Babi na 25 : Fasahar Marubutan Farko
Acikin garin Khan haka a kwana a tashi kwana uku suka wuce.
Armad yana ta tunanin irin abubuwan daya gani a lokutan da suke zazzaga gari dasu Cokali, kuma babban abinda ya kasa cirewa a ransa shi ne sunan Bihanzin mai dauwamammen ciwo!
To da yake dama yana zaune ne acikin ɗaki a wannan lokaci, kawai saiya tashi ya ɗauki alƙalami ya zaro ɗaya daga cikin ganyayyakin da aka kawo masa ko zaiyi rubuta, ya rubuta sunan Bihanzin da manyan baƙi da yaren Alderiya(Aldurish).
Haka ya kwana yana tunane-tunane, bayanda gari ya waye, ya gama kintsawa kenan saiga Iliyásis ya bayyana a gabansa da labarin maza-maza ya kamata su isa wajen Non-toch-teka, domin jiya da daddare saƙo ya iso daga sarki cewa an rage kwana uku akan yadda aka tsara za'a buɗe wajen, saboda wani dalili da ba'a bayyana ba. A azalzale haka Armad ya ƙarasa shiri suka fice tare da Iliyásis.
Har a lokacin da suka fita rana bata ɗaga ba, kuma iskar alfijir tana nan tana kaɗawa, tana kaɗa maɗaurin kan Armad da kuma sajensa, yanayin da ya ƙara masa kyau matuƙa.
Basu ɗauki lokaci ba suka iso wajen da zasu. Tun daga nesa Armad ya hango wani katafaren gini, wanda iyakacin hangenka, dama da hauni, sama da ƙasa duk shi ne, kuma baka iya ganin ƙarshensa.
Iliyásis ya nuna masa da hannu cewa acikin wancan ginin abinda muke nema yake.
Suna isa wajen, akwai mutane ƴan tsiraru waɗanda da dama kallo ɗaya kawai sukai musu suka ɗauke kai, saboda basu sansu ba sannan kuma tuni labari ya gama bazuwa cikin garin cewa yau za'a fara shiga Non-toch-teka, saboda haka ba abin mamaki bane ba kowa ma ya bayyana a wajen.
Amma daga lokacinda suka fara jan hankalin saura shi ne, daga sanda suka zarce harya zuwa ɗaya daga ƙofa goma dake gaban ginin.
Sannan kuma nan take Iliyásis ya miƙa wata takarda inda mai gadin ya karɓa kuma ya buga mata sheda, sannan ya buɗe musu ƙofa suka wuce.
Tun daga wannan lokaci ƙus-ƙus ya fara tashi, su na cewa, ''kaɗai mai iya shiga a wannan lokaci sai dai mai shedar majalisar!
''To su waye waɗancan mutun biyu?'' Haka dai suka ci gaba ƙus-ƙus a tsakaninsu a yayinda jama'a suke ta ƙara zuwa.
Su na shiga ciki, mamaki ya ƙara cika zuciyar Armad, saboda abinda ya gani, yayi matuƙar saɓawa abinda yai tsammani.
Domin shi a tunaninsa wani ginin ko kuma dai wani abun zai ƙara gani, amma bisa mamaki bai ga komai ba.
wato dai a taƙaice babu komai sai fili fetal.
Sannan kuma kamar inda Armad ya gani a lokacin da yake saukowa daga doron ƙasa ta uku, shi ma wannan waje komai launinsa iri ɗaya ne.
Hatta ƙasar wajen da samaniya.
Sai dai a wannan lokaci maimakon shuɗaye kamar na wancan lokaci, waɗannan farare ne!
Duniyar komai fari fat kamar farin kitse.
Babu kowa saisu kaɗai.
Iliyasis cikin sauri-sauri ya fara yiwa Armad bayanin mai ya kamata yayi.
''Wannan wajen gaba ɗayansa na musamman ne. Amma babban inda abin yake shi ne idan ka shiga ƙofa ta gaba!
