Babi na 26 : Littafin Takobi
Bayan ya karanta wasu ɗalasimai, irin ƙofar da suka shigo ta bayyana a gabansu, suka buɗe gami da ficewa.
A wannan rana sun kusan kwana talatin kenan aciki, kuma tuni mutane suka daɗe da cika a wajen ƙofar.
Da dama ma tuni sunzo sun tafi. Musamman tunda ba kowa ke daɗewa ba.
Kuma wasu kawai siyan makami, ko kuma Ayrid ko kuma wani laƙanin, kawai suka zo siya. Wanda kuma sunfi kowa yawa.
A saboda hakan nema, da dama basu wani kula da fitowar su Armad ba, waɗanda kuma sukai sauri, suka ɓace acikin jama'a suka kama hanyarsu.
Basu daɗe ba, suka iso gida ba, inda suka tarar kamar ansan da zuwansu anyi matuƙar ƙawata gidan tun daga nesa ƙanshi yake tashi.
Kuma dai duk da babu mutanen da aka gayyata sabida Nusi wadda ita ce muƙaddasin haɗa komai, ta tabbata komai yayi kama da na musamman a wajen.
Suna isa da ita da Cokali da sauran kuyangin gidan suka taryesu, inda suka shiga ciki tare, zuwa babban falon gidan da aka shirya domin aci asha kawai.
Labari na farko daya isa kunnen Armad shi ne, tun kusan kwanaki ashirin da suka wuce Nusi ta fito daga wannan kogo mai inganta jinin Maikironomada a jikin mutun, kuma ta sami sa'a, ta sami abinda ba'ai tsammani ba. Wato kaso SITTIN na jinin Maikironomada.
Tun a washe garin ranar mutanen ta na birni da kewaye suka so su haɗa mata walima amma taƙi.
Daga baya, bayan ƴan kwanaki an sanar da cewa ita ce ƴar majalisa ta gaba da za'a rantsar a wannan gari na Khan.
Mutane da dama sun nemi su haɗa mata gagarumar walima, kai aciki harda shugaba Sahabi ma, amma taƙi.
Ta bada uzurin ai a ƙarshen shekarar, wato nanda wata bakwai akwai taro da za'ai na musamman saboda ita, na rantsar da ita, saboda haka a yanzu basai sun wahalar da kansu ba.
A zahiri kwata-kwata basu ji daɗi ba, amma haka suka haƙura sabida sun san a irin halinta bazata canja ra'ayi ba.
Babu wanda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa taƙi sai Cokali da sauran mutanen gidanta.
Abinda kuwa ta gaya musu shi ne, tayi amanna a ranta cewa Armad ƙaninta zai samo babbar Izza a Non-toch-teka, saboda haka, tafi so ta bar walimar ta idan ya fito sayi tare.
Taso ta gayawa mutanen ta kamarsu Shugaba Sahabi, cewa ta ɗaga walimar ne kawai akwai abinda take jira, kuma idan yazo zata gayyace su, amma taga bata so ko kaɗan tayi abinda zaisa sunan Armad ya watsu a gari, saboda haka ta bar zancen kuma ƙulla aniyar su kaɗai ma sun isa suyi walimarsu.
Duk kuma maiso ya taya ta murna yayi mata a babban taron da za'ai na ƙarshen shekara.
To da yake katin shedar dasu Armad suka yi amfani dashi wajen shiga Non-toch-tekar nata ne, saboda haka suna buɗe ƙofar ta sani, kuma ta tashi shirye-shirye.
A wannan daren sunci sunsha, musamman idan ka ɗauki Armad da Cokali waɗanda sukai ta rawa.
Suna gasa tsakanin irin rawar mutanen ƙasa ta uku da kuma ƙasar Maikironomada, daga ƙarshe dai aka cinye Armad, inda bayan sun gama kowa ya zaɓi rawar Cokali akan ta Armad, sai mutun ɗaya kaɗai.
Wadda ita ce Nusi, Wadda ta zaɓi ta Armad, amma ita ma daga gani kara tai masa, kawai.
Daga baya dai Armad rai cike da baƙin cikin rasa wancan gasa yace ayi gasar shan fura.
To anan ne ya cinye cokali, saboda saida ya yasha daruka da dama har ya kasa tashi, waɗannan kuyangi sukai ta latsa masa ƙaton cikins suna tsokanarsa.
Haka dai sukai ta raha, suna ci suna sha suna dariya, harya zuwa kwana kusan biyu.
A rana ta uku ne, kowa ya haɗa baki wajen cewa suna son gasar waƙa tsakanin Nusi da Armad.
Armad baiso wannan gasa ba, saboda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa wata waka mai daɗi ba.
Kai ko haddace wa yayi idan yazo bata daɗi.
Amma babu yadda zaiyi tunda kowa ya haɗa baki yana so ayi.
Saboda haka ya ce Nusi ta fara, wadda tun ɗazu take masa dariya.
Nusi ta tashi ta fara waƙa amma kai da kaji kasan wasa kawai take don kada jikin Armad yai sanyi.
Amma abinka da cewa dama tana da zaƙin murya sosai duk da haka saida waƙar tasa masu sauraro nishaɗi.
Bayan ta dawo ta zauna Armad wanda ke zaune yana ta tunanin wanne uzuri ya kamata ya bayar, amma ina kafin yai wata-wata Cokali ya jashi tsakiyar fili.
Murya cike da dariya, Cokali ya ce, ''bari na samo garaya ta nayi maka kiɗa.''
Fuskar Armad babu annushuwa ko kaɗan, saboda da yana murnar yasha da nasara ɗaya, rashin nasara ɗaya, amma yanzu yasan lallai ga wata rashin nasarar nan tazo.
Bayan ya ɗau lokaci yana raba ido daga kan wannan zuwa wannan, su kuwa dariya kawai suke suna nishaɗi, kai hatta waɗannan kuyangi ba'a barsu a baya ba.
Cokali kuwa yama kasa zama, yana gefen Armad furkarsa na nuna alamun tausayi amma kana kallon cikin idonsa kasan dariya ce kawai fal aciki.
Can Armad yana cikin wannan hali idanunsa suka kai kan Nusi tana murmushi, a wannan lokaci kawai wata dabara tazo masa.
Kawai ya buɗe baki ya fara waƙa;
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Djinn Djinn
Wannan waƙa ta Armad tasa da yawa daga cikinsu sunyi dariyar da basu taɓa yiba a rayuwarsu ba.
Har sai da iska ta ringa ɗaukar wannan dariya tana sawa ana jinta a wasu wuraren na nesa dasu.
To haka dai wannan rana ta uku ita ma ta ƙare suna cikin farin ciki da annushuwa.
A ranar ƙarshe wato ta huɗu, Nusi ta tashi tayi jawabin cewa wannan walima ce ta cewa ta karɓi Armad a matsayin ƙaninta na uku bayan Iliyasis da kuma Cokali.
Duk da kuwa furar da suka sha ta kwana da kwanaki tasa rabi da rabi suka ji abinda yake cewa, amma dai-dai wajen mai mahimmancin daya shafi Armad sunji.
Haka suka sukai barci, dukkansu basu san cewa wannan rana zata zama ɗaya daga cikin ranaku ababan tunawa ba a tarihi.
Bayan ƴan kwanaki da yin wannan walima Nusi da Iliyasis da Cokali suka ɗauki Armad zuwa wajen gari, inda sukai tafiya mai nisan gaske har saida suka fara hango wani ƙaton kogi, wanda zaka iya ce masa maliya ma tun daga nesa, saboda girma.
Bayan sun tsaya a wajen sai Nusi ta nuna masa wannan kogi dake nesa kuma tace, ''kaga wancan ruwan shi ne wanda nake gaya maka!
''Indai zaka iya yin wata biyu cir akansa, kuma ka fito da rai da lafiya, to zan yarda ka shiga 'Gasar Jinzidal'."
To daman dai yau kusan sati kenan su huɗun suna muhawara akan kamatar su bar Armad ya shiga ta Jinzidal (wadda akewa laƙabi Deniziyya Kuronikil) ɗin Ko kuma a'a!
Amma dai daga ƙarshe suka tsaya akan cewa indai zai iya rayuwa akan wannan ruwa wanda zaka iya samun daga kan Dordor masu kai ɗaya har ya zuwa masu kai biyar aciki.
