Skip to main content

301-305

 Armad, Nusi, Nostaljiya, Lamarudu, Inara da Cokali suka saɓa jakunkunan su suka fice daga otal ɗin. Har zuwa wanan lokaci sarkin ƙofa Ulbaru yana kwance aƙas a sume. 


Cokali, Inara da Lamarudu suka gyaɗa kai sannan suka rankaya da gudu. Armad, Nusi da Nostaljiya suka taka a ƙafa suka nufi hanyar fada suna tafiya a hankali.


Kamar kullum babu mutane da yawa akan titi, amma garin yana nan da tsarin sa. Iska na kaɗawa, bishiyu suna rangaji, ga kukan tsuntsaye a sama. Duk cikin su babu wanda yace uffan, tafiya kawai suke suna lissafi. Sun gama shirya yadda zasu sace Iluru, kuma suna fatan komai ya tafi daidai, to amma duk wani shiri yana buƙata a bishi da aiki. 


Ba jimawa suka iso wajen wani cin abinci. Waje ne na alfarma an kewaye shi da bishiyu, ga kujeru na ƙawa da alfarma an jejjere, mutane (yawanci attajirai da ɗalibai ƴaƴan manya) na zaune akai ana ci da sha. Kowa abinda ke gaban sa yake, kai kace babu wani tashin hankali dake faruwa a garin. 


Su Armad suka nemi waje suka zauna. Ba jimawa mai raba abincin ya tako wajen da suke ya basu takarda mai ɗauke da sunayen abincin da ake siyarwa a wajen. Nostaljiya ce ta fara karɓa tayi alama akan abincin da take so, sannan ta miƙawa Armad. 


Armad yayi alama akan ruwan sha, wato shi kawai yake buƙata. Nusi kuma ta buƙaci leman tsohuwar darbejiya da nonon ƙaramar saniya.


Mai kawo abincin ya gyaɗa kai ya juya. Ba jimawa ya dawo da abinci akan tire ya ajiye. 


Daga inda suke suna hango toluwar fadar garin daga nesa a ɓangaren kudu.


***


To a dai-dai lokacin da su Armad ke ci da sha a wannan waje, Cokali, Inara da Lamarudu na tsaye a ƙofar fadar wannan gari. Ba tare da cewa komai ba suka afkawa fadar da munanan hare-hare. 


Cokali, kamar kullum, ƙoƙari yake ya haɗiye dukkan fadar cikin littafin sa. Ya ɗauki alƙalamin sa, ya buɗe shafi na casa'in da huɗu ya fara rubutu:


*

Ƙatuawar fada mai ƙofa sama da ɗari.

*


Cokali ya tsaya yana jira yaga fada ta koma haske ta shige cikin littafin sa, amma ina, fadar ko gezau bata yi ba. 


Yayi gyaran murya ya goge rubutun ya canja wani.


*

Fada mai doguwar katanga sama da zira'i dubu.

*


A yau ma fadar ko gezau bata yi ba. Cokali ya ƙara gwadawa amma ba labari. Daga ƙarshe daya tabbatar bazai iya haɗiye fadar ba sai ya dawo kan ƙofar shiga.


*

Ƙatotowar ƙofar shiga ta jan ƙarfe. Zira'i maitan a tsaye.

*


Nan ma dai haka. Ƙofa bata motsa ba. Cokali ya cije baki yana tunanin mai zaiyi.


A ɗaya ɓangaren kuma Inara ya himmatu wajen ƙoƙarin rusa katangar.


"Hannun-Aradu!"


Ya dunƙule hannu ya daki iska. Nan take dunƙulen walƙiya ya tunkari ƙofar fadar gadan-gadan. Sadaukan sarki Iluru suka haɗu guri guda suka tare fadar tare da yin gaba-da-gaba da hannun-aradun. 


Daga gefe wasu mutun goma ne suka ware suka zagayo ta bayan su.


"Mairakana!"


Wata ƙatotuwar ƙusa (zira'i talatin da ɗoriya) ta bayyana akan iska ta afka musu. Kafin su ankara Ƙusar ta fara neman tsire su. Lamarudu yai tsalle sama ya shiga gaban ƙusar tare da sa hannu ya tare ta, kamar zaki ya kama kare. Koda ƙusar ta taɓa hannun sa sai kawai girman ta ya fara raguwa, a hankali a hankali har saida ta dawo kamar ɗan'yatsa sannan ta faɗi ƙasa ba nauyi.


To amma kamar ziga sadaukan akai. Kan kace meye wannan duk wani ma'aikacin tsaro dake kowanne saƙo da loko na garin Seerisha ya rankayo ya taho fada. Sannan ragowar ma'aikatan cikin fadar suma fitowa sukai. Cikin ƙanƙanin lokaci sama da sadaukai dubu sun zagaye su Cokali ana ɗauki ba daɗi tsakanin mayaƙan Iluru da kwamandun Armad.


***


A dai-dai wannan lokaci acikin wannan fada ta sarki Iluru, Iluru ne zaune kan karagar sa tare da ɗan sa Bizaya da Salsa ɗin sa masu fuskoki a rufe da kuma babban kwamanda Deniz Kalhari ana tattauna al'amura yaƙi. 


Suna zaune suka ji rugugi yana tasowa daga ƙofar shigowa.


Iluru ya ɗaga kai ya kalli saitin inda ƙarar take tasowa, ya ce, "Sun zo ne?" 


