A can wannan daji kuwa duwatsu ne iyakacin hangen ɗan-adam, inda daga cikinsu mutane sanye da kayan yaƙi suke ta ƙara ɓulɓulowa su na nufo wajan da su Zahra suke tsaye cirko-cirko tun bayan jin wannan murya.
Kafin kace meye wannan mutane da dama sun kewaye su ta kowanne ɓari.
Ana cikin haka wasu manya-manyan mutane waɗanda su kaɗai ne fuskarsu bata naɗɗaɗe da rawani suka fito fili daga bayan wasu jajayen duwatsu.
Su na fitowa, kai tsaye suka fara kusantar inda su Hasanu suke tsaye.
Dukkaninsu manya-manyan halittu ne tayadda in baka kula ba sosai ba, sai kace samudawa ne.
Na tsakiyar tasu ya ɗan ɗara ragowar tsayi yana sanye kuma da jan rawani wanda kamar kamar rawanin sauran mutanen dake kewaye da wajan ba, bai rufe masa fuska ba.
Yana ɗauke da wani ƙatoton farin gatari.
Idan kuma ka duba zakaga cewa duk da duhun wajen bai hana idanunsa walƙiya ba, wanda idan ka ƙura ido zaka fahimci cewa acikin idon nasa akwai waɗansu abubuwa guda biyu acikin kowanne ido.
Idan ka ƙara ƙura ido zaka fahimci cewa waɗannan abubuwa ba komai ba ne ba illa hoto na taurari waɗanda suka maye gurbin baƙin kowanne idonsa, biyu a kowanne ɓangare wanda ya bashi taurari guda huɗu kenan idan aka tara.
Su kuma mutun biyun dake gefensa idanunsu kamar na kowa ne, amma kuma a goshinsu akwai tambari na Miyura, na ɓangaren daman yana da taurari uku irin na cikin idanun na tsakiyar, su na motsi su na kewaya wannan Miyura dake goshinsa.
Na ɓangaren hagun kuma yana da taurari guda biyu, shima kuma su na kewaya Miyurar dake goshinsa.
Babban nasu mai taurarin a ido ya fara magana, ''Hasanu, a bayyane yake a fili babu yadda zaku iya fita daga wannan waje inba mu muka barku.
''Da farko da muka gano mutun uku kacal na tafiya da Ayrid mai babban mataki, munyi niyyar kawai mu kashesu mu kwace.
''To amma bayanda na gano kaine aciki, sai na canja shawara cewa idan kuka bamu wannan Ayrid, da kuma duk abinda kuka mallaka, to zan barka ka wuce da ranka.
''Duk da kuwa mataimaka na guda biyu basu goyin bayan hakan ba, amma badan komai saboda tuna baya, naga ya kamata kai kaɗai dai na bari ka wuce da ranka.'' Ya ƙarasa maganarsa yana mai waiwayowa yana kallon mutun biyun dake bayansa furkarsa cike da dariyar ƙeta.
Fuskar Hasanu cike da fushi ya dubi wannan jibgegen mutum ya fara magana cikin izgili, ''hmmm Ƙiliƙ, ai ban san ka mallaki taurari huɗu ba, dana nemeka nayi maka murna.''
***
Ƙarin bayanin akan kalmar Ótaki
Kalmar Miyura daga yaren Alderiya take, kuma tana nufin tambari a gaban goshi, kamar Irin wanda Armad yake dashi.
To akwai wani abu dake faruwa a wannan zamani wanda yake da ban al'ajabi kwarai da gaske. Wannan kuwa ba wani abu bane illa haihuwar kowanne mutun da ake da tambarin Miyura a goshinsu.
Kowacce ƙabila tana da irin tambarinta, wanda kuma su kaɗai suke dashi. Harma ana amfani dashi wajen gane asalin ƴan kowacce ƙabila a yayin haihuwa.
