Skip to main content

349-352

 Ɓangaren Dul'Ururu


Doron ƙasa na biyu


Dul'Ururu yana zaune akan karagarsa yana fuskantar Haruta da Maruta. Kallon farko zakaga alamun sarauta da ƙanshin mulki a kowanne sako da loko na dakin. Akwai tambarin babbar masarauta a jikin bangon ɗakin da kuma hannun kujerun da su Haruta suke kai. Ga kambun sarauta akan Dul'Ururu wanda yake nuna tabbacin shi ne sarki bisa doron ƙasa ta biyu. 


"Kamus ya kira," Dul'Ururu ya ce. "Armad ya shiga gadar zare."


Haruta da Maruta suka yamutse fuska. 


"Ya shiga gadar zare kuma?"


Dul'Ururu ya gyada kai. "Ya shiga. A yanzu haka da muke wannan magana yana ciki. Bamu san meye ya kai shi ba kuma har yanzu bamu san mai ya faru dashi a wata guda daya wuce ba. Amma Kamus ya ce a Melmusa aka gano shi."


"Wai anan ya ɓuya duk tsahon wata gudan nan amma duk abinda Nusi tayi bai bayyana ba?" Inji Haruta.


"Babu tabbas," inji Dul'Ururu. "Bamu sani ba. Amma akwai ƙanshin gaskiya a hakan domin kuwa babu inda bamu duba ba amma bamu ganshi ba. Melmusa gari ne da yayi kama da wajen ɓuya."


"To yanzu meye abin yi?" Inji Maruta. "Muna da babban yaƙi a gaban mu. Baza mu bari hatsaniya ta taso daga gadar zare ba."


Dul'Ururu yayi ajiyar zuciya sannan ya miƙe daga kan kujerarsa ya fara kai-komo acikin dakin. 


Bayan ɗan lokaci Haruta ya mike tsaye. "Zan je naga mai yake faruwa. A mace kake son sa ko a raye?"


"A mace," inji Dul'Ururu. "Duk abinda kake buƙata a yayin wannan aiki ka ɗauka."


Ɓangaren Armad


Bayan kira ɗaya-biyu babu wanda ya amsa, Armad ya miƙe tsaye. Ankwar dake jikinsa bata hana shi motsi ba. Hasalima yana tashi tsaye ya fizge ankokin ya zubar a ƙas. Sannan yaja da baya ya taho da gudu ya bangaji ƙofar ɗakin. Ƙofar ta fice daga jikin ginin. Ginin ya fara tsagewa yana darewa saboda ƙarfin fitar ƙofar.


Masu gadin dake wajen sun ankare da abinda ke faruwa to amma kuma kowa acikin su jimamin tunkarar Armad yake yi.


Shi kuwa Armad ko a jikinsa. Ya samar da manya-manyan ƙawanya na walkiya guda biyu domin su haska masa hanya, sannan ya fara tafiya taku ɗai-ɗai. Kamar yadda ya gani a sanda ya shigo akwai jama'a acikin ɗakunan dake jere a kusa dashi. Suna ji suna gani amma babu mai cewa uffan acikinsu. Armad yaci gaba da tafiyarsa yana tunkarar matattakalar dake gabansa. Ruwansu ne su biyo shi ko kuma su zauna su ci gaba da rayuwa a wannan guri. Shi dai burinsa ya tashi hankalin gadar yadda zai janyo hankalin Ururu kansa. Ko babu komai hakan zai bawa su Nusi damar hawa doron ƙasa ta biyu ba tare da tangarda ba.


Kafin Armad ya ƙarasa matattakalar masu gadi aƙalla ashirin sun sha gabansa ɗauke da makamai iri-iri. Babu neman ba'asi sukai kansa da mugun nufi.


Armad ya dunkule hannunsa na hagu. Walkiya ta fara bulbula daga jikinsa tana ambaliya. 


"Hannun Aradu!"


Walkiyar mai siffar hannu tayi kansu gadan-gadan. Kan kace kwabo ihu ya fara tashi. Dole aka bawa Armad hanya ya wuce ya hau kan matattakalar ya fara tafiya yana yin sama. Har ya kusa kai wa ƙarshen matattakalar ya jiyo kofofin dake rufe da fursunonin sun buɗe da ƙarfin tsiya. Ya waiwayo a hankali domin yaga mai ke faruwa. Abin mamaki babu kowa a wajen amma an buɗe kowacce ƙofa. Fursunonin dake ciki sun fara fitowa waje. Babban abinda ya bawa Armad mamaki shi ne dukkaninsu shi suke kallo. Babu wanda ya taɓa gani acikinsu ballantana ace wani abu ya taɓa haɗa su, to amma kuma yadda suke kallonsa akwai damuwa aciki.


