Nazára da Nusi suka dubi Suwainah cikin mamaki. Farar mace (mudubi) mai baƙaƙen idanu dara-dara. Tana da tsayi kimanin zira'i biyu da rabi, da jiki kakkaura ma'aboci kyawun diri, sai dai duk wannan bai ɗau hankalin kowa ba, domin kuwa hankalin su na kan goshin ta. Inda tambarin miyura ke ɗamfare akai.
Da Nusi da Nazara zaka iya cewa sun fi kowa sanin wannan tambari. Sun daɗe suna ganin sa, sun san sharrin sa, kuma sun san ƙarfin sa, badan komai ba sabida suna tare da asalin mai shi.
"Suwainah? Kece yarinyar nan da kika yaudari shugaba a shekarun baya, kika sa aka ƙulle shi cikin Hajarul-Ururu, ko?" Inji Nusi. Tuni Armad ya daɗe da bata labarin tsakanin sa da Suwainah. "Idan zan tuna kina da ƙanwa Zainab... a'a, Zaira, ko? A'a Zeera."
Suwainah tai murmushi cikin ƙafafa da jiji-da-kai, kana gani kasan tana taƙama da mallakar doron ƙasa na farko, tana ji cewa kowa bawa ne a ƙasan ƙafar ta, ita kaɗai ce mai takalmin ƙarfe; kowa ta taka ya taku. "Ina Armad? Idan har shi ne ya baki wannan labari to kuwa lallai kece kika fi cancanta kisan wajen da yake."
Nusi ta yamutse fuska haɗe da taɓe baki. "Wai ke dama Armad kike nema? Hehe..." Ta fashe da dariya. "Babbar izzar K'Narbig tafi gaban ki neme ta, yarinya, idan ana buƙatar ki za'a gan ki, idan ba'a buƙatar sai dai kibi layi." Ta nuna kanta da Nazara da Farin Yashi, wanda a halin yanzu ya miƙe tsaye, ta ce, "A halin yanzu sai dai kiyi haƙuri da iya mu. Iyakacin abinda zaki samu kenan."
Suwainah ta ɗaga gira cikin izgili, sannan ta girgiza kai a hankali, alamun bata buƙata, kafin ta juya ta kalli Hannibal ta ce, "Lokaci yayi."
Hannibal yai ajiyar zuciya ya ce, "Kamfen ko? Kamar yadda na rubuta a rahoto na Bihanzin ya haƙura da muƙamin sa na sarkin Jinzidal, amma Maikiro'Abbas da Deniz Iluru na nan riƙe da muƙaman su, sun bayyana min cewa a shirye suke da a fara kamfen dasu a kowanne lokaci. Acikin ƙasashe ɗari da bakwai na ƙasashen ƙasa mun aikewa da kowacce ƙasa goron gayyata: arba'in aciki sun amince zasu aiko sojojin su domin assasa tafarkin Ururu, goma sun aiko da kayan yaƙi irin su sulke da takubba da garkuwa, ragowar goman kuma, duk da basu turo komai ba, sun amince da biyan haraji da kuma yaɗa kalmar 'kamfen' ɗin ta kafafen watsa labaran su. Sabida haka ragowar ƙasashe arba'in da shida su zamu fi bawa muhimanci a lokacin kamfen ɗin."
Suwainah ta ɗanyi shiru tana kai-komo da maganar acikin ranta kafin daga bisani ta numfasa ta ce, "da fatan ka haɗa komai akan wannan ragowar ƙasashe dake neman yin tawaye ga tafarkin magabatan su?"
Hanibal ya gyaɗa kai. "Eh. Tuni aka gama haɗa komai." Sannan, kamar wanda ya tuna wani abu, ya juya ya dubi Nazara da Nusi da Farin yashi, ya ce, "Akwai wanda acikin ku yake da rai a lokacin wancan kamfen ɗin?"
Ga dukkan alamu basu da niyyar bashi amsa domin kuwa zare makaman su kawai sukai.
Hanibal ya gyaɗa kafaɗa cikin nuna halin ko-in-kula. "Dukkan tawagar kamfen ta haɗu, sarakuna da kwamandun kamfen irin su Ibraham Nil, Haruta wa Maruta, Suwainah, Dul'Ururu, kwamanda Yurba, sarakunan jinzidal. Kai, madalla da dawowar kamfen ɗinnan akan lokaci."
