Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura.
Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.
"Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sauka akan Ƙaraiƙisu. Han'Amuru ya ƙara yamutse fuska tare da matsawa kusa domin ya ƙara ganin fatar ƙaraiƙisu. A ransa yana ganin rufa-ido kawai ake masa.
Bayan ɗan lokaci ana abu guda sai Han'Amuru ya dakata da hare-haren da yake kaiwa ya tsaya ya fuskanci ƙaraiƙisu.
"Kasan tun yaushe nake shirin samun nasara a wannan gasa?" Ya ɗora ba tare da jiran amsa ba. "Tun shekarar dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin da uku. A wancan lokacin aka yaudare ni da farar laya wanda hakan yasa banyi nasara ba. Tun daga wannan rana nake shirya kaina, nake ƙara yawan fasahohi na, nake kuma ƙara zafin wutata. Daga wancan lokacin zuwa wannan na samu dama har guda uku da zan ƙara taka rawa a gasar Jinzidal amma naƙi. Badan komai ba saboda ina so na ƙara shiri. A yanzu nayi shiri, na ƙara shiri, har na gaji da yin shiri. Kana tunanin akwai abinda bazan iya yi ba?"
Yana rufe baki ya ɗora hannu ɗaya akan ƙasa sannan ya ɗaga ɗaya hannun sama. Kamar yana bawa sama umarni sai ta fara kaɗawa tana yin ja. Abu kamar wasa durkokin wuta suka bayyana acikin gajimare. Zai yi wuya ka iya lissafa adadin durkokin domin wasu iya kan ne kaɗai ya leƙo ta cikin gajimare. A wani salo na zafin nama sama ta hautsina, sannan dukkan durkokin suka haɗe guri guda ta yadda suka samar da wata basamudiyar durka guda ɗaya. Sannu a hankali wannan durka ta fara sakkowa ƙasa. Tun daga nesa kowa ya riga yasan akan Ƙaraiƙisu zata dira, amma abin mamaki ƙaraiƙisun bai motsa daga inda yake ba, tun dai daya daga kai yaga durkar sai ya saukar da kansa yaci gaba da kallon gabansa ba tare da ya nuna damuwa ba.
Sannu a hankali wannan durka ta sauka akan kokon kansa. Nan take dan banten dake jikinsa ya narke, filin da suke faɗan akai ya fara zagwanyewa yana bin iska. Iskar dake wajen ta fara kamawa da wuta. Yan-kallon da sukai rashin sa'a suna kusa da filin suka kama da wuta. Nan da nan ihu da iface-iface da guje-guje suka cika wajen. Kowa yana gudun neman tsira.
Sai da aka shafe minti goma cur sannan abubuwa suka lafa. Ƙaraiƙisu ya fito fili. Abun mamaki har yanzu yana nan yadda yake babu alamun ciwo ko rauni a tattare dashi, kai kace ba dashi ake ba. A wannan lokacin Han'Amuru ya zube a ƙasa hawaye suna zuba daga idanunsa. Wannan ita ce mafi girman fasaharsa. Da ita yake narka tsaunuka kuma ya baje garuruwa, dan mai za'ace ta kasa narka jikin dan-adam?
A wannan lokaci ya tuno mahaifinsa na wajen kuma lallai yana kallonsa a wannan lokaci. A hankali ya miƙe yayi kururuwa sannan ya afka kan Ƙaraiƙisu.
Ƙaraiƙisu bai motsa ba har saida Han'Amuru yazo gab dashi. A wannan lokaci yasa bayan hannunsa ya doke Han'Amuru. Wata iska mai kama da guguwa ta ɗebi Han'Amuru tayi cilli dashi cikin yan-kallo. Bakin yan-kallo kawai buɗewa yayi yaƙi rufuwa. Kowa dai yaga abinda ya faru tun daga farkon wannan faɗa har karshensa. Zaka iya cewa ba faɗa akai ba, kawai dai cin-zali akai. Hasalima ko kaɗan ƙaraiƙisu bai nuna alamun wani abu ya faru ba. Da alkalin wasa ya tambayeshi ko yana bukatar hutu sai yace baya buƙata kuma yana so a fara wasa na gaba nan take.
Minti goma-sha-biyar kacal aka ɗauka kafin a shirya wani sabon filin. Nusi ta fuskanci ƙaraiƙisu.
Abin mamaki Ƙaraiƙisu ne ya fara yin magana."Zan so naji menene a doron ƙasashen kudu da arewa wanda babu shi a sashin ikwatora harda zai saka sarauniya guda kamarki ta fito yawon duniya. Shin mulkin ne bai ishe ki ba, ko kuma ƙarin ƙasa kike nema?"
