Babi na 163: Lasina Naitingele Nâra
***
A wannan lokaci Armad yai duba izuwa ruhinsa. Akwai wani waje wanda bai isa ya leƙa ba acikin Tsarin-ruhinsa saboda abinda ke wajen. Tuni Armad ya daɗe da mantawa da wannnan waje. A lokacinda Uznu ya kama shi yayi ƙoƙarin amfani da wannan waje amma saboda ruhinsa baya tare dashi ya kasa. A wannan lokaci yana tare da ruhinsa.
Saboda haka nan take ya buɗe wannan waje. Miyurarsa ta fara wani sabon haske wanda ba'a taɓa gani ba. Idan mai karatu bai mantaba a tsakiyar Miyurar Armad akwai wani hoton mutun-mutumi a tsakiya wanda takubba uku uku suka kewaye. A dai-dai wannan lokaci jini ya fara zuba daga tsakiyar goshin Armad. Tsakiyar goshin ya dare gida biyu wani ɓangwalen jini ya fito. Sannan ya rufe. Jikin Armad yai wata karkarwa mara kyan gani kafi daga bisani jini ya fara zuba daga idanunsa da bakinsa da hancinsa.
Hidaya tai ajiyar zuciya ta girgiza kai amma bata ce komai ba. Kawai ta nuna Armad da ɗan yatsa nan take jini ya daina zuba daga jikinsa. Shi kansa bai san ya akai ba amma yaji kwari a jikinsa. Saboda haka ya miƙe ya tsaya ya fuskanci Uznu yana mai murmushi.
Shi kuwa wannan ɓangwalen jini daya fito daga goshinsa tuni ya fara juyewa izuwa siffar mutun-mutumin dake goshin Armad. Nan take jini da tsoka suka bayyana a jikinsa. Sannan takubba biyi suka bayyana a hannunsa. Ya buɗe idanu ya kalli Uznu kallon raini. A wannan lokaci Uznu yaji wani gumi ya keto masa. Tuni ya fara karkarwa. Ita kuwa macen dake kusa dashi tana ganin wannan mutun-mutumi ta zare ido tana karkarwa tana nuna shi. Sannan ta kalli Armad ta kuma ƙara kallon mutun-mutumin ta girgiza kai kamar abinda take kallo ba abu bane mai yiwuwa ba. Badan komai ba saboda ta taɓa ganin irin wannan mutun-mutumi sak amma ba'a wannan zamani ba. Lallai a halin yanzu ta gane cewa kwata-kwata bata gane waye Armad ba.
Ta juya ta kirawo wasu ɗalasimai sannan tai fitar burtu ta tsaya a gaban Uznu ta ɗaga hannu tana bayani domin kareshi. "Nice Shidaikiyya Wilbafoa ƴar gidan Albarunu Wilbafos ƙanin Aldaima Wilbafos na ƙarni na farko. Ya kai ruhin gidan Wilbafos ina umartarka daka tsaya a inda kake." Tana magana tana haki tasan cewa koda Uznu bai ƙarar da ƙarfinsa ba bazai kai ko'ina ba idan aka haɗashi da wannan mutun-mutumi ba. Domin ita tasan waye. Kawai kwanciyar hankalinta ɗaya tasan a wannan ƙarni babu wani jinin Wilbafos daya fi nata ƙarfi saboda haka wannan mutun-mutumi saiya bi umarninta.
Amma a wannan lokaci mutun-mutumin ya dubi Armad kamar yana jiran umarni. Armad ya gyaɗa masa kai. Haka na faruwa ya motsa daga inda yake ya ɗaga takobinsa. Nan take ya bayyana a bayan Uznu Ururu. Saboda tsananin saurin tafiyar da yayi babu wanda yaga sanda ya isa wajen Uznu, kai kace tafiya yayi acikin lokaci. Abin mamaki kawai sai akaga kan Uznu Ururu ya tashi sama an filleshi. Sannan gangar jikin ta rabe gida biyu. Babu wanda yaga sanda akai saran kawai kan Uznu aka gani a sama yana lilo.
Kamar haka bai isa ba kawai sai gangar jikin nasa ta kama da wuta. Kan kace meye wannan ta ƙone ƙurmus. Uznu ya mutu a jiki da ruhi.
Macen na ganin haka ta kwala ƙara inda ta shiɗe ta faɗi ƙasa sumammiya. A wannan lokaci ankokin dake sama wanda dama tuni suka fara sakkowa suka zo suka ɗaure mutun-mutumin Armad suka matse shi har saida ya rududduge. Ga dukkan alamu yadda mutun-mutumin yafi ƙarfin Uznu shima ankokin sunfi ƙarfinsa.
Haka na faruwa Armad shima ya faɗi ƙasa yana haki saboda gajiya. Uznu ya karɓi hukuncinsa amma kuma faɗan ya ƙarar da Armad. A halin yanzu ko motsa ɗan yatsansa wahala zai masa.
A dai-dai wannan lokacin Hidaya tai ajiyar zuciya ta matso kusa. Dama abinda kawai take jira kenan ta ɗauki Armad su ɓace.
Tana matsowa kusa ita ma Nostaljiya ta rugo kan Armad. Saboda bata ganin Hidaya saita bangaje ta wuce. Hidaya bata damu ba kawai ta matsa gefe a lokacin tana tsaka da tunanin ya zatai ta ɗauke Armad ba tare da Nostaljiya ba. Amma idan abin ya gagara su biyun zata ɗauke. Kawai saboda Armad amma badan tana son haɗa zuri'a da Bihanzin ba. Sai dai kuma a dai-dai wannna lokaci ne fatar Nostaljiya ta shafi jikin Hidaya. Hidaya taji wani irin abu ya daki kwakwalwarta. Nan ta zare ido cikin mamaki. Domin tasan tuni ta kare ruhinta da tunaninta daga dukkan wani hari saboda haka babu wani mahaluƙi a duniya daya isa yayi mata ɗaukan bazata.
Amma abin bai tsaya iya nan ba. Nan take ta fara jin wani irin yanayi kamar ta taɓa ganin Nostaljiya a wani zamani daya wuce. Hasalima har hotuna ta fara ganin acikin kwakwalwarta wanda ke nuna mata ta taɓa rayuwa da Nostaljiya a baya. Idan mai karatu bai manta irin wannan abu sak Armad yaji a lokaci na farko da fatarsa ta taɓa Nostaljiya.
Armad bashi da sani sosai akan tarihi da abinda ya faru a lokacin yaƙin duniya na sarki Eyriyon amma Hidaya tasan komai. Nan take ta haɗe gira. Wasu tunane-tunane suka fara gilamawa ta cikin kanta. Nan take ta fara haki tana kallon Nostaljiya. Amma kafin tayi wani abu ta zaro wani ɗan Ayrid daga cikin jakarta ta tsafi ta turawa dattijo Zaikid saƙo.
Zaikid wanda tuni ya haɗa kwanukan abincin dare yake jiransu ya fara masifa yana cewa. "Dake da babanki kun kyauta. Kunsa nayi girki amma har yanzu babu wanda ya dawo. Mai yasa har yanzu baki ɗakko min jikana bane. Ina babat taki."
Hidaya tayi ƙoƙari ta kama numfashinta bata so ta ɗaga masa hankali. "Hmmm... datttijo gani nan yanzu zanzo. Amma yanzu zan bawa aljani na Ja-Dulruri ya kawo mama gida. Tuni na bata shekarun izza dubu ɗari saboda haka zata farka nanda isha'i."
Zaikid ya ɗan lafa sannan ya ce, "To amma dai kiyi sauri ki kawo min jikana imma ke baza ki dawo ba, ehe."
Yana niyyar kashewa yaji kamar akwai wani abu dake damun Hidaya saboda haka ya ƙara sakkowa ya ce, "Akwai wani abu ne? Ko nazo ne?"
Hidaya tai sauri ta amsa da cewa. "A'a... Hmmm.. Kawai dai ina son tambayarka akan Lasina Naitingele Nara ƴar sarki Aldaima. Kace a gabanka sarki Aldaima ya kashe ta da hannunsa ko?"
Zaikid ya ɗanyi shiru na ɗan lokaci sannan ya amsa da cewa. "Da hannu na binne ta. Ina tunawa cewa har sanda na binne ta idan na taɓa fatarta ina jin sirrin Aldaima a jikinta. Wato ina jin kamar na taɓa ganinta a zamanin daya wuce."
Hidaya tai ajiyar zuciya ta ce, "kana ganin idan bata mutu ba kuma har yanzu tana raye idan na kawo maka ita koda ta canja kamanni zaka gane ta?"
Zaikid ya ce, "akwai hanyoyi dazan gane ta dasu amma mai yasa kike wannan tunani? Lasina Naitingele Nara ƴar Aldaima Wilbafos ita ce wadda fa Aldaima ya haifa bayan ya auri mahaifyarta ƴar ƙabilar Nara kuma da hannunsa ya kashe ta. Ni kuma na binne ta. Babu yadda za'ai ace tana raye."
Hidaya tayi ajiyar zuciya ta ce, "bari dai na kawo maka wata yarinya ka gani ko ita ce. Yanzu zan iso." Tana gama faɗar haka ta kashe ta maida Ayrid ɗin jaka.
Ta zare takobinta domin ta zama cikin shiri sannan ta juyo kan Armad da Nostaljiya.
Sai dai kuma a wannan lokaci ne taji Armad yayi ƙara mai figitarwa. Tana ɗaga kai taga sarki Daljari yana ƙoƙarin sarewa Hasanu kai amma Nostaljiya ta shiga tsakani inda ya caka mata takobin a zuciya. Nan take kowa yai ƙuri ana kallon ikon ALLAH amma rasa yadda akai Nostaljiya ta bar wajen Armad taje gaban Daljari.
***
Mintuna biyu kafin wannan lokaci.
***
Nostaljiya na tafe tana sassarfa zata ƙarasa gurin Armad babu abinda ke cikin ranta sai soyayyar Armad. Tana so ta ƙarasa ta tallafeshi, ta tashe shi daga ƙasa, ta goge masa gumi. Koda Armad yaji yanayin izzarta sai ya daure ya juyo yana murmushi. Murmushinsa kaɗai yasa duniyar Nostaljiya tayi fari. Nan take ta manta tana filin yaƙi. Ta ƙara sauri tana so ta isa majen masoyinta Armad.
Saura taku tara ta ƙarasa amma Nostaljiya tana ji kamar ratar dake tsakaninsu takai ratar dake tsakanin sama da ƙasa. Abin mamaki shima Armad gani yake kamar baza ta taɓa ƙarasowa ba. Nan take Armad ya fara jan ciki zuwa gareta. Koda ya rage saura taku uku sai Armad yaga kamar nisan dake tsakaninsu yana ƙara yawa maimakon ya ringa raguwa. Saboda haka Armad ya miƙa hannu, ita ma Nostaljiya ta miƙa masa hannu.
