Skip to main content

Babi na sha shida : Ido da Ido da Daikirin

''Shekara uku!!'' Armad yai ajiyar zuciya gami da ƙurawa wannan budurwa ido cikin mamaki.

''Ba zan iya yin shekara uku anan ba, saboda akwai abinda nake so nayi sauri nayi, na koma gida. Dan ALLAH yi min cikakke bayani naji abinda ke faruwa da wannan waje.''

Kallonsa kawai tayi na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta girgiza sannan ta ja dogon numfashi gami da ɗaga yatsanta na dama inda ta nuna masa filin dake gabas dasu tace, ''hanyar fita daga wannan waje tana can ɓangaren.

''Daga nan kuma zuwa wajen baifi tafiyar awa ɗaya ba.

''To amma kayi sani cewa gaba ɗaya wurin nan a zagaye yake da wani sinadari mai suna Negrinki.

''Wanda shi ne babban dalilin daya sa baka ga kowacce irin halitta anan duniyar ba.

''Kasancewar shi wannan Negrinki yana iya zuƙe ran duk wani abu mai rai.

''Kuma babban tashin hankalin shi ne iyakacin yadda ka kusance shi, iyakacin yadda zaka fuskanci ƙarfinsa.

''Mafi ƙanƙantar lokaci da aka ɗauka kafin wuce wannan mataki tsahon shekaru da dama, shi ne shekaru uku.

''Amma kaga yanzu acikin shekara ta ukun nan, a iya lissafin da nayi har yanzu ban wuce kaso sittin ba na wannan jarrawabar ba.'' Ta kalleshi kallo mai ƙunshe da tambayar, ''ko ka fuskanci girman wahalar dake gabanka?''

Armad ya gane meke ƙunshe acikin wannan kallo, saboda haka yayi mata murmushi a lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu.

Shi kansa bai san dalili ba, amma kawai sai yake jin cewa hankalinsa a kwance yake da ita, wato dai baya jin wata barazana ko kuma mugun nufi a tattare da ita.

Ya buɗe baki yai kyaran murya sannan cikin girmamawa ya ce, ''baki gaya min sunanki ba, amma idan ba matsala zan iya kiranki yaya.''

Kallonsa kawai tayi ba tare da cewa komai ba, sai dai kawai acikin idonta akwai alamu dake nuna lallai taji daɗin wannan magana da Armad ya faɗa, tamkar yana tuna mata da wani abu daya faru da ita.

Maimakon ta bashi amsa, sai tace, ''naga alamun kamar baka fahimta ba sosai yanayin da kake ciki ba.

''Ina ga muje na nuna maka ka gani da idonka.''

Tana gama magana ta miƙe gami da yi masa inkiyar ya biyo ta.

Cikin ƙanƙanin lokaci tuni Armad ya saɓa takobinsa ya na murmushi yabi ta yana cewa, ''mai yasa kike kyautata min bayan baki taɓa gani na ba.

''Kuma da wuya inma ban zame miki wahala ba.''

To amma tambayar tasa bata samu wata amsa sa ba, inda tayi kamar ma bata ji shi ba, kawai ta ƙara sauri suka ƙara dosar gabas.

Da farko Armad yayi niyyar yayi mata shiru bayanda ya karanci cewa ba mai son magana bace sosai ba, to amma shi ɗin ya kasance mai nutsuwa da kamala, amma kuma hakan bai hanashi bin diddigi ba, kuma koda bai jima da sanin mutun ba, ya kan saki jiki suyi hira sosai dashi.

A taƙaice zaka iya cewa Armad mutun ne mai saurin sabo da mutane da kuma barkwanci.

Yanayin daya ke ji a ransa na cewa babu wata mugunta a ran wannan budurwa yasa ya ƙara sakar jikinsa ya ci gaba da janta da zance, ''hmm.." yai ajiyar zuciya, "kinsan kuwa kece mutun ta farko dana fara gani mai irin launin fatata tun bayan bari na garinmu?

''Kinsan shi ne dalilin da yasa nace in kin yarda, na kiraki yaya!

Haka dai Armad yayi ta ƙoƙarin janta da hira amma ina ko ƙala bata ce masa, har dai ya gaji shima yayi shiru suka ci gaba da tafiya.

Jim kaɗan bayan Armad yayi shiru, sai abinda tun bayan farkawarsa yake ta kai komo a zuciyarsa ya ƙara faɗo masa, inda ya shiga tunani akan fasahar da yayi amfani da ita ya halaka wancan Dordor, wato 'Wilbafosiyan Siwod Dans!'

''Har yanzu acikin ƙarnika goma dake ƙunshe acikin wannan hari, na kasa kwarewa akan koda kaso goma na ƙarni guda ɗaya.