Nusi ta kaɗa kafaɗa.
"Kaga laifi na dan ina neman ƙarin ƙasa? Naji ance hatta kai dinnan da kake mulkin dukkan ikwatora baka daina neman ƙarin ƙasa ba."
Ƙaraiƙisu yayi murmushi baice komai ba. Tsahon mintuna suna kallon juna, kowa acikinsu yana ƙoƙarin gane mai ɗan-uwansa yake tunani.
Bayan ɗan-lokaci Nusi ta buɗe baki tace, "amma idan zan tambaya meye dalilin da yasa ka shiga gasar jinzidal? Na daɗe ina tunanin kana daga cikin kaɗan na mutane wanda basa biyayya ga Ururu. A lokuta da dama na ganka kana ƙoƙarin kai hari doron ƙasa ta farko. Ka hana a gudanar da gasar jinzidal a sashin ikwatora. Shin wane dalili ne zai sa kamar ka ya shiga gasar jinzidal yanzu?"
Ƙaraiƙisu ya fashe da dariya. Ganin haka yasa wasu daga cikin yan-kallon suka wage baki cikin mamaki. Wai daman yana dariya?
"Wannan ita ce tambayar da kowa yake son jin amsa. Sai dai bani da niyar bada amsa. Nafi son kowa ya gani da idonsa idan lokaci yayi. Abu ɗaya zan fada miki: acikin mutane akwai waɗanda zasu iya yin komai domin su cika burinsu. Irin wannan mutane sune suke kafa tarihi. Ni ƙaraiƙisu, ni zan kafa tarihi a wannan zamani."
Nusi ta ɗan-runtse ido cikin tunani. Acikin maganganun Ƙaraiƙisu akwai ma'ana. Babu wanda zai taɓa tunanin sarkin zai yiwa Ururu biyayya harma yazo ya taka rawa a gasar jinzidal, amma kuma gashi yazo. Dole akwai wani ƙulli wanda mutane basu sani ba. Wane irin alƙawari Ururu sukai masa har ya yadda ya fito daga sashin ikwatora? Babu wata hanya da Nusi zata iya sanin hakikanin mai ya faru, amma dai tabbas ta san akwai wani babban dalili da yasa Ƙaraiƙisu yazo da kansa yake taka rawa a wannan gasa. Koda yake a halin yanzu dalilinsa bai dame ta ba, babban abinda ya dame ta shi ne wane irin canji zuwan ƙaraiƙisu zai jawo acikin shirye-shiryenta na kubutar da Fatima da Zaikid? Tabbas idan tayi ƙoƙarin tayar da hayaniya a wajen ƙaraiƙisu zai iya taka mata birki kafin Ururu su sako hannu. Dole tasan hanyar da zata yi amfani da ita.
"Yanzu Ururu kake yiwa biyayya kenan? Kaci amanar sashin ikwatora."
Ƙaraiƙisu ya kaɗa kafaɗa. Bashi da amsar da zai bata, ko kuma kace yana ganin bata amsar bashi da amfani.
Tsawon minti guda cur suna kallon-kallo kafin Nusi ta ɗaga hannu ta zana wani hatimi akan iska. Bayan kimanin dakika biyu sai hatimin ya ɓace sannan a dai dai wajen da hatimin yake wani ƙatoton kwarangwal ya bayyana. A hannunsa akwai wata takobi ta ƙashi wadda take bada haske mai ɗaukan idanu tun daga nesa. Idanun yan-kallo suka juyo kan wannan mutum-mutumi da kuma takobin dake hannunsa. Sai dai kuma basu jima suna kallo ba sai mutun-mutumin da takobin suka ɓace. Ana jira a ga wani abu ya faru sai Nusi ta fara zarya, tana zagaya ƙaraiƙisu wanda ke tsaye a tsakiyar filin bai motsa ba. Bayan ta zagaya sau uku ta afka masa gadan-gadan. Daga nesa idan ka hangeta zaka ga bata fi tsawon idan sahun Ƙaraiƙisu ba, amma kuma babu alamun tsoro ko kaɗan a tattare da ita. Tana tafiya cike da yarda da kai da manyan taku masu nuna kwarewa. Sai da takai nisan zira'i guda daga inda yake sannan ta dunkule hannu ta kai masa duka. A tsakanin hannunta da Ƙaraiƙisu tukunyar dafa magani ta bayyana, muciya ta bayyana akan iska ta fara juya abinda ke cikin tukunyar. Nan take hayaki ya fara tashi daga cikin tukunyar, ƙanshin magani ya cika ko'ina.
