Ance faɗuwar wani tashin wani. A lokacin da ƙarar da Nostaljiya take yi ta firgita su ƙaraiƙisu, a lokacin Inara ya samu damar kubuta daga hannun baƙin basamuden. Yana dirowa ƙasa ya juyarda jikinsa izuwa walkiya sannan yayi wajen Nostaljiya gadan-gadan babu ko alamun tsoro ko razana. Yana ƙarasawa ya saɓa ta a kafaɗa sannan ya juya wajen Lamarudu. Kallo ɗaya yayi masa yasan babu shi sabida haka ya juya ya nufi daji da gudu inda ya bar su Ƙaraiƙisu a ƙasa suna riƙe da kunnuwansu.
Sai da aka shafe kusan rabin sa'a acikin wannan hali sannan ƙaraiƙisu, Kána, Dádara, B. Ururu, da Deniz Ururu suka farko. Wani abin mamaki shi ne su dai ba suma sukai ba, kuma ba bacci sukai ba, kawai hankalinsu ne ya gushe tayadda basa iya gane wanda ke kusa dasu da kuma abinda ke faruwa a kusa dasu, to amma kuma suna tsaye kan ƙafafunsu suna ji suna gani amma kuma idan an kai sakon abinda suka ji ko suka gani sai ƙwaƙwalwar ta kasa fassara. Lallai a wannan rana an bayyanar da sabuwar fasaha ta musamman a fannin tunani.
Ta ɓangaren ƙaraiƙisu kuwa yana wartsakewa kawai Inara da Nostaljiya ya fara laluba. Koda yaga bai gansu ba sai ya juya kan Ayubu wanda shima babu shi babu alamun sa. Wani abu da yaja hankalin kowa nan take shi ne akwai ragowar waɗanda babu.
"Ina Iluru?"
"Ina Bizaya?"
"Ina denizawa dubun dake zaune akan ramukan can?"
Nan take aka fara lalube. Akwai sarkakiya acikin al'amarin. Ga dukkan alamu wani hatsabibi yayi amfani da halin makuwar da suka shiga ya zambace su.
Ƙaraiƙisu ya nemi waje ya zauna ya tankwashe ƙafa ya rufe ido ya shiga tunani.
Kána ya dube shi a fusace ya ce, "wato kana da lokacin hutawa ma kenan? Kana ganin sun gudu. Babu Nostaljiya babu alamun ta. Babu Iluru babu alamun sa. Babu denizawan da zamu yi amfani dasu wajen karya asirin babu alamun su. Gashi kuma ka kashe Lamarudu a banza a hofi amma kuma hutawa kake yi. Wani lokacin sai kasa na fara tunanin ko da gaske yaudarar shugaba Ikenga kake son yi."
Ƙaraiƙisu bai bashi amsa ba. Hasalima ko buɗe ido baiyi ba. A gefe guda su Deniz Ururu komawa gefe sukai suka fara tattaunawa akan halin da suke ciki.
"Deniz Ururu, a ganin ka mai ya faru?"
Tambaya ta juyo kan Deniz Ururu domin ƴan kabilarsa ake magana akai. Kuma daɗin daɗawa Ilurun nan ɗan wansa ne.
"A jiki na bana ji sun karya asirin." Inji shi.
"To idan zan iya tunawa ai dakai da Iluru babu asirin a jikin ku, kaga kenan koda an karya ba lallai ka gane ba." Inji Dádara.
Deniz ya gyaɗa kai. Da ace da asirin a jikinsu da dashi da Iluru baza su samu siffar samudawa ba. Kada dai a manta asalin ƙirar denizawa ta samudawa ce, asirin da akai musu shi ne ya rage musu girma suka dawo ƙananu. Tunda babu asirin a jikin Iluru da Deniz Ururu shi yasa jikinsu ya zauna a yadda yake.
Deniz ya yamutse fuska. "Wai mai kuke ƙoƙarin kuce ne?"