''Yanzu daga dai-dai nan inda muke, zaka rufe idanunka, kayi taku bakwai manya.
''Sannan ka buɗe. Zaka ga wata ƙofa ta bayyana a gabanka. Ka tura wannan ƙofa ka shiga ciki.
''Abu na farko daya kamata ka sani shi ne, kana shiga wannan ƙofa kabar wannan ƙasa, domin kuwa wannan ƙasar da zaka shiga an yanko tane daga gari na huɗu na daular Maikironomada.
''Ƙasar da babu wanda ya isa ya taka face mai ƙarfin jinin maikironomada sama kaso casa'in da biyar a jikinsa.
''Saboda haka ne kafin ka shiga anan zan koya maka wata fasaha.
''Wadda ake amfani da ita wajen shiga wannan waje da ruhinka maimakon jikinka.
''Kai sani cewa yanzu da muka shigo wajen nan babu wanda zai iya ƙara shigowa koda kuwa an buɗe masa ƙofa, har sai mun fita.
''Kuma mu ma baza mu iya fita, ko mun daɗewa indai ba'a buɗe ƙafar gaban dana gaya maka ba.
''Saboda haka ka kwantar da hankalin ka, ka nutsu ka koyi wannan fasaha, saboda ita zata zama gimshiƙi Izzarka anan gaba.
''Sai dai matsalar guda ɗaya anan ita ce ta lokaci.
''A hasashen da mai gadin can ya gayamin mafi ƙanƙantar lokacin da zaka ɗauka shi ne;
''Shekara GOMA!!''
Baki a buɗe, idanu cike da mamaki, sannan kuma zuciya cike da kokwanton ko yaji abinda Iliyasis ya faɗa dai-dai, Armad yai ajiyar zuciya gami da tambaya, ''shekara..... nawa kace???
Kafin Iliyasis yace wani abu tuni Armad ya ci gaba da magana;
''inaaa, kai ka kai, ai wannan ba abu ne mai yiwuwa ba....kawai nuna min hanyar fita dan ALLAH.
''Akwai abinda ya zama wajibi da nayi, wanda kuma shi ya kawo ni wannan ƙasa.
''Sabida haka ina ganin kawai zan nemi wata hanyar da zanbi na inganta Izza ta, kuma koma badan wannan ba ai.......''
Tunda Armad ya fara magana Iliyasis yake ta ƙoƙarin tsayar dashi, amma ina idanun Armad sun rufe ya fituttuke baya ji baya gani.
Sai a wannan lokaci ne ya samu nasarar tsayar dashi da ajiyar zuciya, ''hmmmm!!
''Ka dakata mana kaji ƙarshen maganar, ko.''
Armad na haki ya dubi Iliyasis wanda kawai murmushi ya gani a idonsa, irin murmushin nan mai ɗauke da saƙon 'ka kwantar da hankalinka, akwai mafita!'
Ya ɗan kyaɗa kai tare da kyaran murya da niyyar fara jawabi, ganin cewa hankalin Armad yaƙi kwanciya, kuma daga dukkan alamu indai ba bayani yaji cikakke ba, to fa babu yadda zaiyi ya kwantar da hankalin nasa.
''Abinda baka sani ba shi ne, wannan waje, wajene na musamman, ta ɓangarori da dama.
''Babban abin shi ne lokaci!
''Kai sani cewa duk kwana ɗaya a waje dai-dai yake da kusan kwana ɗari da ashirin anan wurin!
''Kaga kenan duk kimanin kwana uku a waje, dai-dai da kusan shekara ɗaya anan. A taƙaice dai yin shekara ɗaya acikin wajen nan baifi kwatankwacin kwana uku a waje ba.
''Kaga kenan shekaru goma da aka baka hasashe, baza sufi kwana talatin ba a waje.''
Yai shiru fuskarsa cike da murmushi yana karanta mamakin dake cikin idanun Armad. Kai daka ganshi kasan bai taɓa tsammanin wannan abu ba.
Ana haka kafin Armad yai magana, tuni Iliyasis ya ce, ''saboda haka baka da wata damuwa.
