Skip to main content

Babi na sha biyu : Urúrú

Kwanaki huɗu bayan ɓacewar Armad bayanda yayi amfani da wannan hatasabibiyar hanya ya ceto su Zahra daga wannan baƙin ruwa da shuɗin Dordor ya harba musu. Zahra tayi shiru su na tafiya bata kuma yiwa kowa magana ba tun bayan tahowar tasu, duk da kuwa ƙoƙarin kwantar mata da hankali da Hasanu yayi tayi, kai hatta Kiru ma da ya nuna aniyarsa a fili ta so ya halaka Armad a baya, sai da ya sauko ya kuma fara lallamar Zahran yana gaya mata cewa shi dai bai gane mene ne a tsakaninsu ba, amma koma mene ne ta gane cewa, Armad ba irin mutanen da zasu mutu cikin sauƙi ba ne, ya kuma gaya mata da Armad ɗin zai iya mutu da wuri aida tuni ya rigaya ya halaka shi da farar takobinsa.

Ya gaya mata hakan ne da wasa duk da niyyar ko zata ɗan saki fuska, amma ina ko kaɗan bata ma nuna ta jishi ba, idanunta kawai na nuna nutsawa acikin tsananin tunanin wani abu ne kawai.

Tun da farko bata yarda sun baro wajan ba sai da suka kwashe awa ashirin da huɗu cir, tana kallon wajan da Armad ya ɓace.

Babu yadda Kiru bai ba akan ta gaya masa menene tsakanin ta Armad ɗin ba amma bata ce komai ba, ''ba kamar ke ba, bai dace dake ba, ki faɗa cikin wannan yanayi ba, duk ina taƙamar ki da ji da isa ta tafi kuma yau.

''Ca nake gab da zamu taho kika ƙara korar ɗan sarkin Liha ba, wanda kuma shi ne na bakwai a layin ƴaƴan sarakunan da kika ƙi.

''Ji nake ke inba Yarima Deniz Bizaya ba sai rijiya!!''

To haka irin waɗannan maganganu suka ringa fita daga bakin Kiru duk dan ya saussauta mata ƙuncin da yaga ta shiga. Wanda a gari banza ko mai zata bashi ba lallai ma taga dariya a fuskarsa ba, ballantana ma ya tsaya yana yi mata irin waɗannan maganganu.

Amma saboda ganin halin da take ciki ya yanke shawarar hakan.

To! Haka dai ya ci gaba amma ko a jikinta, inda daga ƙarshe ya gaji ya rabu da ita kurum, ya koma wajan Hasanu wanda ke kan dokinsa samfurin Kili, shima ga dukkan alamu akwai abinda ke damun zuciyar sa, domin ya natsa matuƙa a cikin tunani.

To haka dai suka tashi suka nufi hanyar Sisiya akan dawakansu, inda suka shafe kwanaki uku su na tafiya.

Kuma a wannan lokaci tafiyar data rage tsakaninsu da garinsu mai suna Sisiya, bata fi ta sati biyu ba.

Kiru wanda ke tafiya a dama da Zahra, Hasanu kuma a hagu, inda saka ta a tsakiya, yai firgit ya ɗaga kai, kana ya dubi Hasanu idanunsa cike da kokwanto.

Shima Hasanun kamar yasan abinda yake tunani ya ɗaga kai ya dubeshi.

Su na haɗa ido Hasanu bai jira wani abu ba ya fara tambayar Kiru, ''dame-dame ka lura dasu a tattare da wancan yaro waɗanda baka fahimta ba?''

Kiru yaɗan ƙifta ido kasancewar tambayar ta tabbatar masa da abinda yake zato na cewa lallai Hasanun yasan wani abu a tattare da Armad.

Saboda haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kawai ya numfasa ya fara bayani, ''na kula da abu biyu!'' Ya ɗaga ɗan-yatsansa na hagu guda ɗaya yana nuni da ɗaya.

