A dai-dai wannan lokaci sun iso gaɓar gadar zare. Ɗan ƙaramin kwale-kwale ne amma kuma duk iyakacin hankoron da ruwan yake ya kasa kifar dashi. Namun ruwa da aljanun dabbobi duk sun kasa matsowa inda suke. Anyi ittafaki hatta manyan jirage wanda akai musu aiki na musamman basa iya zuwa kusa da doron ƙasa na biyu. Dalili shi ne yawan ambaliya da ruwan yake yi wanda yake kifar da jirage.
Akwai wata katanga wadda ta taso daga bangon duniya tazo ta ratsa ta cikin bango ta dangane da sashin ikwatora. Idan ruwan ya daki katangar sai kaga yayi ambaliya ya dawo yana hankoro. Duk wani abu dake gabansa sai ya kifar dashi; wala mutun, wala jirgi. Wannan yasa namun ruwa manya masu ƙarfin izza suke taruwa a gindin katangar. Indai dabba ta isa sai kaga tana da guri a ƙasan katangar. Sun zama kamar masu gadin wannan katanga.
Suna matsawa kusa manyan halittu suna tasowa saman ruwan a wani yanayi mai kama da barazana. Har yanzu babu wata dabba da tayi ƙoƙarin haike musu sai dai gurnani daga nesa.
Akwai dordor, aljanun kifaye launi daban-daban. Girman kowane kifi yakai na ɗan adam, amma basu da hannaye ko ƙafafu, sai dai jela da kaifafan ƙayoyi. Akwai wani jinsi na daban wanda girmansu ya ɗara na sauran. Farare ne masu fata irin ta dordor. Akwai gashi a saman kansu kamar mutane. Amma banda wannan babu wani abu da zaka gani a jikinsu wanda yayi kama dana ɗan adam. Kakkaurar tsoka ce mara kyan gani a jikinsu wadda tun daga nesa zaka ganta ta dunkule a gurare da dama na jikinsu. Ga wasu ƙasusuwa masu kaifi a kafada. Kallo ɗaya Armad yayi musu ya ɗauke kai.
"Ƴan-ruwa kenan," inji Zaikid. "Kamar sarakai ne a nan. Idan ka lura zaka ga sun koma gefe suna kallo. Baza su saka hannu ba indai ba wani muhimmin abu kayi ba. Ko kuma su ga kana ta kashe ragowar namun ruwan."
Armad ya haɗe gira cikin mamaki. "Wai kana nufin idan na kashe wannan kifayen sai su shigar musu?"
"Eh mana." Zaikid ya gyaɗa kai. "Zaiyi wuya ka gansu idan ba irin wannan gurare kazo ba. Ƴan-ruwa suna ganin duk wata dabbar ruwa a ƙasansu take. Suna jin mulki kamar na sarakunan mutane duk kuwa da basa magana. Kowanne ɗaya acikinsu yana iya kai wa shekaru ɗari biyar zuwa dubu ɗaya. Izza kuwa duk sun haura dubu biyar. Kaga waccan fatar dake jikinsu? Kada ka raina ta, abubuwa kaɗan ne suke iya yanka ta. Waɗancan kasusuwan kuwa dafi ne dasu na musamman. Idan son samu ne kada ka taɓa bari faɗa ya haɗa ku dasu saboda suna da riƙo. Koda sun mutu suna barwa ƴaƴansu wasiyya akan kiyayya."
Armad ya zare ido yana mamakin wannan halittu kamar mutane.
"Waɗannan ƙanana ne fa," inji Zaikid.
Armad ya ƙara yamutse fuska. Girman kowanne ya kai a haɗasu su ukun tare da jirgin da suke ciki amma a haka ƙanana ne?
"Yanzu dai bamu da lokacin tsayawa faɗa da waɗannan abubuwa. Mu kauce musu kawai. Ga katangar can ina hango ta. Idan zamu iya kewayewa yafi mana sauki."
A take suka amince. Suka kada akalar jirgin suka zagaye dabbobin ta baya yadda baza su sha gabansu ba. Inda suka ci sa'a dabbobin basu biyo su ba. A haka suka ci gaba da tafiya tsahon rabin sa'a. Sai da suka kusa ƙarasawa sukai kicibis da wani gungun dabbobin kamar wancan. A yanzu basu da damar kewayewa tunda a jikin katangar suke kuma dabbobin sunyi musu ƙawanya. In kuwa suna so su matsa to sai dai su shiga bango. Wani abin haushi shi ne wannan gungun sunfi wancan harzuka. Tun daga nesa suke kuka alamun kada a matso su. Wasu kifaye koraye sun fara matsowa kusa dasu.
