Skip to main content

446-450

 Can sai kaga kunne a ƙanƙare, can kaga yatsa, can kaga ido, gaba ɗayan Iluru yayi daga-daga ya zama babu. Ko binne shi iyalinsa baza su samu damar yi ba. 


"I...I....Iluru ya mutu," wani sadauki ya faɗa cikin kinkina. Kana gani kasan sun kasa fahimtar abinda ke faruwa. Musamman duba ga cewa Iluru fa sarkin jinzidal ne guda. Ace duka ɗaya an gama dashi. Kuma fa muƙamin su ɗaya da Maikiro'Abbas. 


"Maikiro!"


"Maikiro!!"


"Maikiro!!!"


Mayaƙa suka hau murna da ihu. 


A nasa ɓangaren Maikiro'Abbas bai koma wajen daya baro ba. Tsayawa yayi anan yana kallon Dul'Ururu da mayaƙan Ururu kamar yana ce musu idan sun isa su taho. Ga dukkan alamu sarkin ya fara gajiya da jira.


A dai-dai lokacin da Iluru ya zama ƙanƙara ya tarwatse a lokacin faɗa ya ƙara tsamari a ɓangaren Ururu. Ganin abinda Maikiro'Abbas yayi wa Iluru yasa Dul'Ururu ya taka a fusace wajen da Armad yake kwance da niyar ɗaukar fansa. 


Armad yaji tahowar sa. Jikinsa ya ɗan fara dawowa dai-dai saboda haka yayi ƙoƙari ya miƙe ya fuskanci Dul'Ururu. Mayaƙan dake gurin suka basu guri. 


"Mutu, Armad Wilbafos." inji Dul'Ururu. Ƙarfin izzar Kamalar-ruhi ta shiga sautinsa tayi kan Armad. 


Armad ya ɗaga hannu ya nuna shi. "Mutu, Dul'Ururul Ururiy." 


Ƙarfin ikon Armad ya fito ya daki na Dul'Ururu. Wuta ta tashi tayi sama.


Haske da tartsatsin izza ya cika wurin. A hankali ya dunkule a tsakiya sannan a ya fashe. Wata iska mai ƙarfi ta ɗebi duk wanda ke kusa tayi jifa dashi. Dukkan wanda ke filin yaƙin ya juyo yana kallon ikon ALLAH. 


Bayan da ƙura ta lafa sai aka hango Dul'Ururu a tsaye riƙe da sandarsa. Armad kuwa anyi jifa dashi can nesa. 


Cikin fushi irin na bakaken aljanu, Dul'Ururu ya ɓace ya bayyana akan Armad. Sandar tsafinsa a sama yana niyyar saukewa Armad ita. 


Armad ya haɗe hannu guri guda. Nan take jikinsa ya fara haske. Kafin Dul'Ururu ya ƙaraso Armad yayi bindiga ya tashi da Dul'Ururu dama duk wanda ke kusa. 


Wata nakiya tayi sama ta tokare sararin samaniya. Tsahon dakiku babu abinda ake gani sai haske. 


Bayan hasken ya lafa sai Dul'Ururu ya bayyana. Yana tsaye kikam ya cake sandarsa a ƙasa da hannu biyu. Babu alamun rauni ko ɗaya a fuskarsa. Hasalima ko ƙura fuskarsa bata yi ba. 


Acan nesa Armad ya bayyana yana haki. Yayi tunanin aƙalla zai jefar da Dul'Ururu ƙasa. Ganin yadda sarkin ya tsaya ya shanye harin a tsaye sai zuciyar Armad tayi baƙi. Wannan shi ne harin da yayi jifa da Ƙaraiƙisu fa. Shi ne harin daya kwantar da Diwani tsahon lokaci. Shin ana nufin ace hatta fasa ruhinsa da Armad yayi baiyi aiki ba kenan? Ƙarfin fashewar ruhi yana iya kashe deba kai tsaye. Musamman idan harin ya sami mutun ba a cikin shiri ba. Shi kansa Armad ba kullum yake son yin amfani da harin ba saboda illar da yake yi masa. Amma ace Dul'Ururu ya shanye harin yana tsaye kan ƙafafunsa ba tare da yaje ƙasa ba. Wai wane irin ƙarfi sarkin yake dashi?