''Kuma wannan wata dama ce daka samu da ba lallai ka ƙara samun irin taba, saboda bamu san yaushe ne jikinka zai iya ƙara jure shigowa wannan waje ba.
''Saboda wataƙila baka sani ba, amma akwai adadin da a gabaki ɗayan rayuwar mutun zai iya shigowa wannan waje.
''Kuma da dama daga cikin mutane, baya wuce sau ɗaya, amma ga dukkan alamu zaka iya wuce ɗayan, amma dai ka sani cewa ko shugaba Bihanzin karo huɗu kaɗai jikinsa ya iya ɗauka, sannan kuma na ƙarshen saida yai shekara tara yana jira kafin jikinsa ya iya.''
Yana gama wannan bayani, ya zira hannu cikin ƴar alkyabbarsa, inda ya zaro wata ƴar takarda mai zane-zanen abubuwa guda biyu akai.
Ɗaya zanen mutun ne ɗaya kuma wata ƙatuwar dabba ce mai ƙaho ƙahon-huna akanta.
Kuma abin mamakin shi ne a kallo na farko, sai kayi tunani cewa wannan ƙahun huna sun kusa goma, amma idan ka ƙura ido sai kaga ai basu da yawa sosai, amma kuma idan ka fara ƙoƙarin lissafa su, bisa mamak sai ka kasa.
Komai yadda kayi ƙoƙarin lissafa su baza ka iya ba, hasalima kana ƙara matsawa kusa da su dan ka lissafa, suna ƙara rikita ka.
Hakan ma yasa Armad yai saurin ɗauke idonsa daga kan takardar aaboda tuni kansa ya fara juyawa.
Iliyasis ya ce, ''kamar yadda ka riga ka sani, duk wani ɗan adam yana da yana da ruhi kuma yana da gangar jiki.
Gangar jiki ba wani abu bane ba illa jini da tsoka kawai, wanda zasu iya riɓewa kuma mutun zai iya canjawa.
''Saboda haka a zahiri, sirrin Izza gaba ɗaya ya ta'allaƙa ne da ruhin jikin mutun, wanda baya riɓewa kuma ba'a taɓa canjashi.
''Dan a wannan zamanin ma da wuya ka samu mutun ɗaya dake da wannan bayanin. Kuma a gskiya ban sani ba ko zaima wani amfani ko kaɗan, sai dai yaya Nusi ta barmin umarnin cewa ya zama wajibi komai ka sani.
''Yanzu abu na gaba shi ne.....''
Armad ya katseshi da cewa, ''wato... tunda muka shigo wajen nan nake ta mamakin wani abu.
''Da farko ina kokwanto, amma yanzu da naji labarin nan naka na samu tabbashin abinda nake tunani.
'Wannan kuwa ba wani abu bane ba illa cewa lallai nasan wannan waje naku da kukewa laƙabi da Non-toch-teka ciki da bai!!!
Iliyasis yaci gaba da bayani, "Daga nan inda muke, gangar jikinka bazata iya wucewa ba, saboda haka..." yana faɗar haka ya tafa hannunsa biyu, inda wata akwatun zinare ta fito daga jikin wannan takarda.
"Zaka shiga cikin wannan akwatu, sannan kuma daga nan ruhinja zai futo a matsayin fatalwa, wanda shi zai take maka hanya zuwa ainahin inda zaka ɗauki wannan fasaha.
"Wato dai a taƙaice, gangar jiki bata taɓa wajen da zaka shiga!"
Bayan sun gama yin ƴan ragowar bayane-bayanensu, Armad ya shiga cikin akwatin nan, ya kwanta. Ba'a jima ba kuma, abu kamar wasa saiga wata siffa mai kama da Armad sak, ta taso daga jikinsa, ta futo daga cikin akwatin.
Komai nata irin nasa ne sak, hasalima, idan ba taɓa ta kayi ba, kaji hanninka ya wuce ba, to baza ka taɓa gane cewa ba shi bane.
