"Armad, ka aikata laifuka da dama, amma lokacin kamfen lokacin yafiya ne. Faɗi ra'ayin ka naji, zaka karɓi gaskiya ka goyi bayan manya, ko kuwa zaka bijire ka faɗa cikin ɓatattu kafirai?"
Armad ya dubi Dul'Ururu a nutse, kalmomin sa na 'ɓatattu'da 'kafirai' suna yawo acikin ran sa, amma bai ce komai ba.
Bayan ƴan daƙiƙu Dul'Ururu ya fuskanci ba lallai ya samu amsa ba, sai ya numfasa ya ce, "faɗi amsar ka, Armad Wilbafos."
Maimakon Armad ya bashi amsa sai kawai ya ɗaga kan sa sama ya nuna doron ƙasa ta farko ya ce, "Kuyurussa'ayi Ururu, daga yau, ni Magajin Wilbafos, Armad Wilbafos, na haramta cinikin bayi. Ina umartar ka da iyalan ka da ku fito da duk bayin dake doron ƙasa na farko ku ƴanta su. Zaku bawa kowanne bawa haƙuri ku nemi yafiyar sa da ayrid dubu goma."
Dul'Ururu ya yamutse fuska yai tsaki. "Wannan ce amsar ka? Duk abinda ya same ka kada ka zargi kowa." A wannan lokaci Dul'Ururu yasan cewa babu sauran jawabi a tsakanin sa da Armad. Abinda kawai ya rage shi ne a fafata a fitar da gwani. Duk wanda yayi nasara shi ne gwani.
Dul'Ururu ya tafa hannayen sa biyu ya kira manyan ɗalasimai. Take taskar ruhin dake saman kan sa tana lilo ta fara haske tana curewa a waje guda. Cikin ƙanƙanin lokaci ta juye izuwa takobin haske, sannan ta juye izuwa baƙin ƙarfe.
Dul'Ururu ya cafi takobin ta baƙin ƙarfe yai tsalle ya afkawa Armad da mummunan sara. Cikin kwarewa Armad ya zare tasa takobin sa yai tsalle sama ya tari Dul'Ururu gaba-gaba.
Takubban su na haɗuwa wani nauyi ya sauka a wajen, ƙasar wajen ta fara darewa tana tsattsagewa. Iska mai kama da guguwa ta turnuƙe tai sama. Kan kace meye wannan mabiya kowa ya zare makamin sa.
Armad ya fuskanci Dul'Ururu ido cikin ido, takobi cikin takobi, kowannen su na lissafa izzar ɗan'uwan sa yana neman ta wajen da zaiyi masa illa.
A bayan Armad kwamandun sa na tsaye zare da makaman su, kamar yadda shima Dul'Ururu mutanen sa na tsaye a bayan sa suna jiran kota-kwana. Tsahon daƙiƙu ana tsaye ana kallon-kallo babu wanda ya motsa, kowa ya zaɓi abokin karawar sa yana jiran umarni ya afkawa masa. Idan ka kula zaka ga Babara ya kama Haruta, sai kuma Iliyasis da Cokali da suka kama Maruta, ragowar kuma suna tsaye suna fuskantar juna daga nesa.
Ana cikin haka sai kawai aka ga takobin Armad ta fara haske, kafin Dul'Ururu ya ankara kawai sai gani yayi takobin ta fara yanka jikin takobin sa tana ratsawa tana shiga ciki, kai kace wuƙa ce take yanka albasa, haka takobin Armad ta ratsa takobin Dul'Ururu ta raba ta gida biyu. Bata tsaya anan ba, ta wuce gaba ta sari kafaɗar Dul'Ururu ta hagu ta datse hannun. Jini yai feshi, guntulallen hannun ya faɗi ƙasa yana wutsil-wutsil ba rai. Armad ya sake juya takobin sa cikin kwarewa da hikima ya caki cikin Dul'Ururu. Zanen hatimin dake jikin ƙarfen takobin ya fara haske yana walwali. Armad bai tsaya haka ba, nan take ya zare takobin ya sare kan Dul'Ururu. Kai yayi sama yana feshin jini, ita kuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa shirim. Tun ƙafafun Dul'Ururu suna motsi har sai da suka tsaya cak, ran sa ya ƙarasa ficewa.
