Skip to main content

410-414

 A duk sanda ya taru sai kaga ya ƙara haske. Har wani jaja-jaja hasken ya fara yi, irin launin gemun kwamandan. Ba jimawa kwamandan ya tare hasken guri guda. Ƴar ƙaramar ƙawanya ta bayyana a tsakiyar hannayensa. 


A nasa ɓangaren yarima Umaru tara ƙanƙara ya fara yi guri guda yana ƙoƙarin tare harin. 


Ki'jinu ya ɓace ya bayyana a gaban yarima Umaru. Hannu ɗaya yasa ya danna hasken cikin kirjin yarima.


A lokaci guda yarima Umaru ya daki ƙasa da ƙafarsa. Dai-dai ƙasan ƙafarsa bangon ƙanƙara ya bayyana. A tare wasu bangwayen biyar suka bayyana: ɗaya a kowacce kusurwa ɗaya kuma a sama. Kafin Ki'jinu ya ɗauke hannu daga kirjinsa akwatin ƙanƙara ya rufe su ruf duk su biyun. 


Abu na ƙarshe da Armad ya gani shi ne rubutun da yarima Umaru yake yi da yan'yatsunsa akan iska. Tabbas wannan sabon yare ne wanda Maikiro'Abbas ya kirkira. Su kaɗai suka san harufan da ake rubuta shi. Duk iyakacin bin kwakkwafin Armad ya kasa gane mai suke rubutawa. 


Acikin akwatin ƙanƙarar Ki'jinu da Umaru suka fuskanci juna. Kankarar tana bada haske kamar an kunna fitila. Ki'jinu yana tsaye yana kada kafa guda daya, shi kuma Umaru ya jingina a jikin bangon ƙanƙarar yana hutawa.


Bayan ɗan lokaci yarima umaru ya kawo hannunsa kusa da idonsa yana kallo kamar mai nazarin wani abu a jikin hannun. ya dubi Ki'jinu ya ce, "naji labarin fasahar ka amma ban taɓa ganin ta sai yau."


Kwamanda Ki'jinu ya ɓata rai. 


"Wannan dabarar ɓata lokacin da kake yi baza tayi aiki ba," inji kwamandan. 


A fusace ya jefi bangon dake kusa dashi da gashi guda. Gashin ya koma haske ya shanye ƙanƙarar. Yayi sauri zai fice amma kafin ya fice wani sabon bangon ya bayyana ya maye gurbin wancan. 


"Haha... duk rabin-rabin dakika wata ƙanƙara take bayyana," inji yarima Umaru. " Indai an shigo cikin wannan akwati to babu fita daga cikinsa. Ina baka shawara ka nemi guri ka zauna domin kai da ganin waje sai lokaci ya cika. Fata na a kashe Dul'Ururu kafin lokacin."


Ya rufe zancensa da dariya. Sannan ya nemi guri a gefe ya zauna. Kwamanda Ki'jinu yayi azama wajen harbin ƙanƙarar. A kowanne lokaci zai gama da ita amma kafin ya fice wata sabuwar ta bayyana. Daga waje kuwa ƴan kallo kawai ƙara suke ji basu san mai yake faruwa ba. 


A ƙasa inda su Armad suke yarima Najunanu ne ya matso kusa da Armad ya tsaya domin suyi magana. 


"Zaka iya mantawa da Ki'jinu har zuwa nan da wani lokaci," inji yarima Najunanu. 


Armad ya kalleshi cikin tambaya. Yanayin yadda yariman yake magana hankali kwance yasa Armad tunanin baya tsoron halin da yarima Umaru zai shiga acikin akwatin ƙanƙarar. Armad yana ganin watakila yarima Umaru zai bukaci agaji saboda kowa yasan girman muƙamin kwamanda. 


"Kada ka damu da Umaru," inji Najunanu. "Fasahar Ki'jinu tana da sharri amma kuma tana da iyaka. yana iya juyarda komai ya taɓa izuwa haske na tsahon lokaci. Ya danganta da yawan yadda yayi amfani da ita. Yana gajiya ƙarfin fasahar yana raguwa. Umaru yasan haka shi yasa ya sashi acikin littafin ƙanƙara. Bazai iya fita ba har sai sanda ƙanƙarar ta daina sabunta kanta. Kuma ya riga ya mayar da jikin Umaru haske saboda haka bazai iya cutar dashi ba a yanzu."




Armad ya gyaɗa kai cikin fahimta. Wato ta wani ɓangaren fasahar Ki'jinu bata da hatsari sosai tunda dai baza ta kashe ka ba. To amma hatsarin ta shi ne za ka kasa yin komai har sai jikin ya dawo dai-dai. A irin wannan yanayi idan Ki'jinu ya samu sa'a ya harbi Maikiro'Abbas kaga Ururu sunyi nasara. Haka Maikiro'Abbas yana ji yana gani za'a kashe mutanensa amma kuma baza ka iya yin komai. 


"Fasahar ta dace da Salsa," Inji Armad. "Yawancin salsan dana taɓa karo dasu sunfi amfani da fasahar da zata kare iyayen gidansu daga sharri maimakon fasaha mai karfin hari."


Najunanu ya gyaɗa kai alamun amincewa. 


"Ki'jinu da Binan da Diwani duk salsan Dul'Ururu ne," inji Najunanu. "Binan shima fasahar kariya ce dashi. Yana sarrafa ƙarfe mara iyaka kuma ta haka yake tare hare-haren kamar irin yadda ya tare Ais-bol ɗin sarki ɗazu. Wanda zaka kula dashi shi ne Diwani. Bashi da fasahar kare kai amma al'amudinsa shege ne. Ba'a taɓa samun wanda ya tsira da ransa ba bayan yayi karo dashi. Duka ɗaya yake tarwatsa tsauni. Baya jin tsafi ko sihiri. Akwai bayanai da yawa akan al'amudin amma a zahiri babu wanda yasan tayaya yake aiki."