Bizaya ya gyaɗa kai. "Eh sunzo. Amma mutun uku ne kawai - Cokali (mai amfani da fasahar marubutan farko), Inara (mai amfani da fasahar Sikai), sai kuma Lamarudu (mai amfani da fasahar gidan Wilbafos mai zuƙe fasaha). A halin yanzu bamu san inda Armad, Nusi, Nostaljiya, Nazara, Iliyasis da Babara suke ba."


"Amma labarin da muka samu daga shugaba Deniz Wuyawuya ya ce mutun shida ne kawai - wato tun asali mutun shida ne suka ƙetara iyaka suka shigo garin. Bamu san inda ragowar suke ba." Inji Kalhari.


Iluru ya ɗan yamutse fuska ya ce, "kun tambayi shugaba Yudusu?"


Bizaya ya gyaɗa kai. "Eh, na tambaye shi. Shima mutun shida ya ji."


Nan take fada tayi shiru ana tunanin mai yake faruwa. Bayan ƴan daƙiƙu sarki Iluru ya numfasa, ya ce, "Haakane." 


"To amma mai Armad yake so ya cimma da mutun ukun dake ƙofar fada suna tada husuma a yanzu?" Kalhari ya tambaya cikin tunani.


"Haha..." Bizaya ya kyalkyala dariya. "So yake ya janye hankalin mu tayadda zaizo ya sace sarki bamu sani ba." 


Suna jin haka kowa ya fashe da dariya acikin fadar. 


"To ai lokaci yayi daman, baba, zan iya tafiya?" Bizaya ya tambayi mahaifin sa Iluru. 


Iluru ya gyaɗa kai. "Kada kayi shirme, sama da shekaru dubu kenan muna jiran wannan rana - ranar da zamu karya asirin da akai mana mu koma sama mu bar wannan ƙarƙashin ƙasar."


Bizaya ya gyaɗa kai cikin ladabi sannan ya ɓace. 


***


Armad, Nusi da Nostaljiya suna zaune suna hira cikin nutsuwa. Ga abinci da abin sha an kawo kan teburin su. 


Kafin kowa ya ankara Nusi tai wuf ta janye kwanon dake gaban Nostaljiya. Nostaljiya ta riƙe hannun ta aka fara kiki-kaka. Armad kawai ajiyar zuciya yayi ya girgiza kai. Tabbas duk ranar daya auri Nusi ya haɗa ta da Nostaljiya tofa tabbas ya daina baccin asuba.


"Mai ciki bata cin kitsen aljanin zaki!" Inji Nusi. "Armad, wannan matar so take ta zubar maka da ciki."


Nostaljiya ta harare ta. "Kaaaiii. Na rantse baki isa ba, a ina aka rawaito wannan. Kedai kawai kice kina so kici. Kuma baki isa ba."


Nusi ta cije baki tare da damƙe kwanon. Nostaljiya ta faki idon ta yafuci abincin da hannun ta na dama ta afa a baki. 


"Kuturu.... Armad, wallahi cikin ta zai ɓare. Zai ɓare ina gayamiki ki tofar... Zai ɓare fa... ZAI ƁARE!"


"Kaaiii.. ku taimaka kuyi ƙasa-ƙasa kowa kallon mu yake." Inji Armad amma ko jin sa basu yi ba.


Ana cikin haka ne wani saurayi mara tsayi sosai ya bayyana a gefen teburin su. 


"Au, ashe an samu ƙaruwa ba'a gayamana ba." Inji saurayin daya bayyana.


Nan take kowa ya nutsu hankalin su ya koma kan sa.  


Mai rabon abincin ya garzayo da gudu yana tuntuɓe izuwa wajen wannan saurayi. "Y... yarima, barka da zuwa. Bamu san zaka zo ba da munyi shiri."


Saurayin ya girgiza kai. "Ba komai, Duna, ban kujera." 


Da gudu mutumin mai suna Duna yaje ya kawo wa wannan saurayi kujera ya zauna a gefen Nostaljiya yana fuskantar Armad. Idan ka duba a tsanake zaka fuskanci ba kowa bane illa yarima Deniz Bizaya ɗan sarki Iluru. 


"Yarima, mai kake so a kawo maka?" 


"Kawo ruwa."


Nan take aka kawo ruwa a kofin farin dutse akan ajiye gaban Bizaya. "To, jeka bamu wuri." 


Duna ya juya a guje ya ɓace. Bayan an basu waje sai yarima Bizaya ya juyo ya dubi Armad.


"Armad Wilbafos, baka gayamin zaka zo gidana ba dana tare ka. Akwai amana a tsakanin jaruman da suka fafata a jinzidal ɗin shekarar 1851BA." Inji Bizaya. 


Armad ya tari numfashin sa. "Deniza Bizaya?" 


"Na'am, Armad Wilbafos."


"Ko kasan inda zan ga ƙannen baban ubanka Wuyawuya da Yudusu?" Armad ya tambaye shi a nutse. 


Bizaya ya yamutse fuska ya harari Armad tsahon daƙiƙu kafin daga bisani ya saki fuska. "Na san inda suke."


Nan take akai wani kallon-kallo tsakanin Armad da Nostaljiya. Nostaljiya ta gyaɗa kai.


Bizaya na ganin haka yai murmushi tare da girgiza kai. "Haba, Nostee, kina tunanin zan bar tunani a buɗe nasan zanzo nan? Amma gwada ki gani idan zaki iya karantawa."


