"TULADAN-NAN-GALAK!!"
A dai-dai lokacin da Armad yake ƙoƙarin kiran wannan sabon ɗalasimi da bamu taɓa gani ba a ɗaya ɓangaren Ikenga ne da mutanen sa suke tattaunawa.
"Yaya, ka barni nayi masa aiki." Inji kwamandan Ikenga mai suna B. Ururu. Idan mai karatu bai mantaba B. Ururu shi ne yaron da Ikenga yayi tattaki har zuwa doron ƙasa ta biyu, tsibirin Sido-Ururu, domin ya ɗauko shi. A yayin ɗauko shi bamu ga musayar wuta ba amma anga tsibirin yayi bindiga, wanda hakan ya baiwa su Ikenga damar tserewa da B. Ururu. Tambayar anan ita ce meye tsakanin Ikenga da B. Ururu? Ya akai suka san juna? Tayaya aka bari Ikenga ya shiga har gidan Ururu ya ribato ɗaya daga cikin ƴaƴan su maɗaukaka? Kada fa a manta kaɗai maɗaukaka daga cikin ƴaƴan gidan Ururu ake bawa horo akan wannan tsibiri.
An bayyana cewa B. Ururu lakabi ne: 'B' tana nufin Bayajidda (wato kamar ana cewa yana da jinin Bayajidda kenan), shi kuma lakabin 'Ururu' an bashi ne sabida bakaken idanuwan sa. A takaice har yanzu babu wanda yasan asalin sunan kwamanda B. Ururu.
Ikenga ya girgiza kai idanu cike da kokwanto, "anya kuwa, bana jin zaka iya. Jinin Ayubul-laisiy ne. Ka barni dashi."
B. Ururu ya haɗe fuska. "Kullum haka kake cewa. Idan baka sakar mana akala yanzu ba to yaushe zaka sakar mana? Nifa na gaji da jira. Tun sanda na shigo wannan tafiya ake ta shirin yaƙi amma har yanzu ko bera bamu kashe ba."
Dattijo Kána ya juyo a fusace ya dirarwa B. Ururu. "Wai kai mai yasa baka da tarbiyya ne? Ikengan kake gayawa wannan magana? To gaskiya bazai yiwu ba, idan kasan baza ka iya ba to..."
Ikenga ya ɗaga masa hannu ya dakatar dashi. Sannan ya juya ya nuna B. Ururu, "Jeka mu gani. Sai an gwada akan san na kwarai."
B. Ururu najin haka ya fashe da murmushin murna kai kace babban albishir akai masa. "Toh ƴan baƙin ciki sai ku mutu."
Yayi tsalle yayi kan Armad.
Sai da ya rage saura taku biyar tsakanin sa da Armad sannan yaja ya tsaya. Har yanzu Armad na tsaye bai motsa ba, idanun sa na kan Ikenga ko kaɗan bai damu da B. Ururu ba.
B. Ururu ya dubi Armad cikin girman kai ya ce, "Suna na Ginad Ururu. Ka riƙe sunan domin shi ne na ƙarshe da zaka ji." Ginad na gama magana ya tafa hannayen sa ya kira ɗalasimi irin na ƴaƴan Ururu sannan yayi fitar burtu ya isa ga Armad, amma maimakon ya fara kai masa hari sai ya fara kewaya shi kamar baƙar shurwa na zawarcin ƴan-tsaki. Armad na tsaye yana kallon Ikenga bai motsa ba.
"Ina da Saɓani, ina da Bayani, kuma ina da Haƙiƙa. Ƙari akan Shaibal-shísu. Kana tunanin akwai abinda zakai kaci galaba akaina? Ni ban san mai yasa ka shiga yaƙin ruhi bama. Dududu yaushe ka fito daga gida? 1851. A lokacin izzar ka 51 kacal. Tun a lokacin ina da izza dubu a ruhi na. Tun a lokacin na kware a sarrafa Shaibal-shísu. Tun a lokacin na kai kololuwa wajen sarrafa idanuwa na. Kaifa? Saida ka gama bilayi sannan bayan shekaru huɗu sun wuce a banza ka gano akwai wani abu da ake cewa Negrinki. Ka gano akwai sammai akwai deba. Abinda baka sani ba shi ne tun a lokacin yayana, sarkin izza, Ikenga, yake cikin deba ɗare-ɗare. Kaifa? Ƙassai ne kawai. Tun a shekarar micizi, kafin a haifeka, shugaba, yayan izza, Ikenga yake sharafinsa a matsayin ɗan sarki mara tsara. Wai kai wanne ganganci ne yasa kake tunanin zaka iya jada babbar izza? Wato akwai mutanen da dole sai an nuna musu kuskuren su sannan suke gane matsayin su, kaima naga irin wannan mutanen ne."