Armad ya ƙara lissafa abokan gabarsu sannan ya lissafa kansu. A zahiri kowane ɗaya daga cikin abokan gabarsu yakai muƙamin sarkin jinzidal ko kuma ya kusa. Dole suna buƙatar shiri idan zasu yi nasara.


"Yurba kuma turɓaya yake sarrafawa," inji Najunanu. "Zan iya cewa nasan hare-harensa guda uku. Da wanda yayi amfani dashi ɗazu wato turɓayar gini, da kuma turɓayar fenti da turɓayar badala. Ƙasa ce kala-kala, kowacce akwai yadda yake amfani da ita. Ance a yau da Dul'Ururu zai mutu Yurba zasu bawa muƙaminsa. Saboda haka ka lura dashi musamman saboda zafinsa. Ban taɓa zuwa sashin ikwatora ba,mai zaka gayamin a game da Ƙaraiƙisu da kuma wancan mai kama dakai ɗin?" Ya nuna Ayubu.


Jin sunan Ayubu yasa Armad ya cije haƙora. Yau zai nunawa butulu iyakar su.


"Ayubu yana da fasahohin gidan Wilbafos. Yana iya amfani da zaren izza da kuma Negrinki duk irin nawa. Kada kaje kusa dashi, ni zanyi maganinsa. Ƙaraiƙisu a iya sanina shi ne mafi ƙarfi a sashin ikwatora. Sarkin sune kamar yadda Kuyurussa'ayi yake sarki a duniyar kudu da arewa. Jinsin bakaken samudawa ne kuma tunda nake ban taɓa ganin wani abu ya fasa fatarsa ba. Ni ban taɓa faɗa dashi ba amma ance baya amfani da izza. Duk ƙoƙarin gano zaren izzarsa da nake yi har yanzu ban gano ba. Watakila hakan ne baya amfani da izza, watakila kuma irin sirrin ku yake amfani dashi."


Armad ya ɗan kaurara jimlarsa ta karshe domin Najunanu ya fahimce shi. Shi kuwa yarima kawai murmushi yayi. 


"Ba wani babban abu bane," inji Najunanu. "Izzar ta cikin littafin marubutan farko take wucewa. Hakan yana da amfani wajen hana farar laya aiki akan mu, sannan kuma yana taimakawa wajen rubutun da muke yi. Ina da tabbas zuwa yanzu kaga yadda kannena sukai hare-harensu kuma ka kula da cewa muna da Yaren mu da muke rubutu dashi."


Armad ya gyaɗa kai. Tabbas sai ya samu lokaci ya koyi sirrin wannan babbar ƙabila. Musamman tunda yanzu sun haɗa kai. Koda yake ta bayyana daman tun can kansu a haɗe yake. Shi ne dai bai sani ba.


Wata ƙara ta ƙara tashi mai cike da haske daga cikin akwatin ƙanƙarar da Ki'jinu da Umaru suke ciki. Ga dukkan alamu har yanzu Ki'jinu ƙoƙarin fitowa yake yi. Amma bai samu nasara ba.


"Yarima," inji Armad. Najunanu ya juyo ya dube shi. "Ka jira anan, ina zuwa."


Kafin yarima ya tambayi ina zaije Armad ya kira ɗalasimi.


"Aiban'shisu!"


A ɓangaren Dul'Ururu kowa idonsa na kan akwatin ƙanƙarar da Ki'jinu ke ciki. 


"Haaa...?" Kwamanda Diwani ya wangale baki tare da nuna akwatin. "Wancan yaron yayi jarumta kuma yayi ganganci. Har gobe jikinsa bazai dawo dai-dai ba."


Binani ya gyaɗa kai gami da shafa kai. "Ƙoƙari yake ya rufe Ki'jinu da ƙanƙarar tsahon lokaci. Sai dai ƙarfinsa bai kai yayi hakan ba. Wai mai yasa yara suka fiya gaggawa a rayuwa?"


Diwani yayi ajiyar zuciya yana jimanta abun a rai kaman yana tausayi umaru. 




A gefe Yurba na zaune yayi shiru bai ce musu komai ba. Shi kuwa Dul'Ururu yana tsaye a gaba yana lissafi. Dubunnan sadaukai suna tsaye a ƙasa suna jiran umarninsa. Har yanzu dashi da Maikiro'Abbas basu bawa rundunarsu damar su afka ba. Zaka iya cewa gwada juna kawai ake yi kafin a fara ainihin abin. 


"Aiban'shisu!"


Kwatsam matattakala ɗaya daga cikin matattakalar dake ƙasan wajen da aka ajiye Fatima ta ɓace. A gurbinta ƙasa ta bayyana. Armad ne akai zare da takobi. 


Abinda ya bawa Armad mamaki shi ne ba'a nan yayi niyyar sauka ba. Yayi niyya ya canja dai-dai wajen da aka ajiye Fatima, tare da Fatiman, ya musanya su da wajen daya baro. A wani salo irin na fasahar zaran gwana da Bihanzin yayi amfani da ita a wancan zamani ya ceto Nostaljiya. Sai dai kuma Ururu sun koyi darasi daga abinda ya faru a wancan lokaci. A yanzu sun saka kafi wanda ya hana Armad yin hakan. Hakan ne yasa maimakon Armad ya dira a tsakiyar gadon inda Fatima take sai ya faɗo kan matattakala. 


Kallo ya koma sama. Makiya suka ankare da Armad.