Yana cikin wannan tunani yaji wata ƙara a saman kansa. Wata ƙatotuwar katanga ta baƙin ƙarfe ta bayyana ta tare hanyarsa ta zuwa hawa na gaba. 


Kafin Armad ya gama fahimtar mai ke faruwa fursunonin sun afka masa. Babu makami a hannunsu amma yadda sukai kururuwa kana gani kasan sun yadda su sallawantar da rayukansu indai zasu kai Armad ƙasa. 


Ko kaɗan Armad bai damu da yawansu ba. Ko da ace suna da makami kuma sun fi haka yawa abin bazai daga masa hankali ba. To amma meye dalilin da yasa zasu fara kawo masa hari? Bai san su ba, ballantana ace ya taɓa yi musu wani abu. Kuma zai yi wuya dukkan mutan cikin wajen ace haushin sa suke ji a lokaci guda. Ƴan dakiku kadan da suka wuce yake kokarin ceto su, tayaya za'ace duk maƙiyan sa ne?


Yana cikin tunani suka ƙaraso wajen da yake tsaye. Akwai manyan sadaukai masu babbar izza acikinsu. Watakila hakan ba abin mamaki bane tunda duk wanda Ururu zasu kawo wannan guri su ɓoye dole akwai dalili. A baya kaɗan shugaban masu gadin wajen mai suna Kamus ya bayyana cewa a wannan guri aka ajiye Deniz Ururu. To amma hakan bai tsorata Armad ba. Babu wanda ya kai matakin izzar sa a wurin. Shugabansu Dul'Ururu shi Armad yake hari. Da wannan tunani Armad ya fidda Zaren Mayu domin ya ladabtar dasu. Abin mamaki hakan bai rage musu gudu ba. Hasalima babu wata alama dake nuna cewa an taɓa izzar su. 


"Zaren Manyan Mayu!"


Shi ma a banza. 


"Zaren Mutuwa!"


Bawai izza ce basu da ita ba, a'a, suna da ita. Kuma zaren yana aiki a kansu domin duk wanda ya taɓa zaka ga izzarsa ta ɓace. To amma hakan baya rage musu ƙarfi. Mutun ɗaya kacal da Armad ya sani wanda yake iya sarrafa fasaha ba tare da izza ba shi ne Inara. Kuma shima sabida yanayin Negrinkinsa shi ne yasa yake da wannan dama. Babu yadda za'ai ace dukkan mutanen dake kulle a wannan guri sun zama haka. 


Wani abun haushi shi ne Armad baya so ya kashe su. Domin tabbas yana ganin kamar ba'a cikin hayyacin su suke ba. Idanun su sun rufe. Basa ganin komai sai hauka.


Ba jimawa suka ƙaraso inda Armad yake suka hau shi da duka da naushi.


Bayan ɗan lokaci ana wannan dambarwa, Armad yayi tsaki. Ƙarfin tsakin ya tada wata yar ƙaramar guguwa wadda tayi jifa dasu gefe guda. Ya ɗaga hannunsa sama ya kirawo ɗalasimi:


"Sanyin babban sihiri!"


Ƙanƙarar sanyin babban sihiri ta ƙanƙare ƙafafunsu. 


A wani salo mai ban al'ajabi duk da haka ƙoƙarin kawo masa wafta suke yi. Wasu acikinsu suna ƙoƙarin ɓamɓare ƙafarsu daga ƙanƙarar. Wasu kuma suna ƙoƙarin cire kafar baki daya. A lokacin Armad ya tabbatar basa hayyacin su. Tabbas akwai wata babbar izza daga sama dake sarrafa tunanin su.


Armad na tsaye yana lissafin yadda zaiyi maganinsu ba tare da ya kashe su ba ya jiyo murya daga ƙasan matattakalar. "Baka da wata hanya ban da ka kashe su. Dukkansu suna ƙarƙashin fasahar Kamalar-ruhi. Basa gani basa ji sai sun cika umarnin da aka basu. Wannan umarni kuwa ba wani abu bane illa su kashe ka."


Koda muryar tazo nan a zancenta sai ta fito fili inda Armad zai iya ganinta. Dattijo ne wankan tarwaɗa sanye da rigar fursuna fara mai layi-layin yalo. 


"Suna na Shata Kil'zanki," inji dattijon. 