Ba tare da jira ko kunya ba Nostaljiya ta afka kwakwalwar Bizaya tana ƙoƙarin karanta tunanin sa. Amma abinda kawai take gani shi ne bangon ƙarfe da ruwan teku. Tana ƙara shiga tana ƙara nutsewa. Ga dabbobin ruwa suna iyo suna kawo mata farmaki.


Bayan kimanin daƙiƙa hamsin Nostaljiya ta yamutse fuska, shi kuwa Bizaya fashewa yayi da dariya yana cewa, "na gayamiki."


Take fuskar Armad ta canja. "Bizaya, gayamin mai ya kawo ka nan?"


Wato kallo ɗaya tak zakai wa Armad kasan tambayar ƙarshe yayi wa Bizaya, duk wata amsa mara daɗi data futo daga bakin sa hukunci ne kawai zai biyo baya.


Shima Bizaya ya fuskanci hakan, inda ya ƙurawa Armad ido na ƴan daƙiƙu kafin ya fashe da dariya. "Mahaifi na, sarki Iluru, yana son magana dakai."


Tun kafin ya ƙarasa rufe baki Armad ya miƙe tsaye. "Muje."


Bizaya ya miƙe ya shige gaba. Zuwa yanzu hankalin duk wanda ke cikin wajen ya dawo kan su duk kuwa da kowa ƙoƙari yake ya ɗauke kai ya nuna kamar bai san mai yake faruwa ba sabida tsoron Bizaya.


Suna fita daga wajen Bizaya ya dubi Armad ya ce, "sarki yace na gayamaka zaiji daɗi idan ka tsaida husumar dake faruwa a ƙofar fada. A ganin sa babu amfanin mu kashe juna a wannan lokaci."


"Indai zai bani abinda nake nema ko kuma ya gayamin inda Wuyawuya da Yudusu suke ba matsala." Inji Armad.


"Eh to, wataƙila. Yace dai yana son magana dakai kuma nasan maganar taku zata fi daɗi idan ka tsaida faɗan da akeyi a ƙofar fadar wanda tuni ya fara jan hankalin jama'a."


Armad ya ɗanyi shiru kamar yana tunani wanda a zahiri ya riga ya yanke shawarar abinda zaiyi kawai salo ne.


"Ka gayamasa ba komai." Inji Armad.


"Zaka tsayar da faɗan?" 


"Eh mana. Daman motsa jiki kawai suke."


Bizaya ya yamutse fuska cikin ɓacin rai. Wai motsa jiki? Abinda har mutun goma sha sun halaka amma wai motsa jiki.


A haka suka ci gaba da tafiya kowa yana auna kowa. Suna zuwa ƙofar fadar suka tsaya. 


Armad ya ɗaga hannu. "Cokali, Inara, Lamarudu, ya isa haka." 


Bizaya ya dubi sadaukan sa ya gyaɗa musu kai. "Kuma ya isa haka." 


Nan take faɗan yazo ƙarshe aka rabu ana harare-harare. Su Cokali suka dawo bayan Armad, suma ragowar sadaukan suka jada baya suka basu hanya. 


Bizaya ya jasu izuwa cikin fadar. 


Ba jimawa suka isa ciki inda Iluru yake zaune. Kusan komai yana nan kamar yadda suka ganshi acikin kwakwalwar Ulbaru, hatta filayen horon nan suna nan kamar yadda suka gan su. 


Abin mamaki tuni Iluru yasa an sauke musu girki. Ga ƙatoton teburi na alfarma an gicciye a tsakiyar fadar kewaye da kujerun zama. Iluru na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun, ga Salsa ɗin sa da Kalhari zaune a gefe da gefen sa. 


Iluru na ganin su ya miƙe cikin fara'a tare da nuna musu gurin zama. "Ga waje ku zauna."  


Kai tsaye Armad ya zauna a tsakiya. Cokali, Inara da Lamarudu suka zauna a ɓangaren sa na hagu, sai kuma Nusi da Nostaljiya suka zauna a ɓangaren sa na dama. A ɓangaren Armad su shida, a ɓangaren Iluru suma su shida. 


Kafin a fara cewa komai Iluru ya dubi Armad ya ce, "zan baka abinda kake so indai zaka bani abinda nake so."


Armad ya dube shi tare da ɗaga gira. "Wato ba ɓata lokaci ko? Yayi. To amma kasan mai nake so?" 


"Kana so ka samu fasahar mu ta ƙarfafa jiki (tsoka da ƙashi), wataƙila sabida kayi amfani da ita akan ka ko kuma wani naka. Wataƙila ma abinda ake faɗa akanka gaskiya ne."


Armad ya yamutse fuska. "Abinda ake faɗa akaina?"


"Eh mana. Kada kace baka sani ba. Ance tunda ka ciyo ruhin Hidaya a gasar ruhin Deba kake ƙoƙarin dawo da ita. Hakan nema yasa har yanzu ba kayi amfani da ruhin ka shiga deba ba, wai sabida kana so ka haɗa mata sabon jiki ka dawo da ita. Ai kowa yasan wannan labarin."


Armad yayi ɗan murmushi. "Baka damu da kowa ba amma an dame ka."


