Dul'Ururu ya tafa hannayen sa, lamarin da yasa saman kan sa ya fara walwali da ɗigo-ɗigon haske, wanda ya juye izuwa dunƙulen baƙi, sannan ya koma ƙawanya. Idan ka kalli ƙawanyar zaka ga rami mai zurfin gaske ɗauke da baƙin duhu marar misaltuwa. Wannan rami shi ake kira da Taskar Ruhi.
Taskar Ruhi wata hanya ce da manyan ma'abota izza a gidan Ururu suke amfani da ita wajen tattara izzar su da fasahar su guri guda. Zaka iya cewa duk wani Ururu da sunan sa yakai yana da wannan Taska. Kowa shi kaɗai yasan abinda yake adanawa acikin tasa.
Dul'Ururu ya miƙa hannu cikin Taskar sa ya zaro wani ƙaton littafi daga ciki. Bangon littafin yana ɗauke da zane-zane na kwalliya ƴan ƙananu, da kuma rubutu dara-dara a dai-dai tsakiyar sa an rubuta 'RIJISTA'.
Kai tsaye ya buɗe shafi na ɗari da sab'in da huɗu. A jiki akwai ƙatoton hoton Nostaljiya. A dai-dai ƙasan hoton akwai koriyar tauraruwa mai haske tana walwali. Daga ƙasa kuma akwai rubuce-rubuce da yaren Aldurish kamar haka:
*
Nostaljiya Nara
Martaba: haifaffiyar 'ƴa'
Laifi: kawo hargitsi a cinikin bayi a shekarar 1853, gudummawa wajen kawo cikas a gasar jinzidal, cin mutuncin sarakunan jinzidal, auren iyalin gidan wilbafos da kuma rashin girmama manya. Wannan laifuka sun ɓata miki suna da yawa.
Suna (reputation): -880
*
Dul'Ururu yaja dogon numfashi gami da girgiza kai, ya ce, "Nostaljiya ƴar gidan Nara, kin aikata laifuka da dama, amma lokacin Kamfen lokaci ne na yafiya. Faɗi ra'ayin ki naji, zaki karɓi gaskiya ki goyi bayan kamfen, ko kuwa zaki bijire ki faɗa ɓangaren taɓaɓɓu?"
Nostaljiya ta ɗaga kafaɗa, ta ɗanyi murmushi. "Nima suna na ya shiga Rijista kenan? Ji nake kawai bayi da wanda suka mutu kuke sakawa aciki." Inji Nostaljiya.
Dul'Ururu ya girgiza kai, ya ce, "A'a, ko kaɗan. Ai ita Rijista anyi tane domin adana duk wani abu da zaije yazo a ƙasashen ƙasa. Manya a sama sun san cewa mutanen ƙasa basa son zaman lafiya, idan babu Rijistar da za'a ajiye duk abinda suke aikatawa zasu ringa kaucewa tafarki. Kinga wannan tauraruwar," ya nuna koriyar tauraruwar nan dake ƙasan hoton ta, "idan tayi kore to mutun 'ɗa' ne haifaffe ba 'bawa' ba. Idan kika ga tayi baƙi to 'bawa' ne. Idan kika ga tayi ruwan toka to mutun ya mutu. Duk sanda baƙar tauraruwa ta koma ruwan toka to mun san bawa ya mutu. Kuma dole mu ɗauki mataki muga meye ya kashe wannan bawan. Abin zai baki mamaki, amma munfi kula da bayi akan ƴaƴa. Idan ɗa ya mutu bama bibiya indai ba ƙara aka kawo ba, amma duk wani bawa daya mutu alhakin mu ne, kuma mu zamu bibiyi abin. Badan komai ba sabida jinzidal tamu ce, mu zamu kula da ita."
"Ah.. lallai akwai tausayi a tsarin nan naku." Inji Nostaljiya tana zumɓuro baki.
Dul'Ururu ya haɗe rai, sannan cikin kakkausar murya ya ce, "meye amsar ki?"
"Kai ma kasan ƙarairayin ka baza su taɓa shiga ta ba, hanya ɗaya kaɗai da zan yadda dakai shi ne kayi min DOLE." Inji Nostaljiya.
Nan take Dul'Ururu ya zaro al'ƙalami daga aljihun sa ya kansile sunan ta. Sannan ya rubuta wasu ɗigonguna a ƙasa. Bayan ƴan daƙiƙu sai shafin ya fara haske, tauraruwar ta canja daga koriya ta dawo fara, kuɗi ya bayyana akan sunan Nostaljiya.
*
Nostaljiya Nara
Martaba: Mai laifi
Kuɗi (Bounty) : ayrid miliyan ɗari huɗu da goma sha uku - 413,000,000 mil
NB: da rai ko ba rai.
*
"Kai..."
"Kai.. Ka.. Kai... Ka.. Kai..."
Baki a wangame cikin tsananin mamaki suka ƙurawa Rijistar ido. Dukkanin kwamandun babu wanda ya taɓa tunanin tashin farko zai samu wannan kuɗi haka.
Suwainah tai tsalle ta dira a gefen Dul'Ururu. "Kawu, miliyan ɗari huɗu baiyi yawa ba? Ka ganta fa."