Amma kash... a dai-dai wannan lokaci hankakan mutuwa ya gilma ta tsakanin su. Nan take wani tsafi irin wanda aka daɗe ba'a gani ba a doron duniya ya bayyana. Wani baƙin haske ya kewaye jikin Nostaljiya yai sama da ita yabi wannan hankakan mutuwa.
A can ɗaya ɓangaren filin yaƙin wani hankakan mutuwan ne ya bayyana a kusa da yarima Niyashi. Hankakan mutuwan ya ɗauke shi sama yabi bayan ɗaya hankakan.
A ɓangaren Bihanzin da sarki Daljari tuni yaƙi yai tsamari. Amma abin mamaki hoton duniyar daya bayyana a bayan sarki Daljari da kuma wannan katanga mai ɗauke da wadannin aljanu takwas wadda ta jawo waƙar izza data bayyana, tuni suka matse Bihanzin a kwana. Ko ɗaga takobi Bihanzin ya kasa. Tuni an daɗe da lalata dauwamammen saran dake hannunsa.
Babu abinda Bihanzin yake sai lazimi yana cewa, "Rayuwa dan takobi, mutuwa dan takobi."
Sarki Daljari ya samarda wani al'amudi na baƙar ƙasa. Al'amudin na bayyana wata koriyar wuta mai ɗauke da baƙin hayaƙi ta kewaye al'amudin. Daljari ya ɗaga ya kawowa Bihanzin duka ta sama sannan kuma a lokaci guda ya jefowa Bihanzin mashi ta ƙasa. Bihanzin ya samarda wata takobin daga jakar tsafinsa ya kare al'amudin amma kafin ya ankara mashin ya cimmasa yana neman cake masa zuciya.
A lokacin idanuwan Hasanu sukai jajawur, yai fitar burtu ya tari mashin da wani bango wanda aka halitta da jar iska. Duk abinda ya taɓa wannan jar iska rududdugewa yake amma mashin sarki Daljari ko'a jikinsa. Ya shige fit ya cake Hasanu a ƙirji. Sannan ya ɓulle ta bayansa. Sai dai kuma a lokacin da mashin yake ƙoƙarin cake Bihanzin hankakan mutuwa guda biyu suka bayyana; ɗaya na ɗauke da Nostaljiya, ɗaya na ɗauke da Rafiyan Nazara. Dukkansu suna ganin abinda ke faruwa amma sun kasa motsi.
Wanda ke ɗauke da Nostaljiya ya saka ta a gaban mashin wanda take ya cake ta. Nan take ta fara aman jini. Mashin ya fice fit ta bayanta ya cake Bihanzin a ƙirji.
Ɗaya hankakan ya ajiye Nazara a tsakanin Hasanu da Daljari.
Daljari na tsaye a farko, Nazara na gabansa, sai kuma Hasanu a gabansa sai kuma Nostaljiya a gaban Bihanzin. Mutun uku a cikinsu mashin Daljari ya cake su. Lamarinda ya haɗa jininsu a waje ɗaya.
A dai-dai wannan lokaci duk wanda ke filin yaƙin ya tsaya cak babu wanda yasan meke faruwa. Hatta sarki Daljari kawai kallo yake ya rasa abinda ke faruwa. Mai yasa Bihanzin ya ɗakko Nazara? Meye alaƙar Nazara da Nostaljiya da Bihanzin zai sa hankakan mutuwa ya ɗakko su. Abin mamakin shi ne mai yasa Bihanzin yake ƙoƙarin kashe ƴarsa wadda ya fito yaƙi kacokam dan ya kare ta? Kowa kansa ya ƙulle an rasa mai magana.
Sai dai kuma a wannan lokaci ne Hidaya ta ɓace daga inda take ta bayyana a kusa da Nostaljiya. Tana bayyana wani haske mai kashe ido ruwan ɗorawa ya fara ɓulɓula daga jikinta. Cikin daƙiƙa ɗaya hasken ya tokare da sararin samaniya. Dukkan wanda ke filin yaƙin yaji shekarun izzarsa sun fara rawa suna girgiza. A lokaci guda dukkan wanda ke kewaye da Bihanzin ya nemi shekarun izzarsa ya rasa. Wani haske wanda ke ɗauke da shekarun izzar ya fara tashi daga jikinsu Damjinu Djinn da Naƙata da Kiru da Hasanu yana shiga cikin wannan hasken ruwan ɗorawa. Amma abin bai tsaya anan kaɗai ba, dukkan wanda ke filin harda su Jan-doki da Asifu ruwan bala'i da su Farin yashi suka fara karkarwa. Shekarunsu na izza suna girgiɗi.
Nan take suka ɓace daga inda suke suka jeru a bayan Daljari suka ɓuya. Duk wanda yai sanyi na daƙiƙa ɗaya a lokacin zai rasa dukkan shekarun izzarsa koda kuwa sunkai dubu ɗari. Mutane biyu kacal da suka isa su tsaya a gaban wannan haske ruwan ɗorawa sune Bihanzin da Daljari.
Daljari yai ajiyar zuciya yana kallon Hidaya ido a zare. "HEEDA!? Baƙar Wuta?"
Hidaya bata bashi amsa ba kawai takobi ta zare takobi ta afka kan Bihanzin da mummunan nufi irin na ƙabilar farko. Iskar dake kewaye da Hidaya ta dare gida biyu. Sama da ƙasa ta dare gida biyu. Wani baƙin hadari ya haɗo. Kafin Hidaya ta ƙarasa wannan ankoki da suka fito suka hana Armad wuce izza dubu arba'in suka bayyana sukai kan Hidaya suna neman rufe ta.
Bihanzin yai kururuwa yai ƙaraji. Nan take wasu hankakun mutuwa guda dubu suka bayyana a samansa. Sannan wani kai mai ƙahunhuna ya bayyana a gefen kansa na dama. Wani ma ya ƙara bayyana a ɓangaren hagu. Sannan wani ya bayyana a baya. Kan kace meye wannan Bihanzin ya koma mai kayika huɗu. Kowanne kai yana da ƙahunhuna uku. Jikin Bihanzin ya ƙara girma ya koma kamar na wani basamude. Sannan hannuwa suka fara bayyana a jikinsa. Kowanne kai ɗaya ya samarda hannuwa biyu. Kan kace meye wannan Bihanzin ya koma mai kai huɗu hannuwa takwas. Sannan dauwamammen sara guda takwas ta bayyana a kowanne hannu.
Ana haka shima Bihanzin wannan ankoki suka bayyana a samansa suna neman rufeshi. Kowannensu ya haura shekarun izzar da Ururu suka yadda ayi amfani dashi.
Hidaya ta ƙifta idonta na hagu lamarinda yasa doron ƙasa na huɗu ya dare gida biyu. Wani al'amudi ya bayyana daga ƙarƙashin ƙasa. Yana bayyana yai kan wannan ankoki suka fara fafatawa.
Suma hankakun mutuwan dake saman Bihanzin suka tare masa ankoki. Lamarinda ya bawa wannan hatsabibai biyu damar haɗuwa da juna. Suna haɗuwa, takobin Heeda guda ɗaya ta haɗu da dauwamammen sara guda takwas daga hannuwa takwas na mai dauwamammen sara.
***
Babi na 164: Jini-uku (2)
***
Takubbansu na haduwa ƙasa ta fara tsagewa a wani yanayi mai kama da girgizar ƙasa. Wata guguwa ta ɗebi duk wanda ke filin tai watsi dasu uwa duniya domin wannnan yaƙin ya girmi idanuwansu. Wanda kaɗai suka rage banda Heeda da Bihanzin sai Daljari da Armad da Nostaljiya da Nazara da Hasanu. Wanda abin mamaki babu abinda ya same su.
Takobin Heeda yaluwa ce siririya amma tana ɗauke da nauyin duniya. Domin tuni dauwamammen sara guda takwas suka fara tsagewa.
Hidaya ta nuna Armad Wanda ke gefenta a sume ta ce, "Kayi sani Bihanzin ba kaine wanda TARIFIL-FAKTA yake jira ba."
Bihanzin ya fashe da dariya da kayika guda takwas a wani samfuri mai firgitarwa. Sannan muryoyi guda takwas suka amsa da cewa, "KINA TUNANIN BANSAN SHIRINKI BA, BAƘAR-WUTA? MAHAIFINA SHI NE YA GINA KUJERAR SARKI DAKE DORON ƘASA NA FARKO KUMA NI BANZIRSHISHIRUI NI ZAN MULKI DUNIYA KODA SAMA DA ƘASA ZATA HAƊU.
"KUYURUSSA'AYI, DUMAƘISU, DUL'URURU, AMRAIKUGYU, TARIFIL-FAKTA, TAIDARA, ZAIKID, MAIKIRO'ABBAS, HAN'IBAL, FATI BAYAJIYADDA, duk sai kun durƙusa zarar na gama haɗa fasahar JINI-UKU."
Hidaya tai dariya a fusace tace, "kuma kana tunanin SAMMAI zasu zuba maka ido kayi abinda kake so?"
A dai-dai wannan lokaci sarki Daljari ya juyo a fusace ya ce, "Heeda, ina baki girmanki a fannin izza shi yasa ban tari numfashinki ba, amma kiyi sani wannan yaƙin bai shafe kiba. Yaƙi ne tsakanina da baƙin maraya."
Heeda ta juyo ta kalleshi tsahon lokaci sannan ta numfasa ta ce, "Baba Dalja, abinda Bihanzin yake shirin yi zai zuƙe ruhinka da ruhin ɗanka Nazara da ruhin Nostaljiya. Dukkan rayukanku guda uku idan aka haɗa su zasu iya samarda fasahar data sa aka ci nasara akan kakana sarki Eyriyon. Ban san yadda akai Bihanzin yasan wannan fasaha ba domin duk duniya babu wanda yasanta daga ni sai Eyriyon sai Tarifil-fakta. Amma lallai abinda yake son aikatawa kenan. Kaga tanan yaƙin ya shafe ni tunda ya saci fasahar gida na."
Daljari na niyyar bada amsa Bihanzin ya tari numfashinsa. "Girman kai da isa da nuna izza shi ne abinda ya halaka Eyriyon kuma shi ne abinda zai halaka ki Heeda. Dukkanku ƴaƴan Wilbafos da Urürü haka kuke tun farkon lokaci. Kuna ganin tunda an haifeku da maɗaukakan idanuwa kuna sama da kowa.
