Aiban'zhisu Babban karni!
*************
Tunda Armad ya riga yazo nan to fa bazai koma ba sai ya ɗauki mahaifiyarsa.
"Aiban'Zhisu, babban ƙarni!"
Ɗalasimin yana barin bakinsa, jikinsa ya ɗau hasken walkiya. Tun daga kai har ƙafa babu inda baya tartsatsin walkiya. A lokaci guda walkiyar ta fara juyawa tana zagaya jikinsa tana yin sama. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta dunkule tayi sama ta fasa ta cikin gajimare ta fice ta ƙara lulukawa sama. Ta wuce Hajarul Ururu ta shiga doron ƙasa na farko tayi sama ta haɗe da gajimare. A lokaci guda da walkiyar take yin sama, wata walkiyar ce ta fita daga jikin Armad tayi ƙasa ta fasa doron ƙasa ta uku data huɗu data biyar data shida data bakwai ta shige ƙarƙashin ƙasa. Sannan kafin wani yayi wani abu sai walkiyar ta fashe zuwa ƙawanyar walkiya dubu a sama doron ƙasa ta farko, sannan wata ƙawanyar dubu a ƙasa doron ƙasa ta bakwai. Kowacce ƙawanya acikin dubun ta rabe zuwa ƙawanya ba adadi suka fantsama suka shiga duniya. Cikin rabin dakika wannan kawanyoyi sun isa ko'ina a ban ƙasa. A lokacin Armad ya kaddamar da fasahar Aiban'Zhisu babban ƙarni.
Dul'Ururu ya ɗaga hannu zai ƙara sauke masa sanda amma ya ƙame a inda yake. Binani ya kaiwa Nazára sara amma shima ya ƙame. Haka ma Rabi da mutun-mutumin dake kama da ita suka kame a dai-dai lokacin da suka kaiwa juna sara da takobin waraka.
Armad yana kan wani faifan ƙasa a sama, haka ita ma Fatima ta taso daga inda take a sama. Ƙasar da take kai ta ɓamɓaro ta taso sama a wani salo irin na fasahar Aiban'shisu. Maruta wanda ke kusa da ita yakai hannu zai riƙe ta amma ya ƙame ƙam a inda yake.
Armad ya duba izzarsa da sauri yaga tuni ta ƙare. Ba shida karfin da zai iya yin koda Kaban'shisu. Sai dai daman yasan haka tuntuni kuma ya tanadi yadda zaiyi. Da sauri yayi amfani da jikinsa na izza ya ruga inda Fatima take ya ɗauke ta sannan ya juyo da gudu yayi inda rundunarsu take. Babu wanda yake ganin abinda ke faruwa. Dukkan mayaƙan dake filin sun ƙame. Wasu suna tsaye, wasu suna durkushe, wasu sunkai sara, wasu kuma suna tarewa. A yayinda wasu kuma zaka ga an caka musu makami ana ƙoƙarin zarewa. Dukkan kowa da komai ya tsaya cak, babu wani iko sai na Armad. Idan ka duba ƙasa zaka ga ƙananun walkiya sun jeru a ƙasa waje-waje. Kuma idan da al'ummatai dake rayuwa a sauran ƙasashe zasu iya ganin abinda ke faruwa to da tabbas zasu ga irin wannan ƙananun kawanyoyi sun cika ko'ina. Dukkan wata ƙawanya daga izzar Armad take wanda hakan yake ƙara nuna yawan izzar daya rasa.
Armad yaci gaba da gudu ɗauke da mahaifiyarsa a hannu. Zuwa yanzu yaci dakika huɗu. Abinda Ya rage masa baifi dakika biyu ba, ko kuma mafi yawa uku.
