Babi na 259-261
***
"Armad Djinn ko Armad wilbafos?" Mahaifiyar Armad ta tambayi Hidaya. A zaune a cikin ɗakin akwai Armad wanda ke gishingiɗe kan gado, da kuma farfesa Zaikida wanda ke tsaye a bakin taga yana kallon sararin samaniya. Sai kuma Hidaya wacce ke kusa da Armad. A taƙaice dai Taidara ne kawai babu.
Fatima ta numfasa taci gaba da cewa, "kar dai saboda wancan aljanun sun bawa kakanki martabar farfesa shi yasa kika zaɓi Djinn. Idan ba haka ba akwai sauran suna ye kamar su 'Abarai', 'Kil'zanki', 'Ƙarunu', 'Shata'..."
[Asalin sunan 'Djinn' yana nufin aljani, shi yasa Fatima ta hada shi da aljanun da suka bawa Zaikid martabar Farfesa.]
Hidaya ta girgiza kai a hankali. "Ba haka bane, mama. Kawai sunan Djinn yafi daɗi, kuma yafi girma da tsoratarwa. Shi shugaba dole ya zama yana da kwarjini da tsoratarwa."
Fatima ta kau da kai. Ga dukkan alamu bata lamincin sunan ba. Ta wani ɓangaren baza kaga laifin ta ba tunda wane ne zaiso a sawa ɗansa suna 'aljani'?
A wannan lokaci Zaikid ya shiga cikin maganar. "Indai Armad yana son sunan ai shikenan. Armad?"
"Ni sunan bai dame ni ba, abinda ya dame ni shi ne mai yasa dole sai mun canja sunan mu? Ururu sun sakko damu ƙasa, kuma sunan namu ma sai mun ɓoye." Inji Armad.
"Ja da baya ga rago ba tsoro bane, Armad." Inji Hidaya. "Idan sunan mu ya bayyana tun yanzu akwai jama'a da dama mabiya tsohuwar daular Wilbafos wanda zasu yi mubayi'a. Hakan zai jawo hankalin Ururu. A yanzu bamu da ƙarfin yaƙar su, abinda muke buƙata shi ne muyi sabon shiri a nutse kuma a ɓoye domin tunkarar su. Sabida haka dole muna buƙatar ɓoye wannan suna."
"A bani dalili guda ɗaya kwakkwara wanda zan yadda dashi a sakawa ɗana Djinn." Inji Fatima. Har yanzu sunan bai kwanta mata ba.
"Babu wani dalili mama... wataƙila... sabida aljanin dake cikin Miyurar sa." inji Hidaya.
"Aljanin dake cikin Miyurar sa? Har kin tabbatar aljani ne? Kada ki manta akwai Ji-Daime a jikinsa. Kema kinsan bazai yiwu ace ya mallaki aljani sama da ɗaya ba."
"Eh.... to. Ga sauran mutane haka ne, amma Armad na daban ne. Har yanzu dai bani da tabbas amma zan ziyarci duniyar aljanu na gani da ido na."
**
"Armad! Armad!!" Shal ta ɗaga hannunsa tana ƙoƙarin tashin sa daga baccin da yake yi.
Armad ya buɗe ido. Mafarkin da yake yazo ƙarshe. Baiji daɗin hakan ba domin kuwa a tsahon lokaci wannan ne karo na farko daya ga Hidaya ido-da-ido.
Yana ɗaga ido ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
Nan take kalmomin suka maƙale a maƙogaronsa. Kamar yadda aka bayyana akwai ratar daƙiƙa kusan uku kafin tunanin Armad ya dawo jikinsa. Yana dawowa ya tuno duk abinda ya faru jiya da yadda suka nutsa cikin duniyar aljanu.
Armad ya buga uban tsaki tare da miƙewa tsaye.
"Kaban'zishu."
Ya ɓace daga inda yake ya bayyana a wajen garin, inda ya rankaya izuwa titin Bayajidda. Kafin ya bar garin sai da yayo guzurin abinci da kayan shimfiɗa. Suma ragowar abokan tafiyarsa haka. Saboda haka a wannan rana babu zancen matsalar abinci ko abin sha domin kuwa a shirye suke. Suna haɗuwa Armad ya kira Kaban'zishu ya aika su katangar Bayajidda. Bayan kace-kace da Ranbir'shishirui da Dandir'shishirui suka samu hanya suka wuce.
Armad yayi ƙoƙarin yin sulhu da aljanun dake tsaron ƙofar shiga duniyar amma aljanun suka ƙi amincewa.
"ALLAH suturi-buƙwi nayi sulhu da ɗan tatsitsin bil'adama." Inji shugaban aljanun masu tsaron ƙofar.
Hakan yasa dole Armad yayi amfani da fasahar Zaren Manyan Mayu ya zuƙe dukkan izzar wannan aljanu ya barsu a sume.
Farkon zuwan Armad yana da izza dubu ɗaya. Bayan fafatawarsa ta farko da masu tsaron ƙofar ya samu ya haura matakin izza dubu hamsin. A wannan lokaci Armad ya kai dubu ɗari da dubu daya da kaɗan. Dukkan jikinsa ya fara canjawa, iskar dake kewaye dashi tayi nauyi tana ɗauke da izza abar jinjinawa. Fatarsa ta cika da kwarjini da kyawu. Kai hatta gashin Armad ya ƙara duhu da kyawu. Duk wannan alamu ne cewa izza ta shiga jikin Armad. Ya zama izza ita ma ta zama shi.
A ƙa'ida babu wani mahaluƙi da ya isa ya zuƙi izza mai yawa haka a lokaci ƙanƙani koda kuwa ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Dole ka bawa izzar dama da lokaci ta shiga jikinka sosai ta garwaye da jininka. Idan ba haka ba kuwa a kowanne lokaci izzar zata iya tarwatsewa, saboda bata tsaru ba.
Sai dai shi Armad na musamman ne. Shi kaɗai yake da jikin izza. Sabida haka duk wani sharri na izza bai shafe shi ba.
A waƙar maƙabarta Hidaya ta bar baiti cewa tana da shekarun izza dubu ɗari biyu da uku ta shiga matakin Deba. Armad yana ji a ransa shima bazai wuce hakan ba. Duk inda yakai shekaru dubu ɗari biyu zai shiga Deba, daga nan kuma ya cilla izuwa mataki na gaba.
Sai dai kuma kash. A har kullum abubuwa sukan sauya daga yadda ka tsara su. Armad na kai wa matakin izza dubu ɗari Miyurar sa ta fara haske. Jikinsa ya fara girgiza yana rawa. Nan take Armad ya juye izuwa walƙiya domin yana ji a jikinsa cewa a kowanne lokaci gangar jikinsa zata iya rududdugewa.
Abin mamaki shi ne duk da ya koma walƙiya hakan bai hana shi jin raɗaɗin ba. Kan kace meye wannan baƙar wuta irin ta Hidaya ta kama a jikinsa. Armad yai ƙoƙarin cije baki kada yayi ihu amma ina. Wannan wuta ta banbanta da duk wata irin wuta daya taɓa ji ko mafarki. Wuta ce mai ƙona walƙiya. Take Armad ya sume. Hankalin na cikin jirgin ya tashi, musamman Nusi da Nostaljiya.
Cikin sa'a al'amarin bai daɗe ba. Bayan awa guda Armad ya farka. Abu na farko daya fara fuskanta shi ne rashin ƙarfin jikinsa. Da farko baiyi zaton akwai wani abu ba amma yana dubawa ya iske izzarsa ta dawo dubu ɗaya kacal.
Ya jijjiga kai ya watsawa kansa ruwan sanyi dan ya farka amma bai farka ba, saboda dama can ba mafarki yake ba. Daga izza dubu ɗari da dubu ɗaya ya dawo izza dubu ɗaya. Ko'ina ragowar izzar ta tafi?
Amsar wannan tambaya na cikin miyurar Armad. Mutun-mutumin dake tsakiyar wannan miyura ya fara motsi yana juyawa kamar wanda aka sawa rai. Armad baiji wani sabon canji ba amma yana da cikakkiyar masaniyar cewa akwai wani abu a tattare da wannan mutun-mutumi.
Daga gamuwarsa da Tarifil-fakta zuwa wannan lokaci ya samarda Kaban'zishu, Zaren Mayu, Zaren Manyan Mayu, Zaren Damuna, da kuma Zaren Layya. Wannan fasahai ko kusa basu gamsar da Armad ba. Yana buƙatar izza irin wacca baza ta misaltu ba. Ana cikin haka ga kuma wani sabon al'amari ya taso.
"Lafiya? Mai ya faru?"
"Ya kake ji?"
"Miyurar ka na juyawa."
Haka mutanan jirgin sukai ta nuna damuwarsu ɗaya bayan ɗaya. Amma hankalin Armad na kan Miyurar sa. Shin idan ya ƙara tara wata izza zuƙewa zatai? Shin idan ta zuƙe izzar mai zai faru? Mai wannan mutun-mutumi yake nufi?
A dai-dai wannan lokaci suka iso bakin gari na farko. Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, tun a ƙofar ya fara tambaya.
"Kun san K'Narbig?"
"K'Narbig? A'a. Ina ne kuma haka?" Inji aljanin da suka tambaya.
Armad ya ja dogon numfashi jiki a sanyaye. A jiya babu wanda ya saurare su. A yau kuma babu wanda yasan sunan wajen da suke nema. K'Narbig shi ne sunan da Hidaya ta ambata a baitin ta na wakar makabarta. Armad bashi da masaniya sunan aljani ne ko kuma waje. Watakila ma sunan abinci ne.
Basu yi ƙasa a gwiwa ba haka suka ci gaba da tafiya tsahon awanni suna tambayar wannan suna har zuwa yamma amma babu labari.