"Tsinannan hatsabibin ma'aboci izzar da aka haifa a safiyar duniyar shi ne ya sace fasahar JINI-UKU daga gidan Shishirui. Amma saboda daɗewar lokaci kuna gani taku ce. Da sannu zan nuna muku daku da Ururu cewa ba kowa bane."
Idanum Heeda sukai jajawur da haushi. Ta dubi Bihanzin ta nuna shi da ɗan-yatsa ta ce, "kwamanda Tarifil-fakta kake cewa TSINANNE? Kai sani tun daga ƙarni na farko har zuwa yanzu babu wata halitta mai tsarki kamar Tarifil-fakta, hatta gidan Ururu basa zaginsa. Lallai hukuncin kisa ya tabbata akanka."
Bihanzin ya nuna Nostaljiya da ɗan-yatsa lamarinda yasa haske ya fara ɓulɓula daga jikinta wannan ya haɗe da jikin Nazara sannnan ya haɗe da jikin Daljari. Bayan komai ya haɗu sai hasken ya fara yin kwana yana dawowa jikin Bihanzin. Daljari yai duk wani abu da zaiyi ya kore hasken amma abu yaci tura. Yana ji yana gani hasken ya fara jan ruhinsa.
Nan take idanuwansa suka zazzaro ya dubi Heeda a firgice ya ce, "wannnan wacce fasaha ce?"
Heeda tai ajiyar zuciya ta ce, "Fasahar Jini-uku jinsi-uku wanda akai amfani da ita wajen ƙirƙiro izza a doron ƙasa. Jini-uku jinsi-uku sune ƙabilar uzzus, ƙabilar Nara da ƙabilar Rafiya.
"Sirrin ƙabilar uzzus basa tsufa. Sirrin ƙabilar Nara idan suka mutu ana ƙara haifarsu a wani zamanin. Sirrin ƙaɓilar Rafiya shi ne su kaɗai suke iya haɗa alaƙar auratayya da waɗannan jinsi guda biyu. Kamar yadda ka auri ƴar ƙabilar Uzzus amma kuma ka haifi Nazara wanda yake da jinin uzzus zalla. Idan sauran mutane suka auri ƴar ƙabilar uzzus baza su iya haifar uzzus ba. Kaga anan Bihanzin ya haɗa Nazara wanda ya fito daga ƙabilar Uzzus da kai Daljari wanda ka fito daga ƙabilar Rafiya da kuma Nostaljiya wadda ƴar asalin ƙabilar Nara ce. Bihanzin yana so ya samarda TSAFI wanda tunda aka halicci IZZA ba'a taɓa samarda TSAFI mai girmansa ba.
"Gidan Wilbafos mun daɗe muna ƙoƙarin samo Jini-uku jinsi-uku amma Kuyurussa'ayi ya kashe dukkan ƴan ƙabilar Uzzus da Nara. Uznu ne kaɗai ya rage daga Uzzus wanda shima ya mutu a yau. Idan baka mantaba Daljari mu muka taimaka maka wajen ɓoye matarka muka hana Ururu da kowa sanin asalinta. Sannnan kuma muka ɓoye asalin Nazara tun a farkon lokaci. Duk dan kar kowa ya sani. To amma ban san yadda akaiba Bihanzin ya gano sirrin gidanka. Ina ganin wannnan shi ne dalilin da yasa ya tsaya akan hanya kuka tsince shi a matsayin maraya domin ya shiga gidanka yayi bincike.
"To amma banda koda Bihanzin ya san asalin ka da asalin Nazara dole yana bukatar ƴar ƙabilar Nara domin yayi wannan tsafi. Hatta gidan Wilbafos da muke da alaƙa da gidan Nara bamu san ko mutun ɗaya ba a raye. Idan ɗan ƙabilar Wilbafos ya taɓa fatar jikin ƴar asalin ƙabilar Nara muna iya ganin abinda ya faru a rayuwarsu ta farko wanda hatta du kansu sun manta. Ban taɓa tunanin ƴar riƙon wajen Bihanzin ƴar ƙabilar Nara bace. Daƙiƙu da suka wuce na haɗa jiki da ita na gano cewa ba wata bace illa Lasina Naitingele Nara ƴar sarki Aldaima na farko.
"To amma Lasina ta mutu! Sirrin daya kashe Lasina babban sirri ne. Ko Kuyurussa'ayi bai isa ya dawo da ita ba. To idan ma Bihanzin yayi amfani da wani ɓoyayyen sihiri ya dawo da ita tana bayyana Zaikid zaiji a jikinsa saboda ƘULLIN-RUHIN da Aldaima yasa a tsakaninsu. Babu wata fasaha a duniya da zata iya warware wannan ƙulli. Babu sai guda ɗaya...."
Koda Nostaljiya tazo nan a zancenta sai ta ɗaga ido ta kalli Bihanzin tsahon lokaci sannan ta girgiza kai ta ce, "baka kai wannan matsayi ba Bihanzin."
Ɗaljari yaga yadda fuskar Heeda ta canja yasan akwai wani abu. "Heeda ya akai?"
Ta juyo wajen Daljari a nutse ta ce, "Kada ka damu bazan taɓa bari Bihanzin ya aiwatar da wannnan shiri nasa ba koda kuwa ta kama na kashe ka na kashe Nostaljiya da Hasanu ne da hannuna. Sai dai sarki Armad ya yafeni."
Kamar Bihanzin yana ƙoƙarin ya nuna mata hakan bazai yiwuwa sai dukkan hankakun mutuwar dake sararin samaniya suka juye izuwa katangar tsafi suka kewaye Nostaljiya da Nazara da Daljari.
Hidaya tayi murmushi sannan ta girgiza kai ta ce, "koda ka daɗe a raye, koda ka daɗe kana shiri har yanzu baka san mai ake nufi da izza ba. Kana tunanin hankakan mutuwa zai hanani yin abinda nake so? KAI KODA KAINE YARIMAN FARKO WANDA AKE KIRA DA FARIN-TSORO WANDA YAI JAYAYYA DA TARIFIL-FAKTA a gaba na kai ba kowa bane. A kaf faɗin duniya mutun uku ne kacal zasu iya cetarka a yau."
A dai-dai wannan lokaci Armad ya farfaɗo daga suman da yayi tun bayan ganin da yayi an cakawa Nostaljiya wuƙa. Yana ɗaga kai yaga Hidaya sannan kuma ya hango Nostaljiya acikin hijabin Bihanzin. Ganin Hidaya ya farantawa Armad rai to amma kuma a halin yanzu kawai Nostaljiya yake tunani. Ya yunƙura zai miƙe amma ya kasa. Duk yadda yai ƙoƙari ya miƙe ya kasa. Saboda haka Armad ya fara ƙoƙarin kiran sunan Hidaya yana kakari, "y...ya...yaya.. Hida..ya..."
Nan take Hidaya ta juyo tayi masa sassanyan murmushi kamar ba ita ce ta ɗazu ba. Armad na ganin murmushin hankalinsa ya kwanta. Hidaya ta haɗe hannayenta biyu sannan ta fara kiran wasu ɗalasimai. Nan take wata ƙofa ta bayyana a sararin samaniya. Bihanzin na ganin ƙofar ya fara bayani yana cewa, "hmm... dama nasan akwai yiwuwar ki kira wannan ɗalasimi to kiyi sani awa biyu data wuce na yaɗa labarin SIRRIN DAZAI RIKITA DUNIYA. Kiyi sani a halin yanzu kowa ya san wannan sirri, tuni jama'a sun fara zanga-zanga suna yiwa Ururu tawaye. Gashi ƙaninki ya kashe ɗaya daga cikin Ashura. Babu jimawa Ururu zasu sakko doron ƙasashen ƙasa domin dawo da doka da oda. Kinfi kowa sanin mai zai faru idan hakan ta faru kina nan.
"Ni nasan ke hatsabibiya ce kuma ke kaɗai zaki iya tarwatsa min shiri. Wannan shi ne dalilin da yasa na mallaki Sirrin da zai rikita duniya domin da kin bayyana na yaɗa shi a duniya na zuƙo Ururu. Kinga sai ki zaɓa. Wa kika fi tsana? NI KO URURU? Amma dai kiyi sani yarima Dumaƙisu Kuyurussa'ayi wanda ya kashe Eyriyon da ƙarfin ruhi na nan tafe."
***
Babi na 165: Sirrin Dazai Rikita Duniya
***
Akan doron ƙasashe tuni aka fara ƙone-ƙone ana zanga-zanga. Babu wanda yasan yadda akai amma tun daga ƙasa ta uku har zuwa ƙasa ta bakwai babu inda labarin SIRRIN DA ZAI RIKITA DUNIYA bai jeba cikin ƙanƙanin lokaci.
Akan doron ƙasa na bakwai, dai-dai gefen wani mai shayi wasu ma'abota izza ne ka tattaunawa.
"Kaji abinda Ururu suka aikata?"
"Naji. Abin yayi yawa, banda rukunai biyu na Amri da Jinzidal da suka saka mana ashe akwai wani ƙulli da suke yi a ɓoye."
"Yadda naji wannan shi ne dalilin da yasa suka ƙulle sarki Amraikugyu da sarki Deniz Ururu saboda kada su watsa wannan labarin."
"Kai wallahi baza mu yadda ba. Sai Ururu sunzo da kansu sun bayyana mana abinda ake ciki."
"Naji ance za'a taru a ƙona shalkwatar Mayakan Ururu dake ƙasashen ƙasa, nima dani za'ai."
A can doron ƙasa na shida tuni hayaƙi ya turnuƙe sama saboda ƙone-ƙone. Babu wanda yasan ta ina aka fara amma tuni an ƙone shalkwatar Ururu ta mayaƙan rukunai biyu.
Haka a sauran ƙasashe.
A dai-dai wannan lokaci sarakunan Jinzidal uku wanda basa filin yaƙi suna tsaye a wani sihirtaccen waje suna tattauna wannan al'amari.
Sarki Deniz Iluru ya dube su ya ce, "ban taɓa tunanin Ururu zasu aikata irin wannan abu ba. Amma shugaba Deniz Ururu ya bayyana min cewa dama tun can Ururu suna da wannan niyya. Kuma wannan shi ne dalilin da yasa Heeda, baƙar wuta, ta shiga duniyar aljanu."
Sarki Maikiro'Abbas yai ajiyar zuciya ya ce, "wanda ya fara gano wannan sirri shi ne Tarifil-fakta. Mutun na biyu shi ne Amraikugyu. Amma duk su biyun saida Ururu suka tabbatar sun hana su bayyanawa. Daga baya Bihanzin ya sami wannan sirri kuma shi ne mutumin daya bayyanawa duniya shi lamarinda zai jawo saukar Ururu a kowanne lokaci. Shawara ta rage ya tamu; mu ci gaba da bin Ururu ko kuma mu bi Heeda Wilbafos!!"
