Skip to main content

357-361

 Wani murmushi ne yazo fuskar Armad. A duk sanda yayi amfani da wannan fasaha ya kan rasa lokaci sannan kuma ya tsinci kansa a can wani waje da bai san ina bane, ba tare da yasan yadda yaje wajen ba. A wajen Zaikid ya koyi wannan fasaha. Hasalima a iya saninsa Zaikid shi ne ya samar da wannan fasaha. Kuma ga dukkan alamu yau zaiga yadda ake amfani da ita.


Wani farin hayaki ne ya fara fita daga ƙarfen takobin yana juyewa izuwa hazo. Kafin kace meye wannan hazon ya taru yayi kauri ta yadda baka iya ganin na kusa dakai. A lokacin da Haruta ya gama kiran fasaharsa ta duniyar takobi, a lokacin Zaikid ya saukar da takobinsa. Daruruwan takubban Haruta suka haɗu da takobin Zaikid. Wata ƙara tayi sama sannan tartsatsin wuta ya cika ko'ina. Idan ka ɗaga kanka sama zakaga samaniya tana kaɗawa. Ƙasa kuma tana girgiza tana daddarewa. Iska ta dare gida biyu ta tarwatse. Ana tsaka da haka aka jiyo kiɗan Shata ya fara tashi a dai-dai lokacin da Negrinkin Armad ta cika wajen. Babu wanda yasan abinda kiɗan Shata yake yi amma ga dukkan alamu yana ragewa takubban Haruta sauri. 


Duk ana cikin wannan abin Saif-Al-Barzak ta lallabo ta baya ta kawowa Haruta sara. Takobi ta bayyana akan iska ta tare takobin Saif-Al-Barzak, amma Saif-Al-Barzak ta yanka takobin gida biyu sannan ta ƙarasa ta sari bayan Haruta. Jini yayi feshi daga wajen data sara, wani wawakeken ciwo ya bayyana a bayan Haruta. Yayi ƙoƙarin kiran ɗalasimi domin ya warkar da ciwon ko kuma ya tsayar da jinin amma ga dukkan alamu hakan bata samu ba. A lokaci guda kuma Zaikid na gabansa. Takubbansu a haɗe babu abinda yake tashi sai tartsatsin wuta. 


Babu damar Haruta ya juyo bayansa ya tare Saif-Al-Barzak domin kuwa yana juyawa Zaikid zai aikatashi. Amma kuma rashin juyowar tasa ba mafita bane. Domin kuwa hakan ne ya sake baiwa Saif-Al-Barzak dama ta ƙara saukar masa da wani saran, sannan wani, sannan wani. Duk inda ta sara sai kaga jini yayi feshi. Kafin kace meye wannan Haruta yayi faca-faca da jini. Zaikid da Saif-Al-Barzak suka ci gaba da saransa sai da suka tabbatar bashi da sauran ƙarfin a jikinsa, ko kare kansa baya iyawa, sannan suka tsaya.


"Tuladan-nan-Galak!"


"Tuladan-nan-Galak!"


Armad ya saukar masa da harin miyura guda biyu a jere sannan aka samu izzarsa tayi ƙasa. Zaikid ya sumar dashi.


Zaikid ya juya wajen Armad. "Armad, kada ka daina abinda kake yi domin kana tsayawa zai miƙe. Abinda kawai ya hana shi warkewa shi ne Negrinkin ka. Kai ma Shata ka ci gaba da kida hakan zai hana shi farkawa. Yanzu abinda ya rage mana shi ne ankwar da zamu ɗaure shi da ita sannan mu nemi hanyar fita."


Armad da Shata suka hau aiki. Kafin kace kwabo tuni wajen ya juye izuwa ja, launin Negrinkin Armad. Kakkauran hazo ya gauraye gurin ta yadda na nesa bazai iya ganinsu ba. Hatta Shata dake kusa sai yayi da gaske yake ganin Armad. Hakan yayi matuƙar tasiri wajen danne Haruta da kuma karya alkadarin duniyar. Abu guda ɗaya daya rage shi ne su ƙarasa shi. Tuni Armad ya fara lissafa irin hanyoyin da zasu yi amfani dasu wajen halaka Haruta da kuma irin cece-kucen da hakan zai janyo a duniya. Tabbas babu wata jarida da baza ta rawaito labari akan mutuwar ƙanin babban sarki Kuyurussa'ayi ba. Shin wane mataki Ururu zasu ɗauka?


A lokaci guda Zaikid lalube yake yi acikin jakar tsafinsa: ya fito da wannan ya fito da wancan. Duk abinda ya fito dashi sai kaga ya girgiza kai ya mayar dashi. Armad yana zaune yana kallonsa. Tunda suka haɗu basu yi wata magana kwakkwara da kakan nasa ba, amma hakan bashi yake nuna bashi da tambayoyi ba. Banda tambaya akwai kaɗaici da yake cin sa. Tun yana 'yaro' rabonsa da Zaikid. A ransa yana ji kamar ya tashi da gudu yaje ya rungume shi. 


Kafin ya fita nemarwa mahaifiyarsa magani Zaikid shi ne malaminsa kuma abokinsa. Shi ya koya masa fasahar Wasu-wasi. Kuma shi ne ya taimaka masa ya mallaki aljani Gal-Iyyu. Bayan Zaikid ya fita neman Hidaya Armad bai ƙara samun wata kulawa ta fannin izza ba. Kuma tun daga wannan lokaci basu ƙara haɗuwa za Zaikid ba. A lokacin da akai yaƙin sarakunan jinzidal Armad bai san kakan nasa suna tare da Hidaya ba. Kuma bai san kakan nasa yana gida ya dafa masa abinci yana jira ya dawo ba. Bayan nan mun ga yadda Zaikid ya fita daga gida ya shiga duniya sakamakon kashe Hidaya. Mun ga yadda ya taimaka wajen kammala waƙar maƙabarta. Mun kuma ji yadda Ashura suka kama Zaikid da Fatima duk da bamu san yadda hakan ta faru ba. Kuma zaka iya cewa tambaya ta farko da take cin Armad ita ce: mai yasa iyayen nasa suka tari Ashura? Ko shi kansa yasan hakan ganganci ne.