"Mu wuce filin yaƙin kawai." Inji Armad. "Ina tunanin acan zamu samu labarin abinda da muke nema. Nasan akwai yiwuwar mu jefa kan mu cikin yaƙin da ba namu ba, to amma mun kewaya wannan duniya sama da kwana guda babu wani labari. Kada ku manta muna tafiya ne kan lokaci."
Mutun takwas dake cikin wannan jirgi sukai shiru na ɗan lokaci kafin daga bisani Nazara ya gyaɗa kai cikin amincewa. Nostaljiya da Nusi suka biyo baya. Sannan daga bisani dukkan ragowar fasinjojin.
Nan take suka kaɗa akalar jirgin zuwa yamma.
Wani abin mamaki da duniyar aljanu shi ne duk da kasancewar rashin doron ƙasa amma akwai tsaunika wanda hadari ya haɗiye ƙasansu, saman su kuma a ɓoye yake cikin gajimare. Kusan zaka iya cewa wannan tsaunika su suka cika mafi yawan duniyar aljanu. Garuruwa basu da yawa sosai. Bayan tsaunika kuma akwai bishiyu na gani na faɗa. Bishiyun suna da launi kala-kala amma dukkansu suna da girma na daban. Kaurin kowacce yakai zira'i dubu. Kai akwai wadda sai da suka shafe daƙiƙa maitan suna tafiya kafin su wuce ta. Yawancin bishiyun basu da ganye. Kai kace bishiyun rani ne wanda iskar bazara ta cirewa ɗauri.
Kowa acikin wannan jirgi yasan halin da ake ciki saboda haka hankalinsu na kan horo. Duk wani saƙo da loko na jirgin zaka iske wani yana koyon wata fasaha. Misali, a dai-dai bayan matattakalar data shiga cikin jirgin Cokali ne zaune ya tankwashe ƙafa, idanu a rufe, yana lazimin sabbin ɗalasimansa na Fasahar Marubutan Farko. A gabansa akwai takarda wadda ya rubuta sunayen muggan namun dawa ashirin da yake son ya samar.
Shi kuwa Iliyasisi na zaune acikin ɗaki yana sauya kamanni. A wani sa'in sai kaga ya juye izuwa tattabara, bayan ɗan lokaci sai kaga ya dawo zakara. Sannu a hankali sai kaga ya zama shaho ko dila ko mage. Wannan duk dabbobi ne na gida. Al'amarin Iliyasisi ya wuce haka. Yana iya juyewa izuwa Aljanin-zaki, ko Aljanar-Damisa, ko kuma Aljanar-kura.
Nusi na can bayan jirgin tana dafa magani. Idan mai karatu bai mantaba fasahar Nusi nada alaƙa da haɗawa da sarrafa magani. Asalin hikimar ta ta samo asali ne daga Fasahar Noma ta ƙabilar Kil'zanki. Ta hanyar wannan fasaha sukan iya shuka tsirrai su sarrafa su yadda suke so. Nusi tana iya shuka iri ya fito a lokacin, kuma ta kawo hari dashi duk a lokaci guda. Bayan shigarta Sammai ta samarda Negrinki wadda ta ƙara ƙarfafawa wannan fasaha ta ta ƙafa.
A dai-dai wannan lokaci Nusi tana zaune ta lankwashe ƙafa tana wasa da Negrinkin ta. A duk sanda Negrinkin ta taɓa ƙasan jirgin sai kaga ɓarangwal ya taso daga ciki ya bayyana. Duk wani matacce daya taɓa cin abinci daga jikin itacen da aka haɗa jirgin nan sai ya tashi a matsayin ɓarangwal yayi wa Nusi biyayya. Wannan ita ce fasahar Nusi.
Nostaljiya na zaune ta lankwashe ƙafa acikin ɗaki. Abinda take yi ya banbanta dana sauran. Maimakon ta maida hankali akan ƙarfafa fasahar ta kawai ƙarfin jininta take yaɗawa acikin jirgin. Duk wanda ke cikin jirgin yana amfana da ita. Saurin koyon fasaharsu ya ƙaru matuƙa yadda basa tsammani. Babban abin shi ne basu da masaniya akan cewa ita ce take agaza musu. Kowa yaga fasahar sa ta ƙaru amma basu san dalili ba. Wasu suna ganin cewa saboda canjin duniya ne kawai. Shi kuma Armad kansa ya ɗau caji da yawa ballantana ya lura.
Nazara da Babara basa yin komai. Suna zaune kurum suna kallon duniyar aljanu kamar Armad. Hakan ba abin mamaki bane domin kuwa a duk sanda ka kai ƙololuwar Sammai abubuwa sukan tsaya, komin horon da zaka samu a banza. Dole sai ka shiga Deba kafin abubuwa su dawo. Amma hakan duk a cikin lissafi ne. Zaka iya cewa shiri ne kawai ake yi na afkawa Deba.
Mutun biyu wanda suka fi kowa dagewa sune Inara da Lamarudu. Nostaljiya ta bawa Lamarudu fasahar kwangilar Armad amma har yanzu bai shiga Sammai ba. Shima Inara haka. Duk su biyun suna Jemai kuma ƙoƙarin da suke su kamo sauran na cikin jirgin ta hanyar buɗe Negrinkin su su faɗa Sammai.
"Shirin shi ne mu leƙa filin yaƙin mu wafto mutun ɗaya da zamu tambaya. Idan an dace sai mu kama hanya, idan kuma ba'a dace ba mu samu wani." Inji Armad.
Nazara ya ɗakko wani ɗan littafi dake hannunsa ya dudduba sannan ya ce, "Kara tunamin sunan."
"K'Narbig."
"Babu wani waje mai wannan sunan a taswirar da muke da ita. Sai dai kuma duk wajajen da muka sani inda muke zuwa cinikin ɗalasimai ne a wancan lokaci, dani da baba Dalja." Inji Nazara.
Babara yai tunani ya girgiza kai. "A gaskiya nima a ɗan zuwa na ban taɓa jin wani abu mai wannan sunan ba. Amma kamar yadda kace aljanun duniyar zasu fi mu sani."
A haka suka kwashe awa guda suna tafiya kafin su fara jiyo ƙanshin filin yaƙin.
Babbar matsalar ita ce wanda zai raka su filin yaƙin ma sun rasa. Sabida haka kawai yankar hanya sukai. Babu tabbas zasu iya isa lafiya ko kuma su ɓata a hanya. Sannan kuma dukkanin ɓangarorin biyu (Dordor da aljanu) babu wanda bazai afka musu ba idan suka haɗu.
Hakan ne yasa suka rage sauri, kowa ya zaro kayan aiki suka ƙara kula.
Sai dai kuma duk hakan bata faru. Sabida tsahon shekarun da akai ana gwabza yaƙi duniyar aljanu a miƙe take kamar titi. Duk garuruwan dake cikin daji an cisu da yaƙi. Wanda suka rage sun dawo cikin gari dan neman tsira.
Sabida haka bayan sun bar wannan gari na farko basu zame ko'ina ba sai birni na gaba mai suna Alzaina. Shima kamar na bayansa a cike yake da masakan aljanu matsorata. Babu wanda ya iya bawa su Armad cikakkiyar amsa.
Gari na gaba mai suna Labbasu shima bashi da nisa da Alzaina. Shima kamar na bayansa babu wanda yasan wani abu mai K'Narbig.
Koda magariba ta kawo kai duhu ya fara yi sai haƙurin Armad ya ƙare. Nan take ya kira ɗalasimin Kaban'zishu ya har ba jirginsu gaba. Cikin tsalle ɗaya tak duk sun wuce garuruwan kan hanya sun iso filin yaƙin.
Suna da ragowar awa biyar kafin a juya.
"Ku tsaya anan ku jira." Inji Armad. Shi kaɗai yake da fasahar da zai iya shiga filin yaƙin ya sato mutun ɗaya ya dawo duk ba tare da wani ya ankara ba. Idan ta ɓaci ma zai iya yaƙar duk wanda ya shiga gabansa. Hasalima babu wanda Armad yake tsoro acikin filin yaƙin.
Ba a son ran Nusi da Nostaljiya ba amma haka suka haƙura.
Armad ya cilla ya dira a filin yaƙin. Abu na farko daya fara arba dashi shi ne hayaƙi da warin jini mai tsananin ƙarni. Armad ya tuna da yaƙin sarakunan jinzidal. Yaƙin da yayi sanadiyyar mutuwar Hidaya.
Armad yayi ƙoƙarin kasancewa a gefen filin yaƙin to amma hakan bata samu ba saboda kasancewar yadda filin yaƙin yake a hargitse a cakuɗe. Ko'ina ka duba Dordor ne ko kuma aljanu ana gwabza yaƙi. Hatta su kansu manyan kwamandojin yaƙin suna tsaka da tasu fafatawar, sabida haka babu wanda ya lura da shigowar wani bil'adama guda ɗaya idan banda wani aljani da Armad ya dira akansa.
Armad yai wuf ya cafi aljanin ya ɓace ya dawo cikin jirginsu. Shi wannan aljani Rauhani ne mai jela huɗu da ƙaho uku a tsakiyar goshi. Rabinsa hayaƙi ne amma kuma samansa, tun daga ƙugu har ka, tsokace da jini. Akwai rauni a sassa daban-daban na jikinsa, biyu daga cikin ƙahunhunan sa a ɓalle suke.
Armad ya bashi lokaci ya ɗan sakko daga firgitar da yayi kafin ya cilla masa tambaya. "Menene K'Narbig?"
Aljanin ya ɓata rai. "K'Narbig ɗin uwarka. Akan wannan zaku fizgo ni daga filin yaƙi? Kai bil'adama ka shiga taitayin ka."
Bai ma gama magana ba ya fara kawo musu sara da fatanyar dake hannunsa.
"Zaren Mayu!"