''Na farko na lura ya iya tsaiwa akan iska,'' ya ɗan dubi Zahra kamar wanda yake jira tace wani abu, kafin daga bisani ya ƙara ɗaga yatsunsa guda biyu sama sannan ya ci gaba da bayani, ''Na biyu shi kansa bai san cewa yana da wannan Izza ba ta iya tsayawa akan iska ba, badan komai ba sai dan cewa da fari yayi ƙoƙarin miƙa hannu domin ya riƙe tsandauri dan ya kuɓuta daga faɗawa ramin kamar yadda nima nayi, inda ba daban Zahra ta riƙoshi ba to da akwai yiwuwar ya faɗa ya mutu batare da ya taɓa gano cewa yana da wannan Izza ba.''

Koda Kiru yazo nan a zancensa sai yai shiru ya kuma kalli ƙasa kamar mai jimanta wani abu, kafin can daga bisani ya ɗago kai ya ƙara fuskantar Hasanu, wanda ya taddashi yana kallonsa shima.

Bayan ɗan jira da bai wuce na daƙiƙa biyar ba, Hasanu ya numfasa ya tambaye shi, ''wannan su ne abubuwan da kafi lura dasu?'' Kiru ya kyaɗa kai alamun eh.

''Eh to! Ba komai ina ga kayi ƙoƙari, amma kamar kullum yadda nake ƙara gaya maka, yadda kake maida hankali akan horonka na takobi haka ya kamata ka ƙara maida hankali akan karatu ma, badan komai ba sai dan ka ƙarawa ƙwaƙwalka ƙarfi ita ma.''

A dai-dai wannan lokaci fuskar Hasanu ta nuna alamun muhimmancin maganar da yake yiwa Kiru da kuma sonsa da ace Kirun ya ƙara maida hankali wajan karatun da yake gaya masa.

Bayan ya kalli farar takobin Kiru na lokaci sai ya ɗauke idonsa daga kan Kirun ya kuma fuskanci gabansa inda ya fara jawabi, ''tunda farko da naga wasu abubuwa hankali na ya fara ɗugunzuma, lamarinda yasa na sa masa ido.

''Amma bani da wasu cikakkun hujjoji, wanda hakan ne yasa na ci gaba da bin abubuwan da suke faruwa tsakaninku ba tare da na shiga ba, abisa tsammanin hakan zai kaini ga gano abinda nake tunani.

''Kaga dai abu na farko... shi ne wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshinsa na musamman ne. Haske baya shugewa ta cikinsa, saboda haka indai baka fasaha ta musamman ko kuma ido na musamman baza ka iya ganin mene ne a bayansa ba.''

Kiru wanda ke sauraro ya ɗaga kai cikin mamaki ya kalli Hasanu, ''kyalle kuma??''

Hasanu ya ƙara numfasa wa sannan ya ce, ''ba kyallen bane abin daya ja hankali na sosai bama!

''Abunda kyallen ke rufe dashi. Domin ina kyautata zato, indai ba rafkanwa na samu ba, to lallai akwai irin wannan Miyura da akewa laƙabi da 'Miyura Yinfinita' ko kuma 'Miyura Madauwamiya',  wadda bata taɓa ɓacewa tun daga sanda aka haifi mutum har mutuwarsa, maimakon kwana bakwai data kowa take ta ɓace.

''Kamar yadda ka sani abu ne mai tsananin wahala ka samu irin waɗannan mutane, kai harma yafi wahala ka samu raƙumi acikin kuratandu da ka samu irin waɗannan mutane musamman ma a wannan zamani.

''Wanda har yakai kawai mutane da dama suna tunanin kawai dai labaru ne irin na hikayun gizo da ƙoƙi kurum.

''To amma mu da muka fito daga Burja, munsan cewa yana daga cikin ɗaukakar shugaba Ibasi Burja, Jinn-na-farko irin wannan Miyura.