Armad ya juyo ya fuskance shi a nutse. "Shata?" Armad yana ji kamar ya taɓa jin sunan amma kuma bazai iya tuna a ina ba. "Waye yayi amfani da fasahar Kamalar-ruhin?"


Shata ya kaɗa kafaɗa. "Ban san waye ba, amma ina ganin fasahar ta daɗe. Zaka iya cewa tunda suka shigo cikin wannan gada take jikinsu."


"Kai ya akai bata aiki a kanka?" Armad ya tambaya.


Dattijon ya ƙara gyaɗa kafaɗa. "Saboda ban daɗe ba."


"Kwananka nawa anan?" Armad ya tambaye shi.


"Sati biyu."


Armad ya yamutse fuska. Sati biyu kacal? 


Shata ya nuna fursunonin dake sanƙame cikin ƙanƙara. "Yaya zakai dasu? Zaka kashe su ne ko kuwa?" 


Armad yayi shiru yana lissafi. Mutanen dake gabansa suna kawo masa hari basu da laifi. Mutane ne kamarsa wanda Ururu suka zalunta suka kulle a kurkuku. Sabida haka baya son ya kashe su. To amma kuma idan bai kashe su ba bazai samu hanyar wucewa sama ba tunda dai bashi da wata hanya dazai karya fasahar Kamalar-ruhin dake aiki a kansu. 


"Babu wata hanya da mutun zai bayyana a saman wannan gada ba tare yabi ta matattakalar nan ba?" Armad ya tambaya.


Shata ya girgiza kai. "A iyakacin sani na babu. Da akwai da baza ka ganni anan ba. Amma yadda naji kana magana tabbas kana da hanyar fita." Yayi shiru yana kallon Armad yana jiran amsa. Bayan ɗan lokaci Armad bai ce komai ba sai ya yamutse fuska. "Ko? Ai kana da wata dabara a ƙasa ko?"


Armad ya girgiza kai. "Akwai dabarar data wuce mu banƙara ta karfi mu wuce?" 


Shata yayi shiru yana kallon Armad bai ce komai ba. Bayan kimanin dakika goma ya fashe da dariya. "Wato shigowa kayi babu wani lissafi? Amma a haka kake tunanin zaka fita har ma ka fitar damu? Hahha..."


Armad ya yamutse fuska. Dole yasan akwai hanyar fita. Babu wata gada ko kurkuku da ba'a yiwa hanyar fita. 


"Maimakon dariyar da kake kamata yayi ka kawo shawara," inji Armad.


"Ni ban ce ina da shawara akan hanyar fita ba," inji Shata. "Kuma ai sai an gwada akan san na kwarai. Watakila idan ka saka ƙarfi ka banƙara a bamu hanya."


Armad najin haka ya juya a fusace ya tunkari katangar ƙarfen dake sama wadda ta raba shi da hawa na gaba. Ya daga hannu ya saukar mata da hannun aradu. Dunkulen walkiya ya daki ƙarfen, ƙara tayi sama. Hayaki da ƙura suka turnuke. Matattakalar tayi girgiza kamar zata karye. Bayan komai ya lafa Armad ya ɗaga ido yana tunanin zai ga hanya amma katangar ƙarfen tana nan a tsaye ko gwarzane babu. 


Armad ya ƙara saukar mata da hannun aradu sau uku a jere amma katangar tana nan a tsaye babu alamun canji a jikinta.


"Zaren Mayu!"


"Zaren Manyan Mayu!"



"Ɗorawa Abada!"


Dukkan wannan hare-haren babu wanda yayi akan wannan katanga. Armad ya tashi sama yaje kusa da katangar ya taɓa ta da hannunsa. Jikinta sanyi kalau. Duk wannan hare-haren da Armad ya saukar ko zafi bai sa ta ɗauka ba. 


A hankali ya juyo ya dubi Shata wanda ke tsaye yana kankare farcensa da tsinke.


A wannan lokaci da dama daga cikin fursunonin da Armad ya ƙanƙare sun gama fasa ƙanƙarar sun kuma fito waje. Babu wata fargaba suka ƙara afkawa Armad. 


Shata ya tafa hannunsa. Wani sirri boyayye ya bayyana akan iska. Sautin tafin ya juye izuwa baitin waƙa. Duk wanda ya saurara sai kaga ya fadi ƙasa yana minshari. 


"Indai kana so su daina bin ka to sai dai ka koma cikin ɗaki ka zauna," inji Shata. "Akwai sirri na musamman da yake aiki a wannan guri. Bana jin zaka iya wucewa indai ba babban sarki Kuyurussa'ayi bane ya yadda ka wuce ba."