"Kada ki raina ta. Sharrin ta yana da yawa. Musamman duba ga yanayin fasahar ta da kuma inda take aiki." Inji Dul'Ururu.
Kafin ya rufe baki ya hangi wasu mutane biyu sun nufo inda suke suna gudu akan iska. Suna matsowa Dul'Ururu ya yamutse fuska, badan komai ba sabida ya san su sarai. Wannan mutane dai suna da ban mamaki: fuskokin su a nutse suke (matuƙar nutsuwa), tufafin su farare babu ko ɗison datti, gashin kan su baƙi-ƙirin kamar duhun dokar daji; babu alamun tafiya a tattare dasu ko kaɗan. Hakan zai ƙara baka mamaki idan aka gaya maka daga filin yaƙi suke, domin kuwa ba wasu bane illa Haruta da Maruta.
Basu sauka ko'ina ba sai a kusa da Dul'Ururu. Suwainah da Ibarahm Nil suka ƙaraso suka miƙa gaisuwa.
Haruta ya dubi Dul'Ururu da littafin dake hannun sa cikin mamaki ya ce, "Lokacin yayi kenan?"
Dul'Ururu ya gyaɗa kai. "Idan baza su karɓi gaskiya ba zan ɗaga kuɗin su a kasuwa. Na gaji da jira. Dukkan su su zama nama kawai a huta. Wai me yasa kuka baro filin yaƙin? Ƴan'tawayen sun karɓi gaskiya ne?"
Haruta ya girgiza kai. "A'a, sanda muka taho yaƙin ya cake a kunnen doki tsakanin mutun-mutumin Armad Wilbafos da mutun-mutumin Deniz Iluru."
Maruta ya ce, "mutun-mutumin Armad ɗin nan ba laifi. Yadda yake motsi, da yadda yake magana, da yadda yake tunani... gashi dai bashi da ruhi amma... ba laifi. Ashe akwai masu ɗan lissafi a wannan ƙasashen."
A wannan lokaci Ibraham Nil ya saka baki a zancen. "Da kukai zancen Armad kun tunamin wani abu. Kuɗin da aka saka masa ina ganin kamar yayi masa yawa, ko?"
Dul'Ururu ya harare shi. "Kana min baƙin ciki ne, ko? Baƙin cikin kuɗin da zan karɓa idan na kama shi. Kuma ai ba shi kaɗai bane, kuɗin Bihanzin dana Ikenga suma da yawa ai, mai yasa na Armad kaɗai kuke zance ne. Kuma koma meye ai mai martaba ya riga ya saka hannu akai. Ido na idon Armad ya zama nama. Kada ma wani acikin ku yayi tunanin kewayewa yayi min shisshigi, ko ka kama sai ka sakar min abi na. Har na riga nayi lissafin duk abubuwan da zan siya da kuɗin."
"Gaskiya kawu kuɗin sunyi maka yawa kai kaɗai. Zan raka ka, kaga sai ka bani kaso ashirin cikin ɗari." Inji Suwainah.
Dul'Ururu ya juyo a fusace. "Ki daina wannan zance. Ko kin biyo ni baza ki samu ko sisi ba."
Haruta da Maruta suka fara guna-guni akan yadda son kuɗi yayi wa Dul'Ururu yawa.
"Nidai kawai buri na a bani gawar sa nayi bincike akai. Akwai sirri ka acikin miyurar sa da har yanzu ban gama ganowa ba." Inji Ibraham Nil.
A ɗaya ɓangaren kuma Nostaljiya na tsaye ta buɗe tana mamaki. Banda yawan kuɗin da aka saka mata babban abinda yafi ƙona mata rai shi ne yadda suke maganar Armad kamar wani Ƙassai. Wai masu baƙaƙen idanuwan nan mai suke ji a kan su ne?
"Naji na bar maka Armad amma dole ka haƙura da sauran." Inji Haruta. Ya juya ya kalli ɗan'uwan sa Maruta yayi masa inkiya zuwa Nostaljiya. Su biyun suka gƴaɗa kai a lokaci guda suna dariyar mugunta. Nama ya samu. "Bari mu fara da wannan."
Tun kan ya rufe baki Inara, Lammarudu, Babara, Cokali, Iliyasisi, Nazara da Nusi suka kewaye Nostaljiya. "Idan kana so ka taɓa ta sai dai kabi ta kan mu."
Haruta ya tsaya ya ɗanyi shiru yana kallon su, kafin daga bisani ya sosa gashin kan sa tare da girgiza kai. "Idan ta tsaya cak batai gardama ba zan kama ta a hankali ba tare da naji mata ciwo ba. Amma idan tayi gardama abinda ke cikin ta ma bazai sha ba."
Dul'Ururu yai sauri ya buɗo hoton Babara a shafi na saba'in da takwas acikin Rijistar, ya ce, "kada ka damu Haruta, kowanne cikin su an saka masa kuɗi. Bari na ƙaddamar da su kawai, kaga ka samu kuɗin siyo kifaye ka ƙara a tafkin gidan ka."
Babara yai ƙaraji a fusace, ya ɗaga sandar tsafin sa sama. "Kada ku gaya mana maganar banza. Kuna ganin cin ta, ko? Muje zuwa."
Comments
Post a Comment