''Abu na uku wanda shi ne mafi muhimmanci, shi ne wannan fasaha da yayi amfani da ita ta ƙarshe!!

''Har yanzu dai bazan iya cewa ina da kaso ɗari na tabbashi ba, amma lallai nafi kaso saba'in.

''Cewa na taɓa ganinta acikin wannan littafi na Jána Sisiyu.''

Tuni Kiru ya shiga cikin ruɗani da zuciyarsa saboda abubuwan duk daya ke ji, abubuwa ne da duk da baya son bincike da karatu amma yasan tarihin Ibasi Burja wanda shi ne ma ya kafa kusan gaba ɗayan daular Banfiriya, mutumin da akewa laƙabi da Jinn-na-farko, inda daga baya ma aka kafa sabuwar ƙungiya da suka sakawa sunansa.

Kuma sannan yasan littafin Jana Sisiyu!

Kuma yana da cikakkiyar masaniyar manufar maganar da Hasanu yake yi!!

Saboda haka ya shiga wannan ruɗani.

Hasanu yai kyaran murya sannan ya ƙarasa zancensa da cewa, ''to koma dai meye, yanzu abu biyu ne suka rage mana; na farko dole ne muyi sauri mu ISA Sisiya, domin mu isarda wannan babba sirri da muka gano ga Shugaba!" Ya na faɗar haka ya waiwaya gefe ya kalli Zahra, domin yasan cewa wannan sirri, yana cikin kanta, tun bayan da ta karanta zuciyar Armad ta zaƙulo shi!

"na biyu kuma," ya juyo izuwa Kiru gami da ci gaba da bayani, "zarar muka isa Sisiya, DOLE NE ASAKA MANYA-MANYAN MA'ABOTA IZZA SU BAZAMA SU NEMO WANNAN YARO MAI SUNA ARMAD, duk inda yake a duniya, ko shi ko gawarsa!!''

To a dai-dai lokacin da suka kammala tattaunawar tasu kuma suka dubi gabas, Zahra wadda kwanaki huɗu kenan cir bata ce komai ba tun bayan sanda ta kira sunan Armad, ta buɗi baki, kanta a sunkuye tayadda baza a iya tantancewa ko hawaye take ko kuma ba hawaye take ba, ta furta wata kalma guda ɗaya.

''Shi ne!!''

Cikin mamaki duk su biyun sukai saurin juyawa izuwa gareta bakinsu a buɗe, kai daka gani kasan cewa magana ce mai yawa a bakinsu.

Amma duk su biyun babu wanda ya iya furta wani abu bayanda suka ga yanayin ɗimuwa dake fuskar Zahran, lallai sun san cewa yi mata magana a dai-dai wannan lokaci bashi ba ne mafi kyawun abinda zasuyi ba.

Saboda haka suka haɗiye abinda ke ransu suka ci gaba da tafiya ba tareda kowa yace ƙala ba.

A haka su na tafiya su na yada zango, saffa-saffa har suka ƙara cinye wata tafiyar ta kwana uku.

To a wannan rana su na tafiya suka iso cikin wasu manyan duwatsu masu yawan gaske, sannan kuma ga girma ta yadda kana gani kasan cikinsu zaiyi daɗin fakewa akai harin sunƙuru.

Koda zuwansu nan, sai Hasanu ya bada umarnin su kwana anan in yaso da sanyin asuba, saisu shiga cikin duwatsun ido na ganin ido.

Haka kuwa sukai, inda suka kafa tanti sannan suka kwana, asubahin fari suka ɗaura ɗamara suka shiga cikin wannan duwatsu.

Abu na farko da suka fara arba dashi shi ne sauyin yanayi, inda su na taka ƙafa ciki ɗan hasken daya fara fitowa na asuba suka ga ya dusashe nan take, wani duhu na musamman ya maye gurbinsa.

