***
Babi na ashirin da uku : Matafiyan Alwashi
Tuni labari ya bazu kusan ko'ina acikin garin Khan, cewa ga abinda ke faruwa, kasancewar da dama sunada masaniyar me wannan hasken yake nufi.
Saboda haka tuni mutanen garin suka fara tattauna abubuwa da dama, wasu suna farin ciki wasu baƙin ciki wasu kuma mamaki, kai wasu ma tuni sun fara azama domin isa bakin wannan ƙofa domin ganewa idanunsu.
Amma ina haƙarsu bai cimma ruwa ba domin kafin ma su kansu ƴan tsirarun mutanen da ke wajen su ƙarasa suga fuskar Armad, sun nausa cikin garin.
Sannan kuma wata sa'a data faru, shi ne da dama na mutanen baƙi ne, saboda haka suna da buƙatar subi ta cikin wannan ƙofa a hankali, domin yana daga cikin amfanin waɗannan mutun-mutumi duba zuƙatan masu shiga garin, domin tabbatar da cewa basu zowa garin da sharri ba.
Kuma hakan nema yasa a daular Maikironomada ake auna girman gari da kuma falalar na cikinsa, da adadin waɗannan mutun-mutumi da suke dasu.
Haka dai suka ci gaba hango su Armad har suka ƙule a nesa.
Kafin daga bisani su juyo da dubansu kan waɗannan mutun-mutumi guda shida.
Inda suka ga wannan haske da da ya tashi ya bazu ko'ina, ya fara dawowa yana haɗuwa a tsakiyar waɗannan mutun-mutumi shida.
To amma saboda bada sauri yake dawowa ba, kafin kace meye wannan tuni haske asubahi ya fara kawo kai.
A lokacin kuma da dama na mutanen cikin garin sun fara iso wa wajan, tayadda kafin rana ta ɗaga tuni sama da mutun dubu sun hallara a wajen.
Wajen gaba ɗaya ya canja, daga shiru tsit a yadda Armad ya ganshi zuwa mai kasuwa.
Mafiya yawa kuma abinda suke tattaunawa shi ne, ''wannan karan kuma bari muga wanne irin mutun-mutumi ne zai fito.
A lokacin dake rana ta ɗaga, idan ka lura zaka ga banda banbancin fuska da waɗannan mutun-mutumi ke da shi, yanayin kayan jikinsu ma da banbanci.
Misali; uku daga ciki kawai ƴar shara ce da ɗan bante a jikinsu, kuma babu makami ko ɗaya a hannunsu.
Biyu suna da alkyabba a jikinsu mai kyau duk da babu makami a hannunsu.
Na ƙarshe kuma yana da wani dogon mashi a hannunsa, amma babu alkyabba, kawai alamun doguwar riga ce a jikinsa.
A cikin garin Khan kuwa, a shashin kudu maso gabashin ƙasar, akwai wani ƙato gida mai tsayin gaske. A tsakiyar wani lambu mai yawan bishiyun giginya.
A can ƙololuwar saman gidan acikin wani babban ɗaki, zaune akan kujeru su Armad ne da Nusi da kuma waɗannan mutane guda biyu.
Tuni sun gama yi masa maganin ciwon da yaji a goshinsa, sannan kuma aka gabatar da ƴaƴan itatu da soyayyen nama gami da fura da nono a gabansa.
Nusi ta dubeshi gami da yin ajiyar zuciya, sannan tayi murmushi gami da cewa, ''ban taɓa tunanin irin abinda ya faru da Bihanzin zai faru yau ba, shi yasa ban yi maka bayanin waɗannan abubuwa ba.
''Amma ba komai, yanzu ka huta, ka ɗan samu bacci ko yaya ne, da safe zan shigo na labarta maka duk abinda ke faruwa.''
Tana faɗar haka Armad ya ɗaga kai da niyyar faɗa mata wani uzurin da zai nuna mata cewa shi a yanzu yake son yaji labarin. Kasancewar tuni zuciyar sa take masa sake-saƙen abubuwa da dama, a game da abubuwan da suke faruwa.
Amma ina, tuni Nusi ta juya cikin sauri ta kuma fara fita daga cikin ɗakin, kana ganinta kasan akwai abinda yake ranta, saboda haka bai matsa ba, ya bari kawai saida safe.
A wannan dare shi kansa Armad yayi mamaki, sabida irin baccin daya shaƙa yana da yawa, dan bai tashi ba saida rana ta kusa zuwa tsakiya a samaniya.