"Ba haka bane, Armad. Duk mutun irin ka wanda ya cimma abubuwan da kayi a duniya a ƴan tsirarun shekarun ka ai dole yaja hankali. Kuma kada kayi mamakin yadda nasan kazo ne domin neman wannan fasaha, domin kuwa ba kaine na farko daka taɓa neman ta ba. A Farkon Lokaci ma'abota izza da dama suna zuwa wajen mu da irin wannan buƙata. Duba ga irin alaƙar dake tsakanin ka da Hidaya ba wani abin mamaki bane idan aka ce kana so ka dawo da ita. Hasalima zanyi mamaki ma idan bakai ƙoƙarin dawo da ita ba. Sabida haka daman nasan zaka zo tuntuni."


Armad yayi murmushi, ya ce, "Kuma nake tunanin wai shiri na a ɓoye yake."


"Haha.." Iluru ya kyalkyala dariya. "Shirin ka a ɓoye yake mana. Ai wannan abu ne wanda koda ban sani ba zaka bayyana min da kan ka. Kaga kenan ba wani abu bane da zakai ƙoƙarin ɓoyewa sosai. Abubuwan da zakai ƙoƙarin ɓoyewa su ne wajen da Nazara yake a halin yanzu, da kuma inda Ayubu yake, da kuma inda Babara yake. Sannan kuma da yadda kake ƙoƙarin yaƙar Dul'Ururu da Ikenga da Bihanzin duk a lokaci guda. Na sani kuma kaima ka sani baza ka iya yaƙar waɗannan mutane uku a lokaci guda ba. Sabida haka dole kana da shiri a ɓoye, kuma babu wanda yasan wannan shiri sai kai kaɗai da kwamandun ka."


Armad yaci gaba da kallon Iluru ba tare da yace uffan ba. 


"Nima ina da shiri na na fita daga ƙarƙashin ƙasa na koma sama kamar kowa. To amma kamar yadda ka sani Ururu sune suka danno mu ƙasa a lokacin kamfen na farko, kuma tabbbas baza su bari mu koma sama ba. Kaga idan ka kalli abin ta wata fuskar muna da abokan gaba ɗaya - wato Ururu. Ka taimake ni na yaƙi Ururu na koma sama, kai kuma na baka fasahar da kake nema. Ya kace?"


Armad ya numfasa a hankali ya ce, "Iluru, wataƙila ka girmeni da shekaru ɗaruruwa, wataƙiƙa ka fini wayo, wataƙila ka fini sanin makamar yaƙi da yaudara, to amma kada ka taɓa tunanin dolo ka kama. Indai kawai burinka na yaƙi Ururu ai kasan baka buƙatar ka bani komai, domin kuwa ko ka bayar ko baka bayar ba dole ne na yaƙi Ururu. Ka gayamin gaskiyar abinda ke ranka kafin na canja shawara a tashi daga taron nan."


"Haha..." Iluru ya kyalkyala dariya. "Haakane, haakane. Yi haƙuri, na gwada kane kawai naga irin mutumin da nake magana dashi."


"Idan ka ƙara irin wannan gwajin to zaka ga gwaji mai kyau." Inji Armad a nutse.


Iluru ya ɗan haɗe gira amma bai ɓata rai ba. Can ya numfasa yaci gaba da jawabi. "A zahirin gaskiya akwai asirin da Ururu sukai mana, dole sai an karyashi sannan zamu iya zuƙar hasken rana. Shi yasa kaga koda mun hau saman ƙasa a yanzu bama iya zuƙar hasken rana. Ba komai bane yasa haka illa wannan asiri. A lokacin gasar jinzidal da kuka fafata da Ikenga nayi zaton Ikenga yana da fasahar dazai iya karya wannan asiri. Hakan yasa a ƴan shekarun baya na kira shi domin ya karya asirin amma ya kasa. Daga baya alƙaluma suka nuna min cewa babbar izzar K'Narbig da Idanun Kuyurussa'ayi su kaɗai zasu iya karya wannan asiri. A zahiri tun daga wannan lokaci nake neman waye wannan K'Narbig ɗin tunda dai nasan Kuyuru yafi gaban hannu na. Kuma a shekarar data gabata aljanu suka labarta min cewa kai ne K'Narbig. A gaskiya bazan ɓoye ba tun daga wannan lokaci nake neman ka."


"Na sani." Inji Armad.


Iluru ya yamutse fuska. "Ka sani? Tayaya?"


"Kai dai kawai ka riƙe cewa na san kana nemana kuma nasan dalilin da yasa kake nema na. Abinda ban sani ba shi ne meye yasa kake tunanin zanyi maka wannan aiki?"


"Sabida na baka fasahar da zaka dawo da Hidaya." Inji Iluru.


A karo na farko Armad ya nuna Iluru da ɗan'yatsa. "Indai wannan ne zan iya ƙwata. Idan aka hanani na ƙone garin. Dama kuna cikin wanda kuka taimaka aka kashe Hidaya."


Iluru yayi shiru yana kallon Armad. Can ya numfasa ya ce, "Armad, akwai abinda baka sani ba. Fasahar baza ta taɓa aiki ba sai an karya asirin. Kaga kenan dole muna buƙatar juna."


Armad yayi shiru yana tafa kan teburin da ɗan-yatsa. Idanun sa suna cike da kokwanto. Can daga baya ya numfasa ya ce, "amma ka san bazan taɓa karya wannan asiri ba har sai nasan haƙiƙanin mai ya faru a tsakanin kakanka Deniz Huhutu da sauran al'ummar ƙasashen ƙasa, sai nasan waye Huhutu da kuma yadda yayi mulkin sa. Bazai yiwu na ƙara sakin kura a garken akuya ba."