Sarki Han'ibal yaja gwauron numfashi ya kalli takardar dake hannunsa ya fara karantawa. Duk da Hidaya ta gaya masa wannan sirri amma bai taɓa tunanin abin zai rincaɓe haka ba.
A jikin takardar an rubuta SIRRIN DA ZAI RIKITA DUNIYA.
***
SARKI KUYURUSSA'AYI, SARKI BISA DORON ƘASA NA FARKO, YA KWACE DUKKAN FASAHAR ALJANU YA MAIDA ITA WAJEN DORDOR....
***
Sarki Han'ibal ya ce, "Kunga tunda Dordor halitta ce dake ƙarƙashin Ururu indai wannan hukunci ya tabbata dukkan wani mutun dake amfani da fasahar aljanu ya tashi daga aiki kenan. Wannan shi ne dalilin da yasa Ururu suke yaƙar daular aljanu da niyyar ƙarar dasu, kuma shi ne dalilin da yasa ƴan gidan Wilbafos suke kare ɓangaren aljanu. Mu sarakunan Jinzidal munfi kowa amfani da fasahar Kwangila ta aljanu amma bamu taɓa sanin wannan abu ba ballantana mu taimaka. Lallai ni ina ganin mu koma bayan Heeda."
A wannan lokaci waje yayi tsit kowa yana tunanin shawarar dazai yanke. Haka suka shafe awa biyu amma basu tsaida matsaya ba. Kowa yasan gidan Wilbafos su ya kamata ya marawa to amma kuma ana tsoron matakin da Ururu zasu ɗauka.
***
~Doron ƙasa na farko
~Fadar Ururu
~Yarima Dûmaƙisu Kuyurussa'ayi
***
Komai dake kan wannan doron ƙasa na musamman ne. Idan ka ɗaga kai sama zaka ga gini wanda girmansa yakai girman doron ƙasa ta uku yana kan iska yana lilo babu abinda ya riƙe shi sai madafun izza. Wannan gini ba wani abu bane illa fadar sarki Kuyurussa'ayi. Daga cikin wannan fada wata irin waƙar izza mai ɗaukan hankali na tashi. A dai-dai ƙasan fadar akwai wasu gine-gine guda goma kowannensu yana lilo akan iska. Kowanne gini ɗaya na mutun ɗaya ne daga cikin ASHURA.
Akan doron ƙasar kuma akwai ginen-ginen masu kyawu matuƙa da ƙawa wanda aka yi da ruwan dinare zalla.
Mutane ma'abota baƙaƙen idanuwa suna ta kai komo kowa yana harkonkinsa. Ko kaɗan basu san halin da ake ciki ba.
A dai-dai wannan lokaci wani abin mamaki ne yake faruwa.
Yarima Dumaƙisu ya futo daga cikin wannan fada. Sanye yake da doguwar alkyabba, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Gashin girarsa ya miƙe kamar takobi. Idanuwansa suna sheƙi suna ɓulɓulin baƙin hayaƙi. A bakin fadar ragowar mutun takwas na Ashura ne a tsaye tare da waziri Tadiyraini cikin shirin yaƙi.
Suna ganinsa ya fito suka fara karkarwa domin su kansu sun san wane ne yarima idan ransa ya ɓaci. A tarihi ance babu wani mahaluƙi daya kaishi ƙarfin buwaya da dabarar yaƙi. Shi ne ya kashe Eyriyon. Yayi yaƙi da Tarifil-fakta kuma a ƙarshe Tarifil-fakta ne ya gudu. Shi ne ya ɗaure Amraikugyu. Shi ne ya saukar da al'umma ƙasashen ƙasa kuma shi ne wanda ya tabbatar da dokar Jinzidal. Ance hatta rana da wata basa iya kallonsa ido-da-ido.
"A buɗe hijabai. Sarki ya umarceni na kawo kan Armad Wilbafos."
Nan take waziri Tadiyraini ya gabato da sauri ya ce, "yarima da kanka. Ko ni aka bawa wannan..."
Yarima ya harari waziri yana cewa, "An saukarda sabon RUKUNI. An haramtawa dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos rayuwa."
Koda jin haka sai ya sunkui da kai baice komai ba ya wuce izuwa jami'ar Ururu dake doron ƙasa na farko domin wallafa wannan sabon Rukuni. Ana da Rukunin Amri, da Rukunin Jinzidal yanzu kuma ga wani sabo.
***
Babi na 166-171: Sadaukarwar Nusi
***
A dai-dai wannan lokaci doron ƙasashe bakwai ya rikice babu abinda kake ji sai tashin hankali da ƙone-ƙone. Yaƙin dake faruwa akan doron ƙasa ta huɗu tsakanin Bihanzin da Daljari ya gauraye ko'ina. Badan komai ba saboda Bihanzin ya watsa labarin sirrin dazai rikita duniya.
Mayaƙan Ururu wanda sarki Dul'ururu yake jagoranta tuni suka bazu ko'ina suna kama na kamawa suna kashe na kashewa. Kan kace meye wannan tuni dubban mutane sun rasa rayukansu, da dama daga ciki ƴan ba ruwana ne. A gurare da dama ƙasa tayi jajawur saboda tsabagen jini dake kwaranya.
Idan mai karatu bai manta ba akwai kwamandu guda biyar wanda ke jagorantar mayaƙan ururu a doron ƙasashen ƙasa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Uznu Ururu wanda Armad ya aika lahira. Mutun uku daga cikinsu a ɓoye suke babu wanda yasansu sai rana ta ɓaci irin wannan suke fitowa. A dai-dai wannan lokaci mafarauci wato sarki Dul'ururu, sarki bisa doron ƙasa na biyu yana tafe cikin shirin yaƙi.
Fuskarsa na ɗauke da ɓacin rai irin wanda aka daɗe ba'a gani ba a doron duniya. Abin mamaki wani shinge ne a saman kansa yana masa inuwa. Idan kai duba izuwa cikin wannan shinge dake saman kansa zaka ga wasu taurari masu ɗaukar hankali. Sannan suna bada wani sauti mai ɗauke da tafiyar shekaru. Kayan jikin Dul'ururu baƙaƙe ne wuluƙ. Idan mai karatu bai manta ba Dul'ururu shi ne mutun na farko da Uznu Ururu ya bawa labarin littafin takobi.
Idan akai duba da cewa duk cikin Ashura babu wanda ya shaƙu da Uznu kamar Dul'ururu za'a fuskanci ɓacin ran Dul'ururu yana da asali. Banda wannan kuma ga zanga-zanga wadda taja hankalin sarki Kuyurussa'ayi. A matsayin sarki Dul'ururu wanda aka danƙawa amanar ƙasashen ƙasa lallai wannan zanga-zanga sai tafi shafarsa sama da kowa.
Ba jimawa Dul'ururu ya ƙarasa wani sihirtaccen waje dake cikin fadarsa. Yana shiga ya ƙarasa zuwa ƙuryar dama sannan ya tafa hannayensa. Idanuwansa suka fara ɓulɓular baƙin hayaƙi. Hayaƙin na tafa ƙasa wajen ya dare ƙofa ta bayyana. Dul'ururu ya faɗa cikin ƙofar. Wajen yana da zurfi sosai kamar tsohuwar rijiya. Saida ya shafe kimanin rabin sa'a yana faɗawa cikin ramin sannan ya taɓa ƙasa. Yana dira ya tsinci kansa a wani ƙasaitaccen daji. Wasu manyan bishiyu wadda kowacce tsayin yakai zira'i dubu saba'in sun kewaye ko'ina. Babu abinda ke tashi sai sautin muggan namun dawa da kukan aljanu. Kai kace ba'a wannan duniyar wajen yake ba.
Dul'ururu na bayyana wasu mutun uku suka dira a gabansa. Dukkansu samudawa ne ƴan ƙabilar ururu. Ba wasu bane illa kwamandu uku na mayaƙan ururu wanda ke ɓoye. Abinda mutane basu sani ba shi ne wannan mutun uku sune Salsa ɗin sarki Dul'ururu.
Na farkon ya durƙusa ya ce, "Shugaba Dul'ururu, wa kake so a kashe?"
Na biyun ya zare baƙar takobinsa ya ce, "wacce doron ƙasar kake so a halaka?"
Na ukun ya ɗaga al'amudinsa ya ce, "wace ƙabila kake so a ƙarar?"
Wannan daji wani yanki ne wanda aka yanko daga wata duniyar. Zaka iya cewa dukka faɗin ƙasashen ƙasa babu wajen da yakai wannan daji hatsari. Badan komai aka kawo shi nan ba sai dan koyon dabarun yaƙi. Amma sai wanda ya isa ne yake shiga.
Dul'ururu ya fara da cewa, "Ku ɗebi mayaƙa kuje duk wanda kuka gani a waje ku kashe."
Nan take waɗannan kwamandu guda uku suka amsa da cewa, "an gama shugaba."
Suna ɓacewa Dul'ururu shima ya ɓace ya bayyana akan wani katafaren tsauni wanda duk faɗin doron ƙasa na biyu babu kamarsa. Saboda tsayin wannan tsauni kana ganin taurari suna wucewa ta samansa. Nan take Dul'ururu ya fiddo da sandarsa ta tsafi ya fara farautar taurari. Duk tauraruwar wanda ya kaɗo sai kaga ta tarwatse. Kuma a ko'ina wannan mutun yake sai dai kaga ya faɗi ƙasa matacce.
Su kuwa waɗannan kwamandu guda uku tuni suka fara ƙaddamar da hukunci. Suma ragowar mutanen daulolin duniyar ƙasa suka ɗebi makamai sukai kan mayaƙan Ururu. Nan take jini ya fara kwaranya. A cikin ƴan daƙiƙu mutun dubu saba'in suka mutu. Jini ya fara kwaranya yana haɗuwa da ruwan bango. Lamarinda ya fara sauyawa ruwan launi zuwa ja.
Acan filin yaƙi waje ya koma ɓangare uku. A ɓangare ɗaya akwai sarki Daljari da ɗansa Nazara da kuma Nostaljiya waɗanda ke tsaye cikin ɗalasiman Bihanzin ko motsi basa yi. A ɗaya gefe kuma Bihanzin wanda ne tsaye yana zare da takobi. A ɗaya ɓangaren kuma Hidaya ce da Armad. Daga can nesa wata ƙurya wadda sai kayi da gaske zaka gani sauran mayaƙan ne wanda akai watsi dasu gefe guda.