Yana farkawa abinda ya fara Arba dashi sune wasu kuyangi guda uku dukkansu wankan tarwaɗa, suna jera masa kayan abinci.
Yana tashi suka zube a ƙasa gami da cewa, ''barka da asuba, shugaba Armad, da fatan ka tashi lafiya.''
Cikin tsananin zafin nama Armad ya wartsake gami da kyaran murya da kuma ajiyar zuciya, ya ce, ''shugaba!!??
''Waye kuma shugaba?'' ya tambaya cikin mamaki.
Nan take suka ɗago kai cikin ladabi suna niyar amsa masa, amma a wannan lokacin ne waɗannan samari guda biyu da Armad ya gani suka nemi izinin shigowa ɗakin.
Bayan sun shigo sun gaisa, sun kuma nunnunawa Armad sauran sassan gidan da kuma duk abinda yake sai suma suka fice. Amma har suka tafi babu wanda ya bawa Armad amsar tambayarsa da yayi.
Saboda haka kawai sai ya ƙara shiga cikin shubuha akan wai taƙamaimai maike faruwa.
Bayan ya gama kimtsawa saiya fito ƴar harabar ɗakin da ya kwana aciki domin ya hangi gari.
yana tsaye iskar dake kaɗawa na dukan jikinsa, jan ƙyallen daya ɗaure kansa yana kaɗawa, nan take baisan mai yasa ba sai kawai yaji ya fara tunanin gida da mahaifiyarsa.
Nan fa ya nutsa acikin tunaninsa kan kace meye wannan tuni tsananin begen gida yasa rabin sa'a ta wuce ba tare da ya sani ba.
Yana cikin wannan hali ne yaji magana a bayansa, ''Armad, ka kwana ƙalau!''
Yana waiwayawa yayi arba da Nusi tana masa murnushi.
Ƙarasowarta keda wuya ta tafa hannu, waɗannan kuyangi guda biyu suka bayyana da kujeru guda biyu, wanda suka saka musu domin su zauna.
Bayan sun zauna, sai ta dube gami da yin murmushi kana tace, ''ya kaji iskar garin namu, da daɗi ko kuwa?''
Armad murmushi kawai yayi gami da godiya ta karamcin da take nuna masa.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka suna maganganu na yau da kullum, kafin daga bisani ta numfasa ta fara bayani, ''Kasan kowanne ɗan adam da yadda aka rubuta masa rayuwa.
''Misali, lokacin dana fara tunanin gayyatarka ka biyo ni wannan gari, abinda ke raina shi ne, na samar maka muhalli mai kyau da kuma duk wasu abubuwa da kake buƙata, sannan kuma na nemar maka babbar makarantar koyon Izza ta wannan gari.
''Amma kaga saboda abu ɗaya daya faru, wanda ban taɓa kawowa ba, hakan ba zata yiwu ba.''
Tana faɗar haka ta ɗan ɗaga kujerarta gami da saita ta ta fuskance shi, ta yadda take kalonsa ido cikin ido.
Kallo ɗaya zakai mata kasan cewa a wannan lokaci babu alamun wasa acikin zuciyarta, kuma duk abinda zata faɗa zata faɗe shi ne tamkar tana rantsuwa da abin imaninta.
''Armad kayi sani cewa wancan tsari dana gaya maka shi ne na farko acikin guda uku!
''Amma tunda yanzu bazai yiwuba abinda zaisa mu zaɓi tsari na gaba, duk ya ta'allaƙa da sakamakon daka fito mana dashi idan ka shiga Non-toch-teka.
''Kayi sani cewa a wannan gari, babu wani zancen ƙabila ko kuma ƙungiya, abinda kawai yake nuna matsayinka shi ne, acikin manyan matakan Izza, a ina kake.
Ta ja dogon nunfashi, sannan taci gaba da cewa, "a yau ina ganin ka cancanci na gaya maka sirrin mu, sirrin duk wani ɗan ƙabilar Djinn, wanda kuma shi ne manufar duk wani ɗan wannan ƙabilar!
"Kai sani cewa, mutanen da suka san abinda zan gaya maka a yanzu, basu da yawa a duk faɗin duniya. Saboda haka abinda zaka ji, ka tabbata lallai baza ka taɓa gayawa wani mahaluƙi ba a ban ƙasa.
"Asalinmu mu ƴan ƙabilar Djinn, mun fito ne daga ɗaya daga cikin garuruwan ƙarƙashin ƙasa, wanda ake cewa Shaníza.
"Mun kasance daga cikin mafiya girman ƙabilu a duk faɗin duniyar ƙasa bakwai, harma muna gogayya da ma'abota Ururu!
