A dai-dai wannan lokaci tuni wannan ƙawanyar wuta takai kimanin faɗin ƙafa maitan a kowanne ɓangare, dama da hauni, sama da ƙasa, Armad kuma na tsakiya babu ta inda zai iya guje mata.
Gashi kuma a dai-dai lokacin ƙawanyar ta matso dab dashi, tsakaninsa da ita baifi taku ɗaya da rabi ba.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci na ɗimuwa kwatsam fuskar Armad ta canja kamar wanda wani abu ya shiga jikinsa; ƴan daƙiƙu da suka wuce idan ka kalli idanunsa, alamun wasu-wasi zaka gani, amma kuma a dai-dai wannan lokaci gaba ɗaya yanayin idanuwan nasa suka canja zuwa alamun kafiya da ƙeƙashewa, kamar wanda ya yanke wata shawara acikin zuciyarsa mai wahalar gaske!
A wannan lokaci ne, Armad ya miƙa hannunsa na dama a hankali, zuwa ƙeyarsa inda wannan wannan jan ƙyalle ke ɗaure akai.
A hankali ya warware ɗaurin da hannayensa biyu sannan daga bisani ya cire kyallen, tare da zira shi acikin rigarsa.
Abin mamaki ashe wannan ƙyalle bawai na ado bane kawai. Hasalima bawai gama-garin ƙyalle bane, a'a anyi shi ne da kayan sihiri da kuma audugar Jamsiƙa.
Ana dai amfani da audugar Jamsiƙa ne kurum wajen ɓoye abubuwa mafiya ƙololuwar daraja, a suturcesu daga idanun mutun da aljan, kasancewar irin baiwar da ALLAH ya saka acikin wannan auduga.
To ko me yasa Armad yake amfani da irin wannan ƙyalle domin ɗaure gaban goshinsa?
Amsar tana kan goshin nasa! Domin a dai-dai wannan lokaci da Armad ya kwance wannan ƙyalle wani tambari ne ya bayyana a ɗamfare a jikin goshin nasa.
Kallo ɗaya zakai wa tambarin kasan cewa ba zana shi akai ba, domin a ɗamfare yake a jikin fatar Armad. Kai idan ka matsa kusa ma zaka ga cewa, asali wannan tambari bama a jikin fatar tasa yake ba, hasalima zaifi dacewa ace a jikin ƙashin goshin Armad yake.
Wato dai a taƙaice akwai matuƙar yiwuwar cewa koda an yanke wannan fata ta gaban goshin, wannan tambari bazai ɓace ba.
Tsarin tambarin yana ɗauke da zanen mutun-mutumi daga tsakiyarsa, wanda idan ka lura sosai zaka ga cewa akwai wani al'amudi mai faɗi a hannunsa na dama. Irin yanayin alamun da wannan mutun-mutumi yake ɗauke da ita, idan ka ƙura masa ido, zaka ga tafi kama da ta aljanu.
A kewaye da wannan mutun-mutumi kuwa akwai wasu takubba guda uku, wanda sukai masa ƙawanya. Kowacce acikinsu tana ɗauke da alamun yanayin iskar kabari. Wato irin yanayin nan da mutumin da ya kashe dubban bil'adama da aljanu yake bayarwa idan ya gifta. Kai idan ka fiya kallon waɗannan takubba uku ma, zaka iya rantsewa jini ne ke ɗisa daga jikinsu saboda tsabagen alamun mutuwa dake tashi daga jikinsu.
To daga waɗannan takubba kuma sai wasu rubuce-rubuce, wanda suka kewaye gaba ɗayan tambarin.
Gabaki ɗaya rubutun a sarƙaƙe suke da juna sannan kuma a kewaye. Tayadda koda kasan yaran da akai rubutun dashi, iya karantawa zai maka wahala.
Ballantana ma shi kansa Armad bai san wane yare bane, domin wannan yare baya daga cikin duk yaran da akeyi a wannan zamani.
Kuma ya taɓa tambayar kakansa Zaikid, akan ya fassara masa, amma ya ce masa ba yanzu ba.