Hidaya tafi kowa sanin abinda Bihanzin ya faɗa gaskiya. Hasalima saboda sanin cewa idan mutane suka san wannan sirri zasu yi bore sannan kuma hakan zai jawo zubarda jini shi ya sa Hidaya taƙi bayyanawa kowa sirrin dazai rikita duniya. Amma cikin daƙiƙa kaɗan Bihanzin ya watsa labari kuma abinda ake gudu ya faru. Ko a dai-dai wannan lokaci da take wannan tunani aƙalla sama da mutun dubu ɗari biyu sun rasa rayukansu wanda basu jiba basu gani ba.
Bihanzin ya daɗe yana shiri to amma komai shirinsa kawarda sarkin Jinzidal kamar Daljari ba ƙaramin abu bane.
A wannan lokaci sarki Daljari ya fashe da dariya. Ya tafa hannayensa biyu ya fara zuƙo shekarun izza na kwangila wanda ya daɗe yana tarawa daga duk wani ma'aboci izza da yayi amfani da fasaharsa.
Ƙasa ta fara girgiza sannan duwarwatsu suka farfashe. Samaniya tayi duhu. A lokaci ƙanƙani sama da shekarun izza dubu ɗari suka taru a saman kansa. To amma tunda ba'a jikinsa ya zuƙe su ba wannan ankoki dake ƙayyade shekarun izza basu bayyana ba. Daljari ya ƙara kirawo wannan katanga mai ɗauke da aljanu. Abin mamaki da katangar da shekarun izzar duk sai suka haɗe izuwa wani baƙin al'amudi.
Sarki Daljari baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaga wannan al'amudi sama ya daki ɗalasiman dake ɗaure da Nazara. Yana dukansu wata ƙara mai rikitarwa tai sama. Ɗalasiman suka ɗan buɗe kaɗan, shi kuma al'amudin ya tarwatse. Shekarun izzar dake jikinsa suka wargatse. Ga dukkan alamu sau ɗaya kacal Daljari zai iya amfani da wannan al'amudi.
Sai dai kuma amma wannan ɗan buɗewa da ɗalasiman suka yi ita kawai Daljari yake buƙata. Nan take ya zira hannu ya finciko Nazara daga ciki. Abin mamaki ɗalasiman kamar masu rai sai suka bi hannunsa suna yi kan Nazara. Tuni ƙarfin Nazara ya ƙare, dashi da Nostaljiya ko motsi basa iya yi. Shima sarki Daljari dan tsohon hannune amma wannan ɗalasimai tuni suke zuƙe masa izza ta ko'ina.
Daljari yana ganin Nazara ya fito daga cikin ɗalasiman ya daki goshinsa. Nan take goshin ya dare gida biyu wani ɗigon jini ya bayyana. Jinin na bayyana wani nauyi ya cika wajen kai kace wani ma'abocin iko ne ya bayyana. A dai-dai lokacinda ɗalasiman suke niyyar ƙara rufe Nazara wannan ɗigon jini yai fitar burtu ya dira akan goshin Nazara. Haka na faruwa ɗigon jini ya fara ƙaruwa. Kan kace meye wannan ya fara ɓulɓula ya rufe dukkan jikinsa. Idan ka kalli Nazara babu abinda zaka gani sai jini ya rufe shi ruf kamar ansa a cikin buhu. Duk girman ɗalasiman suna taɓa jinin suka tarwatse. Babu wani ɗalasimi daya ƙara kusantar Nazara.
Daljari yai dariya ya ce, "ina ganin idan na ɗauke ɗaya daga cikin jini-ukun da kake nema shirin zai ɓaci. Ko ya kake gani, baƙin-maraya?"
Ana haka Hidaya ta kawowa Bihanzin sara da takobin izza. Bihanzin yasa takobinsa ya kare da dauwamammen sara. Amma matsalar shi ne takobin Hidaya zuƙe izza take saboda haka nan take izzar Bihanzin ta zagbe. Idan ba dan shima tsohon hannu bane da tuni shirin izzarsa ya tarwatse. To amma bayan zuƙe izza takobin Hidaya tana ɗauke da fasahar nauyi [gravity]. Nan take takobin Bihanzin tai nauyi tai ƙasa ta rinjaye shi. Takobin ta tarwatse, Bihanzin ya durƙushe a ƙas.
Amma abin bai tsaya haka ba, Hidaya bata gama ba. Kan kace meye wannan ta ƙara saukar masa da wani saran. Sara ɗaya. Sara biyu. Sara uku. Cikin ƙiftawar ido ta saukar masa da sara bakwai a jere. Kowanne ɗaya daga wannan saran yana ɗauke da ƙarfin doron ƙasa ɗaya. Koda bakwan suka haɗu sai suka juye izuwa siffar doron ƙasa bakwai.
Bihanzin ya cizi harshensa ya zuƙo wani baƙin jini ɗaga ruhinsa. Jinin na fitowa wata baƙar takobi ta bayyana. Wani yanayi mai ban tsoro ya cika filin. Baƙin hayaƙi na tashi daga jikin takobin. Bihanzin yaja layi akan iska inda iskar ta dare gida biyu. Wani sirri ya fara fita daga cikin iskar wanda Bihanzin yai amfani dashi ya kawowa Hidaya sara. Sara ɗaya. Sara biyu. Sara uku. Cikin ƙanƙanin lokaci Bihanzin ya samarda dauwamammen sara bakwai wanda suka juye izuwa siffar baƙin hankaka wanda yai kan Hidaya.
Bihanzin yai ƙaraji ya ce, "Dauwamammen sara!"
Hidaya a nutse ta ce, "Duniyar Izza!"
Koda saran biyu suka haɗu sai duniyar gaba ɗayanta ta fara girgiza ƙasa na tsattsagewa. Baƙin hankakan ya danna hoton ƙasa bakwai shima hoton ƙasa bakwan ya danna baƙin hankaka. Haka suka shafe daƙiƙu shida kowanne ɓangaren yana danna kowanne.
A lokaci Hidaya ta kalli Bihanzin a hasale ta ce, "BAKA KAI MATSAYIN KAI JAYAYYA DANI BA." Sautinta yana ɗauke da hikimar izza da fasaha irin wadda ba'a taɓa gani ba a doron ƙasa.
Kalmomi bakwai Hidaya ta faɗa. Abin mamaki kowacce kalma ɗaya data fita daga bakinta sai ta juye izuwa ɗalasimi. Kan kace meye wannan ɗalasimai bakwai masu ɗauke da girman izzar sarakunan farko suka bayyana. Ɗalasiman bakwai suka juye izuwa hatimi guda ɗaya wanda yai kan Bihanzin gadan-gadan.
A lokaci na farko tsoro ƙarara ya bayyana a fuskar Bihanzin. Ba shiri ya jawo ɗalasimin dake ɗaure da Nostaljiya da Daljari ya kare kansa.
Hatimin na dira akansa ya tarwatsa ɗalasimin jini-uku inda Nostaljiya da Daljari suka bayyana a fili. Amma duk da haka akwai ragowar ƙarfi a jikin hatimin inda ya wuce ya daki Bihanzin. Ƙarar rugurgujewar ƙasusuwa suka tashi daga jikin Bihanzin. Kan kace meye wannan duk wani ƙashi a jikin Bihanzin ya ɓalle. Sannan kuma hatimin ya wuce ya ɗamfaru a goshinsa.
Haka na faruwa jikin Bihanzin ya mutu ya faɗi ƙasa kamar an zare masa laka.
Amma abin bai ƙare haka ba. Nan take hatimin ya fara matse Bihanzin. Kan kace meye wannan jini ya fara kwaranya daga jikin Bihanzin.
A ɗan ƙanƙanin lokaci jinin Bihanzin ya malale a ƙasa.
Koda ganin haka sai fili yai tsit. Bayan ɗan lokaci mutane dake nesa suka garzayo. Mutanen Daljari na shewa na Bihanzin na kuka.
A dai-dai wannan lokaci Hidaya ta durƙusa kan Armad ta taɓa goshinsa lamarinda yasa wani zaren izza ya fice daga hannunta ya shige goshinsa. Nan take ya farfaɗo.
Da farko Armad bai yadda da idanunsa ba saboda haka ya ƙara nutsuwa ya girgiza kai ya ƙurawa Hidaya ido.
"Yaya..."
Hidaya tai murmushi gami da gyaɗa kai tace, "ka dai girma ballatana kace na goya ka."
Koda jin haka sai Armad ya tabbatar ita ce. Yai tsalle ya rungume ta.
Hidaya bata ce komai ba kuma bata motsa ba. Haka ta tsaya Armad ya gama koke-kokensa har ya sake ta. Sannan ta ce, "hmm.. Kana nan a yadda na sanka... ko?"
Armad najin haka ya haɗe gira cikin wasa ya ce, "kinsan ƙarfin izza ta kuwa? Nine magajin wilbafos, ni ne ma'aboci Al'yaya, ni ne ma'aboci fasahar Eyriyon, ni ne...."
Hidaya ta ɗaga hannu tana girgiza kai kamar bata yadda ba. Koda ganin haka sai Armad ya cije harshe ya ce, "idan baki yadda ba ki tambayi HADIMI na Babara."
Sai da ya tabbatar ya jinjina kalmar 'Hadimi' dan Hidaya ta gane abinda yake nufi.
Hiday taja dogon numfashi ta ce, "to to... na yarda, na yarda, shikenan? Matso kusa kaji."
Armad ya matsa cikin sauri.
Hidaya ta ce, "muga kuncinka."
Armad najin haka ya miƙa kuncinsa cikin sauri dai-dai bakin Hidaya. Hidaya ta saka bakinta akan kuncinsa ta sumbace shi. Sannan tayi masa raɗa a kunne. "Naji ance kayi kuka da aka ce na mutu da gaske ne?"
Armad najin haka ya haɗe rai cikin wasa sannan ya dunƙule hannu ya kutufe ta aciki yana cewa, "idan kika ƙara tafiya kika barni nida kene."
Hidaya ta ɗaga gira cikin alamun tsoro mai cike da tsokana ta ce, "aaarrgh.. Cikina."
Sarki Daljari da sauran ƴan kallo suka zaro ido suna kallon ikon ALLAH. Duk wanda yasan Heeda Baƙar Wuta bazai taɓa tunanin ganin haka ba. Ga dukkan alamu hatta sadaukai tsoffin ma'abota izza akwai inda suke sakkowa suyi dariya kuma su nuna soyayya.
A dai-dai wannan lokaci Armad ya hangi Nostaljiya lamarinda yasa annuri ya fice daga fuskarsa. Ya miƙe cikin sauri ya isa gare ta. Heeda bata ce masa komai ba ta gyale shi. Wata maganar sai an keɓe a gida.