"Babu inda ba'asan sunanmu ba, kuma babu inda ƙarfin mulkin mu baije ba! Kwatsam watarana, sai waɗansu mutane suka bayyana a shashin Ikwatora, wato inda aka fi sani da 'Danja zon!'
"Du du du, adadinsu ɗari ne kacal, duk da wasu suna cewa ɗari da ɗaya ne, wasu kuma da biyu. Amma su kaɗai sai suka addabi dukkan wani mahaluƙi, a doron ƙasa cikin kwanaki bakwai kacal!
"Hatta ma'abota Ururu, babu yadda suka iya dasu, sai kawai komawa da baya da sukai, suka shata musu iyaka da doron ƙasa ta biyu da kuma ta farko. Amma haka suka rabu dasu.
"Kuma babban abin al'ajabin shi ne, babu wanda yasan komai akansu, illa abu ɗaya kacal, wato aniyarsu, wadda aka ce wai suna kan hanyar su ne ta Tafiyar Alwashi!
"Ba jimawa, sai jama'a suka fara ce musu, Matafiyan-Alwashi.
"To ana cikin wannan rikici kwatsam, sai aka nemi waɗannan mutane aka rasa, ko sama ko ƙasa. Har tsahon kwana uku, babu su babu labarinsu.
"Kwatsam a rana ta ukun, sai suka suka bayyana a ƙofar garinmu Shaníza.
"Kafin mu farga sun shige cikin garin, inda suka ƙullo ƙofar ta ciki. Tun daga wannan rana ta litinin, shekarar 683 Bayan Amri (A.A), babu wani mahaluƙi daya ƙara shiga ko kuma fita daga wannan gari, har yau ɗinnan da nake maka wannan zance."
Tai shiru, gami da duban Armad, kafin daga bisani taci gaba da cewa, "nasan mai kake tunani!
"Cewa duk tsahon shekarun nan, idan babu wanda ya ƙara shiga ko kuma fita daga cikin garin, to ta ina muka fito!
"Lallai kam wannan abin tambaya ne, domin kuwa kaɗai daga cikin iyayen mu da kakannin mu wanda suka fito daga cikin garin, kafin shigar waɗannan mutane, su su kaɗai ne suke yawo aban ƙasa yanzu.
"Kuma sune suka hayayyafa, har aka samemu. To amma da yake gaba ki ɗayan yawansu, baifi cikin cokali ba, har yanzu bamu fi a irga mu ba.
"Kuma dukkanin a inda muke, muna gane kanmu, sannan kuma ba muda wani buri, banda muga cewa watarana mun koma cikin garinmu, mun fitar da waɗannan mutane, kuma mun tseratarda miliyoyin mutanen mu dake ciki.
"Sai kuma wata tambayar da zaka iya ƙarayi, cewa idan dai har al'amarin waɗannan mutane ya baza duniya, to ya akai yanzu babu wanda ya sani, bayan dududu ba'afi shekara dubu ɗaya da ɗari biyar da wucewa ba.
"Lallai wannan tambaya ce mai kyau, kuma amsar ta faru ne shekaru biyu bayan shigar waɗannan mutane cikin garin mu;
"Kwatsam sai aka wayi gari Sarki Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu, ya haɗo runduna ta ma'abota Ururu, irin wadda ba'a taɓa gani ba, ya kuma bayyana a bakin wannan gari namu.
"Babu wanda yasan mai ya faru, illa cewa anyi sama da kwana ɗari ana kwabza yaƙi, amma daga ƙarshe, katangar garin nan bata faɗi ba, kuma shi ɗin, bai samu damar shiga garin ba. Haka ya juya ya koma izuwa ƙasarsa!
"Muma iyayenmu da kakannin mu, sunyu iya ƙokarinsu domin suga sun shiga cikin garin, amma ina. Duk da kuwa acikin su, akwai wazirin sarkin mu, wanda yasan duk wasu ɓarauniyoyin hanyoyi da ake shiga.
"Kai daga ƙarshe dai haka suka haƙura.
"To amma abin bai tsaya anan ba, kwatsam bayan ƴan watanni, ba sai aka ji, sanarwa daga Dul'Ururu ba, cewa duk wani ɗan asalun garin nan, ya zama mai laifi, sabida haka da an ganmu a kama mu.
"Sannan kuma acikin sanarwar, aka haramta ƙara ambatar sunan Tafiyar Alwashi, Matafiyan Alwashi, kai dama duk wani abu daya shafesu. Duk wanda ya karya dokar hukuncin kisa.
