya ɗaga ido. Ranar dana zama sarki zan nunawa kowa kai, daga ranar an daina kallonka."
Deniz ya haɗe rai ya harari Ikenga. Shima yasan dalilin da yasa ake kallonsa kenan. To amma abinda ya bashi haushi shi ne ya riga ya rage girman jikinsa ta hanyar amfani wani sinadarin magani amma duk da haka ba'a daina kallonsa ba.
Ikenga yayi murmushi. Ko kaɗan bai ɗauki hararar da Deniz yayi masa a wani abu ba. Idan akwai wani mutun da Ikenga yake girmamawa a duniya bai wuce Deniz Ururu ba.
Ikenga ya zaro kyallen rigar Nusi daga aljihunsa tare da Farar-layar da yayi amfani da ita ya nuna masa yana cewa, "Wannan layar Hidaya ce ta haɗa ta saboda haka tana ɗauke da wani gutsure na izzarta. Wannan kyalle daga jikin Nusi na yankoshi, yana ɗauke da wani gutsure na izzarta. Dukkan wannan abubuwa biyu sun bada launi iri ɗaya dana gwada su da Baƙar-guguwa. Baba Deniz, shin ka gane mai hakan yake nufi?!"
Deniz yai firgigit ya miƙe ya kwace kyallen da layar yana jujjuyawa. "Ni kuwa na gane! Bana gaya maka ba, dole akwai abinda yasa wannan yarinyar Nusi ta zama sarauniya a sashin ikwatora. Kaga yanzu mun samu dalili. Tayaya za'a ce wani bare daga can wani sashi da bashi da alaƙa da Ikwatora ya zo yaci gasar Baƙar-guguwa. Dole wani ne ya taimaka mata. Nayi tunanin mutane da dama amma ban taɓa tunanin Hidaya ce ta taimaka mata ba."
Ikenga ya ja dogon nunfashi sannan ya ce, "koma ta wace hanya Hidaya ta taimaketa bai shafemu ba. Babban abinda ya shafemu shi ne Hidaya ce ta taimaketa ta zama sarauniya, wanda hakan ke nuni da cewa Hidaya tana da iko akan Baƙar-guguwa. Bansan ya akai Hidaya ta sami wannan iko ba amma nasan cewa idan na bari wani ya mallaki ruhin Hidaya to lalle zai kawo min cikas a shirina. Saboda haka ya zama dole na shiga gasar samun ruhin Deban Hidaya."
Deniz yai shiru yana tunani kafin daga bisani ya ce, "muna da ruhin Deba a hannu wanda yakai matsayin ruhin Hidaya idan ma baifi ba. Ka riga ka gama sabawa da wannan ruhin Deba kuma a yau idan kana so zaka iya shiga matakin Deba. Kamar yadda kace idan wani ya mallaki ruhin Hidaya zai iya jawo mana cikas to amma kuma ba dole bane. Duk wanda zai mallaki wannan ruhi ba lalle bane yasan alaƙar Hidaya da Baƙar guguwa sannan kuma akwai hatsari matuƙa acikin gasar mallakar ruhin Deba, kafi kowa sani kaida ka taɓa shiga."
Ikenga yai shiru tsahon lokaci ya samu waje ya zauna. Lalle gasar samun ruhin Deba tana da matuƙar wahala. A ƙarshe ma akwai yiwuwar kowa ya rasa ruhin. Ya taɓa gwadawa baiji daɗi ba domin kuwa da kyar yasha. Amma kuma duk da haka idan bai shiga ba akwai yiwuwar wani ya mallaki ruhin wanda hakan zai jawo masa matsala.
Ikenga ya numfasa ya ce, "kada ka manta akwai sarakunan ikwatora wanda sun daɗe suna bincike kan dalilin zaman Nusi sarauniya kuma kawo yanzu nasan dole wani daga cikinsu ya gane sirrin. Bazan iya bari kujerar ikwatora ta kuɓucemin ba domin kasan shiri na zai wargatse idan hakan ta faru. Yau kwanan Hidaya ashirin da takwas dai-dai da mutuwa, a yau ruhinta zai shiga KWAZAZZABAN-MUTUWA dake BÁBILA a ƙasan Doron-ƙasa ta bakwai. Na yanke shawarar shiga wannan gasa saboda haka kayi shirya dakai zamu je."
Deniz yayi ajiyar zuciya domin yasan cewa bazai iya canjawa Ikenga zuciya ba. "Naji zaka shiga gasar to amma idan kayi nasara mai zakai da ruhin?"
