Skip to main content

285

 *

Abul Babara


Martaba: haifaffen 'ɗa', shugaban ƙungiyar duba a ƙasashen ƙasa (mai ritaya)


Laifi: 1) Cin mutuncin sarakunan jinzidal. 2) Rashin girmama manya. 3) Horar da maƙiyan manya a fannin izza. 


Wannan laifuka sun ɓata maka suna da yawa.


Suna: -91

*


Dul'Ururu yaja dogon numfashi gami da girgiza kai, ya ce, "Babara, ka aikata laifuka da dama kamar yadda na lissafa, amma lokacin Kamfen lokaci ne na yafiya. Faɗi ra'ayin ka naji, zaka karɓi gaskiya ka goyi bayan kamfen, ko kuwa zaka bijire ka faɗa cikin ɓatattu?" 


"Laala-laala!" Inji Babara. "Ko ɗaya."


Kafin ya rufe baki Dul'Ururu ya zana tauraruwa akan sunan sa. Nan take ciniki ya faɗa akai wa Babara kuɗi. 


*

Abul Babara


Martaba: Mai laifi


Kuɗi (Bounty) : ayrid miliyan ɗari biyu da arba'in (240,000,000 mil).


NB: da rai ko ba rai.

*


Babara ya yamutse fuska ya turo baki kamar wani ɗan ƙaramin yaro, ya ce, "kut, wai kuna nufin Nostaljiya ta ninka ni? Da sake wallahi. Ni fa nake da aljani mai kwalkwal da kuma Negrinki mai juya ƙasa ta koma taɓo. Na iya buga ƙasa, na kuma iya ɗaure ƙasa. Amma duk da haka..."


Nusi ta wangame baki. "Huh? Wai kana tunanin abu ne mai kyau kuɗin ka suyi sama? Ai har gwanda ace baka dasu, kaga kamar ni. Yanzu haka zan iya tafiya a doron ƙasa salin-alin na yiwa Armad aiki ba tare da mafarauta suna bibiya ta ba." 


Nostaljiya ta harare ta. Inda ita kuma ta ɗaga hannu alamun ta janye maganar ta. Sai dai kuma ana cikin haka Dul'Ururu ya juyo kan Nusi. 


Hoton ta na kan shafi na dubu biyu da maitan da bakwai.


*

Nusi Kil'zanki


Martaba: haifaffiyar 'ƴa', kansila a garin Khán (mai ritaya)


Laifi: 1) Cin mutuncin sarakunan jinzidal. 2) Rashin girmama manya. 3) Soyayya da Armad Wilbafos (babban maƙiyin manya).


Wannan laifuka sun ɓata miki suna da yawa.


Suna: -54

*


"Nusi, kina da cikakkiyar masaniya kan yadda iyalan Wilbafos na da suka yaudari kakannin ki na ƙabilar Kil-zanki. Kin aikata munanan laifika akan Armad wanda manya baza su iya ɗauke ido daga kai ba. Amma kamar yadda nake ta faɗa wannna lokaci ne na yafiya. Mai zaki ce? Kin amince zaki goyi bayan kamfen...?"


"Uhm-uhm." Inji Nusi tana girgiza kai. "Amma idan son samu ne kada ku saka min kuɗi, kunga laifuka na basu da yawa, kuma har yanzu ina matsayi na na kansila a garin Khan babu wanda ya cire ni ballantana ku saka min 'mai ritaya'. Ko ba haka bane, Cokali?" 


Cokali ya gyaɗa kai cikin sauri. "Har a ɗazu. Indai ba yanzu suka cire ki ba."


Dul'Ururu ya ɗan ja numfashi, sannan ba tare da ɓata lokaci ba ya saka mata hannu.


*

Nusi Kil'zanki


Martaba: Mai laifi


Kuɗi (Bounty) : ayrid miliyan ɗari biyu da arba'in - 330,000,000 mil


NB: da rai ko ba rai.

*


Babara ya yamutse fuska a fusace. "Kut.. Akan wane dalili zaku sa kuɗin ta yafi nawa?! To na fuskanci akwai iskanci acikin abubuwan nan naku." 


Nusi ta nuna kuɗin hannun ta yana karkarwa. "Miliyan ɗari u...u...uku....?"


Iliyasis yayi murmushi, ya ce, "nayi tunanin zai fi haka ma."


Cokali kuwa fashewa yayi da dariya har da dukan cikin sa. "Nusi, hahaha... Nusi kinyi kuɗi."


Nusi ta harari Cokali. "Cokali, ALLAH idan bakai shiru ba a kan ka zan huce." 


