Babi na 24 : Dauwamammen Sara.
Acikin wannan haraba Armad na zaune suna tattaunawa da Nusi inda take zayyana masa dukkan shirinta da kuma sharrin da yake tunkaro shi.
Bayan ta ƙara kurɓar lemon dake gabanta ta kuma tambayi Armad mai yasa baya shan nasa, amma maimakon ya bata amsa, wata kalma ɗaya ce kawai ta fito daga bakinsa, ''Bihanzin!''
Nusi ta girgiza kai, sannan tayi murmushi wanda kana gani kasan akwai firgici acikinsa, gami da cewa, ''Zanso matuƙa nace maka baka cikin wani sharri to amma abin bahaka yake ba. Domin kuwa kasan cewa......."
Armad ne ya ɗaga mata hannu tare da girgiza kai alamun hankalinsa har yanzu a kwance yake, "Kada kiji tsoro! Lallai bazan daina numfashi ba saina cika burin mahaifiyata na nemo Tarifil Fakta.
"Amma ni yanzu ma babban abin da nake so naji shi ne cinikin bayinnan. Shin menene asalin cinikin bayin nan kuma mai yasa babu wanda zai buɗe baki a ɗuk cikin sarakunan duniyar ƙasa bakwai ya ce adaina. Domin ni a gani na zalunci ne kawai da ƙara ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi da kuma danne mara ƙarfi. Amma ke meye ra'ayinki akai?" Ga dukkan alamu wannan al'amari na cinikin bayi da ake yana matuƙar ciwa Armad tuwo a kwarya, kuma ya daɗe yana damunsa.
Nusi ta girgiza kai tare da mummunar ajiyar zuciya, sannan a wani yanayi mai ban tsoro gumi ya fara keto mata tamkar wadda aka kunnawa wuta.
Ta tashi daga kan kujerarta sannan cikin sauri da tuntuɓe ta nufi bakin ƙatuwar tagar dake ɗakin da suke ciki. Tana isa ta leƙa ta fara dube-dube zuciyarta tana dukan uku uku. Koda ta tabbatar babu kowa a wajen tagar saita rufota cikin sauri, sannan saita ƙara juyowa tana gudu ta isa bakin ƙofar ɗakin tana zuwa ta leƙa sannan kuma ta rufeta. Lamarinda yasa nan take ɗakin ya rufe dunɗum da duhu.
Armad bakinsa a buɗe mamaki ya cika zuciyarsa akan meke faruwa, kuma meye dalilin da yasa kawai tana zaune a nutse kwatsam ta rikice. Mamaki yasa ko magana ya kasa.
Wata ƴar fitilar aci bal-bal ce a hannun Nusi wadda ta iya haskaka ɗan iyakacin tsakiyar ɗakin kaɗai inda suke zaune.
To sai a lokacin da Nusi ta zauna sannan Armad ya samu ya iya yin magana, "wai meke faruwa ne? Lafiya?"
Nusi ta ja kujerarta inda ta matsa kusa dashi sannan ta fara magana ƙasa-ƙasa, "kana so ka faɗi abinda za'a hallaka dukkan miliyoyin alummar ƙasar nan ne. Baka da masaniyar cewa iska zata iya ɗaukan maganarka ta kaita kunnen ma'abota Ururu.
"Baka da masaniyar cewa wasu daga cikin mabiya ɗarigar Ururu zasu iya jinka kuma su isarda da labarin abinda ka faɗa.
"Baka da masaniyar cewa Shísu Ururu yana kan wannan doron ƙasa. Lallai kada ka ƙara faɗar wata mummunar magana akan harkar cinikin bayi. Idan dai baso kake a wayi an shafe garin Khan daga ban ƙasa."
Tunda ta fara magana bata shaƙi numfashi ba, saboda haka tana zuwa nan a zancenta dole ta tsaya ta fara haki tana ƙoƙarin kama iska. Amma duk da haka bata dawo hayyacinta ba sai bayan sama da daƙiƙa ashirin.