Buɗe wannan tambari keda wuya, goshin Armad ya fara haske, lamarinda yasa cikin sauri Armad yasa haƙorinsa ya ciji babban ɗan yatsansa na dama har saida jini ya fito. Sannan cikin sauri ya ɗora ɗan-yatsan akan wannan tambari dake goshinsa.
Hakan na faruwa wannan tambari ya fara zuƙar jinin dake fitowa daga inda Armad ɗin ya cija yana shigewa cikin tambarin kamar wanda wani ƙaton baki yake zuƙewa.
Kan kace meye wannan tuni wannan takubba guda uku na cikin wannan tambari sun fara motsi suna kewaya wannan mutun-mutumi.
Abu kamar wasa cikin ƙiftawar ido da bismillah, kamar wanda aka sawa rai, wannan mutun-mutumi ya fara motsi ta hanyar ɗaga hannunsa mai riƙe da wannan al'amudi sama. Lamarinda yasa Armad yai wata muguwar ƙara mai firgitarwa tamkar wanda ake zare wa rai.
Kafin daga bisani gaba ki ɗayan jikinsa ya fara karkarwa, sannan kuma daga baya ya fara tashin wata walƙiya kamar yadda a baya takobinsa tayi.
Zaka iya cewa tun daga ƙololuwar kansa har zuwa tafin ƙafarsa duk inda ka kalla walƙiya kawai zaka gani tana tashi kamar wani wanda ake saukarwa da aradu.
A cikin wannan hali Armad na tsaye, idanunsa a rufe, takobinsa riƙe a hannunsa na hagu, gaba ki ɗaya babu abinda kake gani a jikin Armad inba wannan walƙiya ba.
Bisa mamaki ana cikin haka sai Izzar Armad ta fara yin sama, kuma kan kace meye wannan cikin abinda bai haura daƙiƙa ɗaya da rabi ba ta tashi daga hamsin da ɗaya takai tamanin da uku.
A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya ɓace ɓat daga inda yake, inda ya bayyana a can sama kimanin taku ɗari biyu da hamsin daga inda yake ada. A dai-dai wajenda hatta ita kanta ƙawanyar wutar bata ƙarasa ba.
Yana bayyana a wajen wannan ƙawanyar wuta ta ƙara ruruwa tayo kansa, tamkar ta kula da cewa ya fita daga cikin zagayenta.
Sai dai kuma kash, Armad ɗin wanda idonsa har a lokacin a rufe yake, a lokacin ne ya ƙara ɓacewa daga inda yake ya kuma bayyana a bayan ƙawanyar sannan kuma a gaban wannan mutun. A dai-dai lokacinda Izzarsa har takai mataki na ɗari.
Dukkanin abubuwan da suka faru, tun daga lokacin da Armad ya kwance wannan jan ƙyalle har ya zuwa sanda ya bayyana a gaban wannan dattijo, a rubuce sun ɗauki dogon lokaci wajen bayyana su, amma a zahiri komai daya faru bai wuce cikin daƙiƙa biyu ba.
Dama wannan dattijo tunda yai amfani da wannan koriyar wuta a fasahar nan mai suna Jukisu, ya nutsu da cewa lallai ya gama da Armad, tunda tun a lokacin ya maida takobinsa cikin kufenta.
Amma a lokacinda yaga wannan tambari na gaban goshin Armad sai daya jada baya bakinsa a buɗe, sannan kuma a lokaci guda ya kai hannunsa kan takobinsa da niyyar zare ta, sai dai kuma ina kan ya zare tuni Armad ya bayyana a gaban nasa.
Inda a lokacin ne Armad ya kaiwa wannan dattijo mummunan sara a kafaɗarsa ta dama da niyyar nakasta hannun da wannan dattijo yake riƙe takobi dashi a lokaci guda.
Takobin Armad ɗin ta tafi da tsananin sauri, sannan kuma da ƙarfin tsiya tayadda har iskar wajen saida ta fara ƙugi.