A hankali Dul'Ururu ya zare sandarsa daga ƙasa sannan ya juyo a hankali ya fuskanci saitin inda Armad yake. Mutanen dake kan hanya tsakaninsa da Armad suka kauce cikin tsoro suka basu fili. Armad ya kalli sarkin, shima sarkin ya kalleshi. A lokacin Armad ya fuskanci akwai jini a hancin Dul'Ururu na dama wanda kuma har yanzu yake ɗisa. Harinsa ya jiwa sarkin ciwo kawai sai dai ba yadda yake tunani ba.


Fuskar Dul'Ururu ta ƙara yin baƙi ta turnuke, wani abu wanda Armad baiyi tunanin zai iya faruwa ba tunda dama tun can a murtuke take, ya nuna Armad da sandarsa. Wani haske ya fita daga sandarsa ya daki Armad a kirji. 


A lokaci na farko Armad yayi ƙara. Yana ji kamar ruhinsa zai tsage. Jini ya fara fita daga idanunsa. A take ya fara ganin dishi-dishi. Da kyar ya iya tsayawa kan ƙafafunsa.


Dul'Ururu yayi tsalle ya dira akan ƙasa. Ƙafarsa tana taɓa ƙasa wajen ya tsattsage. Sarkin yayi ƙaraji ya nufi Armad da mugun nufi zai ƙarasa shi. 


Wani abu ya dira a tsakanin sarkin da Armad. Ƙura ta turnuke tayi sama, ƙara ta cika kunnuwan masu kallo. 


Sarkin ya ɗan tsaya yana yamutse fuska yana kallon inda abin ya dira. 


Bayan ƙura ta lafa sai Nusi ta bayyana a wajen. Babu wanda yasan yadda akai ta baro Diwani ta taho nan domin shigarwa Armad. Ganin haka Armad yayi maza ya taho wajenta a guje. Shima Dul'Ururu takewa yayi da gudu ya taho wajen Nusi.


Ita kuwa Nusi bata tsorata. Maimakon ta gudu sai kurum ta durkusa ta ɗora hannu akan ƙasa. 


"Fasahar Noma, ƙarni na uku."


Tana rufe baki ƙasa ta fara girgiza tana darewa. Duk inda ya dare sai kaga gwarangwal din mutane suna fitowa. Kowanne idan ya fito sai ya haɗe da ɗan uwansa. A haka suka girma sosai kafin Dul'Ururu ya ƙaraso. Ƙatoton gwarangwal din wanda a yanzu yafi Dul'Ururu girma ya kawowa sarkin wafta. Iska mai ƙarfi ta tashi sama kamar guguwa. Dul'Ururu yaja da baya ya dunkule hannu ya daki hannun gwarangwal ɗin. 


Tartsatsin haske ya tashi sama. Amma gwarangwal ɗin yana nan a tsaye bai fadi ƙasa ba. Shi kansa Dul'Ururu sai da ya haɗe gira cikin mamaki. 


Armad yana ƙarasowa ya dubi Nusi ya ce, "koma sama."


Nusi ta ɗanyi shiru kamar ta yadda amma daga baya ta girgiza kai. 


"Mu tarar masa mu biyu. Akwai Burjan acan, zai iya tare Diwani."


Armad ya ɗora hannu a kafaɗarta. 


"Nusi, kada ki damu. Ina da shirin samun galaba akansa amma idan kina nan bazai yiwu ba."


Jin haka ta ƙura masa ido tsahon dakiku kafin ta juya ta tashi sama ta koma gaban filin. 


A dai-dai lokacin Armad ya lura akwai wani sirri dake fita daga jikin ƙasa yana shiga jikin gwarangwal ɗin. A duk sanda wannan sirri ya shiga sai kaga wasu ƴan ƙananun layuka sun bayyana a jikin gwarangwal ɗin wanda zasu yi haske na ɗan lokaci kafin su ɓace. 


Dul'Ururu ya ƙara kaiwa gwarangwal ɗin duka ta hagu amma abin ya kauce da saurin tsiya. A take Armad ya fuskanci kamar ƙara gudu abin yake yi. 


Kafin Dul'Ururu ya nutsu ya dawo da hannunsa baya, abin ya kawo masa duka da tsinin ƙafarsa. Dul'Ururu yayi tsalle sama ya kauce. 