Sannan kuma suka fara jin wata iska mai sanyin gaske tana dukan fuskarsu.

Kafin zuƙatansu su gama ankarewa da wannan sabon muhalli suka fuskanci wani sabon firgici.

Inda suka fara jin wata kakkausar murya daga cikin dajin duwatsun na tasowa, ''kwamanda na biyar na rundunar tsakiya daga Burja, Hasanu!

''Ance yiwa ɓarawo sata bashi ce.

''Ba komai nake magana ba illa AYRID mai mataki na shida dake hannunka!!

''Ku bamu ku tsira da ranku, ku hanamu, mu kasheku sannan kuma mu ɗauka da ƙarfin tsiya.''
***
Ururu

A tsohon yaren Aldúrish, kalmar Urú tana da ma'ana biyu; ta farko tana nufin baƙin abu, yawanci ana amfani da ita ne, a abinda yake da alaƙa da jikin ɗan adam, sai kuma ma'ana ta biyu, wato adalin shugaba (yawanci mara dukiya da yawa.)

Shekaru aru-aru da suka gabata (Before Amri, B.A), al'ummar wata tsohuwar ƙabila wadda babu wanda yasan asalinta a dukkan wannan zamani suka bayyana da wani abu sabo.

Wanda ba'a saba gani ba; wato gabaki ɗayan idanuwansu baƙaƙe ne, baƙi ƙirin, babu ko alamar fari acikinsa.

Saboda haka, sai mutanen wannan zamani suka fara kiransu da suna Uru.

To amma, ga dukkan alamu wannan suna baiyi musu daɗi ba, saboda a cewarsu, lallai akwai ƙololuwar rashin kyautawa a ringa kiransu da kalmar da zata iya ɗaukan ma'anar sarki adali mara dukiya. Acewarsu wannan zagi ne ga buwayarsu da ƙarfin mulkinsu aban ƙasa.

Saboda haka, ba jimawa aka maida wannan suna ya koma Urúrú, wato aka ƙara 'rú' a ƙarshe. Wanda ma'anar sunan ta baƙaƙen idanu amma na manyan sarakunan aljanu masu ƙololuwar girman kai waɗanda suka taɓa mulkar duniya, waɗanda kuma aka ce saboda tsananin girman kansu aka shafesu daga ban ƙasa. Domin kalmar 'Rú', indai anyi amfani da ita, to ana nuni da waɗancan aljanu ne.

Wannan ƙabila sun daɗe suna mulkar bil-adama, babu zamani da yazo da bai tafi dasu ba, hasalima a dukkan littafan tarihi saika gansu, wanda hakan yasa mutanen wannan zamani da dama suke tunani kodai dama wannan duniyar tasu ce su kaɗai.

Sunga jiya, sunga yau, kuma ga dukkan alamu babu abinda ya isa ya hana suga gobe.

Su suka ƙirƙiro da Amri, kuma su suke da yaren Aldurish, sannan kuma su suke tsarawa dukkan mazauna ƙasa bakwai tsarin rayuwarsu, a wata hanya da suke cewa Rukunan Urúrú!

Sudai waɗannan Rukunai, guda uku ne asali, amma daga baya saboda wani dalili da ba'asan ko menene ba, suka goge Rukuni na uku, ya dawo saura rukunai biyu kawai.

Rukuni na farko, shi suke kira da Jinzidal! Yana magana ne akan yadda mutane zasu yi rayuwarsu, cewa dukkan mutane sai sun zama iri biyu.

Kaso na farko sai sun zama Bayi, wato su aikinsu bauta kawai!

Na biyu kuma su ake kira da Béligi, waɗanda su kuma aikinsu yaƙi.