''Hasali ma aduk lokacin da nayi amfani da wannan fasaha, saina rasa inda kaina yake, sai dai kawai na buɗe ido na ganni a wata duniyar kawai.

''Gashi yanzu bama tare da Baba Zaikid, ban ma san yadda zan iya ci gaba da koyon wannan fasaha ba!

''Hmmm..'' yai ajiyar zuciya shi kaɗai acikin duniyar tunaninsa.

Can alƙawarin daya ɗauka na cewa lallai sai ya cika burin mahaifiyar sa na ganin cewa ya nemo wannan mutun da akewa laƙabi da Tirifil-fakta kuma ya gabatar dashi a gareta, ya faɗo masa.

Nan take idanunsa suka kaɗa da kafiya da kuma jajurcewa, wanda a wannan lokaci wani sabon tunani ya bayyana acikin kansa, ''na san cewa lallai duk da ban daɗe da zuwa wannan doron ƙasa ba, nasan cewa lallai a yanzu bana daga cikin jaruman gaske abin misali koda kuwa acikin sa'anni na, ina ji a jikina cewa da dama sun fini kwarewa ta kusan kowanne fanni.

''Duk da cewa a yanzu bani da masaniyar yaya wannan tafiya tawa ta nemo wannan mutun zata kasance ba, amma lallai nasan abu ɗaya; cewa a yanda nake ɗin nan bazan ko iya kare kaina daga cutarwa ba, ballantana wani abu.

''Saboda haka abinda ya zama wajibi a gareni shi ne na zama jarumi, ya zama wajibi a kaina na koyi duk wasu hanyoyi na horo da suke akwai a wannan ƙasa.

''A yayinda nake karɓar horo na sai kuma na ci gaba da bincike akan yadda zan cimma manufa ta.

''Bari muga... a doron ƙasa ta uku kowanne yawancin mutane koyarwar manyan gidaje suke bi a makarantunsu, hmm... ban sani ko nanma haka suke.

''Idan haka suke, to kawai sai na duba naga wanne gida ne yafi kama da nawa.

''Tunda ban tawo da wasu kuɗi ba, saina yi aikin ƙarfi na samu kuɗi na biya na shiga.

''Idan ma dai kuma ba wannan tsari suke bi ba, to koma dai yaya ne zanyi duk yadda zanyi, naga na cimma buri na shiga da kuma karɓar horon. Dama a gida ban taɓa samun damar shiga makarantar yaku-bayi ba, saboda haka ina ganin abu ne da zai bada ma'ana.''

Yana zuwa nan a zancen zucin da yake, wani ɗan ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa yana mai ɗokin wanne irin sabon tsari zaije ya tarar, a doron wannan ƙasa.

Yana cikin wannan hali sai yaga wannan budurwa ta tsaya cak inda shima ya tsaya gami da ƙura mata ido yana ƙoƙarin tambaya ko me yasa suka tsaya sai ta rigashi magana  da cewa, ''munzo!''

Armad ya ɗaga kai gami da ƙura ido amma a iya hangensa bai ga wani banbanci ba.

Ya kalli kudu ya kuma kalli arewa amma duk da haka baiga komai ba.

Yana niyyar ƙara yin magana ta ƙara rigashi da cewa, ''a ƙa'idar wannan waje babu wanda yake iya ganin wani, shi yasa duk da bani kaɗai na fara wannan jarrabawa ba, kuma duk da cewa dukkanin masu jarabawar a waje ɗaya suke amma babu wanda zai iya ganin wani.

''Badan komai ba saboda, duk idan wani ya wuce gaba ɗaya hijabin dake rufe hanyar na sinadarin Negrinki zai ɗauke gaba ɗaya.

''Shi yasa kowa dole ne yayi jarabawar sa a wajensa daban. Tana faɗar haka ta ɗaga hannu ta nuna masa can gabansu da ɗan yatsa, ta kuma fara tafiya gami da yi masa inkiya daya biyota.

Har sun kusa ƙarasawa sai ta ja wani dogon numfashi, sannan ta ce, ''koma daga ina kake, kuma koma taya ya kazo wannan waje bai shafe ni ba, amma kayi sani cewa fitarmu daga wannan waje nada matuƙar wahalar gaske.

''Saboda ƙarfi da taurin hijabin sinadarin Negrinki, dake gaba lallai ni kaina yafi ƙarfin na iya wuceshi a shekaru da dama masu zuwa.

''Saboda haka ina gani wannan shi ne iyakacin taimako da zanyi maka.'' A dai-dai sanda ta gama faɗar hakan sun iso wajanda suke iya hangen wani waje irin na musamman a gabansu, wanda gabaki ɗaya ya banbanta da dukkan sauran wajen da Armad ya gani tun shigowarsa.