Fasahar Noma, ƙarni na uku. Armad ya ƙara jinjina sunan. Tabbas Nusi ta samar da babbar fasaha. Ko a yanzu ƙarfin mutun-mutumin yakai Sammai. Sannan kuma ƙara ƙarfi yake yi duk bayan dakika. Sai dai kuma kash, Armad ya riga yasan abin bazai iya ja da sarkin ba.


Ai kuwa kamar sarkin yana jin abinda Armad yake tunani sai kawai yasa sandarsa a fusace ya daki ƙirjin gwarangwal ɗin. Abin yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai Dul'Ururu ya ƙara sauri ya cimmasa kafin ya kauce. 


Suna haɗuwa izzar dake jikin sandar ta fito ta shiga jikin gwarangwal ɗin. A take ƙasusuwan abin suka marmashe suka bi iska. Wato a yanzu Armad ya ƙara tabbatar da cewa sandar tsafin Dul'Ururu ba haka kawai take ba. Tabbas akwai sirri babba acikin ta. Wani abu da Armad ya ƙara ganowa shi ne a zahiri bawai hakikanin izza ce take fita daga jikin sandar ba, a'a, wani abu ne mai kama da izza. Kamar zaka iya cewa Negrinki ce, ko kuma wani abu mai kama da hakan. 


Armad yana cikin tunani yaga gilmawar sarkin ta gefen idonsa. Sandar tsafinsa tana gab da dukan ruwan cikin Armad. 


"Aiban'shisu, ƙarni na biyu!"


Armad ya kira sabuwar fasahar. 


Acikin rabin dakikar daya rage Dul'Ururu ya same shi sai kurum ya ɓace ya bayyana a bayan Dul'Ururu. Yana bayyana ya saukarwa da sarkin Hannun Aradu. Walkiya ta sauka akan Dul'Ururu amma a fuskarsa ko kaɗan babu alamun damuwa. Hasalima mamaki yake yadda Armad ya iya subuce masa har takai bai same shi ba. 


Acikin ƙurar walkiyar, Dul'Ururu ya ƙara kawowa Armad sura. Rabin dakika kafin ya sami Armad sai kawai Armad ya ɓace ya saukar masa da Zaren Manyan Mayu ya zuƙe masa izza.


A take sarkin ya dawo da izzarsa. Sai dai duk da haka sarkin bai daina mamaki ba. Tayaya Armad yake subuce masa. Yafi Armad sauri da gudu da zafin nama ta kowanne bangare. Amma tayaya saura rabin dakika ya taɓa Armad zai ringa subuce masa. 


A duk sanda Armad zai kauce sai kaga ƙasar dake ƙasan ƙafarsa ta ɓace, an musanya ta da ƙasar wajen da Armad zai koma. Kamar fasahar Aiban'shisu ce amma kuma da bambanci. 


Dul'Ururu ya ƙara kaiwa Armad sara amma Armad ya kauce ya kuma saransa da takobin Dorawa Abada. 


Dul'Ururu yaja da baya ya tsaya yana kallon Armad cikin mamaki.


Acan gaba kuma ana ci gaba da fafatawa kamar yadda aka fara. Tahowar Nusi ta bawa Diwani damar kaiwa Rabi hari. Sai dai harin bai cimma manufa ba tunda kwamanda Burjan ya tare Diwani. Nusi tana zuwa kawai sai ta saka rassan bishiya ta kewaye Rabi a wani salo na bada kariya. Idan ka hangi abin daga nesa zaka ga kamar rumbun itace ne ya rufe Rabi. 


"Rabi?" Inji kwamanda Burjan. "Sai kin hanzarta fa."


Komai Rabi take yi har kawo wannan lokaci bata karya kafin ba?


Abin mamaki har yanzu Rabi tana tsugunne ta kasa motsawa. Idanunta cike da hawaye.


***

Bari mu koma shekarun baya. 

***


Bayan Amri, Ururu sun sallama al'ummar ƙasashen ƙasa shekaru da dama. Suna ganin basu da buƙata da ƙasashen ƙasa ko kaɗan. Bayan lokaci ya tsawaita sai masu bakaken idanun suka yanke shawarar su kawo rangadi ƙasa domin ganin halin da mutanen da suka turo suke ciki. Shin sun ƙarasa mutuwa ko kuma akwai saura?