"Armad?" Inji wani saurayi daga cikin mayaƙan Ururu. 


A lokacin kowa ya juyo ya kalli Armad. Zaiyi wuya ka gane waye acikinsu ya fara cewa, "ga Armad a sama!" Amma cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya ɗauka. "Ga Armad a sama!"


Shi kuwa Armad hankalinsa yana kan yadda zaiyi ya karya kafin dake tsare da Fatima, ko kaɗan bai damu da hayaniyar dake faruwa a ƙasa ba.




"ARMAD!" Inji Fatima murya na rawa. A hankali ta haɗiyi yawu mai ɗaci. "Armad!" Ta ƙara kwala masa kira, hawaye na zuba daga idon ta.


Armad ya ɗaga ido ya kalli mahaifiyarsa zaiyi magana amma kawai sai yaji hawaye a idonsa. Ya runtse ido hawayen ya koma domin dai bazai bari abokan gaba suka kukansa ba. A lokaci guda yana ƙoƙarin gano abinda zai gaya mata ya kwantar mata da hankali. 


Bayan ɗan lokaci ya rufe baki ya haɗiye kalamansa. Babu kalma guda da zata bayyana abinda ke ransa. Gwanda kawai ya bari sai ya kubutar da ita tukun.




Ya dawo da hankalinsa kan mayaƙan Ururu. Mutun nawa zai rage acikinsu. Da ace zai iya karya kafin dake tsare da mahaifiyarsa to da hakan zaiyi, sai dai shi kafi banzan abu ne. Duk ƙarfinka dole sai ka san sinadarin da akayi shi dashi kafin ka iya karya shi. Idan abu aka binne to dole sai ka tone shi kafin ka karya kafin. Idan kuma kafi ne irin na aljanu to shi ma dole sai ka kashe aljanun kafin ka karya shi. Akwai kafi na itacen kuka da ganyen magarya da kitsen ƴaƴan aljanu, irin wannan kafin yana da wuyar sha'ani domin karyashi sai matsafin asali. Sanin hakan da kuma kasancewar Armad bai san irin kafin da sukai amfani dashi ba yasa ya ajiye maganar karya kafin a gefe. 


Amma kuma ko kaɗan bai haƙura ba. Tashi sama yayi ya juye izuwa walkiya. A hannunsa na dama ya samar da Negrinki, a hannunsa na hagu ya samar da takobi.


"Mara rabon ganin badi ya ƙaraso."


Jin haka sai ya ƙara fusata mutane irinsu ƙaraiƙisu. 


A kuma gefe kwamanda Diwani ne yaja numfashi. "Hmmm... Nima lokacin da zan ɗana yazo."


Fuskarsa tana nuna ya gaji da zama ya miƙe. Yasa hannu ya dauki al'amudin dake gefensa ya juyo ya fuskanci Armad. Sai dai kafin yayi wani abu ya hangi Ƙaraiƙisu ya tashi. Ga dukkan alamu baƙin basamuden bazai iya jira ba. Tsalle yayi akan iska ya bayyana a gaban Armad. 


"Ance kune izza," inji ƙaraiƙisu yana dariyar mugunta. "Nuna min na gani. Sunana Ƙaraiƙisu."


Kafin ya rufe baki ya kawowa Armad tunkuyi da ƙahon dake gaban goshinsa. Kai kace rago ne abin layya. 


Armad ya kauce a hankali. Kana gani kasan ya raina saurin da Ƙaraiƙisu yake tafiya dashi. Acikin ransa lissafi yake wane irin hukunci ne yafi dacewa da Ƙaraiƙisu. Shin ya jefa shi duniyar Negrinki kamar yadda yayi wa Haruta da yan ruwa? Ko kuma ya sare kansa a huta da girman kansa. A take Armad ya yanke shawarar ya halaka ƙaraiƙisu. Ko babu komai hakan zai rage musu wahala a yaƙin. 


"Ɗorawa Abada!"


Armad ya kira babbar fasaharsa ta takobi. A wannan lokaci Armad bai yadda ya rage komai ba. Idan zaiyi nasara to dole yana bukatar dukkan ƙarfinsa. 


Taurari suka bayyana akan takobin. Cikin sauri irin na Kaban'shisu ya bayyana a gaban Ƙaraiƙisu. Tuni takobinsa ta riga isa wuyan basamuden. 


Ƙaraiƙisu baida ikon kaucewa saboda abu biyu: girman jikinsa wanda ya bawa Armad wajen dazai sara da yawa da kuma kasancewar Armad ya fishi sauri.  


Negrinkin Armad ta isa ƙirjin ƙaraiƙisu ta shige ciki, takobin kuma ta samu naman wuyansa ta sara. Duk kwarin basamuden sai da takobin ta fasa fatarsa ta yanka ta shiga ciki. Wani wawakeken rami ya bayyana. A tsakiyar ƙirjinsa hasken Negrinki ne yake tashi. 


Ɓangaren Ururu suka fara salallami. A bangaren Maikiro'Abbas kuwa babu komai sai shewa. 


A dai-dai wannan lokaci mutun-mutumin Armad ne yake bawa Nusi haƙuri kada tabi Armad. Zaka iya cewa Armad fakar-idon Nusi yayi ya tafi ya barta. Sannan kuma ya samar da mutun-mutumi dan ya hanata binsa kasancewar yasan tabbas idan baiyi hakan ba to binsa zata yi. 


"Nace ka matsa na tafi," Nusi ta daka masa tsawa.


Mutun-mutumin ya ƙara buɗe hannu yana tare mata hanya. 