Da tukunyar, da muciyar, da hayakin dake tashi, duk suka juye izuwa wata yar ƙaramar bishiya. Dukkan abubuwan da suka faru tun daga bayyanar wannan tukunya har zuwa juyewarta izuwa bishiya duk ya faru ne kafin dukan da Nusi ta kaiwa ƙaraiƙisu ya sauka. A dai-dai wannan lokaci hannun Nusi yana gaf da sauka akan Ƙaraiƙisu amma kafin ya sauka bishiyar data bayyana a saman hannun Nusi ta juye daga yar ƙaramar shuka zuwa zangarniya mai rassa daban-daban.
A nasa ɓangaren ƙaraiƙisu bai tsaya harin ya sauka a kansa ba, inda ya jada baya ya dunkule hannu ya kawo duka. Girman hannunsa ya kai akalla goman na Nusi. Mutum zaiyi mamaki da tunanin ta yaya ɗan karamin hannun Nusi zai tare basamuden hannun ƙaraiƙisu. Tuni da dama daga cikin yan-kallo sun daɗe da bawa ƙaraiƙisu nasara. Sai dai kuma hannayen suna gaf da haɗuwa sai kowanne reshe daga cikin rassan bishiyar suka fara tsayi suna tunkarar ƙaraiƙisu da gudun tsiya. Kowanne reshe ya juye izuwa hannu irin na Nusi. Hannaye sama da talatin suka haɗu tare da hannun Nusi suka tari hannun basamuden. Ƙasa tayi girgiza sannan iska mai ƙarfin tsiya ta tashi sama tayi watsi da yan-kallon dake kusa. Wadanda ke nesa kuwa babu abinda suke sai toshe kunne da ido saboda ƙara da rugugi.
Hannayen Nusi suka jada baya suka ƙara kawo duka. Shima Ƙaraiƙisu dunkule hannu yayi ya ƙara afka mata. Cikin dakika bakwai sun kaiwa juna hari goma-goma. Filin da suke kai yayi daga-daga. Ƙura ta turnuke ko'ina tayadda koda ka ƙura idanu baza ka hango komai ba. Nusi da Ƙaraiƙisu sun himmatu wajen kaiwa juna duka.
Wani abin mamaki a dai-dai lokacin da ake tsaka da fafatawa tsakanin ƙaraiƙisu da Nusi, acikin kurkukun da aka ajiye su Fatima wata mace ce tsaye a bakin ƙofar ɗakin. Bari mu ajiye zancen tayadda akai wannan mace tazo wannan guri da kuma tayadda akai ta ratsa ta cikin dubban ma'aikatan dake gadi, mu dubi yadda wannan mace take a nutse, kai kace acikin ɗakinta take tana bacci. Kallo ɗaya kacal zaka gane Nusi ce ba wata ba. Abin tambayar wace Nusin Ƙaraiƙisu yake faɗa da ita? Waccece ta gaskiyar? Shin Armad ya sammata fasahar mutun-mutumi ne ko kuwa ita ma tana da nata sirrin?
"Wacece ke?" Fatima ta tambayi Nusi.
"Suna na Nusi Wilbafos."
Fatima da Zaikid suka kalli juna cikin al'ajabi. Babu ko alamun ƙanshin Wilbafos a jikin Nusi. Hasalima Zaikid yana jin sinadarin gidan Kil'zanki a jikinta wanda hakan shi kansa abin mamaki ne tunda gidan Kil'zanki sun daɗe da ƙarewa.
"Koda yake asalin suna na Nusi Kil'zanki, amma yanzu na canja. Nazo na fitar daku a bisa umarnin sarki Armad."
Nan take Nusi ta zube a ƙasa kan gwiwowinta.
"Gaisuwa ta tabbata ga iyalan Wilbafos manya na Farkon Lokaci."
Zaka iya cewa da Zaikid da Fatima duk sun kasa magana. Sun rasa mamaki zasu yi, ko al'ajabi.
Bayan tsahon lokaci Fatima ta yunkura tace, "a ina kika san Armad?"
"Nasan Armad tun sanda ya fito nemar miki magani. Amma ina jin kamar mun san juna tun daga Farkon Lokaci."
