"Suna na Nusi KIL-ZANKI. Nazo ne akan zancen ɗan uwana Armad Wilbafos."
Sarkin ya ɗan haɗe gira na ƴan dakiku kafin ya tambayi dogarin dake bayansa wani abu cikin murya ƙasa-ƙasa. Nusi bata ji mai suka ce ba duk kuwa da cewa idanunta na kafe a kansu.
Sarkin na zaune cikin isa da izza ya hakimce kan karagarsa. Kana gani kasan ya cika ya tumbatsa yayi tamasi. Alkyabbar dake jikinsa kurum anyi tane da audugar jamsika, sannan kuma anyi mata kwalliya da gashin bakin muridin aljani. Watakila sabida kwarjinin wannan alkyabba ba lalle mu iya gane ainihin ƙiba da girman dantsen wannan sarki ba. Amma tabbas sarkin ba siriri bane domin kuwa yakai tsayin zira'i arba'in. Fuskarsa baƙa ce wankan tarwaɗa kamar ta Nusi. Wuyansa dogo ne kuma kakkaura. Ga tsayuwar kafaɗa madaidaiciya. Idanunsa da goshinsa suna nuni da tsantsar sani da daɗewa a duniya. Akwai wani abin mamaki da idanun wannan sarki. Idan ka kallesu daga nesa zaka ce ruwan ƙasa ne to amma idan ka matso kusa sai kaga abin ba haka bane. Wato wani littafi ne launin ruwan ƙasa wanda ya maye gurbin baƙin idon tayadda idanun suke bada launin ruwan ƙasa duk kuwa da cewa farare ne. Akwai baƙin gashin-ka da baƙin gashin-baƙi a kansa da fuskarsa wanda ko kaɗan basa nuna alamun daɗewar da wannan mutun yayi.
Yana zaune shirim akan babbar karaga samfurin adawa wadda aka gina da itacen ƙanƙara, sannan kuma akai mata ado da zanen ɗalasimai.
Sarkin ya ɗan muskuta kan karagarsa a hankali sannan ya ɗaga kai ya dubi Nusi.
Dogarin dake bayansa ya dube ta ya ce, "kici gaba da magana, amma kisan mai zaki faɗa domin zaki fuskanci hukunci dai-dai da abinda kika faɗa. Kuma kada ku manta nan gida ne na sarkin jinzidal kuma bama tare da iyalan Wilbafos."
Cokali najin haka ya shige gaba ya fuskanci sarkin tare da yin gyaran murya. Bayan ya tabbatar ya tattara hankalin kowa acikin fadar sai ya juya ya nuna Nusi da ɗan yatsa ya fara bayani. "Wannan ita ce Nusi ƴar Affashata, ƴar Dadiyadudu, ƴar Dilarumu, ƴar Yusufu, ƴar Djinn, ƴar KIL-ZANKI na Farkon Lokaci. Ita ce mace ta farko data zama ƴar majalisar a garin Khan. Ita ce Jaura tashi matattu. Ita ce Kibiya fasa bangon kudu da arewa. Ita ce Nusi-ya sarauniya ta farko a daular ikwatora. Ita ce Mahdiya mai dogon zamani, tayi faɗa da samudu da Ururu amma har yanzu an kasa ganin bayanta."
A karon farko wani ɗan mamaki ya gilma ta gefen bakin sarkin. Dogarin dake bayansa ya matso gaba ya durkusa cikin ladabi yana kallonsa cikin biyayya da sadaukar da kai. Bayan ɗan lokaci sarkin ya gyaɗa masa kai. Dogarin ya miƙe ya fuskanci su Nusi ya fara bayani. "Kuna tsaye a gaban babban sarki Maikiro'Abbas na Farkon Lokaci. Mutun na farko da akai wa sarauta a Dogon Zango, marubucin farko, mai ruwa da ƙanƙara, mai Non-toch-teka, mai littafin marubutan farko, mai rana da wata. Maulana mai Anbalu da Kulu da Fulafunu. Uban Rabi, uban Shema'u. Uban Abba, uban Umaru, uban Basharu. Sarki a Farkon Lokaci, sarkin a Dogon Zango, sarki a Rawar Sani."
Gumi ya fara ketowa Cokali bayan jin wannan kirari da falaloli na babban sarki Maikiro'Abbas.