Armad yana amfani da jikin izza da kuma ƙarfin dantsensa ne kawai wajen gudu, amma kuma duk da haka yana da tabbas zai iya tsere musu. Koda bai isa wajen da Maikiro'Abbas yake ba to zaiyi musu nisa kafin lokacinsa ya ƙare. A halin yanzu yazo dai-dai inda Dul'Ururu yake tsaye ya ɗaga sandarsa. Har ya gifta shi ya wuce sai ya kasa daurewa. Yana gudun ya ɗan juyo da kai domin yaga fuskar sarkin. Ai kuwa yana juyowa yaga idanun sarkin a kansa yana kallonsa. Armad ya juya da sauri yaci gaba da gudu sai dai zuciyarsa tana dukan uku-uku.
Wato shi dai Dul'Ururu yafi Armad tsayi da wajen kamu biyar. Saboda haka a duk lokacin da suke faɗa kan Dul'Ururu a ƙasa yake yana kallon Armad. Saboda haka a halin yanzu da Armad yake nesa dashi bai kamata ace yana kallonsa ba. A takaice, kamata yayi ace kan Dul'Ururu yana sunkuye yana kallon ƙasa dai-dai inda Armad ya bari a baya maimakon ace ya ɗaga kai yana kallon Armad ɗin dake nesa yanzu. Sai dai kuma duk wannan tunanin Armad ne kurum, zata iya yiwuwa bai kula bane sosai amma dama kan Dul'Ururu a sama yake tun sanda ya kira fasahar, bawai yanzu ya ɗaga kai ba. To koma dai meye Armad bashi da niyyar tsayawa ya gani. Abinda kawai yake gabansa shi ne ya ƙara gudu.
Kafin dakika biyun ta cika Armad ya bar wajen gadon aba'in ya wuce Dul'Ururu ya tsunduma acikin mayaƙan Ururu. A lokacin dukkan ƙananun walkiyar da suka rufe ko'ina a faɗin duniya suka ɓace. Binani ya ƙarasa kaiwa Nazára duka. Rabi ta ƙarasa saukewa mutun-mutumin da suke faɗa dashi takobin waraka. Ga dukkan alamu dukkaninsu babu wanda yasan abinda ya faru. Sai dai a lokaci guda Maruta ya ankare babu Fatima a gefensa. Amma kafin yayi wani abu ya hangi Dul'Ururu ya tashi sama yayi kan rundunarsu. Koda ya dubi wajen da Dul'Ururu ya nufa sai ya hangi Armad dauke da Fatima yana gudu. Ya cije haƙora da ƙarfin tsiya tare da miƙewa tsaye.
Lissafin Armad kafin kowa ya ankara da abinda yake faruwa ya ƙara yin nisa. Amma ga dukkan alamu Dul'Ururu ya ankara da wuri. Abinda ya kasa ganewa shi ne: shin kamar yadda yayi hasashe Dul'Ururu ya ganshi sanda ya tsayar da lokaci, ko kuma bai ganshi ba sai bayan ya saki lokacin kawai dai sauri yayi ya biyo shi. To koma dai meye bashi da lokacin yin tunani domin kuwa ganin tahowar Dul'Ururu yasa kowa ya dare daga inda yake ya bar Armad a tsaye a tsakiya. Ganin haka Armad ya fara ƙoƙarin tsinke ankwar Bilak-siton ɗin dake hannun Fatima. Ita ma Fatima tsohuwar jaruma ce saboda haka yasan zata iya kare kanta daga Dul'Ururu.
Sai dai yana jan ƙarfen ya yamutse fuska cikin mamaki. Ko motsawa ƙarfen baiyi ba balle ya tsinke. Ya ƙara ja iyakacin ƙarfinsa amma a banza. Abinda Armad bai sani ba shi ne sauran ma'abota izza masu amfani da aljanu basa ko iya taɓa ƙarfen. Shima abinda yasa yake iya taɓawa dan bashi da aljani ne. Amma kuma duk da haka taurin ƙarfen na musamman ne.
Ganin haka Armad ya gwada kiran fasaha.
"Hannun Aradu!"
"Hannun Reza!"
Amma ina, bashi da izza ko ɗigo a jikinsa, ko walkiya ɗaya bai gani ba.
Comments
Post a Comment