Skip to main content

Babi na Tara : Farar Takobi

Armad ne da Kiru a tsaye su na fuskantar juna, kowa da tasa takobin a zare!

Tun dai ƴan mintuna da suka gabata, Hasanu wanda shi ne babban wannan tawaga ya kwance Armad ya kuma bashi takobinsa. Abinda kawai ya rage shi ne Kiru ya nunawa Hasanu da wannan budurwa, wadda ta kasance ƙanwarsa, irin sabuwar fasaha, da ya koyo.

Fuskar Armad bata canja ba ko kaɗan, tamkar babu abinda ke faruwa, yana riƙe da ƙotar takobinsa.

A wannan lokaci ne Kiru yayo kan Armad, yana zuwa ya ɗaga takobinsa ya kawo masa wani wawan sara.

Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi sama yayinda waɗannan takubba nasu suka haɗu a sama, lamarinda yasa dukkan tsuntsaye da sauran dabbobi dake kewayen fara guje-guje.

Kan kace meye wata iska ta tashi daga kewayen su, inda ta bazu ko'ina, har saida ta kaɗa bangon ruwan dake arewa, wanda bashi da nisa da inda ake fafatawar.

Kiru ya kalli takobin Armad idanunsa cike da mamaki, wanda a wannan lokaci fuskarsa taɗan canja, kana gani kasan haɗa takobin da sukai yasa ya rage kallon rainin da yake wa Armad.

Duk da cewa yasan baiyi amfani  da sama da kaso sittin, na ƙarfin Izzar sa ba, a yayin wancan sara, amma yanayin yadda Armad ya murza takobin tasa sannan kuma ya kare saran ba tare da wata damuwa ba, shi ne abinda ya bashi mamaki.

Bama shi ba, hatta Hasanu sai da idonsa ya ɗan ƙifta.

Armad ya ɗaga kai ya kalli Kiru ido cikin ido, lamarinda yasa Kiru yai tsaki, a lokaci guda kuma ya afkawa Armad da sara ta ko'ina.

Cikin abinda baifi ƙiftawar ido ba, tuni sun kaiwa juna sama da sara ashirin.

Aduk lokacin da takubbansu suka haɗu sai kaji ƙara mai kashe kunne ta tashi sama, sannan ƙura ta ƙara turnuƙewa, babu abinda suke sai kai-komo.

Baya kimanin daƙiƙa sittin, dukkaninsu suka tsaya da kaiwa juna sara, gami da ja baya, kowa na kallon kowa, su na haki.

Suma su Hasanu da Zahra kallonsu kawai suke, kuma harya zuwa wannan lokaci, Armad ya kula, babu alamar su biyun zasu shiga cikin faɗan.

Wannan saurayi mai suna Kiru da suke fafatawa da Armad, zaɓaɓɓe ne daga daular Banfiriya, kuma ɗan sarkin garin Sisiya ne.

Kuma yana daga cikin waɗanda mutane da dama suke yiwa kallon shugabannin gobe.

Kuma saboda tarin kayan aiki na horo da zai iya samu aduk lokacin daya buƙata, da kuma manya-manyan malamai a garinsu, da duk suke so karɓe shi a matsayin ɗalibi na musamman, sannan kuma ga dangi na musamman da yake dasu, kai dama sauransu...

Hakane ma yasa, a tsahon tarihin Kiru, tun daya taso, harya zuwa shekaru goma sha bakwai da yake a wannan lokaci, babu wani sa'ansa daya taɓa cin galaba a kansa a fagen fama.

Saboda haka daga kansa har zuwa yayansa Hasanu, wanda shi ne Kwamanda na huɗu a ƙarƙashin wannan ƙungiya da akewa laƙabi da Burja, babu wanda ke da kokwanton Kiru zai samu nasara akan Armad ba.

Kuma su na gani cewa, wannan kai-komo dake faruwa a tsakanin Armad da Kiru bata wuce motsa jini ba a wajen Kiru.