Hannun Armad ya fara narkewa zuwa walkiya. Sauran kiris hannun aradu ya sauka Zaikid yayi sauri ya riƙe shi.
"Bari, indai ba so kake ku fara kiyayya dasu ba. Kaga wannan abubuwan idan suka fara kiyayya dakai sai hawa bango ya gagare ka. Duk wata dabba dake rayuwa a ruwa sai ta zama abokiyar faɗanka. Kana ƙoƙarin faɗa da Ururu wasu abokan gabar sun ƙaru."
Armad yaja numfashi a hankali ya kashe walkiyar.
"Yanzu meye abinyi to? Bamu da sauran wajen guduwa."
"Waye yace?"
Zaikid ya daki ruwan da hannunsa. Take wajen ya dare biyu suka shige ciki sannan ya rufe.
"Kurkukun bango zaka kai mu?" Inji Armad.
"Gwanda mu bi tanan," inji Shata. Idanunsa cike da magagi. Watakila kukan dabbobin ne ya tashe shi ko kuma ƙarar ruwan. "Akwai haɗari amma yafi muyi faɗa da wannan abubuwan."
Armad yaja gwauron numfashi. Irin sanyin da yaji a lokacin da suka zo da Babara ya fara ratsa jikinsa. A wannan lokaci abin bai dame shi kamar a baya ba. Ji yake kamar ana yi masa susa saɓanin wancan lokacin daya fara karkarwa. Ƙawanyar ruwa da haske ta kewaye su tayadda ruwan bazai haɗiyesu ba. Suna tafiya suna jin sautin ruwan daga nesa. Wani lokacin sautin ya juye zuwa gunki wanda yake nuna akwai dabba a kusa. Har suka ƙarasa gaɓa babu wani abu daya kawo musu farmaki.
Maimakon su faɗa ƙasa kamar yadda ya faru da Armad da Babara a baya, sai Zaikid ya kira wasu ɗalasimai jirgin ya juya ya hau saman ruwan yaci gaba da tafiya sukai sama.
"Tanan babu wata dabba da zamu tarar," inji Zaikid. "Suma suna tsoron shigowa kurkukun bango."
"Hakane," inji Armad. "Amma kasan akwai mutane acikin kurkukun nan sama da shekaru dubu. Da dama daga cikinsu sun ƙera jirgi sunyi ƙoƙarin hawa sama domin su fita daga cikin kurkukun nan, amma hakan bashi da amfani tunda idan sun je saman akwai katanga a gabansu. Naji wasu suna cewa katangar nan ta ciki tafi ta waje tauri."
"Nima naji wannan zancen," Inji Zaikid. "Gashi dai katangar guda ɗaya ce amma wasu suna ganin katangar nan ta ciki tafi ta waje kwari. Sai dai duk hira ce kawai. Katanga ɗaya ce da nan da waje babu wani bambanci. Kawai dai fursunonin sun kasa fita saboda haka suke tunanin tasu katangar tafi ta waje tauri. Amma idan ka lura zaka ga abin ba haka yake ba. Suma mutanen dake wajen babu wanda ya taɓa ratsa katangar duk kuwa da sunyi ƙoƙarin hakan. Kuma sunfi mutanen dake cikin nan ƙarfi da yawa. Kaga kenan indai za'ayi amfani da wannan sai ace ta waje tafi tauri. Amma duk iri ɗaya ne. Maganar ita ce: yaya zamu fasa mu shiga ciki?"
Nan take Nusi ta faɗowa Armad. Idan haka hawa doron ƙasa ta biyu yake da wahala to tayaya take ƙoƙarin hawa? Wata guda daya wuce Ururu sun buɗe kofofin doron ƙasar saboda jinzidal. A dalilin haka Nusi ta samu dama ta shiga. Amma yanzu dukkan kofofin a rufe suke babu wata hanya da zasu wuce. Shi kansa Armad da Zaikid fama suke yi suna neman hanya. To Nusi yaya zata yi kenan? Sai dai a kullum Armad yana jinjinawa kwamandunsa. Wajen da babu hanya sai kaga sun samo hanya.