To zai iya shiga wannan gasa, ta Deniziyya Kuronikil!!
Har sun juya zasu tafi, sai ƙasar da suke kai taɗan fitarda wata ƙara mara sauti saosai ko kuma tsoratarwa. Dukkaninsu sunsan mai wannan ƙara take nufi, ba wani abu take nufi ba illa cewa an turowa wani saƙo ta Ayrid.
Ai kuwa ba'a daɗe ba wata ƴar shuka ta bayyana a gaban Armad, wadda ta samarda wata ƴar filawar takarda. Armad na miƙa hannu wannan takarda tayi wajensa, alamun saƙon nasa ne.
Ai kuwa haka ya buɗa ya fara karantawa, ba jimawa wani mugun gumi ya fara keto masa. Dukkanin gashin jikinsa ya miƙe. Idanunsa jajawur ya dubi Nusi yace lallai lokacin komawa ta gida ya zo. Domin kuwa babu shakka lallai saina nemo Tarifil-Fakta acikin wata bakwai masu zuwa!
"Ehh!!!!" Nusi tai wata wawar ajiyar zuciya, "mai kace, wai menene ne acikin saƙon? Waya turo maka? Kayi mana bayani."
Dukkanin hankulan su Iliyasis da Cokali Suma ya tashi, domin sun san koma menene acikin saƙon nan, toba alkhairi bane. Dan babu yadda za'ai a iya tunaninsu mutun yana cikin hayyacinsa ya ce zai nemo Tarifil Fakta acikin wata bakwai masu zuwa. Mutumin da duk duniya suka kasa nemowa.
Dakyar Armad ya iya daina haƙi, sannan ya dube du cikin sauri ya fara jawabi, "Masanin Ƙasa Abul-Babara ya bani adadin wata bakwai na nemo Tarifil-faƙta. Yace ya gama haɗa maganin mahaifiya ta, amma idan nanda wata bakwai ban nemo shi ba, to nama haƙura da nemansa, domin kuwa alƙwarinmu dashi ya tashi."
"Kai…." Cikin tsananin mamakin rashin sanin ya kamata na ma'abota duba dukkanin su ukun sukai ajiyar zuciya tare da riƙe baki. Domin sun san lallai aikin dake gaban Armad ya tashi daga mai-kama-da-mara-yiwuwa zuwa wanda-bazai-taɓa-yiwuwa ba. To amma ganin halin da Armad ke ciki na rikici da firgici, nann da nan Nusi ta fuskanci cewa kamata yayi sunkwantar masa da hankali, su kuma bashi buri maimakon su ƙara kashe masa gwiwa.
"Indai haka ne to kai sani cewa mu ukun nan zamu taimaka maka da iyakacin ikon mu a cikin waɗannan wata bakwan. Abinda ya kamata ka sani shi ne.
"Na farko dai babban mafitar ka ta nemo Tarifil-fakta a yanzu shi ne shiga cikin garinmuna ƙarƙashin ƙasa wanda na labarts maka a baya. Domin ina jin cewa indai muka iya shiga wannan gari, to kamar mun samo Tarifil-fakta ne.
"Amma kai sani cewa, hanya ɗaya da zamu iya shiga garuruwan ƙarƙashin ƙasa shi ne idan akai mana rijista acikin waɗanda zasu biga gasar Jinzidal. Ni zan nemo mana katin shiga na garin Maikironomada. Sannan kuma idan muka shiga sai fake da taka rawa acikin gasar mu silale muyi namu waje.
"To amma Armad kai sani cewa lallai komin saurin da kake baxan bari ka shiga gasar Jinzidal ba, ba tare da na tabbatar da ƙarfin Izzar ka ba. Saboda haka maimakon wata biyu yanzu na maida shi sati ɗaya. Zamu jira anan, kai kuma zaka hau kwale-kwale. Akwai wani tsibiri idan ka miƙe wannan hanya," taɗan tsaya taja numfashi tare nuna masa hanyar da hannunta, "abinda kawai nake so shi ne ka ɗebo min ƙasar dake wannan tsibirin ka dawo nan cikin sati ɗaya." Ta ciro wani Ayrid daga jakarta, inda ta karanta wasu ɗalasimai ta juyarda shi izuwa ɗan ƙaramin kwale-kwale.
Babu ko cewa ƙala, Armad ya hau wannan kwale-kwale ya zare takobinsa, tare da nufar hanyar tsibirin nan.
Nusi tayi ajiyar zuciya tare da kallon su Iliyasis, waɗanda sun kasa cewa komai tunda suka ji zancen wata bakwan nan. Ta numfasa tace, "ko ya nemo Tarifil-Fakta ko ba ya nemo shi ba, duk ya ta'allaƙa da ƙaddararsa. Mudai namu shi ne mu taimakawa abokinmu mu kuma bashi kwarim gwiwa. Saboda kada wani acikin ku ya kuskura yace masa bazai yiwuwa ba. Ku kafa mana tanti, anan zamu jira shi sati ɗaya."
Kwanaki uku bayan da Armad ya ɓace acikin hazon dake kewaye da wannan kogi daya haɗe tsakanin doron ƙasa ta uku da kuma dajin Ikwatora, Armad ne ke tafe yana ta tuƙa kwale-kwalen a hankali, domin ko gabansa baya iya gani saboda hazo da duhu. Domin tunda yai kwana biyu yana tafiya, ya daina ganin rana, kullum dare ne kuma kullum duhu ne.
Sai dai kuma babban abinda ya bawa Armad mamaki shi ne, duk da kasance war wannan kogi da yake kai za'a iya yin ittafaƙi akan cewa yana daga cikin wajen mafi hatsari a dukkanin duniyoyin ƙasa, amma bisa tsananin mamaki babu ko Dordor ɗaya da yai arba dashi. Hasalima babu wata halitta mai hatsari daya gani, kai a rana ta uku ma yana cikin tafiy kawai idanunsa suka kai ƙasan kwale-kwalensa bayanda yaji motsi, ai kuwa yana dubawa yaga manya-manyan kifaye suna gudu a cikin ruwan nan a ƙoƙarinsu na gukewa daga inda Armad yake tsoro.
Nan take Armad yasan cewa akwai wani hatsari dake faruwa, Amma ko kaɗan hakan baisa yaja baya ba, ko kuma ya tsaya ba. Kai tsaye, cikin dakiya da rashin tsoro ya ƙara numfasawa cikin wannan duhuwa da hazo.
A rana ta huɗu da yamma yana tafiya ya fara hangen wannan tsibiri da Nusi ta kwatanta masa. Ai kuwa nan take ya ƙara azama ya nufi wannan waje gadan-gadan.
ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, akan wannan tsibiri waɗansu mutane ne guda huɗu. Dukkan tsibirin babu gida gaba babu gida baya. Babu wata halitta mai rai, face rugurguzazzun gida je da duwar-watsu. Lallai kana gani zaka fahimci cewa shekaru aru-aru anyi babbar alƙarya akan wannan ruwa, amma a yanzu sai dai tarihi.
Iskar dake tashi daga wannan tsibiri duk da a tsakiyar ruwa yake, amma tana da tsananin zafi, sannan kuma tana ɗauke da tsananin tsoro da firgici acikinta. Babu komai sai duhu da kaɗaici da alamun mutuwa da alhini acikin wannan waje.
Amma bisa mamaki waɗannan mutane huɗu, maza uku mace ɗaya suna tsaye a tsakiyar wannan waje. Su su kaɗai ne halitta mai rai duk faɗin wajen.
Dukkanin gashin jikinsu fari ne fat alamun tsufa da daɗewa a duniya. Amma hakan ko kaɗan baya nuna alamun gajiya wa a tattare dasu. Hasalima kowanne ɗaya daga cikinsu zai iya yaƙar daula guda shi kaɗai kuma yai nasara ba tare da ko kwarazane a jinkinsa ba.
Babban cikinsu mai sanye da rawani wanda ya rufe fuskarsa, yana fitar da kamala mai ƙarfin gaske. Wadda ita kaɗai zata iya zubar da ƙananun ma'abota Izza ƙasa a sume. Hasalima Izzarsa shekaru dubu ɗaya ce da ɗari biyu da sha uku (1213 years). Mai biye masa yana da Izza shekaru ɗari tara da arbain da ɗaya. Macen nada ɗari baƙwai da sha uku sai kuma ƙara munsu mai ɗari biyar da huɗu.