Sai dai abinda ke faruwa shi ne, kwana bakwai dai-dai da dai-dai bayan haihuwa, babu ragi babu ƙari, wannan tambarin yake goge wa da kansa, tamkar ba'a taɓa yinsa ba. Sannan kuma bazai ƙara dawowa goshin mutun ba, har sai mutun yakai wani babban matsayi na Izza da ake cewa 'Ótaki' wanda yake nuni da Izza mai mataki na Shekaru ɗari biyar, sannan tambarin zai ringa bayyana a gaban goshinsa, kaɗai lokacin da zaiyi amfani da Izzar data kai ɗari biyar!
Kaɗan daga cikin dalilan da yasa Armad yake ɗaura jan kyalle a gaban goshinsa shi ne, domin ya rufe tambarin Miyurar dake goshin nasa.
Na farko dai, duk wanda ya gani zai iya gane cewa Armad ɗan ƙabilar Wilbafos ne, (idan baku manta ba, wannan mai tsaron ƙofar, Han'Diyuza, mai aljanin wuta, yana ganin Miyurar Armad yake cewa daga ƙabilar Wilbafos yake!).
Ƙabilar Wilbafos dai sunan ta ma ba'a san faɗa. Saboda ƙabila ce da suka taɓa fito na fito da Ururu, wanda a dalilin haka babu wanda yake son yai alaƙa dasu, saboda tsoron Ururu da ake ji. Kai hasalima, har kyauta mutun zai iya samu idan ya kama Armad ya miƙawa Ururu, a matsayin wanda ya fito daga zuri'ar Wilbafos.
Sannan kuma na biyu, kamar yadda na faɗa, ana haifar mutun tambarin yake ɗaukewa, to amma bisa ƙololuwar mamaki irin wanda ba'a taɓa gani ba, tunda aka haifi Armad Miyurar sa bata taɓa ɓacewa ba.
Ana jira aga bayan kwana bakwai ta ɗauke, amma taƙi, har akai shekara, har aka kai shekaru goma, har izuwa wannan rana, bata taɓa ɓacewa ba, koda sau ɗaya!!!
Saboda hakan nema, tun kafin magana ta fara yaɗuwa, mahaifiyarsa ta samu jan kyalle ta rufe masa goshinsa tun yana jariri, wanda kuma dashi ya taso, kuma har a wannan lokaci yake ɗaurashi domin rufe Miyurar. Saboda abu ne wanda zai iya rikita duniya baki ɗaya, idan mutane suka ji wannan labari. Domin kamar a wannan zamani namu ne ace an samu Jaki mai ƙaho ko kuma mutun mai tashi sama ko kuma ace an tsinci raƙumi acikin kuratandu!!
***
Ga dukkan alamu ɗan wannan abu da Hasanu ya faɗa yayi matuƙar ɓatawa Ƙilik rai, kamar wanda yake tuna wani abu a baya tsakaninsa da Hasanu, nan take yai gunji gami da dariyar mugunta yana cewa, ''Yau dai girman kanka lallai yazo ƙarshe.'' Ya nuna jaruman dake bayansa da hannu yana cewa, ''Ina da janar mai taurari uku, ina da mai taurari biyu, sannan kuma ina da sadaukai dubu biyar waɗanda kawai kalmata suke jira su afka muku ba tare da wani tsoro ba.
''Ka gayamin mai kake taƙama dashi, waye zai iya tseratar dakai yau daga hannuna.
''Kai na canja shawara ta ma, yaune ranar shan numfashinka na ƙarshe, Hasanu.'' yai gunji mai razanarwa, lamarinda yasa wata iska mai ƙarfi kaɗawa. Wadda ita kaɗai zata iya karayar da zuciyar abokin karawarsa.
Nan take ya ɗaga hannu sama, ya kuma bada umarnin su afaka musu, lamarinda yasa gabaki ɗayan waɗannan mutane dubu biyar, da kuma su ukun suka afkawa su Hasanu.