Suna zuwa sai suka tarar al'umma sun yalwatu sun ginu. Akwai tsarin rayuwa da gine-gine da masana'antu. Komai yana tafiya a bisa tsarin sarkin samudawa Deniz Huhutu. 


"Ahir ɗinku!" Ururu suka gayawa samudawa. "Dole abi tsarin bakaken idanu ayi biyayya ga rukunai biyu."


Sarki Huhutu ya kira manyan kwamandunsa suka fito yaƙi da masu bakaken idanun. Sai dai a har kullum kamar yadda tarihi ya nuna Ururu sune suke yin nasara indai a filin yaƙi ne. Bayan Ururu sun kashe deniz Huhutu a kamfen na farko sun tura denizawa ƙarƙashin ƙasa sai suka juyo kan ragowar al'umma. 


Tsari ne suka kawo na a daina yaƙi. Suka hana manyan ƙasashe yaƙar ƙananu saboda haka jama'a suka zauna lafiya. Abinda kawai masu bakaken idanun suka buƙata daga mutane a lokacin shi ne su shigo jinzidal. Duk ƙarshen shekara su kawo bayi ayi gasa dasu. Jama'a suka karɓi tsarin saboda sun gaji da yaƙi. Da dama suna ganin hakan yafi sauki akan kashe-kashe da yake-yake da ake yi. 


Cikin wata guda Ururu suka sabunta ginin tsohuwar fadar marigayi sarki Huhutu dake doron ƙasa ta biyu. Sarki Kuyurussa'ayi ya turo babban hadiminsa Dul'Ururu domin yazo ya kula da cinikin bayin. Daga baya aka naɗa Dul'Ururu a matsayin babban wakilin sarki Kuyurussa'ayi a ƙarƙashin ƙasa sannan kuma akai masa sarautar doron ƙasa ta biyu bayan ya gama korar dukkan masu goyon bayan tsohuwar daular denizawa dake rayuwa a doron kasa ta biyun. 


A haka sai da akai shekaru ɗari da doriya Dul'Ururu ne da kansa yake kula da harkokin jinzidal dake ƙasashe shida na ƙarƙashin ƙasa. Wane dalili ne yasa Ururu suka yanke shawarar kirkiro sarautar sarakunan jinzidal? Abinda yazo a tarihi shi ne an kirkiro gasar ne saboda sarki Maikiro'Abbas, to amma ainihin labarin shi ne mutane basu sani ba. 

***


Bari mu koma fadar shugaban arnen daji Maikiro'Abbas. 


"Mai girma, Abbasu," hadimin ya zube a ƙasa ya kwashi gaisuwa. "Masu bakaken idanu sun turo da takarda."


Abbasu ya ɓata rai. Rabi ta wuce gaba ta fizgi takardar ta buɗe zata karanta. Kafin ta fara sai wata mace wadda tama fita fari ta fizge zata fara karantawa. Ita ma kafin ta karanta sai wani namiji baƙi wankan tarwaɗa ya fizge. 


"Kulu?" Macen ta farko data kwata daga hannun Rabi ta daka masa tsawa. "Ka saurara." 


"Kema, Shema'u, ki saurara. Nina fara karba saboda haka a barni na karanta."


"Anƙi a baki ɗin," inji Shema'u. "Naga ni ce babba."


"Kai.." Kulu ya wage baki. "Naga ni aka haifa da maraice."


"Kaiii," Shema'u ta harari Kulu. "To ina ruwana? Koda yaushe aka haifeka bai shafe ni ba."


Nan take kowa ya cafi gefen takardar suka fara ja.


Wani saurayi zaune kusa da Abbasu ya tako da gudu yana cewa, "banzaye, kada ku yaga."


Ai kafin ya ƙaraso kowa acikinsu yaja rabonsa sun yaga takardar. Ɓarin dake hannun Shema'u ya daskare. Ɓarin dake hannun Kulu ya jike da ruwan zafi ya narke. Ɓarin dake hannun Rabi shi kaɗai ya tsira.