Armad ya yamutse fuska cikin rashin fahimta. "Mai kake nufi da hakan?" 


Shata yaja ɗan numfashi ya fara bayani. "Kuyurussa'ayi Ururu yana da duniya ta musamman daya gina. Duk ƴaƴansa suna da fili a wannan duniya. Kai wasu ma har gidaje ne dasu. A wasu lokutan Kuyurussa'ayi yakan yanko wani sashi daga duniyar sa ya kawo shi wannan duniya tamu. Kamar misalin gadar zare. Gaba ki ɗayan ta da abinda ke cikinta wani yanki ne daga cikin duniyar Kuyurussa'ayi Ururu. Babu wani iko da yake aiki anan sai nasa. Da izzar ka da fasahar ka da zaren izzar ka duk baza suyi komai ba sai da izinin sa. Kai bari kaji, ba wai fasahar bakaken idanuwa ce tasa Ururu suka ci galaba akan Eyriyon ba, wannan fasahar duniya ita ce tasa Ururu sukai nasara."


Armad yayi shiru yana saurare. Duk yadda akai Shata bana yau bane. Har ace yasan abinda ya faru a wancan zamani kuma yana bayanin sa kamar yau ya faru.


Shata yaja dogon numfashi sannan ya ɗora da cewa, "indai ba fasahar duniya ce da kai ba to ina ganin babu wata fasaha da za tayi aiki a wannan wuri. Iyakacin daɗewarka iyakacin yadda duniyar zata shige ka. Idan muka ci gaba da zama anan to akwai lokacin da za'a kai dole mu karbi umarnin Kuyurussa'ayi Ururu muyi biyayya. Yadda kaga wannan fursunonin suna kawo maka hari babu dalili to kai ma wataran haka zaka kai wa wani hari babu dalili."


Armad ya ɓata rai. Bazai taɓa bari haka ta faru. Faɗa ma ɓata baki ne. Kuma abinda Shata bai sani ba shi ne yana da fasahar duniya wadda ya samu daga Negrinkinsa. Hasalima duk manyan fasahohinsa irin su Zaren Babbar Mutuwa da ita suke amfani. 


Shata ya nuna fursunonin dake kwance ƙasa suna sharar barci ya ce, "sun kusa tashi. Ni dai zan koma daki. Kai ma zan baka shawara ka koma ɗakinka ka zauna. Watakila idan ka nutsu ka tuni wata hanyar mai ɓullewa."


Da wannan ya juya izuwa dakin sa. Armad kuwa waje ya nema ya tankwashe ƙafa. Tuni ya fahimci cewa dole yana buƙatar ya gyara fasahar Negrinkinsa. To amma hakan bawai shi yake nuna bai isa ba. Har yanzu yana ji komai rintsi komai tsanani zai iya jada Dul'Ururu ko Ikenga ko Bihanzin. Sabida haka abin kunya ne ace ya kawo kansa gadar zare kuma ya maƙale. Kamar yadda Ikenga ko Bihanzin ko Dul'Ururu baza su maƙale ba shima bazai maƙale ba. Meye amfanin halwar izzar daya shiga a duniyar aljanu?


Cikin ƙuduri da babbar aniya Armad ya fara fito da Negrinkinsa tana ambaliya daga jikinsa. Cikin kankanin lokaci ta cika ko'ina. A wani salo na fitar da sabuwar fasaha Armad yayi ƙoƙarin janyo duniyar Negrinkinsa ta shigo cikin wannan duniya domin ta kashe duniyar Kuyurussa'ayi. Hakan bata faru ba, amma kuma a dai-dai ɗan wannan taƙin da duniyar Negrinkinsa taso ta shigo cikin wannan duniya sai da wani babban canji ya faru. Duk wani abu da Negrinkinsa ta taɓa sai kaga ya ɓace ɓat. Har da wannan katanga wadda ta tsare masa hanya, wadda a baya taƙi jin komai.


Armad ya mike ya nufi hawa na gaba. Shata kuwa juyowa yayi yana kallonsa fuska cikin mamaki. Armad yana jiyo shi yana cewa, "abin mamaki! Lallai yaro cike kake da abin mamaki."


Armad ya wuce mataki na gaba. Yana isa ya daki ƙasa da ƙafarsa. Sanyin babban sihiri ya shiga ta karkashin ya ƙanƙare dukkan kofofin dake rufe da fursunonin. Babu wani fursuna da zai samu damar fitowa ballantana ma ya kawo masa hari. Sannan yayi sama zuwa mataki na gaba, sannan na gaba. Ko waiwaye ba yayi.  