A wani na salo na wata irin murya mai saka tsoro a cikin iskar dake kaɗawa, mai biye wa babban yai magana, "Ya shugaba na, yau shekaru sama da ɗari bakwai muna neman wannan littafin-takobin, amma yau gashi ya bayyana a garemu. Lallai jiranmu yazo ƙarshe. Ina so ka bani iko na zo maka da wannan littafi cikin ƙiftawar ido."
Tsahon lokaci wannan nasu baice komai ba, hasalima ko kallon sa baiyi ba. Sai bayan kimanin daƙiƙa sittin wannan mace ta cire mayafin data rufe fuskarta ta kuma rusuna a gaban shugaban nasu tace, "ya shugaba na, ni kuma ina ganin mu bari yaron mai suna Armad ya iso, tunda shi ne kaɗai wanda littafin ya amince ya bayyana a gareshi bayan duk waɗannan shekarun. Idan ya iso saimu kashe shi cikin kwanciyar hankali, mu kuma yi amfani da ruhinsa wajen sarrafa littafin."
Babban abinda mamaki da wannan mace data bada wannan shawara ita ce, kamarsu ɗaya sak da Nusi babu wani abu daya raba su, kama daga kalar fatar har komai da komai. Kai kamar har tafi wadda ke tsakanin yan biyu ma, idan dai banda cewa kana zuwa bakin wancan ruwa zaka ga Nusi dasu Cokali a inda Armad ya barsu ba, toda sai kace ita ce ma.
Wannan littafi da waɗannan mutane suke nema idan mai karatu bai manta ba, shi ne wanda aka labarta acikin 'Gabatarwar' wannan littafi. Wanda hatta ma'abota Ururu suke nema, amma sun rasa. Yanzu gashi su waɗannan mutanen sun gano cewa wannan littafi da Armad ya samo acikin Non-toc-Teka, shi ne dai wannan littafin da suke nema. Kuma gashi nan yana tafe zuwa inda suke bayan shekaru sama da ɗari bakwai da sukai suna nema.
***
Deniziyya Kuronikil (Jinzidal), suna ne da akewa wata gasa laƙabi dashi.
Gasa ce wadda kamar yadda aka labarta a baya wajibi ce, kuma babu wata ƙasa ko kuma wani sarki daya isa yaƙi shiga.
Kowanne sarki daga kan doron kowacce ƙasa zai kawo wani adadi na bayi, waɗanda za'a saka a matsayin kyauta ga duk ƙasar da tayi nasara a gasar.
Akan tara sama da bayi dubu ɗari waɗanda za'a rabasu tsakanin wanda sukai nasara na ɗaya dana biyu da kuma na uku. Ta haka waɗannan ƙasashe su zasu juya akalar cinikin bayi a wannan shekara.
***
Babi na 27 : Tsibirin kaɗaici
Armad na tafe a hankali a hankali, babu abinda yake sosa masa rai sai labarin watanni bakwan da suka rage masa kafin wa'adin da sarkin duba Abul Babara ya bashi ya cika. Lallai yasan cewa duk abinda zaiyi daga wannan lokaci saiya zamo a ƙaiyade da lokaci.
Da yammaci liƙis yakai bakin gaɓa, inda ya sauko hannunsa na hagu bisa kan takobinsa, sannan na dama kuma yana ƙoƙarin ɗaure jirgin a iyaka.
Bayanda daya gama ɗaure jirgin saiya ɗago ya kuma yi duba izuwa cikin wannan tsibiri dake gabansa. Babu komai akai face ƴan gidaje ɗai-ɗai ɗai-ɗai ƙirar mutan da. Wanda tun daga nesa baka da buƙatar ace maka maka babu wata halitta aciki. Domin kuwa banda yana data rufe ko'ina babu komai sai shiru da kaɗaici dake tashi daga kaf ilahirin gida jen. Ga dukkan alamu ko namun dawa basu iya sakewa akan wannan tsibiri. Duk yadda akai yana daga cikin tsibiran da akayi wa mummunan sammu irin na mutanen farko.
Har izuwa wannan lokaci Armad bai daina mamakin dalilin da yasa har ya zuwa wannan lokavi bai gamu da Dordor ba. Domin a iyakacin lissafinsa ya ƙididdiga cewa ya kamata zuwa wannan lokaci ace tskobinsa tasha jinin sama da Dordor arba'in zuwa sama.
Nan take ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai wani abu akan wannan tsibiri wanda hatta su Nusi basu sani ba. Saboda haka nan take ya zare baƙar takobinsa, tare da karanta ɗalasimai kamar haka, "Ƙaban'shisu!"
Nan take walƙiya da tsawa ta fara haɗowa a jikin ƙarfen wannan takobi, inda nan take dukkan ilahirin ta ya cika da wannan walƙiya. Kafin daga bisani ilahirin jikin Armad shima ya ɗau haske yana bada walƙiya tamkar ɗan saƙon mutuwa.
Hasken jikin walƙiyar Armad ya fara haskake dukkan ilahirin wannan tsibiri, lamarin da yasa ya fara hangen alamun wasu mutane daga wata ƴar duhuwa da bata da nisa daga inda yake. Babu shiri yayi linƙaya acikin girman ɗalasiminsa na 'Ƙaban'shísu', ya kuma ɓace daga inda yake, sannan ya bayyana gaban wannan duhuwa.
Ai kuwa idon Armad bai masa ƙarya ba, domin kuwa kamar yadda ya gani haka yake. Mutane ne guda huɗu a tsaye a wajen. Dukkansu da ransu da lafiyarsu, amma kuma babban abin mamakin shi ne, babu wanda acikinsu yake kalli Armad. Tamkar basu ganshi ko kuma basu masan wani yana tsaye a wajen ba. Duk da kuwa haske da zafin Aradu dake tashi daga jinkinsa da kuma na takobinsa.
Armad ya dube su tare da haɗe gira, "kamar yadda babu ruwanku dani, nima haka babu ruwana daku." Yana gama magana ya juya zai tafi. A zuciyar Armad yayi tunani cewa yadda basu kula shi ba, yana nuna tamkar basu damu dashi bane. Sai dai kuma amma kash, abin ba haka yake ba, domin kuwa yana juyawa yaji maganar wata mace daga cikinsu, wanda yake shi baima kula akwai wata mace acikinsu ba.
"Waya ce maka ba ruwanmu dakai," macen na rufe baki Armad ya juyo da niyyar ganin kowa ce ce ke magana, ai kuwa nan take ya buɗe baki tare da kwale ido.
"Nusi??" Armad ya lura cewa wannan mace data gama magana kamarsu ɗaya sak da Nusi daya baro a bakin gaɓa. "Me kikeyi a nan?" Armad ya ƙara tambaya.
"Ba ita bace," ta bashi amsa a nutse, "abinda kawai muke nema a wajen ka shi ne littafin daka samo acikin Non-toc-teka."
Armad ya yatsine fuska cikin fushi, "damme yasa zan baku littafina!"
Wannan mace mai kama da Nusi ta ƙara girgiza sannan tace, "idan da munso yaudararka toda munyi shigar ƴar uwarka Nusi mun kuma ɓata tsakanin ku ts hanyar yin amfani da sunanta mu kwaci wannan littafi. To amma shugaban mu yace mu bika a hankali. Saboda haka ina so ka ƙara tunani kafin ka ƙara bamu amsa. Domin kuwa wannan itace dama ta ƙarshe dazan baka." Tana gama magana ta zare takobinta tare da tsayawa a gaba Armad.
Armad ya lura cewa tana sane take ƙara futo da ƙarfin Izza ta domin ya karanta ya gane matsayinta a fagen Izza. Idon Armad sukai tsinkaye da abubuwa kamar haka;
Izza : 713
Negrinki : Duniya ta biyu
Aljani : Aljanin Iska
Fasahar takobi : Mataki na Shida
Har ya zuwa wannan lokaci babu wanda yai motsi acikin waɗannan mutane uku dake tare da wannan ma'abociyar Izza dake kama da Nusi. Lallai Armad yasan cewa akwai babban aiki a gabansa kafin ya tserewa waɗannan mutane. Domin kuwa yasan cewa a doke lallai bazai iya ja da dukkaninsu ba. Gashi har ila yau ko gwada ƙarfin wannan littafin takobin baiyi ba, ballanta yasan ko akwai wata fasaha aciki da zata iya taimaka masa. To amma wani babban abin mamaki shi ne yana jin cewa bazai taɓa iya bayarda wannan littafi ba. Ko mai zai faru.