Yana rufe baki yayi taku bakwai inda nan take surar sa ta rabe gida bakwai. Kowacce ɗaya tana kama sak da Ginad, sannan kuma tana da ruhi irin na Ginad B. Ururu. Takubba na farin ƙarfe guda bakwai suka bayyana akan iska. Kowanne ɗaya daga cikin bakwan ya damƙi guda, sannan a tare suka afkawa Armad.
Armad yana tsaye a inda yake bai motsa ba. A haka yaci gaba da tsaiwa har zuwa sanda suka ƙarasa saitin sa, ratar su bata wuce ɗan taƙi ba. A lokacin Armad ya miƙa hannu zai cafi wuyan ɗaya daga ciki. Sauran kiris hannun Armad ya taɓa B. Ururu Amma B. Ururu ya motsa zai kaucewa hannun. Duk da cewa yaga ta inda hannun Armad ya taho ta hanyar amfani da fasahar Saɓani, to amma abin mamaki bai san yaya akai kafin ya kauce Armad ya damƙi wuyansa ba. Kawai gani yayi an damƙe shi. Abinda a iyakacin saninsa ba abu ne mai yiwuwa ba.
Armad ya ɗaga shi ya fyada shi da ƙasa, yayi bulala dashi barin hagu da dama. Ginad B. Ururu yana ta ƙoƙarin ƙwacewa amma bin yaci tura. Tun yana gani dishi-dishi har ya daina gani baki ɗaya. Armad yaci gaba da wujijjigashi yana luguiguita masa ƴaƴan cikin sa. Bayan ya tabbatar yaron ya suma ya ɗaga shi sama ya nunawa ALLAH sannan ya dunkule hannu ya daki fuskarsa, dai-dai kan bakaken idanuwan da yake ji dasu. A wannan lokaci fuskar Ginad ta lotse, idanun da hancin da bakin suka haɗe da juna suka shige cikin kansa kamar an fasa ƙwai. Ƙarfin dukan ya ɗauki B. Ururu yai cilli dashi sama. Bai tashi fadowa ko'ina ba sai a gaban Ikenga, kan ƙafar sa.
Nan take ragowar mutun-mutumi guda shida suka ɓace, kai kace dama can ka ƙarya ne.
Waje yayi tsit. Da yawan su suna ƙiyasta ƙarfin Armad, kuma a nasu ƙiyasin baifi waadin Deba ba, to amma a lokacin suka fahimci cewa ƙiyasin da suke yi ba haka yake ba.
Abin mamaki Ikenga ko a jikin sa, waiwayawa yayi wajen ragowar mutun huɗun dake bayan sa yana murmushi ya ce, "akwai wanda yake son ya ƙara gwadawa?"
Sukai shiru.
"Akwai wanda yake son ya gwada?"
Sukai shiru.
Ikenga yai ajiyar zuciya sannan ya juyo ya fuskanci Armad.
"Armad Wilbafos, ta wacce hanya kake so ka mutu? Fille kai? Fasa ruhi? Ƙonewa? Fasa tunani?"
Armad yayi murmushi ya ɗan ja gashin kansa yana kallon sama kafin ya juyo kan Ikenga. "Ikenga, wai kana tunanin ka riga kaci nasara sabida ka tare min hanya ni kaɗai ku biyar?"
Ikenga yayi murmushi ya ce, "kada kayi tunanin zan tsaya bata lokaci akan ka da fasahar juya lokaci, ko kuma fasahar hadari ta aljani Gal-Iyyu, ko kuma fasahar Shaibal-shísu, kamar yadda mukai a gasar jinzidal a baya. Wancan lokaci ya wuce, wancan zamani ya wuce, a wannan zamani wani sabon zance ake yi. Hari ɗaya nake yi! Duk wanda yayi ido biyu da wannan hari to kamar ya tsallaka lahira ne. Bawai kokwanto ake yi ko kuma tunani ba, a'a dole ne ka tsallaka lahira indai ka haɗu da hari na. Bazan so ka mutu a banza ba. Kayi mun mubaya'a kamar yadda na dade ina nema. Wannan ita ce hanya guda ɗaya tak da zaka ceci rayuwar ka data ragowar iyalan ka."
