A babi na shida mun tsaya a inda Armad ya faɗi a sume cikin wannan gari, bayan jin wannan murya. Yanzu zamu ɗora;
***
Babban abinda Armad bai sani ba shi ne, wannan murya da yaji ta kasance kullum saita maimaita sak irin abinda yaji tana faɗa sau casa'in da tara.
Bata taɓa fashin yin hakan ba, sannan kuma babu wani mahaluƙi daya taɓa shiga cikin wannan garin tun bayan da muryar ta fara maganar, sama da shekaru dubu kenan, sai Armad.
A dai-dai wannan lokaci, Armad yana kwance a sume baisan inda kansa yake ba, sannan kuma bashi da masaniyar cewa duk sanda wannan murya ta gama maganarta, gaba ki ɗayan iskar wannan gari kamawa take da wuta, badan komai ba sai dan tsananin ƙarfin Izzar dake ƙunshe cikin muryar.
Kuma hatta a wannan lokaci, abinda ya afku kenan; ɗaukewar muryar keda wuya, gabaki ɗayan ilahirin iskar dake cikin garin ta fara ɗaukan zafi.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wasu tafka-tafkan jajayen kunami masu kafafu Irin na mutane, wanda a tsaye sunkai girman ƙananun giwaye, suka bayyana a dai-dai inda Armad yake.
Kana ganinsu zaka tabbatar da cewa a matuƙar fusace suke, saboda yanayin yadda suke kallon Armad, wanda ke kwance a sume baima san abinda ke faruwa ba.
Waɗannan kunami guda biyu ba wasu bane illa masu tsaron wannan gari.
Kasancewar a dai-dai lokacin da Armad ya shigo garin suka ji shigowarsa, to amma saboda wasu dalilai basu bayyana ba saida ya suma. A wannan lokaci ne suka rikiɗe izuwa siffar mutane sanye da tufafi irin na can-can mutan da, launin ja da rotsi-rotsi, sannan kuma da irin hular nan mai lankwasa da tsoffin da suke sawa.
Na hannun daman ya dubi na hagun tsahon ƴan daƙiƙu, kafin daga bisani ya fara magana a nutse da cewa, "zuri'ar Wilbafos ne, kuma ko badan komai ba, saboda alaƙar dake tsakanin shugaba Amraikugyu da Wilbafos-na-shida, bai kamata mu halaka shi ba."
Yana zuwa nan a zancensa yai shiru tare da ci gaba da duban ɗan'uwan nasa, kamar yana jira yaji mai zaice. Shi kuwa babu abinda yai illa sunkuyawa, ya kuma dangwali jinin dake malale a gaban farar rigar Armad.
Wanda ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙa kusan talatin kamar wanda yake karanta wani haɗaɗɗen littafin da baya son ɗauke ido. Can daga bisani ya ɗago kai ya dubi wannan ɗan'uwa nasa da yai magana da fari tare da cewa, "abinda ka faɗa gaskiya ne, to amma kuma bai kamace mu ba, mu tseratar dashi."
Yana gama faɗar haka ya miƙe, inda dukkaninsu suka kyaɗa kai alamun amincewa, kafin daga bisani su ɓace ɓat, babu su babu alamunsu.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokacin tuni wuta ta fara tashi acikin wannan gari. Kuma duk wani abu da zaka iya gani wutar nan bata barinsa.
Ba jimawa kayan jikin Armad suka fara ci da wuta, kan kace meye wannan tuni fatar jikinsa ma ta fara kamawa.
Ana cikin haka sai kawai wannan takarda dake cikin aljihun Armad ta bada wata ƴar ƙaramar ƙara, mai kama da an fasa tulu. Inda ita ma ta fara cida wuta, kuma kan kace meye wannan tuni ta ƙone.
Armad na kwance a sume, sannan kuma ga jikinsa ya fara cida wuta, sannan kuma ga takardar da ke ƙunshe da ɗalasiman da zasu fitar dashi daga cikin wannan duniya su kaishi zuwa doron ƙasa ta huɗu inda yake sa ran fara neman Tirifil-fakta, ta ƙone.
Lallai da idonsa biyu da ana tamabayarsa zai yadda da cewa yana cikin mafi munin halin da zai iya samun kansa a ciki a wannan lokaci!!!
***
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne da Armad ke kwance a sume, a can wani ɓangare na duniya, wani ƙatoton lambu ne, wanda idan ka ƙiyasta girmansa sai kaga shi kaɗai yakai kimani girman wasu ƙauyukan.