Saboda haka saiya fara ƙoƙarin ɓullo da wata sabuwar hanyar, "mai yasa kuke san wannan littafi." Armad ya tambaye ta a nutse.
Nan take fuskar ta ta fara canjawa, inda a fusace ta bashi amsa, "wannan bai shafe kaba. Zaka bayar ko baza ka bayar ba."
Armad yana cikin tunanin mai zai aiwatar kawai yaji hucin takobinta yana iso shi. Inda nan take ya miƙa tasa ya tare. Sai dai amma banbancin Izzar da yawa, nan take ta danne Armad izuwa ƙasa bisa gwiwowinsa. Badan takobin tasa ma tasha tsimi ba, to da lallai tuni ta tarwatse.
Armad na ƙoƙarin kare kamsa daga wannan sara nata, amma ina, tuni cikin zafin nama ta zira hannu cikin rigarsa. Inda kafin yai wani motsi tuni ta ƙara nuna masa banbancin dake tsakanin Izza shekaru ɗari bakwai da ɗoriya da kuma wadda bata kai shekaru ɗari ba. Inda wannan littafi ya bayyana a hannunta. Armad yai iya ƙoƙarinsa ya riƙo shi amma ina babu abinda yake sai ƙara nisa dashi, yayinda ita kuma tai tsalle take komawa baya.
Kafin Armad yayi wani abu tuni dukkanin su ukun dake bayan wannan mace sukai tsalle tare da matsowa kusa da ita. Sannan kuma a wani salo na samarda ƙawanyar tsafi, dukkaninsu huɗun suka kewaye wannan littafi a yayinda macen ta sashi a tsakiya. Kafin daga bisani su fara karanta wasu a wani harshe wanda Armad bai gane ba.
Dukkan abubuwan sun ɗauki lokaci wajen bayani amma a zahiri basu wuce daƙiƙa ɗaya ba.
Sai dai Armad na niyyar kai musu farmaki ya kwace littafin, kawai sai ya ƙara ganin wani hasken ya bayyana daga sama. Inda kafin ma Armad ya gama zare takobinsa, tuni wani saurayi ya bayyana daga cikin wannan haske, inda kai tsaye ya caka farar takobin dake hannunsa a tsakiyar waɗannan mutane huɗu. Kuma kan wani acikinsu yayi wani abu tuni takobin tasa ta haɗu da jikin wannan littafi dake tsakiyarsu.
Nan take wani baƙin haske mai kama da duhun dare ya gauraye dukkan wajen. Inda kai tsaye ya sumar da Armad cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba. Babu abinda Armad ya ƙara tunawa illa farkawa da yayi bayan tsahon lokaci yai arba dashi kwance acikin taɓo sannan kuma daga can gefe kuma ga littafinsa nan. Sai dai kuma babu kowa a wajen sai shi kaɗai.
Har Armad ya fara tunane-tunane kawai sai ya tuna cewa koma ina suka tafi bai shafe shi ba, tunda ga littafinsa basu tafi dashi ba, abinda kawai ya rage masa shi ne ya ɓace daga wajen.
Sai dai kuma yana cikin saurin da yake ne, kwatsam kan ya kai ga littafin ya gano cewa a gaban goshinsa babu wannan jan kyalle da kullum ke tare dashi. Babu shiri ya tafi da gudu izuwa gefen ruwan nan domin duba wanne irin hali Miyurar sa ke ciki. Shin tana haske ko bata yi. Amma isarsa keda wuya kwatsam ya gano cewa ai babu komai a goshinsa. Miyurarsa bata nan, ta ɓace ɓat. Babu ita babu alamunta. Nan da nan fa ya fara haki, harma yana tunanin anya kuwa shi ne. Babu abinda yake sai dubawa da yake yana ƙara dubawa. Amma ina babu Miyura babu labarinta!
***
Wani abu daya faru awa ɗaya kafin isowar Armad wannan tsibiri.
Waɗannan mutane guda huɗu dake so su kwace wa Armad littafin takobinsa suna tsaye suna jiransa. Kowa aciki yana kawo shawarae yadda za'a gama da Armad kai tsaye a kashe shi sannan a kwace littafin. Amma bayan kowa ya gama, sai shugaban nasu ya numfasa ya ce, "lallai kamar yadda kuka ce kashe shi mu kwaci littafin ba abu ne mai wahala ba. To amma kun manta da cewa acikin wannan littafi akwai ƙarfin Izza wanda zai iya jiya lokaci ya kuma canja zamani? Saboda haka lallai bazan yarda ɗaukan wani hatsari na faɗa ba, inda litrafin yana hannunsa. Dukkaninku kunsan mai zai faru idan jikin takobin wani ya taɓa wannan littafi. Saboda haka mafi kyawun hanya shi ne mu lallaɓa shi mu karɓi littafin sannan saimu kashe shi.
Sai dai kash, abinda basu sani ba shi ne, a dai-dai wannan lokaci wani jarumi ma'aboci Izza yana kan wannan tsibiri. Wanda shi kuma babu abinda yake buƙata face ya hallaka waɗannan mutane huɗu dake neman yiwa Armad kwace. Saboda wani tsohon tarihi dake tsakaninsu. Wannan jarumi ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda.
Wanda kuma ya ci gaba da jira ya fakaitansu har sai da yaga sanda suka shagala suna so suka wasu ɗalasimai su sawa littafin takobin layar zana. Shi kuma ya fito ya caki littafin da takobinsa. Yanzu gashi dukkanin su biyar ɗin har dashi sun ɓace ɓat. Babu su babu alamarsu. Sannan kuma babban abinda ya shafi Armad shi ne sum ɓace masa da Miyura. Duk da har a wannan lokaci bai san taƙamaimai maiya faru ba!!
***
Babi na ashiri da takwas : Ruhin Armad ya rabe gida biyu
Shekara ta 1833
Ƙasa ta bakwai
Ɓangaren Arewa
Garin Jíha
Wannan gari dai shi ne garinsu Ikenga O Bayajidda kamar yadda aka labarta a baya. A kuma wannan shekara ta 1833 aka haifeshi. A wata rana ta laraba.
Wannan rana babansa Sarki Shísu O Bayajidda ya bayyana a gaban mahaifiyarsa sa'anni kaɗan bayan haihuwarsa. Hannunsa ɗauke da wata ƴar tasa mai ɗauke da jini. Yana shigowa ɗakin ko magana baiba, mahaifiyar Ikenga ta gane abinda ke faruwa, duk yadda akai dama sun riga sun tattauna yadda za'ai. Saboda haka ta buɗe bakin ɗan nata, yana kuka irinna na jariri, shi kuma baban nasa ya gabato izuwa garesu. Inda ya buɗe wannan tasa ya kuma juye wannan jini a bakin wannan yaro mai suna Ikenga.
Wannan jini kuwa ba wani bane illa na wani magajin wilbafos da aka kashe badan komai ba, sai dan a shayar da Ikenga jininsa.
Sai dai kuma abinda wannan sarki da matarsa basu sani ba shi ne, bawai su kaɗai ne sluka san abinda ya faru acikin wannan ɗaki a wannan rana ba. Akwai wasu mutane guda huɗu, waɗanda suka daɗe suna neman yadda za'ai su sami jinin magajin wilbafos domin suyi tsafi dashi. Wannan tsafi kuwa ba wani bane illa wanda zaisa su iya mallakar fasahar aljanun dake jikin Littafin takobi. Amma sun rasa. Saboda haka suka biyo wannan sarki suna ta ƙoƙarin kwace wannan tasa mai ɗauke da jini, amma basu samu dama ba saboda ƙarfin Izzar wannan sarki. Haka dai suna ji suna gani ya bawa wannan ɗa nasa Ikenga wannan jini.
