Skip to main content

281: Mafarauci ya sauka

 Babi na 281: Mafarauci ya Sauka

***

Bari mu koma baya kaɗan zuwa kwana guda kafin buɗe kurkukun lokaci. A kan doron ƙasa na farko, fadar babban sarki Kuyurussa'ayi Ururu - sarkin da ganin sa kaɗai ke tarwatsa ruhi. 


Doron ƙasa na farko yana da girma na gaban misali, kuma gaba ɗayansa a haɗe yake (babu sashin ikwatora, babu sashin arewa ko kudu). Kawai manya-manyan gine-gine ne na alfarma wanda aka gina da zinare. Rana guda biyu na juyawa a sama; wata a gabas wata a yamma. A kullum ranar dake gabas tana tasowa daga farkon gabas ta dira a yamma, sannan cikin dare ta ƙara komawa gabas zuwa safiya ta dawo yamma. Ita kuwa ranar dake yamma bata motsi: a tsaye take cak a waje guda. Da daddare tayi duhu da rana tayi haske. Akwai malamai da dama da suke ganin wannan rana idanun sarki Kuyurussa'ayi ne na dama. Ko gaskiya ko ba gaskiya bane ita dai wannan rana tana nan, kuma tana taimakawa mazauna doron ƙasa ta farko ƙarfafa izzar su ta fannoni da dama.


A dai-dai ƙasan wannan rana zaka hanga maɗaukakiyar fada. Fadar da sabida girma tafi sashin ikwatora ɗaya girma, amma abin mamaki tana tsaye kan gajimare tana lilo, kai kace jirgin leda ne. 


Acikin wannan fada akwai hawa-hawa har guda tara; wani saman wani. Iyalan gidan Tasu'a ne ke zaune cikin wannan gidaje hankali kwance. Babu tsoro babu baƙin ciki a tare dasu. Idan ka lura zaka fuskanci cewa akwai bayi masu idanu ruwan ƙasa da miyura a goshin su suna share-share acikin wannan gidaje masu alfarma. 


A saman gidajen akwai wani gida wanda alfarmar sa ta haura ta ragowar, kuma hasken sa ya ɗara na sauran. Acikin wannan gida akwai manya-manyan tanderu wanda girman kowacce yakai girman garin Jekis. Acikin tanderun anan ake karɓar ruhin bil'adama da suka mutu, wanda dasu Kuyurussa'ayi yake haɗa taskar ruhin sa. 


A saman tanderun akwai wata fada wadda anan masaukin Kuyurussa'ayi yake. Mutanen da suka taɓa yin ido da ido da kuyurussa'ayi basu da yawa, badan komai ba sabida ruhin bayi bazai ɗauka ba. Hatta marigayi Uznu wanda ke da jinin Ururu a jikin sa bai kai ya iya haɗa ido da kuyuru ba. An rawaito cewa Tasu'a ne kaɗai keda isar su tsaya gaba da gaba da wannan mutun mai suna kuyurussa'ayi ururu.


A dai-dai wannan lokaci Kuyurussa'ayi na zaune a turakar sa ya kirawo Tasu'a taron gaggawa. A yau Kuyuru na zaune a fili babu wani hijabi. Ana ganin komai a jikin sa banda fuska, inda wani shinge na baƙin haske ya rufe tayadda baka iya ganin komai sai shi. Kayan jikin Kuyuru baƙaƙe ne, ko kuma ince sunyi kama da baƙaƙe domin kuwa babu tabbas idan hakane asalin launin su. Wataƙila baƙaƙen idanun ne suka sauya su. 


Kuyuru yana da ƙirar mutane masu madaidaicin jiki: shi ba zabgege ba kuma shi ba ramamme ba. Tsayin sa zai kai zira'i biyar zuwa shida, faɗin kafaɗar sa zai kai kamu goma. Gashin kansa baƙi-ƙirin ne wanda abin mamaki ne a shekarun sa, ko ba komai yaci aga ƴar furfura koda guda ɗaya ko biyu, amma babu. Akwai wani tambarin ɗalasimai a tsakiyar wuyan sa wanda hatta Tasu'a basa iya kallo. Zaka iya cewa wannan tambari yana da rai, domin kuwa da kansa yake jujjuyawa yana kallon Tasu'a ɗaya bayan ɗayan.