Armad ya buɗe baki zai mayar masa da martani amma Ikenga yayi sauri ya tare shi da cewa, "Ayubu yayi min mubaya'a, sauran kiris Nusi da Nostaljiya suma su hau kan layi. Ragowar mutanen ka duk dawowa zasu yi. Idan a yanzu kayi mubaya'a zan mayar dakai gida na danƙa maka Ayubu ka ɗauki fansar abinda yayi maka. Sannan dani dakai mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu gama da Bihanzin. Kayi tunani, baza ka ƙara samun irin wannan damar ba a rayuwar ka. Ka tuno a wancan lokaci yadda kaƙi amincewa kuma ta dalilin haka Hidaya ta mutu. Kada ka ƙara maimaita irin wancan kuskuren. Ka durkusa ƙasa kayi mubaya'a."
Maimakon Armad ya bashi amsa kawai sai ya nuna Ginad B. Ururu wanda ke gwance rai a hannun ALLAH ya ce, "babbar matsalar ka baka girmama wanda sukai maka mubaya'a. Kaga wannan yaro 'yaya' yake ce maka sabida girmamawa, amma yaji ciwo baka damu ba ko a jikin ka. Soma kake wanda yaji masa ciwon ma ya dawo ɓangaren ka. Shima Ayubu kace yayi maka mubaya'a amma ƙoƙarin siyar dashi kake tun ba'a je ko'ina ba. Wataƙila da za'a wayi gari nayi maka mubaya'a nima siyar dani zakai kamar sauran, haka ne?"
Ikenga yayi murmushi amma baice komai ba.
Armad ya kada kafada. "To kaga kuwa babu wani mai ragowar hankali dazai yi maka mubaya'a."
Ikenga ya sosa goshin sa da ɗan yatsa tare da yin ajiyar zuciya, ya ce, "Wannan ba Irin wancan lokacin bane, duk wanda baya tare dani to maƙiyi na ne. Shi kuwa maƙiya kashe shi akeyi. Bana barin maƙiyana su rayu domin barin maƙiyi shi yake sa su dawo su caka maka wuƙa ta baya. Kayi haƙuri amma kazo ƙarshen tafiyar ka. Sai dai idan kaje can ka bawa su Hidaya labari. Dama akwai ajiya da Iluru ya bari acikin duniyar Negrinki."
Kafin Armad yayi wani abu Ikenga ya tafa hannun sa. Nan take jikin Armad yai bindiga kamar wanda aka daurawa bom aka tasa.
"Daji."
Ana haka jikin Armad ya koma walkiya sannan ya dawo ya haɗe guri guda kamar ba abinda ya faru.
"Busasshiyar ƙasa."
Nan take jikin ya ƙara yin bindiga ya tarwatse.
Jikin Armad ya ƙara hadewa.
"Babbar katanga."
Kafin ya nutsu ya ƙara yin bindiga. Kai kace wanda aka daurawa makami mai linzami wanda bashi da iko aka akai.
"Ruwa."
A karo na huɗu jikin Armad yayi bindiga ya tarwatse. Minti guda aka ɗiba kafin walkiyar data tarwatse a ƙasa ta fara tattaruwa guri guda. Da ɗaya da ɗaya dunkule-dunkulen walkiyar ya fara haduwa a hankali, saɓanin da da Armad yake hadewa da wuri. Kafafu ne suka fara haɗewa, sannan a hankali cinya ta haɗu, sannan ƙugu da ciki da wuya. Kan Armad shi ne Abu na ƙarshe daya haɗu. Jikin Armad ya dawo dai-dai amma kana ganin sa kasan yasha wuya, nishi kawai yake yana haki.
"Wannan sakayya ce akan abinda kayiwa kanina Ginad. Yanzu kuma zaka fuskanci hukuncin daya dace dakai." Inji Ikenga.
Armad ya tofar da yawun dake bakinsa wanda idan ka lura zaka ga acike yake da ɗiso-ɗison jini. Amma kuma a lokaci guda fuskar Armad murmushi ne akai.