To amma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya umarci Kiru da Zahra dasu koma dai-dai bayansa su tsaya, yana mai cewa, ''ku lura sosai, ku zira ido, kuga dukkan abinda zanyi, domin ba lallai ba ne ba, ku ƙara samun dama a rayuwarku ba daza kuga irin abinda zai faru yanzu ba!''
A wannan lokaci da wannan babban nasu ya ɗaga hannunsa sama, dukkansu sukai kukan kura inda suka afkawa mutun uku kacal, wato Hasanu da Kiru da kuma Zahra.
Hasanun wanda tuni ya umarci ƙannan nasa guda biyu dasu koma bayansa, ya ɗaga ƙafarsa ta dama inda yayi taku ɗaya gaba.
Taku ne guda ɗaya kacal, amma a dalilinsa abubuwan da suka faru suna da yawa ta yadda duk wanda ya samu damar ganin abubuwan da suka faru kuma ya tsira da ransa to lallai harya mutu bazai manta da abinda ya gani ba.
A ƙunshe acikin wannan takun, taurari ɗai-ɗai ɗai-ɗai har guda biyar suka bayyana acikin idanun Hasanu, uku a dama, biyu a hagu inda suka maye gurbin baƙin dake cikin idon nasa.
Acikin takun wata iska mai tsananin ƙarfin gaske ta fara fita daga jikinsa.
Kan kace meye wannan tuni wannan iska ta game duk wani abu dake wannan kewayen dutsen.
Acikin wannan takun waɗansu mutun-mutumi guda biyu waɗanda gabaki ɗaya jikinsu anyi shi ne da wanna iska suka bayyana.
Ɗaya a damansa ɗaya kuma a hagunsa.
Bayyanarsu keda wuya wani yanayi mai ɗauke da sanyin gaske, tamkar a tsakiyar hunturu, ya cika wajen baki ɗaya, tamkar ƙankara zata fara sauka.
Fara kaɗawar wannan iska keda wuya dukkan waɗannan mayaƙa dubu biyar dake doso su Hasanu suka tsaya cak a inda suke.
Cikin wani al'amari mai kama da almara kawai wannan iska ta daki jikin waɗannan Jarumai dubu biyar, lamarinda yasa akan idon kowa, wani abu mai kama da ƙanƙara ya fara fitowa daga jikin fatarsu. Sai dai kawai banbancin wannan abu da ƙanƙara shi ne launinsa ruwan toka ne, maimakon fari da aka san ƙanƙara dashi. Amma kuma duk da haka tsananin sanyi ne irin mai ratsa ruhin nan yake shigarsu, wanda tuni yasa suka faɗi ƙasa sumammu.
Duk wanda ya rayu a wannan zamani, yasan sunan wannan iska mai ɗauke da ƙanƙara ruwan toka, wadda ita ake cewa, Sanyin babban sihiri!! Wanda kuma idan mutun yakai matsayin Ótaki yake mallaka.
Babu waɗanda suka rage illa waɗannan manya nasu su uku wanda ke gabda isa kusa dasu Hasanu.
Babu shiri suka ci birki cikin tsananin zafin nama, babban nasu wanda yayi magana a baya wanda kuma ga dukkan alamu yasan Hasanu a baya, ya buɗe baki cikin firgici, jikinsa na rawa, yana cewa, ''kai... yaushe..... ka kai matsayin Ótaki, Hasanu....yaushe??!?''
Bai gama rufe bakinsa ba, mutun biyun dake bayansa suka zube a ƙas, inda wanda keda taurari biyu ya zarce kasa a sume, fatarsa a rufe da wannan ƙanƙara ruwan toka, shi kuma mai taurari uku ya fara faɗuwa bisa gwiwarsa fuska cike da mamaki, kafin daga bisani shima yaje ƙas.
Waɗannan mutun-mutumi guda biyu na iska, dake tsaye a gefen Hasanu sukai ihu mara sauti, inda kafin Ƙilik yayi wani abu tuni sun cimmasa, inda suka ɗaga hannu kawai saiga wani dogon zare shima na iska, ya bayyana a hannunsu.