Sai dai kuma a dai-dai lokacinda takobin take gabda haɗuwa da jikin dattijo wanda yake ta ƙoƙarin kaucewa, sai kawai takobin ta ƙara wani mugun sauri wanda ya wuce gaban hankali, wanda kuma za'a iya fasalta shi da cewa ya ninninka saurin da take tafiya dashi a baya.
Lamarinda yasa ta ɓace ɓat ba'a ko ganinta, kuma abin mamaki a lokacin data ƙara bayyana tana riƙe a hannun Armad. Jikinta wanda da yake cike da walƙiya, yanzu babu komai akai sai farin ƙarfe. Sannan kuma wani abin mamaki kana gani zaka tabbatar da cewa ƙarfen yayi duhu sosai ba kamar sanda Armad ya fito da ita ba.
A dai-dai wannan lokaci babu abinda Armad yai sai kawai kai tsaye mayarda takobinsa da yai cikin kufenta, sannan kuma a lokacin walƙiyar dake rawa a jikinsa ta ɓace ɓat, sannan kuma ya buɗe idanunsa. Babu abinda yake sai haki, kai kace shekara yai yana gudun fanfalaƙi.
Shi kuwa wannan dattijo yana tsaye a dai-dai inda yake baki a buɗe yana kallon Armad wanda yake tsaye yana ta haki.
Sai dai kuma babban abin mamakin shi ne, babu wani alamun sara ko kuma ciwo a kafaɗar wannan dattijo ko kuma a jikinsa.
Amma ga dukkan alamu shi kansa acikin mamaki yake.
Armad na tsaye ya ɗan dunƙufa yana fuskantar wannan mutun wanda shima ke tsaye yana kallon Armad ɗin ba tare da alamun wani ciwo a jikinsa ba.
"hmmm....." cikin mamaki wannan mutun ya fara kallon jikinsa yana yamutse fuska.
Ba wani abu bane ba kuwa ya janyo haka ba illa wani abu daya fara ji a jikinsa.
Wannan abu ba wani abu bane illa fuskanta da yayi cewa Izzarsa akankanta ba tare yayi wani abu ba, ta fara raguwa, daga mataki na ɗari daya barta zuwa ƙasa.
Amma bisa mamaki maimakon hankalin dattijon ya ɗungunzuma, abu na gaba da wannan da yai shi ne murmushi, gami da duban Armad tare da cewa, "nasan wacce ƙabila ce suke da irin wannan MIYÚRA ta gaban goshinka!"
***
Kalmar Miyura ba wani abu take nufi ba illa 'tambari', kuma kalma ce daga yaren 'Aldurish', wanda kamar yadda aka faɗa a baya shi ne yaren da yafi shahara a wannan zamani.
***
Dattijon na gama faɗar haka ya zare takobinsa sannu a hankali, sannan ya fara tafiya taku ɗai-ɗai yana dosar inda Armad yake, a lokaci guda kuma yana bayani, "Ina da tabbas cewa Miyura ce daga zuri'ar Wilbafos!
"Sannan kuma waccan fasaha dakai amfani da ita ɗazu ka tsere daga ƙawanya ta....nasan mece ce!" yana zuwa nan a zancensa ya ɗanyi shiru gami da duba izuwa ɓangaren da wannan ƙawanyar wuta mai suna Jukisu daya harbi Armad da ita ɗazu tayi, kuma har a wannan lokacin tana nan tana dosar ɓangaren da Armad ya baro, duk abinda ya shiga ta cikinta sai dai kaga ta juye izuwa toka. Wala wannan manyan bishiyu wala tsuntsu wala koma meye, hatta iskar dake kaɗawa a wajen bata ƙyale ba.
Ajiyar zuciya kawai yayi, gami da dawo da kallonsa izuwa Armad, wanda a lokacin tuni hasken da wannan tambari na goshinsa yake bayarwa ya fara dusashewa sannan kuma Izzarsa ta sauka ta dawo yadda take a da wato hamsin da ɗaya.