Iluru yayi shiru ya kalli ƙasa. A karo na farko fuskar sa ta cika da jimami. Hatta iskar ɗakin dake kewaye dashi saida ta ɗau sanyi. 


Armad ya haɗe gira. "Meye kuma?"


"A gaskiya tarihin mu abu ne mara daɗin ji ba. Tsohuwar ƙabilar Denizawa wadda suka fara zuƙar hasken rana naman mutane suke ci. Kuma yana cikin dalilin da yasa dukkanin al'ummar ƙasashen ƙasa suka haɗa kai da Ururu suka yaƙe mu. Zan baku wannan tarihi gaba ɗayan sa amma ba yanzu ba. A halin yanzu akwai abu biyu masu muhimmanci da nake buƙata na gayamaka. 


"Na farko: ina so ka san cewa yau shekaru sama da ɗari tara kenan, ni, da shugaba Yudusu da shugaba Wuyawuya muke jagorantar tawagar masana wajen duba izuwa dalilin da yasa kakannin mu suke cin naman mutane. Kuma ya bayyana a garemu cewa abin yana cikin fasahar zuƙar rana da ƙarfafa jikin da muke amfani da ita. Hakan yasa mukai ta bincike domin ganin yadda zamu gyara wannan fasaha tayadda koda an karya asirin bazamu koma cin naman mutane ba. Kuma munyi nasara, zan nuna maka a hankali. Abu na biyu: kayi sani duk abinda zamu yi zai jawo fushin Kuyuru kamar yadda hana jinzidal zai jawo, sabida haka dolen mu mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, mu haɗa rundunar mu waje guda domin tunkarar Ururu. Ni kaɗai bazan iya ba, kai kaɗai baza ka iya ba, amma wataƙila idan muka haɗa kai zamu iya."


Armad ya kaɗa kai ya fara magana ƙasa-ƙasa kamar yana magana da kansa. "Wato Yudusu da Wuyawuya suna cikin garin nan. Mamaki, banajin yanayin-izzar su ko kaɗan." Bayan ƴan daƙiƙu ya ɗaga murya ya ce, "Iluru, dakai da duk wani jami'in jinzidal ba abin yadda bane ballantana har a haɗa kai daku. Kada ka manta kana cikin wanda suke bautar da marasa ƙarfi ku mayar dasu bayi babu dalili, kana cikin wanda suka kashe min ƴar'uwa, sannan kuma kai a kankanka da tarihin ku na denizawa ba abin yadda bane ko kaɗan, a wanne dalili zan haɗa kai dakai?" 


Iluru yayi murmushi. "Nasan na taka rawa a mutuwar yayarka, to amma abinda ya faru ya riga ya faru, babu wanda zai iya dawo dashi. Gaba ita ake kallo. Armad, haɗa kai a yaƙi basai ka yadda da mutun ba, abinda kawai ake dubawa shi ne mafita. Mai zaka samu, mai zan samu? Tunda har ka tako kazo nan kaga kenan akwai abinda kake nema a wuri na, nima kuma akwai abinda nake nema a wurinka."


"Ban yadda ba." Inji Armad.


Ɗakin yayi tsit kowa ya juyo ya ƙurawa Armad ido.


"Nace ban yadda ba. Bana buƙatar ƙara haɗa kai da wani sarkin jinzidal ballantana a maimaita min Bizanzin. Shi ma'aboci izza sau ɗaya kacal ake cizon sa a rami. Sabida haka babu wata alaƙa ta haɗin kai a tsakanin mu; kawai a bani abinda nake so ko kuma a fafata mai ƙarfi ya ɗauka."


Maimakon yaji haushi kawai sai Iluru ya fashe da dariya. "Hahaha... Wilbafos, Wilbafos, Wilbafos... Ƙarfin zuciyar ku yana bani mamaki. Ko a tarihi ƴan ƙabilar ku sunfi kowa bawa kakana Huhutu wahala sabida taurin kai da kafiya. Amma babu komai hakan ma yayi."


Ya zira hannu a aljihu ya ɗakko wata takarda ya miƙowa Armad. 


"Duba ka gani."


Armad ya ƙurawa takardar ido tsahon lokaci bai motsa ba kafin daga bisani ya miƙa hannu ya ɗauka. Yana juyata yai arba da hoton mahaifiyar sa, Fatima, da kakan sa, Zaikid, a jiki.


"Kwana biyu da suka wuce Han'Amuru ya bani labarin Tasu'a sun kama su. Yanzu kuma Tasu'an da kansu suka tabbatar min hakan."


Armad ya haɗe gira amma baice komai ba. 


Nusi ce tayi caraf ta amshe da cewa, "to kai meye naka aciki? Meye alaƙar ka da Han'Amuru harda zai kawo maka wannan labarin? Shi Han'Amurun a ina yaji? Kuma mai ya haɗa Tasu'a dasu?"


Iluru yayi murmushi. A ransa yasan tabbas ya samo kan Armad. Nan take ya kada baki ya fara jawabi, "A duk shekara akwai adadin bayin da ake ɗiba daga cikin bayin da aka tara na gasar jinzidal akai su doron ƙasa ta farko domin suyi bauta. Akan bawa sarakunan jinzidal jigilar wannan bayi daga ƙasa zuwa doron ƙasa ta farko. A wannan shekarar Hanibal aka bawa, shi kuma ya naɗa ɗan sa Han'Amuru. Duk wani labari daga doron ƙasa ta farko Han'Amuru yana jiyo shi. Ni kuma ina da alaƙa ta musamman dashi sabida haka yake kawo min wannan labari. Ta haka naji abinda ya faru da mahaifiyar ka da kakan ka. 