Mutun na gaba shi ne Rafiyan Nazara akan shafi na ɗari huɗu da shida. An buɗe shafin kenan za'a fara karantawa sai Maruta yai tsalle ya dira a gaban Nusi. Takobin sa a zare. "Bari na fara haɗe kan waɗannan kafin ka kira sauran." Inji shi. Da maganar sa da saukar takobin sa duk a lokaci guda suka faru. Cikin daƙiƙa ɗaya komai ya canja. Hankalin kowa ya dawo jikin sa. Idan ma akwai wanda yake tunanin za'a rabu ba tare da an fafata ba to ya canja tunani. 


Takobin Maruta Ururu baƙa ce, baƙa-ƙirin, kai kace gawayi aka shafa a jikin ta. Wani abin mamakin shi ne ƴan daƙiƙu da suka wuce babu takobi a hannun sa, kuma babu wanda yaga sanda ya fito da takobin. Kawai dai takobin ta bayyana a hannun sa kamar dama tun can tana nan kawai ganin ta ne ba'a yi. 


Kai ka manta da takobin, wato shi kansa Maruta Ururu bajimi ne. Idan ka kwatanta shi da Nusi zaka ga kamar ɗa ne da uban sa. Abin mamakin shi ne bawai girman jiki yafi ta ba, amma kawai zunzurutun gwarjini ne yasa. Rigar jikin sa doguwa ce fara mai ɗiso-ɗison ja, tana kaɗawa kan iska tana ɗaukar hankali. 


Nusi tai sauri ta kwanta ƙasa domin kaucewa takobin amma duk da haka sai da ta goge ta. Kafin ta kai ƙasa takobin Maruta ta ɓace daga inda take ta bayyana a gefen fuskar ta. Kaifin takobin yana gab da sare mata fuska Iliyasis ya dira ya tare saran. Wani tartsatsin baƙar wuta yai sama. Takubba suka gurji juna. Ana cikin haka sai takobin Maruta ta ɓace ta bayyana a saitin kan Iliyasis, dai-dai ƙeyar sa. Sai dai ganin yadda takobin ta ɓace a baya yasa Iliyasis ya ankare da wuri. Ya juya cikin tsananin zafin nama ya tari takobin cikin kwarewa. Tartsatsin wuta ya ƙara yin sama. 


Kafin takobin ta ɓace Iliyasis yayi fuka-fuki ya tashi sama ya hau kan takobin. Taku ɗaya tak yayi akai sannan ya ƙara yin tsalle ya kai wafta kan wuyan Maruta da niyyar tsinke masa kai. Amma kafin ya ƙarasa takobin Maruta ta ƙara bayyana a gefen sa. Dole ya dawo da hankalin sa kan takobin. A wannan lokacin maimakon ya tare takobin sai kawai ya kauce mata, sannan yayi juyi a sama ya kaiwa Maruta suka da takobin sa. 


Wato abin ya ɗau lokaci wajen bayani amma a zahiri tun daga shigar Iliyasis har zuwa yanzu a daƙiƙa ɗaya ake.  


Kafin sukan da Iliyasis ya kai ya isa tuni takobin Maruta ta ƙara bayyana ta kawo masa wafta ta sama. 


Iliyasis yai tsalle ya kaucewa takobin ya dira a gefe inda ya fuskanci Maruta ido da ido, kowannen su takobi a zare.


Zaka iya cewa wata sabuwar fasahar takobi Maruta yake nunawa - fasaha mai sarrafa takobi ba tare da an riƙe takobin ba - ko mai Iliyasis zai ce game da hakan. 


"Tun ina yaro na kan ji labarin ƴan uwa biyu: Haruta da Maruta. Wannan ƴan uwa guda biyu suna da gidaje a doron ƙasa na farko amma sun gwammace su zauna a ƙasa, badan komai ba sabida farauta. Sun kasance suna farautar duk wani mutun wanda aka sawa kuɗi. Ance babban mai suna Maruta Ururu hamshaƙi ne a fannin takobi, kuma ance yana da Babbar Rawa a fannin wadda ta ɗara Dauwamammen Saran Bihanzin. Kada ka bani kunya mana. Ka nuna min Rawar na gani." Inji Iliyasis. 


Maruta ya ɗan ɗaga girar sa cikin mamaki. "Ha.. wato suna na yazo gare ka? Yayi kyau. Wacce rawar kake so na nuna maka, Iliyasis? Akwai rawar amare, akwai ta angwaye."


#


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...