"Aaarghh..." Saurayin yaja dogon numfashi. "Wai ku mai yake damunka. Baku da nutsuwa ko kaɗan. Gashi baku da tsari da shiri da tsafta irin ta mutanen farko."


Duk su ukun suka juyo suka kalli saurayin. "Fulafunu, harda zagi?!!"


Fulafunu yaja wuyar farar rigar dake jikinsa sannan ya gyara hannun rigar. Komai dake jikinsa fari ne tun daga sama har ƙasa, babu ko ɗison datti a jiki. Gashin kansa dogo ne, baƙi, mai kyawun haske. Babu abinda yake sai sheki da walwali. Kana gani kasan kullum acikin gyaran wannan gashi ake. 


"Ku ringa tsafta a kowanne lokaci," inji Fulafunu. "Idan da kuna yin tsafta yadda ya kamata to da baza ku ringa yin abinda kuke yi ba."


"Fulafunu? Ka saurara!"


Suna rufe baki suka yi tsalle suka afka kan Fulafunu. Su ukun suka tukuikuye shi suka faɗi ƙasa suna birgima. Da kyar Fulafunu ya samu kansa ya miƙe. Abinda ya fara dubawa shi ne wuyan rigarsa inda ya shafi baƙi. Da gudu ya fice daga tantin yana neman ruwa ya wanke. 


Abbasu wanda yake zaune yana kallon komai sai kurum ya fashe da dariya. 


"Hahaha... Ƴaƴana, ƴaƴana... Yanzu gashi kun yaga sakon da aka kawo mana."


A lokacin Rabi ta tuna ashe ta yadda tsarin takardar dake hannunta. Ta fara dube-dube. Da kyar ta hango shi acan nesa. Ta ɗakko ta karantawa sarkin. 


"....zamu yaƙe ku..."


Iyakacin abinda kurum yake jikin takardar kenan. Babu farko babu ƙarshe. 


Sarki yana jin haka ya miƙe tsaye a fusace. 


"Ayi shirin yaƙi," inji Abbasu. "Zasu yaƙe mu? Yau iskancin bakaken idanun yazo kaina kuma?"


"Wuuu," inji Shema'u. "Yau zamu kashe masu baƙin ido-yau zamu kashe masu baƙin ido."


"Takobina ta ɓalle wancan satin," inji kulu. "Waye zai ara min tasa?"


"Ku tsaya," inji Rabi ta tari numfashinsu. "Baba, ai bamu ji mai suka ce gaba ɗaya ba balle mu yanke hukunci. Ya kamata mu tsaya mu karanta komai tukunna."


"Banda Anbalu da suka kama akwai wani karin bayani da muke nema?" Inji Abbasu. "Ku shirya. Yau da yamma zamu silala mu saro kan Dul'Ururu mu kwato Anbalu."


Da yammaci likis Abbasu ya ɗaura sirdi dashi da mutanensa sukai azama suka tunkari doron ƙasa ta biyu. 

***

Fadar Dul'Ururu a wancan lokaci da jar ƙasa akayi mata daɓe da fenti. Yawanci mutanen da suka zagaye Dul'Ururu masu bakaken idanu ne. An rawaito cewa sarkin baya aminta da wani indai ba ɗan ƙabilarsa ba. 


"Ance ku ajiye makaman ku a waje kunyi gardama," inji Dul'Ururu, yana kallon Abbasu da ya'yansa cikin shirin yaƙi.


"Akan me zamu ajiye makamai a gidan abokan gaba?" Inji Abbasu. 


Akayi kallon-kallo tsahon dakiku kafin Dul'Ururu ya fashe da dariya. Ya taso daga kan kujerarsa ya taho inda Abbasu yake tsaye. 


"Mun kama ɗan ka Anbalu da laifin karya dokokin jinzidal har uku," inji Dul'Ururu. "Mutane na suna ganin kawai mu sare masa kai amma ban aminta ba. Ina ganin mu tattauna. Babu wani abu da baza mu samo amsar sa ba ta hanyar tattaunawa."


Maimakon ya bashi amsa sai Abbasu ya juyo ya kalli Rabi. 


"Dama na gaya miki sune suka kama Anbalu," inji Abbasu. Sannan ya juyo wajen Dul'Ururu. "Kasan ni arnen daji ne. Uba na ma arnen daji ne. Wannan kalkale zance da sarrafa harshe na ƴan siyasa duk ban sanshi ba. Sai dai abinda na sani shi ne idan kaga mutun ya iya zance to yawanci makaryaci ne."