Armad na isa ya rungume Nostaljiya. A lokacin ya dubi ƙirjinta yaga har yanzu yana zubarda jini amma abinda ya kwantar masa da hankali rayuwarta bata cikin hatsari. Numfashinta yana fita dai-dai. Idan ta samu hutu da ƴan maganinnika warewa zata yi.
Nostaljiya ta dubi Armad tana kakari ta ce, "ɗ..ɗanka y...yana lafiya babu abinda ya same shi." Tana magana tana taɓa cikinta da ɗaya hannunta.
Kunya ta rufe Armad yama rasa abinda zaice. "Ki daina magana ki bari ki warke."
Shi kuma Daljari ya danƙawa Nazara wani allon tsafi yana cewa, "ka riƙe wannan a wajenka saboda ɓacin rana. Yau dai Hidaya ta cece mu to amma baka san mai gobe zatai ba."
Nazara ya durƙusa ƙasa akan gwiwowinsa yana gaisuwa ga mahaifinsa yana cewa, "rayuta wata taka, mutuwa ta taka, mahaifina."
A lokacin da Armad yake shirin ɗaukar Nostaljiya ya dawo wajen Hidaya shima sarki Daljari yana shirin cirewa ɗansa Nazara tsarin jinin da yasa akansa.
A dai-dai wannan lokacin akaji wata ajiyar zuciya mai ban al'ajabi. Ga dukkan alamu muryar namiji ce amma kuma tsufan muryar yana da yawan gaske. Kai kace ta taso ne daga farkon duniya. A lokacin da kowa ya tara hankali yana jira yaga mai wannan ajiyar zuciya sai kawai takubba biyu aka gani sun bayyana.
Kowacce takobi takai tsayin sammai da ƙassai domin ba'a ganin ƙarshenta. A jikin kowacce akwai rubuce-rubuce na ɗalasiman farko. Wannan ɗalasimai anyi sune da jinin kowacce halitta dake yawo a doron ƙasa.
Kowa yaga bayyanar takubban biyu a sararin samaniya. Amma abinda ba'a kula ba shi ne tsinin wannan takubba a cake yake da ƙirjin Nostaljiya da kuma Daljari. Babu wanda yasan mai ya faru; kwatsam takubba biyu sun bayyana sun cake mutun biyu. Ba'a ma kula da sanda takubban suka cake Nostaljiya da Daljari. Tamkar dama can suna cake dasu.
Komai a lokaci ɗaya ya faru tamkar an tsayar da lokaci tayadda babu wanda ya iya motsawa kafin abin ya faru.
Yanzu-yanzu Armad da Nostaljiya suke dariya amma kuma cikin daƙiƙa ɗaya suna cikin jini, takobi ta cake Nostaljiya a ƙirji. Hatta Armad bai san abinda ya faru ba.
A dai-dai wannan lokaci da Daljari da Nostaljiya kaf kakarin mutuwa suke. Koda ganin haka sai kan Armad ya nemi yai tsawa. Abubuwan dake faruwa sun fara wuce tunaninsa.
Nazara yai ƙaraji ya rungume mahaifinsa. Cikin daƙiƙa ɗaya kacal Daljari ya faɗi ƙasa matacce. Da jikinsa da ruhinsa kaf sun mutu.
Saboda wani dalili Nostaljiya har yanzu da ɗan ragowar numfashi a jikinta. Ta dubi Armad tace, "Armanos... Kayi haƙuri dani kaji.."
Tana faɗar haka wani hawaye guda ɗaya mai zafi ya fice daga idanunta. Sannan ta faɗa kan kafaɗar Armad a mace.
Armad bai yadda da abinda yake gani ba saboda haka ya fara ƙinƙina yana cewa, "M...mata ta, m..matata... Zahra... Nostaljiya... Ki tashi... Ki tashi... Kin manta nace zan kaiki kiga yaya ta Hidaya? To ga tanan anan... Ki tashi... Ki tashi...."
Amma ina... Jikin Nostaljiya tuni ya fara yin sanyi. Ta rigamu gidan gaskiya.
Koda ganin haka sai kan Armad yai tsawa. Nan take hankalinsa ya gushe idanuwansa sukai fari fat ko kwayar baƙin ba'a gani.
Hidaya tai sauri ta tallafeshi tana kwala masa kira, "Armad... Armad... Armad..."
Amma ina hankalin Armad tuni ya gushe.
A gefe guda kuma Nazara na riƙe gawar mahaifinsa hawaye mai zafi na zuba daga idanunsa. Ya dubi wannan allo da mahaifin nasa ya bashi ya ƙara fashewa da kuka. Babu wanda yake so a duk duniya sama da mahaifinsa sarki Daljari. Nazara baya tsufa shi kuma Daljari ma'aboci izza ne saboda haka dukkaninsu sun daɗe a duniya. Wannan shekarar zasu cika shekara ɗari bakwai da kasancewa tare.
Ana cikin haka siffar wani mutun ta bayyana a bayansu. Idan ka duba zaka ga wannan mutumin ba wani bane illa... BIHANZIN MAI DAUWAMAMMEN SARA. Yana sanye da alkyabba ta sarakunan farko sannan kuma da kambun mulki a kansa. Wani haske mai ruwa dinare yana kewaya jikinsa. Sannan kuma idanuwansa sun canja matuƙa. A wajen ɓakin tsakiyar idon na da a yanzu ja ne.
Hidaya ta dubi Bihanzin cikin ɓacin rai da alhini ta ce, "idanuwan Shishirui?! Kaga dama ka fito dasu duniya ta gani kenan?"
Bihanzin yai dariya ya ce, "ke kika kaini bango amma lokacin futowarsu baiyi ba. Ba daban nayi shirin cewa wani abu irin haka zai iya faruwa ba da tuni kin tarwatsa min shiri."
Hidaya ta dube shi ta ce, "komin shirinka fasahar Jini-ukun dakai niyya ta lalace sai dai ka sake wani."
Bihanzin najin haka ya fashe da dariya yana cewa, "kinga Baƙar wuta wannan shi ne daɗin mutun yai shekara dubu yana shiri. A lokaci na farko da na karanta fasahar Jini-uku nasan cewa bazan samu damar aiwatar da ita a yadda take ba. A ƙa'idar fasahar tana buƙatar na zuƙi jini-ukun gaba ki ɗaya a lokaci guda wanda hakan zai iya ɗaukar kwanaki uku. Ni nasan ko Wilbafos ko Ururu wani daga cikinku saiya kawo min cikas. Saboda haka na shirya. Ya ɗauke ni lokaci amma daga baya na canja tsarin fasahar. Maimakon kwana uku abinda kawai nake buƙata shi ne daƙiƙa ɗaya. Indai na haɗa jini-uku na tsahon daƙiƙa ɗaya sannan daga bisani na kashe ɗaya daga cikin mutun ukun to na gama. Ina ganin a wannan lokaci na samu sama da daƙiƙa dari. Sannan kuma bama ɗaya ba ma na kashe mutun biyu da suka haɗa fasahar. Nan da kwana uku zan samarda fasahar jini-uku. Irin fasahar da akai amfani da ita aka samarda izza a doron ƙasa. Ni Bihanzin sai nafi ƙarfin kowa a doron ƙasa."
Bihanzin ya ƙara kyakyacewa da dariya. Kana ganinsa kaga cikakken matsafi.
Tuni Hidaya ta fuskanci abinda ke faruwa. Wannan haske dake kewaye da Bihanzin alamun fasahar Jini-uku ce. Zarar aka ce Bihanzin ya hattama wannan fasaha to zai samarda sihiri wanda girmansa yakai girman izza kanta. Koda yake babu wanda yasan mai wannan sihiri zai kasance sai Bihanzin amma sanin cewar sihiri ne wanda yakai girman fasahar izza ya isa yasa mutane karkarwa.
Abinda Hidaya bata fuskanta ba shi ne yadda Bihanzin ya samarda wannan takubba kuma ya sa suka kashe Nostaljiya da Daljari ba tare da ta kula ba, saboda haka ta dube shi ta ce, "a ina ka samo wannan takubba? Kuma tayaya kayi amfani dasu yanzu?"
Bihanzin ya fashe da dariya ya ce, "Nostaljiya tare muke kwana muke tashi saboda haka cikin sauƙi nasa Dafi a jikin izzarta wanda na haɗa da wannan takobi. Ita ma bata san da wannan Dafi acikin jininta ba. Shi kuma Daljari a lokacin dana je ƙasarsa na samu na maƙala masa nasa. Kiyi sani cewa a tun farkon wannan yaƙi da naso da tuni na kashe baba Dalja. Kai bama anan ba, da naso da tuni na kashe baba Daljari shekaru ɗari uku da suka wuce. Ko ni idan aka caka min wannan takobi saina mutu. Waɗannan takobi su kaɗai ne a doron ƙasa kuma idan su biyun suka haɗu su ne suke bada cikakken dauwamamman sara. Daljari yasan cewa takobin da nake amfani da ita ba ita ce asalin dauwamammen sara ba to amma abinda bai sani ba shi ne dalilin da yasa naƙi amfani data zahirin. To amma kinga yanzu babu abinda nake jira. Na riga na cimma buri na na haɗa fasahar jini-uku. A yanzu zan nunawa duniya fasahar dauwamammen sara ta haƙiƙa."
Yana faɗar haka ya tafa hannayensa inda takubban guda biyu suka haɗe suka bada takobi ɗaya. Bihanzin ya ɗaga takobin sama ya girgiza ta. Girman takobin yayi wa sama malafa. Kai kace babu wani abu a sammai sai wannan takobi. Sarki Mai Dauwamammen Sara.
Hidaya ta dube shi ta ce, "mutun kamar ka wanda bashi da tausayi ko kaɗan, wanda yake kashe ƴaƴansa dan biyan buƙatarsa bai kamata ya ci gaba da rayuwa ba. Ya zaka ji idan ka mutu kafin fasahar jini-uku ta afku?!"
Bihanzin ya nuna ta da ɗan'yatsa ya ce, "abinda nake ƙoƙarin gaya miki shi ne baza ki iya kashe ni ba. Ko kin kashe ni ya zaki yi da yarima Dumaƙisu dake tafe? Ya zaki yi da sauran sarakunan Jinzidal?"
Hidaya ta murtuke fuska ta ce, "bayan na kashe ka zanji da waɗannan."
Ana cikin sai Nostaljiya ta fara motsi lamarinda yasa gaban Bihanzin ya sara. Nan take ya fara gumi yana karkarwa yana nuna Nostaljiya da hannu. "Ya akai....."