Armad ya yanke shawara ya jira yaga gudun ruwan kakan nasa. Shin zai fara yi masa bayani da kansa ko kuma sai ya tambaya?


Bayan ɗan lokaci Zaikid ya gaji da binciken da yake yi ya juyo ya fuskanci Armad ya ce, "bani da wata laya ko ankwa da zata iya ɗaure shi."


Armad ya yamutse fuska. Yanzu ace duk tulun kayan da Zaikid ya fito dasu babu abinda zai iya ɗaure Haruta? A lokaci na farko Armad ya tsinci kansa yana ƙoƙarin auna girman jakar tsafin Zaikid. Irin yawan tarukucen da Zaikid ya tara aciki bazai misaltu ba. Wasu abubuwan idan aka ce sun shekara ɗari Armad bazai yi musu ba.


To amma mai yasa dole sai sun ɗaure Haruta? 


"Idan zai bamu matsala mu yanke masa hukunci mana kawai a huta," inji Armad.


Zaikid ya girgiza kai. "A'a, kashe shi zaiyi wahala duk kuwa da baya motsi. Sannan kuma zamu iya amfani dashi mu karbi mahaifiyarka."


Haka ne, to amma Armad yana tsoron matsala. Kada sai sun saki jiki Haruta yayi musu illa. Amma dai ya yanke shawarar barin al'amarin a wajen Zaikid. Duk abinda kakan nasa ya amince shi za'ai.


"Matsalar Ururu basa amfani da aljanu," inji Zaikid. "Duk wata farar laya aljani take ɗaurewa ba mutun ba. Saboda haka baza tayi aiki akan Haruta ba. Akwai mai wata dabara acikin ku?"


Armad da Shata suka ɗanyi shiru cikin tunani kafin su girgiza kai.


Zaikid ya numfasa. Dole suna buƙata su ɗaure Haruta kafin suyi wani abu. Musamman duba ga ƙarancin lokacin da suke dashi. Idan lissafinsa dai-dai ne to akwai yiwuwar bai fi saura kwana guda Ururu su yankewa Fatima hukunci ba. 


"Ku ƙara yin tunanin," Zaikid ya ce. "Armad kayi tunani. Bamu da wata hanya da zamu ceto Fatima idan bamu gano yadda zamu ɗaure Haruta ba."


Armad ya gane lissafin Zaikid. Kuma ya yadda hakan lissafi ne mai kyau. Musamman idan suka ɗaure Haruta suka tafi dashi wajen da Ururu suke shirin yankewa Fatima hukunci suka nemi a basu ita a maimakonsa. To amma bashi da wata dabara da zai iya ɗaure Haruta da ita. Rashin amfani da aljanu yana daga cikin sharrin Ururu. Duk wani sihiri da zaiyi aiki akan mai aljani su bazai yi aiki akansu ba. A baya munji cewa Ururu suna amfani da dordor a matsayin aljanu su mallaki fasahohin sarrafa wuta da walkiya. To amma layar aljanu bata aiki akan dordor. Kuma a iyakacin sanin Armad babu wata laya da ake iya amfani da ita domin ɗaure dordor.


"Armad kana da damar da mu bamu da ita," inji Shata. "Kaga wannan ankwar daka tsinke daga jikin Zaikid Bilak-siton ce. Babu wanda yasan adadin farar layar da aka narka aciki. Ni bazan iya taɓa taba saboda aljani na. Shi kansa kakanka Zaikid bazai iya komai ba indai yana ɗaure cikinta. Amma kai baka da wannan matsalar. Watakila Ururu basu san da haka ba shi yasa suka turo Haruta shi kaɗai da Zaikid. Suna ganin babu yadda zamu yi mu tsinke ankwar. Kaga kuwa dole muyi amfani da wannan damar da muka samu domin baza mu ƙara samun irin ta ba."


Armad yana da masaniya akan irin wannan abubuwa da ake kira da Bilak-siton. Idan kana so ka haɗa Bilak-siton sai ka samu sinadarin yeniy ka narka shi, sannan ka zuba farar laya aciki ta narke, sai ka bar su su bushe a tare. Zaka iya haɗa duk abinda kake so daga kan ankwa zuwa ƙofofin kurkuku zuwa takobi da kwari da baka. Indai ka taɓa jikin mai amfani da aljani da Bilak-siton to nan take jikinsa zaiyi sanyi kamar ka ɗaure shi da farar laya. Armad bashi da aljani saboda haka farar laya ko Bilak-siton basa aiki akansa. Watakila hakan yana daga cikin mafi girman makamin da yake dashi wanda zai iya amfani dashi a faɗansa da Bihanzin da Ikenga. Duk su biyun suna da aljanu. Ikenga yana da aljanin hadari, shi kuma Bihanzin yana da aljanin iska. Dole Armad yayi amfani da wannan maimakon kawai gwada kwanji.


Yana zuwa nan a tunaninsa sai wata dabara ta fado masa. "Zan iya ɓoye shi a duniyar Negrinki."


Zaikid da Shata suka juyo suka kalleshi.


"To amma zai iya guduwa," inji Armad. "Kunga Kaizadu da Elbinuil da Hasanu sun gudu. Kafin su mai tsaron ƙofa Han'diyuza ya gudu. Kuma duk ban san ta ina suka fita ba."


Cikin sauri Zaikid ya ɗakko wani ɗauri daga cikin jakarsa. "Muje na gani watakila akwai dabarar da za'ayi."


Armad ya ɗanyi jim kafin daga bisani ya amince. Ya samar da mutun-mutumi domin yaci gaba da samar da Negrinki, sannan dashi da Zaikid suka shiga cikin duniyar suka bar Shata yaci gaba da tsare Haruta.


Duniyar Negrinki, kamar yadda muka sani, duniya ce mai cike da duwatsu; narkakku da busassu. Tana da girma na gaban misali domin har yanzu bamu taɓa ganin an ƙure mata nisa ba. Abu guda da muka sani shi ne duk wanda ya shigo wannan duniya idan ba Armad ba yana fuskantar nauyi wanda yake hana shi motsi. A wasu lokuta nauyin yakan danna mutun ƙasa cikin wutar dake ci. Wasu da dama sun halaka ta dalilin hakan. Amma wasu da dama sun haye. Abin sa'a ne. Ya danganta da wajen daka faɗo a lokacin da Armad ya cillo ka ciki.