B. Ururu wanda daman tun can ba kunya ce ta ishe shi ba ya dubi Deniz ya ce, "abinda muke ƙoƙarin cewa shi ne: da ɗan wanka Deniz Iluru, da jikan ka Bizaya, da Ayubu sun haɗa kai sun karya asirin da akai wa ƙabilarka ta denizawa kuma sun gudu."
Fuskar Deniz Ururu tayi baƙi nan take. Lallai shima yasan akwai yiwuwar hakan, to amma shi yasan hakan baza ta yiwuwa ba. Domin ko ba komai akwai amana da yadda a tsakaninsa da Iluru. Duk wani shiri da Iluru zaiyi sai ya tuntube shi. Kai idan aka koma shekara ɗari da doriya data gabata a sanda Iluru ya fara bincike akan karya asirin sai daya tuntube shi. Dashi akai komai saboda haka yasan komai. Idan Iluru yana niyyar yaudarar Ikenga ko kuma ya karya asirin da kansa ba tare da kowa ya sani ba to lallai zai gaya masa. Akwai wannan yaddar a tsakaninsu.
"To idan kuna tunanin Iluru ya karya asirin to sabida me zai gudu? Dukkanin mu nan mun riga mun san cewa Ikenga shi ne ya samarda dalasimin da za'a karya asirin dashi. Kuma yadda aka tsara dalasimin duk badenizen da asirinsa ya karye to zai dawo ƙarƙashin Ikenga yaci gaba da yi masa biyayya har tsahon rayuwarsa. Ta haka Ikenga zai haɗa rundunar samudawa guda biyu: ɗaya ta samudawan ikwatora wadda ƙaraiƙisu zai jagoranta, ɗaya kuma ta samudawan ƙarƙashin ƙasa wadda ni zan jagoranta. Kuna so kucemin akwai wani ɗalasimin wanda zai iya karya asirin banda na Ikenga?"
Kána ya haɗe gira. Lallai akwai lauje cikin nadi. Tayaya za'ace akwai wani ɗalasimin dazai iya karya asirin bayan shi yafi kowa sanin wahala da shekarun da suka ɗauka kafin su kirkiri wannan ɗalasimi.
"Watakila canja shi sukai bawai sabo suka kirkiro ba," Inji Dádara, "misali su canja wani ɓangare daga cikin dalasimin tayadda maimakon denizawan su koma yiwa Ikenga biyayya sai su koma yiwa Iluru."
Kána ya girgiza kai. "Bazai yiwuba. Sama da shekaru goma muna aiki akan wannan ɗalasimi. Lallai nayi amanna babu wani mahaluki da zai iya canja dalasimin ba tare da ya lalata shi baki ɗaya ba."
A wannan lokaci ƙaraiƙisu ya buɗe idonsa ya juyo ya shiga cikin maganar. "Kana cewa babu wani mahaluki dazai iya bayan gani. A lokacin da kuka yadda da kanku kuka kautar da kai kuna ganin kun samarda dalasimin da babu wanda zai iya canjawa, a lokacin na samu dama na canja taswirar ɗalasimin tayadda ana karya asirin duk samudawan da zasu bayyana ni zasu yiwa biyayya ba Ikenga ba."
Rai a ɓace su Kána suka dube shi suna ƙoƙarin afka masa.
Shi kuwa ƙaraiƙisu ko a jikinsa. Kawai ci gaba da bayani yayi kamar ma baiga kallon da suke masa ba. "Kunga ta ɓangare na kenan. To amma nima ban sani ba ashe Iluru da Ayubu suna ƙasa suna kulla min tsiya. Dan tabbas ko kokwanto babu nasan sun karya asirin. Kuma a halin yanzu suna can wani waje a ɓoye suna samarda rundunar samudawa. Babbar matsalar da Ikenga yake fuskanta shi ne ya yadda da tsafi da yawa. Shi kuma tsafi gaskiyar mai shi ne. Duk abinda ka kulla waninka zai iya warwarewa. Hakan shi ne yasa zan yanke alaƙa ta daku daga wannan waje."
"Amma kai butulu ne. Ikengan shi ne ya dawo dakai bayan ka mutu acikin baƙar guguwa amma kuma abinda zaka saka masa dashi kenan?" Inji B. Ururu baki na kumfa dan haushi.