Hidaya ta dube shi a nutse ta ce, "ka ce zuri'ar Wilbafos suna da girman kai bayan kuma a zahiri babu wanda ya kaika girman kai. Ka samarda fasahar Dauwamammen Sara kana ganin duk duniya babu wanda zai iya warkewa daga ita. Daga lokacin dana gane wace ce Nostaljiya ka rasa damarka ta kasheta." Tana gama magana ta tafa hannayenta lamarinda yasa iska ta ɗakko Nostaljiya wadda har yanzu bata farfaɗo ba ta kawo ta kusa da ita. Hidaya ta cilla ta cikin jakar tsafinta.
Sai a wannan lokaci Bihanzin ya fara nutsuwa bayan ya lura cewa Nostajiiya ce kaɗai ta rayu. Idan da ace harda Daljari to da fasaharsa ta Jini-uku ta lalace. Ya dubi Hidaya ya ce, "mutun ɗaya kacal daya taɓa rayuwa bayan na sare shi da takobin Dauwamammen sara shi ne Tarifil-fakta. Ban taɓa tunanin akwai wanda yake da irin sirrin Tarifil-faƙta ba a raye. Amma koma dai me kikai a banza. Fasahar Jini-uku ta tabbata."
Ana cikin haka sama ta fara rawa tana girgiza. Rana ta dusashe. Nan take hadari ya haɗo aka fara tsawa kafin ruwa ya kece. Ruwan yana da abin al'ajabi domin kafin yazo ƙasa yake ɓacewa ɓat. Bayan an shafe daƙiƙa sittin ana ruwan sai ruwan ya ɗauke sannan sama tayi haske. Idan ka kalli ƙasa ko ɗison ruwa ɗaya baza ka gani ba saboda dama can ruwan bai taɓa ƙasa ba.
Tun farkon sanda aka fara ruwan Bihanzin yai tsalle ya koma gefe ya tsaya takobi a zare. A lokaci na farko damuwa da kokwanto suka bayyana a fuskarka. A ransa yana cewa, "lokaci yayi. Ko ni ko Heeda ko Dumaƙisu wani zai mutu a yau." Nan take Bihanzin ya danna hannunsa cikin ƙirjinsa ya saka wani sihiri acikin ziciyarsa. Lamarinda yasa idanuwansa suka fara walwali suna haske. Sannan dauwamammen sara ta fara walwali.
Hidaya na gefe bata motsa ba. Ta ɗauki Armad ta riƙe shi a hannunta. Saboda wani dalili da ita kaɗai ta sani bata son saka shi cikin jakar tsafinta.
Ana cikin haka dukkan ruwan daya ƙone yabi iska ya fara haɗewa a waje guda. Cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗe izuwa surar yarima Dumaƙisu. Yana sanye da baƙar alkyabba. Yana bayyana iskar sarauta da mulki ta cika waje. A saman kansa akwai wani baƙin haske kamar fai-fai. Idan ka kalli hasken sosai zaka ga rayukan bil'adama na yawo aciki suna kuka da ihu mara sauti kamar wanda ake azabtarwa. Idan ka kalli wannan faifai tsahon lokaci zaka ji an fara zuƙar ruhinka ciki. Wannan faifai shi ake cewa TASKAR RUHI. Ita ce mafi girman fasahar gidan Ururu.
Kamar abin bai isa haka ba sai kwatsam sarakunan Jinzidal uku suka bayyana a bayan yarima. Sarki Han'ibal. Sarki Maikiro'Abbas. Sarki Deniz Iluru. Kowa ya hallara.
Yarima ya dubi Hidaya ya ce, "Hidaya Taidara Yunussa'ayi Albarizzaman Eyriyon Aldaima Wilbafos, alƙiyamarki ta tashi. Idan na saka ruhinki acikin Taskar Ruhina na tabbatar zan fita daga matakin DÉBA na shiga matakin izza na ƙarshe."
[DÉBA (DEVA IN ENGLISH) shi ne matakin dake gaba da Sammai]
Hidaya tai shiru bata ce komai ba kawai tana kallon Maikiro'Abbas da Han'ibal. Babu wanda yasan mai take tunani a wannan lokaci sai mahaliccin ta. Duk su biyun suka sunkui da kansu.
Duk da abinda yarima ya faɗa amma bai kaiwa Hidaya hari ba. Suna tsaye suna kallon juna.
Bihanzin ya numfasa ya ce, "yarima ina son muƙami na na sarkin Jinzidal saboda haka zan taimaka wajen kashe Hidaya." Yana faɗar haka yai tsalle ya koma bayan yarima. Yarima baice masa komai ba kawai kallon Hidaya yake itama tana kallonsa.
Bayan ɗan lokaci Hidaya ta ce, "ka fara koyon al'amuran izza shekaru ɗari biyu bayan na fara amma har ka iso Wadin Déba. Shehu Amraikugyu ya ce babu wanda aka taɓa haifa daya kaika ƙarfin kwakwalwa. Wataƙila kafi Tarifil-fakta. Wataƙila kafi Haruta da Maruta Ururu. Wataƙila kafi shehu Amraikugyu. Wataƙila kafi Kuyurussa'ayi. Amma ko kafi waɗannan baza ka iya kashe Armad Wilbafos ba. Idan ma turo ka akai ka kashe Armad kayi kuskure. Wannan kujera ta FADAR IZZA dake doron ƙasa ta farko Armad aka ginawa ita."
Yarima ya fashe da dariya sannan bayan tsahon lokaci ya ce, "wato kin gane ran Armad aka turoni na karɓa ba naki ba. Lallai kin cika hatsabibiya. Shekaru ɗari bakwai na taɓa kaiwa yarima Maruta Kuyurussa'ayi Ururu ziyara muka tattauna akan al'amuran izza. A lokacin yake gayamin kece halitta ta farko data gano babban sirrin Wadin Déba. Masu bautar rana sun daina bautawa rana sun dawo bauta miki saboda idonki na dama. Masu bautar wata sun daina bautawa wata sun dawo bauta miki saboda idonki na hagu. Lallai bayan na kashe ki ruhinki zai bani gudummawa sosai. Ba wani abin mamaki bane idan aka ce na wuce Wadin Déba na kamo sarki Kuyurussa'ayi."
Hidaya ta nuna sama. Sannna ta nuna ƙasa. Sannan ta nuna gabas, yamma, kudu da arewa. Haka na faruwa wani haske ya fice daga idon Heeda na dama ya juye izuwa wasu ɗalasimai wanda suka kewaye rana. Haka na faruwa wata ya bayyana a kusa da ranar. Wani hasken ya ƙara fita daga idonta na hagu wanda ya juye izuwa wasu ɗalasiman da suka bayyana suka kewaye watan. Bayan haka sai watan da ranar suka fara yiwowa ƙasa-ƙasa suna tunkaro Hidaya. Saida suka zo ƙasa-ƙasa yadda kowa yake iya ganinsu sannan suka tsaya. Hidaya ta dubi yarima ta ce, "Ruhina ko? Ina jira."
A wannan lokaci da yarima da Hidaya suka canja. Iskar dake kewayawa a jikinsu ta canja. Sarakunan jinzidal huɗu suka kewaye Hidaya amma ko kallonsu batai ba. Idanunta nakan yarima.
A lokacin da yarima ya motsa a lokacin Hidaya ta zare takobinta.
Han'ibal ya zare takobinsa ya kawowa Hidaya sara lamarinda yasa balbalin wuta ya fara ruruwa yana yowa kan Hidaya. A lokaci guda Maikiro'Abbas ya samarda tsaunin ƙanƙara ya cillowa Hidaya shi. Deniz ya saukarda aradu mai tartsatsi ya kawowa Hidaya mummunan hari.
Hidaya ta samarda wata ƙawanyar haske wadda akayi da izza ta rufe jikin Armad. Duk haren-haren sarakunan Jinzidal suka sauka akanta amma ko kwarzane basu yi mata ba. A dai-dai lokacin da haren-haren zasu sauka shima yarima ya ɗaga takobinsa zai kawo nasa saran amma a lokacin idanun Hidaya suka fara zubarda jini.
Yarima na ganin haka ya ajiƴe takobinsa ya kirawo wasu ɗalasimai wanda suka sa dutsen Hajarul-ururu gaba ɗayansa ya sakko ya kareshi. Idon Hidaya na dama yana ɗauke da hoton rana na hagu kuma yana ɗauke da hoton wata. A dai-dai lokacin da idanun suka fara jini hoton rana ya bayyana akan iska yai kan yarima. Ranar data sakko ƙasa-ƙasa tai kan yarima. A dai-dai lokacin shi kuma ya kirawo Hajarul-ururu ya kareshi. Ranar da Hajarul-ururu suka haɗu lamarinda yasa dukkan ƙasashen ƙasa suka fara girgiza. Ƙasa ta fara tsattsagewa. Nan take dutsen Hajarul-ururu ya tarwatse yai raga-raga. Ita ma ranar ta tarwatse. Amma duk da haka hoton ranar bai ɗauke ba. Ya ƙarasa ya dira akan yarima. Yarima yai ƙaraji mai tsoratarwa lamarinda yasa tsirrai suka fara mutuwa. Ruhin mutanen dake cikin Taskar ruhinsa ya fara ɓulɓulowa yana shiga jikinsa yana ƙoƙarin kareshi. Amma duk da haka saida ruhinsa ya tsattsage, fatarsa ta tsofe sannan aka ɗaure izzarsa.
Idan ba'a mantaba dutsen Hajarul Ururu shi ne ya raba doron ƙasa na farko da ƙasashen ƙasa sannan kuma shi ne yake ɗauke da ankwar da take hana mutanen ƙasashen ƙasa haura izza dubu arba'in. A lokacin daya tarwatse dukkan ankokin suka watse sannan haske ya sauka zuwa ƙsashen ƙasa. Wani sabon sirrin izza ya fara sauka yana cika ƙasashen ƙasa. Hidaya ta cire hijabi.
Sai dai a dai-dai lokacin da yarima yake tsofewa akwai abubuwa biyu dake faruwa. Abu na farko yarima ya haɗe dukkan ƙarfin Taskar izzarsa acikin mashinsa ya harbawa Hidaya shi. Abu na biyu daya faru shi ne sakkowar wani mashi daga doron ƙasa na farko daga cikin fadar izza ta sarki Kuyurussa'ayi.
Babu wani abu mai rai daya ga fitowar wannan mashi wanda ya yiwo kan Hidaya gadan-gadan sai mutun ɗaya wato Bihanzin. Ta bayanta mashin izza daga fadar sarki Kuyurussa'ayi ta gabanta kuma mashin Taskar ruhin yarima. Dukkansu sun kai ƙarfin fasaharta ta rana da wata.