"Kada ka damu ita tana tare da Maikiro'Abbas," inji Zaikid kamar yasan mai Armad yake tunani.
"Amma tayaya kasan suna tare da Abbas?" Inji Armad.
Zaikid yayi ɗan murmushi. "Bani da tabbas, amma nasan aboki na. Baya son tashin hankali ko kuma wani abu dazai jawo tashin-zaune-tsaye, amma kuma ba'a taɓa shi yayi shiru. Da ace Ururu basu buga a jarida zasu kashe Fatima ba to ba lalle ya taso da kansa ba, amma tunda suka sanar a jaridu to kuwa zaiyi wahala ya kyale. Sun san Fatima a wajensa ta taso da kuma alaƙar dake tsakaninsu. Tunda sukai haka dama suna ƙoƙarin takalarsa faɗa ne."
"Kana ganin shi kadai zai iya jada Ururu?" Inji Armad. Yayi sauri ya ɗaga kafaɗa ganin Zaikid ya haɗe gira. "Nasan abokin kane kuma nasan ya daɗe. Amma Dul'Ururu ma ya daɗe kuma yana daga cikin Ashura. Sannan kuma bashi kaɗai bane: akwai Haruta da Maruta, akwai ragowar mayaƙan Ururu da sauran kwamandunsu. Watakila har sarakunan jinzidal zasu kirawo domin suyi mana taron dangi. Kana ganin Abbas yana da ƙarfin dazai iya tare su?"
Hmmm... Zaikid yaja dogon numfashi.
"Banda wanda ka lissafa akwai Ibraham Nil. Shi ne shugaban fannin kimiya da bincike na babbar jami'ar Ururu dake doron ƙasa ta farko. Na ganshi lokacin jinzidal kuma ina kyautata zaton zai taka rawa a wannan yaƙin. Aikinsa shi ne kwafar fasahar kabilu yana bawa Ururu. Har Umuk-li ya mutu yana jin haushin fasaharsa da Ibraham Nil ya kwafa ya bawa Ururu."
"Nima ya kwafi tawa," Inji Armad. "Ban san yadda akai ba amma naga wasu mutun-mutumi na wata yarinya Suwainah dana gamu da ita a tsibirin Sido-Ururu suna amfani da miyura ta."
Zaikid ya fashe da dariya. "Haha... Tabbas aikinsa ne babu ko kokwanto. Kasan wani irin mutum ne. Ba ɗan ƙabilar Ururu bane. Taidara ya taɓa gayamin asalinsa hadimi ne a gidan Wilbafos. Ya fito ne daga wata ƙaramar ƙabila mai suna Nil. Ƙwaƙwalwarsa ita ce ta ɗaga shi. Tun Ururu suna raina shi suna ganin bazai iya ba har takai babu wanda baya girmama shi hatta Ashura. A cewar Taidara Ibraham ya taɓa taimakon Hidaya a wani abu daya shafi miyurarta. Na tambayi Hidaya amma bata gayamin hakikanin mai ya faru ba. Koma dai meye Ibraham Nil yana da hatsari. Yana da sa-hannu a yawancin karfin rundunar Ururu dake sama. Kaga zuwansa wannan yaƙi zai taimaka musu yadda baka tsammani.
"Akwai Yurba Ururu wanda ya maye gurbin Uznu Ururu daka kashe. Ragowar kwamandu ukun dake rundunar Ururu sune salsan Dul'Ururu. Ga Suwainan daka ambata yanzu. A sarakunan jinzidal Han'ibal kaɗai nake ganin zai amsa goron gayyata koda sun tura. Domin naji denizawa sun kafa sabuwar daula a doron ƙasa na huɗu har sun mamaye daular Sisiya da wasu ɓangarori daga daular rafiyawa wadda daman basu da tsayayyen shugaba. Ban san yadda akai suka samu damar karya asirin da Ururu sukai musu ba har suka fito daga ƙarƙashin ƙasa. Kasan idan ba'ai da gaske ba sai sun ƙara kafa wata daular irin ta Deniz Huhutu?"
Armad ya runtse ido. Kusan laifinsa ne duk da shima bai san yadda abin ya ƙare ba. Tun daga sanda ya bar mutanensa a fada yabi Iluru bai san mai ya faru ba. Ya kwashe duk abinda ya sani gayawa Zaikid.