Zaikid yaci sa'a a dai-dai saman wani tsauni Armad ya cillo shi. Amma duk da haka da kyar yake iya daga ƙafarsa saboda nauyi. Armad yayi ƙoƙarin cire nauyin amma ya kasa. Hakan yana daga cikin abinda yake ciwa Armad tuwo a kwarya. Duniyar bata bin umarninsa. Kamata yayi ace nauyin akan abokan gabarsa kaɗai yake aiki. To amma duk wannan abubuwa ne wanda Armad ya ƙuduri niyyar gyarawa zarar ya samu nutsuwa.


Zaikid ya buɗe ƙullin daya ɗakko daga jakar tsafinsa ya fito da wasu hatimai.


"Armad, ina zuwa."


Ya bar Armad a wajen ya sauka ƙasan tsibirin ya nemi waje ya haƙa rami ya binne. Ya ƙara ɗakko wani ƙullin ya ƙara binnewa. Bayan ya kammala ya dawo wajen Armad.


"Ko zaka iya faɗa min mai ka binne?" 


"Kafi ne," inji Zaikid. "Ina fatan zai hana Haruta fita." 


Ya nunawa Armad duk wajajen daya ɓoye hatiman. Daga nan suka juya suka fito waje. 


Har yanzu Haruta na kwance a ƙasa yana numfarfashi. Jini bai daina zuba daga sassa daban-daban na jikinsa ba. Shata da mutun-mutumin Armad suna tsaye a kansa. 


Armad ya kalli Zaikid wanda ya gyaɗa masa kai. Ya buɗe ƙofa ya jefa Haruta cikin duniyar Negrinkinsa ya kuma tura mutun-mutuminsa ya kula dashi. 


Sannan suka kama hanyar fita daga cikin gadar. 


Mintuna kaɗan suna tafiya suka zo ƙarshen ginin inda yayi iyaka da bangon arewa. Zaikid ya fito musu da kwale-kwale suka shiga suka kama hanyar zuwa doron ƙasa na biyu. Awa guda suna tafiya babu wata tangarda da suka samu. A lokacin nutsuwa ta fara zuwar musu. Kodai ba sosai ba amma sun dawo hayyacinsu. Misali, Shata yana kwance idanunsa a rufe. Armad bashi masaniyar bacci yake ko kuma kawai rufe ido yayi. Shi kuwa Zaikid yana zaune a gaban jirgin yana kallon hanya. Lokaci-lokaci zaka ga dordor ko kuma aljanun ruwa sun taso musu amma suna jin yanayin izzarsu sai kaga sun canja hanya. Armad yana zaune a bayan kwale-kwalen yana kallon Zaikid. Ga dukkan alamu kakan nasa bashi da niyar yi masa bayanin komai.


Haƙurin Armad ya ƙare. Zaka iya cewa ya gaji da jira. Yana buƙatar amsa a yanzu-yanzu. "Wai tayaya Ururu suka kama ku? Duk shekarun da kuka yi a baya baku kamu ba sai yanzu? Kuma wane dalili ne yasa kuka tari Ashura?"


Zaikid ya ɗan juyo ya kalleshi sannan ya juya yaci gaba da kallon hanya ba tare da yace komai ba. Armad ya fusata ya tashi da sauri ya isa wajen da yake zaune.  


"Farfesa, wai mai yake faruwa ne?"


Zaikid yaja ɗan numfashi sannan ba tare da ya kalleshi ba ya ce, "jika na Armad, kada kayi gaggawa. Sannu a hankali zaka fahimci duk abinda yake faruwa..."


Kafin Zaikid ya ƙarasa Armad ya fara huci. Ya daki gefen jirgin da hannunsa.


"Wane irin sannu a hankali? Sama da shekara goma kenan kowa acikinku yayi nasa waje babu ko sallama. Sannan kuma yanzu mun haɗu kana nema kace baza ka gayamin komai ba. Na gaji da irin wannan hali da kuke nuna min. Idan har yanzu ba zaku aminta dani ku bayyana min gaskiyar abinda ake ciki ba to gwanda kowa yayi masa waje."


Armad yana magana bakinsa yana kumfa. Kusan zaka iya cewa ɓacin ran shekaru ne daya taru yake fitowa. Tun daga kan mahaifiyarsa zuwa Hidaya zuwa Zaikid babu wanda ya taɓa gaya masa wani abu. A kullum ƙoƙari suke yi su kaucewa tambaya ko kuma kai tsaye su ƙi bashi amsa. Armad ya gaji. 


Zaikid yayi shiru yana kallon sa. A fuskarsa babu ɓacin rai amma kuma babu alamun zai amsawa Armad tambayoyinsa.


"Yanzu dai maganar Haruta muke yi da yadda zamu karɓo mahaifiyarka," inji Zaikid. "Kada ka raba hankalinka."


Armad yaji kamar yayi tsalle ya kai masa duka. Da kyar ya danne zuciyarsa. 


"Wallahi idan baka gayamin gaskiya ba a yau to nan ne ƙarshen tafiya ta dakai," inji Armad. 


Zaikid ya juyo ya ƙura masa ido.


Bayan kimanin minti guda Zaikid bai ce komai ba Armad ya miƙe ya nufi gefen jirgin yana ƙoƙarin fita.


"Kayi haƙuri," inji Zaikid. Armad ya juyo ya kalleshi. "Ka samu iyaye masu ƙarancin tausayi. Baga Fatiman ba, baga Taidaran ba. Duk su biyun sun watsar dakai. Idan banda jarumi ne kai da tuni maƙiya sunga bayanka."


Armad ya dawo ya zauna yana sauraronsa.


"Kana so kaji abinda yake faruwa?" Inji Zaikid.


Armad bai amsa ba domin a wajensa bada amsar wannan tambaya ɓata lokaci ne. Shakara nawa yau yana son yaji abinda yake faruwa.