A haka aka ci gaba da kallon-kallo kowa yana jiran ɗan uwansa ya motsa. Can bayan ɗan lokaci Nusi ta matso gaba ta tsaya. "Ɗan uwana Armad Wilbafos..."
Sarki Maikiro'Abbas ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. "Waye Armad ɗin nan ne da kike ta faɗa."
Nusi ta yamutse fuska kamar tana mamakin yadda zaice baisan Armad ba. "Armad Wilbafos fa."
"Nasan Wilbafos amma bansan Armad." Inji Abbas.
Nusi ta kada baki ta ce, "wanda ka bawa littafin takobi acikin Non-toch-teka."
Maikiro'Abbas yayi murmushi a karo na farko tare da cewa, "ƴar budurwa, ina kyautata zaton baki fahimci yadda fasahar Non-toch-teka take aiki ba. Babu wanda nake bawa wani abu." Ya gyara zama kaɗan sannan yaci gaba da bayani. "A safiyar duniya, lokacin ina yawon duniya, naci garuruwa da dama a yaƙi kuma na ribaci abubuwan amfani na izza da dama. Bayan da girma yazo min a shekarun ƙarshe-ƙarshen Farkon Lokaci sai na dawo gefe guda na zauna. A wancan lokaci jama'a masoya suka taru suka naɗani sarki. A duk sanda akai zaman fada idan mai buƙata yazo sai na dauki wani abu daga cikin kayayyakin dana samo a tafiyata na bashi. A haka labari ya bazu a faɗin duniya har mutanen dake zuwa waje na da buƙata suka fara yawa. A ƙoƙarina na bawa kowa damar da yake buƙata sai na rubuta fasahar Non-toch-teka. Sannan na samar da ita, kuma na saka dukkan kayana aciki, sannan na bawa kowa damar ya shiga ya ɗauka. Iyakacin izzarka iyakacin abinda zaka samu. Ni kaina ban san iya adadin abubuwan da mutane suka ɗauka aciki ba. Watakila ma yanzu babu ragowar komai aciki. Idan ɗan uwanki ya samu wani abu to bani da hannu aciki."
Nusi da Cokali suka ɗan yamutse fuska. Ko kaɗan basu taɓa tunanin haka Non-toch-teka take aiki ba. Akwai lokuta da dama da suka tattauna da Armad akan yadda ya samo littafin takobi kuma mafi yawansu sun yadda cewa Maikiro'Abbas yana da hannu aciki. Abinda basu gane ba shi ne meye alaƙar Armad da Maikiro'Abbas. Abinda ya kawo Nusi wannan fada kenan. Tana so ta gano wannan alaƙa, kuma idan da dama tasa sarkin ya taimaki Armad.
"To mai yasa ka bashi Al'yaya?" Inji Nusi fuska cike da alamun tambaya.
Maikiro'Abbas yayi ɗan numfashi ya girgiza kai. "Ƴar budurwa, nifa ban bawa wannan Armad ɗin da kike faɗa komai ba, a haka tsarin gari na yake. Idan ka shigo ta ƙofa to akwai na'ura da zata duba jikinka. Idan akwai ƙarfin jini wanda ya dace da Al'yaya to anan zaka iya samun Al'yaya. Shikenan kawai."
A wannan lokaci Cokali yasa baki. "Mai martaba, idan na fahimce ka jinin mutum ko kuma ƙabila su ne suke bada Al'yaya da kuma fasaha acikin Non-toch-teka, to kaga kenan dole akwai wasu kabilu daka zaba ka saka wanda su kaɗai zasu yi aiki. Haka ne?"
Maikiro'Abbas ya gyaɗa kafaɗa. "Hakane. Amma mai kake so kace?"
Cokali yayi murmushi ya risuna. "Mai martaba, kamar kai ne ka tsara wannan kabilu, ko?"
"Ni ne na tsara su," inji Maikiro'Abbas. "Amma kuma hakan bashi yake nuna ina da alaƙa da kabilun dana saka ba. Da ina da alaƙa dasu to da Bihanzin bai mallaki Al'yaya ba. Mutane da dama (maƙiyan wannan daula) sun sami fasahai acikin Non-toch-teka badan ina so ba. Ina so ka gane cewa ita daular maikironomada ta kowa ce." Ya nuna Nusi da ɗan yatsa. "Kamar yadda ƴar'uwarka tana bakuwa amma ta zama ƴar majalisar Khan, haka kowa ma zai iya samun wani abu indai ya dage."