Ikenga ya amsa da cewa, "Baba Deniz, kai ka riga ka zama Deba da kai zan bawa. B. Ururu yana da hanyar zama Deba ba tare da ruhi ba. Tsakanin Kána da Daddara zan bawa wani. Kaga idan na ƙarasa haɗewa da ruhina na zama Deba B. Ururu ya zama Deba muna da Deba guda huɗu kenan."
Deniz Ururu ya gyaɗa kai. Lallai mallakar ruhin Deba yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarawa runduna ƙarfi sai dai kuma akwai hatsari. Amma ya yadda da ƙarfin Ikenga saboda haka ya amince suka fara shiri.
Doron ƙasa na huɗu
Sashin Arewa
Garin Jekís
A wannan gari acikin kasuwa mutane ne ke tattauna wani gagarumin abu daya faru.
"Kaji yadda fafatawar ta kasance?"
"Naji mana! Yarima Hasana da yarima Niyashi ɗan marigayi sarkin Jinzidal Daljari sun fafata tsahon kwana bakwai a tsibirin Zanna amma babu wanda yayi nasara."
"Nima na karanta a jaridar aminiya. Ance Niyashi shi ne ya fara takalar sarki Bihanzin da faɗa. Ya nemi Bihanzin yazo su fafata. Amma maimakon Bihanzin ya bashi martani sai Hasanu ya fita. Ance fafatawar tayi tsamari sosai har saida suka baje tsibirin baki ɗaya. Amma daga ƙarshe babu wanda yayi nasara sai dai muggan rauni da suka samu."
Haka dai mutanen wannan gari dama na sauran sassa na duniya suka ci gaba da tattauna wannan batutuwa.
A fada kuwa Bihanzin ne ke zaune tare da ɗansa Hasanu yana masa bayani kan harkokin mulki na duniya.
Hasanu ya gyaɗa kai ya ce, "indai ruhin Hidaya ne kada ka samu damuwa kamar na kawo maka shi ne."
Hasanu ya tafa hannu baƙin sulke ya bayyana a jikinsa sannan ya miƙe ya nufi waje.
Bihanzin yai murmushi ya ce, "Ina da ruhin Deba wanda na ajiye maka wanda yafi na Hidaya ƙarfi. Saboda haka koda baka sami damar mallakar ruhin ba ka tarwatsa shi kowa ya rasa. Na baka dama kayi amfani da dukkan ƙarfin izzarka da jininka na Shishirui da sabuwar fasaharmu ta jini-uku LAIDÁN."
Hasanu ya juyo ya kalli mahaifin nasa sannan ya gyaɗa kai ya ce, "an gama ya shugabana."
Wata jar iska mai ƙarfi ta ɗaukeshi ya ɓace.
Hasanu na tafiya Bihanzin yai shiri ya nufi wajenda sukai zasu haɗu da sauran sarakunan Jinzidal domin zuwa fadar Sarkin-sarki.
Acan wata duniya...
Ƙabilar Elbis
Fadar Sarkin-sarki
Sarkin-sarki na zaune kan karaga tana wasa da carbin Ayrid a hannunta. A gabanta akwai wani saurayi wanda suke matuƙar kama. Yana sanye da jar tufa wadda akaiwa ado da gashin aljanar-giwa. Ita kuwa sarkin-sarki tana sanye da kayanta na haske. Duk sunyi shiru ba mai cewa komai.
Bayan tsahon lokaci ta buɗe baki ta ce, "ita ce ta farko data fara zuwa wannan gari ba tare da gayyata ba. Ta shigo da yamma liƙis kuma kafin magariba tayi mana sata ta gudu. Na daɗe inaso na kama ta amma ban samu dama ba. A halin yanzu ta zama ruhin Deva kuma abinda ta sata yana cikin ruhin nata. Babu wanda zai iya shiga gasar ruhin Deba sai Sammai. Kaine ƙanina uwa ɗaya uba ɗaya. Nayi amanna babu wani mahaluƙi dake matakin Sammai wanda zaici galaba akanka. Kaje ka kawomin ruhinta. Duk wanda ya shiga gabanka ka kasheshi, ko wayeshi."
Saurayin yayi murmushin mugunta tare da motsa kunnensa na dama kafin ya ɓace.
Doron ƙasa na farko
Dajin Bakin-wuya
Aljanu bakwai wanda tuni sun kai matakin Deba haɗe da Dordor bakwai suma matakin Deba da kuma mutane masu idanun Ururu suma guda bakwai. Deba ashirin da ɗaya sun saka shi a tsakiya suna kawo masa sara ta ko'ina. Saurayin mai idanun Ururu a tsaye yake ƙiƙam ko motsi bayayi. Duk wani duka da wata fasaha da suka jefo masa kawai tsayawa yake ya sameshi kai tsaye. Idan suka dakeshi sai kaga sun narke kamar ruwa. Jikinsa ko kwarzane babu.