Fatima ta ƙura mata ido. Akwai yadda da soyayya a idanun Nusi duk sanda ta ambaci Armad. Ga zaren izza maɗaukaki a jikinta. Tun daga inda take tana ganin yadda izzar Nusi ta tsaru ta jeru a layi kamar ta manyan sarakuna. Da Armad ya tambayeta da zata bashi shawara ya auri wannan mace mai suna Nusi.
"Hmmm.." Fatima tayi wani murmushi mai ɗaci. "Wato babu wanda yasan gobe sai mahalicci. Waye zai taɓa tunanin ƙoƙarin da nake na hana Armad da Abijan koyar izza da shiga al'amuran duniya shi ne zai zamo musabbabin lalacewar komai?"
Tana magana ƙasa-ƙasa lamarinda yasa Nusi ta fahimci bata buƙatar amsa saboda haka tayi shiru duk kuwa da bata fahimci abinda take cewa ba. Hasalima bata san wacece Abijan ba.
Shi kuwa zaikid yasan sarai abinda yake faruwa. A lokacin da Fatima ta fita yaƙin tawaye wanda ya faru a shekarar 1853 ta fita ne domin ta kare Abijan wadda ke tsare a hannun Ururu. A sakamakon haka ta fara rashin lafiya wadda ta tilastawa Armad fita neman magani. A dalilin haka Armad ya shiga duniya. Haka a yanzu ma ta fito ne domin ta bayar da kanta a wajen Ashura a maimakon Armad. Tayi tunanin Ururu zasu karɓe ta su haƙura da kamfen kamar yadda a baya suka karɓi Abijan, amma hakan bata samu ba. A dalilin haka yanzu gashi Armad da mutanensa sunzo domin su ceto ta. A dalilinta (ita da take gudun yaƙi da tashin hankali wanda har hakan yasa suka rabu da mijinta) gashi za'ai wani gagarumin yaƙi wanda babu wanda yasan rayukan dazai ɗiba.
"Ina Armad?" Inji Fatima.
Nusi tayi shiru tana tunanin amsar da tafi dacewa. Shin ya kamata ta gaya musu Armad ya ɓata, ko kuwa? Gashi baza ta iya yi musu ƙarya ba kasancewar a gaban mutanen Farkon Lokaci abin kunya ne ayi ƙarya.
"Armad... ya ɓace," inji Nusi. Ta kwashe duk abinda ya faru ta bayyana musu.
Nan take suka shiga tauna maganar. Kowa yana kawo abubuwan da yake tunanin sun faru. Daga ƙarshe dai abinda ya katse su shi ne takun masu gadi da suka jiyo sun taho.
"Kuyi haƙuri bazan iya tafiya daku ba a yanzu," inji Nusi. "Amma zan kwace ku a hannun wanda ya siye ku komai tsanani."
Da wannan Nusi ta ɓace. A lokacin da masu gadin suka iso babu komai sai fili.
Idan muka koma filin gasar inda Nusi take fafatawa zamu ga babu kowa acikin filin sai Ƙaraiƙisu. Bayan da ƙura ta lafa komai ya fito fili sai ƴan-kallo suka fara salallami.
"Ya narka ta!"
"Dama naji ance samudawa sukan iya juya mutun izuwa toka."
"ALLAH sarki Nusi! Da kamar zata yi abin kirki."
Tsahon lokaci yan-kallo suna maganganu. Kusan dukkansu sun aminta Nusi ta mutu. Har ma suna ganin Ƙaraiƙisu ya gama da gangar jikinta shi yasa basu ganta ba. Amma kuma manyan baƙi dake sama da sauran manyan ma'abota izza dake cikin wajen basu yarda da hakan ba. Acikin idanunsu akwai kokwanto domin sun san Nusi bata mutu ba, amma kuma sun kasa gano inda take.
Bayan tsahon lokaci alkalin wasa yayi gyaran murya.
"Shin hakan na nufin sarkin ikwatora, Ƙaraiƙisu, shi ne yayi nasara kenan?" Inji alkalin wasan. Yayi shiru kamar yana jiran wani yayi masa bayanin mai ke faruwa, ko kuma ace ba haka bane. Bayan ɗan lokaci ya leƙa ɗakin manyan baƙin inda yaga har yanzu tattaunawa suke yi akan sakamakon. "A halin yanzu zamu je hutu na rabin sa'a. Kowa ya zauna a wajensa. Muna dawowa zamu bayyana wanda yayi nasara."
Da wannan alkalin wasan yayi dabara ya bawa mahukunta dama suyi shawara kafin ya bayyana wanda yayi nasara.
"Kaji yadda abin ya faru," inji Nazára.