Nan take Iliyasis, yai sauri ya rufe akwatin.
Wani sirri da wannan akwati yake dashi, shi ne, indai ka shiga ciki, to fatalwarka da zata fito, zata fito da ilmin duk yadda ya kamata tayi, da hanyoyin daya kamata tabi acikin wannan waje mai suna Non-toc-teka!
Tana fitowa, kawai ta nufi arewa ta fara yin taku cikin tsari. Taku bakwai kaɗai tayi, wata ƙofa ta bayyana a gabanta, kana daga bisani ta buɗe. Wannan fatalwar halitta wadda ga dukkan alamun babu ƙashi babu jini a jikinta, hasalima kamar hoto kawai take, ta shige cikin wannan ƙofa kai tsaye.
A wajen ƙofar kuma inda Iliyasis ke tsaye, ajiyar zuciya kawai yai, sannan ya nemi waje ya zauna ya fara addu'a.
Acikin wannan ƙofa kuwa, fatalwar Armad ta bayyana a wani fili mai ɗauke yanayin daɗewa a duniya, kai kace ya shekara miliyan da samuwa. Irin yanayin da idan baka da ƙarfin zuciya zai iya kaika ƙas cikin zafin nama.
Take wannan fatalwa ta rufe idonta gami da dosar gabas maso kudu ta fara tafiya, a wani salo na taku masu tsayi da tsari, iri ɗaya sak.
A haka saida tayi taku arba'in cif-cif sannan ta tsaya ta kuma buɗe ido.
Tana buɗewa cikin zafin nama kamar wadda ke lissafa lokaci, tayi sauri gami da rufe idonta na dama, sannan ta juya izuwa ɓangaren yamma maso kudu ta fara taku wanda girmansu dai-dai yake dana baya.
A haka saida tayi taku ashirin cif-cif, sannan da sauri kamar a baya, ta ƙara rufe idonta na hagu sannan ta buɗe na daman, inda ta ƙara juyawa izuwa ɓarin gabas maso kudu, kuma ya fara tafiya komai kamar a baya.
A wannan karan ma taku ashirin tayi cif, sannan ta ƙara tsayawa, gami da buɗe idanunta.
A wani salo na kwarewa wannan fatalwa ta ƙara juyawa izuwa ɓarin yamma maso kudu, sannan ta rufe duk idanunta guda biyu ta aiwatar da taku arba'in cif-cif sannan ta tsaya.
Amma a wannan lokaci bata buɗe idonta, kurum kawai tayi a tsaye cak.
Bayan wucewar lokaci mai tsayi wanda yakai kamar kwana biyar ko shida, sannan ta buɗe, kuma ta nemi waje ta zauna ƙafafu a tanƙwashe tana fuskantar gabanta.
Babu wani abu na musamman daya faru, kai hasalima babu abinda ya canja ko kaɗan. Komai yana nan shiru kamar kullum.
Haka dai abubuwa suka ci gaba da gudana, kafin kace meye wannan wata yayi babu abinda ya faru, wannan fatalwa tana nan a zaune tana fuskantar gabas.
Wata biyu, wata uku, wata huɗu, biyar..... shekara ɗaya......haka dai lokaci yaci gaba da wucewa har akai shekara tara da rabi cif-cif, wannan fatalwa batai ko gezau ba, kai hasalima ko rufe ido ba tayi ba.
A wata rana ta litinin, sha huɗu ga watan Yuri (wata na uku a kalandar Aldurish), wannan fatalwa na zaune, sai kawai ruwa ya fara sauka kamar da bakin kwarya daga wannan farin sararin samaniya, dake wajen.
Kuma wani abun mamaki shi ne shi kansa wannan ruwa ja ne, jajawur kamar jini.
Bayan an ɗauki kwanaki da dama ana wannnan ruwa, sannan ya tsaya cak.
Anyi ruwa mai ƙarfi, amma dukkansa wannan farar ƙasa ta tsotse kaf, babu ko alamun ragowa, kai idan ka zo a bayan an gama ma, ba lalle kace anyi ruwan ba.