"Labarin yana da tsaho kuma bashi da daɗin saurare, ka tabbata kana so kaji?"


Armad ya haɗe rai. Babu wata dabara da zaiyi masa a yau.


"Ina ka shiga wata guda daya wuce? Tunda aka kama mu ban ji duriyarka ba."


"Wilbafosiyan Siwod Dans," inji Armad. 


Zaikid ya buɗe baki zaiyi magana Armad ya katse shi. "Nasan ka hanani amfani da ita. Amma kafin kace wani abu ka sani dole ce tasa nayi amfani da ita. Kuma a hakan ma an samu ci gaba. A baya shekaru biyu na rasa ba wata guda ba"


Zaikid ya haɗe gira. "Har sau nawa kayi amfani da ita?" 


"Sau biyu ne kacal," Inji Armad. "Kuma duk dole ce ta sa. Ni dai yanzu a bar wannan zance ya riga ya wuce. Ka bani amsar tambaya ta."


"Gayamin meye alaƙar ka da gidan Kil'zanki," inji Zaikid.


Armad na jin tambayar ya gane abinda ke faruwa. Tabbas Zaikid ya haɗu da Nusi Kil'zanki.


"A ina ka gamu da Nusi?" Armad ya tambaye shi.


"A gasar jinzidal," inji Zaikid. "Har cikin kurkukun da Ururu suka ajiye mu tazo. 'Suna na Nusi Kil'zanki, nazo na kubutar daku,' ta ce. Ko da Fatima ta tambayeta meye alaƙarta da kai sai ta dage ita ƴar-uwarka ce duk kuwa da Fatima ta bayyana mata ita ta haifeka amma bata. A ina ka samo babbar mace haka?"


"Labari ne mai tsahon," inji Armad. "Gayamin duk abinda ta gaya maka dalla-dalla. Kada ka cire komai."


"Babu abinda ta gayamin," inji Zaikid. "Ta tafi da niyyar zata dawo amma bata dawo ba. Daga baya naji ance a hanya tayi gamo da masu bakaken idanu. Ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane ban sani ba. Amma dai har aka siyar damu a cinikin bayi ban ƙara ganinta ba."


Hakan ya dace da abinda Liman Umaru ya faɗa masa ya gani a jarida. Amma duk da bai bayyana masa inda Nusi take ba ko kuma dalilin da yasa Nusin take ganin zata iya ja da doron ƙasa ta biyu ita kaɗai. Sai dai kuma watakila ba ita kaɗai bace.


"Ita kaɗai ka gani? Babu kowa a tare da ita?"


Zaikid ya gyada kai alamun eh. Armad yaja dogon numfashi. Matsalar bai san inda zai samu Nusi ba. Fatan kawai da yake su haɗu a doron ƙasa ta biyu tunda dukkaninsu lissafin yadda zasu ceto Fatima suke yi. A ɗaya ɓangaren kuma har yanzu Zaikid ƙoƙarin dauje tambayar Armad yake yi.


"Har yanzu baka amsa tambayar da nayi maka ba," inji Armad. "Mai yasa mama ta tari Ashura?" 


Zaikid yaja dogon numfashi tare da ajiyar zuciya. A lokaci na farko idanunsa suka kaɗa. "Baza ka fuskanci dalilin Fatima na aikata abinda ta aikata ba har sai kasan yadda abin ya faro tun asali. Kaga dai Taidara mutun ne wanda ya daɗe da yawa a duniya. Zaka yi mamaki idan nace ya girme ni sosai da sosai. Ni kai na ban san adadin shekarunsa ba. Ni na haifi mahaifiyarka Fatima. Munyi aure da babarta Kulsum Bayajidda shekaru da dama kafin na gamu da Taidara. Iyalan gidan Wilbafos da suka rage a lokacin basa goyon bayan auren. A cewarsu idan na auri wadda ba ƴar asalin Wilbafos ba to na karya jinin Wilbafos. Akwai waɗanda suka so su kashe Kulsum kafin ayi auren amma basu samu nasara ba. 


"Bayan anyi auren rigima bata daina tashi ba. Dole na ɗauke Kulsum muka bar sansanin Wilbafos dake doron ƙasa ta shida a lokacin muka shiga duniya. Ana haifar Fatima na canja mata suna daga Fatima Wilbafos zuwa sunan mahaifiyarta wato Fatima Bayajidda. Na kai ajiyarta wajen abokina, marubucin sarki - Maikiro'Abbas. A daular maikironomada Fatima ta taso tare da ƴaƴan Abbas. Bari na nuna maka yadda abin ya kasance. Watakila idan ka ga komai da idonka zaka fuskanci dalilin Fatima na sadaukar da rayuwarta."


Zaikid ya zaro irin ayrid a jakar tsafinsa ya samar da faifan bidiyo. Tarihi ya fara gudana a gaban idon Armad. A yau zai ga yadda komai ya faro tun kafin a haifeshi.


***

Shekarar 644 Bayan Amri

***

Doron ƙasa na biyar

Sashin arewa

***


Runduna ce ta mutun dubu suke tafe akan dawakansu. Dukkansu suna sanye da farin sulke sun rufe ko'ina a jikinsu. Shugaban tafiyar yana gaba riƙe da wani sanda na ƙanƙara. A saman kansa akwai wani shinge na baƙin ruwa yana zagayawa. Idan baka lura ba sai kace sauran kiris ruwan ya zubo masa, amma a zahiri ba haka bane, tunda wannan mutumi ya kai matakin deba yake ɗauke da ruwan a saman kansa kuma har yanzu bai zubo ba.


Ba jimawa wanan tawaga suka iso ƙofar wani gari. Suka danna kai cikin garin. Wani abun mamaki shi ne masu gadin suna tsaye. Bakinsu a buɗe cike da mamaki da Wasu-wasi. Fuskarsu tana nuna tsananin kokwanto. Babu ciwo ko rauni a tattare dasu amma kuma babu tantama akan mutuwar su domin kuwa basa numfashi.


Tawagar ta wuce cikin garin. 