"Abinda baka sani ba shi ne ana buɗe kurkukun lokaci Tasu'a suka sakko domin tafiya dakai. Fatima da Zaikid da Shata su suka tare su. Ance an kama Fatima da Zaikid amma ba'a san inda Shata yayi ba. Wasu daga cikin al'ummar doron ƙasa ta farko suna cewa cikin garayar sa ya shige ya ɓace, amma labarin bashi da tushe. Kuma ba'a ga mahaifin ka Taidara ba. Ni kuma.."


Armad ya daki teburin yana huci. "Meye naka aciki da kake gayamin?"


"Ina da hanyar da zamu kuɓutar dasu." Inji Iluru. 


Armad yaja wani dogon huci. A karo na farko ya kasa kunne tare da tattara hankalin sa a guri guda. 


"Ance ka kama yarima Ƙaizadu, hakane?" 


Armad ya gyaɗa kai. "Eh."


"To yanzu dashi zamu yi amfani mu kuɓutar dasu. Han'Amuru yana kan hanyar sa ta zuwa doron ƙasa ta farko, idan ka yadda a yanzu haka sai na tura a gayamasa ya gayawa yarima Dumaƙisu idan suna son Ƙaizadu to su kawo Fatima da Zaikid."


Kai tsaye Armad ya miƙe. "Muje na gaya masa da kaina. Wannan aikin yafi ƙarfin saƙo."


Iluru ya girgiza kai. "A'a, ai haka bazai yiwu ba. Amuru yana ganin ka ta ɓaci. Tun shekarun baya yake zancen yadda zai ɗau fansa akan abinda kayi masa a gasar jinzidal, yana ganin ka zai fasa idan ma da yayi niyya. Ka barni ni nasan yadda zan tura saƙon. Acikin kwana biyu zan dawo maka da mahaifiyar ka da kakan ka, kawai kayimin alƙawarin zamu haɗa kai. Ka karya asirin da akai mana, ni kuma na baka fasahar da kake buƙata ka haɗa Hidaya, sannan kuma mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu karya Dul'Ururu."


"Nayadda." Inji Armad kai tsaye. Kwata-kwata ya manta cewa yanzu-yanzu yace bazai haɗa kai dashi ba. Wato idan kana neman lagon Armad ka kama iyalin sa. 


"Hahaha... Haka nake so naji, Armad Wilbafos." 


Iluru ya zagayo gefen Armad ya miƙa masa hannu. Armad ya cafi hannun suka gaisa. 


"Daga yau an kafa haɗakar gidan Deniz da gidan Wilbafos. Zamu haɗa babbar walima zarar muka samu nasarar ƙwato Fatima da Zaikid." Inji Iluru. 


Armad har yanzu haki yake yana nishi. "Kaga, Iluru, tura saƙon. Yi sauri ka tura."


Iluru yayi murmushi sannan ya saki hannun Armad. "Kada ka damu. Da kaina ma zanje. Bani awa uku zuwa biyar. Kuci ku sha anan kafin na dawo. Bizaya, a nunawa kowa ɗakin sa. Idan na dawo zamu ci gaba da tattaunawa."


Yana rufe baki ya juya ya fice. Armad ya miƙe daga kan kujerar sa ya fara kai-komo. A zahiri tunda wannan labari ya bayyana a gare su abincin ya ficewa kowa a rai, kuma dama tuncan baya gaban su. 


***


Tuni duhu ya fara yi. Kowa na zaune a fada an haɗa kai da gwiwa ana jimami. Wasu suna buƙatar su huta wasu kuma suna buƙatar su kwanta, dole suka yadda Bizaya ya jasu cikin fadar inda aka ware musu ya nunawa kowa ɗakin sa. Armad ne kaɗai bai bi suba, yana tsaye a fadar yana kai-komo. Ya gama yanke shawara dole ya ɗauki mataki na musamman akan rabuwa da mahaifiyar sa. Ga dukkan alamu a duk sanda suka rabu sai wani jafa'in ya afku. A wancan lokaci a sume aka kawo ta, a yanzu kuma an sace ta. 


"To wai ita ya akai ma ta tari Tasu'a ne?!" Armad ya cije baki ya dunƙule hannu. Kwata-kwata bai gane mai yake faruwa ba amma yasan dole ya ƙwato mahaifiyar sa da kakan sa duk wani abu daga baya ne. 


Can tsakiyar dare (bayan kimanin awanni huɗu da rabi da tafiyar su Nusi) Armad yana ta kai-komo yana lissafin yadda zaiyi sai ga Iluru ya dira a fadar. Saɓanin yadda Iluru ya saba - zaka ganshi a nutse cike da kamala, a wannan lokaci haki yake yana nishi kamar wanda yaga sarkin aljanu. 


"Armad, taho akwai matsala. Yi sauri." Abinda kawai ya faɗa kenan ya juya a guje. 


Armad ya zare takobi ya bishi. Koma mai yake faruwa Armad a shirye yake. Yanzu ba da bace. Koma ya ake ciki baya tsoron komai.