Kan kace meye wannan sun gama naɗɗaɗe arnan daji Ƙilik dashi, sannan cikin tsananin sauri suka fito da wata jaka irin ta tsafi suka cillashi aciki.
Kai ko damar yin ihu bai samu ba, kafin sun cillashi cikin jakar, sannan kuma daga bisani suka dawo gefen Hasanu suka tsaya.
Dukkan abinda ya faru zai ɗau lokaci a wajen bayani, amma a zahiri ya faru ne cikin ƙiftawar ido da bismillah.
A dai-dai lokacin mamakin dasu Nostalgiya da Kiru suke ciki yakai matuƙa, inda tuni ma suka manta da abinda ya gaya musu na cewa su lura zai koya musu wani sirri daga cikin sirrikan Sihri.
''Ku lura sosai, yanzu ne zan nuna muku abinda na faɗa!'' Muryar Hasanu ta cika kunnuwansu da wani ƙarfi duk da cewa maganar a hankali yayi ta.
Amma nan take suka dawo hayyacinsu suka kuma ƙura masa ido su na kallon wannan sirri da za'a saukar musu.
Dukda cewa dukkaninsu sun san irin yadda ake ji da ƙarfin na Hasanu, bama a iya Sisiya ba, har iyakacin dukkanin Burja.
Ko ba komai shi ne kwamanda na biyar a dukkanin jerin kwamandun ƙungiyar Burja.
Amma duk da haka abinda suka gani yanzu ya firgita su saboda wannan bashi bane karo na farko ba da suka taɓa ganin faɗa da Ótakí ba, amma banbancin Izzar da suka ji a jikinsu yanzu tsakanin wancan da wannan tamkar banbancin sama da ƙasa ne!
Hasanu ya ja numfashi matsakaici, kamar wanda yake zuƙar wani abu acikin sanyin iskar dake kewaye dasu, nan take idanunsa suka canja inda suka cika da tsananin imani da nutsuwa.
Duk da kasancewar har a wannan lokaci gabansa yake fuskanta, wato tun bayan wannan taku guda ɗaya da yayi na farko, amma duk da haka saida suka ji ajinkinsu yanayin yadda fuskarsa ta canja.
Wanda hakan yasa nan take suka fuskanci tsananin muhimmancin abinda zai gaya musu wanda yasa suka ƙara nutsuwa da tara hankalinsu.
Har a lokacin da Hasanu ya buɗe baki ya fara magana bai waiwayo ya kallesu ba, sannan kuma bai ɗaga ƙafarsa daga inda ya ɗora ta ba tun farko sannan kuma dukkanin abubuwan da suka faru, waɗannan mutun-mutumi guda biyu dake tsaye a gefen Hasanu kansu a rusune yake tamkar waɗanda dukkan alamarinsu ya ta'allaƙa da kareshi komai wuya komai tsanani, ko kuma wasu bayi waɗanda suka kai maƙura wajen jin daɗi cikin bautar abin bautarsu, sannan kuma da wannan yanayi na sanyin-sihiri da yake kaɗawa acikin wannan jar iska, komai yana nan a inda yake bai motsa ba, bai kuma canja ba kamar yadda shima Hasanun bai motsa ba.
''Kuyi sani cewa duk wani Sihiri dake faɗin duniyar kafin ya zama kai ka zama shi, sai ka sadaukar da wani abu daga cikin sassan jikinka wanda yake motsi." yaci gaba dai musu bayani, muryarsa a nutse.
"Wannan abu da zaka sadaukar ya zama wajibi ya zamanto kana da dukkan iko na sarrafa shi.
''Saboda wannan waje shi ne zai zama ma'ajiyar dukkan fasahohinka.
''Kuma yadda zaka iya sarrafa wannan ɓari na jikinka haka zaka iya sarrafa dukkanin sihirinka, yadda zai zamo wata hanya da zaka rinƙa sarrafa sihiri irin yadda kaga dama.