Suna wuce ƙofa suka tadda wata runduna akan dawakansu sun tsaya cak. Babu wanda yasan yaushe ko kuma tayaya amma da mutanen da dawakan babu wanda yake numfashi. Ga mamaki da Wasu-wasi akan fuskokinsu. Kana gani kasan basu zaci mutuwa ba. Wasu acikinsu sun zare makamansu suna niyyar kai sara. Wasu kuma suna ƙoƙarin zare makaman amma basu samu dama ba. Abu guda da dukkansu suke dashi shi ne mamaki da kokwanto akan fuskokinsu. Sun mutu suna cikin wasu-wasi da kokwanton meye ya kashe su. Koda sun farka a kabari baza su samu amsar tambayarsu ba. 


Shugaban tawagar ya ce, "kowa ya zare takobinsa. Ku zamo cikin shiri. Ko sauro ya wuce ku kashe."


Nan take suka zare makamansu suka danna cikin garin. Suna shiga suka fara bi gida-gida suna dubawa ko zasu ga wanda yayi wannan aiki. Tunda ƙaramin gari ne cikin ƴan awanni suka kammala zagaye shi. Basu samu wanda ya kawo harin ba amma kuma sun samu waɗanda aka kaiwa harin. Ba yaro ba babba, ba mace ba namiji, dukkan mutanen garin sun mutu. Fuskokinsu cike da mamaki da wasu-wasi, suna kokwanton yadda akai suka mutu. 


Sadaukan da suka zagaya cikin garin suka dawo suka suka bayyanawa shugaban tafiyar basu samu wani mai rai acikin garin ba. 


Shugaban nasu ya kai duka bishiyar dake kusa dashi cikin fushi. Babu abinda yake sai huci da kai-komo. Bayan kimanin awa guda ɗaya daga cikin sadaukan yayi ƙarfin hali ya matsa kusa dashi yace, "ya kamata mu koma gida, yarima. Koma su wane suka aikata wannan ta'addancin sun daɗe da guduwa."


Shugaban nasu wanda ya kira da yarima ya girgiza kai. "A'a, ina da yaƙinin koma waye yayi wannan aiki yana kusa. Ina jin yanayin izzar su. Akwai wani hijabi da yake tare ni gabarin su. Kuma tabbas bazan koma wajen sarki ba sai da kawunan su. Babu wani ɗan ta'adda da zai shigo mana iyaka sannan mu rabu dashi yayi yadda yaga dama. A matsayina na babban ɗan sarki, yarima mai jiran gado, sai naga bayan wannan ƴan ta'adda. Idan kuwa ba haka to nayi alkawari bazan sake sala ƙafa a fadar Maikironomada."


Koda jin wannan alwashi da shugabansu yaci sai kowa ya gyara tsaiwar sa. Sun san babu sauran zancen komawa gida indai ba yan-ta'addan aka kama ba.


Suka raba kansu mutum goma-goma sannan suka bazu cikin garin suka fara dubawa lungu da sako. A kwana biyu sai da suka bankada ko'ina acikin garin. Amma duk da haka basu samu kowa ba. Sun lissafa adadin mutanen da suka mutu wanda ya kama mutum dubu biyu da ɗari uku da goma sha daya. Kuma dukkan su babu ko ciwo a jikinsu. Sai dai kawai basa numfashi, sannan kuma ga mamaki da kokwanto a fuskokinsu. 


Da fari wannan tawaga sunyi tunanin bayan kwana ɗaya ko biyu wannan gawarwaki zasu fara canjawa amma hakan bata faru ba. Ko wacce gawa ka taba za kaji ta sanyi kalau kamar an saka ta acikin kankara, sannan kuma mamakin da yake jikin kowacce fuska bai canja ba. 


Yarima bai damu ba. Yasa aka kafa tanti. Da safiya suka yi farauta suka samu na kalace, sannan suka koma aiki. Sannu a hankali sai da yarima ya kwashe kwana uku cir a wannan waje ba tare da sunga wani mahaluki ba. A rana ta huɗu da maraice suna zaune a bakin wuta wasu mutum biyu suka shiga shingen yanayin izzar sa. Zumbur ya mike ya zare takobin sa. Sadaukan dake kewaye dashi suna ganin haka suka miƙe. 


Yarima ya bada umarni suka nufi inda ya ji tawowar mutanen. Suna zuwa ya rabawa kowa inda zai tsaya. Wasu akan bishiya, wasu acikin gidaje, wasu rami akai suka shiga suka rufe, wasu kuma a duhuwa. Duk suka ɓoye. Daga nesa idan ka hango wajen ba zaka ce akwai mutum ba. Bayan kimanin minti ashirin da sai ga wata budurwa nan sanye da doguwar riga ruwan ɗorawa tare da wani mutum sun tunkaro wajen. Suna tafe suna hira. Akwai takobi tsirara rataye a kafaɗar macen saɓanin namijin wanda babu makami a jikinsa. 


Har suka zo tsakiyar inda mutanen yarima suka ɓuya basu san halin da ake ciki ba. Kai har sai da yarima da kansa ya diro daka kan bishiyar da yake ɓoye ya sauka a gabansu sannan suka ankare. Sai dai kuma duk da bayyanar yarima bai sa sun tsaya ba. Wucewa kawai sukai kamar ma basu ganshi ba suka cigaba da hirar su. Watakila hakan zai iya nuna cewar tun daga nesa sun san da mutane a wajen kawai dai basu damu bane saboda wani dalili nasu. 


Yarima ya daka musu tsawa. "Ku, marasa kunya! Ku tsaya kuyi bayanin kan ku."


Mutanen guda biyu watakila kurame ne domin ko tsayawa ba suyi ba ballantana kayi tunanin zasu waiwayo. Yarima na ganin haka ya gane akwai shakiyanci aciki. Bai bawa rundunarsa dama su fito daga inda suke ɓoye ba, amma a lokacin ya zare takobi yayi kansu. "Ko ku tsaya ko kuma iyayenku su haifi wasu." 