"Abu ɗaya dazan gayama, wanda kuma wataƙila ka riga ka sani shi ne, wannan abu daka aikata zai ƙara maka ƙarfi ta kowacce fuska na ɗan taƙi, amma a dalilin hakan kuma adadin tsahon rayuwarka zai ragu!
"Ta hanyar kallonka kaɗai zan iya gaya maka cewa a ƴan daƙiƙun daka ɗauka kana amfani da wannan tambari na goshinka, kayi asarar sama da shekara biyar na ainihin rayuwarka!"
A dai-dai lokacin da yazo nan a zancensa tuni yana dai-dai gaban Armad, takobinsa na riƙe a hannunsa na dama. Kana ganinsa kasan cewa a shirye yake daya afkawa Armad a kowanne lokaci.
Sai dai kuma a lokacin ne Armad yai sauri ya ce, "dattijo, kafin ka aika ni lahira kuwa, baza kaso kaji maiya biyo dani wannan duniyar ba!"
Dattijon ya buɗe baki zaice wani abu, amma kamar Armad yana jin tsoron kada ya ce baya son ji, nan take yai firgigit ya ce, "TIRIFIL-FAKTA!
"Na fito ne neman Tirifil-fakta!"
"Hmmmmm..... eh.... Tirifil-fakta?" cike da mamaki kuma cikin ƙinƙina, wannan tsaho ya furta sunan gami da jada baya, jikinsa yana karkarwa, tamkar wanda akaiwa albishir da al'amari mai tsananin firgici.
Sama da kimanin daƙiƙa goma wannan dattijo yana cikin wannan hali na ɗimuwa daya tsinci kansa aciki.
Sai dai kuma amma yana cikin wannan hali ne, kamar a mafarki yaji hannunsa na dama dake riƙe da takobinsa ya fara karkarwa da ƙarfin gaske, lamarinda yasa hatta takobin dake riƙe a hannunsa ta fara girgiza tana neman faɗuwa ƙasa.
Mamaki ne rubuce akan fuskarsa asanda ya jada baya gami da ƙurawa Armad ido cikin wani yanayi mai cike da kokwanto da WASU-WASI.
Amma haƙiƙa da ace a iyakacin karkarwa komai ya tsaya, to da ba wani abin tashin hankali bane, amma a dai-dai lokacin ne daga dai-dai kan kafaɗarsa ta dama harya zuwa ƙasan ƙirjinsa ya dare tayadda ana iya gano farin ƙashinsa.
Nan take jini yai tsiri zuwa sama, tare da feshe gaba ɗaya wajen. Kan kace meye wannan ƙasar wajen ta koma jajawur.
A dai-dai lokacin ne wannan dattijo ya kasa riƙe takobin tasa, inda ta faɗi ƙasa. Shi kuwa tsalle yai tare da matsawa can nesa baya da Armad.
A jikin fuskarsa babu komai sai tarin Wasu-wasi. Wasu-wasi akan cewa yaushe ne?
Yaushe ne har Armad yai masa wannan mahaukacin saran bai kula ba. Duk da yana cikin wannan hali na rai a hannun ALLAH, amma ƙoƙari yake kawai yake ya tsayar da jinin dake feshi daga ƙirjinsa ya kuma tambayi Armad yaushe ne?
Koya samu wasu-wasin dake dukan ruhinsa ya sassauta!
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne ya ji muryar Armad na cewa, "daƙiƙa ashirin da bakwai!
"Lallai na samu ci gaba, a wancan lokacin daƙiƙa ashirin ashirin da uku kawai ya ɗauka, kaga an samu ƙarin daƙiƙa huɗu kenan!"
Alamun nutsuwa da yadda dakai ya bayyana ƙarara a fuskar Armad sanda yake waccan magana. Nan take ya fara tafiya taku ɗai-ɗai izuwa wannan dattijo, a wani salo mai kama da yadda shima dattijon ɗazu ya isa wajensa.