Abu kamar wasa sai da ya haura matakai goma. Da ma'aikatan da masu gadin da Kafin dake wajen da fursunonin duk babu wani abu da yake yi masa waigi. Idan ka hange shi daga nesa zaka ga wani gungumen aljanin mutuwa ne wanda baya jin bari. Duk inda Armad ya ratsa sai dai kaga ja da fari. Ba jimawa ya iso ƙarshen matattakalar wato hawa na goma sha biyu. 


Katon fili ya tarar saɓanin yadda ragowar matattakalun na ƙasa suke a cunkushe. Daga can ƙarshen filin runduna ce a ajiye tana kallonsa. Ko baka tambaya ba kasan dama shi suke jira. 


Armad ya taka ɗai-ɗai izuwa gaban wannan runduna. Tun daga mataki na farko Shata yake binsa a baya. Armad bai tambaye shi dalilin da yasa yake binsa ba, shi kuma bai yi masa bayani ba. A haka suka isa gaban wannan runduna wadda aƙalla yawansu yakai dubu biyar. Suna tsaye kan layi sahu-sahu riƙe da makamai.  



A bayan rundunar akwai ƙatoton gadon aba'i a ajiye. Daga saman gadon aba'in wani dattijo ne a durkushe akan gwiwowinsa sanye da ankwa. Mutun biyu na tsaye a bayan wannan dattijo riƙe da takubba na fille kai. Daga bayansu kuma kanin babban sarki Kuyurussa'ayi ne wato Haruta yake tsaye tare da Kamus. Idan ka lura sosai zaka ga dattijon da ake shirin kashewa ba wani bane illa Farfesa Zaikid, kakan Armad Wilbafos. 



Ganin Zaikid a wannan waje ya saɓa da abinda Liman Umaru ya gayawa Armad. A cewar limamin Fatima da Zaikid suna tare a doron ƙasa ta biyu kuma tare za'a yanke musu hukunci. Amma kuma ga Zaikid a gadar zare. 


Abinda ya kawo Armad gadar zare shi ne ya tada hankali tayadda zai ɗauke hankalin Ururu daga kan Nusi da tawagarta. To amma ganin Zaikid dole ya canja lissafi. Babu tayadda za'ai Armad ya tafi ya bar kakansa a wannan waje. 


Haruta ya miƙa hannu ya karɓi bututun maganar dake hannun ƙamus ya fara jawabi, "Armad Wilfabos, sannu da zuwa. Tunda kazo wannan mataki da wuri haka bazan kashe maka gwiwa ba. Ga Zaikid a kan gwiwowinsa." Ya kalli agogon dake hannunsa sannan ya ɗago kai ya ƙara duban Armad yace, "na baka awa sha-takwas. Idan zaka iya kashe sadaukai na dubu biyar dake gaban ka, ka kashe Kamus, sannan ka kashe ni duk acikin wannan awa goma sha takwas to zan baka Zaikid. Idan kuwa bazaka iya ba to kuwa lallai a gaban idon ka zan saka takobi na sare masa kai, sannan kuma kaima na sare ka domin tuntuni ka riga ka kafircewa manya kamar iyayenka da kakanninka."



Armad na tsaye tare da Shata Kil'zanki suna sauraron jawabin Haruta. A wannan lokaci tuni Armad ya riga ya gama yanke shawarar hukuncin da zaiyi. Ba tare da neman shawara daga Shata ba ya tashi sama akan iska ya samar da takubba guda biyu a hannunsa sannan ya afkawa wannan runduna. 


A ɗaya ɓangaren rundunar kukan kura sukayi suka afka masa. Sai dai kuma kafin su haɗu suka ji kiɗan garaya yana tashi akan iska. Dolen rundunar suka tsaya suna dube-duben daga ina wannan kiɗa yake tashi. Shi kansa Armad tsayawa yayi yana dubawa domin yaga daga ina kiɗan yake. A zahiri wannan kiɗa na musamman ne, zaka iya cewa koda mutun ya taɓa jin kiɗa to fa ba irin wannan ba. Akwai wani salo na musamman wanda yake sa kiɗan yana shiga har cikin tsakiyar kwakwalwar masu saurare yana yi musu illa. Kai kace wani umarni ne yake sauka daga sama


Idanun Armad suka kai kan Shata Kil'zanki. Idan mai saurare zai iya tunawa wannan mutum mai suna Shata shine wanda muka gani acan baya lokacin da Fatima takai masa ziyara, harma mukaji cewa yana daga cikin mutanen da suka rubuta waƙar maƙabarta. Kuma a wancan lokaci munga yadda ya tara mutane masu yawan gaske yana kaɗa musu garaya suna saurare. To a yanzu ma Shata waƙar yake ba tare ya kula da cewa a filin yaki yake ba. 