"Armad Wilbafos bawai kai ba, a'a sauran mutane zaka duba. Domin kuwa Ururu babu ruwansu da yara ko mata ko tsofaffi. Saboda hakaina roƙonka, indai zaka faɗi wata magana akan ɓatanci ga harkar cinikin bayi toka bari harsai kakai matakin Izzar da zaka iya kare mutane daga tsananin ƙarfin mulkin da mayaƙan azaba na Ururu keda shi."
Idanunta kafe akansa, babu abimda take so taji inba amince warsa ba.
"Amma kinsan wani abin mamaki, sak irin wannan magana da kika gayamin ita kakana Zaikid ya gayamin." Maimakon ya bata amsa saiya canja akalar zancen.
" 'kada ka yaƙi cinikin bayi idan baka da ƙarfin da zaka iya kare mutanen ka daga abinda zai biyo baya.' haka yake gayamin a duk lokacin da zancen cinikin bayi ya tashi." Armad yai shiru yana kallon ƙasa, a yayinda ita kuma Nusi take kallonsa.
Lallai ya daɗe al'amarin cinikin bayi yana ci masa tuwo a kwarya. To amma ga dukkan alamu babu abinda zai iya a wannan lokaci.
"A shekara ta ɗari bayan saukar da mutane zuwa ƙasashe shida na ƙasa, su kuma Ururu suka gaje ƙasa ta farko, wato shekaru dubu ɗaya kenan da ɗari huɗu. Kaka na ya labarta min cewa harkar cinikin bayi ita ce Rukuni na farko da Ururu suka fara wanzarwa a dukkan doron ƙasa shidanan." Nan take Armad ya shiga bada labarin dukkan abinda ya sani akan harkar cinikin bayi tun daga asalinta, da zummar ko zaiji wani abu da bai sani ba daga Nusi.
Hasken fitilar aci bal-bal yana tashi inda yake haskake jan kyallen dake ɗaure a gaban goshinsa yana kaɗawa akan iska.
"Farko da Ururu suka bayyana suma suna cikin waɗanda suke shiga cikin gasar cinikin bayin. A wannan lokaci ta fara ne da wata gasa mai suna Jinzi, wadda acikinta kowacce ƙabila babba da ƙarama zasu kawo wani adadi na bayi a ƙarshen kowacce shekara, waɗanda za'a fafata akansu duk wanda yaci nasara daga ƙarshe, to shi za'a bawa kyautar dukkanin waɗannan bayi da kowacce ƙabila suka tara.
"Saboda haka wannan ƙabila da taci nasara su zasu juya akalar kasuwar bayi a wannan shekara.
"A haka wannan gasa ta Jinzi ta fara kafin daga bisani a maida sunanta Jinzidal bayanda Ururu suka koma doron ƙasa ta farko.
"A tsahon sama da shekaru dubu da akai ana yin wannan gasa ta cinikin bayi, Ururu suna daga ƙasa ta farko suna zuba ido suga ko wani zai kawo mata tangarɗa. Wanda kuma da dama sun aikata hakan amma a yanzu babu zuri'arsu a ban ƙasa. Ururu sun riga sun gabatar dasu izuwa lahira.
"Akwai manya-manyan sarakuna guda biyar wanda su suka fi kowa muƙami acikin wannan gasa. Waɗannan kuwa sune Sarki Hanibal na ƙasa ta uku da sarki Maikiro Abbas na ƙasar Maikironomada da sarki Deniz Ururu wanda ya zaɓi ya zauna a ƙasashen ƙasa shekaru dubu da suka wuce lokacin da zuriarsa ta ma'abota Ururu zasu koma ƙasa ta farko. Sai kuma Sarki Rafiya wanda akewa laƙabi da mai Izza dubu ɗari, sai kuma Sarki Bihanzin Mai dauwamammen sara. Nasan cewa waɗannan sarakuna biyar su su suke da iko akan duk wata Izza dake doron ƙasashen nan shida na ƙasa.
"Kuma nasan cewa duk wanda ya taɓa cinikin bayi waɗannan Sarakuna sune zasu fara gamawa dashi kafin ma URURU SU SAUKA. To amma duk da haka bana cire ran watan watarana zan hana bautar da bil'adama da ake. Bari dai kawai yanzu ta rashin lafiyar mahaifiyata nake.