Yana zuwa baiyi wata-wata ba ya kai musu sara. Kafin takobinsa ta ƙarasa takobi ta bayyana a hannun namijin. Ya juyo cikin kwarewa ya tare takobin yarima. Yarima ya ƙara kai masa sara ya kauce. Abin mamaki macen ko tsayawa batayi ba kuma har yanzu bata waiwayo ta kalle su ba. Ganin haka ya fusata yarima ya nuna ta da hannunsa na hagu. Faifan ruwan dake saman kansa yayi kanta gadan-gadan. Yana zuwa saman kanta ya fara kumbura, kan kace kwabo ya zama wata ƙatuwar ƙawanya wadda ta rufe budurwar. A ɗaya ɓangaren kuma yarima yaci gaba da kaiwa namijin sara da takobinsa.


Bayan kawanyar ta rufe budurwar sai wasu daga cikin mutanen yarima suka fara fitowa daga inda suke ɓoye ba tare da ya basu izni ba. Domin dai  a nasu ganin wannan faɗa an riga an kammala shi. Babu ko kokwanto yarima yayi nasara.


"Wannan itace Ƙawanyar Maliya. Hatta deba basa tsere mata. Duk izzar da mutum yake ji indai ya shiga cikinta to kuwa kwanansa ya kare. A duk faɗin garin Maikironomada babu wanda ya taɓa tsere mata. 


"Naji ance sarki Maikiro'Abbas da kansa ya yabi wannan ƙawanya."


"Nima naji. Kuma ku baka sani ba, ance akwai sirrin rubutu na marubutan farko acikinta. Tabbas wannan mace ko wace ita kwananta ya kare."


A yayinda wannan jarumai suke tattauna abinda suke tunanin zai faru, a lokacin wannan budurwa tasa ƙafa ta fice daga cikin ƙawanyar. Har yanzu tafiyar ta take ba tare da ta waiwayo ta kalle su ba, ballantana ma ta gane suna nan. 


Koda ganin haka sai wannan jarumai sukai kanta. Hatta ragowar da suke ɓoye fitowa sukai suka afka mata. Sai data bari sun kusa kaiwa gareta sannan ta zare takobinta ta kai sara kan iska. A lokacin jikin takobin ya koma ruwan ɗorawa, wani haske ruwan ɗorawa ya fita daga jikin takobin ya ratsa ta jikin wannan jarumai ya fice ta baya. Take dukkansu suka faɗi ƙasa a sume, babu sauran numfashi a jikinsu. 


Yarima wanda ke gefe suna fafatawa da namijin kawai tsayawa yayi baki a buɗe kamar an zare masa laka. Bai taba ganin fasahar takobi irin wannan ba a tsawon rayuwarsa. A lokacin ya fuskanci cewa macen tama fi namijin hatsari. Nan take ya zaro littafinsa na marubutan farko ya fito da wani ƙatoton mutum-mutumi na ƙarfe, da Al'yaya, da takobinsa ta ainihi. Ya damƙi takobin sannan a lokaci guda Al'yayan ya nutse acikin jikinsa. Shi kuwa mutum-mutumin kan namijin ruwan zafi yana fita daga bakinsa. Duk abinda ruwan ya taɓa sai kaga ya narke. Hayaki ya cika ko'ina. Kamar ana bashi umarni sai hayakin ya kewaye mutumin ya fara matse shi. Dukkan abubuwan nan sun faru ne kafin mutun-mutumin ya iso inda mutumin yake.


Sai dai kuma kash, kafin yarima ya isa wajen macen ya gano akwai gyara a lissafinsa, watakila namijin yafi macen sharri. A wani salo na girman kai da isa namijin yasa ɗan'yatsa ya daki mutum mutumin. Lokaci guda hayakin ya ɓace, mutun-mutumin ya koma toka. Ko da ganin haka sai yarima ya ci birki, tabbas yasan yin faɗa da wannan mutane zaiyi wahala ya samu nasara shi kaɗai, ko babu komai dukkansu sun kai matakin deba. Da sauri ya bude littafinsa ya rubuta sako gida sannan ya tsaya yana jira yaga mai zasu yi. Idan shi ne tarar masa zai sa ayi a gama dashi kafin agaji yazo. Kuma watakila haka zasu yi...


To amma kuma mai yasa namijin ya koma gefe ya nemi waje ya zauna? Ga dukkan alamu a yanzu baya niyar shiga faɗan. Sai dai kuma hakan zai iya canjawa idan ya ga yarima zaici nasara.  


Tsahon lokaci suna kewaya juna kafin yayi kukan kura ya afka mata. Ya kai mata sara ta ɓangaren dama. Kafin saran ya sauka, igiyar ruwa ta bayyana akan iska ta ɗaure ƙafafunta. 


Sai dai kuma kash, igiyar ruwan bata hanata kaucewa ba. Tana kaucewa kafin takobin ta dira ta zare tata takobin ta kai masa sara. Bashi da damar kaucewa tunda karfinsa ya riga yayi gaba ya rinjaye shi. Al'yayan daya shiga jikinsa ya fito yayi ƙoƙarin tare saran da hannayensa. Yaluwar takobin ta sare hannayen sannan ta tsarge shi gida biyu. 


Yarima yayi amfani da ƴar damar daya samu ya motsa gefe. Cikin sauri da kwarewa ya mirgina a ƙasa ya kawo mata sara ta baya, ba tare da ta juyo ba tasa takobinta ta kare. Takobinsu na haɗuwa yarima ya daki ƙasa da ƙafarsa, dai-dai inda macen take tsaye ya juye ya koma ruwa. Zakai tunanin macen zata faɗa ciki amma hakan bata faru ba. Kamar tasan mai zai faru tayi tsalle ta canja waje. Sai dai kuma wani abin mamaki a lokacin da tayi tsalle sai kawai hannunta ya shige ta cikin takobinta. Tana dira tayi sauri ta miƙa hannu domin ta riƙo takobin amma hannunta ya shige ciki. Ta miƙa hannun hagu amma shima ya shige. Duk yadda tayi domin ta ɗauki takobin abin ya gagara.


"Kinsan ba'a kama ruwa," yarima ya ce cikin ƙasaita. A muryarsa zaka ji yadda da kai. Watakila shi kansa a yanzu ya yadda yayi nasara. "Ina da Negrinki ta musamman. Duk ƙarfen dana taɓa zan iya maida shi ruwa ta yadda mai shi bazai iya riƙe shi ba. Kina ji kina gani amma baza ki iya taɓawa ba. A yanzu da kika rasa wannan takobi da kike taƙama da ita meye ya rage miki?"