"Minti biyar kaɗai aka halicce nayi," inji shi. "Kuma a wannan minti biyar ɗin aiki na kurum na hanaki binsa. Saboda haka sai inda ƙarfina ya ƙare."


Nusi ta fara kiran ɗalasimai a fusace zata gama dashi. A lokacin Cokali ya dafa kafaɗarta.


"Yar'uwata, mai zai hana mu jira mu gani. Akwai alamun Armad yana da shirinsa. Haka kawai bazai kai kansa halaka ba yana sane."


Nusi ta kalli Cokali zata yi magana amma nan take ta fasa. Wato yanayin fuskar Cokali babu wasa aciki. Kana ganin kasan bazai bari ta tafi ba sai dai idan kashe shi zata yi. Kuma bashi kaɗai ba. A dai-dai wannan lokaci Nazára, Asifu, Jan doki, Giwa, Inyaya, Shísu, Barilu, da sarkin Bai duk sun taso. Babu inda zasu bar Nusi ta tafi indai suna numfashi. Nusi ta cije haƙora. Babu yadda ta iya haka ta juya taci gaba da hango Armad daga nesa. 


A dai-dai wannan lokaci Negrinkin Armad ta kasa zuƙe jikin ƙaraiƙisu zuwa duniyar Negrinki. Hayakin Negrinkin ya rufe kirjinsa amma kuma ya kasa cimmasa. 


Kamar akwai wani shingen kafi da yake hana Negrinkin taɓa fatar ƙaraiƙisu. Armad wanda ke kusa yasan abin ba haka bane. Wato Negrinkinsa ta taɓa jikin ƙaraiƙisu. Amma matsalar shi ne taki aiki. Kamar zaka iya cewa sirrin tsafi da sihirin dake jikin Negrinkin wanda yasa take yin abinda take yi na zuƙe jikin mutun zuwa wata duniyar ya kau. Gashi dai Negrinkin tana nan amma kuma bata aiki. 


Cikin mamaki Armad ya saki Negrinkin ta taɓa ƙarfen dake gefen ƙafarsa. Nan take ƙarfen ya ɓace ɓat. Wato dai har yanzu Negrinkin tana aiki, kawai dai a jikin ƙaraiƙisu ne baza tayi aiki ba. 


"Ga dukkan alamu baka sani ba," inji Ƙaraiƙisu. "Ai kayan izza ko sihiri ko tsafi basa aiki a kaina. Idan baka yadda ba zaka iya gwadawa."


Ya buɗe hannu ya bawa Armad kirjinsa ya sara. A dai-dai lokacin Armad ya lura cewa ciwon da yaji masa a wuya tuni ya warke. Kada a manta ɗorawa Abada hari ne mai kama da dauwamammen sara. Baya warkewa kuma baya ƙarewa. Kamata yayi ace har yanzu jini yana zuba daga ciwon.


Armad yaja da baya. Abinda aka sani shi ne fasaha mai amfani da izza. Haka tsarin sihiri yake tun a Farkon Lokaci. Hakan ne ya ɗora ma'abota izza akan ragowar bil'adama wanda basu da izza. Amma ace an samu halitta wadda bata jin izza... Hakan kamar ya saɓa da al'ada ne. Kuma hakan lallai wata barazana ce ga duk wani mahaluki dake amfani da sihiri. Lallai ya kamata masu sihiri da masu izza suyi kama-kama su halaka wannan halitta wadda bata dace da al'ada ba. 


"Jiki na yana karya sihiri kowane iri ne," inji Ƙaraiƙisu cikin alfahari. 


Armad ya shiga lissafi. Watakila Inara shi ne mafi dacewa daya fafata da Ƙaraiƙisu. Inara yana iya sarrafa fasaha ba tare da izza ba. Har yanzu zaka iya cewa Inara bai gama gane yadda abin yake ba sosai kuma bai kware ba, amma lallai da taimakon Negrinkinsa yana iya yin hakan. Inara baya tare dasu saboda haka meye mafita?


"Mashiyal-Atu!"


Armad ya kira fasaha. A take tsayuwarsa ta canja. Sirrin ilmin wannan fasaha ya fito daga cikin waƙar maƙabarta dake cikin jinin sa ya shiga ƙwaƙwalwarsa. A hankali ya fara gane yadda zaiyi. 


Hannu, kafa, gwiwar hannu data kafa. Ko'ina acikin wannan wurare yana iya kai duka yayi illa ta musamman. Sirrin wannan fasaha shi ne ƙara ƙarfin dukan da kayi da jikinka. 


Ya bayyana a saman Ƙaraiƙisu inda ya sauke masa gwiwarsa a kafaɗa. Wani ƙarfi mai ɗauke da nauyi na musamman ya shiga kafaɗar Ƙaraiƙisu. Ƙaraiƙisu yayi jim a tsaye tsahon dakiku sannan ya farfaɗo. 


"Babu izza acikin dukan ka," ya gayawa Armad cikin mamaki. "Haha... Wannan ita ce irin fasahar da nake nema na ware dantse na."


Armad ya ƙara sauke masa ɗaya gwiwar akan ɗaya kafaɗar. kafin sanda jikin Armad ya haɗu da nasa sai kaga jikin ya juye izuwa dutse. Karfin harin ya ninka kansa sau bakwai. Babu ciwo a waje amma Armad yana da yaƙinin illa yake yi ta ciki. Shima Ƙaraiƙisu ga dukkan alamu ya fuskanci hakan. Amma kuma abin mamaki murna yake yi yau ya samu abokin karawa. 