"Butulu fa kace?" Ƙaraiƙisu ya girgiza kai. "A'a, ko kaɗan Ni ba butulu bane. Tsari na guda ɗaya ne: ina biyayya ga wanda yafi ƙarfi na. Lallai a lokacin da naga fasahar lokaci ta Ikenga nayi tunanin ya kere kowa a ƙasashen ƙasa kuma bashi da sa'a. To amma abin ya bayyana a gare ni ba haka bane. Kuna tunanin ni da nake da sashin ikwatora baki ɗaya a ƙarƙashina da sarakuna biyar da dauloli shida zan yiwa wanda bashi da komai kuma bashi da ƙarfi mubaya'a? Ai abin bai ma bada ma'ana ba kuma babu daɗin ji ko kaɗan. Ni ina da banbanci daku baki ɗaya: ko kaɗan bana mubaya'a sabida ƙabila ko kuma gida, wannan shirme ne kawai. Idan wani mutun yana so nayi masa mubaya'a to saiya gamsar dani ta hanyar karfin dantse." Ya miƙe tsaye a hankali sannan ya juya ya nufi sashin ikwatora. "Idan kun gamu da Ikenga ku gaya masa ina nan a sashin ikwatora ina jiransa idan ya shirya. Amma idan ya ƙara zuwar min ba'a shirye ba akwai yiwuwar na kashe shi kowa ya huta."
Koda ya gama faɗar haka sai ya tashi sama ya ɓace.
Su kuwa su Kána zama sukai a gefe sukai tagumi. Lallai akwai matsala. Babu wanda zai taɓa tunanin yadda suka fito a shirye abubuwan zasu wargatse musu haka. Gashi abin haushi basu masan ina Ikenga yake ba. Gashi denizawan sunyi butulci. Ga ƙaraiƙisu ya fandare. Duk da Kána bazai iya faɗa ba amma tabbas anci su da yaƙi. Kuma yasan cewa indai suna so su farfaɗo to fa sai sun sake shiri kafin yaƙin ruhi. Abu na farko shi ne su nemo Ikenga.
To a lokacin da ake wannan tataburza tuni Inara yayi nisa acikin daji yana ta gudu da Nostaljiya a kafaɗa. Har yanzu ihu take kuma tuni ya daɗe da gano cewa bata san a inda hankalinta yake ba. Inda ya godewa ALLAH shi ne ƙarar bata damunsa tunda ya juyarda jikinsa izuwa walkiya. Amma kuma hakan yake nuna masa cewa Ayubu wanda shima zai iya mayarda jikinsa izuwa walkiya tabbas ya kubuta daga harin.
Yana cikin tunanin nan kawai yaga bango a gabansa ya tokare da sararin samaniya. Mai karatu zai iya tunanin bangon kudu ko na arewa Inara ya gani, to amma basu bane. A zahiri tulun tururuwai ne kurum wanda suka sa baya iya hango gabansa. Sunyi tsiri sun samarda wata katanga kamar bango wadda ta rufe hanyar babu ta inda zai wuce.
Yana cikin wannan hali wata ƙatuwar tururuwa wadda lallai tafi shi girman jiki koda an haɗa shi da Nostaljiya a guri guda ta bayyana a bayansa. Yana waiwayowa kafin ya ankare ta cafi wuyansa. Kawai ji yayi idanunsa sun rufe sabida dafin data soka masa. Abu na ƙarshe daya gani shi ne haɗiye Nostaljiya da tururuwar tayi ta juya ta gudu. Jikinsa yayi sanyi kuma ko motsi baya iyawa. A haka ya suma a wajen yana ganin tururuwan suna wucewa. A ransa babu abinda yake tunani sai sarauniya Nostaljiya.
