"Mayaƙan Ururu!" Maruta ya daka musu tsawa ganin suna jada baya. "Mai kuke yi haka? Ku kashe shi? Mutum ɗaya ne fa, tsoho tukuf? Tsoron mai kuke ji?"
Jin haka mayaƙan suka ƙara azama suka danno kan Maikiro'Abbas. Ganin haka Maikiro'Abbas yayi dariya. Yana tsaye ya jira suka ƙaraso sannan ya kaɗa sandarsa yayi kansu. Da farko mayaƙan sunyi baya, amma da suka ga babu alamun hari a tare dashi sai suka zagaye shi, su kuwa mayaƙan Maikironomada juya sukai da gudu baya. Sun riga sun san halin uban gidansu.
Wani daga cikin mayaƙan Ururu ya samu ya ƙarasa kusa ya sari Maikiro'Abbas a idon sahu, jini yayi sama.
"Dama yana zubda jini?"
"Aka ce jininsa na ƙanƙara ne?"
"Haha... Indai yana jini kuwa ai za'a iya kashe shi."
Inji mayaƙan.
Ganin haka suka ƙara azama wajen kai masa sara, harbi, da suka. Sai da yaje tsakiyarsu sannan ya tsaya. A hankali ya ɗaga ƙafa ya daki ƙasa ya kira ɗalasimi.
"Jinin ƙanƙara!"
Da farko babu abinda ya faru amma a hankali sai kawai mayaƙan Ururu suka fara faduwa suna zubewa a ƙasa. Duk wanda ya faɗi sai kaga yana aman ƙanƙara.
Daga can baya mayaƙan Maikironomada ne suka ci gaba da gudu suna ƙara jada baya. Sun san fasahar da sarkin yayi amfani da ita sarai. Fasahar tana samar da wani shinge na tsafi a kewaye da sarkin. Duk wanda ya shiga cikin wannan shingen a take jininsa zai daskare. Maimakon fatar ka tayi ƙanƙara sai jinin ka yayi ƙanƙara ta yadda zaka daskare ta ciki. Tsahon minti guda babu wanda zai iya kusantar sarkin har sai shingen ya ƙare.
Ganin halin da ƴan uwansu suke ciki yasa mayaƙan Ururu suka manta da umarnin Maruta suka fara gudu.
Maruta ya daki ƙasa da ƙafarsa. "Ku kashe shi nace!"
Wani mayaki mai neman suna ya ɗaga takobi yayi kan Maikiro'Abbas. Kafin ya ƙarasa ya faɗi a ƙasa matacce, ƙanƙara tana zuba daga bakinsa da idonsa da hancinsa.
Maikiro'Abbas ya danna cikin mayaƙan yayi kan Maruta.
Ganin ya samar musu da hanya. Mutun goma wanda suka haɗa da Burjan, Zaikid, Nusi, jan doki, Najunanu, Cokali da mutanen ikwatora guda hudu sukai amfani da damar suka tashi sama suka wuce ta saman mayaƙan Ururu inda suka tunkari wajen da Armad yake.
Duk abinda ke faruwa bai tsayar da Dul'Ururu ba. Kawai saukarwa da Armad luguden duka yake a baya. Armad bashi izza ko kaɗan a jikinsa dazai iya kare kansa. Sannan kuma harin da Dul'Ururu yake saukar masa yasa bashi da nutsuwa ko kuma damar yin amfani da zaren izza ya ɗebi izzar mutane. Abu ɗaya kawai da yake iyawa shi ne tare dukan domin kada ya samu mahaifiyarsa. Ita kuwa Fatima a nata ɓangaren ƙoƙarin ture Armad take gefe domin ta kare masa dukan sai dai ankwar dake jikinta ta hana.
A wannan lokaci Maikiro'Abbas ya ƙaraso. Ya dubi Maruta yaga bashi da niyyar yaƙar sa saboda haka kai tsaye ya juya yayi kan Dul'Ururu.
Sai dai a dai-dai wannan lokaci, a wani daji da bashi da nisa daga Filin Jiri, sarki Ƙaraiƙisu ne kwance a ƙasa jini yana malala daga jikinsa. A gefe Saif-Al-Barzak ce take kallonsa ido a zare cike da mamaki. Bata taɓa gani ko jin labarin mutun irin Ƙaraiƙisu ba.
"Saif?" Inji Ƙaraiƙisu. "Naji daɗin wannan atisaye, amma kiyi sani a yanzu dole na koma filin daga domin naga daga ina wannan izza take tahowa." Ya ɗanyi shiru yana shanshanar iska kamar yana so yaji ƙanshin izzar dake yawo akan iska. "Ina tunanin zan samu abokin karawa acan wanda yafi ki."