Armad ya zuƙe izzar dake jikin fatanyar inda ta tarwatse nan take. Amma maimakon aljanin ya shiga taitayinsa sai ya ƙara azama wajen kawo wafta da kaifafan faratansa.
"Zaren Manyan Mayu."
Armad ya zuƙe dukkan izzar dake jikin wannan aljani sai ƴar kaɗan daya bar masa, dan kada ya mutu. A wannan lokaci aljanin ya shiga taitayinsa. Cikin ƙinƙina ya fara jawabi. "...K'Narbig.. Ban taba jin wannan suna ba."
Armad ya yatsine fuska. Shi yasan haka kawai Hidaya baza ta ambaci sunan ba sai idan yana da matukar muhimmanci.
Abu guda shi ne akwai yiwuwar aljanin ƙarya yake, ko kuma aljanin bai sani ba sabida ƙanƙantar muƙamin sa. Sabida haka nan take Armad ya ƙara wata tambayar.
"Su waye shugabannin tawagar aljanu a wannan yaƙi?"
Aljanin yai shiru yana jimamin amsawa, amma yana tuna abinda ya faru da izzarsa ya fara magana. "Sarakunan aljanu biyar: sarkin iska Ji'Ruha; sarkin ruwa Kil'ma'i; sarkin ƙasa Ƙas'turubu; sarkin walƙiya Sil'rudu; da kuma sarkin wuta Wut'naru."
Nan take Armad ya yanke shawara. Koma mai ake ciki wannan aljanu biyar sun san K'Narbig. Idan ya samu ya farauto ɗaya daga cikinsu to lallai zai samu bayani.
Armad ya juya zai koma kawai sai yaji jiri ya ɗebe shi. Kafin yayi wani abu ya faɗi ƙasa yana numfarfashi. Da farko yayi tunanin ko miyurar sa ce to amma sai ya fuskanci abin ya shafi dukkan mutanen da ke cikin jirgin. Yana hango Nostaljiya ta fadi a ɗan nesa dashi. Wasu ma tuni sun suma.
Yana cikin haka hankalinsa ya gushe. Daga nan bai ƙara sanin abinda ya faru ba.
**
"Armad! Armad!!" Shal ta ɗaga hannunsa tana ƙoƙarin tashin sa daga bacci.
Armad ya buɗe ido a hankali.
Ya ɗaga kai ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
A wannan lokaci daƙiƙa ukun ta cika ya dawo hayyacinsa. Ya tuno duk abinda ya faru da kuma yadda duk na cikin jirgin suka suma lokaci guda.
Take ya miƙe ya kira Kaban'zishu. Yana isa titin Bayajidda ya zauna yana saƙe-saken abinda ya faru kafin abokan tafiyar su zo.
Ranaku shida sun tafi. Saura ranaku hamsin da huɗu. Babbar ayar tambaya anan ita ce menene ya faru jiya? Mai yasa ranar ta yanke kafin lokacin ta ya cika?
A kullum ya kan shafe awa guda kafin jirgin su Nusi ya ƙaraso sabida haka a ɗan wannan lokaci ya yanke shawarar ya samarda wata sabuwar fasahar.
Shekaru kaɗan da suka wuce a yaƙinsa da Uznu Ururu ya samarda mutun-mutumi na walƙiya wanda ya taimaka masa wajen cin nasara akan Uznu. Wancan mutun-mutumi baya iya tunani ko kuma aiwatar da wani babban aiki da kansa. Shi yake sarrafa shi kamar kataku. A halin yanzu ya yanke shawara ya samarda mutun-mutumi wanda zai iya yin tunani na kansa. Mutun-mutumi mai siffar mutane ba walƙiya ba. Wanda zai iya aikawa wajaje da dama su aiwatar da al'amura ba tare da yana nan ba.
Nan take ya ɗebi ƙasa ya kwaɓa ta izuwa siffar mutun. Ya buɗe waƙar-maƙabarta ya kira wasu ɗalasimai wanda suka sa siffar mutun-mutumin ta juye daga kasa ta koma tsoka da jini. Sannan fuskar da jikin suka hade suka koma na Armad sak, babu maraba tsinke.
Sannan a wani salo na kwarewa Armad ya zaro zaren-izzar sa wanda shi ne yake ɗauke da duk wata fasahar sa da rayuwarsa ya saka acikin wannan mutun-mutumi. Ya bishi da manyan ɗalasimai daga waƙar maƙabarta.
Bayan ɗan lokaci idanun wannan mutumi suka buɗe. Ya dubi Armad da irin kallon da zaka yiwa fatalwar ka ya ce, "kai kuma fa? Ya akai kake kama dani?"
***
Babi na 262-264
***
Armad yai murmushi mai cike da alfahari. Abinda yake buƙata shi ne wannan mutun-mutumi nasa yayi magana kamar mutun, kuma yayi. Asalin fasahar ta sarki Aldaima ce, wadda ya rubuta acikin Waƙar Maƙabarta. Tun daga kan ɗalasiman da ake buƙata da yawan ƙasar da ake kwaɓawa. Aldaima ya sakawa wannna fasaha suna USKUSHI. Bayanin mutun-mutumin Uskushi ya haɗa da abubuwa guda uku: tunani, murya da kuma fasaha.
Acikin Uskushi akwai tunani amma bada yawa ba. Yawanci kawai tunani ɗaya kacal ake sa musu. Misali, a kan sakawa mutun-mutumi tunanin ya kashe wani. To wannan mutun-mutumi aikinsa da tunaninsa zasu zama na kashe wannan mutumi ne kawai. Kuma a yawaicin lokuta yana aiwatar da kisan zai narke ya koma turɓaya. Abu na biyu murya, yawaici ana saka musu muryar 'robot' ne, daga baya da ilmi ya ƙara yawaita sai aka koma saka musu muryar wanda suka ɗauki kamarsa. Amma duk da haka acikin maganar su zaka ga babu lanƙwasa da karin harshe irin na bil'adama. Abu na ƙarshe Fasaha, yawaici fasaha ɗaya ƙo biyu kacal akan iya sakawa wannan mutun-mutumi. Daga ƙarshe Aldaima ya taɓa haɗa mutun-mutumi wanda ya saka masa fasaha ɗai-ɗai har biyar. Hakan ya jawo hankalin al'umma da dama masana izza.
Aldaima yayi bayani sosai acikin Waƙar Maƙabarta kan yadda ya haɗa wannan mutun-mutumi. Armad yayi amfani da wannan hanya wajen haɗa nasa mutun-mutumi, to amma sai ya ƙara zaren-izzar sa aciki. Sabida haka mutun-mutumin Armad wanda ya haɗa yanzu yana da tunani da cikakkiyar murya da fasahai irin na Armad sak. Zaka iya cewa kawai wani Armad ɗin aka samu.
Duk da haka akwai matsala guda: sabida amfani da zaren izza ɗaya, mutun-mutumin zai ringa zuƙe ƙarfin izzar Armad yana amfani dashi.
Nan take Armad yai wasu lissafe-lissafe ya gane cewa mutun-mutumin zai ringa ɗibar kaso goma na izzarsa. Hakan ke nuna cewa idan ya ƙara samarda da wani mutun-mutumin adadin zai ninka zuwa ashirin.
Banda wannan, muryarsa irin ta Armad ce sak, fasahar sa irinta Armad ce, tunaninsa cikakke ne irin na Armad. Hasalima yana ganin Armad ne ya kwafe shi.
"Ina tambayarka, waye kai?" Inji mutun-mutumin.
Armad ya ja numfashi a hankali. Haƙarsa ya cimma ruwa amma abu na gaba shi ne ya nunawa mutun-mutumin waye riƙe da linzamin.
Ya miƙa hannu ya ja zaren izzar dake riƙe da mutun-mutumin. Nan take mutun-mutumin ya zube a ƙas, ilmin waye shugabansa ya shiga jikinsa.
"Shugaba, Armad, mai kake buƙata?"
Armad ya ƙara yin murmushi.
Amma maimakon ace ta baki-da-baki zasu rinƙa ganawa sai Armad ya daki ƙasa ya fara zana ɗalasimi. Bayan ya gama sai ya goge, sannan ya zana irinsa sak akan zaren izzarsa. Nan take wata sabuwar fasahar ta shiga jikinsa.
"Komm!"
Sunan wannan fasaha kenan. Ta hanyarta Armad zai iya magana da mutun-mutuminsa batare da furuci ba, komai nisa.
Yanzu abinda ya rage guda ɗaya ne: ya sakawa fasahar mutun-mutuminsa suna. Da farko yayi tunanin saka mata suna Uskushi kamar yadda Aldaima ya sa mata, to amma daga baya ya canja shawara.
"Zaren Halitta!"
Yana saka mata sunan yaji abin ya dace da yadda yake so.
"Na saka maka suna Áyúbu, ina so kayi tafiya zuwa sashin ikwatora kaga mai ke faruwa. Daga nan ka leka doron ƙasa na huɗu, daular Sisiyu, kaga mai ke faruwa."
Mutun-mutumin yai murmushi ya ce, "Ayubu? Lallai wannan suna ya kyautata. Zan zama mai cika umarni. Ko ba komai idan ka mutu nima mutuwa zanyi."
Ayubu ya kyakyace da dariya ya kira Kaban'zishu ya ɓace.
Arnad yai ajiyar zuciya. Tabbas indai mutun-mutuminsa halinsa ya yiwo to bazai yadda ya zama bawa ba. Hakan zai iya jawo matsala, musamman idan aka wayi gari Ayubu ya shiga gari yana sharholiyar sa.
"Hmmm.. Idan baya abinda aka saka shi zan iya katse shi a kowanne lokaci." Armad ya gayawa kansa.
A dai-dai wannan lokaci Armad ya fara jin yanayin izzar mutanensa sun ƙaraso.