Take fuskar Zaikid ta canja zuwa yanayin jimami.
"Shi yasa banso a baka waƙar maƙabarta. Kowacce fasaha daka gani tana da amfani kuma tana da sharri. Iyakacin ƙarfin fasaha iyakacin sharrin da zata iya haifarwa. Babu yadda za'ai ka haɗa mutun-mutumi mai tunani wanda kuma bashi da kayyadadden lokacin mutuwa kuma kace matsala baza ta faru ba. Kana tunanin Aldaima bai san yadda zai ƙarawa mutun-mutuminsa tunani da shekaru ba? Amma ya bar su a haka. Saboda sanin sharrin da zai faru shi yasa. Kaga duk sanda ka samarda mutun-mutumi to kamar ka samar da wata halitta ne. Yana ƙara daɗewa yana ƙara wayo. Dole akai lokacinda bazai bi umarni ba. Kai dole akai lokacin da zai ji shima fa mutun ne kamar ka. Watakila ma ya fara tunanin kai ne na ƙaryar. A hankali sai kaga ya fara lissafin kashe ka. Watakila gwanda tun yanzu da Ayubu ya bayyana maka halinsa ka gani ba sai gaba ba.
"Dole ka kashe Ayubu idan ba haka ba sai ya zama mafi girman abokin gaba da kake dashi. Duk wata fasahar ka zai iya koya. Yana da tunani irin naka. Yana da izza irin taka. Banbancin ku dashi bashi da yawa. Daga yau kwata-kwata ka daina amfani da duk wata fasaha daga cikin waƙar maƙabarta sai kayi bincike akan yadda take da asalinta da kuma sharrinta. Kuma idan son samu kawai ka dogara da taka fasahar domin baza ka taɓa sanin sharrin wata fasahar ba dole sai kayi amfani da ita."
Daga nan Zaikid yaci gaba da faɗa akan Ayubu. Wai dan me Armad zai saka masa sunan kakansa Ayubul-laisiy Al-wilbasi? Hakan bai dace ba, dole a canja masa suna nan take. Bayan kai-komo aka canjawa Ayubu suna zuwa Hamanu.
Daga nan suka koma zance kan littafin takobi. Takobi ce kuma littafi. Littafin shi ne waƙar maƙabarta. Takobin ita ce Saif-Al-Barzak.
"Kasan Saif-Al-Barzak wata irin takobi ce," inji Zaikid. "Bata da iyaka wajen abinda zata iya yi, amma kuma zata iya dakushewa a hannun ƙaramin mai izza."
Zaikid ya fara dogon bayani akan Saif-Al-Barzak. Armad yasan takobin da wani sinadari na musamman take amfani; shi ba izza ba, kuma shi ba Negrinki ba. Wato kamar yadda aljani zai samar maka da walkiya ka ɗiba kayi amfani da ita haka alaƙar take a tsakanin mutun da takobin daya aura. Akwai wani shinge acikin tsarin ruhi wanda zaka tara wannan sinadari, ita kuma takobin ta ɗiba tayi amfani dashi. Shi wannan sinadari kamar wani abinci ne na takobi wanda ake hadashi daga Negrinki da izza da kuma dantse. Iyakacin yawan ƙarfin dantsenka da izzarka da Negrinkinka, iyakacin yawan sinadarin da zaka samar kuma iyakacin ƙarfin takobinka. A hannun mara izza mara ƙarfin dantse takobin banza ce. Amma a hannun mai ƙarfin dantse da izza tafi komai sharri. Saurinta da kaifinta a kullum bazai taɓa daina ƙaruwa ba. Indai Armad zai karfafa dantsensa ta hanyar horo ya kuma ƙara ƙarfin izzarsa da Negrinki to kuwa Saif-Al-Barzak zata ci gaba da girma. Yana girma tana girma. Wannan shi ne aure tsakanin mutun da takobi.
Banbancin Saif-Al-Barzak da sauran takubba da aka aura shi ne ruhi. Saif-Al-Barzak tana da ruhi nata na kanta. Tana ji, tana tunani (duk da ba tunani irin na mutane ba), kuma tana gani. Ba sai Armad ya ɗakkota da hannunsa ba. Kawai tunani zaiyi ta biya masa buƙata. Suna yin magana ta zuci kuma su fuskanci juna. Tana kayyade sinadarin da zata ɗiba dai-dai misali tayadda Armad bazai cutu ba. Armad baya sanin an diba. Saɓanin da dama daga irin wannan takubba da suke zuƙe jinin mai su su kashe shi saboda rashin ka'ida.