Acikin fada kuwa a dai-dai wannan lokaci kwamandun biyar Armad suka kawo ƙarshen tattaunawar da suke yi ta musamman akan halin da ake. Abu ne ba ɓoyayye ba suna gidan abokan gaba. Kuma lallai tabbas babu wanda acikin su baya cikin shiri. Zaka iya cewa zaman su a fadar da rashin komawar su otal ɗin da suke yana cikin shirin su.


"Nifa ban yadda dasu ba." Inji Inara. 


"Nima haka." Inji Lamarudu.


Nusi ta numfasa ta gyaɗa kai. "Ai babu wanda ya yadda dasu. Dole akwai wani ƙulli a ƙasa. Kawai dai kada mu nuna musu komai har sai mun samu abinda muka zo nema, amma kowa ya zama cikin shiri. Nostaljiya ki tafi wajen Armad ki taho dashi. Koma ya ake ciki a yanzu Armad bazai saurari komai ba idan ba zancen yadda za'a dawo da mahaifyar sa ba." 


Nostaljiya ta girgiza kai. "A'a, kije ki taho dashi." 


Nusi ta haɗe gira cikin mamaki. "Yau kuma?"


"Eh. Ina so na salallaɓa cikin fadar nan na karanta tunanin mutane naga ko akwai wani sharri da suke ƙulla mana, shi yasa. Kije ki taho dashi. Kawai dai kada naji kada na gani." Inji Nostaljiya. Ta tashi ta rufe jikin ta da doguwar riga baƙa sannan ta ɗaura rawani ta fice. 


"Cokali, Inara, Lamarudu ku zauna a ɗakin ku. Bama son suzo su tarar bama nan suyi tunanin wani abu. Amma kunga ko sunzo baza su shiga ɗakin mata kai tsaye ba. Ni zanje na taho da Armad."


Nusi ta miƙe ta nufi ƙofa. 


Kai tsaye ta tunkari inda suka baro Armad. Duk wanda ta gani a hanya idan ya tambaya sai ta gayamasa wajen Armad zata. A haka har ta isa inda Armad yake ba wata matsala. Tana zuwa ta tarar da Armad ya haɗa kai da gwiwa yana jimami.


Ta tsaya daga nesa ta ɗanyi tunanin mai zata ce masa kafin daga bisani ta ƙarasa. 


"Armad..."


Armad bai amsa ba. Amma tana ganin idonsa a buɗe daga inda take sabida haka tasan yana jinta. 


"Menene?"


Har yanzu bai ɗago ba ballantana ya bata amsa.


"Wai menene ne, ka fara bani tsoro?"


Ta miƙa hannu ta ɗago fuskar sa. Abu na farko data gani shi ne hawaye. Idanun sa sunyi jajawur.


"Ka gayamin menene? Maiya faru?"


"Ba komai. Meye amfanin ɗan da yake zaune yana hutawa uwar sa tana kurkuku?" Inji Armad. 


Nusi ta miƙa hannu ta share masa hawayen sa.  


"Ba laifin ka bane. Kuma zamu ƙwato su ko za'a mutu. Amma yanzu dai ka daina wannan hawayen kafin kasa na fara."


Armad ya goge fuskar sa ya juyo ya kalleta. "Ji nake kamar bani da amfani a duniya. Hidaya ta tafi, nafi shekara goma sha biyar banga mahaifina ba alhalin kuma yana da rai, ga mahaifiya ta kullum a wahale."


"Waye yace? To ai duk abinda ka faɗa babu laifin ka. Kaga ka ajiye wannan zancen, tashi muje ka kwanta. Kana samun bacci ka wartsake yaka ji daɗi."


Armad ya buɗe baki zaice a'a amma Nusi ta jashi ya miƙe. "Muje. Idan kayi bacci zaka ware. Duniya ai sama da ƙasa ce. Kuma ba yau aka fara ba. Haba, Armad, kai da zaka mulki duniya har wannan ya girgiza ka."


Ta riƙe masa hannu ta ɗora a kafaɗar ta sannan tayi masa jagora suka nufi cikin fadar.


"Wai Iluru har yanzu bai dawo ba?"


"Bai dawo ba, ban san ina ya tsaya ba."


"To, fatan dai ALLAH sa lafiya."


"Amin dai."


Ba jimawa suna hira har Armad ya saki jiki. Suna ƙarasowa masaukin su ta nuna masa ƙofar ɗaki na farko ta ce, "ga ɗakin ka."


Ta murza ƙofar ɗakin ta buɗe ta shiga da Armad ciki. 


Ƙaton ɗaki ne da ƙaton gado samfurin sabuwar amarya. Da mudubi da banɗaki da teburin rubutu da gujera. Sai kuma ƴar kantar littafai acan gefe.


"Ka kwanta kayi bacci. Da safe zaka wartsake, nayi maka alƙawari."


Ta juya zata fita amma Armad yayi wuf ya riƙe mata hannu. "Kada ki tafi. Ki zauna kiyi min waƙa, wataƙila hakan yasa na samu na ɗanyi bacci." 


Nusi ta cuno baki tana hararar sa. "Har yaushe ka fara son ayi maka waƙa kafin kayi bacci? Malan ka kwanta kayi bacci kawai idan zakai."


Armad ya haɗe rai cikin wasa. 


Nusi na ganin haka ta fashe da dariya. 


"To zanyi kwanta. Shikenan."


"Shikenan." 


Armad yai tsalle ya ɗare gado. Nusi ta kwanta a gefen sa ta fara rera waƙa. 


***

Wataran ayi zafi.