***
Acan ɗaya ɓangaren kuma Inara da ƴan-goma suna kwance a ƙas, Suwainah ta zuƙe musu izza baki ɗaya, tamkar dama can ba ma'abota izza ba ne.
Tana tafiya taku ɗai-ɗai ta gabato izuwa gaban Inara. Ta buɗe baki zatai magana kawai sai ta fasa ta rufe bakin ta, ta zira hannu cikin aljihun rigarta ta ɗakko wata ƴar ƙaramar wuƙa tana wasa da ita. "Idan kana da wasiyya ka faɗa."
Inara ya ƙura mata ido bai ce komai ba. Bayan ƴan daƙiƙu ana kallon-kallo a tsakanin su sai kawai ta yanke shawara ta gaji da jira. Ta nufi wuyan sa da wuƙar gadan-gadan. Suma ragowar Suwainah biyar ɗin dake gefe suka afkawa ƴan-goman dake bayan sa.
Sai da ya rage baifi ɗan taƙi ba tsakanin wuƙar da wuyan sa ba yai maza ya miƙa hannu cikin tsananin zafin nama ya cafi wuyan ta. Yai walanƙeluwa da ita ya buga ta da ƙasa sannan ya saukar mata da Hannun-Aradu a ciki. Dunƙulen walƙiya yai tsiri yai ambaliya ya daki cikin ta ya fice ta baya. Babu shiri tai feshin jini daga bakin ta. Abubuwan da suka afku suna da yawa amma a zahiri cikin rabin daƙiƙa komai ya faru. Kafin Suwainah ta ankare tuni taje ƙas.
"Shugaba Armad ya koyar damu faɗa acikin kowanne irin hali: da izza ko babu izza." Inji Inara. Duk da cewa shi kaɗai ne ya tsira to amma hakan yai matuƙar firgita Suwainah. Bata taɓa tunanin akwai mutumin da zai iya sarrafa fasahar aljanu ba tare da izza ba, kuma tana gani da idonta ta tabbatar cewa babu izza a jikin Inara, amma duk da haka gashi yana sarrafa walƙiya. Wataƙila saurin da Inara yayi ya cafi wuyan ta shi ne ya firgita ta, ko kuma wataƙila firgitar da tayi na ganin yana amfanin da walƙiya ba tare da izza ba ne, ko kuma dai wani abun, to amma dai Suwainah ta kasa amfani da idon ta na Saɓani ta kaucewa harin Inara. Inara yayi amfani da damar ya saukar mata da Hannun-aradu biyar a jere, kafin daga bisani ta dawo hayyacinta tai tsalle ta koma baya.
Inara yai kan ragowar Suwainan dake ƙoƙarin halaka ƴan-goma, ba shiri suma sukai tsalle baya. Ya buɗe zoben tsafi dake hannun sa ya cilla su aciki. A halin yanzu Inara ne shi kaɗai tare da Suwainah guda biyar. Amma duk da haka babu tsoro a tare dashi.
"Lallai ka samu horo mai kyau." Inji Suwainah cikin nishi da haki. "To amma wannan bai isa ya tseretar dakai ba." Nan take su biyar ɗin sukai rubdugu akan sa shi kaɗai.
***
A ƙofar gari kuwa yaƙi yayi tsamari tsakanin ɓangaren Lamarudu da ɓangaren Tagwayen-auni. A tsarin girman fasaha sun fi Lamarudu, to amma duk fasahar da suka aiko Lamarudu zuƙe ta kawai yake, komai girman dunƙulen wuta daya tunkare shi sai kaga ya narke. Babu wata dabara ko kuma fasaha da zasu yi amfani da ita face ya lalata ta.