Bayan komai ya daidaita suka ɗau hanya. Kamar kullum Ranbir da Dandir suna ganinsu suka basu hanya sabida tsoron Ayubul-laysi. Su kuwa aljanun tsaron ƙofar shigar sai da Armad yai musu ladabi.
Ba jimawa suka ɗauki hanyar zuwa filin yaƙin.
"Ina ganin abinda ya faru jiya yana da alaƙa da aljanin da muka ɗakko, ko kuma da sarakunan aljanun. Mai zai hana a wannan lokaci mu gwada ɗakko Dordor?" Inji Babara.
Armad ya girgiza kai. "Zata iya yiwuwa, to amma bana tunanin haka. Bawai na raina ƙarfin aljanu ba, amma har ace sun halaka mu babu wanda ya gani acikin mu. Abin da mamaki."
Nazara ya gyaɗa kai. "Gaskiya ina tunanin ba aljanu bane. Nafi tunanin wani abu ne da yake da alaƙa da Kurkukun lokaci."
Nan fa aka shiga tattaunawa akan dalilai. Kowa yana tofa albarkacin bakinsa. A ƙarshe babu wata matsaya da aka cimma sai hasashe kala-kala.
Bayan sun ƙarasa gab da filin yaƙin sai suka tsaya. Armad ya fara hangen yadda zaiyi ya sato ɗaya daga cikin sarakunan aljanun nan.
Yana yanke shawara ya kira Kaban'shisu. Amma maimakon ya ɓace kawai sai yaji jiri ya ɗebe shi. Kafin yayi wani abu ya faɗi ƙasa yana numfarfashi. Abu na farko daya faɗo masa a rai shi ne abinda ya faru jiya, musamman ganin, kamar jiya, abin ya shafi dukkan mutanen da ke cikin jirgin. Nostaljiya da Nusi sun zube a ɗan nesa dashi. Cokali da Iliyasisi tuni sun sume. Sauran mutanen na cikin hali na ƙaƙanikayi.
Ana haka shima hankalinsa ya gushe. Daga nan bai ƙara sanin abinda ya faru ba.
**
"Armad! Armad!!" Shal ta ɗaga hannunsa tana ƙoƙarin tashin sa daga baccin da yake yi.
Armad ya buɗe ido a hankali.
Ya ɗaga kai ya kalli mai maganar inda yai arba da wata tsaleliyar budurwa cikin kayan yaƙin Rundunar Ururu.
Armad ya dubi budurwar ya ce, "Shal! Mai ya faru kike..."
A wannan lokaci daƙiƙa ukun ta cika ya dawo hayyacinsa. Ya tuno duk abinda ya faru da kuma yadda ya ƙara faɗuwa acikin jirgin.
Take ya miƙe ya kira Kaban'zishu. Yana isa titin Bayajidda ya zauna yana saƙe-saken abinda ke faruwa.
Ranaku bakwai sun tafi. Saura ranaku hamsin da uku. Babbar alamar tambaya anan ita ce menene yake faruwa? Mai yasa ranar take yankewa kafin lokacin ta ya cika?
**
Jim kaɗan su Nusi suka ƙaraso.
"Wai menene yake faruwa ne?"
"Tunda suma yankakkun ranakun ana lissafi dasu, to kuwa akwai yiwuwar mu ci rabin kwanakin mu ana abu ɗaya. Ya kamata musan nayi." Inji Nusi.
Nan fa aka fara kace-kace.
Nazara ya numfasa ya ce, "naji labari a gidan jarida cewa Ikenga yana kai hari doron ƙasa na farko. Ko meye dalili ban sani ba. Wataƙila hakan nada alaƙa da abinda ke faruwa."
Nan take Armad ya miƙe. "Yana kai hari doron ƙasa na farko?"
Nazara ya gyaɗa kai.
"An faɗi dalilin da yasa yake kai harin?"
"Ba'a bayyana ba, amma majiya mai ƙarfi daga shugaban jaridar aminiya ta bayyana cewa Ikenga yana kaiwa sarki Kuyurussa'ayi Ururu hari, gaba da gaba."
Armad ya yamutse fuska. Ayubu bai kawo masa rahoto ba, sannan kuma akwai yiwuwar ranakun suna ƙarewa ne kafin lokacinsu sabida Ikenga yana mutuwa.
Koma dai meye gaskiyar wannan al'amari sai dai a jira rahoton Ayubu.
Kai tsaye suka wuce gaba suna jimamin halin da ake ciki. Idan har Ikenga ya kai ya tari Kuyurussa'ayi gaba da gaba to fa lallai akwai damuwa babba. Sannan kuma ga ranaku suna yankewa kamar kayan tsohuwa.
Abin mamaki a wannan rana ko ƙofa basu ƙarasa ba aka juya.
Washe gari haka.
Wata washe garin ma haka.
Zuciyar Armad tayi baƙi sosai. Dan me zai zamo idan Ikenga ya mutu dole a juya koda kowa bai gama abinda yake ba. Akwai yiwuwar duk ranaku sittin ɗin su ƙare ana haka. Lamarinda yasa Armad ya fara haɗa gumin baƙin ciki. Kai bama shi kaɗai ba, dukkan jirgin babu wata annushuwa. Kowa ka gani fuskarsa a murtuke take, babu mai cewa kowa komai.
Bayan an shafe kwanaki goma a haka sai ranakun suka ɗan fara yin tsayi. Kamar yau sun wuce ƙofa har sun gama da masu gadin. Izzar Armad tana kaiwa ɗari Miyurar sa ta ƙara zuƙewa. Mutun-mutumin dake ciki ya ƙara azama wajen zagayawa.
Akwai matuƙar yiwuwar akwai wani sirri ɓoyayye acikin Miyurar to amma Armad bashi da lokacin jira ya gani. Musammman duba ga cewa sai ya tara shekaru dubu ɗari sannan miyurar take zuƙewa. Kuma yana ɗaukar kwanaki biyu kafin ya tara shekarun.
Sabida haka Armad ya jera mutanensa masu buƙatar izza a layi.
Nostaljiya ce a farko, sai Inara, sai Cokali, sai kuma lanarudu. Nusi da Iliyasisi suna ɓangaren Nazara wanda zaiyi amfani da rumbun izzar da baba Dalja ya bar masa wajen ɗaga su zuwa Deba. Babara na tsaye da sandar tsafinsa.
"Zaren Layya!"
Armad kawai kiran ɗalasimi yayi. Nan take zarurruka guda huɗu suka tashi daga jikinsa suka shiga jikin mutun huɗun dake gabansa.
Shi kuwa Nazara allon izza ya ɗakko ya saka a tsakiyarsu, kowa ya sa hannunsa akai. Izza ta fara shiga jikinsu.
Babara na da hanyarsa ta musamman. Babu wanda yasan mai yake ciki amma izzar na ƙaruwa.
Cikin ƙanƙanin lokaci Armad da Nazara sun raba musu izza dubu goma-goma.
Kan kace meye wannan tuni su Nusi da Nostaljiya dasu Inara sun fara kwara amai, jiri yana ɗibansu. Nan take suka zube a kan jirgin suna layi.
Armad da Nazara da Babara su kaɗai suka rage a tsaye. Wannan shi ake cewa Ƙwannafin Izza. Duk wanda ya zuƙi izzar da tafi ƙarfinsa sama da yadda jikinsa zai iya ɗauka, dole yai fama da wannan cuta. Akan shafe kwanaki zuwa sati guda ana abu ɗaya. Amma baya kisa, sai dai a sha wahala, ruwan jiki ya ƙare.
Suna cikin haka ranar ta ƙare aka ƙara juyawa. Kwanaki goma sha ɗaya babu wanda ya shiga Deba acikin wannan jirgi mara suna.
Wani abin mamaki shi ne ana juyawa duk aman da suke ji da tashin zuciyar ya ɓace, amma kuma izzar su tana nan.
"Kun shirya?" Armad ya tambaye su cikin murmushi da tsokana. A nasa lissafin ya kamata su huta. Amma yana yin tambayar, Nostaljiya ta shige gaba ta miƙa masa hannu.
"Mai zamu jira. Deba kawai."
Armad ya gyaɗa kai. Daga cikin abubuwan da baya so akwai tashin zuciya da amai, yana ganin da shi ne ya shiga abinda suka shiga jiya zai iya ɗan saurarawa ya huta. Wataƙila.
Nan fa suka ƙara shiga aiki. Armad da Nazara suka ci gaba da loda musu izza. Ita ma wannan rana bata kai azahar ba ta ƙare. Kwana sha uku kenan. Saura kwana arba'in da bakwai.
Ɓangaren Ayubu
Áyúbu shi ne mutun-mutumi na farko da Armad ya ƙera. Kuma shi ne samfurin Armad na farko. Yana da tunani nasa na kansa. Fasaha irin ta Armad da kuma murya irinta Armad.
Yana fita ya kira Kaban'zishu ya shige sashin ikwatora. Bai zame ko'ina ba sai sashi na shida inda fadar sarki Ƙaraiƙisu take. Yana bayyana ya cilla kusa da fadar. Abinda ya kawo shi shi ne ya duba halin da sashin yake ciki. Ya kuma ga irin shirin da Ikenga yake yi. Zaka iya cewa kamar leken asiri yazo. Kuma yana gamawa da nan zai wuce garin Sisiyu yaga halin da Bihanzin yake ciki.
Akwai tafkeken lambu ɗauke da bishiyun kanya dana zogale sun zagaye fadar. Ayubu ya lissafa yawan bishiyun sun kai subu ɗari.
Akwai halittu kala-kala a wannan sashi, kai harda samudawa da Dordor da mutane. Kowa na sha'anin gabansa. Musamman duba ga cewa akwai ginin katafariyar kwalejin izza a kusa da fadar.