Wani abu daya sa Saif-Al-Barzak ta zama ta musamman shi ne ikon da take dashi na gyara sinadarin da Armad ya tara. A cewar Zaikid babu wata takobi da take haka a duniya sai ita. Tana rage izza ta ƙara ƙarfin dantse tunda shi aka fi buƙata a sarrafa takobi. Idan Armad ya tara ƙarfin izza hamsin, ƙarfin dantse hamsin, sai ta rage izzar ta koma ashirin da biyar ta ƙara ƙarfin dantse zuwa saba'in da biyar. Hakan yana ƙara mata sauri da kaifi na gaban lissafi. Kaji takobi mai lissafi. Wani abin mamaki aljanun da suka nuna masa yadda zai yi amfani da takobin basu faɗa masa wannan ba. Watakila basu sani ba ko kuma sun manta.
Haka suka ci gaba da tafiya Zaikid yana yi masa bayani-bayani, faɗa-faɗa akan abubuwa da dama. Armad yayi shiru yana jinsa. Daga baya yayi shiru; watakila ya gaji ne, watakila kuma ya fuskanci faɗan yayi yawa.
"Ba wai faɗa nake maka ba," Inji Zaikid. "Kawai dai abin ne ya ɗan bata min rai. Amma kada ka damu zamu samo bakin zaren. Bari dai mu gama da Ururu."
Zaikid yayi kidansa yayi rawarsa kuma har ya gama Armad bai ce komai ba. Bawai haushi Armad yaji ba kawai dai bashi da abinda zai faɗa masa ba. Na farko dai duk abubuwan da Armad yayi tun daga lokacin daya fita daga gida har zuwa yanzu duk akan kansa yayi su, babu wani mai gyara masa ko ɗora shi akan hanya. Yana da buƙatarsu amma babu wanda yazo ya taimakeshi dan haka indai za'ai magana ta gaskiya acikinsu babu mai bakin magana ko mai Armad ya aikata. Amma dai tunda kakansa ne baya so yayi masa musu saboda haka yayi shiru ya rabu dashi.
Awa guda suka ɗauka suna tafiya kafin su isa katangar. Narkeken baƙin ƙarfe ne ya cika sama ya makare, baka ganin gaba baka ganin baya. Idan ka kalli gabas shi zaka gani, haka yamma, kudu, da arewa, ko ina shi ne. Gashi dai fuskarsa kaɗai Armad yake gani, amma kuma kallo ɗaya yasan yana da kauri na gaban misali. A rufe yake ruf babu wata ƙofa ko taga a jikinsa. Sa'ar kawai da suka ci shi ne babu wasu namun ruwa da suke ƙoƙarin kawo musu farmaki. Zaikid ya ragewa kwale-kwalen nasu sauri amma duk da haka wata irin iska ce mai ƙarfi take turasu baya. Suna yin gaba iskar tana ƙaruwa. Akwai wani yanayi na izza wanda Armad ya kasa fahimta. Yana ji tsigar jikinsa tana tashi amma kuma ya kasa gane meye asalin abin.
Zaikid ya miƙe tsaye ya zare takobinsa ya tashi akan iska ya nufi kantangar gadan-gadan. Kafin ya ƙarasa takobin ta fara haske kamar walkiya. Yana zuwa ya sari katangar. Daga inda yake zaune Armad yana jiyo Zaikid yana kiran 'Wilbafosiyan Siwod Dans'. Koma wace irin katanga ce Armad yana da yaƙinin takobin farfesa tafi ƙarfinta, kawai jira yake yaga ta tarwatse.
Bayan komai ya lafa katangar ta bayyana ko kwarzane babu a jikinta. Armad yayi mamakin hakan matuƙa kuma a lokacin ya fara yiwa katangar wani sabon kallo.