Budurwa ta girgiza kai amma bata ce komai ba. Ta samar da wata takobin.


Yarima yayi dariyar mugunta. "Ko takobi nawa zaki haɗa sai sun ƙare. Muje zuwa."


Ya kai mata sara. Takubbansu na haɗuwa sai takobinta ta zame daga hannunta ta fadi ƙasa. Gashi dai takobin har yanzu ƙarfe ce amma kuma a banza; ba zata iya riƙe ta ba. 


To amma ba wannan kaɗai abin mamaki ba. A dai-dai wannan lokaci shi ma yarima ya kasa riƙe tasa takobin. A duk sanda yayi ƙoƙarin riƙe ta sai hannunsa ya shige ciki kamar ya damƙi ruwa. A takaice dai fasaharsa ta dawo kansa.


"Ƙarya ne," inji yarima. "Rufa-ido ki ke amfani dashi. Wannan ai fasaha ta ce, dan me zatai aiki akai na?"


"Rufa ido?" Budurwar ta girgiza kai, fuska a yamutse. "Babu wani rufa ido, idan zaka farka ka farka. Idan ba haka ba kuma ni bani da matsala na tura ka lahira kaje ka ƙaro ilimi."


A lokaci guda suka samar da wasu takubban sannan suka sake kaiwa juna sara. Takubbansu na haɗuwa hayakin Negrinki ya shiga jikin kowacce takobi. Nan take takubban suka narke suka faɗi ƙas. Hakan bai sa yarima ya karaya ba. Gashi dai yaga matar tana amfani da Negrinkinsa amma hakan azama ya ƙara masa. Ya samar da wata takobin ya afka mata. 


Yarima yana da littafin marubutan farko. Duk abinda yake so kawai rubuta sunansa yake sai ya bayyana. Idan yana don takobi sai ya rubuta takobi, sai takobi ta bayyana. Saboda haka bashi da matsala komai daɗewar da za'ai ana wannan faɗa. Yasan ko ba daɗe ko ba jima takubban abokiyar karawarsa zasu ƙare. Sai dai kuma abun da kamar wuya. Babu wanda yasan hanyar da budurwar take amfani da ita amma duk sanda ta ɗaga hannunta sama sai kaga sabuwar takobi ta bayyana akai. Tun yarima yana lissafi har ya daina.


A hankali a hankali ya samu nutsuwa takubban budurwar baza su ƙare ba. Ya kuma tabbatar yaƙi da takobi bazai bashi nasara ba. 


Ya yadda takobin yaja da baya ya daki iska. Igiyar ruwa ta fita daga hannunsa tayi kan budurwar. Kafin ta ƙarasa ta rabu zuwa igiya goma. Kowacce igiya ta juye izuwa siffar aljani tayi kan budurwar.


A nata ɓangaren budurwar ɗaga hannu tai sama, ta dunkule shi, sannan ta daki iska. Wani ƙatoton hannun wuta baka-kirin ya fita daga hannunta ya afkawa yarima gadan-gadan. Wuta da ruwa suka haɗu a tsakiya. Wuta na ƙoƙarin ƙone ruwa, ruwa yana ƙoƙarin kashe wuta. Idan wannan ya danno sai wannan ya danno. Haka suka ci gaba da fafatawa tsawon rabin sa'a babu wanda yayi nasara.


"Shikenan iyakacin abinda kake dashi?" Inji budurwar.


"Hmm... Ki fito da wani abun sai a nuna miki wata fasahar. Ko kina tunanin zaki min hargagin banza ne dan saboda wanki yana gefe?" Yana magana yana kallon namijin daya zauna a gefe yana kallonsu. 


Budurwar ta ɗan yamutsa fuska. "Akwai kuskure a maganar ka guda biyu: na farko, wannan ba wa na bane, baba na ne; na biyu, acikin fasahohi na har yanzu banyi amfani da kaso goma ba."


Babanta? Yarima ya ƙara mutumin. Shekarunsa baza su haura talatin zuwa talatin da biyar ba. Ita kuma budurwar aƙalla takai ashirin da biyar. Zai yi wuya ace mahaifinta ne. To ko waye bai shafe shi ba. Abinda Ya shafe shi ne mutumin zai iya kawo mata agaji a duk sanda yake buƙata. Yarima bai yadda cewa batai amfani da kaso goma na fasahar ta ba. To amma koda fasaha ɗaya ce ta rage mata wadda ba tayi amfani da ita ba zata iya yin nasara a kansa tunda yayi amfani da duk manyan fasahohin sa. 


"Bari na nuna maka wata fasahar," inji budurwar.


Ta zare wata sabuwar takobin daga jakar tsafinta. Wannan takobin fara ce saɓanin na baya ruwan ɗorawa. Ta girgiza ta inda wani haske ya fice daga jikin ƙarfen ya watsu ko'ina. Babu damar kaucewa hasken tunda ya gaurayu da hasken rana ya shiga ko'ina. Jikin yarima ya fara karkarwa. Ba sanyi yake ji ba, ba kuma zazzaɓi yake yi ba, amma kuma jikinsa rawa kawai yake yi. Izzarsa ta fara rawa tana neman tarwatsewa. Duk wani shirin tsafi da Kafin sihiri dake jikinsa ya fara narkewa. 


Nan take ya yanke shawara takobin dake hannunta ita take bashi matsala. Saboda haka da sauri yayi kanta da niyyar ya karya takobin. Amma kafin ya ƙarasa yaji kamar an zare masa laka. Ƙafafunsa sun kasa ɗaukansa. Dole ya faɗi ƙasa yana nishi. 


"Na tsinka zaren izzar ka," inji budurwar. "Baza ka ƙara amfani da izza ba. Bazan kashe ka ba saboda ina so ka kai min sako wajen wanda ya turo ka."


Ta zaro takarda daga cikin jakar tsafinta ta saka acikin aljihunsa sannan ta ɗora shi akan doki.


"Ka kaiwa wanda ya turo ka. Duk shawarar da kuka yanke ku dawo muna nan muna jira."