Ayubu kamar sauran mutane yake. Babu wani banbanci, sabida haka babu wanda ya kula dashi. Yana dira yabi ta gefen kwalejin ya dudduba hanyar da zata fi masa sauƙin shiga cikin fadar. Bayan kimanin awa guda ya samo hanya.
Yana gab da wajenda zai kira Kaban'zishu ya cilla cikin fadar sai yaji murya a kunnensa.
"Akwai ɗalasimin Dafi a katangar, kana haurawa za'a kama ka."
Ayubu yai shiru na ƴan daƙiƙu kafin ya juyo ɓangaren mai maganar. Kujera ce doguwa ta farin dutse. Wata budurwa kyakkyawa na zaune akai tana shan lemo wanda aka daskarar da ƙanƙarar sanyin babban sihiri.
Abu ne sananne indai baka ganin izzar mutun to ya ninka izzar ka sau aƙalla biyu. Ganin cewa Ayubu baya ganin izzar wannan mace yasa ya miƙa hannunsa kan takobinsa.
"Um um.. baka buƙatar takobi anan. Ga waje." Inji budurwar. Ta nuna masa gefen kujerar da take zaune.
Abin al'ajabi kawai sai yaji ƙafafuwansa suna tafiya da kansu suna kusantar wannan budurwa.
Nan take ya gane mai ke faruwa. Fasahar Kamalar-ruhi!
Yana matsawa yana ƙara ganin surar wannan mace. Ba jimawa ya gane cewa kyawunta ya so ya kere na Nostaljiya. Kunnuwanta sune mafiya tsayi daya taɓa gani. Idanuwanta sune mafiya kyawu da haske. Hanci mafi zubi da ƙira abar labartawa.
"Suna na Sarkin-sarki. Na kwana biyu ina jiran ka anan."
Ayubu ya ciji harshensa yayi amfani da zafin ya fitar da kansa daga ɗaurin Kamalar-ruhin. Wannan ita ce matar da taso ta kashe Armad a lokacin gasar Ruhin Deba. Komai mai take so a yanzu?
"Bani da abinda zance miki." Inji Ayubu. Ya juya a fusace zai wuce.
Sarkin-sarki tayi gyaran murya ta ce, "kana da buƙatar kaji mai zance. Minti ɗaya yayi yawa."
"Idan ƙaninki Elbinuil Randuil kike nema to nima ban san inda yake ba."
"Ƙani na ba shi ne dalilin zuwa na ba."
"Ko?"
Sarkin-sarki ta tafa hannayenta, take ƙanƙara abar ƙawa da ɗaukaka ta kewaye su, tayadda babu wanda yake iya ganinsu ta waje.
"Ikenga shi ke da iko akan Kurkukun-lokaci, kuma tuni Ikenga ya gama shirinsa. A halin yanzu ya tafi yaƙi da Kuyurussa'ayi domin ya ƙara ƙarfafa fasahar sa. A duk sanda Kuyurussa'ayi ya kashe shi ranar zata ƙare sabida ikon da yake da shi akan Kurkukun. Idan kai ko Bihanzin kuka mutu rana zata ci gaba da tafiya. Amma idan Ikenga ya mutu komai ya tsaya. Akwai yiwuwar Ikenga yaci gaba da wannan faɗa da Kuyurussa'ayi har zuwa ƙarshen kwanaki sittin ɗin nan. Kaga damu da kai muna ruwa. Domin nasan har yanzu baka shiga Deba ba. Nima bazan ɓoye maka ba, akwai shirye-shiryen mu da bamu ƙarasa ba."
Ayubu yai shiru yana jin ta. Akwai abubuwa da dama da suke zagayawa acikin kansa. Meye dalilin da yasa shi Bihanzin ɗin da kansa bai zo ba? Meye dalilin da yasa basu sami Armad ba suka same shi? Sannan kuma mai sarkin-sarki take so ayi? Shin tana son su haɗa kai ne? Wannan bazai yiwu ba. Koba dan komai ba akwai yaudara a halayen Bihanzin.
"Mai kike so?" Inji Ayubu.
Sarkin-sarki tayi murmushi sannan ta gyara zama ta nuna masa gefenta. "Zo ka zauna."
A wannan lokaci bata yi amfani da Kamalar-ruhi ba. A ganin damarsa Ayubu ya gabato ya zauna. Ko babu komai shi mutun-mutumi ne, kashe shi bazai cutar da Armad sosai ba. Sannan kuma babu laifi a saurarar ta.
Yana zama ta nuna masa wani ɗan farin hankaka mai fararen idanu akan katangar fadar dake kusa dasu, ta ce, "kaga wancan hankakan? Kada ka damu, fari ne ba baƙi ba irin na Bihanzin. Kalli idanunsa ma farare ne."
Ayubu yai tsaki. "Ki faɗi abinda kike so ki faɗa kurum."
"Akan kira ni da Abigail Randuil, mahaifi na Randuil abokin Ayubul-laisiy Alwibasiy ne. Tunda ka gamu da Ranbir da Dandir, ƙannen Bihanzin, dole sun gaya maka labarin Ayubul-laisiy. Mai zai hana, da kai da mu, mu haɗa kai?"
***
Babi na 265-266
***
Ayubu ya kalli sarkin-sarki a nutse ya ce, "Mu haɗa kai?"
Sarkin-sarki ta gyaɗa kai cikin murmushi ta ce, "eh, mu haɗa kai."
Ayubu ya ƙarayin wani tsakin ya ce, "mu haɗu a filin yaƙi."
Har ya juya zai tafi ya ji muryarta. "Baka fahimta ba, shi wannan haɗa kan kai zai taimakawa. Mu shirin mu zamu iya haɗa shi acikin kwana biyu masu zuwa. Kai kuma fa?"
Ayubu ya haɗe gira. Bai gane mai take nufi ba.
"Nasan baka sani ba, amma bawai Ikenga kaɗai ba, kowanne acikin ku akwai ɗalasimi acikin ruhin sa wanda idan ya danna gaba ki ɗaya kwana sittin ɗin zasu ƙare su dawo kwana biyu. Wannan kwana biyu baza su yanke ba koda Ikenga ya mutu. Idan Ikenga yaci gaba da abinda yake yi a kowacce rana bai fi ka samo awa guda ba, idan ka haɗa baki ɗaya baifi awa talatin ne ya rage maka ba. Idan ka yadda muna so muyi amfani da ɗalasimin dake jikin Bihanzin da wanda ke jikinka mu samarda kwana huɗu. A wannan kwanaki huɗu koda Ikenga ya mutu baza a juya ba."
Ayubu ya buɗe baki zaiyi magana amma ta riga shi.
"Kaje kayi tunani nan da kwana ɗaya. Idan ka yadda ka dawo nan wajen gobe a dai-dai wannan lokaci. Idan kuma baka yadda ba zamu yi amfani da namu ɗalasimin mu yanke kwanakin su dawo kwana biyu kacal. Zaɓin ka, kwana huɗu ko biyu?"
Tana gama magana ta ɓace.
Ɓangaren Armad
Armad na zaune cikin jirgi yana tunani kawai yaji saƙon Ayubu ya shigo.
Duk bayanin Sarkin-sarki yazo masa.
"Ya kuka gani?" Armad ya tambayi na jirgin bayan ya labarta musu abinda ke faruwa.
"Ai kwata-kwata Bihanzin ba abin yadda bane. Hasalima gamuwa dashi ba ƙaramin hatsari bane. Akwai matuƙar yiwuwar duk lissafi ne kawai." Inji Nostaljiya wadda a da Bihanzin babanta ne. Kuma zaka iya cewa tafi kowa saninsa.
Nazara ya gyaɗa kai alamun amincewa. "Nima ban yadda ba. Duk tsafin daya haɗa da ruhi kada ka yadda dashi. Akwai yiwuwar ya saka maka wani abun wanda zaiyi tasiri akan ka a lokacin babban yaƙi."
"Nima ban amince ba. Duba ga tarihi Bihanzin babu wanda bai yaudara ba." Inji Babara yana kallon Nostaljiya.
Cikin ƙanƙanin lokaci kowa acikin jirgin ya amince a rabu da Bihanzin. Babu wani ɗa mai ido da za'a samu idan aka haɗa kai dashi.
Kamar an gayawa Bihanzin, suna yanke wannan shawara Armad yaji a jikinsa cewa Bihanzin ya canja kurkukun. A takaice ya maida ita kwana biyu kacal.
Daga gobe ne!
Armad yai shiru tsahon lokaci yana tunani. Kafin daga bisani ya miƙe tsaye a fusace, idanuwansa sunyi jajawur kamar gauta. Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya wuce gaban jirgin ya tsaya. A zahiri indai abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka to babu shakka mutuwarsa kawai yake jira. Haka zai mutu a manta dashi, haka zai mutu a banza, haka zai mutu bai ɗau fansar Hidaya ba, haka zai mutu bai kauda cinikin bayi ba, haka zai mutu bai gama da Ururu ba. Abubuwan da yake so yayi suna da yawa, bashi da lokacin wasa ko bacci ko aure. Yaƙi yana gabda cimmasa bai shirya ba. Yaƙi ba makaranta bace da zaka ce baka shirya ba. Indai an futo jini sai ya zuba. Waje ne da za'a sare kayukan mutane da aljanu da Dordor da Ururu.
Nan take idanuwan Armad suka juye izuwa wuta. Jan gashin kansa ya kama da wutar Negrinki. Jirgin da suke ciki ya fara girgiza yana neman tsagewa.
Wai ya manta da abinda ya faru a yaƙin sarakunan jinzidal ne?! Ya manta da cewa a hannu a ka ɗauke shi aka fita dashi?! A hannu aka cece shi kamar jariri?! Ta dalilin cetar sa Hidaya ta rasa ranta?! Wai ya manta ne?! Ya manta da mashin daya sauka daga Maɗaukakiyar fada ya cake Hidaya?! Wai ya manta da murmushin da Bihanzin yake a lokacin da yai nasarar samar da fasahar Jini-uku?!