Armad ya dunkule hannu ya daki cikinsa da ƙarfin tsiya har sai da yasa yaja da baya yayi tari ya tofar da jini. Tabbas wannan fasaha ta illa ta ƙaraiƙisu ta ciki. Asalin sunan mai fasahar Subiyunu Wilbafos. A lokacin da ƙabilar Wilbafos suka shahara a fannin izza, a lokacin da babu abinda yake ci in ba izza ba, a lokacin Subiyunu ya dage wajen nunawa duniya ya kamata a samu canji. Ya samar da sirrin fasahar da yake amfani da karfin dantse kaɗai. Idan ka daki mutun sai yaji kamar dutse ka buga masa, sannan kuma dukan ba iyakacin waje yake aiki ba, a'a, har cikin yake shiga ya illa ta kayan ciki. Ban da kuma ninka karfin dantsen mutun da fasahar take yi sau bakwai. Subiyunu ya ɗan bada gajeren tarihinsa a ƙasan fasahar. A cewarsa har ya mutu wannan fasaha tasa daya sawa suna Mashiyal-Atu bata samu karɓuwa ba. Kuma bai ga laifin gidan Wilbafos ba a lokacin tunda kowa yana ganin bata lokaci na kawai. Waye zai tsaya amfani da ƙarfin dantse bayan zai iya bautar da aljani ya samar da wuta da ƙanƙara?


Subiyunu ya mutu yana da shekaru ɗari da ashirin na haihuwa. Kuma ya bar fasaharsa acikin waƙar maƙabarta ba tare da yayi tunanin za tayi amfani ba. Amma kuma tayi a lokacin da babu wata fasaha da zata yi aiki sai ita. Ko a dai-dai wannan lokaci ruhin Armad yana tare da Subiyunu acikin tsarin ruhinsa yana koya masa wannan fasaha. Watakila hakan ne yasa suna faɗa da Ƙaraiƙisu yana ƙara nuna kwarewa wajen sarrafa fasahar. 


Sai dai kuma duk da jinin da Ƙaraiƙisu ya tofar bai daddara ba. Abin haushi dariya ma yake yi. 


"Ka cancanci nayi faɗa dakai," inji Ƙaraiƙisu da babbar murya. "Ba kamar wadancan yaran Ikenga ba. Da zarar ka tare izzarsu sai su kasa komai. Amma kai na daban ne, lallai zanji daɗin faɗa dakai kafin na halaka ka."


Ƙaraiƙisu ya tashi sama ya kawowa Armad duka. Armad ya kauce da fasahar Kaban'shisu. Iska mai ƙarfi ta tashi sama kamar guguwa. 


Armad ya sullube ta ƙasa ya kawo masa duka da hannu. Ƙaraiƙisu baiyi ƙoƙarin kaucewa ba. Sai dai yayi ƙoƙarin kai masa duka. 


Armad ya kauce a nutse. Wato daɗin abin shi ne Armad ya ninkashi sauri sau da yawa saboda haka zaiyi wuya ya same shi. Amma ba dan haka ba da duka ɗaya zai iya tarwatsa ƙashin mutum. Lallai ƙaraiƙisu da jinsin Ururu ne, ko kuma ace yana iya amfani da fasahar saɓani da an shiga-uku. 


Sai dai kuma a dai-dai sanda Armad ya kaucewa dukan ƙaraiƙisu, a lokacin Diwani yayi amfani da idonsa na Ururu ya saki Saɓani. Ta haka ya bayyana a dai-dai inda Armad zai bayyana ya kuma kawo masa duka da al'amudi. 


Armad bai tashi ankarewa ba sai da ya bayyana a kusa da al'amudin. A lokacin bashi da damar kaucewa. Musamman duba ga irin gudun da al'amudin yake yi. Akwai yiwuwar Armad zai iya shanye dukan al'amudin komai ƙarfinsa, amma kuma zai iya yi masa rauni. Kuma abin shi ne yanzu aka fara yaƙin. Babu dabara ace Armad ya bari an fara taɓa shi tun yanzu. Amma tayaya zai kauce bayan al'amudin sauran kiris ya cimmasa? Sannan kuma kamar ƙara masa gudu ake yi. 


Maimakon kaucewa sai Armad ya dunkule hannu ya daki al'amudin da fasahar Mashiyal-Atu. Kara mai kashe kunne tayi sama kamar ƙarfe ya daki ƙarfe. Abin mamaki sai Armad yaji hannunsa yana shigewa cikin al'amudin kamar roba. Kafin ya ankara ya shanye masa hannu. 


"Nayi kamu!" Inji Diwani yana lashe baki kamar tsohon maye. 


Armad yayi ƙoƙarin janye hannunsa amma ya kasa. Kamar hannun zai cire baki ɗaya. A hankali ya fuskanci cewa al'amudin ya zama wani yanki na hannunsa ta yadda ko taɓawa akai yana ji. Ta baya kuma Ƙaraiƙisu ya kawo masa duka. Yayi ƙoƙarin yin tsalle amma sai yaji hannunsa wanda al'amudin ya riƙe ya ƙara nauyi. Babu alamun zai sake shi kuma duk bayan dakika nauyi yake ƙarawa. 


"Al'amudina na musamman ne," inji Diwani. "Bari na nuna maka wani abun."


Al'amudin ya fara girma yana ɗaukan zafi. Cikin ƙanƙanin lokaci Armad yaji kamar wuta ake kunna masa. Daga hannun sai dukkanin jikin ya ɗauka. Ya juyarda hannun izuwa walkiya amma duk da haka bai daina ji ba. A dai-dai wannan lokaci ƙaraiƙisu ya ƙaraso. Jikin Armad ya juye izuwa walkiya amma sai da yaji saukar hannun ƙaraiƙisu a wuyansa. Yana dubawa yaga wajen ya dawo tsoka. Wato duk inda Ƙaraiƙisu ya taɓa sai kaga walkiyar ta ɗauke. Tsafi baya zama guri ɗaya da baƙin basamuden. 