Zaikid ya ƙara kaiwa katangar sara a karo na biyu. Tartsatsin wuta ya tashi. Katangar ta bada wani amo mai rikitarwa wanda Armad yaso ya kashewa Armad kunne. Abin mamaki cikin dakika guda sautin ya baje ya ɗauke kamar wani abu ya zuƙe shi. A karo na uku Zaikid ya ƙara kaiwa katangar sara amma babu wani abu daya faru. Zaikid ya dawo cikin jirgin inda su Armad suke fuska a yamutse. Ga dukkan alamu shi kansa baiyi tsammanin hakan ba.
Armad ya miƙe ya samar da takobin Wilbafos mai taurari bakwai a hannunsa na dama. Sannan ya samar da wata takobin a hannunsa na mai ɗauke da Negrinki. Ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban katangar inda ya saukar mata da sara. Tartsatsi tsari yayi sama amma daya baje babu ko kwarzane a jikin katangar.
"Hannun aradu!"
"Ɗorawa Abada!"
"Zaren Babbar Mutuwa!"
"Zaren Manyan Mayu!"
Duk babu wata fasaha da Armad bai kira ba amma a banza. Daga ƙarshe sukai haɗin gwiwa da Zaikid: shi yana zuƙo Negrinki domin ragewa duniyar ƙarfi, shi kuma Zaikid yana saran katangar. Amma ko ɗiso balle kwarzane. Kai kace shafata suke yi.
Zaikid ya juya wajen Shata ko zai gwada tasa dabarar. Shata ya girgiza kai. A zahiri Zaikid yasan baya buƙatar Shata ya gwada komai domin bashi da sirrin daya wuce na Wilbafosiyan Siwod Dans. Amma tunda sun kasa ai babu laifi a bawa wani ya gwada.
"Watakila nima nayi girman kai," inji Zaikid. Yaja wani nishi mai kama da nadama. "Nasan da wannan katanga amma banyi wani shiri na musamman akanta ba. Nayi tunanin muna zuwa zan saka takobina na yanka ta na samar mana hanya."
"Ba kai kaɗai ba," inji Armad. "Nima nasan da katangar amma na shigo gadar zare ban shirya mata ba. Amma jimami babu inda zai kai mu. Yanzu ina mafita?"
Nan take suka shiga tattaunawa akan hanyoyin da suke dasu. Daga ƙarshe suka yanke shawara su shiga sashin ikwatora su nemi hanya ta ciki tunda babu katangar anan.
***
Akan doron ƙasa na biyu akwai gine-gine dogaye wanda daga ko'ina zaka iya hango su. Wani ginin ya kai hawa talatin, wani yakai hawa arba'in, kowanne an shafe shi da baƙin fenti samfurin Ururu. Akwai garuruwa da dama da ƙauyuka wanda mutane suke rayuwa acikinsu. Kusan kowacce ƙabila daka sani a duniya zaka same ta akan doron kasa ta biyu. Kawai bambancin duk wani mutum daka gani a wannan ƙasa masoyin Ururu ne. Dul'Ururu da kansa ya zabo su ya kuma basu waje suke rayuwa a ƙarƙashin kariyarsa. Watakila wannan shi ne dalilin da yasa kabilu irinsu Yeren (ƙabilar nan masu dogon wuya da Armad ya gamu dasu a doron ƙasa ta bakwai lokacin da yaje neman Nusi tare dasu da Iliyasisi da Cokali) suka fi yawa a wannan ƙasa. Duk garin daka je baka rasa ɗan ƙabilar Yeren da mukami babba.
A garin Fitla dake sashin arewa kusa da ikwatora akwai wani wajen shan shayi da fura da nono. Mutane daga kowanne sashi na wannan ƙasa suna zuwa wannan waje akai-akai domin ci da sha. Dalilin mai sauki ne: daga garin Fitla sai garin Bisad inda babbar shalkwatar Ururu take. Idan ka samu fili a garin Fitla ya tsaya ka ɗaga kai tsaf zaka hangi doguwar toluwar shalkwatar da ƙarafa dogaye wanda akai musu ado da bakaken idanu.
A dai-dai wannan lokaci acikin wajen mutane ne zaune suna shan fura suna labari. Wasu daga cikinsu acikin farin-ciki da raha suke badan komai ba sai dan labarin yana yi musu daɗi. Wasu kuwa akwai damuwa akan fuskokinsu.
"Lokaci yayi da zamu share maƙiya, mu kafa babbar daula irin ta doron ƙasa ta farko a dukkan ƙasashen ƙasa."