Wasu irin dogayen bishiyu ne na ƙasaita da isa da alfarma, masu fala-falan ganyayyaki, yawanci masu launin kore, yalo da ja suka kewaye dukkan wannan lambu. Daga cikinsa kuma ƙananun bishiyu ne a jejjere a layi-layi sahu-sahu. Babu komai akan waɗannan bishiyu banda ƴaƴan itatuwa kala-kala masu yawan gaske, waɗanda tsabagen yawansu da dama daga cikinsu ma idon bil'adama bai taɓa gani ba.
Sannan kuma a tsakankanin waɗannan bishiyu dake jere akwai wasu ƙoramu suna kwaranya, masu ɗauke da wani tataccen ruwa garai-garai, wanda saboda kyawunsa, kai kace ba daga duniyar nan yake ba.
Dukkanin waɗannan abubuwa sune suka sa tun daga nisan sama da tafiyar kwana ɗaya da wuni mutun zai iya fara jin ƙanshi mai sanyaya rai, na tashi daga cikin wannan lambu.
Sai dai kuma a zahirin gaskiya duk wannan bashi ne abinda yasa wannan lambu ya zama na musamman ba.
Abun kuwa da yasa hakan ba wani abu bane illa wani ɗan ƙaramin gida dake a tsakiyar wannan lambu, wanda yake ta bada wani irin haske mai tsananin ƙawa da kyawun tsari, wanda bazai taɓa misaltuwa dai-dai da dai-dai ba.
Kuma wani babban abin mamakin shi ne babu alamun wata fitila wadda za'a ce ita ke bada wannan haske, a'a sai dai kawai hasken na ɓullowa ne daga cikin wannan gidan.
Acikin wannna gida kuwa akwai wani ɗaki wanda shima a tsakiyar gidan yake. Kuma abin mamaki dukkan wannan haske da wannan gida yake bayarwa asalinsa daga wannan ɗaki yake fitowa.
A dai-dai wannan lokaci wasu mutun biyu ne a tsakiyar wannan ɗaki akan wani gadon alfarma da aka yiwa ado da fatar fararen aljanu.
Waɗannan mutun biyu ba wasu bane illa wata budurwa da kuma wata dattijuwa wanda ba daban kayan dake jikinsu sun banbanta suba, da idan ka kalle su ta baya sai saika ce ma ƴa da uwa ne, saboda dukkanin jikinsu haske yake.
Amma ina, kallo ɗaya kacal zakai ka tabbatar da cewa lallai ratar dake tsakaninsu irin wadda ke tsakanin sarauniya da kuyangarta ce.
Domin kuwa bisa ƙololuwar mamaki, duk wannan haske dake tashi wanda ya mamaye mutanen biyu da kuma gidan baki ɗaya, sannan kuma har yake fita waje yana haskaka wannan lambu baki ɗayansa, daga jikin wannan budurwa yake tashi.
Tun daga baya idan ka dubi wannan budurwa zaka ji wani tsananin gwarjini irin na manyan sarakunan farko na tashi daga jikinta, wanda shi kaɗai zai iya saka maka tsananin firgici da tunanin wace ce wannan budurwa.
Amma kuma wani ƙarin abin mamakin shi ne hatta wannan dattijuwar dake kama da kuyangar wannan budurwa, Izzar ta takai mataki na ɗari uku da arba'in da biyu, wanda hakan zai ƙara nuna ma girma da falalar wannan budurwar.
A dai-dai wannan lokaci wannan dattijuwa ta kyaɗa kai alamun amincewa. Kai daka gani kasan cewa basu daɗe da gama tattauna wani abu mai matuƙar muhimmanci ba. Sannan kuma ta tashi daga inda take ta nufi jikin bangon ɗakin da wannan budurwa take fuskanta, inda ta tsaya ta kira sunan wani ɗalasimi, "Hai-há-ka!"
Faɗar wannan ɗalasimi keda wuya kawai sai wannan bango ya fara haske, inda kan kace meye wannan wata ƴar ƙofa ta bayyana a jikin bangon.
Cikin sauri wannan dattijuwa ta juyo ta dubi wannan budurwa tare da cewa, "gimbiya ta lokaci yayi, wannan ne gwaji na talatin da ɗaya, wanda kuma kamar yadda muka yanke shawara yanzu shi ne kwaji na ƙarshe, indai ba'a samu nasara a wannan karanba, to dole mu bi umarnin shugaba Bihanzin mu koma gida!"