Armad ya haɗe gira cikin rashin fahimta. "A'a, to ta yaya kuka gudu daga filin wasan?"
"Cokali," inji Nazára. "Kafin mu shiga sai da muka tabbatar Cokali zai iya rubuta mu acikin littafinsa. Muka bashi lokaci."
***
Cokali yana zaune akan dutse. A kewaye dashi akwai kwamanda Jan-doki da kwamanda Asifu, da Inyaya takobin jini, da mai unguwa Shísu, da sarkin Bai. Dukkansu suna kewaye da dutsen a wani salo na bada kariya. Daga wajen idan ka nutsu zaka hangi dogayen gine-gine a can nesa irin na doron ƙasa ta biyu. Daga ɗaya daga kuma zaka hango bango. Duk yadda akai suna bakin gaɓa.
A hankali Cokali yaci gaba da rubutu.
Bayan da ya kammala sai ga hoton Nusi da Nazára da Giwa sun bayyana. Daga nan ya fito dasu daga cikin littafin.
"Yaya? Kun gansu?" Inji Cokali.
Nusi ta gyaɗa kai. "Suna ciki a ɗaure."
"Yaya yanayin tsaron?" Inji jan doki.
Nusi tasa hannu a jakar tsafinta ta ɗauko zane a takarda na taswirar ginin ta nuna musu.
"A wannan ƙofa akwai mutum goma sha daya, dukkansu ƙassai. Idan ka miko ta wannan barandar akwai ma'aikata uku suna gadi, dukkansu sammai. Sai kuma wasu ukun a dai-dai ƙarshen katangar nan. Daga nan zuwa inda aka kulle su akwai ƙofofi guda uku, a kowacce ƙofa akwai ma'aikata biyar-biyar, uku sammai, biyu ƙassai. Ina ganin babu wata hanya da zamu iya kubutar dasu ba tare da munyi gaba-da-gaba da Ururu ba. Shi yasa na yanke shawara mu bari sai an siyar dasu sai mu tare wanda ya siya a hanya mu kwace su."
Asalin yadda suka tsara su kwato su Fatima kafin a siyar dasu. Amma basu da ƙarfin da zasu iya shiga har inda aka ajiye su Fatima su kwato su.
Bayan ɗan lokaci Nazára ya numfasa yace, "Nima na yarda da wannan shawara. Mu jira a siyar dasu daga baya sai mu bisu. A lokacin sun bar hannun Ururu."
Nan take suka amince akan haka.
Nusi ta ƙara zaro wata takarda mai ɗauke da sunaye daga jakar tsafinta ta miƙawa Cokali.
Cokali ya miƙa hannu ya karɓi takardar.
"Akwai sunayen otal guda huɗu akai, akwai adireshin kowanne da kuma kuɗin daki," inji Nusi. "Kada ka buɗe sai mun rabu. Zai fi mu rarrabu domin koda abokan gaba sun cin mana ba zasu tarar damu a waje ɗaya ba."
Ta zaro wasu takardun ta miƙawa kowa acikinsu banda Nazára. Kowacce takarda a nannade take tayadda babu wanda zaiga abinda ke cikin ta sai an buda.
Kowa ya kalmashe takardarsa ya saka a aljihu. Abinda suka riga suka sani shi ne suna gidan abokan gaba kuma lallai ya kamata su zamo cikin shiri ko da wani abu zai faru acikin wannan kwanaki.
Bayan bayani akan abubuwan da kowa ya kamata yayi da kuma sunan da kowa zai canja sai suka juya suka nufi cikin gari.
Suna cikin tafiya suka jiyo hayaniya a bayansu. Fuska cike da mamaki suka juya suna ƙoƙarin gano mai ke faruwa.
Ƙura ce ta turnuke daga can nesa jikin bango. Nusi ta kalli Nazára suka haɗe gira cikin kokwanto. Aƙalla sun ji izzar mutun dubu goma acikin ƙurar.
Ba jimawa suka ga kurar ta kara turnukewa alamun faɗa ya kacame.
A ransu kawai tambayoyi ne irin su: su waye? Ta ina suka fito?"
Shísu, da Inyaya, da sarkin Bai, da Barilu suka zare makamai cikin shiri.
A hankali ƙura ta lafa na cikin ƙurar suka fito fili. Sadaukai ne sahu-sahu akan dawaki. Yawansu a ƙiyasi zai kai dubu goma-sha-biyar. A lokacin Nusi ta fara hango fuskokin data sani. Baki a wangame, fuska cike da mamaki, suka tsaya suna kallo har rundunar suka iso.