Yana rufe baki ya miƙe tsaye sannan ya tashi sama akan iska. Minti guda bayan wannan tattaunawa Ƙaraiƙisu ya bayyana a saman Filin Jiri. Girman jikinsa ya rufe rana lamarinda yasa samaniya tayi duhu. Dukkan wanda ke filin ya ɗaga ido yana kallo. Shi kuwa ƙaraiƙisu nutsuwa yayi ya lalubo inda yake jin tashin izzar data zuƙo shi ya dawo filin. Bayan ɗan lokaci sai kawai ya tunkari ƙasa gadan-gadan. Mayaƙan Ururu suka dare sun zata kansu zai fado. Amma a hankali ya sauka a gaban Maikiro'Abbas.
"Baba Abbasu," inji Ƙaraiƙisu. "Izzar ka ce ta zuƙo ni. Saboda haka duk abinda ya same ka kada ka zargi kowa sai kanka."
Yana faɗar haka ya dunkule hannu ya kawowa sarkin duka.
"Ƙaraiƙisu," Inji Maikiro'Abbas a fusace. Ya kawo masa duka da nasa hannun. Suna haɗuwa hannun ƙaraiƙisu ya ƙanƙare tun daga kafaɗa har ƙasa. Amma abin mamaki kafin mutane su gama gane abinda ke faruwa ƙanƙarar ta marmashe tabi iska.
"Haha..." Ƙaraiƙisu ya fashe da dariya. "Maikiro'Abbas, shin tsufa yasa ka manta cewa sihirin ku baya aiki akaina?"
Ƙaraiƙisu yayi tsalle sama ya diro kan Maikiro'Abbas da gwiwa. Maikiro'Abbas ya dunkule hannu ya daki gwiwar lamarinda yasa tayi gefe ya samu damar kaucewa. Amma Ƙaraiƙisu bai bashi damar hutawa ba; yana dira yaci gaba da kawo masa duka ta hannu da kafa.
"Kashe shi ka samu babban rabo," inji Maruta wanda ya matso kusa yana kallon faɗan. Ƙaraiƙisu bai damu da wani babban rabo ba. Kawai so yake yi ya gwada gwanji.
A gefe guda kuma Dul'Ururu ya ɗaga sanda zai ƙara saukewa Armad.
"Wilbafosiyan Siwod Dans."
Zaikid ya saka takobi ya tare. A lokaci guda Nusi ta ƙarasa ƙasa ta ɗauke Armad da Fatima. Sun juya zasu tafi Diwani ya bayyana ya kawo musu duka da al'amudinsa. Jan doki, wanda ke bayan Nusi, ya shigo gaba ya saka takobi ya tare. Al'amudin ya haɗiye takobin sannan yayi bindiga. Dole Najunanu ya ƙaraso ya rufe jan doki da igiyar ruwa domin kada wutar ta ƙona shi. Bayan komai ya lafa, Diwani ya jada baya yana jira al'amudinsa ya ƙara haɗa jikinsa, shi kuma jan doki ya miƙa hannu ya ɗauki takobinsa wadda babu abinda ya same ta banda ɗan baƙi da tayi. Nusi ko tsayawa bata yi ba ta wuce gaba da gudu.
A wajen gadon aba'in kuma Nazára da Rabi sun ci gaba da fafatawa. Amma ganin sun kwato Fatima sai suka fara neman hanyar da zasu gudu. Musamman duba ga cewa yaƙin ya bar inda suke. A halin yanzu hatta Maruta yayi gaba yana kula da mayaƙansu. Shima Dul'Ururu ya tafi wajen Armad. Ibraham Nil da Suwainah da Han'ibal da Ayubu basu nuna alamun zasu kai musu hari ba.
"Kwamanda Binani," inji Nazára. "Kayi sanyi. Ga dukkan alamu koma mai Maruta yayi amfani dashi ya ƙara maka ƙarfi ɗazu yanzu ya tafi."
Jin haka Binani ya cije baki. Fasahar Maruta tana iya ninkawa duk wani mutum dake tare dashi ƙarfi, amma kuma bata daɗewa. Mafi yawa takai minti biyar ko kuma ƙasa da haka. Ya danganta da yawan mutanen da aka yiwa amfani da ita. Sai dai duk da haka Binani yana da yaƙinin zai iya cin galaba akan Nazára cikin sauki. Matsalar kawai Nazára ba yaƙin cin nasara yake yi ba, a'a, kawai yaƙin jan lokaci yake yi tayadda zasu samu su gudu da Fatima.
Binani yana cikin tunani Nazára ya miƙa hannu da sauri wajen da Rabi take. Yashin ƙarfe ya fita daga hannunsa yayi kan Rabi. Yana zuwa yabi jikin Rabi ya rufe ta ruf kamar akwatin ƙarfe tun daga sama har ƙasa. Nazára ya tafa hannu ya kira ɗalasimi a zuci. Kafin Binani ya ankare Nazára ya ɓace ya bayyana a kusa da akwatin ƙarfen da Rabi take ciki. Ya ɗauke ta sannan ya juya da gudu ya nufi yamma. Ance jada baya ga rago ba tsoro bane.
Sai godiya Dr
ReplyDeleteThanks for reading
Delete