A lokaci guda al'amudin bindiga yayi da hannun Armad kamar an tashi nakiya. Armad ya buɗe baki zaiyi ƙara saboda zafi amma ya cije.


Fatima wadda ke kusa tana kallo ita ce tayi ihu na razana. Tana kallo ana nema a halaka mata ɗanta. 


Al'amudin ya ƙara haɗa jikinsa sannan ya ƙara yin bindiga. Ƙaraiƙisu kuwa wanzuwa yayi yana dukan Armad ta sassa daban-daban na jikinsa. Kasancewar Armad yaƙi faduwa ko ya galabaita sai ya ƙara musu azama. Kafin lokaci mai yawa sun yiwa Armad jina-jina. Suna ji a ransu dole ya kamata ace Armad ya saduda saboda haka suka ɗan tsaya suna kallonsa. 


Armad yayi shiru yana kallon ƙasa. Filin yaƙin yayi tsit ana sauraro. Ɓangaren Ururu suna jira suga ya faɗi su fara shewa. Ɓangaren Maikiro'Abbas kuwa jimami suke yi. Musamman Nusi wadda hankalinta yafi na kowa tashi.


A hankali Armad ya motsa. Ɗaga hannu yayi ya goge jinin dake bakinsa. 


"Kunyi min lamba," inji Armad yana dariyar irin ta mugunta. "Kuyi sani irin wannan lamba nake buƙata na gwada sabuwar fasaha ta."


Kafin kowa yayi wani abu armad ya haɗe hannayensa guri guda. Ba tare da furta wani ɗalasimi ba sai kawai ya fara kumbura. Cikin rabin dakika ya fashe. Wata ƙara mai rikitarwa ta tashi. Ƙasa tayi girgiza ta dare. Ƙura ta turnuke. Babu abinda kake ji sai tsagewar iska da ihun bil'adama.


Sai da aka shafe tsahon mintuna sannan ƙura ta lafa. Zaka iya cewa kowanne bangare kallo suke yi su ga mai ya faru. Shin Armad ya mutu? Shin meye ya jawo wannan ƙara mai kama da nakiya?


Abu na farko daya fara bayyana shi ne Ƙaraiƙisu acan gefe cikin rusasshen gini. Kallo guda zaka fuskanci jifa akayi dashi yaje ya daki ginin ya fasa ya shige ciki. Matattakalar da Armad yake tsaye akai kafin fashewar nakiyar tayi daga-daga. Iyakacin ɓangaren gadon inda yake da kafi shi kaɗai ne ya rayu. Maruta yana kusa da Fatima ya runtse ido yana nazarin abinda ya faru. Daga ƙasa a ɓangaren dama wasu mutun uku na tsaye a rufe cikin baƙin haske. A ɓangaren hagu kuwa an nemi sarki Han'ibal an rasa. Iluru ya juye izuwa jikinsa na basamude amma duk da haka jini yake zubarwa ta baki. Ayubu yana tsaye fuska a murtuke amma babu alamun ciwo a jikinsa. A gaban Suwainah da Ibraham Nil wasu mata ne cikim shirin yaƙi a zube a ƙasa. Yawansu yakai goma. Basa motsi ko kaɗan kuma ba abin mamaki bane ace sun mutu duba ga irin bakin da fatarsu tayi.


Wato dai a takaice gaba ɗaya teburin Ururu ya rikice, babu wanda yake cikin nutsuwa. 


Armad babu shi babu alamunsa. Amma kwamanda Diwani yana kwance a ƙasa a wajen da sukai faɗan baya ko motsi. 


Bayan tsahon dakiku ƙaraiƙisu wanda ke kwance cikin rusasshen gini ya fara motsi. Da fari kawai dube-dube yake yi kafin ya samu ya tashi zaune. A hankali ya ɗaga hannunsa sama yana kallo. Cikin fushi yayi ƙoƙarin miƙewa amma ya kasa. Ba shiri ya dawo ƙasa kan gwiwowinsa, jini yana zuba daga bakinsa. 


"Ɗan iska, yayi min illa," inji Ƙaraiƙisu fuska cike da marmarin yaƙi. 


Diwani har yanzu bai motsa ba. Sai dai taskar ruhi ta bayyana a saman kansa tana kewaya shi. Watakila warkar da ciwon dake jikinsa take yi.


Daga gefe kuma sifofin mutun uku dake rufe da baƙin haske sun bayyana. Sarki Dul'Ururu ne da kwamanda Yurba da kwamanda Binani. Suna tsaye babu alamun rauni a jikinsu amma fuska a murtuke. Idanunsu suna kan abokan gaba. 


Daga can sama Maruta yana tare da Fatima wadda bakinta yake a buɗe ya kasa rufuwa. 


"Lallai ɗan nan baki bashi da tsoro," inji Maruta. "Yayi mana lamba ya kuma shammace mu."


Fatima har yanzu bakinta a buɗe yake ta kasa rufewa tana kallon ƙasa. 


Maruta yaja dogon numfashi ya girgiza kai.


"Amma duk da haka mune da nasara."


Fatima bata ce masa komai ba. Watakila mamakin abinda ya faru ya hanata bashi amsa, ko kuma bata da lokacinsa. 


A ɗaya ɓangaren hatta Maikiro'Abbas bakinsa a buɗe yake. Kowa ya wangale baki yana kallon abinda ya faru. Wasu sun fahimci abinda ya faru, wasu kuma kawai kallo suke yi suna mamakin yadda Armad yakai kwamanda da Ƙaraiƙisu ƙasa a lokaci guda. 