Shi kuwa Armad duk da shi, ba zaɓaɓɓe bane daga kowacce masarauta ba, amma a dai-dai wannan lokaci da yake tsaye yana fuskantar Kiru, babu abinda yake gayawa kansa sai cewa, yanzu ya fara wannan tafiya tasa ta neman Tirifil Fakta, kuma lallai shima jarumi ne, kuma wannan faɗa kamar wata dama ce ALLAH ya bashi da zai fita daga cikin halin da yake ciki.

Saboda haka babu abinda yake tunani face hanyar da zai kuɓuta daga waɗannan mutane koma su waye.

Armad ba dolo bane, kuma yasan iyakacin ƙarfinsa, saboda haka nema tunda farko Armad ya gama lissafa cewa, a iyakacin ƙarfinsa a wannan lokaci babu yadda zaiyi da waɗannan mutane uku. Amma yana jin cewa da mutun ɗaya, zasu kara sai yaji daɗi, domin yasan akwai yiwuwar mafita.

A dai-dai lokacin da yake wannan tunani kwayar idonsa ta motsa daga kan Kiru izuwa kan Hasanu.

A lokacin ne yaji nan take tsigar jikinsa ta tashi da wani irin tsoro, irin wanda rai ke fuskanta a dai-dai lokacin mutuwarsa.

Ba komai bane ya janyo haka ba illa ratar ƙarfin Izza daya ji a jikinsa wadda ke tsakaninsa da Hasanu!

Lallai yasan Hasanu ba sa'an sa bane.

To amma a dai-dai lokacinda zuciyarsa take ɗarsa masa cewa, Kiru ba komai bane ba, Hasanu shi ne abin ji!

Shima Kiru yaga kallon da Armad yayi wa Hasanu da kuma yadda ya tsorata dashi, saboda haka bai ɗau lokaci ba ya gano abinda Armad ke tunani a ransa.

Wanda hakan yai matuƙar ƙona masa rai, ya ɗaga kai sama yai ƙaraji, idanunsa ja-jawur.

Ba komai bane ya jawo haka ba, illa ji da yayi acikin ransa cewa Armad ya raina shi, yana gabansa amma bata tasa yake ba.

Nan take ya maida takobin dake hannusa cikin kufenta, sannan ya fito da wata daga cikin kufen.

Sai dai ita wannan ta biyun fara fat ce, babu abinda take sai matuƙar kyalli, idan rana ta haska ta sai kaga tana haske ido, haske na tashi kamar walƙiya.

Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin matuƙar fushi, ya afkawa Armad.

Da farko Armad baiyi ko gezau ba, amma a lokacinda idon sa yakai kan wannan takobi, kyallin da take, ya daki idonsa, nan take yaji wata rawar-ɗari ta gifta ta jikinsa.

Abinda yasa dukkan tsigar jikinsa ta tashi. Babu abinda zuciyarsa take ɗarsa masa sai alamun hatsari a tattare da wannan takobi.

Bai ko ɓata lokaci ba yaja da baya, ya kuma zare takobinsa gami da karanta wasu ɗalasimai daya koya a wajen kakansa, waɗanda babban abinda suke shi ne ƙarawa takobi ƙarfi.

Amma duk da haka Kiru yana ƙara matsoshi alamun hatsarin da zuciyarsa ke nuna masa a tattare da wannan farar takobin bai daina ƙaruwa ba.

Baima ko gama karanta wannan ɗalasimai ba, alamun hatsarin da yake fuskanta daga takobin nan yakai ƙololuwa, bayanda ya fuskanci cewa wani farin haske mai kashe ido ya fara taruwa a gefen wannan farar takobin dake hannun Kiru!

Kan kace meye wannan, hasken ya ƙaru matuƙa inda yake bada alamun walƙiya-walƙiya, wanda kuma a dai-dai lokacin ne ya iso gaban Armad, inda ya kawo masa wawan sara da takobin.