Wasu fusatattun mayaƙan Ururu suka zare baka suka saita Abbasu zasu harbe shi saboda yayi batanci ga sarki. Shema'u ta ɗan daki ƙasa da ƙafarta. Nan take daɓen dake fadar ya ƙanƙare. Sannan ƙanƙarar ta yadu ta cika fadar. Kafin kace kwabo duk wanda ke kusa da Shema'u ya ƙanƙare harda Rabi da Fulafunu da Kulu.


Shi kuwa Abbasu kawai ci gaba da magana yayi kamar ma bai ga abinda ya faru ba. 


"Zaka bani Anbalu ko kuwa?"


Dul'Ururu ya ɗan bata rai kafin ya ƙara fashewa da dariya. 


"Jinin sanyi," inji Dul'Ururu. "Tabbas kaine Maikiro'Abbas ɗin da ake faɗa. Na tabbatar ka karanta wasika ta kuma kasan abinda nake so. Mai zai hana baza ka bani amsa yanzu ba? Kada ka damu, Anbalu yana nan lafiya."


Jin Anbalu yana lafiya sai Abbasu ya ɗan sakko. Ya juya yana kallon Rabi ta tuna masa domin kuwa tuni ya manta abinda wasikar tace. 


Ganin haka Rabi ta fara kinkina. "Ah.. sun rubuto... Zasu yaƙe mu..."


Dul'Ururu ya haɗe gira. Tabbas yasan basu karanta wasikar ba. A lokacin zuciyarsa tazo iya wuya amma ya danne yayi murmushi. Ashura sun riga sun gama yanke shawarar yadda zasu yi da Maikiro'Abbas. Babu buƙatar ya kashe shi.


"Mai yasa baka karanta ba kuma kazo?" Inji Dul'Ururu.


"Nice na yaga," inji Shema'u, tana shafa gashin kanta. "Ko akwai magana ne."


Dul'Ururu ya ƙura mata ido. Ita ma ta kalle shi. Suna cikin haka sai ihu ya fara tashi daga waje. Wani hadimi ya garzayo yayi wa Dul'Ururu rada a kunne. 


Nan take jikin Dul'Ururu ya fara karkarwa. Ya juya wajen Abbasu yana kallonsa cikin tsananin mamaki.


"Mai ka aikata?"


Ai kafin ma Abbasu ya bashi amsa jama'ar gari sun shigo fada da gudu suna kuka. Dattijan gari suka zube a ƙasa sukai gaisuwa.


"Babban sarki," inji wani dattijo. "Amfanin gona ya mutu. Dukkan abinda muka noma na wannan shekara ya ƙanƙare."


"Nima a waje na haka," inji wani.


"Nima a ƙauye na haka," inji wani. 


"Ruwan rafi ma ya daskare," inji na farkon daya fara magana. "A halin yanzu babu ruwan a garin Dulkin."


Ba ruwan sha, ba amfanin gona? Dul'Ururu ya dunkule hannu yana shirin kaiwa Abbasu naushi. Tabbas yasan wannan yinsa ne. Baya ko kokwanto. 


Sai dai lokacin ne Yurba ya afko cikin fadar ta cikin taga. Yana zuwa ya zube a gaban sarki yana haki. Idan ka kalle shi zaka ga yaro ne ɗan ƙarami wanda ko gemu bai fara. A lokacin yana muƙamin ƙaramin kyaftin wanda ake turawa rangadi.


"Kyaftin," inji Dul'Ururu. "Meye ma'anar abinda ka aikata. Na tabbata ta ƙofa kowa yake shigowa."


Yurba yana haki ya fara bayani. Ko kaɗan bai damu da hukunci daza ayi masa daga baya ba, shi dai kurum ya ya faɗi abinda ya gani.


"Bango... Bango... Bango..."


Dul'Ururu ya zare ido yana jira yaji mai Yurba zai faɗa. 


"Bangon arewa dana kudu sun...."


Yurba yayi shiru yana jimamin faɗar kalma ta gaba. 