A ƙarƙashin wannan tsari, duk shekarar duniya sai anci gagarumar kasuwar cinikin bayi, wadda akeyinta a bisa tsarin da ake kira da suna Jinzidal.
***
Jinzidal shashi ne mai zaman kansa acikin wannan littafi, wamda za'a zo kansa na bada daɗewa ba. Inda zaku ji yadda Ururu suka ɗaurewa cinikin bayi gindi.
***
Shi kuwa rukuni na biyu, shi ake kira da Izza Ristirikta!

A ƙarƙashin wannan tsari, dukkan wani ɗan adam dake rayuwa abisa doron ƙasa bakwai, idan ka cire ƴan ƙabilar Ururu, saiya karbi jarrabawar daga Ururu, idan dai yana so ya haura daga matakin Izza na ɗari zuwa sama.

Haka daga na ɗari biyu zuwa sama, haka haka, wato duk bayan shekaru ɗari na Izza, sai ka karɓi wannan jarrabawar kafin ka wuce gaba.

Wannan jarrabawar ba wani abu bane illa, Ruwan wuta da za'a saukar maka daga doron ƙasa ta farko kai kaɗai.

Idan ka wuce shi ka rayu, to kaci wannan jarrabawa, amma idan ka mutu shikenan.

Kuma duk bayan mataki ɗaya, wahalar daɗa ƙaruwa take. Wanda hakan nema yasa kaɗan ne suke iya ci gaba da ƙarawa Izzarsu yawa zuwa wani mataki, indai kai baɗan ƙabilar Ururu bane.

A ƙarƙashin wannan Rukuni akwai abubuwa da dama, waɗanda Ururu ke amfani dasu wajen tabbatarda cewa babu wani mahaluƙi daya kuɓucewa wannan jarrabawa.

Wannan abubuwa za'aji su anan gaba kaɗan.
***
Wannan shi ne kaɗan daga cikin girman iko da Ururu ke dashi a ban ƙasa a wannan zamani.

To wannan sirrin dai da Armad yaji a wajen su gimbiya Nostalgiya, yana da alaƙa da rukuni na farko, wato Rukunin Jinzidal (cinikin bayi), dama kuma wani ɓangare na Rukunin Izza Ristirikta.

Sabida haka, ko'a wannan lokaci da iska tayi cilli dashi zuwa wata duniyar, kafin hankalinsa ya gushe abinda ya fara faɗo masa kenan.

Lallai yasan cewa akwai babban tashin hankali, koma kuma mummunan yaƙi dake gabatowa indai aka aiwatar abinda yaji.

To amma mai ya kamata yayi? Wannan ita ce tambayar daya kasa bawa kansa amsa.

Comments

Most Popular

398-403

 Yayi taku ɗaya lamarin da yasa kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Ƙarfin gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Tun daga nesa babu abinda zaka gani sai ƙuwa da kururuwa da wannan kawanyoyi suke. Dukkan ilahirin iskar dake wajen ta ɗau zafi. Kamar masifar bata isa haka ba, Han'Amuru ya ƙara wani takun, nan take kowacce ƙawanya ta ƙara rabewa. Gudun da suke ya ƙara ƙaruwa. Iskar wajen ta ƙara ɗaukan zafi. A haka saida Han'Amuru yayi taku hudu sannan ya tsaya ya nuna ƙaraiƙisu da hannayensa guda biyu. Dukkan kawanyoyin su kayi fitar burtu suka daki ƙirjin ƙaraiƙisu wanda baiyi ƙoƙarin kauce musu ba. Ƙara da rugugi sukai sama, baka ganin komai sai ƙura. Amma duk da haka bayan ƙura ta lafa sai ga ƙaraiƙisu ya bayyana fata sumil kamar ta jariri.  "Ƙarya ne," Inji Han'Amuru baki yana kumfa. "Babu yadda za'ai ka rayu babu ko kwarzane bayan ka karɓi wannan harin. Yana magana yana ƙara aikawa ƙaraiƙisu hari. A jere a jere sai da hari sama da talatin na kawanyoyin wuta suka sa...