Wani abin al'ajabi dake faruwa shi ne mutun-mutumin Armad dake tare da Nusi ya kasa tsayuwa. Yana durkushe kan gwiwowinsa yana mataguguwa da hannu a kai. 


"Nace mai yake damunka," Nusi ta tambaye shi cikin damuwa. A lokaci guda ta ɗora hannu akansa. Tafin hannunta yana taɓa kansa ta ɗauke da sauri kamar ta taɓa wuta.


"Zafi," inji mutun-mutumin. "Zafi nake ji."


Nan fa kowa ya tsaya yana kallon ikon ALLAH. Abin yana da ban mamaki musamman duba ga cewa har yanzu babu wanda yaga Armad. 


Cokali ya janye Nusi daga kusa da mutun-mutumin domin kada ta rungume shi cikin tausayi. 


Har yanzu dai kowa jiran bayani yake yi. Zaka iya cewa mutane kaɗan ne suka fuskanci abinda ya faru. 


Minti guda da faruwar hakan wani guri kusa da mutun-mutumin Armad ya fara haske. Armad ne ya bayyana a gurin. Mutun-mutumin ya dubi Armad a fusace.


"Sauran kiris ka kashe ni," inji mutun-mutumin. "Kasan zafin da naji. Ai ka gayamin kace ga abinda zaka yi."


"Naji," inji Armad. Ya kada hannunsa mutun-mutumin yabi iska. Su Nusi suka matso kusa suna neman bayani. 


"Mai ya faru?"


"Ina ka tafi?"


"Ya akai kaci galaba akan su?"


"Yanzu meye abin yi?"


Tambayoyi da dama suka fara kwaranya daga mutanen da suka kewaye Armad.


Amsa ɗaya Armad ya basu kafin ya wuce gaba wajen Maikiro'Abbas.


"Yaƙi da saura. Bamu yi nasara ba."


Suka bishi da kallo. 


Yana ƙarasawa ya tsaya a kusa da sarkin ya ce, "sun karɓi sakon."


"Hakan yana da muhimmanci," inji Maikiro'Abbas. "Su fuskanci manufar mu. Dul'Ururu bai shirya mutuwa a wannan yaƙin ba. Hakan shi ne zai bamu nasara akansa."


Armad yai tsam yana tunani. Dama ance yaƙi ɗan zamba ne. Idan ka tsorata abokin karawarka tun kafin a fara to kamar kayi nasara ne. Zaka iya cewa Armad yayi nasara duba ga irin firgici dake kan fuskokin mayaƙan Ururu dake ƙasa.


Kada mai karatu ya manta a idanun wannan mayaƙan babu wanda yakai girman kwamanda. Ace an buge su lokaci guda dole a karayar musu da gwiwa. 


Kamar yana ƙarawa ciwon gishiri sai Armad yasa fasahar kaurara magana ya fara da cewa, "mayaƙan Ururu, Ni Armad Wilbafos ina yi muku kashedi. Kunga dai abinda ya faru da manyanku. Idan kuna so uwarku ta haifi wani to ku tsaya. Idan kuwaa take a yanzu kuka juya kuka tafi to nayi muku afuwa."


Yana rufe baki yaji kaifafan idanun Dul'Ururu akansa. Ya ɗaga ido suka haɗa ido. Tsananin kiyayya ce acikin idanun Dul'Ururu. Idanun sun ƙara baƙi sun ƙara muni. Wata wuta ta fara ci a saman kansa dai-dai inda taskar ruhinsa take. Babban abinda yake kona masa rai shi ne kowa yana ganin abinda ke faruwa a faɗin duniya. Tuni manyan gidajen jaridu irin su Aminiya suka hallara domin yaɗa abinda ke faruwa. 


Armad yayi masa dariya. 


A gefe guda Maikiro'Abbas ɗaga hannu yayi ya bada umarni. Yafi kyau suyi amfani da damarsu su yi illa kafin Ururu su farfaɗo daga alhinin da suke ciki.


"Iyalan maikironomada," inji Maikiro'Abbas. "Fatima taku ce. Ku kubutar da ita, ku halaka Ururu."


Nan fa waje ya rikice da ihu da shewa. Aka fara kiran suna. 


"Maikiro!"


"Maikiro!!"


"Maikiro!!!"


Zaka iya cewa a wannan lokaci kwarin gwiwar mayaƙan yakai makura. Sun manta da yawan da Ururu suka fisu. Cikin karaji da kuwa suka afkawa Ururu. 


A dai-dai wannan lokaci Ƙaraiƙisu ya motsa a hankali. Da kaɗan da kaɗan ya fara ganin haske. Idanunsa suna dawowa dai-dai ya fuskanci acikin ginin cin abincin kyaftins na mayaƙan Ururu ya faɗo. Abin mamakin shi ne wannan gini yana can ƙarshen Filin jiri ne daga jikin katanga. Idan zai iya tunawa a ƙasan gadon da aka ajiye Fatima sukai faɗa da Armad wanda kuma a tsakiyar filin yake. To mai ya kawo shi nan?


A hankali ya miƙe tsaye inda ya hango Fatima durkushe akan gadon. Ga Dul'Ururu a tsaye tare da kwamandu, ga Maruta a kusa da Fatima, ga kuma su Han'ibal a gefe. Daga ƙasa wajen da sukai faɗan kwamanda Diwani ne kwance kamar gawa. 


"Hmmmm..." Yaja dogon numfashi. "Wannan yaron ne ya cilloni kenan."


Da wannan ya taka ya nufi kan gadon. Yana tafiya mayaƙan dake ƙasa suna kallonsa suna kus-kus. 