Babban sarki mai babban iko ya fito. Tasu'a na tsaye ko numfashi basa iya yi sabida firgici. 


"Da fatan baku manta abinda ya faru a wancan lokacin da aka shiga kurkukun lokaci ba?" Inji babba Kuyurussa'ayi. Muryar sa na guga tana tartsatsi kamar ana hura ziga-zigi. 


Suka amsa a tare. "Bamu mantaba, mai martaba." 


Kuyuru yayi shiru tsahon daƙiƙu baice komai ba. Dumaƙisu yayi ta maza ya ƙara da cewa, "Tarifil-fakta yayi ƙoƙarin samar da wata kurkukun lokacin amma ƙarƙarin ta kwana sittin da bakwai. Babu abinda zai canja, mai martaba."


Tambarin dake wuyan Kuyuru ya juyo kan Dumaƙisu, lamarin da yasa Dumaƙisu karkarwa nan take. 


"Idan baku mantaba mai yasa har yanzu baku ɗau mataki akan ruhin Armad ba?" Inji Kuyuru. Abin zai baka mamaki ƴadda muryar sa take fita. Wato kowacce kalma idan aka furtata sai kaji kamar ana goga tsohon ƙashi akan dutse, idan kuma ka haɗa dukkan kalmomin waje guda zuwa jimla sai kaji sautin ya koma kamar ana hura wuta. Wani abin al'ajabin shi ne babu alamun ɓacin rai a maganar sa. Ko kaɗan babu damuwa, kawai dai akwai alamun mamaki, wato kamar ace yana mamakin yadda akai haka ta faru. Kamar misalin malami ne yake tambayar ɗalibin sa ya akai baici maki ɗari ba yaci maki casa'in da tara.


Dumaƙisu ya ƙara yin ta maza ya ce, "a shekarun baya lokacin ɗaurin auren Armad da Nostaljiya, mai martaba kaje doron ƙasa ta huɗu inda ka saje a zuwan bil'adama mai suna Maikiro Zarru domin kaga Armad da idanun ka. Mai martaba, ka ganshi ido da ido kuma ka bayyana mana cewa ba shi ne 'K'Narbig Gaus Wilbafos' ba. Ba shi ne K'Narbig ɗin da muka fafata dashi acikin kurkukun lokaci ba."


Koda jin wannan batu sai ya bawa Dul'Ururu ƙarfin gwiwa shima ya matso gaba ya ce, "mai martaba, dama abinda muka shirya shi ne mu jira sakamakon yaƙin da za'ai a tsakanin Bihanzin da Ikenga da Armad. Duk wanda yayi nasara acikin su sai mu ƙarasa shi."


A lokaci na farko fushi ya bayyana a muryar Kuyuru. "Mai ya haɗa zaki da faɗan ƙananun cinnaku?" Inji Kuyuru cikin fushi. "Dul'Ururu, kai zaki ne, waɗannan daka lissafa cinnaku ne wanda basu gama iya cizo ba. Wa yake jiran cinnaka ya tsufa kafin ya mittsike shi?"


Nan take Tasu'a suka zube a ƙas, babu wanda ya iya ƙara ɗaga kai acikin su, sunyi shiru cikin ladabi, kamar bawa a gaban ubangidan sa. Tsahon lokaci ya wuce a haka. Kafin daga bisani Kuyuru ya bada umarnin sa. "Dul'Ururu, a fara kamfen."


Da wannan babban sarki ya ƙaddamar da kamfen na biyu a tarihi ƙasa bakwai. Kamfen ɗin da yaci karo da yaƙin ruhi. Babu wanda yasan mai gobe zata haifar, shin jami'an Ururu zasu yi nasara a kamfen ɗin da suka ɗakko? Waye gwarzon da zai ciri tuta a yaƙin ruhi? Ina Sarkin-sarki sarauniya a duniyar ɓoye? Ina Ƙaraiƙisu shugaban ikwatora? Ko ka shirya ko baka shirya ba, babban yaƙi wanda zai gauraya duniya na nan tafe.

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...