Bayanda haka ta faru, sun riga sunsan sun rasa wannan jini, sai suka bazama duniya domin samo wata hanyar da zasu iya sarrafa aljanun dake jikin wannan littafin takobi domin su ɗakkota daga Non-toc-teka, amma shekara da shekaru basu samu ba. Saboda haka a ƙarshe suka yanke shawara su dawo su samu wannan yaro Ikenga, su gwada amfani da jininsa ko zasu samu sa'a tunda dai shi ne ya shanye wannan jini da suke nema.
Waɗannan mutane ba wasu bane illa mutanen nan guda huɗu da Armad ya gamu dasu akan wannan tsibiri. Wanda suke tafe da wannan mace mai kama da Nusi.
To amma suma sunsan cewa baza su iya tunkarar Ikenga ba idan babansa nada rai ba. Saboda haka tun daga wannan lokaci suka fara bin Ikenga a ɓoye, suna neman yadda za'ai su faki idon babansa su sace shi. To amma haka bata samu.
Har sai da yaƙin daya afku tsakanin Ururu da garinsu Ikenga ya afku a shekarar 1851 Bayan Amri. Wanda yai sanadiyyar halakar dukkan mutanen garin Jíha kamar yadda aka labarta a babi na sha huɗu.
Sai dai kuma kash, duk da wannan yaƙi Ikenga ya ƙara kuɓucewa waɗannan mutane guda huɗu masu burin mallakar littafin takobi. Amma basu haƙura ba, haka suka ci gaba, suna biye dashi suna biye dashi, sun hana Ikenga sake wa yayi yawo aban ƙasa kwata-kwata. Kwatsam sai allon tsafin dake hannunsu ya nuna musu cewa lallai an samu wani yaro mai suna Armad Wilbafos, wanda shima Magajin Wilbafos ne, kuma lallai tsafin da suka daɗe suna so su aiwatar domin fito da Littafin takobi daga Non-toc-teka, tofa wannan yaro ya aiwatar dashi. Kuma yana nan tafe da wannan littafi a hannunsa.
Saboda haka waɗannan mutane suka manta da Ikenga, inda suka zo suka fake akan wannan tsibiri domin jiran Armad ya kawo musu wannan littafi da sukai shekara sama da ɗari tara suna nema.
Sai dai kuma Ikenga ba'a sanshi da yafiya ba, kuma a rayuwarsa kullum hallaka garinsu da akai yana sosa masa rai kuma yana motsa masa azabar son yaƙi. Saboda haka koda yaga sun daina binsa, sai shima yayi nasa binciken, ya kuma gano abinda ke faruwa, saboda haka ya shiryo shima ya bazamo wannan tsibiri, domin ɗaukar fansar abinda waɗannan mutane huɗu sakai masa.
Sai dai kuma ba haka kawai ya taho ba, Saida ya tsuma takobinsa acikin Ruwan-Kogin-Lokaci. To ko mene ne wannan ruwa na kogin lokaci da Ikenga yasa akan takobinsa da niyyar ɗaukan fansa.
Amsar tana cikin tsakiyar wata sahara dake can ƙarshen kan doron ƙasa ta biyar shashin arewa. Duk da tsananin rana dake tsananin soya fata acikin wannan saharar, amma ko a jikin wani siririn tsoho wanda ke zaune a cikin wannan sahara.
A gabansa wata da'ira ce da akai da layu masu ɗauke da ƙasar tsofaffin kabarirrika. Duk da irin yanayin yadda iska ke wasa da yashi a wajen, amma sai kaga zarar yashin ya matso wajen wannan layu ya tarwatse. Tamkar tsoron abinda ke cikin tsakiyar wannan ƙawanya yake. Shi kuwa wannan tsoho tuni fatar jikinsa takai matuƙa wajen yamushewa domin tsananin zafi da rashin ruwa.
Amma duk da haka, babu abinda yake face kiran waɗansu ɗalasimai irin na mutanen farko. Lallai tun daga nesa zaka san cewa ana haɗa babban tsafi a wannan da'ira. Yana cikin wannan hali tun safe har rana tai sama, sannan tabi yamma ta faɗi. Amma ko gezau baiyi ba.
Kwatsam tsakiyar dare bayanda wata daren sha takwas ya bayyana a samaniya, sai hasken wannan wata ya fara haɗuwa da ɗalasiman dake tashi daga bakin wannan tsoho mai yawan farin gashi. Ai kuwa ba jimawa iska ta fara kaɗawa a tsakiyar wannan da'ira, inda yashin sahara mai zafi yai sama yai tsiri ya rufe ko'ina acikin wannan da'ira.
Bayan daƙiƙu masu yawa komai ya lafa saiga wani saurayi ya bayyana a tsakiyar wannan da'ira, tamkar wanda aka cillo daga sama.
Idan ka dubi wannan saurayi zaka ga ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda, jika a wajen bayajiddan asali. Babu komai ajikinsa, koda wando.
Saboda haka yana bayyana yai tsaki gami ɓata rai tare da rufe gabansa, ya kalli wannan dattijo daya daɗe yana karanta ɗalasimai a wajen ya fara masifa, "To ai Kána baka gayamin cewa idan mutun yai tafiya acikin lokaci kayansa yake bari a baya ba!"
Wannan tsoho mai suna Kána ya rusuna tare da sunkui da kansa ƙasa, sannan ya ce, "ya shugaba na aimin gafara, ga kayan nan na tanadar maka a gefe." Ya miƙawa Ikenga ƴar shara mai ɗan tsayi irin ta mutan da, tare da wani ɗan wando.
Ba jimawa Ikenga ya gama shiryawa kuma ya karɓi jakar tsafinsa da kuma takobinsa daga wannan hadimi nasa, sannan kuma suka kama hanya izuwa duniyar garuruwan ƙasa. Wanda za'a fafata gasar Jinzidal ta wannan shekara.
Akan hanyarsu ne Kána ya dubi Ikenga tare da cewa, "Yanzu meye ya rage ya shugaba na?"
Ikenga yai kyaran murya tare da fara bayani, "a halin yanzu na ɗau fansata, kuma nayi cilli dasu izuwa wani zamanin na daban. Babu ruwana koma wanne ne. Yanzu kawai abinda ya rage shi ne mu fara aiwatar da shirin mu na ɗaukar fansa akan Ururu. Lallai saina ga bayan Ururu kafin na daina numfashi. Mataki na farko shi ne haɗa runduna mai ƙarfin Izza irin wadda zata iya tsayawa da ƙafafunta. Idan kuma muna buƙatar runduna, to muna buƙatar kuɗi. Saboda haƙa babu wata hanya da zamu samu wannan kuɗi cikin sauƙi banda ta hanyar cinikin bayi. Saboda haka zamu je gasar Jinzidal, kuma duk wanda ya shiga gaba na zan gama dashi ba tare da ɓata lokaci ba."
Haka suka ci gaba da tattauna yadda Ikenga yake shiri domin fafatawa da Ururu. A irin lokacin da kowa yake tsoron furta koda sunan waɗannan mutane masu baƙaƙen idanuwa, amma shi wannan saurayi jikan Bayajidda yana gefe yana shiryawa yadda zai yaƙe su ya ɗau fansar iyayensa da ƴan garinsu da suka kashe.
***
A wani gari nisan kimanin shekaru hamsin daga inda Armad yake tsaye, a wata daula dake tsakiyar ruwa wadda ke tsakanin ƙasa ta farko data biyu, wasu yara ne ƴammata ke wasa a gefen wani kogi.
Kana ganin ƙirar yaran da kayan jikinsu zaka san cewa lallai ƴaƴan sarauta ne. Dukkan idanunsu farare ne babu ko kwayar baƙin dake cikin ido. Kai kace ma makafi ne.
Amma zaka gane cewa suna gani tar-tar kamar kowanne ɗan adam a yayinda farar daga cikinsu mai gashi ruwan roɗi-roɗi ta ga wani mutun a kwance a gabanta tana wanka ruwa ya koroshi. Ba shiri taja rigarta sama, ta kuma fara kiran ƴar uwar ta, "Suwee! Suwee!! Suwee!!!"
Ƴar uwarta ta ta jiyo kiran ta kuma jiyo izuwa gareta. Asalin sunan ƴar uwar shi ne Suwainah, amma ƙanwarta ta, Zeera, ta fiso ta ringa kiranta da Suwee ɗin.