"Daji, Busasshiyar ƙasa, babbar katanga, ruwa... Kayi ƙoƙari daka ɓoye duk wannan abubuwan acikin duniyar Negrinki ba tare da na kula ba. Amma duk da haka ina ganin baka gama sakawa kaninka yadda ya kamata ba, duba ga cewa har yanzu a sume yake, ni kuma ina numfashi. Ga Iluru kuma can a ƙasa, waya sani ne ko yana numfashi ko ya tsallaka lahira. Shima kana bukatar ka rama masa. Yaya za'ai kenan?"
Ikenga yayi wani murmushin mugunta da hakori guda sannan ya murtuke fuska ya mika hannunsa kan takobin sa. "Kana da wasiyya?"
"Wasiyya? Hahaha..." Armad ya fashe da dariya, "ina da ita. Idan kaje lahira ka gaida Amraikugyu."
Ikenga najin wannan ya yamutse fuska.
Armad ya kada kai ya ce, "daina yamutse fuska. Wai kai da ALLAH kana nufi babu wanda ya sani? Ka daina yaudarar kanka. Ba kaine Amraikugyu ba, kuma ba kaine Baya Azaba na asali ba. Yaro ne kai ɗan shekara ashirin da ɗaya zuwa da biyar. Abinda kawai kake takama dashi shi ne ruhin magabatan ka irin su Amraikugyu da Baya Azaba kana yiwa mutane basaja wai kaine Amraikugyu. Kai dan ALLAH ko kunya baka ji?"
A karo na farko fuskar Ikenga tayi baƙi. Duk wani annuri ya kau daga kai.
Armad ya haɗe gira, ko a jikin sa yaci gaba da bayani, "ah, to ai ina taso na gaya maka naga wani ruhi a tare dakai lokacin gasar jinzidal a can shekarun baya. Kuma nasan ka gaji ruhin Amraikugyu, ka kuma gaji ruhin Baya Azaba. Kaga uku kenan. A ka'idar fasahar Shaibal-shísu ruhi shida kake da ikon haɗawa. To ka samu uku saura uku. Tunda a gasar jinzidal da izza 100 kazo kuma bayan kammala gasar na ganka a kurkukun bango izzar ka ta ƙaru matuƙa kaga kenan dole acikin ragowar ruhin nan guda uku akwai mai sarrafa izza. Wannan shi ne ya ƙara tunomin cewa babanka Shísu shi ne ya kashe magajin Wilbafos data rayu kafin ni, kuma tarihi ya nuna kai aka bawa jinin ta ka sha. A takaice dai ruhin magajin Wilbafos daka sata ta hanyar shan jini shi ne ruhin ka na huɗu. Saura biyu. Akwai ruhin dake jikin ka tun kana yaro wanda yake sabunta tsokar jikinka yana hanaka mutuwa. Shi ne ruhin dakai amfani dashi sanda Deniz Curu-curu ya tsince ka a filin yaƙi a cake da takubba. Saura ruhi ɗaya kacal wanda bamu san a ina ka samo shi ba. Sanin wannan ruhi zai taimaka min wajen tsallakar dakai lahira. Ko zaka gayamin wanne ne?"
Ikenga ya ciji harshen gami da yamutse fuska. A ka'ida kawai afkawa Armad zaiyi yaga bayansa sabida maganganun Armad sun ɓata masa rai, to amma abinka da tsohon hannu. Kwantar da hankalinsa yayi ya nutsu. Sannan ya dubi Armad ya ce, "wato, Armad Wilbafos, da kayi zancen ruhi sai ka tuno min da wani ruhi dakai amfani dashi a yakin sarakunan jinzidal ka kashe Uznu. Idan zan iya tunawa wani digon jini ne ya fito daga goshin ka, wanda kayi amfani dashi ka dakko ruhin. Haka ne?"
Armad yayi murmushi. "Kana wajen kenan?"
Ci gaba da bayani Ikenga yayi kamar baiji shi ba, "kasan banbancin ruhin ku na gidan Wilbafos da namu na gidan Bayajidda? Bari na gaya maka. Akwai bambanci guda uku: na farko, ku naku kawai aiki kuke sawa yayi muku da ƙarfin sa, mu kuma namu ƙarfin sa yake bamu muyi abinda muke so dashi; na biyu, naku bana musamman bane, kowanne ɗan gidan Wilbafos da yakai kololuwar kwarewa da miyurar sa yana iya sarrafa shi, mu kuwa mutun ɗaya ne tak a kowanne zamani yake da wannan dama; na uku ma'abota fasahar Shaibal-shísu ruhi bakwai suke dashi ba guda ɗaya ba kamar ku. Duk ruhin da muka kusanta yana shiga jikin mu ya zama mu, mu zama shi. Muyi amfani da fasahar sa kamar tamu. Kaga idan mutane suka ce ni ne Amraikugyu ba suyi ƙarya ba. Domin kuwa ni na gaji ruhin sa da fasahan sa.