Yana zuwa ya ce, "dattijo, tunda nai maka kallon farko nasan cewa babu yadda za'ai na taɓa samun nasara akan ka, badan komai ba saboda yawan Izzarka, banma kai matsayin da zan iya karanta ta ba saboda yawanta.
"Sai dai kuma saboda sanin cewa ba kullum bane wanda yafi ƙarfi yake samun nasara a yaƙi ba. Saboda haka ban fitar da rai ba.
"Amman ina jin kace zaka ƙayyade Izzarka izuwa mataki na ɗari nasan cewa iskar sa'a ɓangare na take yowa!
"Domin nasan cewa duk da Izza ta a mataki na hamsin da ɗaya take, lallai nasan cewa ina da waccan fasaha da zan iya shammatarka da ita!
"Kaga dai kamar yadda kai hasashe lallai wannan fasaha ina amfani da ita ne abisa hatsari. Domin ta ƙunshi aro Izza daga iyaye da kakanni na ta hanyar wannan Miyura dake goshi na, wanda hakan lallai zai rage min yawan kwanaki na a duniya, amma kuma ni indai zan cimma burina na nemowa mahaifiya ta wannan mutun mai suna Tirifil-fakta, to ya ishe ni na mutu acikin murmushi!
"Kuma idan da ka kula tun daga lokacin dana kwance ƙyallen dake goshina na kuma saka jini na akai, Izza ta ke ƙaruwa, har saida takai matakin ɗari da sha ɗaya. Lamarinda ya bani damar yin amfani da fasahar saran takobin da ake cewa Wasu-wasi!
"Wadda fasaha ce ita kaɗai ce fasahar da tasha gaban fasahar 'gayawa jini na wuce', domin ita 'gayawa jini na wuce' bata ɗaukan sama da daƙiƙa ɗaya zuwa biyu, saran daka aiwatar yake bayyana, amma a wannan fasaha akan iya ɗaukar tsahon lokaci kafin mutun ya gane an sare shi, badan komai ba saboda tsananin sauri.
"Wanda hakan ne yasa duk wanda aka sara yake tsintar kansa acikin yanayi na WASU-WASI akan cewa yaushe ne? Yaushe ne aka sare shi!" Armad ya girgiza yana duban wannan dattijo wanda shima idanunsa suna kansa, amma daga dukkan alamu hankalinsa wani abun yake tunani.
Cikin yarda dakai Armad yaci gaba da cewa, "nasan zan iya aiwatar da fasahar WASU-WASI koda ina kan mataki na hamsin da ɗayan, to amma tunda fasaha ce wadda take amfani tsananin sauri da zafin nama mai kama dana walƙiya, saboda haka nasan baza ta taɓa yiwuwa ba, indai Izza ta bata haura taka ba. Wanda shi ne dalilin da yasa na buƙaci Izza ta ta haura ɗari.
"Saboda haka kai sani bama wannan ba, koma mai ya kama a halin wannan tafiyar tawa, koma mene ne, koda kuwa sama bakwai da ƙasa bakwai zasu haɗe, nayi alƙawarin saina nemo wannan mutun." A lokacin da Armad yake faɗar wannan magana idanunsa cike suke ƙololuwar kafiya da ƙeƙashewa irin kafiyar nan da ita kaɗai ka iya tarwatsa rundunar abokan gaba dubu da ɗoriya!
"Hmmmmmm..." Ajiyar zuciya kawai wannan dattijo yai sanda yaga kafiyar dake cikin idanun Armad, kafin daga bisani ya ce, "a iyakacin mataki na Izza ɗari babu yadda zanyi na iya shawo kan wannan raunin da kaimin ya daina zubar da jini!" yana faɗar haka ya kalli wannan wawakeken rami dake ƙirjinsa.
Sannan yaci gaba da cewa, "tunda kuma na riga nayi alƙawarin faɗa dakai a iyakacin matakin Izza na ɗari, bazan saɓa alƙawari ba.
"Saboda haka na yarje maka ka wuce ta wannan hanya!