Kuma duk abinda ke faruwa, wannan fatalwa na zaune har a wannan lokaci batai ko gezau ba.
Toh, kwana uku da gama wannan ruwan, wata rana da safe komai a wannan duniyar ya fara girgiza kama za'ai girgizar ƙasa.
An daɗe ana hakan, kafin daga bisani komai ya fara lafawa.
Bayan ƴan mintuna ƙura ta lafa, wasu ƙofofi guda uku su bayyana a gaban wannan fatalwa.
Suna bayyana, dukkansu suka buɗe a lokaci ɗaya, kuma abubuwan dake cikinsu suka bayyana ga idanun wannan fatalwa ta Armad.
Acikin wannan akwati dake ɓangaren dama babu komai sai wata tasa da wani ruwa acikin ta. An rubuta Farkári ajikin tasar.
Na tsakiya kuma wani ɗan littafi ne mai jan bango, kuma anyi rubutu da jini a jikinsa, wanda kodai bai fita ba sosai, ko kuma lokaci da shekaru yasa ya fara gogewa. Amma dai dukkanin girmansa baifi tafin hannu ba.
Acikin akwatin ɓangaren hagu kuma wani mashi ne, wanda a tsininsa akwai wuta tana ci, wadda ga dukkan alamu tafi shekaru dubu tana ci bata taɓa ɗaukewa ba, kuma bata da niyyar ɗaukewa.
Ajikin mashin an rubuta Mashìral-Iburish!
Bayyanar abubuwan nan keda wuya wannan fatalwa ta tashi daga inda take, a lokacin farko tun bayan shekaru tara acikin wannan duniya ta Non-toc-teka.
Bayan ta miƙe ta ɗaga hannunta sama, kuma babu ko alamun tsoro, ta caka shi acikin ƙirjinta, inda da kyar bayan lalube, ta fito da hannun nata a tsininsa akwai alamun jini, wanda bai wuce ɗigo ɗaya zuwa biyu ba.
Cikin sauri, kamar wadda take tsoron jinin zai iya ɓacewa idan ta ɓata lokaci, ta matseshi a babban ɗan yatsanta na dama, inda ta nunoshi gaban waɗannan akwati uku.
A wani yanayi mai ban mamaki duk waɗannan abubuwa uku dake cikin akwatin wato da mashin da tasar da kuma littafin, suka fara girgiza da ƙarfin gaske, kamar waɗanda suke so su fice daga cikin akwatunan.
Hakan ya ɗau lokaci yana faruwa, kafin daga bisani wannan littafi ya taso da gudu ya faɗa kan tafin fatalwar.
Hakan na faruwa, ragowar abu biyun suka daina motsi kwata-kwata, hasalima akwatinan da suke ciki komawa sukai suka rufe, kafin daga bisani su ɓace ɓat.
Shi kuma wannan littafi kafin kace meye wannan tuni wannan ɗigon jini ya hau kan jan rubutun dake kansa, wanda bai fita ba sosai.
Kafin kace meye wannan, wannan rubutu ya juye izuwa sunan Armad wanda ya fito tar-tar.
Hakan na faruwa wannan duniya ta fara disashewa kuma kan ƙiftawar ido da bismillah ta ɓace inda wannan fatalwa ta ƙara bayyana a inda ta bar Armad acikin akwatin nan.
Koda bayyanar ta, sai Iliyasis wanda ke zaune gefe guda ido ya ɗago kai ya kalleta, acikin zuciyar yace, "har ila yau kwananta bai kai talatin ba."
Sai dai kuma amma acikin duniyar data shiga, lissafin ya haura na shekaru
Tana bayyana riƙe da littafin a hannu sai ta fara kusantar wannan akwati, amma bisa mamaki wata iska mai ƙarfin gaske ta miƙe inda ta shiga taakaninsu da akwatin, a wani yanayi na nuna cewa lokacin komawarta baiyi ba.
Har a wannan lokaci, wannan fatalwa bata kalli Iliyasis ba, kawai sai ta koma gefe guda ta nemi waje ta zauna.