Kafin ta gama rufe bakinta tunu wannan budurwa wadda ba'a iya tantance launin kayan jikinta da kamanninta kwata-kwata, badan komai ba saboda tsananin haske mai kashe ido dake tashi daga jikinta, ta tashi tsaye gami da duban wannan dattijuwa tare da kyaɗa kai. Kafin daga bisani ta shige cikin wannan ƙofa. Tana shiga ƙofar ta ɓace ɓat, a lokacinda ita kuma wannan dattijuwa tai ajiyar zuciya tare da cewa, "sa'a tana tare dake gimbiya Nostalgiya Nára!"
***
Bayan kwana huɗu da shigar wannnan budurwa cikin wannan ƙofa, a zaune a bakin wani kogi mai ɗauke da baƙin ruwa, ita ce. Inda take zaune cikin nutsuwa, ƙafafunta a tankwashe, kanta a kafe akan wannan ƙatoton kogi tana nazari, wannan ruwa wanda gaba ɗayansa baƙi ne, baƙi-ƙirin!
Abin al'ajabi a kefenta kuma wani saurayi ne kwance a sume dukkan kayan jikinsa sunyi daga-daga, tayadda sama da rabin jikinsa a fili yake a bayyane.
Fatarsa ta ƙoƙƙone, sannan kuma duk jikinsa ƙasa ce da kuma datti ko'ina ka kalla.
Sannan kuma bisa mamaki akwai wani farin haske mai siffar miciji yana ta kewaya jikin wannan saurayi dake kwance a gefe bai san inda kansa yake ba.
Sai dai kuma duk da wannan hali da wannan saurayi yake ciki, akwai wani jan kyalle a ɗaure a goshinsa, wanda babu alamun ƙonewa a tattare dashi ko kaɗan. Hasalima ko datti babu a jikinsa tamkar daga baya aka ɗaura masa shi.
Idan ka lura da wannan saurayi sosai zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos!
A kwana a tashi Armad na kwance a sume a gefen wannan budurwa, har tsahon kwana uku, ita ma tana zaune tana nazarin wannan baƙin ruwa ko motsi batai ba tsahon wannan kwanaki.
Sai a ƙarshen wannan rana ne, wannan budurwa ta ɗauke idonta daga kan wannan baƙin ruwa, ta kuma juyo ta kalli Armad da dara-daran kyawawan idanuwanta.
Wannan budurwa ta kasance nada matuƙar kyawun gaske, tayadda a lokaci ɗaya zata sa duk wanda ya kalleta cikin zulumi da tunanin anya kuwa ya taɓa ganin mai kyanta akaf tsahon rayuwarsa da mafarke-mafarkensa da labaran daya taɓa karantawa. Da kuma kokwanto ko anya ma kuwa mutun yake gani!
To kamar dai ƙirar jikinta tsayin fuskarta ya dace matuƙa da faɗinta, lamarinda ke bayarda fasalin tsananin cikar kyawun diri.
Idanuwanta dara-dara ne, wanda farin cikinsu fari ne fat, kuma baƙin cikinsu baƙi ne wuluk. Sannan kuma ga hanci wanda tsahonsa ya dace da girman fuskar tata.
Tana da yawan gira, wadda take a saice dai-dai da dai-dai a saman idanunta.
Duk da cewa tsahon baƙin gashinta ya kai har gadon bayanta, amma wannan ba abu bane da Armad bai saba gani a ƙasar daya baro ba, amma babban abinda zai bashi mamaki dazai farka shi ne, wannan yadda wannan gashi yake kyalli yana sheƙi, tayadda idan ka ƙura masa ido zaka iya faɗawa wasu tunane-tunane basu dace ba.
Tun kafin tai murmushi akwai alamun dimful dake bayyane akan madaidaicin kuncinta.
Idan ka haɗa cikakken kyawun diri da ƙololuwar kyawun fuska da wannan budurwa ke dashi, sannan kuma ga yanayin yarinta dake tashi daga ilahirin jikinta, sai kaga cewa lallai samun wadda takai ta kyau abu ne da zaiyi matuƙar wahalar gaske koda tsakanin mafi kyawun fararen aljanu da mutane farko.
Kai lallai babu wata tantama idan kace kasancewar wannan budurwa a wajen da take yayi matuƙar ƙarawa wajen kyau, tamkar kyawun surar ta yana shafar shi kansa muhallin da take musamman duba ga irin hasken da jikinta yake bayarwa yana ƙarawa bakin wannan kogi ƙawa.
Bayan ta juya ga Armad ta ɗaga hannunta na dama, inda ta ɗorashi a ƙirjinsa.
Abin mamaki hakan na faruwa nan take gaba ki ɗayan ciwukan dake jikin Armad suka fara warkewa. Kan kace meye wannan tuni sun gama haɗewa, jikinsa ya koma kamar ba'a taɓa jin rauni ba akansa.