Sannun a hankali kiɗa yaci gaba da tashi. Kwatsam sai wasu daga cikin wannan sadaukai suka fara layi. Idanunsu suna rufewa suna yarda makamansu gefe suna faduwa ƙasa. Kan kace kwabo sai kaga sun fara minshari. Cikin kankanin lokaci sama da mutum ɗari acikin wannan runduna sun je ƙasa. Koda ganin haka sai Armad ya gyaɗa kai alamun jinjina sannan ya wuce gaba izuwa gadon aba'in da Zaikid yake kai ya bar Shata da wannan runduna. Ko babu komai alamu sun bayyana cewa Shata shi kaɗai zai iya ja da wannan mutum dubu biyar.


Duk da wannan abubuwan dake faruwa Kamus da Haruta suna tsaye ko gezau basuyi ba. Kana gani kasan a fuskokinsu babu alaun tsoro ko baƙin ciki, kai kace basu damu da wannan sadaukai dubu biyar da Shata yake ƙoƙarin gamawa dasu ba. 


Suna tsaye Armad ya iso dai-dai inda suke. Tsalle ɗaya tak ya haye kan gadon aba'in sannan ya miƙa hannu domin ya ceci Zaikid. 


Ratar dake tsakanin hannunsa da Zaikid bata fi kamu biyu ba, amma hannunsa ya kasa ƙarasawa. Bawai riƙe shi akayi ba, a'a, kawai ya kasa motsa jikinsa ne. Armad ya ɗaga kai yaga Kamus a kansa. Armad yasan Kamus shi ne shugaban gadar zare. Amma banda wannan bai san wani abu a kansa ba. Bai san wace irin fasaha Kamus yake amfani da ita. Bai san wane irin aljani Kamus yake dashi ba. Waɗannan abubuwa sune suka sa dole Armad yayi taka-tsantsan domin dai baisan dawa yake faɗa ba. Abu na farko da Armad ya fara yi shine juyar da jikinsa zuwa walkiya sannan ya rufe shi da Negrinki. Abin mamakin hakan bai sa ya motsa ba, kai kace kusa aka saka aka kafe shi akan iska.


Kamar masifar da Armad yake ciki bata isa ba, Kamus ya dora a gabansa ya kawo masa suka da mashi. Yana ganin tsinin mashin ya tabbatar idan bai motsa ba ƙarshensa yazo. 


"Saif-Al-Barzak!"


Kawai gani akai hannun Kamus dake rike da mashin ya guntule yayi sama. Jini yayi feshi ƙasa. A lokacin Armad ya samu ya motsa. Koma wane asiri Kamus yayi masa ya karye. Kafin Kamus ya ankare Armad ya bayyana a kusa dashi ya cafi wuyansa ya ɗaga shi sama da hannu ɗaya sannan ya buga shi da ƙasa. Armad ya ɗaga hannunsa na hagu ya saukar masa da hannun aradu. Walkiya tana ambaliya ta daki fuskar Kamus. Daga nesa babu abinda zaka gani sai hayaki. 


Armad yaci gaba da dukan Kamus har sai da ya daina motsi. A lokacin Armad ya lura cewa hannunsa wanda yake dukan Kamus dashi yana zubar da jini. Sannan kuma saɓanin yadda idan jikinsa yana walkiya baya jin zafi a wannan lokaci wani mugun zafi yake ji a hannayensa dai-dai inda jinin yake zuba. Duk da haka Armad bai tsaya da dukan Kamus ba. Yana dukansa zafin yana ƙaruwa, jini yana zuba. Zaka iya cewa yadda jini yake zuba daga fuskar Kamus shima haka jini yake zuba daga hannunsa da fuskarsa. Idanun Armad sun rufe ballantana ya tsaya ya tambayi kansa dalilin da yasa jini yake zuba daga fuskarsa. Domin dai akwai mamaki tunda babu wanda ya dake shi a fuska. 