"A haka aka ringa kashe mutanen mu, har takai saida muka daina amfanu da sunan mu kwata-kwata. Kuma a haka dukkan wannan labari ya mutu. Labarin dani da ragowar mutanenmu , baza mu taɓa mantawa ba.
"Amma kai sani cewa bamu haƙura ba, kuma haka ta ƙarƙashin ƙasa mukai ta bin diddigin dalilin da yasa Ururu suka shiga al'amarin.
"Bayan sama da shekaru dubu muna bincike, muka gano cewa, Ururu sun sami tabbashi daga wata majiya da bamu sani ba, cewa waɗannan mutane suna da alaƙa da Tirifil-fakta, kuma wannan shi ne dalilin da yasa suka shiga faɗan. Harma kuma suke son a rufe zancen!
"Toh, Armad Wilbafos, wannan shi ne labari ne! Da fatan zaka riƙe shi har iya ƙarshen numfashin ka."
Armad yaja dogon numfashi, gami da yin ajiyar zuciya, yana kallonta cikin mamakin wannan labari nata.
Musamman duba ga cewa, a karon farko, ya sami wani abu mai alaƙa da abin da yake nema, wato Tirifil-fakta!
Tunda fari, bai san mai yasa ba, amma tunda dadewa idan ya kalleta abinda yake ji acikin ransa ba komai bane ba illa ƴan uwan taka, saboda haka daya ga irin kallon da take masa, sai kawai zuciyarsa ta cika da tunanin mai yasa take gaya masa duk wannan sirrikan, shim bata tunanin ya fallasata?
''Kuma wani abu da kake da buƙatar ka sani da wuri shi ne," taci gaba da bayani, kamar bata fuskanci kallon da yake mata ba, "wannan haske da kaga ya tashi sama kuma daga baya ya fara tattarewa a wajen ƙofar gari, idan ya gama haɗuwa kaf, shima sifar mutun zai bayar, wanda kuma ba kowa zai zamo ba face kai!!
''A halin yanzu duk da binciken da jama'a keyi zaiyi musu wuya su gano ka, amma daga lokacinda aka ce wancan mutun-mutumi ya gama bayyana, kallo ɗaya kacal ya isa kowa ya gane ka indai ya taɓa ganinka.
''Mafi tsayin lokaci da yazo a tarihi wanda wannan mutun-mutumi da ake cewa Al'yaya, ya ɗauka kafin ya gama haɗewa shi ne wata uku!
''Mafi ƙanƙanta kuma kwana tara!
Ta ɗanyi shiru kamar tana tunani, kafin daga bisani ta girgiza kai, sannan ta ci gaba da cewa, ''ya wajaba akan ka kayi azama ka maida hankali a Non-toch-teka da zaka shiga nan da ƴan kwanaki masu zuwa, domin idan son samu ne kafin mutun-mutuminka ya gama haɗuwa yadda mutane zasu iya ganeka ya zamanto ka fice daga cikin garin nan.
''Domin babbar matsalar ka a yanzu bawai masu farautarka a matsayin Magajin Wuobafos bace, babbar matsalarka ita ce mahaifin gimbiya ZAHRA Sisiyu(Nostalgiya) daka labarta min kun haɗu a baya, wato Sarki BIHANZIN wanda akafi sani da Shugaba Bihanzin mai DAUWAMAMMEN SARA!!!
"Babban sarki mai kula da harkar cinikin bayi a wannan doron ƙasa, mutun na farko daya fara mallakar Alyaya mai takobi a garin khan. A dukkan tarihin duniya ba'a taɓa samun wanda ya kaishi ƙarfin saran takobi ba. Kuma indai yace saiya halaka mutun tofa lallai ƙarshensa yazo.
"Saboda wani dalili da ba'a sani ba, duk wanda ya taɓa mallakar mutun-mutumin daka samu a ƙofar wannan gari, saida Bihanzin ya hallaka shi. Kayi sani cewa a halin yanzu, a dukkan doron ƙasa bakwai, babu wani mahaluƙi da baya tsoron kaifin taƙobin shugaba Bihanzin. Hasalima akwai dalili na musamman da yasa ake kiranta da suna DAUWAMAMMEN SARA.
"Kai sani cewa bani da ƙarfin da zan iya kareka daga takobin Bihanzin kuma lallai kaima baza ka iya tsayawa a gaban Dauwamammen sara ba. Domin kuwa ina so na labarta maka cewa da DAUWAMAMMEN SARA aka kashe Magajin wilbafos na uku."
Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad. Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta. Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...
Comments
Post a Comment