Sai dai kuma abin mamaki a lokacin gaba ɗaya hasken dake jikin wannan budurwa a lokaci guda ya zuƙe ya ragu sosai, tayadda kallo ɗaya zakai mata kasan cewa warkar da ciwukan Armad da tayi Armad yana da farashi mai tsauri.
***
Tana ɗauke hannunta ta fara haki tana nishi irin wanda ya dace da ma'abota ƙololuwar kyawun sura da ruhi, na ɗan tsahon lokaci, kafin daga bisani ta dawo hayyacinta, inda ta fiddo da wata takarda daga cikin rigarta, ta kuma sakawa Armad acikin ragowar fatattakakkun kayansa.
Haka na faruwa ta miƙe, inda tayiwa wannan baƙin ruwa kallon ƙarshe, sannan ta juya tabar Armad a kwance a inda yake. Kuma kan kace meye wannan, wannan kyakkyawar sura ta ɓace daga wannan waje.
To a ƙarshen wannan ranar ne shima ya farka a wani yanayi na kasala.
Abinda ya fara bashi mamaki shi ne ya tabbatar da cewa acikin wannan gari ya faɗi ya suma, bayan yaji wannan murya, amma kuma yanzu gashi nan a kwance a gefen wani kogi.
Sannan kuma ga kayansa nan a ƙoƙƙone, alamun tabbas wuta ce ta ƙona su, amma kuma shi babu ko rauni ɗaya a jikinsa.
Yana ganin haka abu na farko daya fara faɗo masa shi ne wannan takarda wadda yasan cewa ita ce manuniyar hanya a wajensa, indai yana so ya fita daga cikin wannan duniya lafiya.
Saboda haka cikin sauri ya miƙa hannunsa cikin aljihun wandonsa duk da yasan ba'anan ya saka ta ba, to amma kamar yadda ya gani shishi kaɗai ne aljihun daya rage a jikinsa.
Sai dai kuma bisa mamaki sai yaji takarda aciki. Yana fito da ita mamaki ya ƙara kamashi, bayanda ya fara ganin canje-canje a jikinta, lamarinda ya tabbatar masa cewa ba wancan takardar bace.
Domin a ƙasan wannan takardar hadda rubutu, ansa 'Gimbiya Nostalgiya Nára' an kuma saka hannu daga can ƙasa. Abubuwan da duk babu su a wancan takarda da Armad ya sani.
Cikin mamaki ya fara tunanin me ya faru bayan ya suma, amma ina duk yadda yai ƙoƙari baya iya tuna no komai.
Sai dai kawai abu ɗaya da yake iya hasashe shi ne cewa, lallai cetarsa akai daga cikin wancan gari daya suma aciki, kuma ga dukkan alamu waɗanda suka ceto shi sun san muhimmancin wancan takarda. Wanda hakan yasa da suka ga tasa ta ƙone suka canja masa wata.
"To amma su wane ne suka cece ni?" Wannan ita ce tambayar da yake ta yiwa kansa kuma bashi da amsa illa abu ɗaya, wato sunan 'Gimbiya Nostalgiya Nára', wanda ya gani a jikin takardar. Sunan da bashi da masaniyar ko na waye!!!
Armad bashi da masaniyar cewa ga wadda ta ceto shi, sannan kuma a wannan lokacin za'a iya cewa kusan duk su biyun basu da masaniyar cewa wannan shi ne abu na farko da zai haɗa tsakaninsu a wani irin tarihi da baza a taɓa mantawa dashi ba!!!
***
Sai dai kuma ba jimawa Armad ya yanke shawarar lokaci yayi da ya kamata ya fita daga cikin wannan duniya izuwa doron ƙasa ta huɗu. Inda ya yanke shawarar zai fara neman Tirifil-fakta daga nan.
Saboda haka nan take ya ajiye tunanin gimbiya Nostalgiya Nára a gefe ya kuma dubi takardar dake hannunsa inda ya fara karanto wasu ɗalasimai daga ciki.
Yana gama ambatarsu, ba daɗewa ya fara hango wani ɗan ƙaramin kwale-kwale yana isowa inda yake.
Yana zuwa baiyi wata-wata va ya ɗare akai, sannan ya ƙara karanta wasu ɗalasiman ƙamarinda yasa wannan jirgi ya fara tafiya izuwa gabas masi kudu akan wannan baƙin kogi!!
Armad ya fuskanci gaban kwale-kwalen nan, yana ta miƙa ido ko zai hango gaba, amma ina. Har gari ya waye, rana taje tsakiya bai ga komai ba.