Nan fa aka fara kallon-kallo. Duk wata alaƙa dasu Nusi suke tunani a tsakanin Armad ko gidan Wilbafos da Maikiro'Abbas ta ɓace. Wato ta wata fuskar sai kaga kamar Maikiro'Abbas yana taimakon Armad, amma kuma ta wata fuskar sai kaga maƙiyi ne. Misali kaga dashi aka yaƙi Hidaya a faɗan ƙarshe. Amma kuma ya bawa Armad littafin takobi da Al'yaya. Kuma duk abinda zai faɗa Nusi ta riga tasan babu yadda za'ai ace ya bada littafin takobi a bisa rashin sani. Dole akwai wata kullalliya a ƙasa.
"To idan baka da alaƙa da Armad to ai kasan iyayensa - Taidara, Zaikid, da Fatima."
Maikiro'Abbas ya haɗe gira cikin mamaki. "Wai Armad ɗin da kike ta faɗa dama ɗan wajen Fatima ne?"
Kafin Nusi ta bada amsa sai dogarin sarkin dake gefe ya durkusa yayi wa sarkin raɗa a kunne. Sarkin ya ƙara haɗe fuska. Nan take ya zira hannu a aljihunsa ya zaro jaridar Aminiya ya cilla wa Nusi. Abin mamaki shi ne jaridar tafi girman aljihunsa amma kuma ta shiga lafiya kalau ko tudun ta ba'a gani. Kai kace ba daga aljihun ta fito ba.
Nusi ta cafi jaridar ta fara karanta shafin farko wanda ke ɗauke da hoton wata mace a durkushe kan gwiwowinta cikin ankwa.
***
Babbar ƙungiyar mayaƙan Ururu ta yanke wa Fatima Wilbafos hukuncin zama baiwa har abada sabida laifin yin kutse a doron ƙasa ta farko. Za'a siyar da ita a doron ƙasa ta biyu, ranar Alhamis da zarar an gama jinzidal.
***
Rai a ɓace Nusi ta mikawa Cokali jaridar shima ya karanta. Ranar talata mai zuwa wato nan da kwana biyar kenan za'a gudanar da gasar jinzidal a doron ƙasa ta biyu. Kaga kenan bayan kwana biyu a ranar alhamis za'a gudanar da cinikin bayi a siyarda Fatima. Babu labarin Zaikid aciki saboda haka basu da cikakkiyar masaniyar a ina yake ko kuma mai ya faru dashi.
Dogarin dake gefen sarki ya katse su da cewa, "wai ku mai ya kawo ku ne?"
A zahiri Nusi zuwa tayi ta nemi taimakon Maikiro'Abbas Abbas wajen nemo Armad kasancewar sati biyu kenan babu labarin sa. To amma a wannan lokaci kalmomin suka maƙale a bakinta. Tun farko dai tayi tunanin akwai wata boyayyiyar alaƙa a tsakanin Armad da Maikiro'Abbas wadda zata iya sawa sarkin ya taimaki Armad, to amma a halin yanzu ta gano cewa abin ba haka yake ba. Akwai lauje acikin kullin.
Cokali yayi ta maza ya shige gaba. "So muke ka taimaki Armad wajen karya cinikin bayi."
Nusi, da dogaran dake fadar, da sarkin, dama duk wani wanda ke cikin fadar ya juyo da sauri ya kalli Cokali. Anya kuwa acikin hankalinsa yake?
A wannan lokaci sarki Maikiro'Abbas yasa aka sallami kowa daga fadar. Daga shi sai dogarinsa sai kuma Nusi da Cokali. Bayan sun samu nutsuwa sarkin ya dubi Cokali ya ce, "bani dalili guda ɗaya tak da zai hanani yi maka hukuncin kisa. Kasan cewa abinda ka faɗa zai koma kunnen Ururu, kuma magana zata iya zama wata iri idan banyi maka hukunci ba."