Da kyar Armad ya iya kai tasa takobi ya tare saran. Wannan takubba na haɗuwa wata gagarumar ƙara ta tashi sama.

Ƙarfin saran na Armad, ya daki takobin ta Kiru, inda wannan ɗalasiman daya karanta suka fara fita daga jikin takobinsa, kamar kibiya su na bi ta cikin takobin Kiru sannan su shige jikinsa.

Wani mummunan zafi mai cike da gunji ya cika jikin Kiru, wanda acikin lokaci ƙanƙani yasa ya fara gani dishi-dishi.

Wani tari na dole yazo wuyansa, wanda yayi iya ƙoƙarinsa kada yayishi amma ina
Tarin na fitowa kuwa saiga alamun jini a jiki, wanda hakan ke nuna cewa lallai wannan ɗalasimai, sun jiwa wasu daga cikin kayan cikinsa ciwo.

To amma a dai-dai wannan lokacin shima Armad ƙarfin saran takobin Kirun ya cimmasa, wanda yabi ta jikin takobinsa sannan ya shige jikinsa a kimanin abinda bai wuce rabin daƙiƙa.

Abu na farko da yayi arba dashi shi ne, wani haske mai tsananin haskake ido, wanda yayi kama da hasken daya gani a farko wanda ke kewaye da takobin ta Kiru tun lokacin daya fara isoshi. Sai dai kuma amma wannan hasken da yake gani, yafi wancan ƙarfi sau da dama, domin yama fi kama da hasken WALKIYA.

Bayan wani ɗan lokaci da bazai iya ƙayyade shi ba sai yaga hasken ya ɓace ɓat. To amma kuma kafin ma yayi wani tunani dangane da yanayin daya samu kansa aciki, sai kawai ya fara fuskantar wata uƙuba irin ta musamman.

Shi dai yasan lallai abinda yake fuskanta yafi gaban ace masa zafi, to amma bashi da taƙamaiman kalmar da zai kira shi, saboda haka ya gayawa kansa cewa wannan lallai uƙuba-ce-irin-ta-musamman.

Babu abinda yake ji a dukkanin sashikan jikansa illa irin wannan uƙuba, wadda tasa yake ji tamkar kowanne ɓangare na jikinsa gab yake daya farfashe, ya kuma tarwatse.

Baima san lokacin daya rufe idonsa ba, saboda tsanani zafin da yake fuskanta, wanda yasa yama manta cewa a tsakiyar faɗa yake.

Can bayan wani lokaci da bazai iya ƙayyadewa ba, sai kawai yaji tamkar ruhinsa ya fara marmashewa tamkar busasshen yashi.

Yana bin iska da ƙarfin gaske, wanda hakan yasa ƙura ta fara tashi.

Dukkanin wannan abu da Armad yake fuskanta, yasan a mafarki yake jinsa, amma kuma lallai uƙubar da yake fuskanta yasan cewa a zahiri take.

Babu abinda yake juyawa acikin idonsa banda wannan abubuwa uku; WALKIYA da FASHE-FASHE da kuma ƘURA.

Yayi taga-taga, ya jada baya kamar zai faɗi, sannan bayan kimanin taku uku ya tafi ya nufi ƙas tamkar zai durƙushe akan gwiwowinsa guda biyu!

Da kyar ya samu ya ɗan iya buɗe idonsa, inda ya cake takobinsa a ƙas, ya tallafi kansa da ita, lamarinda ya taimake shi bai je ƙas ba.

Amma babu abinda ke fita daga bakinsa sai jini! Kallo ɗaya zakai masa, kasan yafi Kiru jin jiki a waccan karawar da sukai.

Da kyar ya miƙe akan ƙafafuwansa ya kuma zare takobinsa daga ƙas.

Ya ɗaga ido ya ƙara fuskantar Kiru, wanda tuni shima ya jada baya ya kuma tsaya daga ɗan nesa yana karanta abubuwan dake faruwa cikin haki, a zuciyarsa kawai yana auna ƙarfin abokin fafatawarsa ne, daga wannan haɗuwa da sukai guda ɗaya, musamman tunda gashi har tasa yayi tarin jini guda ɗaya.

