Nan take abubuwa da dama, musamman hikayoyi da suka shafi wannan mutun-mutumi dake wannan waje, suka fara kai-komo acikin ranta.
Cikin tsammani ta buɗe baki da niyyar fara yi masa tambayoyi, to amma da yake shima kamar sunyi anko ne, domin babu abinda ke kai-komo a zuciyar ta, banda tambayoyin nan guda biyu; wai shin wanene wannan yaro da har ya isa ya ga mutun mutumin Daikirin, kuma daga ina ya fito?
Hakan ne yasa duk su biyun sukai anko wajan buɗe bakunan su da niyyar yiwa juna tambaya, amma a dai-dai wannan lokaci ne kwatsam babu tsammani idanun Armad suka rufe ruf, sannan babu alamar rai a tattare dashi, ya faɗi kasa da ƙarfi a sume.
Kallo ɗaya kacal zakai masa kasan yayi zazzafan suma ne irin wanda bashi da nisa sosai da mutuwa.
Cikin tsananin mamakin abinda ke faruwa da Armad tayi firgit ta matsa daga kusa dashi zuwa nesa, inda ta zauna tana haki.
Ta dubeshi cikin mamaki da firgici zuciyarta cike da tunanin maike faruwa ne, kuma mai ya kamata tayi?
To amma bata ma gama tunanin nata ba, Armad ya ɗan farka, inda ta dubeshi fuskarta cike rashin sanin mai ya kamata tayi.
To amma a wannan lokaci yana farkawa nan take ba tare da ya cika cikakkiyar daƙiƙa ba, ya ƙara faɗawa cikin suma. Sannan kuma jikinsa ya fara jijjiga.
Tana dubansa ta tabbatar da cewa lallai wannan shi ne lokaci na ƙarshe da zata yanke shawarar kota taimaki wannan yaro da bata taɓa sani ba a rayuwarta, ko kuma ta bari ya halaka!
Badan komai ba sai dan cewa wannan suma na ƙarshe da Armad yayi, ya bayyana ƙarara a fuskarsa da jikinsa cewa ruhinsa gaba ɗaya bazai iya ɗaukan wahalar wani suman ba, kuma lallai idan haka ta faru to lallai zai halaka, wato dai dukkan alamunsa sun nuna ya kai iyakacin ƙololuwar juriyarsa.
Fuskarta ta yamutse cikin tunani, kai daka ganta kasan cewa tana cikin ruɗani ne da ruhinta, akan cewa ta rasa wanne mataki ya kamata ta ɗauka.
Bayan sama da daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali, a wannan lokaci jikin Armad ya fara karkarwa irin wadda duk baiyi ba a baya.
Nan take fatar jikinsa ta fara tsufa tamkar wanda ya wuce shekaru aru-aru a ɗan wannan lokaci, kai daka ganshi kasan ya tashi daga wannan ɗan yaro mai yawan murmushi da barkwanci, zuwa wani tsohon mutum mai yawan shekaru.
''Yanzu haka zan bar doron ƙasa ba tare da kammala alƙawari na, na nemo Tirifil-fakta ba?'' Wannan ita ce tambaya ɗaya dake gilmawa acikin zuciyar Armad, yayinda yake tsaka da wannan suma nasa.
To amma a dai-dai lokacin da rayuwarsa take cikin tsananin hatsarin salwanta...
Sai kawai yaji wani abu ya shiga bakinsa.
Bama shida ƙarfin taunawa, amma jim kaɗan sai yaji ya narke a bakinsa, ya kuma wuce maƙogoronsa, inda ya zarce zuwa cikin cikinsa.
Haka na faruwa, cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗaya ba, Armad yaji wani mahaukacin ƙarfi ya bayyana acikin kwakwalwarsa inda nan take yaji lurarsa ta ƙaru matuƙa sama ma da da kafin ya fara suman.
Nan take wannan haske ya daki idanunsa inda suka buɗe tarai.
Hasken ya wuce ya daki zuciyarsa da hannayensa da ƙafafunsa da dukkan kayan jikinsa.
Kafin kace meye wannan dukkan tsufan da da jikinsa ya fara yi ya ɓace ɓat, inda fatarsa ta dawo kamar yadda take ada.
To, duba da irin halin faran-faran da barkwanci na Armad, yana farkawa ya fara murna , inda yayi dogon numfashi gami da cewa, ''hmmmmm!"Yana faɗar haka yana miƙa hannunsa na dama yana share gumi a goshinsa.
Duk da bashi da cikakkiyar masaniyar mai ya faru, amma zai iya cankar cewa wannan budurwa tana da sa hannu aciki, saboda koba komai irin wannan taimako a irin wannan waje da wuya ya faɗo daga sama.
Nan take ya fara dudduba damansa da hagu yana nemanta. Can idanunsa suka kai kanta daga ɓangaren arewa maso gabas tana zaune ta haɗa kai da gwiwa.