"Amma kafin ka wuce, bari nayi maka kyautar-kashedi saboda samun nasarar da kayi!!" Yana faɗar haka ya tafa hannayensa guda biyu, lamarinda yasa cikin ƙiftawar ido Izzarsa ta fara hawa sama.
Kan kace meye wannan tuni wannan ciwo da Armad ya ji masa ya haɗe da kansa tamkar ma ba'a taɓa jinsa ba. Sannan Izzarsa kuma hawa kawai take tayi da ƙarin hamsin-hamsin babu alamun zata taɓa tsayawa.
Tun Armad yana iya lissafa ta har saida abin yazo ya wuce gaban ikonsa. Lamarinda yasa Armad ya ƙame a waje ɗaya tare da haɗiyar yawu gami da ajiyar zuciyar duk a lokaci ɗaya, a ransa babu abinda yake tunani illa ratar dake tsakaninsu da wannan mutun ta fannin Izza, da kuma sa'ar da yaci da har ya yadda ya fafata dashi a matakin Izza na ɗari. Domin a lokacin Armad ya fuskanci cewa ko rabin-rabin Izzarsa baiyi amfani da ita ba wajen fafatawar da sukai!
"Wannan kyautar-kashedi ba wani abu ba ce illa, labarin abinda ya faru shekaru ɗaruruwa da suka gabata, akan mutun mafi girman Izza daya taɓa wuce wa ta wannan hanya!
"Wannan mutun sunansa AMRAIKUGYU!"
Armad najin wannan sunan ya haɗe gira gami da bayyana alamun mamakinsa ƙarara a bayyane. Ba komai bane ya janyo haka ba illa cewa wannan suna ba ɓoyayyen suna bane, hasalima kowa kusan yasan shi, kuma saboda daɗewar labarin mai wannan sunan, ba kowa ne yake yadda dashi bama.
Ganin yadda Armad yayi sai wannan dattijo ya tambayeshi, "mene ne?"
Armad ya kada baki ya fara da cewa, "Ai nasan labarin Amraikugyu, na karanta shi ba so ɗaya ba, ba sau biyu, domin duk da wasu suna cewa ba labarin ba gaskiya bane, ni yana ƙayatar dani.
"Wai ko bashi ne wanda bama mutane ba, hatta aljanu saida suka fara rusunawa a gaban Izzarsa ba?
"A zamaninsa kuma saida yayi abinda bai taɓa faruwa ba a tarihi tun farkon duniya, wato tsayawa ƙafa da ƙafa a gaban ma'abota baƙaƙen idanu (URURU).
"Kai daga ƙarshe, shi shi kaɗai ya ɗauki takobinsa mai suna YURA-SHÍRA izuwa doron ƙasa ta biyu, ya yaƙi sarkin wannan ƙasa wato Dul'Ururu, yaƙin da aka shafe kwana ɗari ana yi, amma kuma daga ƙarshe har yau babu wanda yasan wanda yai nasara tsakanin Dul'Ururu da Amraikugyu!
"Amma daga ƙarshe, ance tunda wannan mutun ya shiga ƙasar wasu mutane da ake cewa MATAFIYAN-ALWASHI ba'a ƙara jin labarinsa ba har yau!
"Sai dai ance kanya tafi ya bar takobinsa Yura-shíra a kwazazzaben Yúga, wadda tsahon shekaru ba'a samu wanda ya samu nasarar ɗauko ta ba, saboda hatsarin wajen."
Tunda Armad ya fara jawabi baiko haɗiyi yawu ba, kana ganin yadda yake bada labarin kasan cewa jarumtar wannan mutun mai suna Amraikugyu tana ƙayatar dashi.
Wannan dattijo yai murmushi bayan Armad ya gama bada wannan labari, sannan ya ce, "lallai kasan ɗan wani abu acikin tarihi.
"To amma kasan sunan wannan mutun na gaskiya?"
Armad yai kasaƙe dajin wannan tambaya, kafin daga bisani ya ce, "sunansa na gaskiya kuma? Ai sunansa Amraikugyu...."