Tana zaune wannan littafi na hannunta, kawai saiya fara haske, inda ba tare da ɓata lokaci ba wannan littafi ya rikiɗe izuwa siffar wata takobi, wadda bisa mamaki a jikin farin ƙarfen ta aka rubuta sunan Armad a jiki.
Tana da ƙota baƙa mai ɗauke da zanen wasu ɗalasimai a jiki, sannan kuma a ɗayan ɓangaren ta, wanda babu sunan Armad ɗin, an saka RIFLEGZIYA!
Jikin takobin farin ƙarfe ne kawai, wanda kuma duk da kyallin da yake, a kallo na ɗaya abinda zai faɗo maka rai shi ne, gama garin ƙarfe ne kawai!
Dukkanin abubuwan dake faruwa akan idon Iliyasis suke faruwa, kuma daga ganin yadda ya miƙe tsaye cikin firgici, idanun sa acike da ɗimauta kasan cewa an kai maƙura wajen gigita shi da abinda bai taɓa tsammani ba!
Babu abinda ke fita daga bakinsa face wasu kalmomi guda uku, ''Fasahar... marubutan..... farko!!!!''
***
Abu ne sananne a wannan zamani cewa, kusan kowacce babbar ƙabila suna da ire-iren fasahohinsa na sarrafa Izza na musamman.
Da dama daga cikin irin waɗannan fasahohi kamar wata shedar mallaka ce dasu, wato ana gani ansan cewa ƙabila kaza ce, kuma koda wani ya samu ya ɗan kwafe to zaka samu basu da yawa, kuma sannan da dama basa iya kaiwa matuƙa wajen kwarewa akan irin wannan fasaha.
Ta hanyar wannan fasaha zaka iya rubuta sunan abu wanda kake so, kuma wannan abu ya tashi daga siffar rubutu izuwa wannan abu.
Sannan kuma daɗin daɗawa zaka iya juyarda abinda ya riga yake a gaske izuwa rubutun.
Misali; zaka iya sanya sunan takobi, sannan kuma ka rubuta yanayin yadda kake son wannan takobi ta kasance a gaske.
Idan kayi amfani da wannan fasaha sai wannan rubutu ya juye izuwa takobin da kake buƙata.
Sannan kuma a ɗaya ɓangaren idan kana da takobi kana so ka ɓoye, to zaka iya rubuta bayanin wannan takobi taka, sannan kayi amfani da wannan fasaha ka maida ita zuwa rubutu.
Tarihi yazo cewa Maikiro Abbas, wato sarkin Maikironomada na biyu a duk tarihi shi ne ya samarwa da ƙabilar wannan fasaha.
Kuma kamar yadda yazo Maikiro Abbas yana daga cikin mutane da bakwai da suka ƙirƙiro rubutu a dukkanin wannan zamani.
Toh! gashi dai sa'a ko kuma ƙaddara ta kawo Armad ya mallaki takobi ta wannan hanya.
To ko wanne sirri ke ɗauke ajikin wannan takobi, ko waye yai amfani da irin wannan fasaha wajen adana ta, ko ta waye, sai ku biyo mu kusha labari.
***
Acikin wannan waje kuwa a wannan rana da wannan takobi ta bayyana, fatalwar Armad da Iliyasis su na zaune su na jiran lokaci.
Tsaho kusan shekara goma kenan tun bayan shigar Armad cikin wannan akwati.
Amma idan ka kalli Iliyasis, wanda suka shiga a tare zaka samu cewa yana nan tamkar ranar da suka shigo, ko kaɗan jikinsa bai canja ba.
Hasalima kai baza kace yayi sati bama.
Wannan ba wani abu bane ya jawo haka ba, illa sirrin wannan waje.
Wanda suka haɗa da canjin ƙidayar lokaci tsakaninsa da waje, sai kuma cewa baka buƙatar cin abinci ko kwaya idan kana cikin wannan waje.