Zuciyar tana dukan uku-uku ta kalli idanun Armad ta kuma tabbatar da cewa lallai abinda yake faɗa har cikin ransa yake, kuma babu wasa aciki.
Babu yadda ta iya, haka tai ajiyar zuciya bayan dogon lokaci tana kallonsa. Kafin daga bisani ta girgiza kai gami da cewa;
''Muhimmin abindai anan shi ne, babu ruwanka da harkar cinikin bayi a yanzu, zaka shiga cikin fasahar Non-toch-teka, idan ka fito kuma zamu duba muga hanyar da tafi kamata ka nemo Tarifil fakta ko ka koma izuwa mahaifiyarka.
''Sabida haka a yanzu babu abinda zan iya akai sai dai kawai ka jira zuwa nan da kwana shida.''
Armad ya ɗago kai cikin murmushi, amma baice komai ba, inda yabarta taci gaba da jawabi, ''ni yanzu kamar yadda na gaya maka ina da buƙatar na shiga cikin kogon Asúlu, domin fuskantar wankin Izza saboda haye matakin jarabawar can da nayi za'a ƙaramin matsayi.
''A iyakacin lissafina bazan fi kwana biyar ba, komai daɗewa, Zuwa yamma zan shiga, amma a yanzu zanje na shirshirya, kuma da ana zuwa rakiya, to da ka rakani, amma ba'ayi, daga ni sai waɗanda na zaɓa daga cikin majalisa.
''Saboda haka muyi sallama kawai. Sai ka huta kuma na haɗaka da aminaina guda biyu Iliyásis da Cokali su nuna maka gari.'' Faɗar haka keda wuya kamar ta tuno wani abin dariya, sai ta fashe da dariya, gami da cewa, ''su na da kirki da kuma saurin sabo, nima tare muka shigo nan, amma bayan wani lokaci ALLAH yasa na wuce su matsayi. Ka kwantar da hankalinka a game dasu.
''Iliyásis baya magana sosai, amma yana da tunani mai ƙarfin gaske. Ka lura da duk abinda zaiyi zaka koyi abubuwa da dama.
''Shi kuma Cokali.....'' tuni dariya ta ƙara kwace mata daga faɗar sunan kawai. Da kyar ta ƙarasa da cewa, ''yana da ban dariya, amma duk da haka jarumi ne!
Washe gari acikin garin Khan akan wata hanya data wuce ta cikin wasu gida je, waɗansu mutane uku ne suke tafiya.
Dukkansu babu alamun baƙin ciki a tattare da zuƙatansu, sai dai ɗaya daga cikinsu wanda duk yaɗan fisu haske da kuma siranta fuskarsa acike take da fara'a sannan kuma bakinsa motsi kawai yake yana jawabi.
Bayan wani lokaci ya buɗe baki yace, ''ni suna na Cokali!'' Sannan kuma ya nuna ɗayan dake ɗaya ɓangaren, ya ce, ''wannan kuma shi ne, Iliyásis.''
Yayinda yake maganar idanunsa nakan kan saurayin da ke tsakiyarsu, wanda ya kasance mai matsakaicin jiki da kyakkyawar fuska.
Fatarsa wankan tarwaɗa ce, sannan kuma saboda tsayinsa kai kace ya haura shekaru ashirin da haiwuwa.
Idanunsa nada haske sosai, kuma idan baka kula ba sosai sai kace har haske suke fitarwa.
Yana da ɗan ƙaramin saje daya ƙara inganta kamalarsa, sannan kuma idan ka haɗa da rigar dake jikinsa wadda ta kasance ƴar shara, ta yadda cikakken dantsensa ya fito sosai, ga kuma doguwar takobin dake rataye a kafaɗarsa, da kuma jan kyallen daya ɗaure kansa wanda ya saje da farin wandon dake jikinsa da kuma farar rigarsa, sai kaga lallai yana fitar da kamalar jarumai a tattare dashi.
Wannan saurayi dake tsakiyarsu ba wani bane ba illa Armad Wilbafos, wanda kwanakin baya kaɗan a wani ɗan ƙauye aka laƙaba masa Magajin-Wilbafos.
Sunan da ya rasa murna zaiyi saboda shi ko kuma baƙin ciki.