Hidaya tana lure da mashin Taskar ruhin yarima kuma tuni tayi niyyar amfani da idonta na hagu ta tarwatsa shi. To amma a lokacin data motsa a sannan taji gashin wuyanta ya miƙe wata iskar tsoro ta rufe ta. Tana waiwayawa ta ankare da mashin yana gabda tsire Armad.
Ga mashi a gaba yana neman tsire ta ga kuma wani a baya yana neman tsire Armad. Ko ita ko Armad.
Ba tare da ɓata lokaci ba Hidaya tayi amfani da idonta na hagu ta tarwatsa mashin da zai kashe Armad. A lokaci guda mashin yarima ya cake ta a ƙahon zuci.
Haka na faruwa jini ya fara feshi daga ƙirjin Hidaya. A lokaci guda ta ƙara hango wani mashin ya taso daga doron ƙasa ma farko ya tinkaro Armad.
Idanun Hidaya suna ɗauke da fasahar rana da wata amma indai tayi amfani dasu to sai ta shiga halwa ta ƙara yin shiri. Indai tayi amfani da fasahar sau biyu a jere to idanun zai makance har abada. Amma a halin da ake ciki kafin tayi wani tunani tuni mashin yana kan Armad. Hidaya ta ƙara tarwata mashin da fasahar wata lamarinda yasa idonta na hagu ya rufe ruf ya makance. Sannan a lokaci guda tayi amfani da fasahar rana dake idonta na dama ta ɗaure doron ƙasa na farko. Babu wani mahaluƙi mutun ko aljan da zai iya ƙara fita daga doron ƙasar indai akwai ɗaurin.
Yarima ya kalli jikinsa yaga dukkan izzarsa ta bushe ta sanƙare. Ya dubi Hidaya rai a ɓace ya ce, "kina tunanin zanzo kashe ki ba'a shirye ba? Minti nawa ɗaurin da kikai zai ɗauka? A lokacin zaki fuskanci kuskurenki, makauniya."
Yana zuwa nan a zancensa idanuwan Hidaya sun makance babu alamun haske aciki.
Hidaya ta ciji harshe. Ita ma tasan ɗaurin da tayi wa doron ƙasa na farko bazai daɗe ba. Saboda haka nan take ta juya ta nufi sashin Ikwatora. Har yanzu mashi na cake a ƙirjinta, jini na zuba.
Yarima na ganin wajen da Hidaya tayi ya dakawa sarakunan Jinzidal tsawa. "Ku kawo min ita kafin ta ƙarasa ikwatora. Da ita da yaron dake hannunta."
Yana rufe baki Dul'ururu ya sauka daga doron ƙasa na biyu. A bayansa akwai rundunar Dordor sama da dubu maitan. Idan ba'a mantaba duk mai bi takan ruwan saiya biya idan ba haka ba Dordor su cinyeshi. Sarki Dul'ururu shi ne mamallakin wannan Dordor dake rangadin Bango. Yana bayyana suka haɗu da sarakunan Jinzidal suka bi bayan Hidaya.
Dul'ururu yana jifa da taurari su kuma sarakunan Jinzidal suna aikawa Hidaya hare-hare daban-daban. Dordor na ƙoƙarin tare mata hanya. Mutun ɗaya da har yanzu bai kai sara ba shi ne Bihanzin. A taƙaice dai har yanzu babu wanda yaga zahirin dauwamammen sara. Hidaya ta makance saboda haka ba jimawa suka sha kanta. A lokacin Hidaya ta fito da Nostaljiya daga jakar tsafinta. Abin mamaki kamar wadda aka saka a asibiti tana fitowa ta ware babu alamun ciwo a jikinta.
Hidaya ta danƙa mata Armad ta ce, "zan riƙe su anan ki shige sashin ikwatora."
Ba tare da jiran amsaba Hidaya ta danƙa mata Armad sannan ta juya ta fuskanci Dul'ururu da sauran sarakunan Jinzidal.
Nostaljiya tayi wa Bihanzin kallon tsana guda ɗaya kafin ta ciji harshe ta arce.
Bihanzin ya fashe da dariya ya ce, "kina tunanin kyale ki zamu yi?"
Nan take Bihanzin da Dul'ururu suka sha kwana zasu bi bayan Nostaljiya amma Hidaya ta ɗaga hannunta sama tare da kiran wasu ɗalasimai a sirri. Haka na faruwa wata wuta baƙa-ƙirin ta fara ɓulɓula daga ruhinta. Cikin daƙiƙa ɗaya wutar ta haɗe da samaniya sannan ta tokare da titin bayajidda dake gabas da yamma ta toshe duk wata hanya da zasu iya bin Nostaljiya.
Dul'ururu yai ƙaraji ya ce, "Baƙar-wuta ko? Wutar da akace duk abinda ta taɓa sai ta ƙone ƙurmus. Dordor ku danna." Yana rufe baki dubban Dordor dake bayansa suka afkawa wutar. Amma duk wanda ya taɓa ta sai kaga take ya narke.
Hidaya na tsaye jininta ya kus ƙarewa. Zuciyarta a cake da mashi wanda yake ta zuƙe mata ruhi. Sannan kuma ga baƙar wuta wadda ita ma da ruhinta take amfani.
Deniz, Dul'Ururu, Maikiro'Abbas, da Han'ibal suka raja'a wajen kaiwa Heeda hari. Hanya ɗaya da zasu kawarda baƙar wuta shi ne su kashe Heeda. Amma duk da kasancewarta a makance su biyar sun kasa cimmata. Duk da kasancewarta a makance tana sarrafa takobinta kamarda.
A dai-dai wannan lokacin wani mashin irin wanda ya taso daga fadar doron ƙasa na farko ya ƙara tunkaro Hidaya daga doron ƙasa na farko. Taji tahowarsa lamarinda yasa ta gane cewa lallai akwai wani abu dake faruwa wanda bata sani ba.
Kaɗai yarima Dumaƙisu da sarki Kuyurussa'ayi ne ke iya sarrafa irin wannan mashi. Ta riga ta ɗaure yarima sannan kuma ta ɗaure doron ƙasa na farko to daga ina mashin yake? Tana cikin tunanin yadda zatai da mashin sai taji wani mashin ya tashi daga doron ƙasa na biyu ya nufi Armad da Nostaljiya. Kamar abin bai isa haka ba wani mashin ya ƙara tashi daga doron ƙasa na uku da na huɗu da biyar da shida. Dukkan mashin sukai kan Armad.
Hidaya ta gane abinda ke faruwa to amma tuni idanuwanta suka makance yadda baza ta iya amfani da fasahar rana da wata ba. Nan take ta ɓace daga inda take ta bayyana a gaban Armad da Nostaljiya wanda ke dafda shigewa ikwatora.
Mashi na farko ya cake a ciki. Na biyu ya cake ta a ƙugu. Na uku a cinyar hagu. Na huɗu a cinyar dama. Na biyar a kafaɗa. Na shida yayi ƙoƙarin kauce mata ya cake Armad amma ta miƙa wuyanta ya cake ta a wuya. Dukkan kayanta sun koma launin jini.
A dai-dai wannan lokaci tayi amfani da ragowar ranta ta cilla Nostaljiya da Armad cikin Bango suka shige sashin ikwatora.
A wannan lokaci sarakunan Jinzidal suka iso tare da Dul'ururu. Dul'ururu yai tsalle yabi bayan su Armad amma kanya isa sun shige.
Abin mamaki ran Hidaya na gabda fita amma murmushi tayi. Sarakunan Jinzidal suka hauta da sara da suka. Dul'ururu yana caka mata takobi tako ina. Amma duk da haka Hidaya tana tsaye bata je ƙas. Har saida ta daina motsi suka tabbatar ruhinta ya fice sannan suka tsaya.
Dul'ururu yayi ƙoƙarin kama ruhinta kafin ya ɓace amma ƙarfinsa bai kai ba.
Bihanzin ne ya fara ɓacewa. Burinsa ya cika. Sannan sauran sarakunan Jinzidal. Shi kuwa Dul'ururu wajen yarima ya koma.
Yarima na ganinsa ya ce, "ka kama ruhin?"
Dul'ururu ya girgiza kai ya ce, "amma dai Hidaya ta mutu. Sai dai wata. Zaka iya motsawa?"
Yarima ya girgiza kai ya ce, "duk da ta mutu wannan ɗaurin da tayi min zai ɗauki watanni kafin na iya motsawa na dawo da izza ta."
Dul'ururu ya numfasa ya ce, "zan kawo runduna na ajiye anan domin kai. To amma ban gane daga ina masun da suka kashe ta suka taso?"
Yarima ya kyakyace da dariya ya ce, "abinda ya yaudare ta shi ne ilminta na yadda aka kashe Eyriyon. Kowa yana tunanin mashin da nai amfani dashi na mahaifina ne. Ana ganin ban isa na samarda mashin dazai kashe Eyriyon ba. Saboda haka nayi amfani da wannan ilmin kafin na fito daga doron ƙasa ta farko na dasa masu uku a fadar ta yadda zan iya sakarsu a ko'ina nake. Kaga idan na harbo mata su zatai tunanin sarki ne yake kawo mata hari. Hakan zaisa tayi amfani da idonta a inda bai kamata ba. Domin da tasan nine na harbo mashin da baza ta ɓata lokacinta wajen ɗaure doron ƙasa na farko ba.
"Sannan bayan na sakko abinda na fara yi shi ne dasa mashi ɗaya a kowacce doron ƙasa. Abinda kawai nake jira shi ne ta saki jiki cewa ta kama ni kuma ta rufe doron ƙasa na farko. A lokacin zanyi amfani da masun dana ɓoye a ƙasashen ƙasa. Amma duk da na kashe ta ban cika aikin da aka bani ba. Aikina na kashe Armad amma gashi ta ɗaureni kuma Armad ya gudu. Ina Bihanzin? Sarki ya ce akaishi."
***
A dai-dai lokacin da yarima suke tattaunawa Bihanzin ne ya bayyana a ƙarƙashin ƙasa ƙofar garin Shadeniza inda matafiyan alwashi suka shige. Garinsu Nusi Djinn. Daularda aka ƙulle tsahon zamani.
Abin mamaki sai ƙofar ta buɗe. Matafiyan Alwashi su ɗari suka fito sannnan aka ƙara ƙulle ƙofar. Suna bayyana suka faɗi gaban Bihanzin sukai gaisuwa.
Suka haɗa baki suka ce, "Ya shugabanmu mai kake so mu aiwatar."
Bihanzin na tsaye bai amsa ba kawai tunani yake. Tunaninda babu wanda yasani sai mahaliccinsa.
Comments
Post a Comment