"Aaaarghhhh!" Armad yai ƙaraji lamarinda yasa bakin hadari ya taso. Nusi tai tsalle ta dira a gabansa da niyyar ta rungume shi ta kwantar masa da hankali amma kafin ta ƙarasa jikin Armad ya kama da wutar sabida tsabagen tafasa da jininsa yake yi.
"Kaban'zishu!"
Ya ɓace. Bai bayyana a ko'ina sai a filin da akai yaƙin sarakunan Jinzidal.
Ƙasar wajen ta koma jajawur, ciyayin da suke fitowa a wannan wajen sun koma jajaye. Ururu sun ɗauke gawar Hidaya daga wajen amma Armad yana tuna wajen data mutu kamar rana.
Ya guntsi ƙasar wajen da jinin Hidaya ya zuba ya watsa ta a idonsa. Yai ihu yai ƙaraji. Ya ƙara ɗiban ƙasar ya zuba a idonsa na hagu. Har zuwa ranar da zai ɗau fansar rayuwa Hidaya bazai wanke ƙasar ba.
"MAHAIFIYA TA... ƳAR'UWA TA... IYAYE NA... KAKANNI NA... ƘABILA TA..."
Armad ya daki ƙasa da ƙafafunsa inda ƙasa ta tsage gida biyu. Ya kalli doron ƙasa na farko cikin tsana da takaici.
"NI ARMAD WILBAFOS ƊAN TAIDARA ƊAN ZAIKID, INA MAI RANTSUWA DA MAHALICCIN SARKI EYRIYON SAI NA KASHE DUK WANDA YAKE DA SA HANNU A MUTUWAR HIDAYA, SAI NAGA BAYAN CINIKIN BAYI A BAN ƘASA."
Idan ka kalli Armad abu na farko da zai zo ranka shi ne ƊAN-AIKEN MUTUWA.
"Zaren Mutuwa!"
A take Armad ya samarda fasaha irin wadda ba'a taɓa gani ba. Zare ne guda ɗaya mai aman Negrinki da zuƙe izza: ya zuƙe maka izza, ya zuƙe maka jini da jiki da ruhi.
"Kaban'zishu!"
Ya dawo cikin jirgin inda ya tarar da su suna jiransa. Kowa ya gyara kwalarsa domin kuwa a yanzu ne za'a fara tafiyar. Idan baza ka iya ba ka bada waje.
"A awa ɗaya zan zama Deba, a awa ɗaya zaku zama Deba." Abinda kawai Armad ya ce kenan, kai kace shi ke da akalar ƙasa bakwa a hannunsa. Babu wanda yace uffa domin suna ganin idanunsa cike da ƙasa, gashin kansa yana ci da wutar Negrinki suma sun san lokacin wasa ya wuce.
Kai a wannan rana takan Ranbir da Dandir aka fara. Duk wani mai alaƙa da Bihanzin kwanansa ya ƙare. A wajen Armad tuni an fara YAƘIN SARAKUNA UKU.
"Ku faɗi abinda ya kawo ku nan." Inji Ranbir.
Dandir yana gefe yana nazarin abinda yake faruwa. Can daga bisani ya dubi Armad ya ce, "Jinin Ayubul-laysiy ne..."
Kafin ya ƙarasa Zaren Mutuwa ya dira akansa da Ranbir. Take izzarsu ta ɓace ɓat. Jikinsu ya shige cikin duniyar Armad. Wato banbancin Zaren Manyan Mayu da Zare Mutuwa shi ne, shi Zaren Mutuwa a lokaci guda yake zuƙe komai sannan kuma ya haɗa da jikin ka. Babu tausayi ko sassautawa a tattare da aikinsa.
A lokaci guda izzar Armad ta tashi sama ta wuce dubu ɗari takwas.
Amma a lokacin Miyurar Armad ta zuƙe izzar. Ya dawo farko. Ko kaɗan hakan bai dame shi ba.
Suka wuce wajen masu tsaron ƙofar wanda kamar kullum a yau ma hana su shiga sukai. Dama haka Armad yake so. Tuni ya sakar musu zaren mutuwa aka wuce wajen.
Garin farko da Armad ya fara tararwa bai ɗaga masa ƙafa ba. Yasan basu da haƙƙi to amma ana juyawa zasu dawo da izzarsu saboda haka nan take Armad ya zuƙe dukkan izzar mutanen garin cikin ƴan daƙiƙu.
IZZA MILIYAN ƊAYA TA SHIGA TSARIN RUHINSA.
Abin mamaki nan take miyurar Armad ta zuƙe su. A wannan lokaci sabida ɓacin rai da fusata Armad baya ko kula da abinda ke faruwa acikin Miyurar tasa.
Suna ƙarasawa filin yaƙin, maimakon yadda ada Armad yaƙe laɓewa ya sato mutun ɗaya, a wannan lokaci Armad kai tsaye ya dira a tsakiyar filin. Nusi ta firgita matuƙa, jikinta na ɓari ta rankaya zata dawo da Armad, sabida duk ta inda ta kalla ƙarfinsa bai kai ya tsaya a filin yaƙin nan ba.
Nostaljiya tai wuf ta riƙe ta. "Ki rabu da miji na, idan kika shiga mutuwa zaki yi."
Nusi ta fizge. "Idan kina jin tsoro ki zauna a nan. Ina nan akan alƙawari na: ko wuta ya shiga ni zan bishi."
Nusi ta tashi sama ta nufi tsakiyar filin yaƙin. Iliyasisi da Cokali suka bi bayanta.
Bayyanar Armad a tsakanin manyan sarakunan aljanun biyar da manyan sarakunan Dordor bakwai dake filin yasa kowa ya tsaya cak ana kallonsa. Wannan wanne mara hankalin bil'adaman ne.
A lokaci guda, ba tare da tambaya ba, dukkan ɓangarorin guda biyu suka afka kan Armad da mahaukatan makamai irin wanda kalma baza ta iya faɗar su ba sannan ido bai taɓa gani ba.
"Zaren Mutuwa!"
Nan take aljanu da Dordor dubu suka ɓace, izzarsu ta shige cikin ruhin Armad.
Tuni izzar Armad ta haura miliyan, amma a kowanne lokaci sai Miyurar sa ta ɗebe.
Sarakunan aljanun suka ja da baya cikin mamaki. Badan komai ba sai dan sunga fasahar Hidaya. A lokaci guda suka kira aljanun dake ɓangaren su da su jada baya. Amma ina tuni sun makara. A wannan rana an cire imani ko tausayi a zuciyar Armad.
Kalmar kawai da yake ji acikin kwakwalwarsa ita ce 'KISA'. A yau sai ya kashe komai da kowa: mutun da aljan da Dordor da Urúrú.
Tuni Armad ya fuskanci cewa Zaren Mutuwa yayi kaɗan. Take ya yanke shawara lokaci ne da zai kashe kowa da komai, tsirrai da aljanu, har sai ya rage babu wani ruhi daya rage da zai yi dariya akan mutuwar Hidaya.
Hakane... Dama can dariya suke masa... Dariya suke yiwa Hidaya saboda ta mutu... Dariya suke yiwa gazawar sa...
Wannan muryoyi dake yawo acikin kansa sune suke ƙara tunzara shi.
Nan take Armad ya yanke shawara. Kashe komai zaiyi: da wanda sukai dariyar da wanda suka ji dariyar.
"ZAREN BABBAR MUTUWA!"
"ZAREN ƘARE DANGI!"
Fasaha biyu a lokaci guda.
Nan take Armad ya fara tsufa. Gashin kansa ya fara canjawa daga ja zuwa fari. Kana ganinsa kasan ya rasa wajen shekaru ashirin na ainihin rayuwarsa. Ko'a jikinsa. A yau sai ya kashe komai da kowa, da duk wanda yayi wa Hidaya dariya, da wanda suka ji daɗin dariyar, da wanda aka yi dariyar basu ce a bari ba.
Cikin daƙiƙa guda filin yaƙin yai shiru. Idan ka kalla zaka iya cewa mafarki kake domin kuwa a halin yanzu babu kowa a filin sai ƙura. Daga Armad sai Nusi da jirginsu.
Yana ƙara samun izzar yana ƙara haukacewa. Abinda kawai yake so shi ne ya kashe wanda sukai wa mutuwar Hidaya dariya, da wanda suka ji daɗin abinda ya faru, da wanda suka ji anyi dariyar basu hana ba. Kai a wannan lokaci a wajen Armad babu wani mara laifi.
Hasalima abu na gaba da yayi ya bawa kowa mamaki.
"Kaban'zishu!"
Ya ɓace ya dawo duniyar mutane. Bai zame ko'ina ba sai daular Sisiyu garin Bihanzin.
"Zaren Babbar Mutuwa!"
"Zaren Kare Dangi!"
Da mai laifi da mara laifi da wanda ya sani da wanda bai sani ba. Azaba ta sauka.
Da asubahin fari mutanen wannan gari suka tashi suka tarar da annoba a sararin samaniya. Mutun ne amma jikinsa yana ci da wuta kamar garwashi.
Abinda kawai ya ceci mutanen wannan gari shi ne a lokacin a ka juya.
**
Wani abin mamaki ana juyawa Armad ya farka ya tuna abinda ya faru ko kaɗan baiyi dana sani ba. Hasalima a yanzu yake ƙarajin wai mai yasa tun asali bai bi takan wanda sukai wa Hidaya dariya ba.
Take ya turawa Ayuba sako: [A kashe duk wanda yaji dadin mutuwar Hidaya.]
Abu guda ɗaya daya tsayar dashi shi ne saƙo da yake karɓa daga miyurar sa. A ƙalla izuwa wannan lokaci miyurar ta zuƙi yawan izzar da bai san adadin ta ba.