Bayan tsahon lokaci ana abu ɗaya ya numfasa a hankali gami da girgiza kai ya buɗe idonsa.
A hankali ya furta, "[Sarautar Ururu]."
Yana rufe baki wani baƙin haske ya fice daga idanunsa ya daki Deban ashirin da ɗaya. Nan take suka sanƙame suka daina motsi. Jikinsu ya juye izuwa wani baƙin-ruwa suka zube a ƙasa matattu. Kaga Sammai mai take Deba kamar kiyashi.
Guda ɗaya daga cikin aljanun wanda yai ƙarfin hali ya fice da gudu ya nufi daji yana tsinewa kansa da gangancin da yasa ya takali wannan majanunin saurayi.
Saurayin ya murza ɗan'yatsansa biyu inda Taskar-ruhi ta bayyana a samansa sannan ta ɓace ta bayyana akan aljanin dake ƙoƙarin guduwa. Cikin ƙiftawar ido da bismilla Taskar-ruhin ta zuƙe aljanin ciki.
Saurayin ya kaɗe rigarsa ya ɓace. Bai bayyana a ko'ina ba sai a cikin maɗaukiyar fada. Anan ya tadda yarima mai jiran gado, yarima Dumaƙísu na zaune yana jiransa.
Yarima na ganin shigowarsa yai murmushi ya ce, "yakai ɗana Ƙaizadussa'ayi, kayi sani cewa nasan Hidaya sarai. Mun haɗu a lokuta da dama tun a farkon lokaci. Mun haɗu da ita tun kafin mu haɗu da Tarifil-fakta. Ruhinta daban ne. Ko badan muyi amfani dashi ba baza mu bari wani mahaluƙi ya mallakeshi ba. Na umarceka daka tafi Kwazazzabon-mutuwa dake Babila ka kawomin ruhinta. Zansa duk kafafan watsa labarai na doron ƙasa ta farko su haska fafatawar saboda haka ka nunawa duniya girman idanun Ururu. Ka nunawa duniya sarautar Ururu. Idan kaje Babila ka gaisheda Haruta da Maruta kafin ka wuce."
Yarima na gama magana ya ɓace. Tun bayan sanda Hidaya ta ɗaure ruhinsa a filin yaƙi yake samun matsala. Da farko lissafi ya nuna sai yayi wata shida zai kwance. Amma saboda taimakon jami'ar Ururu da ƙannen ubansa Haruta da Maruta wanda malamai ne a jami'ar izza ta farko dake Babila sun rage lokacin ya dawo kwana sha uku. Amma duk da haka ruhinsa bai dawo dai-dai ba, saboda haka baya iya daɗewa a waje. Idan akwai wanda ya karɓi shedar Hidaya to shi ne.
Ƙaizadu shi ne kaɗai ɗan yarima Dumaƙisu. Tunda suke Dumaƙisu bai taɓa neman wani abu a gurin ɗansa ba sai wannan rana.
Ƙaizadu yai murmushi. A ransa yana cewa, Wannan shi yafi komai sauƙi. Idan duk ruhin Deban dake doron ƙasashen ƙasa kake so zan kawo su.
Nan take Ƙaizadu yayi shirin yaƙi yasa aka buɗe masa ƙofa ya sakko doron ƙasashen ƙasa akan dokinsa na baƙin ƙarfe. Duk wata izza da wata fasaha babu wadda Ƙaizadu bai fito da ita ba domin shi baya raina yaƙi. Ko waye abokin gabarsa baya rage komai. A kullum yana fita da dukkan ƙarfinsa domin ya yadda cewa ɗan hakin daka raina shike tsone maka ido.
Kamar haka a dukkan faɗin duniya ƴaƴan manyan sarakuna da ma'abota izza suka rinƙa yin cincirindo domin fita neman ruhin Heeda. A ɓangare guda kuma ƴan kallo sun taru a dukkan saƙo da loko na faɗin duniya. Duk inda kaje zaka ga hoton bidiyo na tashi ana haska wannan gasa. Irin wannan bidiyo shi Armad ya gani acikin wannan gari. Kasancewar suna cikin kurkuku labari baizo musu ba.