To a dai-dai wannan lokaci ne, Armad ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya wajan da yake tsaye acike yake da ƙura matuƙa, domin da ƙyar ma yake hango abokin karawarsa daga nesa.

Yana cikin tunani akan mai ya jawo wannan turnuƙewar ƙurar, wadda a iya tunawowarsa baya hango lokacin da sukai bata kashin da har wannan ƙura zata tashi haka.

To amma a dai-dai wannan lokaci da yake wannan tunani ne yaji muryar Kiru, ''kayi ƙoƙari daka iya kuɓuta daga farar takobina.

''Kayi sani cewa ka shiga cikin kaɗan waɗanda suka cancanci suji bayani akan sirrin wannan takobi tawa!

''Sunan wannan takobi; Walƙiya-Tarwatsi-Ƙura!

''Da abinda kaji da kuma abinda kake gani na game da ƙura yanzu da idonka, duk zahiri ne bawai mafarki ba ne!'' Yana zuwa nan a zancansa ya ƙara taku ɗaya izuwa Armad, sannan yaci gaba da bayani, ''Duk sara guda daga jikin wannan takobi, yana tafiya ne da farin haske wanda waɗanda abin ya shafa sukan kwatanta a matsayin Walƙiya.

''Sannan kuma abinda zai biyo baya shi ne tarwatsewar abinda saran ya shafa, wanda hakan shi ne yake yin bayani ga kalmar tarwatsi dake cikin sunan.'' A dai-dai wannan lokaci ne Kiru ya ƙara ɗaukan taku ɗaya izuwa ga Armad, sannan yayi shiru, ya kuma kalli gefen Armad daga ƙasa, wanda a dai-dai lokacin ƙurar ta ɗan fara lafawa.

Armad wanda ke gabansa, zare da takobi yana karantar abokin fafatawar tasa, yana kuma sauraran mai yake cewa, shima idon nasa ya motsa inda ya kalli gefen nasa daga ƙasa.

Cikin tsananin mamaki ya jada baya, bama tare da ya sani ba, saboda abinda idonsa ya gani.

Gaba ki ɗayan shatalen gefen nasa ya rarake yayi wani mummunan rami, tamkar wanda aka haƙe da ƙarfin gaske.

To a sannan nan ne ya fuskanci cewa ƙurar na dake tashi daga wannan rarakakken rami take fitowa.

Bai ɗau lokaci ba ya gane duk abinda ke faruwa kuma ya gane abinda kalmar ƙarshe ta sunan takobin take nufi, ''wato kalmar Ƙura wadda ke nufin ƙurar dake turnuƙewa bayan abinda aka sara ya tarwatse!''

Yana cikin tunani ya ƙara jin muryar Kiru wanda a daidai lokacin ne yayi taku na uku inda ya ƙara kusantar Armad, yadda ya rage baifi kamu biyu bane a tsakaninsu ba ''nasan zuwa yanzu ka riga kasan ma'anar kalmar ƙarshe dake cikin sunan takobi na.

''Kuma kasan irin sa'ar daka taka yadda ka tsira da jikinka a haɗe.'' Yayi wata dariya ta mugunta da gefen bakinsa sannan ya cike da cewa, ''amma nasan kasan cewa sa'a bata zuwa sau biyu a lokaci ɗaya a kuma cikin tsakiyar fafatawa ɗaya!''

Armad ya kalli gefensa yaga cewa babu inda  ba'a rarakeba, inba ɓangaren da Kiru yake ba, kai hatta bayansa.

Nan take yasan cewa babu wata hanya, ta guduwa ko kuma canja waje, abu ɗaya kawai daya rage shi ne su afkawa junansu.

Yana cike da masaniyar cewa idan ya bari wannan farar takobin, ta ƙara cimmasa a irin lokacin haka, to ba lallai ya tsira da ransa ba!

Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...