"Nima dai ba ƙaramin daɗi nake ji ba da hakan zata faru, duk da ina jimamin abinda Maikiro'Abbas zaiyi."
"Wai wane irin Maikiro'Abbas? Muna da sarki Dul'Ururu, muna da kannen babban sarki Kuyurussa'ayi Haruta da Maruta, muna da kwamanda Yurba, muna da samudawa uku, muna da sarakunan Jinzidal wanda zasu taka rawa. Kuna tunanin Maikiro'Abbas zai iya ja dasu?"
"Nima dai haka na gani. Mutane suyi ta zuzuta shi. Bana jin yana da wani ƙarfi. Idan ma yana da ƙarfi mutun ɗaya ne kurum. Mai mutun ɗaya zai iya?"
Haka dai wannan mutane suka ci gaba da shan fura suna labari. Ko'ina ka zagaya a wannan gari zancen da ake yi kenan. Idan mutum ya daga kai ya gano toluwar Ururu sai kaga yaci gaba da zance.
Sai dai saɓanin garin Fitla, a garin Bisad tuni aka kulle dukkan guraren siye-da-siyarwa. Duk wani saƙo da loko idan kabi zaka tarar babu kowa sai fili. Duk mutanen garin sun koma gida sun kulle kansu kamar yadda sanarwa ta fita. A duk bayan minti goma zuwa sha-biyar zaka ga ma'aikata sun zagayo suna dubawa. Duk wanda suka kama a waje ya zama nama.
Idan ka matsa kusa zuwa ƙaramar hukumar Ganya inda shalkwatar take zaka ga tsaron ya wuce duk yadda kake tunani. Duk wani waje daka sani ma'aikata ne. Babu masaka tsinke. Kana gani kasan wannan shirin ba Nusi kaɗai ake yiwa ba.
Acikin shalkwatar akwai wajaje daban-daban masu dogon tarihi. Ɗaya daga cikin wannan gurare shi ne wani katon fili dake gaban shalkwatar wanda ake kira da Filin-Jiri. Duk wani yaƙi da akai a shalkwatar a wannan fili akayi shi. Ko yaƙin maƙabarta anan akai.
Wato tun daga nesa zaka san Ururu sun shirya. Sadaukai ne ma'abota izza a jere a layi a Filin-Jiri. Filin yana da girma sosai amma hakan bai ɓoye yawan sadaukan ba. Sunyi shiru suna kallon gabas suna jiran umarni. Daga nesa idan ka hangesu kawai duhu zaka gani saboda bakaken kayan dake jikinsu.
A dai-dai wannan lokaci acikin shalkwatar akwai wani ƙaton dakin taro. Mutun huɗu suna zaune a ɗakin akan kujera. Suna sanye da dogayen riguna bakake masu zanen bakaken idanu. Akwai suna a kafaɗar kowacce riga wanda yake cewa kwamanda. Wani abin mamaki shi ne uku daga cikinsu samudawa ne. Girman jikinsu ya haura zira'i arba'in. Suna zaune suna muzurai kamar zasu ci babu. Mun taɓa ganinsu tare da Dul'Ururu a lokacin yaƙin sarakunan jinzidal. An bayyana cewa salsan Dul'Ururu ne. Na ƙarshen kuma madaidaicin jiki ne dashi kamar kowanne mutun. Zamu tuno shi a ƙarshen littafi na uku lokacin wata tattaunawa tsakanin Dul'Ururu dasu Haruta da Maruta da shi. Sunansa Yurba Ururu. A lokacin shi ne ya dage sai an kaiwa su Armad hari a yayinda Dul'Ururu yake ganin a jinkirta a jira ɗaya daga cikinsu ya kashe ɗaya sai a ƙarasa shi.
Da sauri mai gadi ya shigo ya tsaya a bakin ƙofa ya ƙame tare da ɗaga hannu cikin girmamawa.
"Barkanku da safiya."
Yurba ya gyada masa kai yana bashi umarnin yaci gaba.
"Lokaci yayi," inji mai gadin.
Ɗaya daga cikin samudawan uku ya yamutse fuska yana kallon agogon dake hannunsa. "Saura awa huɗu fa. Tun yanzu kuke so mu fita?"