"Sannan kuma bari na baka wani ɗan labari daya faru kafin a haifeka a lokacin yaƙin littafin takobi. Akwai wani makaho wanda yake haye kan doki samfurin kili. Wannan makaho babu abinda yake ƙoƙari sai ya cika umarnin babban sarki Eyriyon ya tseratar da littafin takobi daga hannun Ururu. Asalinsa ba makaho bane, makancewar ta samo asali ne daga sanda ya samar da wata fasaha wadda hatta shugaban sa Eyriyon bai santa ba. Ta hanyar wannan fasaha yana iya auran takobi ya maye gurbin idanunsa guda da ita. Sannan kuma yana iya auren aljana ya maye gurbin idanunsa guda da ida. Ance a lokacin yaƙin littafin takobi su uku aka gani: ɗaya daga ciki yana da idanu samfurin takobi, ɗaya kuma yana da idanun mage. Abinda mutane basu sani ba shi duk su ukun mutun ɗaya ne. Mai idanun takobin matar makahon ce ta biyu wadda ta maye gurbin idon sa hagu. Mai idanun magen kuwa aljanin daya aura ne wanda ya maye gurbin idon sa na dama. Tun daga kan wannan kwamanda babu wata sabuwar fasaha da ƴaƴan Wilbafos suka ƙara samarwa. Kullum kawai maimaita abinda yayi kuke. Kamar Taidara da Tawagar Matattun sa, Zaikid da Wilbafosiyan Siwod Dans, da Fatima da Shata, babu wanda acikin su ya samarda sabuwar fasaha. Kullum kawai kwaikwayon abinda makahon nan yayi kuke. Kamar kaima ɗin nan. Abin haushi ka shiga kurkukun lokaci ka samu duk wata dama da zaka samarda sabon tsarin fasaha, amma sai ka zaɓi kabi layin da iyayenka suka bi ka zama makaho."
Armad ya kada kafada. Ko kaɗan surutun Ikenga bai dame shi ba duk kuwa da gaskiya yake faɗa. "Hmmm. Shi yasa naga Shaibal-shísu sabuwar fasaha ce da Ikenga ya kirkiro."
Ikenga yayi shiru yana kallon Armad kafin ya juya baya izuwa Kána. "Kana, kasan mai ake cewa ɗan shagwaba?"
A daidai wannan lokaci Kána sakace yake yi da ɗan'tsinke a haƙoransa. Ya tsaya da abinda yake yi ya ɗanyi tunani kafin daga bisani ya girgiza kai. "Kai, gaskiya ban sani ba."
Ikenga ya dubi ragowar tawagar, "ku fa?"
Suka girgiza kai alamun basu sani ba.
"To bari kuji. Ɗan shagwaba shi ne wanda iyayensa da yayarsa suka ga yana da fasahar Negrinki irin ta babban sarki Kuyurussa'ayi. Tun daga nan sai suka ka ƙwallafa ransu akansa suna ganin shi ne wanda zai ceto su ya mayar dasu doron ƙasa ta farko. Suka fara yi masa tanadi suna yi masa shiri tun yana ciki. Duk dan ya taso ya zama ma'aboci izza. Ɗan'shagwaba bai san wahala ba: komai bashi akai a baki. Wai fa duk dan ya zama shahararren mai izza amma abin yaci tura, har yanzu babu labari. Yayar sa saboda shi ta mutu duk dan ya girma ya kirkiri tasa fasahar amma abin yaci tura."
Armad yayi murmushi ya ce, "koma mai akai ai baikai bawa jariri jinin matacce ba. Ace sabida yunwar izza uba yayi kisa ya shayar da ɗan sa jinin. Abin ya zama abin kaico." Ya girgiza kai, "ALLAH ya kyauta."
Ga dukkan alamu sun gaji da mayarwa da juna martani domin kuwa shiru sukai suna kallon juna. Watakila zuwa wannan lokaci Ikenga ya fahimci cewa duk abinda zai ce Armad yana da martani sabida haka yayi shiru. Bayan ɗan lokaci ana kallon-kallo sai suka jada baya suka gyara tsayuwa.