***
A ɓangaren Nusi da mutanenta kuwa tunda suka fice daga gidansu Armad suka shiga duniya suna yawo suna neman Armad. Daga wannan gari zuwa wannan, daga wannan gari zuwa wannan. Sai da suka shafe sati Uku suna abu ɗaya. Zaka iya cewa tun daga doron ƙasa ta uku har zuwa ta bakwai babu inda basu je ba. Bayan sun gaji da kewaye-kewaye da tambaye-tambaye Nusi ta bugi kirji ta yanke shawarar abinda ya kamata tayi. Kai tsaye ta wuce doron ƙasa na biyar garin Khan. A wannan gari har yanzu sunan Nusi yana cikin ƴan majalisar garin. Sabida haka zakai tunanin tunda ta dawo zata nemi muƙaminta to amma batai hakan ba. Suna shiga garin suka zarce gidansu inda suka iske shi a rufe. Tun daɗewa sanda su Cokali da Iliyasis suka fita neman Nusi suka sallami ma'aikatan gidan. Ita kuma babbar hadimar su, Jimmu, dama tuni ta bar garin tayi hijira. Wannan ne yasa dole sai rufe gidan sukai tunda koda sun saka ƴan haya babu wanda zai karɓi kudin idan lokacin biya yayi.
Suna tura ƙofar yana da ƙura tayi musu sallama. Farfajiyar gidan ta cika da ƙura da busassun ganyayyaki. Da kyar suka kewaya shiga cikin falo. Inda suka samu ɗan sauƙin datti shi ne su Cokali sunyi ƙoƙari sun rufe dukkanin muhimman kayan gidan irinsu kujeru da gado da mayafi sabida haka akwai rangwamen ƙura anan.
Giwa, Inyaya, Shísu, Barilu, da kuma Sarkin Bai suka shiga aikin shara da goge-goge. Nusi da Cokali suka zagaya baya wajen tafkin da suke wanka suka ga tuni ruwan ya bushe, gansakuka da ƙura da kwari sun cika ramin. Suka shiga cikin ɗan lambu dake bayan gidan suka zagaya. Mangwaro, kwanda, abarba, inibi da tufa duk sun fado ƙasa sun bushe sun zama kwallo. Wasu bishiyun sunyi tsayi sosai da sosai tayadda sai ka daga kai sosai zaka hangi ƙarshen su. Sabida rashin gyara micizai da beraye da ƙudan zuma sun cika wajen. Sannan kuma ga duhuwa daga can cikin lambun ta rufe ko'ina. Lallai ba wani kuskure zakai ba idan kace za'a iya samun ƙananun namun dawa a wajen irinsu dila da botorami.
Haka suka ci gaba da zagaya tsohon gidan nasu wanda anan suka taso suka girma. Wannan shi ne gida na farko da suka sani a rayuwarsu. Lallai baza su manta dashi ba kuma baza su manta da wanda ya basu shi ba.
A hankali jiki a sanyaye suka dawo cikin gidan inda suka tarar tuni an gyara musu ɗakin kwanciyar su. Kai tsaye suka shiga cikin ɗakin da suke kwana su uku sanda suna yara.
Abu na farko daya fado musu shi ne sanda wani saurayi mai jan gashi ya fara kawo musu ziyara a wannan gida. Hankalinsu ya tashi a lokacin. Harma suna tunanin gidan yankan kai aka kawo su. Sai bayan shekaru suka gano cewa ashe wannan saurayi mai jan gashi ɗan'uwa ne kuma amini abin yadda. Lallai ya taimake su.
Cokali ya buɗe akwatin adakar da suke ajiye kaya inda yayi arba da kayan su na sawa wanda suka siya sama da shekaru goma sha da suka gabata. Nan take hawaye ya ciko idonsa. Yana ƙoƙarin goge hawayan ya fuskanci ashe ita ma Nusi kukan take yi. Lallai suna jin ciwon rabuwa da wannan muhalli wanda suka taso aciki a lokacin da basu da komai a duniya.
Cokali ya miƙe ya ƙarasa wajen da take ya rungumeta dukkanin su suna hawaye.