Akwai wata murya da yake ji daga mutun-mutumin nan mai ɗauke da al'amudi dake tsakiyar miyurar sa. Idan ba'a mantaba acikin miyurar Armad akwai mutun-mutumi, akwai takubba uku wanda tuni yake iya amfani da guda ɗaya bayan ya samun jikin izza. Sannan akwai rubuce-rubuce wanda bai iya karanta su ba. An bayyana cewa wannan mutun-mutumi shi yake ɗauke da duk zaren izzar da Armad yake amfani dasu. To amma shi kansa mutun-mutumin Armad bai san menene ba. A halin yanzu zaka iya cewa Armad kawai takobi ɗaya yake iya amfani da ita acikin miyurar sa.
Wannan muryar daga mutun-mutumin take tashi. Bai gane mai muryar take cewa ba, wataƙila sabida ƙasa-ƙasa take magana, ko kuma sabida yaren bai san shi ba. Yaren yayi kama da tsohon Wilburish amma kuma ba shi bane.
Amma kuma akwai wani abu acikin miyurar tasa wanda yake gaya masa abinda ya kamata yayi. Kamar yana yi masa kwatancen wajen da zaije.
Take Armad ya miƙe ya nufi titin Bayajidda. Yana zuwa ya jira abokan tafiyarsa suka iso. Nusi bata jira komai ba tazo ta rungume shi.
"Maiya faru? Lafiya? Ka tsorata mu jira."
Armad ya girgiza. "Ba lafiya. Yau ne ranar karshe ban shiga Deba ba kuma ban kashe duk wanda sukai wa mutuwar Hidaya dariya ba."
Koda jin haka sai Nusi ta jada baya a firgice. Nostaljiya da dukkan wanda yake cikin jirgin suka fuskanci lallai wani abu yana faruwa da Armad. Komai halin da ake ciki Armad baya zancen kashe mutane. Ko sanda aka kashe Hidaya bai kashe mutane ba. Mai yasa yanzu yake wannan tunani. Babban abin tsoron shi ne ko a jikin Armad. Kuma da gaske yake.
Mutun ɗaya tak da bai damu da wannan canji ba shi ne Rafiyan Nazara. "Irin wannan Armad ɗin muke buƙata indai muna buƙata muyi nasara akan Bihanzin da Ikenga. Armad mai tausayi da sanyi babu inda zaije."
Nostaljiya ta harare shi.
Ita kuwa Nusi kawai tsayawa tayi a gaban Armad ta durƙusa ta ce, "ko kana kan gaskiya, ko kana kan ƙarya, ni dai nayi mubayi'a. Na baka rayuwa ta, kuma bazan taɓa canjawa ba. Ni, Nusi Kil'zanki, taka ce ko a wuta, ko a aljanna."
Armad ya durƙusa ya ɗago ta cikin alfahari da ita, ya ce, "Na sani, Nusi. Akwai wanda sukai wa Hidaya dariya bayan ta mutu, da wanda sukai farin ciki, da wanda akai dariyar basu hana ba. Duk sai na kashe su da iyalansu. Daga nan zamu kashe Bihanzin da iyalansa da danginsa da mutanensa, yara da manya da tsoffi. Sai na kashe kowa tun daga doron ƙasa ta farko har zuwa ta bakwai."
"Ko zaka kashe mahaifa na, imani na bazai canja ba. Kai ko ka kashe ni idan na dawo bazan daina biyayya ba. Tuni na baka ruhi, a nan da can." Inji Nusi.
Nostaljiya tai tsalle ta shiga tsakaninsu. "Armad mijina, kada ka yadda da duk abinda kake ji acikin ranka a yanzu, wannan miyurar ce ta goshin ka. Tun ɗazu nake jin wata Baƙar Izza na fitowa daga cikinta. Ina jin akwai wata halitta aciki da take son ɓalle. Kada ka canja akan yadda kake. Kada ka canja daga Armanos ɗin dana sani."
Nan take gashin kan Armad ya ƙara kamawa da wuta. Ya dube ta a fusace ya ce, "kada na canja? Na zauna a yadda nake a gobe Bihanzin ya ƙara kashe ni ko? Dole kice haka, wataƙila dama can bakya so a kashe shi."
Nostaljiya da duk wanda yake cikin jirgin sai da yai ajiyar zuciya. A wannan lokaci suka tabbatar akwai wani abu acikin kan Armad.
Tunda suka ga abinda yace wa Nostaljiya babu wanda ya ƙara cewa uffan. Haka suka wuce zuwa duniyar aljanu babu wanda yace uffan.
A wannan rana tun daga nesa Armad ya kira Zaren Babbar Mutuwa ya ƙarar da masu tsaron ƙofar. Kai cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarar da duk wani aljani dake duniyar wanda baya cikin filin yaƙin.
Amma a wannan rana kafin ya ƙarasa filin yaƙin wannan sarakunan aljanun biyar suka gabato gabansa.
Suka haɗa baki a tare suka ce, "Barka da zuwa K'Narbig! Mun daɗe muna jiran zuwan ka."
***
Babi na 267-269
***
"K'Narbig?" Armad ya kalli sarakunan aljanun cike da mamaki. Lallai akwai sunan acikin baitin Hidaya to amma babu wani ƙarin haske akansa.
Aljanun suka ƙara zubewa a ƙasa sukai gaisuwa. "Barka da zuwa K'Narbig."
"Mai kuke nufi? Kuyi bayanin kan ku."
Aljanun manya-manya ne, tayadda zaka iya cewa samudawa koda acikin aljanu. Kowanne acikinsu yana ɗauke da shaidar fasaharsa. Na farko a ɓangaren dama yana riƙe da tukunyar wuta a saman kansa. Ya dubi Armad ya ce, "ni suna na sarkin wuta Wut'naru."
Na kusa dashi akwai tubalin ƙasa na yawo a saman kansa ya amsa da cewa, "ni suna na sarkin ƙasa Ƙas'turubu."
Na kusa dashi mai sanye da rigar walƙiya ya amsa da cewa, "ni suna na sarkin walƙiya Sil'rudu."
Na kusa dashi mai ɗauke da hular iska ya amsa da cewa, "ni suna na sarkin iska Ji'Ruha."
Sai kuma na ƙarshe ya amshe da cewa, "ni suna na sarkin ruwa Kil'ma'i. Dukkanin mu rana muke jira da zamu miƙawa K'Narbig saƙon da aka bar mana. Aldaima, Eyriyon, Ayubul-laysi... Dukkaninsu sun amince mana da wannan ajiya, kuma a yau muna farin cikin miƙa ta ga wanda ya cancance ta."
Nan take aljanun biyar suka tafa hannayensu inda nan take hadarin dake ƙasansu ya dare gida biyu suka shige ciki. Duniyar da suka sani ta juye suka bayyana a wata sabuwa.
A wannan duniyar babu komai sai fili da haske. Baka iya banbance gaba da baya, ko'ina launi ɗaya ne. Babu tudu, babu kwari. Babu sama, babu ƙasa. A wannan waje komai iri ɗaya ne.
Armad ya dubi mutanen sa ya tabbatar kowa yana nan kalau kafin ya juyo kan sarakunan aljanun.
Ƙas'turubu ya tari numfashin sa ya ce, "Armad sunan ka K'Narbig, Negrinkin ka da duniyar Negrinkin ka sunan su K'Narbig, Miyurar ka da aljanin da aka ɗaure aciki sunan su K'Narbig, tsarin ruhin ka sunan sa K'Narbig, wannan duniya sunan ta K'Narbig. A yau zamu koya maka tsarin fasahar K'Narbig. A yau zamu baka fasahar Wilbafosiyan-siwod-dans. A yau zamu koya maka amfani da takobin dake cikin littafin-takobi. A yau zaka zama ɗaya da Miyurar ka, da tsarin ruhinka da takobin littafin-takobi, da walƙiyar ka ta Sikai."
"Kune zaku koyamin? Ji nake yanzu kuka fuskanci hukuncin Zaren Mutuwa?"
Aljanun biyar suka fashe da dariya, sannan a wata irin kakkausar murya suka haɗa baki suka ce, "sabida alƙawarin dake tsakanin mu da Hidaya fasahar ka zata iya aiki a akanmu a waje. Amma acikin wannan duniya baka da iko akan komai, ƙarfin ka kaɗai zai cece ka. Dukkanin mu biyar kowanne ya kai matakin gaba da Deba, sannan kuma babu wani mahaluƙi daya kaimu iya sarrafa fasahar ƙasa, wuta, ruwa, iska da walƙiya. Mu muke raba wannan fasaha, kuma mu muke da iko akanta. Kana tunanin zaka ci nasara akan mu? To ka gwada mu ga..."
Kafin su rufe bakinsu Armad ya saukar musu da Zaren Ƙare Dangi, ya bishi da zaren Babbar Mutuwa, sannan ya nannaɗeshi da zaren Manyan-Mayu.
A lissafin Armad da mutun takwas dake bayansa an gama da wannan aljanu, amma bisa mamaki sai kawai wannan aljanu suka riƙe zarurrukan izzar suka finciko Armad. Sannan suka fyaudashi da ƙasa. Basu tsaya anan, nan take suka fara hajijiya dashi suna cille-cille dashi. Armad yai ƙoƙarin saɓulewa ya gudu amma a kowanne lokaci sai ɗaya daga cikinsu yai sauri ya cafi zaren ya riƙe. Zaren izzar da Armad yake alfahari dashi a yau shi ne ya zame masa jigila. Kafin kace meye wannan tuni Armad ya galabaita. Nusi tai ƙoƙarin shigowa amma Ƙas-turubu ya tayarda wani ƙaton bango ya raba tsakaninsu.
Cikin ƙanƙanin lokaci sukai wa Armad ligi-ligi, jini da majina.