"A'a ba haka bane!!" Wannan dattijo ya katse Armad cikin zafin nama. Sannan cikin fushi ya ci faba da cewa, "Matsalarku kenan yaran wannan zamani, ba wani yare da kuka sani inba Aldurish ba, to bari kaji kalmar 'Amraikugyu' kalma ce daga cikin yaren WILBIWRISH.
"Wadda take nufin mafi girman sarki acikin daula, tunda yawanci a wancan zamanin kusan zaka ga duk manyan dauloli suna da sarakuna manya guda bakwai, wanda acikinsu zaka samu mafi girma guda ɗaya, wanda shi ake cewa AMRAIKUGYU da yaren Wilbiwrish!"
Baki a buɗe Armad ya ƙurawa wannan dattijo ido, wanda ga dukkan alamu rashin sanin yaren Wilbiwrish da Armad baiba yai matuƙar ɓata masa rai kamar wanda aka ce ƙabilarsa bata da muhimmanci.
Wannan dattijo ya ci gaba da cewa, "to sunansa na asali BAYAJIDDA! Daga baya ne bayan yaci galaba akan dukkan abokan gabarsa na gida aka koma yi masa laƙabi da Amraikugyu."
"BAYAJIDDA!" Idanun Armad suna neman fitowa saboda mamakin jin sunan BAYAJIDDA. "Bayajidda ba shi ne wanda ya kafa ƙabilar Bayajidda ba, a ƙarni na bakwai bayan anyi yaƙin Yékashínu ba!"
Tsohon nan kawai kyaɗa masa kai yai, alamun maganar daya faɗa haka take. Sannan ba tare da ya bashi damar farfaɗowa daga halin da yake ciki na ɗimuwa ba ya ɗora da cewa, "ba komai bane yasa na kawo maka maganarsa ba illa abu ɗaya, wanda kuwa shi ne, shi kansa shugaba AMRAIKUGYU, gabaki ɗayan rayuwarsa da fafatawar da yayi, yayi tane akan neman wannan mutun mai suna TIRIFIL-FAKTA!!!"
"Ehhhhhhhhh!!!" Mamaki ya fara sa Armad matsawa baya daga inda yake, yana neman faɗuwa.
Wanda dattijo baiko lura da halin da Armad yake ciki ba ya ɗora da cewa, "Amma a ƙarshe baiyi nasara ba!" Yana zuwa nan a zancensa yai shiru gami da kallon Armad cikin yanayin tausayi, kafin daga bisani ya ci gaba da cewa, "zan iya tunawa a wancan zamanin, shima saida ya faɗamin kusan sak irin abinda ka faɗa yanzu!
Yake cewa, " 'Ni BAYAJIDDA, ina rantsuwa da mahaliccin sarki WILBERIYA, saina nemo TIRIFIL-FAKTA, koda kuwa zan kashe dukkan mutun da aljani dake ban ƙasa akan yin hakan. Wannan alƙawari ne tsakani na da ma'abocin wannan raƙumi!!!' "
Wannan dattijo ya ƙara yin ajiyar zuciya tare da girgiza kai, sannan ya ce, "Yadda kaji haka ya faɗa a wancan lokacin kalma da kalma bazan taɓa mantawa ba.
"Kawai sai bayan shekaru casa'in da biyu naji cewa shima ya salwanta a hannun MATAFIYAN ALWASHI.
***
Idan mai karatu bai manta ba sunan littafin nan gabaki ɗaya TAFIYAR ALWASHI, domin sunan MAGAJIN WILBAFOS sunan littafi na ɗaya ne daga cikin jerin littattafan TAFIYAR ALWASHI.
***
Dattijon yai wani kwauron ajiyar zuciya tare da tambayar Armad acikin wani yanayi na hangen nesa, "Duk da wannan labarin dana gaya maka kana ji har yanzu baza ka canja shawara ba?"