Yarima yayi dariyar baƙin ciki, ya buɗe baki a hankali ya ce, "Kina tunanin zan koma gida ne ba tare da na sare kan ki ba? Ki daina wannan tunanin. Idan kika ga na bar wajen nan to naci nasara a kan ki. Ban san irin sulkullen da kike amfani dashi ba, amma indai ina da ragowar numfashi to kuwa ni ne da nasara."


Budurwar tayi shiru tana kallonsa. Bayan ɗan lokaci kawai ta juya wajen namijin da tace babanta ne ta zauna suka ci gaba da hira. Yarima yana kan doki yana kallonsu. Tun yana hararar har ya gaji ya rufe ido. A hankali jikinsa yana ƙara sanyi har takai baya iya motsa gaɓɓansa balle yayi wani abu. 


***


A can daular maikironomada kuwa sarki ne ya kirawo babban taro na dukkan sarakunan dake ƙarƙashinsa. Fada ta cika makil. Duk wani wanda ya isa yana gurin. Idan kaga baka cikin wannan fada to kai ba kowa bane a ƙasar maikironomada.


Sarki Maikiro'Abbas yana zaune akan karagarsa. Wasu samari biyu suna tsaye a ɓangaren hagunsa, sai kuma wata mace dake tsaye a ɓangaren damansa. Armad na ganin macen ya gane mahaifiyarsa ce ba wata ba.  Akwai sarakuna huɗu sun bi layi a ɓangaren hagu, sai kuma salsa suna tsaye a ɓarin dama. Daga bayansu ƴan majalisa da manyan kwamandu ne. Kowa cikin shirin yaƙi yake, ɗauke da sulke da takubba a zare. 


Sarki yayi gyaran murya kowa yayi shiru. A lokacin Fatima ta ɗaga littafin dake hannunta sama kowa ya gani. Littafin marubutan farko ne amma kuma da hoton yarima mai jiran gado a jiki. Ta buɗe shafin farko inda suka ga ya juye daga fari zuwa baƙi. Ta buɗe shafi na biyu dana uku wanda duk sun koma bakake. 


A daular maikironomada manyan sadaukai suna da littafin marubutan farko guda biyu. Ɗaya Hassan, ɗaya Hussaini. Idan sadauki zai fita yaƙi suka ya bar Hussainin a gida ya fita da Hassan ɗin. Duk abinda ya samu sadaukin a filin daga za'a gani acikin Hussainin.


"Wannan shi ne Hussainin da yarima mai jiran gado ya bari," inji Fatima. "Maƙiya sun kama shi sun yi masa mummunan sihiri."


Nan take aka fara kus-kus acikin fadar. Kowa yana mamakin yadda abin ya faru. Har ace akwai wani mahaluki da zai iya yin nasara akan yarima?


"Waye zai je ya gama da wannan maƙiya, ni kuma nayi masa babbar kyauta?" Inji sarki Maikiro'Abbas.


Nan take samari biyun dake tsaye a gefen sarki da Fatima suka amsa a tare. Kowa yana cewa shi zai je ya kawo kan su.


Jin haka dukkan fadar ta ɗauka a lokaci guda.


"Zamu sadaukar da ran mu domin ka, ya kai sarki mai adalci, kuma bama buƙatar kyauta."


"Zamu sadaukar da ran mu domin ka, ya kai sarki mai adalci, kuma bama buƙatar kyauta."


Koda jin haka sai sarki Abbas yayi murmushi sannan ya miƙe ya koma gida. 


Fatima ta taka gurin samarin biyu ta ce, "kamata yayi ku zauna a gida ku kula da gari. Sarki yana cikin radadin rashin yarima mai jiran gado. A matsayin na ƴaƴan sarki bana so kuma ku tafi ku ɓata."


Ɗaya daga cikin samarin bai bata amsa ba kawai juyawa yayi ya fice daga fadar. Shi kuwa ɗayan kawai murmushi yayi. "Haba, Fatima, na gane dabarar ki. Wato mu rabu dake ki dawo da yaya gida sarki ya ce ke kaɗai kike abinda ya kamata ko? Haha... ki canja tunani. Duk inda yarima mai jiran gado yake to mu zamu fara nemo shi. Idan baza ki damu ba mai zai hana ke ki zauna a gida?"


Yana rufe baki ya juya ya ɓace. 


Wasu daga cikin manyan jaruman dake fadar suma shiri sukai suka fita neman yarima. Cikin kankanin lokaci sama da mutun ɗari daga cikin mafi girman izza a garin sun fita. Burinsu su dawo da yarima mai jiran gado gida sannan kuma su kama wanda suka aikata wannan ta'asa.


Washegari da safe sarki Maikiro'Abbas ya fito zaman fada. Yana zuwa ya iske Fatima tana tsaye a gefen karagarsa. Ga jama'ar gari masu ƙara sun hallara. Ga hakimai da alkalai duk sun zo domin yin hukunci. Jama'ar dake wajen sunyi mamakin ganin Fatima domin kuwa ita ce ta farko da suke ganin zata fara fita neman yarima. Musamman duba ga irin rade-radin da ake yi na cewa ita yarima zai aura.


Sarki ya zauna aka fara sauraran ƙara. Bayan an kammala ana ƙoƙarin tashi daga zaman fadar, sarki ya tambayi labarin wanda suka fita neman ɗansa. Fatima ta bayyana masa babu labari. 


Washegari sarki ya ƙara fitowa fada ya tambayi labari. Fatima ta bayyana masa babu labari.


A rana ta huɗu ana tsaka da zaman fada mai shela ya garzayo fadar da gudu. Yana zuwa ya bayyana musu cewa yarima Umaru yana ƙofar gari rai a hannun ALLAH. 


Fatima ta ɓace ta bayyana a ƙofar gari. Tana zuwa ta shimfida mayafin tsafi akan iska ta ɗora yarima Umaru akai sannan ta dawo dashi gaban sarki. 


Yarima Umaru baya iya ko magana. Littafinsa yayi baƙi. Da kyar ya zaro wasika daga aljihunsa ya miƙawa Fatima.


Fatima ta karba ta karanta.

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...