"Kai, kyaftin," Dul'Ururu ya daka masa tsawa. "Ina baka umarnin kayi magana."


Yurba ya nutsu ya tara hankalinsa.


"Bango ya daskare," inji Yurba. "Ya zama ƙanƙara. Ya riga ya zama ƙanƙara. Bamu da hanyar komawa sama."


Jikin Dul'Ururu ya fara rawa. A hankali ya juyo ya kalli Abbasu. 


"Wannan... aikin... kane?" Ya tambaye shi a hankali. Ya kasa aminta da abinda yaji. 


"Faɗi ka ƙara faɗa," inji Shema'u. "Aikin baban mu ne."


A take haƙurin Dul'Ururu ya ƙare. Ya daga hannu sama wani haske ya bayyana a tafin hannunsa. Akan idon mutane hasken ya juye izuwa ƙawanyar tauraruwa. 


"Sitar Bulasta!" Inji Dul'Ururu, ya cillo musu tauraruwar.


Tauraruwar ta tunkare su gadan-gadan zata cinye su. Maikiro'Abbas ya samar da ƙawanyar ƙanƙara ya kewaye su. 


Hakan bai saka tauraruwar ta tsaya ba. Kai tsaye ta tafi ta daki ƙanƙarar sannan ta fashe. Wata tsawa ta sauka akan Maikiro'Abbas da ƴaƴansa. Ƙanƙarar data rufe su ta tsattsage tayi daga-daga. Akai jifa da ƴaƴan Maikiro'Abbas gefe. Shi kuwa Maikiro'Abbas yana tsaye yana haki. 


Dul'Ururu ya nuna shi da sandar tsafinsa.


"Baka da sauran tsira tunda ka taɓa bango mai daraja," inji Dul'Ururu. "Da sannu zan nuna maka kuskurenka."


Maikiro'Abbas yayi murmushi tare da miƙewa ya kaɗe jikinsa. 


"Hmm. Wato kai ne Dul'Ururun da ake faɗa, ko? Muje zuwa."


Da wannan jaruman biyu suka afkawa juna da sara da suka. Babu abinda kake gani sai tashin manyan fasahai. 


Kwana uku cir aka ɗauka ana wannan faɗa. Tun suna yi acikin gari sai da suka fita can wajen gari tayadda suna hango bango. 


Maimakon ruwa, bango Ya daskare ya koma ƙanƙara ziryan. Tun daga nesa kana hango kyallin ƙanƙarar. 


Ganin da gaske Maikiro'Abbas ya taɓa muhibbar wannan bango da Ururu suke ji dashi yasa Dul'Ururu ya ƙara fusata. Faɗa yayi tsamari har sai da aka jiyo ƙarar karawarsu a doron ƙasa ta farko. 


A yayinda Maikiro'Abbas yake fama da Dul'Ururu, Rabi da ƴan uwanta sun sulale cikin kurkukun dake filin jiri sun ɗakko yayansu Anbalu. Har sun fito suna niyyar guduwa sai sukai arba da wani saurayi.


"Ranki ya daɗe," saurayin ya zube a ƙasa. "Kada ku koma cikin gari. Uznu Ururu da sauran mayaƙan Ururu sun tare hanya."


Rabi da ƴan uwanta suka tsaya suka kalli saurayin. 


"Waye kai kuma?" Shema'u ta tambayi saurayin domin kuwa wannan ne karo na farko da suka taɓa ganinsa.


Saurayin ya kalli Rabi. Rabi ta gyaɗa masa kai alamun yayi bayani. 


"Ni ne hadimin Rabi mai kawo mata bayanan sirri," inji saurayin. "Sunana Maikiro Zarru."


Babu wanda acikinsu ya taɓa sanin Rabi tana da wani hadimin sirri. Sai dai kuma sun san halin Rabi kuma tabbas zata iya yin hakan ba tare da kowa ya sani ba. Daɗin daɗawa a halin da suke ciki basu da lokacin yin musu.


"Ina rundunar mu take?" Rabi ta tambayeshi.


"Kyaftin Yurba da Uznu sun kashe da dama daga ciki," inji shi. "Sauran duk sun gudu. Nima dalilin da yasa na tsira dan bana tare dasu ne a lokacin."


Rabi ta yamutse fuska. Duk sun mutu? Anya kuwa?