Akan gadon kuwa kwamanda Diwani ya samu dama ya buɗe ido. Taskar ruhin dake kewaya shi ta dawo kansa ta tsaya. 


"Dul'Ururu," inji Diwani daga inda yake kwance. "Zan iya kashe Armad?"


"Ɗari bisa ɗari," inji Dul'Ururu. 


Koda jin haka sai wata dariyar mugunta tazo gefen bakin Diwani ta tsaya. Ya tashi zaune ya riƙe kansa tsahon minti guda har sai da Ƙaraiƙisu ya ƙaraso. Ya miƙe tsaye suka fuskanci juna.


"Bani da sani akan abubuwan nan naku na izza," inji Ƙaraiƙisu. "Mai yaron can Armad yayi?"


"Ruhinsa ya fasa," inji Diwani. "Fasaha ce wadda ake amfani da ita wajen kunar-baƙin-wake. A ka'ida duk wanda yayi amfani da fasahar to shima mutuwa zaiyi domin ruhinsa zai tarwatse yayi daga-daga." Diwani ya ɗaga ido ya hango Armad a inda yake tsaye. Acikin idanunsa akwai tsana da marmarin yaƙi. "Amma ga dukkan alamu Armad ya samo hanyar dazai iya amfani da wannan fasaha ba tare da ya mutu ba."


"To amma tayaya fasahar zatai aiki a kaina," inji Ƙaraiƙisu. "Ko ka manta ni fasaha bata aiki akaina."


"Hmm. Amma ai kana da ruhi, ko?" Inji Diwani. "Wannan ba fasaha bace a zahirin kalmar. Kamar kace ya mayar da ruhinsa nakiya ne kawai. Saboda haka ko fasaha tana aiki a kanka ko bata yi idan nakiya ta fashe zata ji maka ciwo. Abinda ya faru kenan. Ka godewa ALLAH da ruhinka baiyi daga-daga ba, ko ni dana mallaki fasahohin kare ruhi manya sai da naji a ruhi na."


"Ah," Inji Ƙaraiƙisu baki buɗe. "To ko shi yasa dana tashi bana gani sosai kuma har yanzu nake jin jiri?"


Diwani ya gyaɗa masa kai. 


Ƙaraiƙisu ya murtuke fuska. 


"Wato so yayi ya kashe ni?" Inji Ƙaraiƙisu. "To ai kuwa ya rubuta takardar mutuwarsa. Diwani, ni zan kashe yaron nan."


Diwani ya girgiza kai.


"A'a, Ƙaraiƙisu, ai abin kunya zai zamar min idan aka bar filin nan ban aikatashi ba. Dole ina bukatar na ɗauki ruhinsa na ƙara a taskar ruhi na."


Jin haka Ƙaraiƙisu ya bata rai.  


"Haka ma kace!"


Suka shiga kallon-kallo da Diwani. Daɗinta duk su biyun samudawa ne. 


"Kaga tsaya," inji Diwani. "Duk abu ɗaya muke nema kuma a ɓangare ɗaya muke. Bana jin akwai amfani muyi faɗa akan wazai kashe shi. Mai zai hana mu kashe shi a tare, in yaso bayan ya mutu sai ka barmin ruhin nayi tsafi dashi. Kaga dai kai bana jin kana buƙatar ruhinsa. Ya kace?"


Ƙaraiƙisu yayi shiru yana tunani. Tabbas haɗa ƙarfi da wani wajen yaƙar wani ya saɓa da tsarinsa. Shi kaɗai yake fita yaƙi kuma yayi nasara. To amma kamar yadda kwamandan ya faɗa akwai buƙatar kada su yaƙi juna. Su fara kaɗe Armad, in yaso daga baya ya dawo kan kwamandan ya nuna masa kuskurensa. 


Idan muka dawo ɓangaren su Armad zamu ga tuni mayaƙansu sukai fitar burtu suka afkawa mayaƙan Ururu. Ratar dake tsakaninsu bata fi ƙafa ɗari biyar ba. Kafin su ƙarasa Dul'Ururu ya ɗaga hannu ya bawa dubunnan mayaƙansa umarni. 


"Kune Ururu," inji Dul'Ururu. Kamar hakan daya faɗa ya wadatar baya buƙatar ƙarin bayani sai ya nuna gaba. "Ku afka musu."


Comments

Most Popular

456

Aiban'zhisu Babban karni!  ************* Tunda Armad ya riga yazo nan to fa bazai koma ba sai ya ɗauki mahaifiyarsa.  "Aiban'Zhisu, babban ƙarni!" Ɗalasimin yana barin bakinsa, jikinsa ya ɗau hasken walkiya. Tun daga kai har ƙafa babu inda baya tartsatsin walkiya. A lokaci guda walkiyar ta fara juyawa tana zagaya jikinsa tana yin sama. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta dunkule tayi sama ta fasa ta cikin gajimare ta fice ta ƙara lulukawa sama. Ta wuce Hajarul Ururu ta shiga doron ƙasa na farko tayi sama ta haɗe da gajimare. A lokaci guda da walkiyar take yin sama, wata walkiyar ce ta fita daga jikin Armad tayi ƙasa ta fasa doron ƙasa ta uku data huɗu data biyar data shida data bakwai ta shige ƙarƙashin ƙasa. Sannan kafin wani yayi wani abu sai walkiyar ta fashe zuwa ƙawanyar walkiya dubu a sama doron ƙasa ta farko, sannan wata ƙawanyar dubu a ƙasa doron ƙasa ta bakwai. Kowacce ƙawanya acikin dubun ta rabe zuwa ƙawanya ba adadi suka fantsama suka shiga duniya. Cikin rabin dakika...