Yarima Najunanu, da yarima Umaru (wanda shi ne yarima mai jiran gado yanzu), da yarima Abba suka sakko daga kan dawakansu suka nufo inda suke tsaye.
"Nusi Wilbafos?" Inji yarima Najunanu.
Nusi ta haɗe gira. Har yanzu ta kasa gane mai ke faruwa.
"Ya akai kuka taho kuka barmu?" Inji yarima Umaru.
Nazára ya shige gaba yana cewa, "kwana ukun da kuka bamu ne suka cika. Ko kun canja shawara ne?"
"Hmmm.. ko mun canja shawara?" Yarima Najunanu yayi ɗan murmushi. "Kana tunanin zan bar ƴar-uwata a hannun Ururu ba tare da nayi komai ba?"
"Ƴar-uwarka?"
Nusi ta ƙara yamutse fuska. Shekaran-jiya suke fama da Maikiro'Abbas ya yarda Fatima ƴarsa ce amma yaƙi amincewa.
"Fatima yaya ta ce," inji yarima Najunanu kamar yana mamakin yadda akai Nusi bata sani ba. "Koda mahaifina bazai zo ba, ni ya zamar min wajibi."
"Wato duk ƙarya kukai mana kenan?" Inji Cokali. "Kuka ce baku da alaƙa da ita? Wannan ya saɓa da al'adar mutanen Farkon Lokaci."
"Ba ƙarya acikin zancen sarki," inji yarima Abba. "Sarki bashi da alaƙa ta jini tsakaninsa da Fatima. Abokinsa Zaikid shi ne ya haifi Fatima. Riƙo aka bamu ita a wancan zamanin. Tunda lokaci ya tsawaita zaiyi wuya ku samu asalin labarin. Mahaifinmu yana so ya tabbatar da niyyar ki ne kawai. Shin da gaske zaku iya yin komai akan ku ceto Fatima da Armad? Domin sai mun san haka zamu iya bayyana muku shirin mu na rusa Ururu a doron ƙasashen ƙasa."
Jin wannan kalami yasa kowa yayi shiru yana kallon ƴaƴan sarkin uku da kuma rundunar dake bayansu. Wai daman sarkin kawai gwada ta yake yi?"
Nusi ta daki ƙasa da ƙafarta. "Kun ɓata mana lokaci a banza. Shi sarki Maikiro'Abbas bashi da ikon ganin aniya ta. Kallo ɗaya yasan bada wasa nake ba."
Nusi ta fara huci. Nazára yayi sauri ya tallafeta da kalmomi na bada haƙuri. Sannan ya juyo wajen ƴaƴan sarkin.
"Yanzu meye shirinku?"
"Mataki na farko," inji yarima Najunanu. "Zamu shiga garin Bisad mu ɓuya gidajensu. Daga nan zamu jira umarnin sarki."
A'a, wai sarki Abbas zaizo da kansa?
Yarima Umaru ya gyaɗa kai kamar yasan mai Nazára yake tunani.
"Idan sarki bai zo ba waye zai jagoranci yaƙin?"
***
Koda Nazára yazo nan a labarinsa sai yaja dogon numfashi ya dubi Armad wanda ke gefe yana sauraronsa.
"Dukkan rundunar mu suna cikin garin Bisad suna jiran umarnin sarki Maikiro'Abbas. Labarin yadda akai muka shigar da rundunar mutun dubu goma sha biyar garin da shalkwatar Ururu suke ba tare da kowa ya ankare ba yana da tsaho, a yanzu babu lokacin baka shi, amma dai kayi sani tuni runduna sun hallara."
A dai-dai wannan lokaci sun iso bakin wani rafi da yayi iyaka da garin Farsa - ɗaya daga cikin ƙananun ƙauyukan doron ƙasa ta biyu.
"Mu jira anan saboda kada mu shiga gari mu fallasa mutanen mu dake ɓoye," inji Nazára. "Zamu hango umarnin sarki daga nan."
"Ta yaya umarnin zaizo?" Inji Shata.
"Ance idan umarnin yazo zamu gane," inji Nazára.
Zaikid yayi murmushi. Yasan sarai abinda abokinsa yake niyyar aikatawa saboda haka ya gyada musu kai.
"Ina kyautata zaton na gane umarnin da sarki yake nufi. Mu jira kawai."
Armad da Shata suka kalleshi cikin tambaya. Bayan ɗan lokaci baice komai ba sai suka rabu da zancen. Yawanci idan Zaikid yayi irin wannan to yana nufin zasu gani da idon su.