Duk wannan abubuwa dake faruwa a zahiri suka faru akan idon kowa, da mutanen Armad da mutanen Dul'Ururu duk kowa ya gani kuma yasan gaske ne. Babu rufa-ido aciki. Kai hatta Nostaljiya wadda ke gani har hanji da idanun ta tasan hakan ya faru. Sai dai kuma kash... Duk abinda ya faru ya faru ne a wannan lokacin, a wannan zamanin, a wannan duniyar, a kuma wannan wajen. Acan wani lokacin, a wani zamanin, a wata duniyar, a kuma wani wajen, takobin Dul'Ururu ita ce ta ratsa takobin Armad ta yanka ta ta shige ciki ta sari Armad a wuya. Jinin Armad ya zuba a ƙasa, sannan a wani salo na rashin tausayi Dul'Ururu ya ƙara saukar wa da Armad sara ta sama. Kafin Armad ya ankare takobin ta sare masa rabin fuska. Dul'Ururu yayi amfani da damar ya cake takobin a zuciyar Armad, kafin daga bisani ya fille masa kai.
Armad ya faɗi ƙasa matacce.
Nostaljiya, Nusi, Babara, Iliyasis, Cokali, Inara, Lamarudu da Nazara duk sunga abubuwan da suka faru. Babu ko shakka aciki - Dul'Ururu ya mutu, Armad ya mutu. To amma kuma babban abin al'ajabi duk su biyun gasu nan a tsaye riƙe da takubban su suna fuakantar juna babu ko rauni a jikin su. Abinda kaɗai zaka kalla kasan wani abu ya faru shi ne tufafin su: rigar Dul'Ururu ta kece ta kafaɗa dai-dai wajen da Armad ya sare shi, sannan kuma ta ɓule a ciki dai-dai wajen da Armad ya caka masa takobi. Shima Armad yana da ɓula a rigar sa a dai-dai saitin zuciyar sa wajen da Dul'Ururu ya caka masa takobi a ƙirjin.
To wai meke faruwa ne? Abubuwa biyu sun afku a lokaci guda; ɗaya ya ƙare da mutuwar Armad, ɗaya kuma ya ƙare da mutuwar Dul'Ururu. To amma duk mutun biyun ga su a tsaye da ran su da lafiyar su. Ga dukkan alamu bamu kaɗai ba, ko Nusi - idan ka lura da kallon da take yiwa Armad - kasan bata da masaniya akan abinda ke faruwa.
Abu ɗaya da kowa ya yadda dashi shi ne: a yau wata babbar fasaha ta sauka. Abin tambayar anan shi ne: fasahar Armad ce ko kuma ta Dul'Ururu?
Bayan ɗan gajeren lokaci ana kallon-kallo sai Dul'Ururu ya kaɗa kai ya maida takobin sa. Ya dubi Armad ya ce, "yanzu ka gani da idon ka; duk duniya babu wanda zai iya cin galaba akai na. Ni ne Dul'Ururu - babba ɗan babba, jinin Ururu. Zan yi kamfen na kwana talatin, daga nan zan gabatar da babbar jinzidal a garin nan, kazo muna jiran ka. Abu na ƙarshe ina so ka sani cewa Uznu yaro ne mai girman kai da rashin lura, to amma duk da haka haƙƙin yi masa ladabi ba a hannun ka yake ba. Da sannu zan rubuta maka ƙaddarar ka." Yana faɗar haka ya juya ya tafi. Maruta, Haruta, Hanibal, Ibraham Nil da Suwainah biyar da suka rage suka bi bayan sa.
Maimakon Armad ya tanka masa sai kawai ya maida takobin sa. Ya juyo izuwa mutanen sa yana murmushi, ko kaɗan babu damuwa a fuskar sa. Sai dai kuma saɓanin Armad, su Nusi da Nostaljiya da sauran kwamandun sa hankalin su a tashe yake.
"Wai meya faru?" Inji Nusi.
Kafin Armad ya bata amsa Babara ya amsa da cewa, "Mafarauci kenan. Na tabbatar Armad yaci galaba akan sa da farko, to amma ya canja abinda ya faru ya ƙara rubuta wani zamanin. Babu wanda yasan yadda Mafarauci yake aiwatar da fasahar sa, amma, kamar yadda ya faɗa, cin akan sa ba abu ne mai yiwuwa ba. Naji ance bai taɓa zuwa ƙasa ba tunda ya balaga."
Armad na jin haka ya juyo ya ɗora hannun sa akan kafaɗar Babara. A wannan lokaci Babara yaji kamar an sauke masa izzar dake duniya baki ɗaya. Ƙafafun sa sukai sanyi ya fara rawar ɗari. Ya ɗago a hankali ya dubi Armad.
Armad ya dube shi ido cikin ido ya ce, "shaihu Babara, babu wanda ba'a cin galaba akan sa a yaƙi, wuyar ta kawai a shirya a fito."
Comments
Post a Comment