"Kizo kinga wani ma, ina ragowar ukun?"
"Baba ya tafi dasu wajen sarki." Suwee ta bata amsa.
"Baba!" Zeera ta buɗe baki cike da mamaki, "kina nufin baba da kansa! To gaskiya ne kenan abinda ake faɗa cewa daga wata duniyar aka jefosu!"
Tun kafin ta rufe baki yayar tata mai kimanin shekaru sha shida wadda kuma ta bada shekaru uku, ta taho wajen da take nuna mata da gudu. Domin taga wannan mutun da ƙanwarta take nuna mata. Amma tana zuwa ta rufe ƙanwarta ta da faɗa, "ba baba yace mu daina faɗa ba, so kice wasu suji. Yana ina?"
Zeera ta nuna mata wani yaro kwance a gefen kogin, duk taɓo ya shafe masa jiki da fuska. Amma duk da haka idan kalura sosai zaka ga cewa akwai ɗaurin jan kyalle a gaban goshinsa. Kuma lallai idan kasan Armad Wilbafos mamallakin Aljanin walƙiya zaka gane cewa shi ne ba wani.
Suna tsaye suna tunanin ya zasu yi kawai sai suka ji hayaniyar sauran ƴam matan garin daga nesa suma suna kusanto wannan kogi.
"Yaya to ya zamuyi dashi, ga mutane nan!" Zeera ta dubi ƴar uwarta. Suwaina kuwa nan take ta fito da wata ƴar ƙaramar jakar tsafi a cikin rigarta ruwan hoda, inda ta bawa ƴar uwarta ta. Suka kuma fara tala ta har saida takai dai-dai tsayin yadda zasu iya zira Armad aciki.
Ƙanwar ta miƙa hannunta domin ta fara saka kan Armad aciki, amma a lokaci alamari ya canja.
Domin kuwa tana taɓa jikin Armad hannunta ya shige cikin kansa tamkar babu komai a wajen. Cikin sauri ta zaro hannunta ta kuma ƙara taɓawa dan ta tabbatar, amma hakan dai ta ƙara faruwa a karo na biyu.
Nan da nan ita ma Suwaiba ta miƙa nata hannun ta taɓa ƙafarsa, amma taga itama hannunta ya shige cikin. Cikin tsananin mamaki suka fara tunanin ko mafarki suke. Amma maganar ƴan uwansu matan dake ƙara matsowa ita ce ta tabbatar musu cewa ba mafarki suke ba. Nan take suka fara bin duk wata hanya domin zira jikin Armad acikin wannan jaka, amma ina.
Kuma suna cikin haka ne ɗaya daga cikin matannan masu ƙarasowa ta hango su, ai kuwa nan take suka fara kwala musu kira, tare da tahowa inda suke.
***
A wannan waje kuwa, Armad na tsaye shi kaɗai akan wannan tsaibiri. Ya rasa abinda yake masa daɗi. Ya kasa gaba ya kasa baya domin yasan muhimmancin Miyurar sa. Amma yanzu gashi ta ɓace ɓat, babu ita babu alamunta. Baima san maiya faru ba ballantana yasan inda ta tafi. Hasalima ji yake kamar bashi ba. Sai shafa goshinsa kawai yake yana dukan fuskarsa wai ko zai farka idan mafarki yake. Amma ina babu Miyura babu labarinta.
***
Babi na ashirin da tara : Jinzidal
Armad na cikin wannan hali su Nusi suka bayyana akan wannan tsibiri. Inda suka samu labarin dukkan abinda ke faruwa dalla-dalla daga Armad. Ganin cewa hankalin Armad ya tashi, babu wanda ya nuna masa cewa rasa wannan Miyura tasa da yayi abu ne mai kyau ba. Domin su suna ganin cewa hakan zai sa masu neman hallaka shi su ragu. Sai dai shi kuma kwata-kwata baya jin tsoron masu neman nasa ko kaɗan.
Ita kuwa Nusi ta shiga cikin zulumi tunda taji ance anga mai kama da ita sak.
To a haka dai suka lallashi Armad ya fara gudanar da horon sa wanda yazo yi tunda fari. Wato fafatawa da waɗannan halittu masu suna Dordor.
A wannan lokaci da Armad ke fafatawa a tsakanin waɗannan halittu da akewa laƙabi da Dordor, a can waɗansu wajaje sauran ma'abota Izza ne da dama suma ƙoƙari suke suga suma sun nuna kansu a duniya a wannan gasa da za'ai ta Jinzidal ƙarama (Wadda akafi sani da Deniziyya kuronikil).
Wasu daga ciki, kamar su Ikenga O. Bayajidda, wanda idan mai karatu bai manta ba, a lokaci na ƙarshe da aka ganshi, yana kan hanyarsa ta zuwa garin Denizawa domin shiga wannan gasa ta Deniziyya Kuronikil, duk da kuwa akwai ragowar watanni kusan biyu kafin zuwan gasar.
To ko mai yasa mai yasa shi tafiya da wurin??
Amsar dai tana cikin wani daji mai yawan giwaye.
Wannan daji ba a ko'ina yake ba, illa acikin daular Denizawa ta ƙarƙashin ƙasa.
Kuma ɗaya daga cikin dazuka na musamman da aka warewa babban ɗan sarki Deniz Iluru, wato Deniz Bizáya, domin motsa jiki.
Kusan zaka iya cewa duk wata dabba mai rai data rage acikin wannan daji tsahon lokaci ta daɗe da zama abincin waɗannan giwaye.
Ko kuma dai tuni sun shige ƙarƙashin ƙasa sun ɓoye kansu, ko kuma waɗanda suke da sa'a sun shiga rububi sun guje daga dajin da kyar.
Waɗannan giwaye lallai na musamman ne, domin kuwa duk da cewa girman jikinsu ya ɗara na da yawa daga cikin giwaye, jikin nasu bai hanasu yin tsalle mai tsayin gaske ba.
Misali a wannan lokaci, saboda abinda ke faruwa a ƙasan wannan daji tsakanin waɗansu mutum biyu, dukkanin giwayen nan sun yi tsalle sun haye can saman waɗansu bishiyu masu kama dana dabinon farko. Babu abinda suke sai hangen abinda dake faruwa, cikin tsananin burin ɗaya daga cikin waɗannan mutane ya faɗi matacce su sami abincin buɗa baki.
Koda yake sukan ci wata dabbar idan sun samu, amma a ƙa'idarsu an gina jikinsu ne kawai domin yin buɗa baki da naman ɗan adam.
Saboda haka nema wajen ya zama abin so ga Deniz Bizaya, domin lokaci-lokaci yakan yazo ya fafata da waɗannan giwaye.
Amma a duk tsahon lokacinsu dashi, basu taɓa ganinsa yana fafatawa da gaske ba irin satin daya wuce.
Saboda haka nema kaf giwayen nan suka haye bishiyu suna fatan waɗannan samari biyu su hallaka kansu, su kuma su sakko su samu na buɗa baki.
Idan ka kallo cikin dajin daga sama, babu abinda zaka iya hange face mutun biyu a tsaye.
Ɗaya yana riƙe da fafalo-mai-lanƙwasa launin ja. Irin jan nan mai abin mamaki ta yadda zaka kasa gane cewa kalarsa ce a haka, ko kuma jinin abokin gabarsa ne yasa ya zama haka.
Wannan saurayi ba wani bane, illa Deniz Bizáya!
A ɗaya ɓangaren kuma wani saurayi ne, wanda shima daga saman bishiyun waɗannan giwayen babu abinda suke iya gani sai doguwar takobinsa dake ta kyalli tana ɗaukar ido.
Wannan takobi duk da cewa saurayin dogo ne, zaka iya hangen cewa ta fishi tsayi.
Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda!
Kayansu tuni sun daɗe da komawa kalar ƙasa, saboda azabar fafatawa, kai da gani kasan an kai kwanaki da dama ana wannan bata kashi.
Sannan kuma abu na ƙarshe da giwayen nan suke iya hange daga saman, wanda kusan shi kaɗai ne abinda yake ɗan faranta musu rai shi ne, haki da kowannensu keyi. Kana gani kasan waɗannan samari biyu sun gaji. Saboda haka nema waɗannan giwaye suke gani ko su na da rabo.