Yurba ya miƙe tsaye. Aikin da aka bashi ya ɗebi runduna yake ya laɓe wajen da Armad zaiyi fada da Bihanzin ko Ikenga. Idan ɗaya ya kashe ɗaya ya ƙarasa ɗayan. Tunda wancan faɗa bai kasance ba ya dawo gida kuma yanzu yana cikin wanda zasu taka rawa a wannan yaƙi.
Bayan Yurba ya fice sai ragowar mutun ukun suka miƙe a tare suka bi bayansa. Duk da sau ɗaya muka taɓa ganinsu munsan muƙaminsu ɗaya da Yurba, wato muƙamin kwamanda, amma basa fitowa sosai tunda salsan Dul'Ururu ne. A wancan lokacin zanga-zanga mai zafi ta barke a ko'ina a duniya saboda abinda Bihanzin yayi na bayyana sirrin dazai rikita duniya. Dul'Ururu ya basu dama su kashe duk wanda suka gani a waje domin kawo ƙarshen zanga-zangar. A yanzu sunzo domin yankewa Fatima hukuncin kisa.
Na farkonsu ƙatoton al'amudi ne a hannunsa ruwan rawaya-rawaya. Fari ne mai sanko da gashin-baki. Sunansa kwamanda Diwani.
Na biyun shima fari ne amma yana da gashi baƙi mai tsaho. Babu makami a hannunsa wanda hakan yake nuna kodai makaminsa a ɓoye yake ko kuma da aljanu yake amfani. Sunansa kwamanda Binani.
Na ƙarshen yana da duhun fuska. Yayiwa gashin kansa dana gemunsa kitso. Abin mamaki gemun ja ne amma gashin kan baƙi ne wanda hakan zai sa ka fara tunanin ko ƙunshi yayi.
A can wani ɗakin kuma sarki Han'ibal ne zaune yana shan shayi. Sama da minti goma kenan wanda aka turo wajensa yake tsaye yana jiransa ya bashi dama yayi magana. Bayan ɗan lokaci mutumin ya ƙara buɗe baki ya ce, "mai girman sarkin jinzidal, idan ka kammala zan rakaka zuwa wajen da zaka tsaya domin bada gudummawar ka."
"Kai," Han'ibal ya daka masa tsawa. "Ka dame ni. Har yanzu akwai ragowar awa huɗu. Kuna tsammanin naje na tsaya ina jira har tsahon wannan lokaci kenan?"
Dole mutumin ya haƙura yaci gaba da jira.
A ɗaki na gaba kuwa Ibraham Nil ne da Suwainah.
"Na tambaye ki baki bani amsa ba," inji Ibraham Nil. "Yaya kike ganin yaƙin nan zai kasance?"
"Kamar yaya?" Suwainah ta yamutse fuska. "Mu zamu yi nasara. Har akwai wani kokwanto aciki?"
"Ehem... Kinga, ki fada min gaskiya babu wanda zan gayawa. Daga ni sai ke. Kina ganin akwai wanda zai iya kashe Maikiro'Abbas acikin mu?"
Suwainah ta ɓata rai. "Kai... Wai kai Nil mai yasa kake so ka ringa raina Ururu ne? Kana tunanin duk mayaƙan mu dake doron ƙasashen ƙasa babu wanda zai iya kashe Maikiro'Abbas?"
"To meye?" Nil ya ɗaga kafaɗa. "Ai ba kowanne Ururu ne yake da ƙarfi ba, yarinya. Nasan da dama da basu da izza. Kuma ni nasan waye Maikiro'Abbas shi yasa nake tambayar ki. A wancan lokaci dole ce tasa sukai masa sarautar Sarkin jinzidal. Ba daban shi ba da baza ayi sarautar sarkin jinzidal ba. A yanzu suna ganin kamar sun gama amfani dashi zasu watsar. Marubucin sarki fa ba yaro ba."
A dai-dai lokacin wanda aka turo ya kira su ya shigo. Suwainah tayi tsaki ta fice ta bar Ibraham Nil a wajen. Shima bayan ya canja riga yabi bayanta ya nufi Filin-Jiri.
A babban ofishin sarki Dul'Ururu, Maruta ne yake zaune ya yamutse fuska. Dul'Ururu yana kan karagarsa yayi shiru yana kallonsa. Duk su biyun babu wanda yake cewa komai.
"Ina jin sun kama shi," inji Maruta.
Comments
Post a Comment