To amma abin bai tsaya a fuska. Kawai sai duk wata kofa a jikin Armad ta fara zubarda jini. Duk inda ka kalla jini ne yake zuba. Da kyar ya iya daga Kamus ya juya wajen Zaikid. Babu abinda yake so illa ya tsinke wannan ankokin dake jikin kakan nasa domin ya ceto shi. Amma kuma abin da kamar wuya, yana miƙewa ya fara gani dishi-dishi, jiri yana ɗibansa. Watakila jinin daya zubar ne yasa yake jiri. To amma meye dalilin zubarda jinin?




Kafin ya ƙarasa Zaikid ya fara rabe masa. Daga mutum ɗaya ya koma biyu. Daga nan sai ya fara gani uku-uku. Yayi taga-taga zai faɗi ƙasa, da kyar ya miƙa takobinsa ya tare kansa. 


Yana tsaye acikin wannan hali yaji muryar Haruta a kunnensa. "To yanzu ya kake so ayi kenan, Armad? Ka riga ka ɗebi dafi daga wajen Kamus. Naji ance alluran da yake amfani dasu sun jiƙu a tsumi. Saboda tsabar dafin da yake jikin su ko aljani idan suka soka to karshensa kenan. A gani na banajin zaka rayu daga wannan dafi." 


A lokacin Armad ya fuskanci mai yake faruwa: dafi Kamus yasa masa a yayin faɗan. Zaka iya cewa wannan shi ne karo na farko da Armad yayi arba da ma'abocin fasahar dafi. A ilmin izza irin waɗannan fasahohi sun fi saura sharri. Domin koda kafi ƙarfin mutum, dafin sa zai iya aiki akan ka. 


Haruta ya ƙaraso inda Armad yake. Tsayawa yayi yana kallonsa yana girgiza kai, kai idan baka san waye Haruta ba sai kace tausayin Armad yake ji. Maimakon Haruta ya zare takobi kawai sai ya ɗaga ƙafa ya kawowa Armad duka. Cikin layi Armad yasa ƙafa ya tare, sannan a wani salo na kwarewa ya kai wa Haruta sara da takobi biyun dake hannunsa. Amma duk wannan dabara ce kawai dan ya ɗauke hankalinsa. Asalin halin ta baya ya taho. Saif-Al-Barzak ta zagaye ta baya tana niyyar tsarge Haruta gida biyu.


A ɗan wannan taƙin takubba biyu suka bayyana: ɗaya ta gaba ɗaya ta baya. Ta bayan ta tare takobin Saif-Al-Barzak ta gaban kuma ta tare takubban Armad guda biyu na Dorawa Abada. A lokacin guda Haruta ya ɗaga ƙafarsa ta hagu ya ƙara dukan Armad da ita. Dukkan abinda ya faru cikin rabin dakika ya afku. Kafin Armad ya ankara tuni ƙafar Haruta ta sake shi. Ƙarfin dukan yayi cilli dashi zuwa can ƙasan matattakalar. 


Abubuwa da dama sun faru a ƴar wannan gajeriyar fafatawa. Na farko dai wannan shi ne karo na farko da wani ya iya tare takobin Saif-Al-Barzak. Sarkin jinzidal Iluru ko ganin ta baiyi ba a lokacin da tayi masa aiki. Amma Haruta ya ganta kuma harma ya iya tare ta. Kuma yanayin yadda ya tare ta shi ne abinda yafi konawa Armad rai. Ko juyawa baiyi ba. A yadda Armad ya lissafa Saif-Al-Barzak zata iya tare dauwamammen sara. Hasalima wannan shi ne dalilin da Armad ya samar da ita. Shin hakan na nufin takobin Haruta tafi dauwamammen sara kenan? 


Armad bai samu damar amsa wannan tambaya ba. Yana dira a ƙasa wani baƙin jini ya fito daga bakinsa. Kana gani kasan wani abin ya fashe acikinsa. Amma a haka ya miƙe ya fara tafiya taku ɗai-ɗai yana dawowa kan matattakalar. Duk bayan taku ɗaya sai ya tsaya ya huta. Sannan duk da haka sai da yayi amfani da takobin sa a matsayin sanda domin kada ya fadi. A hankali a hankali ya rarrafa ya biyo ta cikin filin dagar inda Shata yake fafatawa da wannan runduna ta sadaukai dubu biyar. 