Armad ya juya wajen Nazára.
"A takaice dai Nusi ta bar Nostaljiya da Lamarudu da Inara a garin Iluru, kai kuma kaje baka gansu ba. Zata iya yiwuwa har yanzu suna garin, ko kuma sun gudu bayan sun gano Ayubu."
Nazára ya gyaɗa kai. "Kada ka damu zamu nemo su duk inda suke zarar aka kammala yaƙin nan. Nusi tana ganin akwai yiwuwar mu haɗu dasu a nan ma."
Armad yayi shiru baice komai ba. A ransa kawai tunani yake akan abinda ya faru. Wai har Nusi ta gane Ayubu amma Nostaljiya ta kasa ganewa. Yayi ƙoƙari matuƙa ya ɓoye ɓacin ransa amma sai da ya bayyana.
Zaikid ya dafa kafaɗarsa acikin lallashi amma baice komai ba.
A ran Armad kawai lissafa irin kisan da zai yiwa Ayubu yake yi. Lallai idonsa idon Ayubu sai yaga bayansa.
Ya nemi waje ya zauna ya rufe ido. Nazára da jan doki da Asifu suka ja gefe. Zaikid rubuce-rubucen ɗalasimansa ya fara. A yayinda Shata ya gishingida ya rufe ido.
Basu jima suna jira ba samaniya ta fara kaɗawa. Ruwan dake cikin rafin dake gabansu ya fara tashi sama kamar wanda ake zuƙowa. Kafin kace kwabo rafin ya tashi sama baki ɗaya. Idan ka kalli ramin babu komai sai ƙasa da kifaye suna wutsil-wutsil. Dukkan ruwan dake ciki ya tashi sama akan idonsu. Tun yana tafiya a hankali suna hango shi har suka daina ganinsa. Haka kudiddifai da koguna dake doron ƙasa ta biyu a gurare da dama suka ringa tashi suna yin sama. Kafin kace kwabo sama ta juye, ta rikide, ta rincabe.
Zaikid yayi murmushi ya dubi su Armad.
"Ga umarnin sarki nan."
Armad ya miƙe. Lokaci yayi. Bazai iya amfani da fasahar Aiban'shisu ya kai su garin Bisad ba tunda bai taɓa zuwa ba. Saboda haka ya umarci Nazára ya samar musu da jirgin sama irin wanda sukai amfani dashi a duniyar aljanu. Shi kuma Armad ya ɗaurawa jirgin fasahar Kaban'Zishu.
Nan da nan suka ɓace a sararin sama. Minti sha uku da yan dakiku suka iso garin Bisad. Tun daga nesa suke hango abin mamaki.
Wato kamar yadda aka bayyana an saka dokar hana fita a garin. Kowa yana gidan a kulle. To amma a dai-dai wannan lokaci ƙofofin gidajen ne ke buɗewa mutane suna fitowa daga ciki. Da farko zakai tunanin mutanen garin ne waɗanda suka gaji da zama a gida, amma idan ka nutsu zaka ga sadaukai ne ma'abota izza sanye da kayan yaƙi. Kai idan ka matsa kusa zaka fuskanci ba wasu bane illa rundunar da yarima Najunanu da yarima Umaru suka kawo.
Wato Ururu sun hana mutane fita, sun kulle su a gida saboda kada abokan gabarsu su saje dasu, sai dai basu san tuni abokan gabarsu suna cikin gidajen a ɓoye ba.
Nan da nan aka buga kugen yaƙi. Duk wani ma'aikaci dake kusa ya zare makami ya tunkaro wajen da niyyar hana rundunar haɗuwa. Sai dai duk wanda ya matso sai kaga ya zube a ƙasa yana karkarwa ya kasa komai. Tun daga nesa Armad yana jin ƙarfin izza ta musamman wadda ita ce ta saka ma'aikatan rawar ɗari.
Armad bai taɓa jin irin wannan izza ba. Tayi kama da yanayin hunturu amma kuma tafi sanyin babban sihiri sanyi. Akwai shekaru ababen daɗewa acikinta. Da wasu zarurruka ababen kauri, da buwaya, da haske. Kallo guda Armad da kansa ya gigita ya rufe ido. Kai kace mafi girman rana ce ta haske masa ido. Da Armad, da Nazára, da Shata, da su jan doki kawai ƙoƙari suke yi su gane waye mai wannan izza amma sun kasa saboda yawan mutanen dake taruwa a bayansa.
Duk sadaukan dake fitowa daga gidajen sai kaga sun hau layi a bayan wannan izza. Kafin wani lokaci tuni mutun sama da dubu sun taru a bayan ma'aboci wannan izza.