''Yanzu ku ɗauki misali dani, dukkanin sihiri na yana da alaƙa da ƙafata, wato dai kamar wannan jar iska da kuke gani.
''Ku kula kugani!'' Yana gama faɗar haka sai ya ɗaga ƙafarsa ta dama wadda ya riga ya taka da ita tunda farko, ya dawo da ita baya.
Faruwar hakan keda wuya, kamar a mafarki dukkan wannan jar Iska dake ta kaɗawa ta ɓace ɓat, sannan babu alamun waɗannan mutun-mutumi guda biyu babu alamunsu, sannan kuma babu wannan sanyi na babban sihiri dake kaɗawa, komai ya ɗauke cak tamkar ba'a taɓa samar dashi ba.
Babu abinda ya rage banda, waɗannan Arnan daji dake kwance fululu a ƙasa a sume.
Hasanu yaja numfashi sannan ya juya yai duba izuwa Zahra da Kiru waɗanda bakinsu yake a buɗe cike da mamaki, ya ce, ''wannan shi ne mataki na gaba da zaku shiga yayinda kuka gama kwarewa akan wannan mataki da kuke kai.
''A yanzu kawai abinda nakeso shi ne ku buga tambarin dukkan abinda kuka gani da abinda kuka ji a wannan rana acikin ranku, domin cikin shekaru masu zuwa zaku kai matakin da zaku fara koyar amfani da irin wannan sihiri, a lokacin zaku ga amfanin abinda na nuna muku yanzu.''
Yana gama faɗar haka ya ƙara ɗaukan taku ɗaya wanda ya isar dashi gabansu.
Yana isa cikin mamaki sai suka ga wata iska mai jan launi ta bayyana ta kuma zagaye su, inda kafin su buɗe baki suyi magana tuni wannan iska ta sure su tayi sama dasu, inda suka ɓace cikin samaniya suka kuma nausa cikin sauri izuwa garin Sisiya.
Su na cikin tafiya acikin wannan iska Kiru ya kasa daurewa, inda ya haɗiyi yawu sannan idanunsa cike da ƙara ganin girman Hasanu ya tambaya, ''wato idan na fahimta, aljaninka na jar iska ne, sannan kuma sihirinka a ƙunshe yake acikin takun ƙafafunka. Tayadda idan kai niyya kawai ɗaga ƙafa kake da buƙata kawai kayi, domin ka bayyanar da aljaninka na jar iska?''
Hasanu yai ɗan murmushi gami da kyaɗa kai alamun yadda da abinda Kiru ya faɗa.
Kiru ya ƙara jan numfashi ga dukkan alamu kuma bai gama tambayoyinsa ba, gami da cewa, ''Shin Yanzu matakai nawa ne suka rage min na Izza kafin nakai wannan mataki?''
Yayi tambayar ne fuskarsa da idanunsa cike da buri da kafiya na ranar da shima zata zo ya kira kansa ma'abocin irin wannan Izza.
Hasanu ya ɗau lokaci mai tsaho su na tafiya ba tare ya bashi amsa ba, inda har ya fara tunanin ko bazai amsa masa ba. Amma daga bisani Hasanu ya ɗaga kai ya kalleshi gami da girgiza masa kai yana mai cewa, ''kada ka zamo mai hanzari acikin al'amarin Izza da sihiri.
''Komai lokaci ne, kuma hasali ma a yanzu mafi muhimmancin abu a gareku shi ne ku ƙure kuma ku kai matuƙa akan matakan da kuke.''
Yana magana yana dubansu biyun kamar dukansu su ne sukai tambayar, idanunsa cike da ma'ana.
''Kunga saura sati uku kawai a buɗe *Non-toch-teka* dake birnin Maikironomada, kuma tuni ƙungiyarmu ta Burja, ta biya farashi mai tsadar gaske wajen kama muku babbar ƙofa, kunga wannan shi ne lokaci mafi dacewa da zaku tabbatar da horonku.

Comments
Post a Comment