Mafi yawan rundunar sunyi bacci, amma kuma wanda suka rage sun rarraba kansu gida-gida suna harbawa Shata kibiya daga nesa. Sunyi amfani da duwatsu sun toshe kunnensu domin kada suji kidan da yake tashi. Duk da hakan ya taimaka wajen kare su daga wannan kida amma fafatawarsu da Shata tana tsaka da ɗaukan zafi. Shata bashi da wani makami banda garaya, kuma shi kaɗai ne, amma kuma sun rasa yadda zasu yi dashi. Babu wanda yasan mai Shata yake yi amma duk wata kibiya da suka harbo sai kaga ta fadi kasa kafin ta ƙarasa inda yake. Kai saboda tsamarin da yaƙin yayi har Armad yazo ya wuce ta kusa dasu basu kula dashi ba.


A haka a haka har sai da Armad ya koma wajen matattakalar. Har yanxu Haruta yana tsaye a bayan Zaikid wanda yake durkushe cikin ankwa. Idanun Zaikid a rufe suke, kansa a sunkuye yake, ya kasa ɗagowa ya kalli Armad. Babu wanda yasan abinda yake cikin zuciyar Zaikid, amma dai idan ka kalli fuskar sa zaka ga tsananin damuwa, nadama, dana-sani, ɓacin rai, kai dama wasu abubuwan da dama na takaici. Armad jikansa ne kuma ɗalibinsa, amma kuma ace yau Armad shi ne yazo ceto shi. 


Armad ya kama matattakalar nan ya hau sama. Kai tsaye ya wuce kan Zaikid da niyar ya cire ankwar da take jikinsa. Haruta ya doke hannunsa da ƙafa. Armad ya dunkule hannunsa na hagu ya juyar dashi izuwa walkiya ya kai masa duka da hannun aradu. Haruta ko kaucewa baiyi ba. Ya tsaya walkiyar ta dake shi. Bayan komai ya lafa ya bayyana tsaye cikin tufafinsa ko kwarzane babu a jikinsa. Har yanzu dafin Kamus yana aiki a jikin Armad. Abin kamar ƙaruwa yake yi. Ganinsa dishi-dishi yake ƙara yi. Ƙarfin hali yasa Armad ya ƙara dunkule hannunsa ya saukar da wata walkiyar akan Haruta, amma a banza. Armad yayi-yayi amma Haruta yana tsaye babu ko alamun yasan ma yana yi. Wanda hakan ba abin mamaki bane duba ga waye Haruta. Sannan kuma jinin Armad acike yake da dafi a wannan lokaci. Watakila da wani ne ko motsi ma bazai iya yi ba. 


Bayan kimanin rabin sa'a ana abu daya, Zaikid ya gaji ya buɗe ido. A hankali ya juya ya dubi Haruta.


"Haruta, ka rabu da Armad ya tafi. Ni zan miƙa wuya. Komai kake so zanyi. Komai Ururu suke so zanyi. Amma dai ka rabu da Armad ya tafi."


Haruta ya kyalkyale da dariya. "Hahaha... Haba, farfesa, kana tunanin akwai wani abu da zaka fadamin da zan yadda da kai? Koda ace na yadda, akan me zan bar ɗaya daga cikin ku ya tsira? Ai bari kaji, wannan rana ta sha biyu ga watan shida rana ce wadda zamu ga ƙarshen duk wani ɗan ƙabilar Wilbafos. Bama ku biyu ba. Dalilin da yasa kaga har yanzu baku isa lahira ba guda ɗaya ne: ina so naji daɗin kashe ku, inaso na samu nishadi a yayin kashe ku. Ina so mutuwar ku ta zama farin ciki a gare ni nan da shekaru dubu daza suzo. Saboda haka zan kashe ku a hankali a hankali, har sai naji daɗin kashe ku." 


Yana zuwa nan a zancensa ya ɗaga ƙafa ya sake buga Armad. Armad yayi sama ya dira acan baya. Yana dira kasusuwansa guda biyu na kirji suka ɓalle, jini ya fito ta hanci da baki da ido. Yayi ƙoƙarin tashi amma ƙafafuwansa suka kasa ɗaukansa, dole ya zube a ƙasa. Sai da ya shafe rabin sa'a anan sannan ya rarrafa ya miƙe, a lokacin jinin ya daina zuba amma har yanzu jiri ne yake ɗibansa sa daga dafin da yake jikinsa. 


Har ya fara tafiya domin ya dawo wajen da Zaikid yake, amma a lokacin ya jiyo muryar kakan nasa. "Armad, kada ka dawo, kada ka dawo nan, wannan faɗan tsakani na ne da Ururu. Bana son ƙaddarata ta shafe ka. Ka koma gida, kayi rayuwar ka irin wadda kake so, amma dai faɗa na da Ururu bai shafe ka ba."  


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...