Dud da bai kalli fuskarta ba, amma wannan kallo ɗaya ya isa yasa yaji irin jimamin dake tashi daga zuciyarta.
Nan take sama da tunani goma sha, da wataƙila su suka faru har ya samu sauƙi, suka gifta ta cikin kansa.
Kafin kace meye wannan fuskarsa ta canja inda ya nufi inda take cikin zafin nama.
Yana isa ya durƙusa a gefenta inda daga bisani bayan ya kalli yanayin da take ciki ya yanke shawarar kada yayi magana a lokacin, wato ya ɗan jinkirta.
Nanfa ya zauna a gefenta inda bayan wani ɗan lokaci ya juyarda kansa daga ita ya sunkuyi da kansa inda nan take juyayi na tunanin meke faruwa da kuma maiya kamata yayi, suka cika masa kai.
Tun rana tana tsakiya suke zaune babu wanda yace uffan acikinsu har saida rana ta kusa faɗuwa inda a wannan lokaci ne wannan budurwa ta ɗago kai ta dubeshi, wanda a wannan lokaci zuciyarsa tuni ta gama gano masa mafi yawaicin abinda ke faruwa.
Ta numfasa gami da fara jawabi, ''Suna na Núsi Djinn.
''Mutane na na ƙabilarmu da muka rage a duk faɗin doron ƙasashe bakwai bamu da yawa.
''Kuma a wannan zamani bamu da ƙasa ta kanmu, hasalima da dama daga jama'armu basu da taƙamaiman wajen zama, sannan kuma kamar muma da muka samu muhalli muna iya ƙoƙarin mu wajen ganin cewa mun ɓoye sunan Djinn ɗin dake nasabarmu.
''Kuma saboda wannan hali da muke ciki nema muka samar da hanyoyi da dama, waɗanda indai ɗaya daga cikin mu yaga ɗan uwansa na ƙabila nan take yake ganeshi!''
Tana faɗar haka ta ɗago ido ta kalli Armad, irin kallo mai cike da ma'anar cewa; ''nasan kai ba ɗan ƙabilar Djinn ba ne, (ba Armad Djinn sunanka ba)!''
Armad dama tunda farko yasan ba Djinn ɗin bane shi, amma kamar yadda tsarin danginsa yake, bazai baƴyanawa kowa sunan gidansu ba.
Armad ya juya ya kalleta gami dayi mata yaƙe idanunsa a rufe, fuskarsa cike alamun bata haƙuri.
Bata ce masa komai ba, kawai sai ta ɗauke kai kuma taci gaba da bayani,
''Djinn ƙabila ce data bada gudunmawa ta musamman a babban yaƙi mafi girma daya faru a duniyar aljanu shekaru aru-aru tun kafin al'umma su fara rayuwa akan ƙasashen ƙasa.
Koda tazo nan a zancanta sai ta ja numfashi gami ajiyar zuciya, sannan tayi murmushi mai ɗauke da alamun zurfin tunani.'
Ta rufe jawabinta da cewa ''Wannan shi ne wani abu daga cikin labari na, manufa ta da kuma ƙudiri na aban ƙasa, wannan wani abu ne wanda bazan iya gaya maka ba!''
To haƙiƙa duk da cewa Armad yana da ƙarancin shekaru, amma ba dolo bane. Domin tun daga lokacin daya farka ya kuma ga yanayin data shiga da kuma yadda ta fara bashi labarin kanta kwatsam, yasan cewa akwai wani abu dake damunta.
Musamman yanayin yadda take bada labarin a wani yanayi irin mai kama da bankwana, ko kuma ɗebe haso.
Saboda haka duk da cewa labarin nata ya motsashi, kuma zaiso yaji menene manufarta da ƙudirinta, shin itama neman Tárifil-faktan take, ko kuma tana tare da waɗancan mutane su Gimbiya Nostalgiya, ko kuma nata ɓangaren daban yake. Amma zuciyarsa tana kan tambayar dake cikin zuciyarsa.
Inda ya numfasa idanunsa cike sanin ya kamata ya ce, ''Yaya Núsi, me ya faru ne wai?''
Bayan ɗan lokaci sai tayi murmushi, sannan ta ɗaga kai, ta dubi wannan ƙasa mai launin ja haɗe da kore a jikinta, tace, ''bamu da wani tsammani na fita daga wajen nan yanzu.''
Sannan ta ƙara wani murmushin tana cewa, ''ALLAH mai iko, ban taɓa tunanin rayuwata anan zata ƙare ba!''
Idanun Armad suka kaɗa da ruɗanin rashin fahimtar mai take faɗa, inda cikin sauri yace, ''wai me kike nufi ne? kiyimin bayani yadda zan gane!''
Comments
Post a Comment