Wataran ayi sanyi.


Wataran ayi inuwa.


Wataran ayi rana.


Da zafi da sanyi da inuwa da rana duk abu ɗaya ne.


Kawai ya danganta da yadda kake kallon su.


Wataran ayi zafi.


Wataran ayi sanyi.


Wataran ayi inuwa.


Wataran ayi rana.


Da zafi da sanyi da inuwa da rana duk abu ɗaya ne.


Kawai ya danganta da yadda kake kallon su.

***


Tana rufe baki Armad ya tashi zaune ya rungume ta. "Kin iya waƙa."


"Banda ƙarya." 


"Da gaske."


"Ka rantse."


"Na rantse."


"To naji. Sake ni nima naje na kwanta. Na gaji."


Har a wannan lokaci Armad na rungume da Nusi. Kuma duk da tace ya sake ta bai sake ta ba. 


Wasu daƙiƙu uku masu nauyi suka wuce babu wanda yace uffa acikin su. 


Nusi ta ɗan tura Armad baya amma bai motsa ba. 


Take jikin Nusi yayi sanyi. Da kyar ta buɗe baki ta ce, "kana so ka kashe auren ka ne?" 


"Bana so na kashe aure na, amma ina son ki." Inji Armad.


Nusi taja da baya. "Kana so na?"


Armad ya gyaɗa kai. "Eh, kuma gobe zan aure ki. Amma fa idan kin yadda. Dama ai babu wanda ya haramta mata biyu."


Nusi tayi ƙuri tana kallon sa kamar wadda taga gawa. 


Shi kuwa murmushi kawai yayi, ya ce, "to ai yaba kyauta tukuici, Nusi-ya, idan nace har yanzu ban san kina so na ba duk abinda kikai min ai na zama butulu. Sabida ni meye baki rasa ba? Da tuni ke sarauniya ce. Mutanen da a duniya zasu iya sadaukar da kansu kamar ke basu da yawa. Ina son ki."


Nusi tayi kasaƙe tana kallon ikon ALLAH.


***


Wannan kenan. 


A dai-dai wannan lokaci da Armad yake ƙoƙarin ɗaura igiyar aure da Nusi Kil'zanki, abin mamaki sarki Iluru ne da wani Armad ɗin suke ta keta hazo.


Idan mai karatu bai mantaba, a kewaye da daular ƙarƙashin ƙasa akwai katafaren daji mara iyaka. Ance babu wani mahaluƙi daya taɓa tsinkaye cikin wannan daji ya dawo da ransa. A kewaye da wannan daji akwai busasshiyar ƙasa wadda ita ba sahara bace amma bata ɗaukar shuka, ko ciyawa babu akanta. Masana sunce girman wannan busasshiyar ƙasa kaɗai ya haura girman duk garuruwan dake ƙarƙashin ƙasar. To idan ka wuce wannan busasshiyar ƙasa zaka tadda katanga wadda aka gina da jan dutse ziryan ta tokare da sama. Kallo ɗaya tak zaka san babu wani mahaluƙi da zai iya shallake wannan katanga. Kuma babu wani littafi daya rawaito akwai ƙofar shiga a jikin wannan katanga. Kai wasu malaman ma suna ganin ba'a gina ta dan a shiga ba, sabida haka bata buƙatar ƙofa. 


To amma abin mamakin a bayan wannan ƙofa ruwa ne. Wasu sunce wannan ruwan ya haɗe da ruwan maliya dake can saman doron ƙasa ta farko, ko gaskiya ne ko ƙarya ne babu wanda ya sani, amma dai girman wannan ruwa ya haura gaban misali. Zaka iya cewa sai an haɗe dukkan dazukan farko kafin su kaishi girma. 


Armad da Iluru ketawa kawai suke ta cikin hazo suna ƙara dannawa cikin wannan dazuka.


Bayan ɗan lokaci Armad ya ƙara duban Iluru ya ce, "kace akwai ɓarauniyar hanya da zata kaimu doron ƙasa ta biyu ta nan?"


"Eh mana, mun kusa zuwa. Amuru yana can yana jira, kuma a halin da ake ciki baza mu iya bi ta sama ba. Kasan dai Dul'Ururu bazai bari ka shigar masa ƙasa ba. Kuma wannan abu ne muke so muyi cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba."


Armad ya yamutse fuska, bai san mai yasa ba amma akwai wani abu wanda ba dai-dai ba acikin al'amurin dake faruwa. Ya kasa gane meye amma yana ji a jikin sa akwai matsala. 


Bayan ɗan gajeren tunani yayi duba izuwa tsarin ruhin sa ya tura saƙon karta-kwana. "Miyura, Zaren-izza, Al-yaya, ku shirya. Komai zai iya faruwa."


Sannan ya juyo izuwa idon sa rufaffe na hagu, ya ce, "Saif-al-Barzak, shirya."


"Dama da kabi shawara ta mun kashe kowa da komai da ba shikenan ba sai muyi rayuwar mu mu biyu." Inji muryar Saif-al-Barzak wadda shi kaɗai yake iya ji.


Armad bai bata amsa ba, juyawa kawai yayi izuwa cikin duniyar Negrinki. "Hasanu, Ƙaizadu, Elbinuil, kuma ku shirya."


#


To fa, ana dara ga dare yayi, wai wanne Armad ɗin ne na gaskiya? Kuma waye ɗayan? Mai Iluru yake shirin yi?


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...