Ana cikin haka Nostaljiya, Cokali, Iliyasisi da Babara suka bayyana a filin yaƙin. Idan mai karatu bai mantaba tuni tawagar su tayi nasara a garin Jekis na sarki Bihanzin, to amma suka gamu da boren talaka. Duk da hatsaniyar da ake ciki Bihanzin yana taimaka wa mutanen sa, wanda hakan yasa suka bijirewa duk wani ƙoƙari na su Nostaljiya na su shawo kan su. Koma dai meye ya biyo baya a yanzu sun baro wancan garin sun dawo garin Faideba domin taimaka wa ƴan-uwan su wajen tarwatsa shirin Hanibal da Ururu. Koma dai yaya ake ciki, koma yaya za'ai dole ɓangare ɗaya ne tak zaiyi nasara. Kuma a yau za'a ware aya da tsakuwa.
***
Acan doron ƙasa ta bakwai, sashin arewa, kusa da makarantar Babila, tuni kamfen yayi nisa. Manyan malamai na jami'ar Babila da wasu ma wanda suka sakko ƙasa daga babbar jami'ar doron ƙasa-ta-farko sun tara dubban jama'a, manya da yara, mai-kuɗi da talaka, mai-sarauta da mara sarauta, suna ta wa'azi.
"Kalma ta farko ita ce ZAMAN LAFIYA. A tun farkon Ururu bamu da tafarki sai na wanzar da zaman lafiya. Bamu yadda mai ƙarfi ya cuci mara ƙarfi ba." Inji shaihun malami Almasar Ururu. "Shekaru dubu da suka gabata duniya bata san meye zaman lafiya ba. Babu wata ƙasa tun daga doron ƙasar nan na bakwai har zuwa na ɗaya inda ake zaune lafiya. Babu. Kawai duk sanda mai ƙarfi ya bushi iska sai yayi shiri ya tara runduna ya yaƙi ƙasar dake kusa dashi wadda bata kai shi ƙarfi ba. Ya riba ce matayen su - wanda za'a yiwa fyaɗe a bautar dasu sune masu gwanda-gwanda - da dama safarar su za'ayi ta ruwa zuwa wata uwa duniya ayi tsafi dasu. Sarkin adalci, sarkin al'umma, sarkin gaskiya, sarki Kuyurussa'ayi Ururu yazo ya tsayar da wannan zalunci. Ya hana duk wani salo na yaƙi tsakanin ƙasashe. Ya hana duk wata ƙasa ta yaƙi wata. Idan kana da matsala da wani sai dai ka jira ku ware raini a lokacin gasar jinzidal. Tunda aka fara jinzidal babu wata ƙasa da aka taɓa yaƙa. Iyyakacin faɗa baya wuce gasar jinizdal. Ko a baya da akai yaƙin sarakunan jinzidal sabida bijirewar Bihanzin ne, bawai sabida gazawa ta ɓangaren doron ƙasa ta farko."
Waziri Tadiyraini, wanda shi ne kujera ta biyu a doron ƙasa na farko, ya gyaɗa kai alamun amincewa. Kujerar sa na gefe yana nazarin taron cikin tsanaki. Shekarar sa dubu da ɗoriya kenan rabon sa da ƙasashen ƙasa, amma a yanzu dole tasa yazo. Domin mutane suna buƙatar a tuna musu baiwar da babban sarki Kuyurussa'ayi yayi musu.
Bayan sa akwai baƙin fuskoki da dama a wajen: mutun bakwai daga ƙabilar Ururu, mutun sittin da ɗaya duk sarakuna ne daga ƙasashe sittin da ɗaya dake goyon bayan kamfen ɗin, wanda kuma suka yadda cewa kamfen ɗin nan wajibi ne.
***
A yayin da kamfen ya fara harama, a can ƙarƙashin ƙasa Ayubu ne ke shagalin sa. Shifa Ayubu bashi da asara: idan an kashe shi babbar izzar K'Narbig zata dawo dashi; irin yadda aka halicce shi a farko haka za'a ƙara halittar sa a karo na biyu. Yana tsakiyar rundunar dubunnan sadaukai ma'abota izza abokan gaba. Duk da cewa Haruta da Maruta sun koma gefe basu shiga fafatawar ba, hakan bai hana Deniz Iluru, Deniz Bizaya da Deniz Kalhari yin rubdugu akan Ayubu ba. Acan gefe guda wasu sadaukai ne uku (wanda sune salsan Iluru) suke jagorantar rundunar mutun dubu goma wajen afkawa mutun dubu ƴan ƙabilar Wilbafos da suka rako Ayubu.