Armad ya cizi yatsan sa jini ya fito sannan ya shafa jinin akan goshin sa. Take goshin ya dare gida biyu, a dai-dai saitin miyurar sa ƙatoton dunƙulen jini ne ya fito. Yana bayyana mutun-mutumin dake tsakiyar miyurar ya ɓace. Jinin ya juye izuwa siffar mutun-mutumin. Da farko mutun-mutumin na haske ne, kafin daga bisani ya koma rairayi, sannan daga ƙarshe ya juye ya zama dutse. Tsayin sa zira'i matan, faɗi zira'i goma. Ga sulken baƙin dutse, ga hular dutse, ga baƙin al'amudi na dutse. Idan ba'a mantaba wannan mutun-mutumi shi ne ya aika Uznu lahira a yaƙin sarakunan jinzidal. Yana bayyana idon Armad da yake buɗe shima ya rufe. Wato dai Armad ya koma makaho baki ɗaya.
Idon Saif-Al-Barzak ya fara haske, nan take Saif-Al-Barzak ta bayyana a gefen sa a irin siffar da aka saba ganin ta - ƴar budurwa mai siffar takobi.
Idanu a rufe Armad ya daki iskar dake gabansa. Abin mamakin kawai sai iskar ta fara juyewa izuwa zaren izza. Ana haka kawai sai ga ankokin Ururu sun fara zuba daga sama. Tuni an wuce iyakar da aka yadda al'ummar ƙasa suyi amfani da ita.
A ɗaya ɓangaren shima Ikenga a shirye yake. Domin kuwa ba'a san yaushe ba amma mutane biyar ne suka bayyana a bayansa. Ɗaya daga cikin su shi ne dattijon da Armad ya gani a gasar jinzidal wanda yazo ya bawa Ikenga izza. Ɗaya kuma shi ne Amraikugyun da aka gani da Hidaya a can baya. Ɗaya kuma mace ce budurwa wadda bata wuce shekaru ashirin ba. Akwai tambarin miyura na gida Wilbafos a goshin ta. Idan Armad zai canka to wannan ita ce magajin Wilbafos da aka kashe aka shayar da Ikenga jinin. Akwai wani dattijon wanda zai wuce shekaru hamsin amma bai kai Bayajidda tsufa ba. Akwai kuma wani abu mai siffar mutun amma kuma jikin sa na wuta ne. Acikin biyun ƙarshen za'a samu Baya Azaba, ɗayan kuma ya zama ruhin da yake sabunta jikin Ikenga yana hanashi tsufa. Kaga biyar kenan; har yanzu akwai ruhi guda da Ikenga bai bayyana ba.
Armad da Ikenga suka jada baya suka afkawa juna. Kafin su isa duniyar da suke ciki ta rabe gida biyu. Ɓangaren Armad ya rine izuwa ja jajawur launin Negrinki. Negrinkin sa ta bayyana ta cika ko'ina tana ambaliya tana zabalbala kamar wutar Farkon Lokaci. A ɓangaren Ikenga hadari ne ya taso mai ɗauke da ƙanƙara amma fa bata sanyin babban sihiri, wannan ƙanƙara ta azaba ce domin kuwa wuta ce take ci acikinta.
Idan ka hangi wannan jarumai biyu daga nesa zaka ga kowa acikin su ya mallaki nasa ɓangaren duniyar. Suna gab da haɗuwa da juna. Haɗuwar da idan ba'ai wasa ba zata tarwatsa komai a faɗin ƙassai da ƙasashen ƙasa.
Kafin su haɗu Armad ya ƙara kiran dalasimin sa:
"TULADAN-NAN-GALAK!!"
Nan take tambarin miyurar Armad ƙatoto guda ɗaya ya bayyana kan iska yayi kan Ikenga.
Sauran kiris hatimin ya hadiye Ikenga amma a lokacin aka ji babbar wakar izza ta fara tashi daga bayan Ikenga. Kida da sauti amma fa samfurin aljanu irin wanda baki bashi iya bayani kuma kalmomi basu iya bayyanawa. Lokaci yayi da Armad da Ikenga zasu fuskanci juna a ware raini. Watakila kuma a yau ne zamu ga waye ya kamata yayiwa wani mubaya'a.
Comments
Post a Comment