***
A can daular Infiriya kuwa, wani saurayi ne zaune shi kaɗai yana ta kuka.
Wannan saurayi yana kan kogin ƙasa ta huɗu wanda ya haɗe da Bangon arewa, acikin kwale-kwale. A gefensa kuma akwai wata gawa wadda idan kai mata duba na tsanaki zakaga cewa suna kama sosai da wannan gawa.
Babu abinda ke fita daga cikin jajayen idanun wannan saurayi, sai kwalla kawai.
Kana kallonsa bama ka buƙatar a gaya maka cewa wannan mutun dake kwance acikin kwale-kwalen mai suna Firius Firesa, makusancinsa ne.
A rataye a bayan wannan saurayi, wani mashi ne wanda ke ɗauke da wasu rubuce-rubuce irin na da.
Kuma idan ka kusanci mashin sosai, sai kaji kamar daga daga cikinsa magana ce ke tashi. Wadda kuma kamar ita ma kukan take!
Wani babban abin mamaki, duk da fuskar saurayin nan a sunkuye take, sai dai ɗigar hawaye kawai da ake gani, amma ko motsi bayayi, amma a wannan waje da yake akwai Dordor sama da hamsin waɗanda bawai ganinsa ne basu yi ba, a'a tun ɗazu suke nufarsa da mugun nufi, amma suna kusan ƙarasawa sai kaga sun koma da baya.
Hasalima ƴan mintuna da suka wuce, wani Dordor mai kai biyar ruwan ƙasa ya nufoshi, amma shima haka ya juya kamar sauran.
Kayan jikin wannan saurayi na sarauta, amma daga gaba duk sun jiƙe da hawaye.
Wannan saurayin ba wani ba ne illa Yarima Niyashi, daga daular Infiriya, garin Shífa.
Bayan kimanin rabin sa'a, tuni a wannan lokaci adadin Dordor ɗin da suka kewaye shi, ya haura ɗari.
Amma a wannan lokaci ne ya ɗago kansa a hankali, ya kalli sama, gami da yin ƙuwa mai ƙarfin gaske.
Wannan ƙuwwa na tashi, wani abin mamaki ya faru; tamkar da wasa wani haske ya tashi daga jikin mashin nan nasa, wanda yana fitowa wannan ruwa ya fara girgiza kamar wasu abubuwa zasu fito daga ciki.
Bayan ƴan daƙiƙu, ruwan ya fara ambaliya, amma bisa mamaki kwata-kwata bai haɗa da kewayen wannan jirgi ba.
Acikin wannan hargitsi wata murya mai cike da tsananin ɓacin rai da fushi, kai kace so take ta hallaka duniya baki ɗaya ta fito daga bakin wannan saurayi, ''ɗan uwa Firius, kayi ɓangaren ka, yanzu saura nawa!
''Nayi maka alƙawarin ɗaukar fansarka da kuma samun nasara!!!''
A wani salo mai ban mamaki wannan murya ta ringa ƙaruwa tana bazuwa ta cikin iska da wannan ruwan da kuma ƙasa.
Kafin wani lokaci da dama daga cikin waɗanda aka yarda suji wannan magana suka jita, a ko'ina suke kuwa a faɗin ƙasa bakwai.
***
Haka dai waɗannan samari dama wasunsu waɗanda zasu fafata a gasar Jinzidal ɗinnan mai zuwa suke ta shiri baji ba gani.
A kan doron ƙasa ta huɗu kuwa, a shashin arewa, acikin wani daji mai ban al'ajabi
Mutane ne sama da dubu a tsattsaye, wasu na kallo wasu, wasu na tattaunawa cikin raha, kamar suna murnar haɗuwar tasu.
Babban abin mamakin wannan dajin shi ne, gashi dai kallo ɗaya tak, zakaiwa wajen kasan cewa daji ne mai shekaru da dama a duniya, domin iskar dake tashi daga wajen ma zaka ji daɗewa ta shekaru acikinta.
Amma bisa mamaki babu wani abu daga cikin gimshiƙan kayayyakin daji a wajen; misali bishiyu, namun dawa, da dai sauransu!
Babu bishiya ko ɗaya tak a wajen, kuma babu alamun koda dabbar dawa guda a wajen.
Hasalima idan baka shiga wajen ba, ko kuma kawai ka hangeshi daga nesa, cewa zakai kurum fili ne, amma kana zuwa wajen jinin jikinka zai baka cewa acikin ƙasurgumin daji kake.
Bawai anan abin mamakin ya ƙare ba, idan kuwa da haka ne to da da sauƙi, amma idan ka ɗauke kewayen da waɗannan mutane ke tsaye, to zaka fuskanci cewa kusan ko'ina acikin dajin manyan ramika ne kawai.
Iya ganinka, duk inda ka hanga waɗannan ramika ne kurum.
Sannan kuma waɗannan ramika kaf ɗinsu idan ka leƙa baka ganin ƙarshensu, hasalima abinda yazo a tarihi shi ne, da damansu basu da ƙarshe.
Abin al'ajabi na gaba shi ne, abu ne sananne dama daular Denizawa a ƙarƙashin ƙasa take, kuma ta cikin waɗannan ramika ake zuwa can ɗin.
Idan sun yarda kenan!!!
Kuma suma ta ciki suke fitowa suyi mu'amala da sauran mutanen duniya.
Wanda wannan shi ne ɗaya daga cikin babban abinda yasa da dama suke tsoron takalar Denizawa da faɗa, saboda baka da tayadda zaka iya cimmusu.
Domin abu ne bayyananne duk wanda ya shiga ramin nan bai taɓa fitowa da rai ba.
Babban dalili kuma shi ne, waɗannan rami ka bawai daular Denizawa kaɗai suka je ba, a'a dama sauran wurare da suka daɗe da ɓacewa a tarihi, waɗanda saboda tsananin haɗarinsu, tuni ma aka gogesu a tarihi. Waɗanda suma duk a ƙarƙashin ƙasa suke.
Kuma babban abinda ke jiran duk wanda ya faɗa wannan waje shi ne ɗaya daga cikin waɗannan wajaje, idan dai har ba Denizawa ne suka buɗe buɗe masa tasu hanyar ba.
Kai akwai wata hikaya ma data daɗe tana yawo a bakin mutane, cewa ɗaya daga cikin waɗannan duniyoyi da aka goge na karƙashin ƙasa, akwai wajenda mutuwa da kanta ke gadi.
To koma dai ba gaskiya bane, kowa yasan babu wanda ya taɓa shiga ya fito, saboda haka babu wanda yake so ya kwada.
Shi ne yasa kowa ka gani a wajen yake kaffa-kaffa, duk da kuwa baƙin Denizawa ne, kusan duk waɗanda ka gani a wajen.
Mutane ne kawai da suka zo halartar Deniziyya Kurónikil. Wasu sune zasu shiga da kansu, wasu kuma ƴan rakiya ne, wasu kuma manyan baƙi ne.
Tuni mutane suka fara bin layi, suna biyan kuɗin shiga inda za'a haɗa su da wani Badenize dake wajen ya faɗa dasu cikin ɗaya cikin ramikan dake kewaye dasu.
Kowa ka gani sanye yake da kaya daban-daban, kai kasan daga ƙasashe daban-daban suke.
Kafin jimawa da dama daga cikin waɗannan jama'a sun shige cikin waɗannan ramika, izuwa cikin wannan gari.
Daular Denizawa zaka iyai mata kallon kamar wani ƙatoton gari ne mai tsananin girman ƙasa.
Wanda acikinsa akwai birane manya guda biyar.
Birane huɗu sune a zagaye da wannan gari guda ɗaya, wanda ya kasance a tsakiya, kuma ya ɗan haurasu girma.
Sun tsara ginin kowanne gari ne, yadda zai zamo, a kewayen kowanne gari, akwai ƙaiyadaddun adadin ramika dake kewaye dashi, wanda kuma ta ciki ne, mutane ke ɓullowa bayan sun shiga ta waɗannan dajika na waje.
A kewaye da waɗannan birane huɗu, dazuka ne kala-kala, iri-iri, wanda girman ƙasar da suka ci, shi kaɗai ya haura girman gaba ɗaya garuruwan nan guda biyar.