Zaka iya raba filin yaƙin gida uku: a ɓangare ɗaya Haruta da Maruta na gefe suna kallo; a ɗaya ɓangaren kuma Iluru, Bizaya da Kalhari sun tarar wa Ayubu; sannan kuma a ɓangare guda kuma turnuƙu ne faɗan iblisai ke wanzuwa tsakanin dubban sadaukai. Zaiyi wuya ka gane maike faruwa, sabida yawan takubban dake wulƙawa da kuma ƙura. Kayi ka sun wanzu suna tsalle suna rabuwa jikkunan su. Jini na malala. Ƙura ta turnuƙe. Haniniyar dowakai da hankakan mutuwa na ta yawo.
"Kun san cewa duk mutun ɗaya daya mutu a wajen nan ƙarfi kuke ƙarawa Bihanzin? Iyakacin yawan rayukan da hankakan mutuwa ya ɗiba iyakacin girman izzar Bihanzin." Inara ya tambayi abokan fafatawar sa a takanin sara da suka. Kafin su bashi amsa sai da kowannen su ya kawo masa sara sama da biyar. Kalhari, wanda da mashi yake amfani, yafi kowa zaƙewa wajen kai hari ɗai-ɗai har sha bakwai.
"Idan a matsayina na sarkin jinzidal ban san wannan ba to meye amfani na." Inji Iluru. Ya ɗaga ƴan'yatsun sa ya fara lissafa falalar Bihanzin. "Na ɗaya: Dauwamammen sara; na biyu: hankakan mutuwa; na uku: Laidán; na huɗu..." Yayi shiru kamar yana jimamin faɗa kafin daga bisani gyaɗa kafaɗa. "Bihanzin fa shi ne Mai Haske - wanda ya taka rawa a wancan kamfen ɗin da akai, kamfen ɗin daya janyo aka mayar da ƙabila ta ƙarƙashin ƙasa. Kana tunanin kune na farko da kuka fara yiwa Ururu tawaye? Hmmm. Da kasan tarihin ƙabila ta da baka fara yin tawaye ba. Munyi alƙawari baza mu bayyanawa kowa wannan labari ba, hatta ƴaƴan mu, har zuwa sanda wani kamfen ɗin zai zo. A yau wannan alƙawari ya cika. Kamfen ya zagayo. Saurara kaji labarin ƴan-tawaye na farko. Wanda suka sa akai kamfen na farko a doron ƙasashen ƙasa." Sarkin Jinzidal Deniz Iluru yana bayani yana dariya mai ƙuwwa da amo. Acikin dariyar akwai kafiya wadda ƙarfin ta ya zarce hankali. Kana ji kasan an ɗaɗe ana muradi, an daɗe ana bege, an daɗe ana so, amma an kasa samu. Kaikace macen da aka sacewa miji ce tsahon shekara goma kwatsam aka ce mata gashi ya dawo yana tsaye a ƙofar gida. Idan mai karatu bai mantaba tun a gasar jinzidal Iluru ya bayyana wa ɗansa Bizaya cewa gano sirrin Ikenga yafi samun nasara a gasar. Badan komai ba sabida burin su na ganin cewa sun bar ƙarƙashin ƙasa sun dawo sama.
"DÉNIZ HÚHÚTU, kaka na kuma sarki na farko a ƙabila ta, shi ne mutun na farko dayai gaba da gaba da babban sarki Kuyurussa'ayi tun bayan Eyriyon. Shi ne..."
Ayubu ya finciki zaren izzar Iluru da hannun dama sannan ya kai masa sara da takobin Negrinkin dake hannun sa na hagu. Bizaya da Kalhari sukai sauri suka shiga tsakani, lamarin da ya bawa Iluru damar suɓucewa, ya kewaye ta baya ya saukarwa da Áyúbu ƙusar mairakana guda hamsin a jere, a lokaci guda kuma yana ci gaba da bashi labari. "Shi ne ya fara gina makarantar Babila. Duk wani labari da zaka ji akan wanda suka gina ta ƙarya ne."
#
Comments
Post a Comment