Armad na jin wannan tambaya kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi da hunturu, yai firgigit ya farka daga ɗimuwar daya shiga tare da cewa, "bazan taɓa janye magana taba koda zan rasa raina!" Sannan a wani salo na alamun nuna ƙaguwa da sauri kamar wanda ke tsoron kada wani ya rigashi yaci gaba da cewa;
"Na gode, sosai da wannan tsohon tarihi daka bani, baka san yadda zai ƙaramin kwarin gwiwa ba, domin har na ƙara jin ina da buƙatar nayi sauri na tafi domin na fara neman wannan mutun, kona dawo na haɗu da mahaifiya ta da wuri!"
Bakinsa abuɗe, wannan dattijo yama rasa abinda zaice saboda ganin irin kafiya ta Armad tare da rashin tsoro, ƙura masa ido kawai yai yana kallonsa, wanda shi kuwa tuni ya maida takobinsa cikin kufenta yana jira yaga wacce hanya dattijon zai nuna masa.
Can bayan wani ɗan lokaci, kamar wani abu ya shiga jikinsa, dattijon ya numfasa ya ce, "suna na HánDiyuza, kada ka manta suna na, domin zai ma ka amfani wataran!"
Armad na jin haka ya buɗe baki zai faɗa masa sunansa, amma cikin sauri dattijon ya ɗaga masa hannu, yana mai cewa,
"bashi da amfani ka gaya min sunanka, domin bana riƙe suna ye, amma kai sani duk inda muka ƙara haɗuwa zan tuno kamannin ruhinka, domin bana taɓa manta kamanni ruhi!"
Nan take dattijo HánDiyuza ya zira hannu cikin rigarsa gami da fito da wani ɗan littafi, inda ya buɗe shafin farko acikinsa. Sannan bayan ya gama karanta wani rubutu mai motsi aciki ya ɗago kai ya dubi Armad tare da cewa, "a halin yanzu ƙasa ta huɗu ita kaɗai ce a buɗe!
"Amma zuwa nan da ƴan awanni ƙasa ta biyu zata buɗe ita ma.
"Ƙasa ta biyar sai nan da kamar sati, sai kuma ƙasa ta shida wadda zata ɗau lokaci mai tsaho gaskiya, amma ƙasa ta bakwai babu rana tunda ba'a daɗe da kammala yaƙi akanta ba!"
Cikin sauri kamar wanda yake son yai sauri ya rabuda Armad, dattijon yaci gaba da cewa, "Wacce kake son zuwa?"
A wani yanayi mai nuna ƙaguwar da Armad yayi, ya amsa da cewa, "ƙasar da tafi kowacce sauri mana, wato ta huɗu kenan!!"
Dattijo HánDiyúza yana jin haka bai tsaya yiwa Armad wata magana, ya bubbuɗa cikin wannan littafi, gami fito da wata takarda mai cike da rubutun ɗalasimai aciki gami da miƙawa Armad ita, sannan ya rufe maganarsa da cewa, "shekaru sha takwas da suka wuce wani mutun mai suna BIHANZIN ya wuce ta wannan hanyar, kuma yana ɗauke da takobin Shugaba Amraikugyu Bayajidda! Ban san ya akai ya mallaketa ba, amma lallai ita ce!
"Ka kula sosai idan ka haɗu da wannan mutun mai suna BIHANZIN, domin a halin yanzu yafi kowa ƙarfin Izza a doron ƙasa ta huɗu, idan son samu ne kada ka taɓa yin faɗa dashi!"
Yana gama faɗar haka ya juyawa Armad baya ya fara tafiya, a lokacin ne shi kuma Armad ya buɗe baki da niyyar tambayarsa mai ya kamata yayi, sai dai kafin yai magana yaji gaba ɗayan kansa ya fara juyawa, inda daga bisani ƙasar da yake tsaye akanta yaji ta fara narkewa tana komawa kamar ruwa.
"Aaarrrghh" muryar Armad kenan bayan da yaji kwatsam ya rufta ƙasa. Wanda a lokacin ya tsinci kansa a wani yanayi mai kamada mutun yana faɗawa wawakeken rami mara ƙarshe, sai dai abinda Armad yake fuskanta a lokacin yama fi haka.

Comments
Post a Comment