A lokacin Cokali ya fara yaƙe. Shi kansa bai san dalilin da yasa ya faɗi haka ba. Domin su zo ne kurum su nemi taimakon Maikiro'Abbas wajen nemo Armad, ko kaɗan babu lissafin su gayawa sarkin zasu tarwatsa cinikin bayi ballantana ma su nemi taimakonsa. Musamman duba ga cewa sarkin ɗaya ne daga cikin sarakunan jinzidal kuma shi aka naɗa shugaban gasar jinzidal ɗin da za'a fara nan da sati guda.
"Ah... kayi haƙuri da abinda kanina ya faɗa. Ba haka yake nufi ba." Inji Nusi cikin risunawa tana janyo Cokali baya.
Sarkin yayi shiru yana kallon su kafin daga bisani yayi ajiyar zuciya ya nuna Nusi da ɗan yatsa. "Ki gayamin gaskiya, meye ya kawo ki nan?"
Nusu ta amsa da cewa, "nazo ne domin a taimaka min na nemo ɗan uwana Armad."
Sarki Maikiro'Abbas ya ƙura wa Nusi ido yana tunani. Zaiyi wuya su gane abinda sarkin yake tunani domin lallai fuskarsa ba zata karantu a wajen ƙaramin mai izza ba.
"Mai zaki iya yi wajen cimma wannan burin naki?" Inji shi.
"Komai." Inji Nusi.
Maikiro'Abbas yayi dariya har saida ya tashi daga kan karagarsa ya nufi inda take. Yana zuwa ya tsaya a gabanta. "Zaki iya bada ranki?"
Cokali na gefe yayi caraf ya ce, "banda rai dai."
Ita kuwa Nusi bata ce komai ba. Tasan lallai Cokali bazai bari ta mutu sabida wani ba, komai wuya.
Maikiro'Abbas yayi ajiyar zuciya tare da fara jawabi da cewa, "kunsan kowa yana da iyakar shekarun izzarsa. Idan ka ƙarar da naka to babu yadda za'ai ka ci gaba da rayuwa. Hasalima akwai daɗewar da ma'aboci izza zaiyi a duniya koda ƴaƴan Wilbafos basu isa su ceto shi ba. Ina daga cikin kaɗan ɗin ƴan adam wanda sukai wannan daɗewa. Kuma kamar kowanne mutum bana son na mutu. Akwai hanyar dana samar wadda zata dauwamar dani a ban ƙasa. Ina buƙatar wasu sinadarai na ƙarasa haɗa ta. A hirar da mukai da baba Dalja kafin ya rasu ya gayamin tarihinki da kuma alaƙar ki da ɗansa Nazára. Ina ganin jininki zaiyi abinda ake so wajen samarda wannan fasaha tawa. Amma bazan ɓoye miki ba, a sakamakon hakan zaki rasa ranki."
"Mai kake buƙata?" Inji Nusi kai tsaye.
"A'a fa, koma me kake so baza ka samu ba. Idan zaka taimaka mana a haka ba tare da mun biya komai ba ka taimaka, idan kuma baza ka taimaka ba shikenan."
"Mai kake buƙata?" Nusi ta maimaita tambayarta kamar ma bata ji abinda Cokali ya faɗa ba.
"Jininki da ruhinki. Bayan nan zaki yi wata guda kalau kafin a hankali ki fara rashin lafiya sannan kuma daga bisani ki mutu." Maikiro'Abbas yayi mata bayani.
Nusi ta ɗaga kai ta kalleshi ido cikin ido, ta ce, "mai zakai min a maimakon haka?"
"Komai. Zan biya miki buƙatar ki guda ɗaya ko mecece. Koda kuwa daura siddi na fita yaƙi da Ururu ne."
Nusi tayi shiru tana tunani. A lokacin hankalin Cokali yayi dubu ya tashi. Ya jata gefe yana cewa, "kada ki sake ki yadda da wannan abin. Shi kansa Maikiro'Abbas ba abin yadda bane, kuma koma da gaske yake akan me zaki mutu sabida wani ya rayu. Wannan ba zance bane. Kawai mu haƙura mu ci gaba da neman Armad. A hankali zamu samo shi."
Nusi tayi wa Cokali murmushi sannan ta juya ɓangaren da Maikiro'Abbas yake tsaye, tace, "na yadda."
Comments
Post a Comment