A gefensa na hagu akwai samari uku, a gefensa na dama Nusi ce da Cokali da wasu mutum huɗu. A bayansa mutun uku ne dattijai wanda Armad yake tunanin salsa ne.
A ɗaya ɓangaren abokan gaba sun kasa komai sai jada baya suke yi. Zuciyarsu tayi rauni a gaban wannan izza.
Bayan ɗan lokaci Armad ya samu dama ya danna kai cikin izzar wannan mutum. A lokacin ya ƙara ganin girmanta. Tuni ta haura duk wani abu daya taɓa ji a jikin ɗan-adam.
Da sauri suka ƙarasa. Armad da Nazára dasu jan doki suka tsaya a gefen Nusi wadda ta kalleshi tayi murmushi amma bata ce komai ba. Shata ya tsaya a kusa da Armad, a yayinda Zaikid ya koma bayan Maikiro'Abbas ya jeru da mutun ukun dake wajen.
Kowa ya hallara. A lokacin Armad yaga fuskar ma'aboci wannan izza. Ba wani bane illa sarki Maikiro'Abbas.
Ba tare da cewa komai ba suka rankaya izuwa Filin-jiri. Koda ma'aikatan suka tabbatar baza su iya yin komai ba sai suka rankaya da gudu izuwa Filin-jiri suka bayyanawa Dul'Ururu halin da ake ciki.
Dul'Ururu ya miƙe tsaye a fusace. Yasan duk abinda zaiyi bazai iya hana Maikiro'Abbas zuwa Filin-Jiri ba saboda haka yayi umarni a buga kugen yaƙi.
Mikewar Dul'Ururu yasa sauran kwamandun Ururu suka miƙe.
A lokacin Maikiro'Abbas da tawagarsa suka iso Filin-Jiri.
A ɓangare ɗaya Dul'Ururu ne, da mayaƙan Ururu, da masu goyon bayan Ururu, da kuma masu neman suna a wajen Ururu. A ɗaya ɓangaren kuma Maikiro'Abbas ne, da ƴaƴansa, da zuri'ar Wilbafos, da kuma masu goyon bayan gidan Wilbafos.
Zaka iya cewa Fatima ita ce ta haɗa wannan yaƙi wanda a halin yanzu yinsa ya zama wajibi. Duk wanda yayi nasara to shi zai kafa daula a ƙasashen ƙasa. Da dama acikin masana masu rubutu akan al'amuran yau da kullum suna ganin wannan yaƙi yafi gaban Fatima ita kaɗai. Ururu suna so su kawar da Maikiro'Abbas su kafa babbar daula a ƙasashen ƙasa wadda zata shafe ko'ina. Suna so ƙasashen su fara yaren Ururu kamar a doron ƙasa ta farko.
Shi kuma a nasa ɓangaren, Maikiro'Abbas idan yayi nasara to ta tabbata shi ne uba kuma sarki a doron ƙasashen ƙasa.
Taku dai-dai, Maikiro'Abbas ya matso gaba. Kamar sama tana biyayya ga aniyarsa sai ruwa ya fara zuba. A lokacin Armad ya lura sarkin acikin shirin yaƙi yake. Babu sulke, babu kwalkwali, babu takobi, amma kallo guda zaka san acikin shirin yaƙi yake. Gabjeje ne mai tarin damatsa da kauri daga buwaya.
Ga littafi nan a rataye a kafaɗarsa ta dama, da kuma jakar tsafi a rataye a kafaɗarsa ta hagu. Boka yakai boka.
Armad yana hango Dul'Ururu ya dunkule hannu. Ibraham Nil kuwa kawai gumi yake. Suwainah ta nutsu tana nazarin izzar Dul'Ururu. Ƙaraiƙisu kawai murmushi yake. Kana gani kasan yana cikin farin ciki. Dama ya daɗe yana neman ma'aboci izza da zai kara dashi ya rasa, yau ga dama ta samu.
Kafin wani yayi wani abu kawai sai ga Ayubu da Deniz Iluru sun shigo filin yaƙin. A take Dul'Ururu yasa aka basu guri kamar daman sun shirya.
A wannan lokaci kowa ya hallara. Abinda kawai ya rage a zubda da jini. Mai ƙarfi sai ALLAH ya isa.
Maikiro'Abbas ya ɗaga hannu sama ya kira babbar izza....
#
Ƙarshen Book 4....
Alhamdulillahi.
Comments
Post a Comment