Lamarinda yasa ya yanke shawarar ya ɗan rintsa kaɗan kafin ya isa, inda ya nemi waje ya kwanta, hannunsa akan takobinsa.
A lokaci daya tashi baiga rana a sama ba, hasalima yana kallon gabas yaga alamun ɗagowar rana, lamarinda yasa yasan lallai safiya ce, abinda ke nuna cewa ya kwana ya kuma wayi gari yana bacci.
Yayi mamakin yadda yai bacci da yawa haka, lamarinda yasa ya fara ƙoƙarin tuno lokaci na ƙarshe daya kwanta yai bacci haka, ya kuma tuno cewa ai tun sanda aka ƙwanƙwasa masa ƙofa aka ce ga mahaifiyarsa ta dawo daga yaƙi amma bata san inda kanta yake ba.
"Hmmmm!!" Ajiyar zuciya kawai yai, ya kuma ƙara ji a ransa cewa lallai yana so yai sauri ya nemo wannan mutun mai suna Tirifil-fakta, koya koma gida yaga mahaifiyarsa.
Amma yana cikin wannan tunani ne yaga wani abun; wannan kuwa ba komai bane, illa sararin samaniyar wannan waje.
A iya saninsa, a kullum idan rana ta fito, akwai rana ɗaya wadda take tasowa daga gabas ta faɗi a yamma, sannan sai kuma ɗayar wadda bata motsawa tana tsaye a tsakiyar sama cak.
To amma banda a wannan waje, inda duk yadda ya duba guda ɗaya tak yake iya gani, wadda ke tasowa daga gabas.
Bai san mai ya janwo hakan ba, amman babban abinda yake gabansa shi ne yaushe zai isa bakin gaɓa.
A zuciyar sa tun daga sanda ya taka ƙafa ya shiga wannan ƙofa da Abul-Babara ya buɗe masa, yake ta tunanin dame zai fara wannan alƙadari nasa na neman TF, idan ya isa doron ƙasa ta huɗu.
Armad nata tafiya acikin wannan jirgi, babu abinda ke ransa sai son ya isa bakin gaɓa.
A rana ta biyar yana cikin tafiya yunwa ta tayar masa, inda ya rasa yadda zaiyi, kawai saiya rufe ido ya fara rera wakar da mahaifiyarsa take masa sanda bai kai shekara goma ba, idan tana so yai bacci.
Ai kuwa haka akai, ba jimawa bacci ya ƙara ɗauke shi, yana kwance yana bacci, kwatsam girgizar jirgin da yake ciki tasa ya farka.
Yana buɗe ido, yayi arba da abinda ya daɗe yana jira, wato bakin gaɓa.
Sai dai kuma ba a yadda yai tsammani ba. Domin kuwa abinda ya hango daga nesa shi ne bango ruwa, wanda kallo ɗaya kawai yai masa yasan cewa lallai wannan yana kama da bangon duniya.
To amma ba wannan ne abinda ya firgita shi ba, illa wani ƙatoton waje mai kama da wawakeken rami dake tsakanin wannan bangon da kuma wannan baƙin ruwa da jirginsa yake kai, wanda lallai idan da za'a auna zai kai kimanin faɗin taku dubu da ɗoriya.
Kuma daga yanayin tafiyar jirgin, ya fuskanci cewa bashi da niyyar tsayawa ko kaɗan, hasalima yana ƙara kusanto wannan rami yana ƙara sauri, tamkar dama aikinsa ya jefa Armad cikin wannan rami.
A lokacin da Armad ya farka tuni wanki hula ya kaishi dare, saboda baifi saura taku biyar ba tsakaninsa da wannan rami ba, amma a wannan lokaci saura taku uku kacal.
Tuni Armad yake ta tunanin wacce hanya zaibi ya tsayarda wannan jirgi, amma ina babu wata hanya mai ɓullewa data zo kansa.
Duk tunanin da yayi sai yaga bamai ɓullewa bane, saboda babu wani abu mai kama da alamun Armad zai iya riƙewa ko kuma ɗanewa wanda zai iya sawa wannan kwale-kwale ya ƙi faɗawa wannan rami.
Yana cikin wannan tunani ne, ba shiri wannan jirgi nasa yaje bakin wannan rami, inda bisa mamaki kawai ya tsaya cak, sannan kuma kafin Armad ya ƙarasa ajiye ajiyar zuciyar da yayi tuni wannan kwale-kwale ya ɗaga shi sama, inda cikin sauri ya cilla Armad cikin wannan wawakeken rami, shi kuma ya juya ya koma inda ya fito!!!
Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Comments
Post a Comment