Sannan kuma a kewaye da waɗannan dazuka kuma katanga ce, wadda akayi da wani sinadari na musamman, shidai ba ƙasa ba kuma dutse ba, ba kuma ƙarfe ba!
Katangar nada girma sosai, tayadda baka iya gano ƙarshenta dama da hauni, sama da ƙasa.
Acikin wannan gari dake tsakiyar garuruwan nan, akwai wani ƙaton fili wanda ya kasance a kewaye.
Idan ka shiga cikinsa zaka ga cewa yama fi yadda kake tunani girma.
Daga farkonsa a zagaye yake da kujerun zama na alfarma waɗanda yawansu bazai lissafu. Idan kai musu kallon farko abinda zaizo ranka shi ne, komai yawan mutane zasu iya ɗebe su.
Daga cikin filin kuwa wasu ƴan ginannun wajaje ne ƴan ƙananu waɗanda suma suna da ɗan yawa kuma suna gaban waɗannan kujeru na farko.
Daga tsakiyar filin kuma wani ƙatoton fili ne wanda akai masa tsarin filin danbe, kuma aka kewaye shi.
Kai daka gani kasan wannan fili yaga fafatawar Mazan jiya.
Domin duk da sabon mashimfiɗi aka lulluɓeshi dashi ta kowanne ɓangare, hakan bai hana kaji yanayi mutuwa na tashi daga jikinsa ba.
Akwai fitilu na musamman dake kewaye da wannan filin na tsakiya suna bada haske mai ba sha'awa da sawa kaji marmarin yaƙi na tashi acikin ranka.
Duk da cewa babu kowa acikin filin tsakiyar, daga cikin waɗannan ƴan ƙananun wajaje kuwa waɗanda basu da nisa sosai daga filin tsakiyar akwai mutane kusan acikin guda shida daga ciki.
Kana gani zuciyarka zata baka cewa waɗannan sune mutanen da suka zo daga sauran manyan kabilun nan da sauran ƙasashe.
Wani abu mafi ban mamaki da ba'a ambata shi ne, wani ƙaton gini daya tashi ta ɓangaren gudu maso yammacin wannan fili na tsakiya. Wanda ya kasance shi ne waje mafi kusanci da filin tsakiyar. Gilashi ne ke kewaye da wurin baki ɗaya, tayadda ana iya ganin komai dake ciki.
Kuma a wannan lokaci zaka iya hangen kujeru na alfarma waɗanda yawansu bai wuce goma sha ba aciki.
Akan waɗannan kujeru kuma dake zagaye da duk filin, mutane ne da dama, ana ta mayar da labari akan ire-iren waɗannan gasanni da suka gabata.
Amma duk wannan kaɗan ne idan ka kwatanta da yawan mutanen dake tsattsaye a bakin ƙofar shigowa wannan waje.
Babu abinda kake ji sai hayaniya akan suna yen taurarin da ake saran zasu buga wannan gasa.
Kuma ga dukkan alamu waɗanna mutane sun san taurarin nasu basa wajen, wanda hakan nema ya sasu fitowa bakin ƙofar domin kallon sanda zasu shiga.
A dai-dai wannan lokaci saura ƙasa da awa ɗaya a fara wannan gasa, a yadda aka ƙayyade lokacin farawar.
Ana cikin hakan ne wani saurayi ya bayyana, mutun bakwai na bayansa, dukkansu sanye da kaya mai fari da yalo.
Tun daga nesa wasu daga cikin waɗannan mutanen daje jira suka fara nunashi.
Koda jama'a suka kyalla ido suka ganshi, sai kuwa hayaniya ta ƙara tashi. Babu abinda kake ji sai, ''kai....... aikuwa da gaske ne!!!
''Kai..ka...kai....., wannan karan hardasu, lallai za'a sha fama.
''Wallahi shi ne!!!'' Can daga cikin taron waɗannan mutane, wani yaro mai ƙarancin shekaru, yana tsaye a ɓangaren arewa, babu abinda yake sai jan rigar wani dattijo Badenize, ya na tambayarsa, ''baba wanene? Baba wanene?''
Baban ya waiwaya, gami da cewa, ''ƴan ƙabilar Hán, daga doron ƙasa ta uku!
''Kuma ina kyautata zaton wancan yaron na gaba shi ne Hán-na-bakwai, wato Hán-Amuru, ko kuma sunansa cikakke Hanamúru Zulkiflu!!''
Kafin wannan dattijo ya gama bayani muryarsa ta fara rawa, kamar wanda yake tuno wata azaba.
Kamar yaron ya fuskanci maike faruwa da sauri ya ce, ''shikenan baba na gane!''
A dai-dai wannan lokacin wannan tawaga suka zo suka wuce, suka shiga cikin wajen.
To kamar yadda tsohon ya faɗa dai haka ne, wannan tawaga data wuce daga ƙasa ta uku suke, kuma wannan yaron shi ne, Hánamuru, wanda akewa laƙabi da Hán-na-bakwai.
Shima yazo wannan gasa, kuma tuni suka gabatarda adadin bayi dubu goma ga Jinzidal kamar dai yadda sauran ma daga sauran ƙasashe suka kawo.
Ana cikin hakane waɗannan mutane suka ƙara ruɗewa zaka hango kusan tawaga har guda uku tana tafe.
Kan kace meye wannan tuni shewa da ihu mai cike da murnar gani gwanayensu ta cika wajen.
Kusan zaka iya cewa duk cikin garin nan ana jin wannan ihun.
Nan take maganganu suka fara tashi, ''Shugaba yarima Bizaya!!
''Ah! ga Ikenga O. Bayajidda can ma!!
''Ga kuma hmmmm....Maikironomada!!''
Tawaga ta farko mai ɗauke kusan mutum sha biyar, dukkaninsu sanye da fararen kaya, ita mutanen keta nunawa
suna murna gami da kiran sunan 'Bizaya'!
Ya biyun kuma wadda ita ce mafi ƙanƙanta, mutane uku ne kawai, dukkaninsu sanye da kaya masu baƙi da ɗorawa. Kuma ita ake nunawa ana kiran sunan Ikenga.
Sai kuma ta ukun wadda ke ƙunshe da kusan mutun goma, waɗanda mafiya yawansu kaya daban-daban suka sa.
Kuma wani abin mamaki duk da irin girman wannan ƙabila ta Maikironomada, waɗannan mutane dake wajen basa nuna wani buri akansu.
Hasalima tuni sun ɗauke kansu daga garesu, suna ta ɗagawa Bizaya da Ikenga hannu sunai musu fatan alkhairi.
Bayanda aka gama sallamar tawagar Bizaya da Ikenga, kuma aka basu shedar shiga da kuma wajen da zasu tsaya idan sun shiga, sai da dama daga cikin mutanen nan dake tsaye suma suka juya baya suka rufa musu baya, ba tare da ko damuwa da ƙarasa kallon tawagar Maikironomada ba!
Tundai abin baya damun ƴar tawagar, har takai wasu sun fara tsaki.
To amma a dai-dai wannan lokacin ne wata tawaga guda biyu suka doso wajen, kuma duk da nisan da suke dashi kafin su ƙaraso, tuni ƴan tsirarun da suka rage sun fara nunasu da hannu suna kwalawa, ''Kaiiiiii......kai wannan shekarar Infiriya Yarima Niyashi suka turo, lallai, wataƙila za'ai Deniziyya Kurónikil ɗin da ba'a taɓa yi ba!
''Wallahi shi ne!! Yarima Niyashi, mashin mutuwa!!!
''Kaiiii! Ku duba gefe ga tawagar Banfiriya can ma!!
''Dama su a duk shekara yarima suke turowa!!!!
''Kaga wannan shekara yarima Kiru suka turo!!
''Shi ne yayan gimbiya Nostalgia!!
''Oh...Zahra Kyau!! Kana tunanin kuwa tana cikin waɗancan Babysawan uku dake cikin tawagar tasa!!''
Kan kace kwabo, tuni irin waɗannan maganganu sun cika wajen.
Kuma waɗannan mutane da da suka juya baya suka fara tafiya, yanzu sun dawo, wasu ma har gudu suke suna tunkuɗe mutanen dake shiryen-shiryen shiga ƴan tawagar ƙasar Maikironomada!!! Lallai mutanen wajen basu da wani gwani a Maikironomada, ko mai yasa?
Comments
Post a Comment