Domin kuwa ko gajiya ba'a yi, ba kuma a bacci, kai Iliyasis ko ƙifta ido ma baƴayi.
Amma abisa dole saboda wani haske mai kashe ido dake tashi daga jikin takobin dake hannun fatalwar Armad ya saka shi rufe ido a wannan lokaci.
Kafin kace meye wannan wannan haske ya cika ko'ina baka ko ganin gabanka.
A haka sama da daƙiƙa sittin ta wuce, Iliyasis yana ta ƙoƙarin buɗe ido yaga meke faruwa, amma haƙar sa yaƙi cimma ruwa.
To yana cikin haka ne, wannan haske ya fara ɗaukewa da kaɗan da kaɗan. Inda bayan wani lokaci ya ɓace ɓat, Iliyasis ya samu damar buɗe idonsa, amma sai idanun nasa sukai masa arba da abinda bai zata ba.
Domin kuwa babu abinda ya gani face Armad shi kaɗai a tsaye a inda da wannan akwati da take.
Duk da yana da nisa daga inda Armad yake, amma tun daga inda yake, yana jiwo yanayin babbar Izza na tashi daga jikin Armad.
Sannan kuma ga tambarin Miyurar dake goshinsa na fitarda wani jan haske ta cikin kyallen dake ɗaure a goshin nasa.
Idan kuma da babu wannan kyallen da Iliyasis ya samu damar ganewa idonsa wani sabon tauraro dake kewaya tambarin dake gaban goshin na Armad.
Sannan kuma daga irin yanayin babbar Izzar dake tashi daga jikin Armad da kuma wata sabuwar takobi dake rataye a wuyansa ta ɓangaren dama, Iliyasis yasan cewa Armad yaci nasarar samun babbar fasaha a wannan waje mai tsohon tarihi da ake kira da Non-toc-teka.
Daɗin daɗawa gashi Al'yaya, kuma gashi Magajin Wilbafos.
Tunda Iliysis baisan sunan Armad na gaskiya ba, saboda haka tuni a wannan lokaci ya fara yi masa shigen kallon girmamawar da yake yiwa shugaba Bihanzin.
Hasalima yana gab da zubewa a ƙasa ya kwashi gaisuwa wajen Armad, Armad ɗin ya iso gareshi gami da dafa kafaɗarsa, lamarinda yasa ya dawo hayyacinsa, amma duk da haka yakai maƙura wajen gigita da ƙarfin aniyar Armad da kuma yanayin yadda yaga ƙaddara tana tare dashi.
Armad cikin wasa ya fara magana, ''ahhh..Iliyasis! yi haƙuri, inaji a jikina mun ɓata lokaci da yawa ko?'' maganar da wasa yake yinta amma girman izzar da take ɗauke da ita yana da yawan.
Wanda har yakai yadda yasa Iliyasis ya kasa bada amsa, babu abinda ya iya sai kawai girgiza kai, ƙafafunsa na karkarwa kamar bazasu iya ɗaukansa ba.
Kuma yana da kyau mai karatu ya sani cewa Iliyasis baya daga cikin na ƙasa a fagen Izza, hasalima a ko'ina kakaishi za'a saka shi acikin jarumai madaidaita, domin tuni matakin Izzarsa yakai ɗari da ashirin da ɗaya.
Amma a bisa mamaki ƴar wannan tambaya da Armad yayiwa Iliyasis ta rikita shi.
Armad ɗin ya fahimci haka, kuma baiji daɗi ba, duk da kuwa yasan baya sane hakan ya faru. Tunda yana da cikakkiyar masaniya cewa wata sabuwar Izza ta shiga jikinsa kuma yana buƙatar zallar fafatawa da mazaje kafin ya iya sarrafa ta, inba haka ba kuwa, zata iya jawo matsala babba, domin zata iya fin ƙarfinsa.
Saboda haka ya bawa Iliyasis haƙuri, wanda daga baya ya nuna masa ai ba komai.
Ya kuma gaya masa cewa shima yana nan tafe. Sukai dariya kawai.
Comments
Post a Comment