"Kai," Shema'u ta daka masa tsawa. "Ƙarya kake yi. Ina Baba Abbasu?"


"Wallahi da gaske nake," inji Maikiro Zarru. "Muje ku gani idan baku yadda ba, amma idan muka haɗu dasu a hanya kada kuce ban faɗa muku ba. Baba Abbasu kuma yana can daji suna faɗa da Dul'Ururu."


"Ban yadda ba," inji Kulu. "Muje mu gani da idon mu."


Sun juya zasu tafi amma Rabi ta tsaya tana tunani. 


"Ya akai, Rabi?" Fulafunu dake ɗauke da Anbalu ya tambaye ta.


Rabi ta ɗago kai ta dube su.


"Ni na yadda da abinda ya faɗa," inji Rabi. "Muje mu ajiye Anbalu sai mu dawo. Idan faɗa ya ritsa damu muna ɗauke dashi abin bazai yi daɗi ba."


Shema'u ta juyo a fusace. "Kina nufin mu tafi mu bar Baba anan shi kaɗai?"


"Baba zai iya riƙe Dul'Ururu," inji Rabi. "Babban abinda ya kawo mu shi ne mu ɗauki Anbalu kuma mun yi. Babu buƙatar muci gaba da jira."


"Ni dai ban yadda ba," inji Shema'u. "Kawai muje mu gani da idon mu."


Nan take suka harde da musu. Wasu suna ganin ya kamata a koma, wasu kuma suna ganin a tafi.


"Ayi kuri'a," inji Maikiro Zarru. Suka juyo suka dube shi. Tunda kowa yaƙi saki tabbas za'a iya rabawa ta hanyar kuri'a.


Shema'u ta amince aka jefa kuri'a. A ƙarshe Rabi da Fulafunu suka yadda a tafi gida akai Anbalu sai a dawo. Shema'u da Kulu suka ce a koma filin yaƙi domin a tabbatar da abinda Maikiro Zarru ya faɗa. Saboda haka suka rabu gida biyu: su Shema'u suka koma cikin gari domin nemo sauran yan uwansu da kuma Baba Abbasu. Su Rabi kuma suka nausa daji domin komawa gida su ajiye Anbalu sannan su dawo. 


Bayan minti talatin suna tafiya sai Rabi ta tsayar dasu. "Mu tsaya anan." 


Fulafunu dake ɗauke da Anbalu da kuma Maikiro Zarru dake biye dasu duk suka tsaya. 


Suna tsayawa Rabi ta matso kusa ta ɗora hannu akan ƙirjin Anbalu. Hannunta ya fara haske. Bayan kimanin minti guda sai hasken ya fara shigewa cikin jikin Anbalu. Haka suka shafe mintuna talatin suna abu ɗaya kafin Rabi ta miƙe. 


"Yayi haka," inji Rabi. "Ina ganin ƙarfin jikinsa zai dawo nan da kwana guda. Idan muka koma gida sai a kirawo masu magani na gaske."


Fulafunu ya gyada kai. Yasan aljanin yar uwarsa yana bata dama ta warkar da ƙananun cututtuka. Amma kuma a lokaci guda yasan iyakarta. Babu ko kokwanto abinda yake damun Anbalu ya wuce inda zata iya. Amma dai baya so ya kashe mata gwiwa tunda duk abu ɗaya suke nema.


A haka suka tunkari daji. Kamar yadda sunan ya bayyana arnen daji a daji yake rayuwa. Kasancewar dukkan mutanen dake rayuwa a daji sun aminta da Maikiro'Abbas a matsayin sarkin su zaka samu Abbasu yana da fada a kowace ƙasa. Ba jimawa su Rabi suka fara shiga daji. 


"Ra...bi..." Anbalu ya kira sunanta a hankali. Ta juyo ta kalleshi fuska a yamutse. 


"Anbalu? Kaine kayi magana yanzu?" 


Fulafunu ya kalleta cikin mamaki. 


"Haba, Rabi, ki duba fa ki ga ciwukan dake jikinsa. Tayaya zai iya magana?"


Rabi ta haɗe gira. 


"Wallahi naji yayi magana, amma..."


Ganin ita kanta bata da tabbas sai kawai suka ci gaba da tafiya. 

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...