Bayan kwana biyar da fara wannan gasar mutane huɗu sunyi suna matuƙa. Babu wanda baiga fuskarsu ba tun daga doron ƙasa na ɗaya har zuwa na bakwai. Wannan mutane sune wanda Armad ya gani akan faifan bidiyon dake tsakiyar garin wato Ikenga, Ƙaizadussa'ayi, Hasanu da kuma Randuil Abigail ƙanin sarkin-sarki ɗan ƙabilar Elbis.
Ɓangaren Armad
Armad bashi da masaniya akan dukkan wannan shirye-shirye dake afkuwa a faɗin duniya domin mallakar ruhin yayarsa. Lokaci na farko daya fuskanci abinda ke faruwa shi ne acikin wannan gari bayan yaga hoton bidiyon. Tuni Armad yayi ƙoƙarin fita daga garin domin zuwa ya shiga gasar to amma ya haɗu da Han'Diyuza. Gabda ya gama da Han'Diyuza ƴan ƙabilar Elbis guda uku suka bayyana.
Duk da ƙara ɓata masa lokaci amma yasan zai samu bayani daga garesu. Hakan nema yasa ya tara hankalinsa yana yiwa wannan mata mai suna Dinanduil Sanfuil tambayoyi.
"Ki bani amsar tambayoyina daki-daki kuma acikin tsari."
Matar mai dogayen kunnuwa tayi ƙiƙam tana kallonsa bata da niyyar amsa masa tambayoyinsa ko kaɗan.
Armad ya dube ta ya ce, "nasan mai kike tunani; idan ma kin amsa ko baki amsa ba kasheki zanyi. Amma kinyi kuskure. Amsarki kawai nake buƙata kuma idan kika amsa zan sakeki ki tafi. Amma bani da lokacin ɓatawa akanki. Na baki minti ɗaya, idan baki amsa ba zanyi abinda baza kiji daɗinsa ba."
Matar mai suna Dinanduil Sanfuil ta ƙeƙasa ƙasa taƙi magana. Acikin idanunta akwai girman-kai da ƙafafa. Armad yayi murmushi tare da tashi daga inda yake ya ɗora hannunsa akanta.
Acikin Baitikan Hidaya akwai Baiti na musamman kan fasahar [Saikika]. Wannan Baiti sunansa [Fassara] kuma ɗaya ne daga cikin fasahohin dake ƙarƙashin fasahar [Saikika]. Kamar yadda aka sani fasahar [Saikika] tana bawa ma'aboci izza damar ya sarrafa tunanin abokin gabarsa. To abin ba anan ya tsaya ba. Akwai fasahohi na sarrafa tunani kala-kala. Akwai wanda suke iya gogewa mutun tunaninsa su sa ya manta wani abu, irin wannan su ake kira da [Gogau]. Akwai wanda suke ƙirƙirar tunani na daban su saka acikin kwakwalwar mutun wanda su ake kira da [Ɗarsau]. Akwai wanda suke iya karanta tunanin mutun suga mai yake tunani irin wannan su ake kira da [Buɗau]. Akwai na mugunta wanda suke iya tarwatsa tunanin mutun baki ɗaya su sa ya haukace, irin wannan su ake kira da [Ɓallau].
Fasahar [Fassara] a ƙasan fasahar [Ɓuɗau] take. Misali idan muka ɗauki fasahar [Saikika] a matsayin sarki to fasahar [Gogau] da [Ɗarsau] da [Ɓallau] da [Buɗau] duk hakimaine dake ƙasan sarkin. Ita kuma fasahar [Fassara] dagaci ce a ƙasan hakimi.
Illar fasahar [Saikika] shi ne tana da illa ga kwakwalwar wanda akayiwa. A sau da dama duk wanda akaiwa [Fassara] yakan iya mutuwa ko kuma ya samu taɓin hankali musamman idan wanda yayi yafi ƙarfin izzar wanda akayiwa. Hakan ne yasa Armad ya tausayawa wannan mace amma tunda baza tayi magana ta sauƙi ba babu wanda zai iya kare ta daga ƙarfin fasahar Armad.
Cikin daƙiƙa bakwai duk wani abu dake cikin kwakwalwar Dinanduil Sanfuil ya bayyana acikin kansa.
"Shekararki ɗari shida da uku a duniya.
"Ke ƴar gidan Sanfuil jikar Zarfuil ce.
"Kina daga cikin rundunar leƙen asiri ta birnin Ƙilsuir wanda shi ne sunan wannan gari.
"Akwai mutane aƙalla dubu ɗari shida acikin wannan gari kuma da dama sunga shigowarmu. Mutanenki suna amfani da ƙololuwar fasahar Yanayin-izza wajen ɓoye kansu da ƙanshin jikinsu da izzarsu tayadda ba mai ganinsu.