Can bayan tsahon lokaci suka koma cikin gidan inda suka tarar tuni an gyara musu ko'ina. Hatta tafkin daya bushe yanzu ya cika da ruwa garai-garai babu alamun ƙura ko gansakuka. Nusi ce ta fara yin wanka sannan shima Cokali yayi. Daga bisani suka koma cikin gidan suka fara tattaunawa akan abinda zasu yi. Ba jimawa Giwa ta kammala girki tunda dama tuni sarkin Bai ya siyo kayan miya. Aka kawo abinci da abin sha aka girke a gaban Nusi da Cokali. Suna cin abincin Giwa tana yi musu fifita kuma tana basu labarai masu saka nishadi da kwantar da hankali. A kofar ɗakin kuma Inyaya, Barilu, Shísu da sarkin Bai suna tsaye suna gadi. Lallai babu wani mahaluki daya isa ya kawo musu harin bazata komai shirinsa.
A haka dai suka kwana acikin wannan gida mai tsohon tarihi kafin da safe Nusi da Cokali su shirya su saka sabbin kayan da suka siyo jiya a kasuwa sannan suka nufi hanyar fita.
"Nusi-ya," Giwa tasha gaban Nusi ta durkusa, "anya kuwa kina ganin dake da Cokali kun isa basai mun raka ku ba? Nifa ina jin tsoron abinda zai iya faruwa."
Nusi tayi murmushi tare da miƙar da ita ta tsaya a saitin ta. "Babu komai, Giwa, lafiya zan dawo muku. Kuma ko babu komai ai ina tare da ɗan uwana." Ta yiwa Cokali inkiya da ido wanda ya ɗagawa Giwa ɗan yatsa tare da ƙifta mata ido. Nan take fuskar Giwa ta cika da kunya ganin kallon da Cokali yayi mata. Ba shiri ta juya ta koma cikin gidan cikin kunya. Nusi ta yamutse fuska ta kalli Cokali kallo mai cike da tambaya. Shi kuwa Cokali kawai ɗauke kai yayi ya kalli gefe. A haka sukai sallama sannan su biyu suka nufi hanyar fita daga garin Khan.
Bayan sun fita sai suka ɗauki hanya zuwa babban birnin Maikironomada. Tafiyar sa'a biyar ce. Amma bayan sun isa saida suka shafe sa'a guda a layin dake bakin garin kafin su shiga. Damma har yanzu Cokali yana da katinsa na shedar zama ɗan ƙasar da abin yafi haka wahala. Ita ma Nusi tana da nata katin to amma a matsayinta na yar majalisa tana nuna katin zai jawo magana wadda kuma ba haka suke so ba.
Dogeyen gine-ginen garin sukai musu sallama. Kusan kowanne gida zaka samu yana da benaye akalla uku. Kuma an gina su ne da zallar dutse saɓanin gidajen da suke garin Khan da sauran garuruwan. Babu cunkosu a garin kuma komai a tsare yake acikin ka'ida. Koda ace Nusi bata taɓa zuwa garin ba neman fadar garin baza tayi mata wahala ba. Ballantana wannan bashi ne karo na farko data zo wannan gari ba. Sabida haka cikin ƙasa da awa guda ta isa filin dake gaban fadar garin inda anan sarki Maikiro'Abbas yake rayuwa.
Tuni yamma ta kawo kai sanda suka isa. A lokacin an gama zaman fada na ranar. To amma a wannan lokaci ne Nusi tayi amfani da katinta na majalisa ta shiga har cikin fadar. Kai tsaye ta tsallake kowa duk kuwa da yadda dogarai suke nema su shiga tsakaninta da karagar.
"Tsaya cak a inda kike kiyi bayanin mai ya kawo ki." Babban dogarin sarki ya daka mata tsawa. Cokali ya harare shi sannan ya ɗora hannunsa akan littafin sa marubutan farko cikin shirin kota-kwana. Dogarin yana ganin haka shima ya ɗora hannunsa akan takobinsa ya harari Cokali.
Nusi bata damu ba. Tsayawa tayi cikin yadda dakai ta fuskanci sarkin dake kan karagarsa ta ce, "suna na Nusi KIL-ZANKI. Nazo ne akan zancen ɗan uwana Armad Wilbafos."
Comments
Post a Comment