"Shi kansa zaren izzar taka ya fiya girma da yawa. A haka kowanne ɗan tatsitsin ma'aboci izza zai iya kamashi yai hajijiya dakai indai yasan mai yake." Inji sarkin walkiya Sil'rudu.
"Kuma zaren yayi sanyi da yawa. Kana buƙatar ka mai dashi wuta abar ƙonuwa tayadda koni da aka halitta da wuta ƙonewa zanyi idan na taɓa." Inji sarkin wuta Wut'Naru.
"Kuma yayi kaushi da yawa. Ya kamata yai santsi tayadda ko ni da aka halitta da ruwa bazan iya riƙewa ba." Inji sarkin ruwa Kil'ma'i.
"Kuma zaren naka bashi da kwari, ya kamata ace ƙasa baza taci shi ba." Inji sarkin ƙasa Ƙas'turubu.
"Kuma zaren yayi shafal-shafal da yawa. Ya kamata ace iska bata ɗibansa." inji sarkin iska Ji'ruha.
"Wai ma kasan mai yasa har yanzu takobin littafin-takobi bata bayyana a gareka ba? Johoho... saboda baka da izza, baka da iko. Sai kana da Kamalar-ruhi zaka iya sarrafa ta. Dukkanin mu biyar ɗinnan babu wanda baya sarrafa Kamalar-ruhi. Kana tunanin zaka iya gamawa damu ka samarda fasahar ka ta K'Narbig acikin ƴan awannin da suka rage maka?" Inji Ƙas'Turubu.
Maimakon Armad yaji haushi ko ya hasala kawai wani murmushi ne yazo bakinsa. Dama can abinda yake nema kenan.
Ya juyo ya dubi abokan tafiyarsa ya ce, "kowa na bashi adadin izzar da ya kamata ace ya isa Deba. Lokaci yayi da zan shiga halwa. Ina saran kafin na fito kowa ya haura Deba."
***
A dai-dai wannan lokaci a doron ƙasa na biyu, sarki Dul'Ururu tare da Haruta Urúrú da Maruta Urúrú da kwamanda Yurba Ururu ne ke ta tafka mahawara.
"Mu barsu kawai su kashe kansu, wanda yai ragowa mu ƙarasa shi. Kunga mun gama dasu a ɗauka ɗaya kenan." Inji sarki Dul'Ururu wanda akafi sani da Mafarauci.
"Ni kuma ina ganin mu far musu kawai mu halaka su ba tare da jira ba." inji kwamanda Yurba Ururu, wanda shima kwamanda ne kamar Dul'Ururu.
"Har yanzu ƙoƙari muke yi mu ƙarasa gyara ɓarakar da muka samu saboda ɓarkewar sarakunan Jinzidal, bamu da sojojin da zamu shiga wannan faɗan. Shawarar Dul'Ururu ita ce, zamu yi shiri mu jira a gefe. Duk wanda yayi nasara tsakanin Bihanzin ko Ikenga ko Armad sai mu ƙarasa shi." Inji Haruta Ururu, wanda ƙani ne ga babban sarki Kuyurussa'ayi Ururu.
Maruta Ururu yai gyaran murya ya ce, "a halin yanzu duniyar ƙasashen ƙasa tana cikin juyin-juya hali na barazanar juyin mulki. Maikironomada sunfi karkata ga gidan Wilbafos, Hanibal da Deniz Iluru sun karkata ga Ikenga, shi kuma Bihanzin yana da sarkin-sarki da matafiyan alwashi. Koma waye zaiyi nasara a wannan yaƙi miliyoyi zasu halaka, za'a shafe da dama daga ban ƙasa, sannan kuma sarakuna zasu mutu. Nima na yadda mu koma gefe mu jira wanda zaiyi nasara kawai sai mu ƙarasa shi."
Yurba Ururu bai ji daɗin wannan hukunci ba. Ya dubi Dul'Ururu ya ce, "wai a halin yanzu sarakuna da garuruwa nawa ne a doron ƙasashen ƙasa baki ɗaya? Ina so nasan nawa ne a ƙarƙashin ikon mu."
Dul'Ururu ya kalleshi amma bai bashi amsa ba domin kuwa yana da cikakkiyar masaniyar Yurba yasan amsar tambayar sa, kawai dai yana yi ne.
A yanzu zaka iya cewa akwai manyan sarakuna ɗari da bakwai (107) a dukkan ƙasashen ƙasa. Sha uku a ƙarƙashin Hanibal, goma sha ɗaya a ƙarƙashin Deniz Iluru, tara a ƙarƙashin Maikironomada, ashirin da takwas a ƙarƙashin Bihanzin. Wanda ya rage saura hamsin da huɗu kenan wanda dukkaninsu suna ƙarƙashin Mayaƙan Ururu.
Kwamanda Yurba yana ganin babu dalilin da zaisa ace suna da mafi yawan sarakunan kuma su ringa zuƙewa yaƙi. A yanzu idan suka bada umarni duk sarakunan dake ƙarƙashin su fitowa zasu yi. Sabida haka yana ganin bai kamata su tsaya jiran wa zaiyi nasara ba.
"To ai ka manta da garuruwa masu ƴancin kansu." Inji Maruta Ururu. "Suna da manyan sarakuna aƙalla talatin, kuma sama da rabi sun karkata ga Fatima Wilbafos da Shata Kil'zanki. Idan ka haɗa dana Maikironomada zaka ga adadin ya canja. Banda wannan akwai farfesa Zaikid da Taidara. Taidara shirin sa a ɓoye yake, amma kai kasan ba mutun ne da zaka raina ba. Zaikid yana da rinjaye a makarantar Babila, rinjayen sa har yakai ya hana makarantar shiga yaƙin duk da kuwa ƙoƙarin shugaban makarantar na ya shigarwa Ikenga."
"To amma Dul'Ururu yana da iko akan sama da kaso sittin na Dordor ma'abota izza da suke rayuwa akan Bango. Shi kaɗai ya isa ya juya akalar yaƙin idan yayi niya." Inji Yurba.
"Hakane, to amma Bihanzin yana da ɓoyayyen sirri wanda har yanzu bamu da masaniya akai. Ka ɗauke ta Laidan da Dauwamammen Sara, akwai fasahar da yake amfani da ita tun kafin waɗannan. A har kullum yafi kyau ka lissafa nasara mafi sauƙi kabi layinta. Meye amfanin nasara mai wahala? A halin yanzu muna da damar kashe mutun uku mafi ƙarfi a ƙasashen ƙasa cikin sauƙi. Muna gamawa dasu gaba ki ɗayan ƙasashen ƙasa zasu dawo ƙarƙashin ikon mu."
Yurba yai ajiyar zuciya. "Na yarda. Amma zan ɗebi runduna ta na jira a kusa da filin dagar. Duk wanda ya faɗi acikinsu ni zan fara ƙarasa shi."
Maruta ya gyaɗa kai alamun amincewa. "Saura awa uku kurkukun ta ƙare a buɗe labulen yaƙin. Ka ɗebi rundunar sadaukai dubu goma ka laɓe ka jira. Duk wanda ya faɗi ya zama nama. Amma ba kai kaɗai zaka tafi ba. Akwai ƴar saƙo daga sama an turo."
Yana rufe baki wata zankaɗeɗiyar budurwa ma'abociyar baƙaƙen idanuwa ta fito fili. Wannan budurwa bata da tsayi sosai amma kuma tana da kyawun diri. Duk wata cikar halitta da kyawu na ƴa mace ya bayyana a jikinta. Kana ganinta zaka ga nutsuwa da hangen nesa a tattare da idanuwanta. Kai kace ta daɗe da sanin abinda zai faru tun kafin ya faru. A goshin wannan budurwa akwai tambarin Miyura. Babban abin al'ajabin shi ne Miyurar dake goshinta irin ta Armad ce sak.
Kai idan ka lura sosai zaka ga wannnn budurwa ba wata bace illa Suwainah Ururu, wadda suka haɗu da ruhin Armad a shekarun baya sanda ruhinsa ya rabe gida biyu.
"Suwainah, dake da Yurba zaku kula da filin yaƙin, duk wanda ya faɗi ku ƙarasa shi." Inji Haruta Ururu. "Kai kuma Dul'Ururu zaka kula da Taidara, ina tsoron abinda wannan mutun zai aikata. Dani da Maruta Ururu zamu kula da sauran."
Áyúbu
Ayubu na tsaye a kan doron ƙasa na uku, acikin garin Kanyu. Duk inda ya tsaya sai kaga ya haƙa rami ya binne zaren izza. Cikin ƙanƙanin lokaci ya zagaye garin da ramikan. Sannan ya samarda wani zaren wanda yai amfani dashi ya haɗe duk zarurrukan dake cikin ramikan a waje guda. Ya saƙalo wannan zaren ya jashi zuwa doron ƙasa na huɗu daular Sisiyu, garin Bihanzin, yai rami ya binne.
Bayan nan ya sakko doron ƙasa ta uku ya ringa bi gari-gari yana haƙa irin wannan rami yana binne zarurrukan. Kan kace meye wannan ya binne sama da dubu a dukkan faɗin garuruwa ɗari da bakwai dake doron ƙasashe shida.
Sannan ya saƙala wani zaren a cikin Bangon arewa, ya janyo shi har zuwa garin Jiha, garin su Ikenga, ya ɗaure. Ya ƙara saƙala wani zaren guda ɗaya dogo yayi wa doron ƙasa shidan ɗankwali. Tayadda a ko'ina akwai zarensa.
Bayan wani lokaci Ayubu ya koma can ƙasan doron ƙasa ta bakwai yai rami ya binne kansa.
A dai-dai wannan lokaci saura daƙiƙa goma kurkukun lokaci ta ƙare, a buɗe filin daga.
Comments
Post a Comment