"An haifeki acikin garin nan amma ƙabilarki ta Elbis ba sune na farko a wannan gari ba. Hasalima yaƙi sukai da asalin mutanen garin suka kashesu.
"Ƙabilar Elbis yawanci suna rayuwane a tsakankanin doron ƙasashe; ƙasashe kamarsu koriyar duniya. Wasu kuma suna rayuwa tare da mutane. Wasu kuma su kwace garuruwa masu albarkatu kamar su Tsohuwar-daula su zauna. A duk inda ƙabilar Elbis suke suna amfani da ƙololuwar fasahar Yanayin-izza su ɓoye kansu tayadda babu wanda yake iya ganinsu ko jinsu. Hakan ne ma yasa wasu suke kiransu da DAULAR-ƁOYE.
"Han'Diyuza shi ne mai kula da ƙofofin garuruwan wannan ƙabila ta Elbis wanda hakan ne yasa Armad ya gamu dashi a baya sanda zai ratsa ta tsakanin doron ƙasa ta uku data huɗu.
"Abu biyu ne yasa ba'a iya fita daga garin. Na farko Han'Diyuza wanda yakai matakin Lardin Deba, sannan na biyu kuma shi ne wani ɗalasimi wanda ƴan ƙabilar Elbis ne kaɗai suka sani."
Nan take Arnad ya binciko wannan ɗalasimi daga kwakwalwar Dinanduil ya haddace shi.
Wannan sune kaɗan daga cikin abubuwan da Armad ya gani acikin kanta. Haɗe da bayani akan abinda hoton tsakiyar garin ke nufi.
A dai-dai wannan lokaci hanci da idanun wannan mace ya fara zubarda jini saboda ƙarfin fasahar da Armad yake amfani akanta. Amma abubuwa biyu suka sa Armad yaƙi tsayawa. Na farko yana so ya gane sirrin yadda suke amfani da fasahar [Yanaƴin-izza] su ɓoye jikinsu. Na biyu kuma abinda ƴan ƙabilarta sukaiwa mutanen Wilbafos da suka tarar acikin daular. Sun kwace musu gidansu kuma sun kashesu.
Armad ya ƙara danna kai cikin kwakwalwarta. Kan kace meye wannan yaga komai. Yana ɗauke hannunsa ta zube a ƙasa a mace.
Armad ya dubi Cokali da Babara ya ce, "muje zuwa naga duk abinda nake so."
Take suka fito daga cikin kogon suka nufi ƙofar gari. Suna zuwa ƙofar Armad ya kirawo ɗalasimin daya gani akan Dinanduil ƙofa ta buɗe.
Babara ya dubi Armad ya ce, "shin baza mu ɗau fansa akan wannan mutane ba? Sun kashe kakannin su Lamarudu da duk mutanenda Eyriyon ya bari. Sannan kuma sun sace duk dukiyar da Eyriyon ya bari. Ina ganin sun cancanci hukunci."
Armad ya juyo ya kalleshi a nutse ya ce, "ai wannan dole ne. Ina mai tabbatar maka sai na ƙone su gaba ɗaya da walƙiyata da maidasu toka. Acikin kwakwalwar wancan matar na ga bayani akan yadda ta koyi wancan fasaha da suke ɓoye kansu da ita. Mataki na farko sai mun koyi wancan fasaha zamu yaƙe su; suna ganinmu muna ganinsu. Amma kayi sani cewa a halin yanzu ina da abinda yafi wannan muhimmanci."
Cokali ya ɗagowa Armad jakardake hannunsa ya ce, "na tattaro dukkan kayan da mutanen cikin kogon can suka bari. Ina kyautata zaton sune ragowar mutanen Wilbafos wanda suka gudu ɓuya a daji. Rashin abinci da yunwa yasa suka rasu."
Armad da Babara suka gƴaɗa kai alamun amincewa.
Armad ya ce, "ka riƙesu idan na dawo zan duba."
Cokali da Babara suka zare ido suka kalleshi cikin tambaya. Ina kuma zaije bayan ga ƙofa ya buɗe?
Armad yai ajiyar sannan ya kwashe labarin dukkan abinda ke faruwa da ruhin Hidaya ya gaya musu.
"Saboda haka daga nan zamu rabu. Zan koma cikin wannan gari nayi amfani da Ayrid ɗin dake nuna hoton bidiyon can na shiga wannan gasa. Bazan bari wani ya mallaki ruhin Hidaya ba koda zan rasa raina."
Kafin Cokali ko Babara suyi wata magana Armad ya watsosu waje ta cikin ƙofar sannan ya koma cikin garin.
Comments
Post a Comment