Kallon farko da Armad yayiwa wajen yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske wanda sai da yasa ya ɗan ja baya.

Ba komai bane ya janyo haka ba illa wani mutun mutumi dake tsaye kimanin taku ɗaya bayan an shiga wajen.

Gaba ki ɗayan shashin dake gaban nasu a rine yake da launin shuɗi wanda yake garwaye da launin ja.

Kama daga ƙasar wajen zuwa sama zuwa komai dake kewayen wannan launi ne dashi, face wannan mutun-mutumi shi kaɗai.

Wanda ke riƙe da doguwar takobi a hannunsa na hagu, wadda ke a ɗage tana nuni izuwa  gabansa da ita, kai kace yana neman fafatawa ne da dukkan duniya baki ɗaya.

Sanye yake da sulke sannan kuma akwai tambarin Miyura a goshinsa wanda ke ɗauke da wani yare da Armad bai sanshi.

Gashi dai mutun-mutumi ne kawai, amma irin girman izzar da Armad yake ji tana tashi daga jikinsa yasan cewa babu wani abu dazai iya kwatanta tata dashi, kai bai ɗau lokaci bama ya tabbatarwa da kansa cewa baima kai matsayinda ko kuma kace baima cancanci ya ce zai auna buwayar wannan Izza dake tashi daga jikin wannan Mutun-mutumi ba.

Amma a dai- dai wannan lokaci da Armad ya jada baya idanunsa suka kai kan idanun mutun-mutumin inda nan take mutun-mutumin ya buɗe idonsa ya kuma kalli Armad.

Babu abinda Armad yake gani a ransa illa irin wannan kala data cika wajen dake gabansa cike acikin wannan idon.

Babu shiri yaji tsananin ruɗani da firgici acikin ransa irin wanda bai taɓa ji ba.

Kafin ƙiftawar ido da bismilla zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa idan ya ci gaba da kallon idon wannan mutun-mutumi zuwa daƙiƙu biyu masu zuwa, to lallai gabaki ɗaya jikinsa sai ya tarwatse gabaki ɗayansa.

To amma tashin hankalin shi ne tuni yake ta ƙoƙarin janye idon nasa amma abin yaƙi yiwuwa tamkar ba'a jikinsa yake ba.

A dai-dai lokacin da ya fara ɗebe haso daga rayuwa saboda tsananin firgici, a dai-dai lokacin ne wannan mutun-mutumi ya rufe idonsa, wanda hakan yasa Armad ya dawo cikin hayyacinsa.

Amma kafin kace meye wannan ya jada baya kimanin taku biyar imda ya faɗi ƙasa gami da yin aman jini.

Can bayan wani lokaci ya farfaɗo, yana buɗe ido yaga wannan budurwa tana riƙe dashi duk fuskarta cike da damuwa.

Amma tana ganin ya farka saita sakeshi, gami tambayarsa mai ya faru.

Baima tsaya tunanin wani abu ba ya gaya mata duk abinda ya gani.

Yana ambatar cewa sun haɗa ido da wannan mutun-mutumi, yaga fuskarta tayi matuƙar canjawa, wanda nan take ta cika da firgici gami da miƙewa tsaye tana kallonsa.

Bayan ƴan daƙiƙu ta fara magana aciki, idanunta cike da hargitsi, ''waye kai!!!

''Kuma daga ina kake!!!"

Comments

Most Popular

BABI NA 129-139: Zaran Gwana

 Babi na 129: Albishir Bayyanar rundunar Uznu Ururu keda wuya labari ya fantsama cikin garin Jekis. Saƙo da loko duk inda kabi mutane ne cikin tsoro suna tattauna abinda ka iya faruwa.  A layin kasuwar Zána dake yamma da fadar garin Jekis masu ciniki ne sunyi cirko-cirko suna tofa albarkacin bakinsu. "Wai da gaske ne Kwamanda Uznu Ururu ne yazo da kansa?" "Haƙiƙa shi ne, wanda ya gani da idonsa ne ya gayamin. Sannan kuma ya zoda runduna ta Mayaƙan Ururu kusan dubu ashirin." "To amma ance shi ba yaƙi yazo ba, wai kawai so yake a miƙa masa Armad angon gimbiya. Indai akai haka ba ruwansa da sauran mutanen gari." "Kai.... To amma wannan ai abu ne da sarki Bihanzin bazai yadda dashi ba. Tunda an ɗaura aure ai shima Armad ya zama jinin sarauta, duk wanda ya taɓa shi ya taɓa sarautar Sisiya." "Eh.. to. Da wannan dan wannan to amma babu wanda yake son faɗa da Mayaƙan Ururu. Kuma sunce Armad shi ne ya fara takalarsu ƴan kwanaki da suka wuce a garin D...