Kafin Cokali ya ɗauke idonsa daga kan Armad sai ya tambayeshi, ''idan nace maka ɗana ba matsala?'' Idanunsa babu ko alamun wasa aciki, hasalima cike suke da soyayar ɗa da uba, a lokacin da yake tambayar.
Tunda suka haɗu acikin gidan da aka sauki Armad, bayanda suka ƙara zuwa wajensa, ya ƙare musu kallo, kuma Armad ya tabbatar cewa acikinsu ukun Cokali ne ƙarami.
Sannan kuma ɗaya daga cikin su Iliyásis da Nusi ya zama babba.
Amma to ita kanta Nusi baza tafi ashirin ba.
Sabida haka daya ji wannan tambaya, sai kawai ya fashe da dariya, kuma ya tuna da abinda ta gaya masa akan cewa Cokali ɗan cafta ne kawai.
To amma yana niyyar amsawa masa tambayar da yayi sai kawai idanunsa yakai kan wani zabgegen rami daya gifta ta inda zasu wuce an ɗan kewaye shi da ƙarafa.
Yana kallon cikinsa yaji wata irin Izza mai tsananin gaske, wadda tasa yaji tamkar idanunsa zasu fashe daga kallonta kurum.
Babu abinda yake iya tunawa daya gani acikin ramin face baƙi da duhu da kuma wani tiriri mai alamun mutuwa da kanta.
Amma dai abinda ya tabbatar shi ne lallai yana da matuƙar zurfin gaske, hasalima idan akace bashi da ƙarshe baza ai musu ba.
Nan take ya ɗaga ido inda ya ƙara hango irin wannan rami a gabansu, saboda haka cikin zafin nama ya juya domin tambayarsu meke faruwa a wajen, domin lallai yaji gashin jikinsa ya tashi, ruhinsa ya fara zafi, kuma tambarin Miyurar dake goshinsa ya fara haske da kansa ba tare da ya taɓa shi ba.
Amma kafin yace wani abu yaji maganarsu;
''Ba'a kallon cikin waɗannan rami ka, lallai ka kiyaye, saboda har halaka zaka iya yi idan kalli cikin manya daga ciki. Kaga har can nesa duk sune. Danma an kewaye manyan ciki da bangon sihiri. Suma waɗannan ɗin da a kewaye suke, amma a hankali a hankali suka cinye bangwayen da aka kewaye su dashi.
''Ramika ne da Bihanzi yayi da takobinsa wato Dauwamammen Sara.
''Shekaru da dama da suka wuce, a lokacinda ya fara shigowa wannan gari kuma ya zama Al'yaya.
''Da dama daga cikin ƴan majalisun wannan gari a wannan lokaci basu yarda ba, saboda sun san cewa idan suka barshi ya girma zasu iya rasa muƙaminsu.
''Saboda haka a ɓoye suka saka a hallaka shi kwanaki kaɗan bayan shigowarsa!
''A sakamakon haka suka fafata, kuma a ƙarshe ba komai ya faru ba illa waɗannan rami ka da kake gani.
''Ya dai bayyana cewa duk waɗanda Bihanzin ya jiwa ciwo a wannan rana basu ƙara kwana da yawa ba suka mutu.
''Ba dan komai ba sai cewa duk ciwon da yayi da takobinsa, to fa bazai taɓa warkewa ba har abada!!
''Kai bama jikin mutun ba, hatta ƙasa, ko kuma duk wani abu mara rai, domin duk waɗannan ramika da kake gani sakamakon saran takobin Bihanzin ne daya sari ƙasa a lokacin.
''Bayan tafiyar shugaban babu yadda sabon shugaban majalisa baiyi ba domin rufe waɗannan ramika ba, amma ina, ga sunan har yanzu kuma har abada, an rasa yadda za'ai dasu, sai dai kawai a kewaye waɗanda za'a iya. Yau shekaru arba'in da biyu kenan!!!
"Musamman mutane suke yiwo tattaki suzo suga wannan ciwo da aka jiwa ƙasa, da dama shiɗewa suke saboda irin girman Izzar dake cikinsa.
"Wanda daga haka aka koma ambatonsa da, Bihanzin mai Dauwamammen Sara!"
Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad. Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta. Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...
Comments
Post a Comment